DAN TAKARA PART 1 BY MAMAN NUR

Watoh a rayuwa akwai ya’yan da aka haifesu cikin gata da Jin dadi wanan ajin ake Kira da born with the silver spoon ,wasu iyayensu attajirrai ne Wanda har su koma ga Allah Basu san wahala da kunci rayuwa….wasu Kuma tunda suka Zo duniya suke fuskarta takaici da wahalallu rayuwa har ya Kai suna ganin kasawar iyayensu….wasu Kuma su ba gatan kudi ko Jin dadi rayuwa suke bukata ba….a ganinsu kasancewar da iyayensu Kuma kasan asalinka shine babban arziki a ce ka waye gari yau kasan mahaifinka ka Kuma San mahaifiyarka da danginka shine arziki Kai Koda a ce iyayen sun mutu ne ka taso ba tare da saninsu ba ka samu labari wata kwanciyar hankaline than a ce,tsintar ka akayi ko Kuma tashi kayi a gidan marayu ba tare da sanin kowa naka ba….da ciwo a ce ka taso baka San asalinka ba toh fah tamkar baka da rayuwa ne domin ba gari ba duniya gabad’aya zafi zatayi maka…..shin Mai karatu ka tab’a Zama kayi tunanin yaran da Suka tsinci kansu a wanan yanayi,akwai millions of Yara da Basu San asalinsu ba sun girman ne sun gan kansu gidan marayu shin me ki/ka Yi Dan ganin ka Basu farin ciki???shin kin/ka kasance uwar/uba mijin da Baki son matar d’anki da Allah ya jarrabta da rashin haihuwa ta d’auko maraya ta bashi gata da identity?watoh adoption shin ko ki/ka kasance cikin uwa/uba da kuka hana dan ku auro Mara asali?shin kina cikin Wanda ke kyamatar marasa asali ko Wanda suka taso gidan marayu????hmmm shin ki/ka ganin wayau da dabaran ka/ka ne yasa Allah Kare ka/ki samun kanki/ka a wanan yanayi…Suma fah ba laifinsu bane,wasu hassada kishiya kesa a sato su daga gidanjen iyayensu a kawo su wani gari a yashar,wasu Kuma Kuma cikin shege ne saboda rashin Imani a haifesu a yashar a titi….wasu Kuma kaddarar rayuwa Kamar inda akwai dalilai mabanbanta but koma dai menene su din ya’ya ne.ance abinda ya baka tsoro wataran zai baka dariya Allah yasa mu dace ya Kuma sa Mana tausayin marayu a zukantanmu …….. Wanan dalilin yasa zamu ke leka👇👇👇

 *Hajara menorial orphanage* 

Juye juye take a karamin gadonta wanda take step by step kamar na yan boading duk wani mai rai dake wanan building bacci yake banda Ashnoor da ta kasa bacci tana saka da warwarewa tunaninta ya za ayi tayi meeting demand din goverment in har ta bari watan nan ya kare toh fah hajara nemorial orphanage zata zama tarihi.. 

Sake juyawa tayi bata manta wasiyyar mummy kafin ta bar duniya ba, rintse ido tayi komai na dawo mata a Randa zata bar duniya ta dubeta ta Kama hanunta tace”Ashnoor na bar wanan gidan marayu a hanunki, nauyi da girma ta dawo kanki sweetheart mahaifiyata ta bude wanan gidan ne da dukkan soyyayarta ta bada gudumawa a rayuwar marayu da dama irinta wanda aka wofitar da rayuwarsu,wasu iyayensu mutuwa sukayi aka rasa marikinsu, wasu kuma kaddara ce ta sa suka tsinci kansu a wanan wurin kamar case dinki da tun randa aka haifeki aka ajiyeki a bola cikin kwali da badan mutane irinsu mummy ba da tuni an shafe tarihinki,
mummy watoh hajiya zainab da kira daya aka musu an tsinci jaririya suka je su ne gatan ta gashi yau ba mummy an bar Mata responsibility tasan zafin maraici ba zata so su wahala ba , anan ta tashi yanzu haka itace babba a gidan marayun kasancewar mummy rikon ya’ ta mata saboda bata da haihuwa sai ya zamo komai na gidan ita ke gudanar dashi kafin cancer yayi sanadin mummy
Ta samu tayi karatu mai zurfi domin tana da degree ne a political science, babban gidan marayu ne dake da girman gaske dan da farko ma akwai primary a ciki harda secondary suna da likitoci da suke kira in bukatan haka ta taso domin duba lafiyar yara, da mummy ke raye suna samun donation saboda tana da connection a gwamnatin tun bayan mutuwarta abubuwa suka tabarbare har ya kai ga basa iya biyan kudin malamai masu koyawa yara karatu, abinci ma gagaransu take babu donation ngo na niman mutuwa ga yara kusan goma kwance ba lafiya duk wani nauyi ya rataya a wuyanta kullum tana cikin tunani mussaman da aka kawo notice akan cewa In basuyi meeting demand din gwamnati ba za a rufe gidan ,Bata son a rufe gidan marayun nan tana son ta cigaba daga inda mummy ta tsaya but how?””

Ashnoor muma abinda muke so Jin kenan how…domin gwanatin tana son maidashi public orphanage ba private ba ganin yaran karkashinku wahala suke ba abincin kirki,bare sutura,ko Kuma karatu…in har kuka gagara cika wanan sharud’an Dole fah su kwace komai ya dawo hanunsu

  Tashi tayi ta zauna tayi tagumi Bata rintsa ba har aka Kira sallah....ta tashe sauran Yan matan ta fita ta bi d'akuna tana tashinsu tana cewa su tashi suyi sallah,soyyaya ce me karfi tsakaninta da yaran dan duk Wanda ta tasa sai ya Mata kiss Yana good morning anty,Shafa kansu take tace"how was your night rungumeta duk kanana sukayi tace"oya kuje kuyi ablution kuyi sallah sanan ku fito mu gyara gida"tana fadin Haka ta juya tana sauri d'akin da aka kebe marasa lafiya taje ta tarar dasu zaune ta tab'a goshinsu da kissing dinsu...a lokaci daya Suka rungumeta kowa da complain dinsa idanunta akansu cikin kokarin danne hawayenta tace"kuyi hakuri zamu fita aiki dasu Rabi'a mu samo kudin magani,,,Wani karamin cikinsu me suna Farhan yace"anty da gaske za a rushe Mana gida Ina zamu koma"ya Kare da fashewa da kuka...ta duka ta Kama hanunshi tace"sweetheart nothing is gonna happen to our home I know God will send someone to help us,ko da a ce bamu samu Mai taimako ba bawai rusa gidan za ayi ba but za a maidaku orphanage na gwamnati ne and za a rabamu"kuka suka fashe dashi sosai ta rungumesu ganin zatayi missing asuba ta duka tace"karku damu I promise hakan bazai faru ba maza muslems suyi alwala suyi sallah Christian should have there morning devotion

tana fad’in hakan ta juya tana sauri tana zuwa ta gabatar da sallah asuba ita da sauran Yan matan da d’akinsu daya,bàyan ta idar duk sukayi azkhar suna gamawa ta mike tace”Rabi’a ya za ai “

Rabi’a tace”toh ai fita zamuyi niman sa’a “ta jinjina Kai dukkaninsu wanka sukayi suka shirya cikin Riga da wando jeans suka rataya jaka su biyar ciffff

,tafiya me nisa ya kaisu sashin samarin maza cike da soyayyar juna suka gaisa cikin girmama juna harda dan hug…ta kalli dawood da a kalla zaiyi 20years tace”zaku iya fita yau kuwa?”Shafa Kai yayi yace”ba dole ba anty Yara ba lafiya”Shafa fuskarsu tayi tace”take care of yourself bro and becareful please”yace”sai kun dawo”peck tayi me ta juya suka fita kusan su biyar duk Yan Mata ne

Saida sukayi tafiya me Dan nisa Suka Isa babban titi Rabia CE ta tare Keke napep Suka ce Dana pharmaceutical zaka kaimu”

 Shiga sukayi Ashnur na Baki baki tana zuba surutu tace"Rabi'a yau mu dawo da wuri ba wacce zatayi night "adaidaita tsayawa tayi a roundabout saboda cinkosa daya rasa dalilinsa d'aya tarar sai yayi ta kalle kalle 

  Poster Dan takara da zee ta hango ne agefeb titi jikin wata polewire yasa ta dafe kirji tace"lahhh Rabia ga poster honourabla Aslim wanan gayen na narkar min da zuciya"

Rabi’a ta kalli poster tace”ba ke kadai ba ai honour abin so ne Kuma fa ance yafi kyau a zahiri fiye da poster din nan,Shahida ta zare Ido tace”Kuma??”

 Hafsat tace"eh Mana ai akwai Randa na gansa ne wallahi' skin dinsa sai shekin hutu yake ga daukan Ido ai nasan ma shi zaiyi wining kodan kyaunsa mutane zasu zabe sa"

Rabi'a tace"Ni ko in na gansa a tv Yana magana a house of reps ji Nike kamar in shige tv in Masa magana"

Ashnoor ko kallon poster batayi ba itafa da za a tsareta a tambayeta akan wa suke magana akai ba sani tayi ba irin abubuwan Nan be dame ta ba karshe ma haushinsu ta shiga ji ta daka musu tsawa tace”Dan Allah kuyiwa mutane shiru kun ishemu da surutu ku ko kunya Baku ji kuyi ta Koda Wanda besan da ku ba Allah dai ya saka hankali a kawunan ku Ni na rasa wanan jaraba na son maxa na kusan had’a ku da incharge wallahi”

Tsit sukayi Dan baza su so a had'a su da incharge ba,bazasu iya da jarabarsa ba yanzu karamin abin Nan sai ya daukakasa yace"Barbara suke "

Ganin keken yaki tafiya yasa ta kallon me keken tace”Kai Kuma fahh malam

Yace”ke Baki ganin cunkoso ne na rigimar da akeyi a gaba wancan bakar motar ta buge me machine madadin ya basa hakuri sai ya kai Masa duka ba tare da yayi la’akari da matar da ya goyo ta ji ciwo ba

Kallon inda aka Tarun tayi ta gan motorci ne sunyi line up masu tsadar gaske da alamu convoy ne na wani babba in hankalinta ya Bata dai’dai toh wanan me wulakanta me babur din Nan security dinsa ne

Ganin Yana niman wulakanta macen yasa ta fita a keken tana zuwa ta cire takaliminta flat da ta Sha paci ta Fara kaiwa security suka dashi ta baya

A fusace ya juyo ya d’aga hanun zai Kai Mata Mari ta rike hanun Babu alamun tsoro

Cikin daga murya tace”ka manta macece ta Haifa ka ne da zaka wulakanta mace ko ko kudi haukane da zaisa ka kasa ganin darajar mace har ka nimi wulakanta wanan baiwar Allah”

Muryarta yasa honour janye wayar da yake a kunninshi sai yanzu ma ya Lura da motar Bata tafiya gashi an taru tsakiyar titi daya tabbatar masa fad’a akeyi

Da dai Kamar bazaiyi magana ba saboda miskilancinsa sai Kuma ya bude bakinsa kamar an Masa tilas yace”mudi meke faruwa ne??_

Musu driver yace”yallabai motar security ne ya buge wancan me babur din madadin ya Basu hakuri shine ya tsaya Yana niman wulakantansu sai ga wancan yariyar me matsifar tsiwa ta fito ta Fara kaiwa Abbas duka

  Ranshi ya mugun b'aci da alamu dai a yau zai sallami abbas ya koma station dinsa domin bashi da halin kwarai abinda ya tsana kenan a take talaka 

  Be ce komai ba dukda da magana a bakinsa hakan yasa mudi fita a motar dan ya fahimci me ogan nasa ke nufin da Haka 

Tunda mudi ya fita ya zubawa wurin Ido baya ganin fuskarta sai muryarta Dake tashi alamun b'acin Rai cike da matsifa da tsiwa 

Cikin tsiwa data tace" Kai dai jaki ne shashasha wanan matar ai ta haifeka kake niman wulakanta ta 

Abbas da zuciyarsa ta Kai wuya ya wani bangajeta da karfinsa daidai karasowar mudi ya tarota da sauri

Shi kansa Dake Mota saida ya zabura ganin zata fadi,

Fisge jikinta tayi daga rikor da mudi yayi Mata tayi wani irin juyowa tana fuskarta motar hakan ko ya bashi Daman ganin fuskarsa clearly gabanshi yayi wani irin duka da besan lokacin daya dafe kirji ba Hadi da lumshe ido,ya kura Mata Ido Yana kallonta sai matsifa take zazzagewa ta d'ago matar da Bata ma iya tsayuwa ba saboda azaba da zugu da kafarta keyi 

Ta dubi abbas tace" wallahi sai Allah ya saka Mana mugu azzalumi kawai sai Kuma ta fashe da kuka 

Wanan ne yasa dariya subuce masa ganin duk wanan tsiwar Kuma tana kuka ya kalli bakin tsiwar ya ganta cikuli,Haka kawai yaji tsigar jikinsa ya tashi ya kauda Kai Kamar me tunanin wani abu sai Kuma ya Kai hannu lips dinsa Yana shafawa ya lumshe Ido

Yana kallo ta ja matar gefe sanan ta dawo tsakiyar titi ta zauna a cewarta babu wanda zai wuce har sai Abbas ya bawa matar kudin magani,

Mudi ya karasa ya duka a gabanta yace”za ayi inda kike so Amma ki Matsa Wanda ke cikin mota babbane ..”

Mikewa tayi cike da matsifa tace”in babba ne sai a cutar da bayin Allah babba ai a zuciya yake bawai a Shiga mota ayi ta Shiga hakkin bayin Allah ba in har Yana son musan shi babbane ya fito ya nunawa security dinsa yayi ba dai’dai ba “

 Abbas yace"mudi barta ai taketa zamuyi "

Mudi yayi me kallo me cike da gargadi tuni ya Kama kansa

Kasa kasa mudi yace”honourable Aslim ne D’an Takarar gwamna please ki bashi hanya zai makara Yana da meeting ne”

Ihu tayi ta mike tana cewa”Ina ruwana da Wani Aslim? ba abinda ya dameni dashi kawai a Bata kudi magani harni za a bawa kudin tunda ya tureni,

Honourable ya gyara Zama da yike yanzu be ganinta da kyau tunda gaban motar security take hakan yasa motar taresa Amma Yana juyo muryarta tana ihu a iya saninsa duk inda aka Kira sunansa mutane ihuuuu suke Amma jibi yariyar Nan tana kiransa cike da raini

 Murmushi ya kumayi ya Kau da fuska ai beyi aune ba yaji ta 

Salon na daban ne…..purely love story…….

DOWNLOAD PART 1 COMPLETE BELOW ⬇️

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE