DA MA NI CE CHAPTER 2 BY JAMILA UMAR TANKO
Malaika ta yi murmushi ta ce, “sunana
Malaika Shamaki. Ke fa, yaya sunanki?”
Ta kalle ta, amma bata yi mamaki da yawaba kasancewarta ‘yar jarida wataqila ko ta santa a talabijin ne.
Budurwar ta yi murmushi fararen hakoranta suka bayyana,yar siririyar wushiryarta ta haska ganin Malaika, ya yin da gefen kuncinta dukka biyu suka lo6a (beautiful points), Kamshin cigam din _bakintamai kamshin minti ya buso cikin hancin Malaika.
« Sunana Nasrin Abdul-Nasir.” Malaika ta zabura ta ce,cancandi! Sunan ma irin na ku na ‘yan gayu. Kina aiki anan ne? Ko mahaifiyarki ce naga ta wuce yanzu? Dan kuna kama wallahi.”
Tabbas Nasrin ta ga rashin kamata a wadannan tambayoyi amma ta daure kasancewar ta san darajar dan Adam, bata wulakanci.
Sai Nasrin ta yi murmushin karfin hali ta girgiza kai ta ce, *aiki na zo yi daga NTA talabijin Abuja, ni’
‘yar jarida ce, zan yi hira da
wannan bakuwar ne da kike fada.
“Ita wacece a kasar nan? Ta yi kama da
Minista ilimi.” In ji Malaika.
Nasrin ta yi dariya ta ce, “ministan ilimi ai namiji ne. Wannan babar likita ce, ‘yar
Nigeriya ce amma a Amerika ta fi zama. Me kike nema ne?”Malaika ta yi murmushi ta ce, “Yarona sikila ne jiya ba mu bacci ba, ki rokar min ita ta duba shi, ke kuma ki dauke mu a jarida ki yadawa duniya ko za’ a bamu taimakon kudi in kai shi turai, na ji an ce ana zuke jininsu a zuba wani saisu warke gaba daya.”
Dariya ta subucewa Nasrin ba tare da ta yi shirin yinta ba. Ta dafa kafadar Malaika ta ce “kawata, ki je wajen likita ya duba shi wannan bakuwa ba mararsa lafiya ta zo dubawa ba. Ta zo ne akan binciken makasudin barkewar cutar sakarau data bulla a wasu wurarena garin nan.Daga America aka turo ta.Malaika ta ji dadin da ba zai masultu ba, yau ‘yar gayu ta dafa kafadarta. Sai ta washe baki ta ce,cafdijam! Ashe
babba ce sosai, likitan likitoci za kice min. ki yi min hanya in ganta mana.”
Nasrin ta fara fahimtar cewa bada me cikakken hankali take tsaye ba, sai ta girgiza kai ta fara tafiya.
Malaika ta zabura ta rike hannunta ta ce,
“yake ma’abociya kyau da ilimi! Ki saurare ni mana, ki fahimci in da na sa gaba. Ki yi hira da ni a nuna ni a talabijia nima, dan duniya ta
san mu talawa muna shan wuya.
Dariya ta kwacewa Nasrin ta kama haba ta fada a bayyane cikin mamaki “ikon Allah, Allah mai halitta kala-kala. Ke kuma hira kike so ayi da ke duniya ta ganki. “Dai-dai lokacin wasu maza biyu suka tunkaro su dauke da manyan kyamarori, Usman da Ishak, da alama abokan aikin Nasrin ne. Su ma suka ja suka tsaya a in da suka ga Nasrin, suna tambayarta meyasa ta tsaya anan?
Nasrin ta yi dariya ta ce, “kawa nayi yanzun nan tana so ayi hira da ita, danta yana da sikila. Usman ya girgiza kai, yace dama da masu sikila
za muyi hira ba da masu sankarau ne ba.”
Ishak yace, “ai duk ciwo ne za mu iya hira da ita mana.”Nasrin ta ce, “hakika mun yi babban kamu dan wannan matar zata iya magana sosai, na ji muryarta da zaki kamar ganga. Hajiya Malaika kin iya turanci?”
Malaika ta yi dariya ta gyada kai ta ce,
“zan iya, irin na mu na Hausa dai.” Gaba daya suka tuntsire da dariya.
Nasrin ta dafa kafadarta ta ce, “ki jira ni to in shiga in gama hira da Dr. Hala Hamma Yaro. Dan kada ta tafi kin ga takanas dan ita muka zo Kano.”
Malaika ta yi musu jinjina da hannu, ta yi dariya ta ce, “Allah Ya tsare min ke. Sai kun fito, ki gaishe min da ita sosai.”
Nasrin da abokan aikinta suka tura kofar ofishin suka shiga gami da yin sallama Fiye da mintina talatin basu fito ba Malaika kuwa na nan a tsaye akan baranda bata tafi ba, haka ta ma manta da abinda ya kawo ta asibitin. Da ta ji shirun ya yi yawa sai ta tura kofa ta shiga ofishin kanta tsaye, tana tafe tana sanda har ta isa wajen wata kujera, Likitoci biyu su na ta yi mata nuni da hannu ta koma amma ta ki, babu wanda ya yi magana saboda an dora kyamara akan Dr. Hala tana bayani, yayin da Nasrin na kusa da ita tana mata tambayoyi.
Malaika ta sami waje ta zauna bata damu da hararrar da likitocin nan suke yi mata ba.
Ta na zama danta yace bai san zance ba, ya fara yunkurin kuka, nan da nan ta sauke shi ta kafa masa nono a baki. Ita fa a dole sai ta ga kwakwaf.
Tana kallonsu tana murmushi abinda take gani a talabijin yau gashi a fili.
•Da aka kammala hira da Likita kafin a rufe kyamara Nasrin ta taso da sauri ta ce da su
Usman masu dauka su juyo su dauki hirarta da Malaika. Har za su yi mata musu, Nasrin ta ce su dauka kawai zata fada musu dalili idan an gama.
Hmmm