DA MA NI CE CHAPTER 8 BY JAMILA UMAR TANKO
Anty Zainab ta ce,”Dinah! kin sami
ladan Kawarki da kika fito da ita daga daki, tun
• da la’asar ta rufe kanta taqi ta fito gashi ni kadai Ogana bai dawo ba sai sha dayan dare.”
Dinah da Nasrin suka yi dariya.
Dinah ta ce, “na ga alama bincikenwani abu aka bata a wajen aiki.
Nasrin ta ce, “kada ki damu bari in raka :ta in dawo. Anti Zainaba kin ji?”
Suka isa wajen • dankareriyar motar,
‘Adam yana ciki a zaune, bayan ya rage gilashi wundo sai suka gaisa da Nasrin, kowannensu cike da fara’a.
•Nasrin ta yi dariya ta ce, “kuna son junanku kullum Kuna tare a gida da ofis. Wai me zai hana ayi bikin nan a cikin. shekarar nan daga mun gama bautar kasa.”
Adam da Dinah suka kwashe da dariya, da alama Nasrin ta soso musu in da yake yi musu kaikayi. Sai suka kalli juna daman kamar tayi duba shawarar da suke yi kenan.
Adamyace, “kamar kina duba yanzu fa maganar da muka gama kenan, amma tare da aurenku ke da Fu’ad za’a hada. Nasrin ta yi dariya ta ce,
“sai ya koyi zaman Nigeria sannan za mu yi aure.”
Adam ya ce, “wallahi Engineer Fu’ad ya fi ki son zaman kasar nan amma ana bukatarsa a Embassy Amerika, shiyasa kullum yake bisa hanya, shi yake taimakawa Daddy da aiki. To ke meye damuwarki tunda kin kusa gama bautar kasarki ba sai ku yi zamanku a can ba?”
Nasrin ta tabe baki ta ce, “Ba na son zaman Amerika,a tattakure na daure na yi shekaru ukun nan inagama karatu na garzayo gida, ni fa babu kasar da na fi son zama irin kasata Nageria.”
Dinah ta yi murmushi ta ce, “uwar iya yi, Engr. Fu’ad yana hakuri da ke komai sai kinyi iya yi.
Nasrin ta harare ta ce, “au daman har na kai ki iya yi?”
Adam ya yi dariya yace, “za kú zo daya.
dai, ai daman kawaye ne.
Kawai dai
Engr.Fu’ad ya fi ni hakuri ne shiyasa ni ba’ayi min kwainane da yawa.” Su kayi dariya su dukka, ya ja mota su ka tafi. Nasrin tana daga musu hannu har suka fita daga get din gidan.
Nasrin ta dawo gida cike da fara’ a ta iske
Yayarta Zainab har yanzu kallo take yi ita kadai.
Ta fara bawa Zainab labarin yadda suka yi da Dinah cewar sun kusa yin aure, Adam ya ce a hada bikinta da fu’ ad. Zainab ta yi farin ciki da jin haka ta yi mata fatan Allah Ya sa ayi cikin shekarar nan ta . Nasrin ta tabe baki ta ce, “ba Amin ba, sai Fu’ad yagama yawon kasar wajen ya dawo gida ya zauna tukunna in za’ayi ayi, dan ni ba zan yi aure a turai ba rayuwar ba dadi.”
Zainab ta harare ta ta ce, “iyayenki suna can kina cewa ba zaki zauna a kasar ba, ke ai gida ne.”
Nasrin ta ce,
“na fi sha’awar kasata
Nijeriya.
Ta tashi ta shiga daki tana tafe tana girgiza ko ba komai ta san ta bada haushi haka kuwa aka yi Zainab ta bita da harara. Nasrin ta dafe kai ta ce, “Darlin! Na dawo daga aiki kaina ya yi min nauyi, ka bari za muyi maganar da week end ina son hutu
yanzu. Ya yi dariya yace, “ba damuwa gimbiya yau babu doguwar hira kenan?”
Ta ce kwarai ina son hutawa.”
Ya ce
*sannu kina kokari ma, dan ban
zaci zaki iya ba.
Su ka yi sallama suka kashe waya, ta tashi ta shiga bandaki, wanka da alwalla ta yi ta fito, ta yi sallar nafilfili sanna ta saka kayan bacci ta koma kan gado ta kwanta ta jawo laptop ta ci gaba da bibiyar Dr. Jalo. Sai kuwa ta ci sa’a ta gan shi akan layi (online)a facebook.Ta Cika da murna cikin
zumudi, hannunta na karkarwa ta
rubuta sallama ta tura masa, sai da ya dauki awa guda sannan ya ba ta amsa ya tura mata Wa’alaikissalam. Yana amsawa kuma ya fita, jikinta ya yi sanyi.
Har yanzu tana ta karanta sabon rubutun da ya turo (post), ya yi magana ne akan illar
Hmmmm