DA MA NI CE CHAPTER 5 BY JAMILA UMAR TANKO

dawo ba. Ba dai a wajen masu kudin kika zauna ba.

Malaika ta fada cikin gadara da tsiwa

“kamar ka sani kuwa acan na bata lokaci. Allah ma Yayi mana yatsu wani ya fi wani girma dan mu san ba daidai kowa ya ke ba, wani ya fi wani. Dan haka dan na rabi mai kudi dan in sami danshin inuwa ban yi laifi ba.’

Shamaki ya damke hannu yayi tamkar zai kai mata naushi, sai ya fasa saboda tsantsar takaici. Ya rasa amsar da zai bata, kwalla ta cika masa ido ya yi tsaye yana hangenta tana zaune a falo, ta dora kafa daya kan daya tana girgizawa.

Yace “Malaika! ki je ki nemo maganin jahilci dan wanna ciwon yana damunki. Sau biyu ina sayo miki Form din makarantar matan aure sakandire ta yaqi da jahilci kin ki shiga.

Na siyo miki na islamiyya kin ki zuwa. Kin gwammace kina ta yawo a gari kina kallon masu ilmi kina sha’awa.”

Ta murguda baki ta ce, “ka je ka nemo maganin talauci dan talauci na damunka kai kuma.” Yace “na godewa Allah a yadda ya barni dan na fi wasu, da yawa a jikina suke cin abinci. Ko a haka na dauwama Allah Ya yi min komai da Ya bani imanin sanin Sa da yarda dakaddara. A koda yaushe bakya taba kallon na kasa da ke sai wadanda suka fi ki dan haka ba zaki taba godewa Allah ba. Kin fi wasu, wasu kuma sun fiki.”

Ta ce “ko a layin nan ma kowa ya fi mu.

•Yanzu baka jiyo Karar Jannareto a gidan Alh.

Ayuba ba? Toda shi suke kwana da shi suke yini mu kuwa fa ko injin ba mu da shi. Gidan haya daki biyu kanana.””Auzubillahi minal shaidanir Rahim.

Innalillahi wa’ inna ilaihi raju un. Allah Ya sa ki gane.” Shamaki ya fada a lokacin da ya yi baranda ya mika wuya a gaban mahalaccinsa, dan abin na ta ya shallake tunanin mai hankali.

Malaika ta murguda baki ta ce, “a kanka, dan ni ba shaidan ba ce.”

Shamaki ya fada cikin sanyin jiki “zo kiyiwa Kasim tsarki, ga ruwan wanka nan na dora kiyi musu. Ni zan Karasa dafa abincin.” Malaika ta girgiza kai ta ce,

“wallahi a gajiye na dawo ga yunwa bazan iya ba, ai na sha cewa ka dauko min masu aiki ka ki. Ni ba baiwa bace, gidan kowa da masu aiki.”

Yace “Sai dai in auro mai kular min da yara tunda kin gaza.”

Ta zabura ta dire Ahmad a kasa akan leda a fusace,

“garakayi auren ma da ka

taimaka min dan kana yin aure fitazan yi. Haka kawai da me zanji da talaucin ko da fada da kishiya?”

Shamaki ya shiga kicin da sauri ya gyara murfi a tukunyar da take bori, ya fito da sauri ya dauko Kasim akan fo zai je bandaki yayi masa tsarki, yayin da Aliyu ya calla ihu ya yar da tabarya ya rike ido barkono ya fallatso masa a ido. Yara ukun gaba daya kuka suke yi.

Shamaki ya zama kamar zautacce yayi nan da gudu ya lallashi wanna ya dawo ya lallashi wancan.

Malaika na zaune tana ta kiran lambar wayar Nasrin bata dauka ba, sai sake kira take, gami da tura sakonni tana mai gabatar da kanta dan ta gane mai kira, duk da haka bata amsa ba alhali kuma wayar tana shiga. Ranta idan ya yi dubu ya baci, ta rasa in da zata saka ranta.

BAYAN KWANAKI UKU…. KANO

Da dare misalin karfe takwas da rabi shamaki da matarsa

Malaika suna zaune a falo, yana

karatatun jarabawa yayin da ita kuma take cin soyayyen kifi tana kallon talabijin, yara sun yi bacci.

Wayarta ce a caji take ta dau Kara, da gangan ta ki ta dauka dan ko tantama babu ta san Saude mai siyar da atamfofi ceke kira, dan wata ya kare bata biya bashin da ta dauka ba.

Shamaki ya kalle ta, ya juya ya kalli wayar, ya sake juyawa ya kalli matarsa.

Malaika ta sha kunu ta ce, “Saude ce mai kayan siyarwa, ban biyata bashin dana dauka ba dan kudin da ka bani na kashe sai wani watan zan biya.

Hmm

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE