DA MA NI CE CHAPTER 3 BY JAMILA UMAR TANKO

Malaika aka gyara riga da mayafi aka juyo da fuskar tamushashshan jaririnta ana murmushi.

Dr. Hala ta gyara gilashi ta zubawa

Malaika ido tana kallo cike da mamakin yadda ta shigo ofishin ba da izini. Sai taga kamar da akwai alamar sanayya a tsakaninta da ‘yan jaridar, dan haka ta rage mamakin.

Turancin dai ba laifi, ta yi kokari ta yi bayanai akan ciwon danta, ta Kara bayanai akan gwamnati ta shigo cikita taimaka.

Da aka gama sai Dr. Hala ta kira Malaika kusa da ita, tana mata tambayoyi akan ciwon danta cikin rada.

Gami da karbar dan ta

dudduba shi, ta bata shawarwari.

Malaika fa ba sauraron abinda Likita take fadaba take, sarka, dan kunne da zobunan lu’u lu’u (Diamond) din jikin Dr. Hala kawai take kallo, har da bude baki, suna ta walwali suna haske saboda kyau. Da likita ta gama bayani sai Malaika ta nemi data bata lambar wayarta.

Likita ta girgiza kai ta ce bata da takamaimiyar lambar waya guda daya,kullum canja layi take yi.

Malaika bata ji dadi ba, ta tashi ta goya danta ta Karasa wajen Nasrin, wacce ke zaune tana ta rubuce-rubuce akan tebur,Malaika ta tambaye ta lambar wayarta, Nasrin ta yi ta hanya-hanya bata so ta bayar amma da ta ga Malaika ta dage har ta fito da kujajjiyar wayarta zata dauki lamba sai Nasrin ta bata, burin ta kawai Malaika ta kara gaba dan ta bar su, su yi aikinsu. Farin ciki ya cikawa Malaika Kalbi, ta tafi tana godiya.

Har ta jima da fita sai gata ta dawo, daya daga cikin manyan likitocin daya jima yana jin haushinta sai yanzu ya sami damar more bakinsa. Dr. Gumel ya yi mata tsawa gami da balbale ta da fada har da kunfar baki.

Dr.Gumel ya ce,

“Malama! Kina damunmu mu na aiki sai shige da fice kike yi.

Wai shin waya baki izinin shige da fice a cikin ofishin nan?”

Malaika ta fusata ta harare shi, ta yi gatsine ta ce, “Malam, ba wajenka na zo ba, manyan ma basu yi min magana ba, ‘yan kasar waje wadanda Amerika da Obama su ka san da su, sai kai da kake tare da ni a Kano.”

Gaba daya aka yi carko-carko ana kallon

Malaika. Tabbas bata san da wa take magana ba, da ta san ko shi waye ba zata fada masa haka ba. Dr. Gumel likitan da ake ji da shine a kasar nan ta fanni dashen koda.

Sai ya kasa magana ya ci ganba da karatun jarida.

Nasrin ta ji kamar ta barke da kuka dan

Malaika ta dame ta, ta fada cikin shagwaba da takaici, “Malaika me zan yi miki kuma?”

Malaika ta washe baki tayi dariya ta ce, «yaushe za°a saka hirar da muka yi? Dan in gani, kuma awacce tasha za’a nuna?”

Nasrin ta ce,”tunda kina da lambar wayata za mu yi magana a waya.

Malaika ta gyada kai ta ce, “zan kira ki idan na fitazan saka katin Naira dari biyu dan mu dade muna hira. kin ji kawata.”

Malaika ta juya ta nufi kofar fita, har ta isa bakin kofa ta juyo ta harari Dr. Gumel ta ce “dan bakin ciki sai ya mutu, Allah ne Ya hada ni da hadaddun ‘yan gayu babu mai raba mu.”

Sai kowa ya bude baki yana kallonta cike da takaici, Usman ya zabura zai yi mata magana, Dr. Gumel ya yi masa nuni da hannu, alamar ya yi shiru ya kyale ta. Bayan ta fita suka tuntsire da dariya gaba dayansu, sun yi Amanna tana da tabin hankali, dan haka sun yi mata uzuri.

MALAIKA SHAMAKI

Sai yanzu Malaika ta tuna abinda ya kawo ta asibiti, rashin lafiyar danta. Ta dauko katinta daga jaka ta tafi da sauri tana ta salati, tabbas ta san ta makara dan karfe takwas ake gama karbar Katina, gashi yanzu karfe goma daidai. Tana isa ta iske dandazon mata suna tsaye a layi, wajen babu masakar tsinke.

Dakyar ta kutsa ta cusa kai cikin ofishin duk da tarin da mata na kan layi suke yi mata bata kula su ba. Ma’aikaciyar jinya (Nurse) ta tare ta da sauri ta tambaye ta, ina zata je? Sai Malaika ta mika mata katinta wai a taimaka mata. Ma’aikaciyar jinya ta harare ta sama da kasa ta watsar, gami da yi mata tsawa ta ce,”Sannu isasshiya, sannu shafaffiya da mai, sai yanzu za ki zo? To an rufe karbar kati sai gobe, idan goben ma baki zo da wuri ba sai wani satin.”

Malaika ta harare ta, kama kugu ta murguda baki ta ce, “Toh mai gadin kofa ke ba likita ba kin fi likita zakewa. Da irinku ne likitoci da karasa marar lafiya za ku yi saboda babu imani da tausayi.”

Wata mata dake kan layi ta zabura ta dafa kafadar Malaika ta ce,haba baiwar

Allah! Yaya zaki dinga zagin mata akan aikinta?”

Malaika ta juyo ta sauke kwandon masifa akan matar da ta yi magana. Nan da nan waje ya hargitse aka dinga hayaniya, gaba daya Malaika aka bawa rashin gaskiya sai kadan ne suka bi bayan Malaika, su ma irin matsalarsu daya da ita sun zo a makare anki karbar katinsu.

Malaika ta hada hayaniya har likitocin da kansu suka firfito suna bada hakuri.Daga

Hmmm

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE