D’AN SARKI SAUBAN COMPLETE BY UMMU SAFWAN

Manyan motocine bak’ake guda biyar a jere da juna, suna tafiya a kan lafiyayyen titi wanda yaji kwalta sai jiyaniya kakeji Tana tashi ” Wanda motar jami’an tsaroce Suka rako yarima sauban domin Kula da lafiyarsa.”

A katafaren wani babban gida Mai girman gaske mai d’auke da kwalliyar sarauta a jikin gidan duk wanda yaga gidan yasan gidan sarauta ne dibo da yanayin gidan da kuma fadawan dake, gadin get din kofar gidan,
Idan ka diba KO wanne yana sanye da uniform dinsa blue tare da Dan sirkin ja a, jikinsu,
gidan adalin SARKI ne maiji da mulki da k’asaita.”
Fadawa dake gadin get d’in k’ofar gidan zasu Kai kusan su ashirin ko wanne da abinda yake Kula dashi a wurin,
Suna jiyo jiniya da sauri ko wannensu ya mik’e tsaye jiki na rawa Suka bud’e get sai murmushin farin ciki sukeyi tare da d’agawa motocin hannu cike da farin ciki, sai da motocin Suka gama Shiga cikin gidan gaba, d’aya snn suka rufe get d’in, Suka runtuma su dukansu sukabi bayan motocin suna zubawa yarima Sauban kirari.”

jiniya tare da kid’e kid’e da bushe bushe ya karad’e gidan sarautar ga baki d’aya Wanda duk, wani halitta dake rayuwa a cikin gidan yasan yarima sauban ya iso mahaifarsa.”

Da gudu sarkin gida ya Isa fada ya durk’usa a gaban maimarba sarki Abdullah ya Kai gaisuwa gareshi cike da, girmamawa tare da yimasa Albishir na isowar yarima cikin k’oshin lafiya.”

Murmushi sarki yakeyi Yana girgiza kai, Wanda duk Wanda ya kalli fuskar sarki kasan, yana cikin farin, ciki d’ansa Wanda yafi soyuwa a ransa ya, dawo, cikin k’oshin lafiya,

, fadawa suka shiga cewa sarkin gida, “sarki yaji dad’in wnn Albishir naka, sarkin yayi murna, sosai, tukuicin ka na musamman ne a wurin sarki Mai Adalci.”

“Runsunawa sarkin gida ya Kuma Yi Yana “fad’in godiya nakeyi Allah ya k’ara Nisan kwana, da lafiya,
Snn ya tashi ya fita cikin sauri yanufi sashen fulanin sarki domin y Kai mata Albishir d’in dawowar sauban.”

Cikin saurin masu Kula dashi suka fito daga motar da suke,
suka zagaye motar da yake ciki sai da aka d’auki kusan minti biyar suna zagaye da motarsa snn suka bud’e Masa ya fito, duk da dama hakan Al’adarsa take baya saurin fitowa a mota da zarar anyi parking sai ya d’auki kusan minti biyar a ciki snn yake fitowa.” Saboda tsaro😎

Kyakkyawar K’afarsa yafara zurowa a waje Mai d’auke da rufafin talkaminsa masu tsananin kyau,
duk Wanda yaga yanda ya fito da k’afar sa a waje yasan mamanlakin k’afar ya Kai k’arshe wurin had’uwa da gayu,
cikin k’asaita ya Kuma ziro k’afarsa d’aya sai da a kuma d’aukar minti biyu snn,
Cikin isa da mulki yafito da gangar jikinsa daga motar,
subahanallah tsarki ya tabbata ga mamanlakin wnn halitta,
Dogone Mai matsakaicin tsawo fari ne fes, kakkaura Mai cikar halitta, fuskarsa Tana zagaye da saje Mai had’i da gashin Baki Wanda ya kwanta luf a fuskarsa ya k’ara yiwa fuskar k’awanya da adon kyau, hancinsa dogone har baka yana da manyan idanu, tare da d’an k’aramun bakinsa, fuskarsa Tana d’auke da murmushi Domin Yana cikin farin cikin ganinsa a cikin k’asarsa ta haihuwa wato Nigeria.”

*SAUBAN KENAN D’AN SARKI ABDULLAH*

Busa Kakeji tak’ara tashi tare da kid’e kid’e Ana zuba Masa kirari tare da yimasa sannu da zuwa a Nan take harabar gidan sarautar ta cika da kuyangi da bayi tare da fadawa ko wanne sai kawo gaisuwa yakeyi cike da girmamawa
Murmushi kawai yake sakar masu tare d’aga masu hannu Alamar ya Amsa,
Kasancewar Sauban mutum ne Wanda baya wulak’anta nak’asa dashi, snn yana daraja d’an Adam musamman bayinsa da kuyanginsa da duk Wani Wanda yasan yana k’asa dashi,
Dan hakan suma suke matuk’ar son sa suke gurmamasa tamkar sarki dake mulki,
snn suka bi bayansa sukayi masa rakiya har zuwa sashensa.”

Hakince take akan kujerarta ta sarauta wacce tazo da ita tin daga gidan mahaifinta,
da gudu d’aya daga cikin bayinta tashigo ta Kai durk’ushe a gabanta tana fad’in “ranki ya dad’e Allah ya taimakeki ya k’ara maki lafiya da Nisan kwana ya uwar gijiyata nazo maki da Albishir Mai dad’i, jarumin mijinki d’a d’aya tamkar da dubu kyakkyawan mijinki Mai cikar Kamala da haiba mai kyawawan halayya irin naki, a yanzun nan ya dawo daga k’asar England ranki ya dad’e na ganesa da idona yanzun nan ya nufi b’angarensa duk wannan k’id’e kid’e da bushe bushen da kikeji duk shi akeyiwa Ana tayashi murnar dawowarsa.”

Tsawa matashiyar budurwar Wanda bazata wuce shekara 25 ba, ta daka mata cikin d’aga murya tace “yimun shuru rufemun bak’in bakinki mummuna kawai marar kyawon gani tabbas yau sai kin fuskanci hukunci Mai tsanani a gareni tinda har kike iya durk’usawa a gaban idona ki dinga zanyanomun suffar mijina tare da yabonsa,
Hakan ya nuna a duk lokacin da Kika gansa sai kinbishi da ido kina k’are masa kallo kina masa kallon k’urullah, kina kallemun shi tes tin daga k’asansa har samansa.”
shin ko kin Manta ban had’a yarima da kowa ba?
Shin ko kin manta da Nasha fad’a maku da zarar kunga fitowarsa ko wacce daga cikinku ta rufe idonta kada ta kuskura ko sawon k’afarsa ta kalla bare a Kai ga kayan dake sanye a jikinsa.”

Ta nuna mata wani fili dake can bayan sashenta nesa da ita sosai filine Wanda ba komai a cikinsa sai itacen mangwaro da gwaiba tare da iccen bedi Wanda ya rufe wurin ruf ko wacce irin halittar k’waro mai cutarwa zaka iya samunta a wurin kasan cewar ba kowa yake zuwa wurin ba,
Ta nuna mata wurin tace “a can Zaki dinga kwana har tsawon sati d’aya batare da anbaki abinci ko ruwan Sha ba, snn kada ki kuskura nazo wurin na tarar da kwarar ganye d’aya ya fad’o k’asa batare da kin d’aukeshiba.”

Runsunawa tayi tana fad’in tuba nakeyi ranki ya dad’e godiya nakeyi Allah ya k’ara girma da d’aukaka, snn ta tashi tanufi wurin da aka umurceta tana tafiya tana sharar hawaye domin tasan dolene ta aikata abinda uwargijiyarta tasakata Wanda tasan da zarar tashiga wurin mutuwa kawai zatayi domin batasan iya abinda zata tarar a wurin ba ”

Yana shiga harabar b’angarensa ya d’agawa fadawa hannu alamar su dakata cak suka tsaya tare da runsunawa cike da girmamawa snn yayi masu nuni akan suyi tafiyarsu,
Cikin sauri suka juya suna fad’in kahuta lafiya yarima mai jiran gado, suna zuba masa kirari suka bar wurin, Wanda ya dad’e da shigewarsa sashensa. ”

K’ofar bithdrom d’insa ya tura yashiga komai yana nan a gyaransa tsaf tamkar yana rayuwa a cikin d’akin Wanda yasan aikin Amintattun bayinsa ne masu kula da b’angarensa tare da abincin sa. ”

Ajiyar zuciya ya sauke ya kai kwance akan lafiyayyan gadonsa Wanda yaji zanen gado na Alfarma, yashiga furta Alhmdulillah tare da kai hannunsa a fuskarsa yashafi sajen dake kwance a kan kyakkyawar fuskarsa har, zuwa gemonsa ya lashe leb’onsa na k’asa tare da lumshe idonsa yashiga tunanin rayuwarsa ta, baya tare da, rayuwar da akeyi a cikin masarautar nan tare da dalilin tafiyarsa, England. ”

Doguwar ajiyar zuciya ya sauke Tare da mik’ewa tsaye ya soma cire kayan jikinsa domin ya d’an watsa ruwa ya shirya ya tafi fada domin gaida maimartaba mahaifinsa
Bayan ya kammala yin wankan ne yafito d’aure da towel hannunsa yana d’auke da d’an k’aramun towel yana tsane ruwan jikinsa zuwa kansa,

Turo k’ofa akayi cikin isa da k’asaita ba tare da anyi sallama ba aka shigo,

K’amshin turarenta ya tabbatar masa da wacce tashigo, masa d’aki a dai dai wnn lokacin,
Ransa yab’aci matuk’a da rashin yin sallamarta, wato har yanzun saudat tana nan da halinta bata sauyawa ba,
shi har ga Allah ya manta da yana da wata mata a rayuwarsa.” Saboda Sam ya tsani halin saudat da duk wani mai hali irin nata,
Ci gaba yayi da abinda yakeyi yayi kamar bai san tashigo d’akinba. ”

Tsaye tayi wuri d’aya ta hard’e hannayenta a k’irji tana k’are masa kallo sama da k’asa cike da burgewa tare da sha’awa mai cike da so da k’aunar gwarzon mijin nata, amma isa da mulki tare da girman kai da takeji yana mata yawo ya hanata zuwa ta tunkareshi domin tayi masa sannu da zuwa tanajiran sai ya farayimata magana snn.”

Jallabiyarsa ya d’auka ruwan madara yasaka tare da fesawa jikinsa turarensa mai dad’in k’amshi ya d’auki wata kyakkyawar leda wacce ya ajiye wuri d’aya da alama wani muhimmin abune ke cikinta ya zura talkaminsa ya rab’a ta gefenta zai fita. ”

Gabansa ta sha tana kallonsa tana murmushi cikin k’asaita take fad’in haba sadaukina sai kace baka ganniba, bayan kasan wurinka nazo, kaddai ace har yanxun halinka yana nan baka canzaba,
Ko ka manta da cewa ni matarkace ta sunnah wacce katafi kabarni shekara d’aya KO waya baka mun bayan kasan Ina sonka Ina cike da kewarka.”

Kallo d’aya ya mata ya kuma tanke fuska ba alamar wasa a tare dashi ya sanya kai yayi ficewarsa ya nufi fada wurin maimartaba. ”

Sarkin gida a gaban fulani a durk’ushe yana kwasar gaisuwa, “Ranki ya dade Allah ya k’ara maki lafiya da nisan kwana, sarauniya a wurin sarki gimbiya a wurin sarki kece mai mulkin masarauta daga sarki saike wani Albishir naxo maki dashi “d’anki yarima Sauban ya sauka lafiya yanzun hakan yana cikin masarauta yana hutawa. ”

Gaban fulani ya fad’i tayi saurin mik’ewa daga kishin kid’en da take zuwa zaune, a nan take ta had’e fuska,
Ta juya ta kalli sarki gida cikin k’asaita tace “bani labarin yanda ka gansa ”

Sarkin gida ya saki murmushi ya kuma gyara zama yace “ranki ya dade yarima ya k’ara fari ya k’ara k’iba da cikar kamala dakin gansa kinsan yana cikin kwanciyar hankali da walwala. ”

Tsawa ta daka masa tace “yimun shuru bashi na tambayeka ba,
Tanuna masa hanyar waje tace tashi kafita. ”

Jiki na rawa sarkin gida yafita yana mamakin fulani KO dai akwai wani abin da yake faruwa ne da ita? . ”

Cikin fushi da bak’in cikin abinda yarima ya Mata tashiga b’angarenta, ta zauna akan kujerarta ta mulki,
A nan take bayinta suka zagayeta KO wacce tashiga yimata hidima, a can mai kula da kayan marmarinta tashigo d’auke da tire na kankana tare da Apple ta durk’usa k’asa ta ajiye a gabanta ta yanko kankana tare da sunkuyawa tabata tace “ranki ya dade gata kisha idan kina da buk’ata. ”

Wani irin wawan kallo ta wurga mata ai bata bari ta sauke hannunta ba ta d’auke mata fuska da Mari tare da kifa Mata tiren kankanar a jikinta, tana fad’in tashi kifita Dan ubanki na fad’amki Ina bukata ne?”

Mik’ewa tayi jiki ba kwari tashiga tsince duk kankanar da ta zube, tafita tana sharar hawaye tare da tsinewa hali irin na gimbiya saudat matar d’an sarki Sauban ‘ya ga sarki Abdul’rahaman sarkin Bauchi
Amini ga sarki Abdullah mahaifin sauban sarkin da ke mulkin Adamawa. ”

DOWNLOAD COMPLETE BELOW 👇
DAN SARKIn SAUBAN (1-End)

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE