DA MA NI CE CHAPTER 6 BY JAMILA UMAR TANKO
Ya dauko wayar ya duba sunan ya karanta sunan mai kiran a bayyane “Nasrin Abdul Nasrin.
Bai rufe bakinsa ba ta zabura ta kwace wayar ta mike tsaye a gigice har da dukawa sannan ta danna.
“Lah kawata, Nasrin kece?”
Nasrin ta yi murmushi ta ce, “Kawata Malaika nice. Yi hakuri na ga sakonninki mu na ta aiki dare da rana sai yau da rana na dawo Abuja.
Na kira in shaida miki yau za’a saka hirarmu da ke a labaran NTA na karfe tara, na fada miki ne dan ki gani.”
•Malaika ta dinga tsalle tana mura tana godiya. Nasrin ta kashe waya, yayin da Shamaki ya rasa abinda su ke nuf, sai da ta wayar masa. da kai sannan ya fahita. Amma a zatonsa tatsuniya take ba gaskiya ba ne dan haka bai ce da ita komai ba, sai da aka fara labarai ya ga matarsa. tsumu-tsumo cikin tsumma tana bayanai ga kyamusasshon dansa akan cinyarta yana kyallara ido sannan ya tabbatar da gaske take. Sai ya fara salati yana hada ta da Allah ya isa, ta cuce shi.
Bakinta baya mutuwa kuwa, sai kare kanta take har ma tana shaida masa in ya ga dama ya sake ta ta koma aikin jarida. Kan kace kwabo jama°a da dama sun ganta ana ta kiransu a waya ana sanar da su an ga Malaika.
Murna take tana darwa, ana ta taya ta murna.
Yayin da shima ‘yan uwa da abokai suke kiransa suna neman Karin bayani, ya ma kashe wayarsa dan takaici.
Suka yi ta musanyan yawu shi da ita, kai kace wuta zata fito daga bakunansu su Kona junanansu. Sai dif aka dauke wuta ma,amma a haka cikin duhu suka ci gaba da yagar juna.
Yau sai da ya ji a ransa da zai iya sakinta da ba zata kwana a gidansa ba, to Allah Ya hada shi da wani masifaffan ciwo wai shi So.
Yana sonta a ransa, da kuma babu yadda zai yi da yara idan ta tafi ta barshi da su, mahaifiyarsa ta tsufa babu mai rike masa su.
Ga aiki ga karatu ba zai iya zama da su ba da sai ya raine su har su girma.
Ya ga da gaske Malaika hada kaya take zata tafi gidansu, ya shiga lallashi yana bata baki akan shi baice zai sake ta ba amma bata kyauta masaba ne, tamkar bara take tana neman taimako alhali shi kuma bai gaza ba.
Gashi yanzu ta jawo masa gori a wajen abokai, wadanda basu santa ba zasu ga sunansa radau an rubuta kowa ya san matarsa ce.
Ta ce ita kawai ta gaji da zaman ne kawai gara ta tafi, yanzu gashi ko gama nunawa ba’ayi ba aka dauke wuta, basu da injin da zasu kunna su ga haske. Sai da ya yi mata alkawarin Janareto wani watan, sannan ta hakura ta fasa tafiya.
Yana kwance yana hawaye cikin dare ya ma kasa karatun jarabarwar da yake da ita gobe da sassafe.
Asuba ta gari!
ABUJA
Кarfe hudu da rabi na yamma, Nasrin ta jawo wayarta cike da sanyin jiki ta kira
wannan lamba mai matukar muhimmanci a wajenta. Bayan tsawon watanni biyu cur tana kiran lambar bata cin sa’a dan ba’a dauka kuma tana shiga, sai yau aka amsa mata. Ta ji farin ciki tamkar an jefa ta a gidan aljanna dan murna. Cikin zumudi ta yi salama, sautin wata kamilalliyar murya ce ta daki kunnenta.
Ta gaishe shi cikin ladabi, ya amsa cikin mutuntawa gami da ambaton sunanta ‘Nasrin’.
Ta tambaya cike da mamaki “Dr.Jalo, daman kana da lambata amma na sha kira baka. dauka?”
Jalo ya yi sanyayyiyar dariya, yace, “tun ranar da mukayi musanyan lamba na ajiye ta da sunanki a wayata, amma ban cika amsa wayaba ne, ban ma cika bude wayar ba ma a rufe take yawanci.”
Ta lumshe ido ta ce,sannu da
kokari.Aiki ya yi maka yawa ko? Kana wanne gari ne?”
Bai amsa mata ba sai ya yi shiru, nan da nan ta canja tambaya ta ga alamar ba shi da niyyar amsa mata.
Ta lumshe ido, ta ce, “rubuce-rubucenka suna birge ni ina so in shahara in kware in zama kamar ka a harkar rubutu.”
Ya yi murmushi yace, “ko? Allah Ya sa ki fi ni ma.
Ta kyalkyale da dariya ta ce, anya
kuwa? Ban isa in kamo kaba ma, ranka ya dade.
Ya yi sauri ya katse hirar yace, “to na ji dadi da kiran da kika yi min kuma na gode Allah Ya bar zumunci. Sai mun yi magana wani lokacin.
Bai jira amsarta ba ya katse waya, yayin da Nasrin ta sankare a zaune nanike da waya a jikin kunnuwanta.Can da aka jima ta ajiye wayar cikin sanyin jiki, hakika ta ji ba dadi a
Hmmm