DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 10 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 10 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Ta shiga inganta masa rayuwar don ta
mantar dashi abinda yake damun sa.
Weediyan ita da Mah suna hira Mubarak ya
shigo da rake a leda an yanko shi, ya ce.
“Mah, ga rake”.
Tayi murmushi ta ce, “Allah Sarki Mustapha, shi ne mai son rake”.
Weediyan ta ce, “Shan rake ne da shi Mah?” Tayi murmushi ta ce, “Ai wato idan suka hadu su biyun suna sha cikin ki sai yayi ciwo”.
Mubarak ya ce, “Mah, ai ni na daina shan rake saboda na rasa kaunar amini na wanda yaso ni don Allah, ina takaici ina jin haushin Momi da ta

wargaza amincin mu. Ina ji a jikina zai yi wuya mu koma kamar da, duk da cewar har yanzu shi bai saurare ni ba”.
Weediyan ta ce, “Mustapha mutumin kirki ne, mai zumunci da tausayi, ban taba ganin yaro matashi mai zumuncin sa ba. Yana rike manyan kudi, amma indai yana kasar nan dangin sa sai sun san yana nan. Sam baiyi halin Momin shi ba”.
Mah tana jinsu suna hirar sa, wayar Weediyan tayi ringin, ta duba ta ce.
“Kanwata ya aka yi?” A daya bangaren aka ja tsaki, aka ce.
“Wacece kanwar taki?”
Ta ce, “Ke din mana
“To shanshani, abba yazo
Ta ce, “Da gaske?”Ta ce, “Allah”.
Ta mike tsaye ta ce, “Gani nan”. Mubarak ya ce, “Lafiya?”
Ta ce, “Weesal ce ta ce min Abban mu yadawo”.
Ta dubi Mah ta mike, ta ce.
“Mah, zan wuce gida”. Ta rataya jakarta , Mah ta ce, “To tafiya za
kiyi?”Ta ce, “Fada zai yi ya ce na fiya yawo, don
ma Momi za ta kare ni tunda ta san ina nan”. Ta mike ta ce, “Bari inje in samu Adai daita sahu”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya mike, “Muje in raka ki”.
Suka jera, ya ce, “Kina da number din Mustapha?”
Ta ce, “Eh, amma zan yo maka (text) dinta”.


Ya ce, “Okey”. Ya sa ta a Adai daita sahu, ya ce..
“Wai ina motar ki?” Ta ce, “Tana gurin wanki”.
Ta shiga ya ja suka tafi ya kai ta, mai Adai daita sahun ya soma surutu don akasarin su suna da magana, in mace ba ta ja anyi hirar ba to su sun ja.
Ya ce, “Kinga Adai daitan nan yau na soma sojan haya da shi, haya faces muke yi ni da yayana, wallahi na tara masa kudi da shi har shekarar ta cika dubu talatin ne ban cika akan alkawarin mu ba amma sai kawai ya kwace mukullin ya sayar ya dauki kudin don zalunci ya ban canji. Kinga ni ya cuce ni”.
Tayi tsaki ta ce, “Allah Ka shiga tsakanin mu
da talauci”.
Ya ce, “Amin Hajiya”.
Ta ce, “Kuma dan uwanka?” Yace Yayana, ubanmu daya, kin san abin haushi?”
Ta girgiza kai.
“Inzo in karbi sabo na gano zalunci ne, so yake inyi ta tara msa kudi ni kuma a wahale. Kuma ina da mata daya da yara har biyar, da ya siyar baki ga halin da na shiga ba. Yanzu fa sojan haya nake”.
Ta ce, “Ni ina jin haushin mutane marasa adalci, in mutum yana kasan ka sai wulakanci, meye amfanin in fika ban taimaka maka ba? Samu na bashi da amfani”.
Ta ce, “Zan taimake ka”. Ta mika masa complement dinta, ta ce.
“Gashi, ka tuntube ni”. Ya aje ta, ta ce, “Nan gidanmu ne”.
Ta mika masa dubu daya, ya ce, “A’a Hajiya,
ki barshi”.
Ta ce, “Haba, wallahi sai ka karba”.
Ta ce, “Ka bar canjin”. Ta juya cikin gida.
Tana shiga tayi falon Abban nasu, irin
gaisuwar su tayi masa, yana dariya ya ce.Ina aka je?”
Tayi murmushi ta ce, “Abba na je gurin wata mata mai neman taimako ne”. Ya ce, “Weediyan sarkin taimako, Allah Ya
baki ikon taimakon”.
Ta ce, “Amin Abba”. Haj. Marka ta fito tana duban Weediyan, ta ce, “Sannu sarkin yawo”.
Tana murmushi ta ce, “Momy, taimako ne
Ta ce, “Allah Ya taimake mu baki daya”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Amin”.
Tayi dakin su ta ajiye jakar ta da mayafin ta, ta nufi kicin don ta san Weesal ba zata wuce kicin ba, don ita Allah Ya yi ta mai son girke-girke ce, kuma dama shi ta karanta.
Tana shiga ta ga tana aikin cake, ta gutsura taji dadi har cikin ranta, ta ce”Wow! Dadi”.
Ta juya ta dauko lemo a fitij ta haye ta zauna tana ci, Weesal ta ce.”Ina Barek?”
Ta ce, “Wai ‘yar aiken ki ce ni? Oho, nima
ban ganshi ba”. Ta ce, “To ina Mah dinsa?”
Ta ce, “Tana gida”.
Ta ce, “Ni fa na jima banga mace mai kirkin mahaifiyar sa ba, kinyi sa’ar sirika”.
Ta ce, “Au, an gaya miki sirika ta ce?”
Ta ce, “Au, ke baki san na bashi ke ba?”
Ta ce, “Okey, sannu Momy. Ai ko ita ba zata yi wannan katobarar ba”.Tace, “Toni nayi
Izzzat ta nutsu a dakin Umma ita da Surayya. Umma na gefen gado a zaune, Surayya ta ce. umma ta, kiyi hakuri ki fada mana gaskiyar al’amarinki   Ta ce, “Zan fada muku ‘ya’yana, ba zan boye muku komai ba
Na yi soyayya mai zati wacce her yau  sonsa bai barni ba. Wallahi Izzatu ke ‘ya ce mai albarka, ke ‘ya ce yar sunna, don na same ki da aure illah wani alamari da ya gifta wanda Allah Shi yasan gaskiyar al’amarin”.
Ta ce, “Kamar yadda kuka san suna na Fatima, asalin mu yan wani gari ne da ake kira Kaltingo dake Gombe, ana kiran mu tarigalu sunan kabilar mu, shi ne sunan jama’ar da nake cikin su.
To kuma akwai manoma, a gaskiya mutanen garin mu yawancin su duk manoma ne, da yawa mutan kaltingo kowa da addininsa hakan bai hanamu zaman lafiya da kaunar juna ba.
Garin mu ana karatun boko sosai, mahaifina Musulmi nes, duk da a lokacin Musuluncin bai samu karbuwa a garin Kaltingo ba, domin yawancin su suna addinin gargajiya, domin suna wani tsafi mai suna Kamarku, shi ne abinda yawancin ‘yan garin
Kaltingo suka bawa gaskiya, domin shi ne abin bautar su. Hakan shi yasa lokacin da addinin ya shigo kowa da abinda ya zаба.
Yawanci garin Kaltingo za kaga uwa da ‘ya’yanta kowa da abin bautar sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kaka na shi ya fara zuwa Kaltingo a matsayin Musulmi, ya sha bakar wuta a garin kafin ya samu masaya bayan sa, hakan ya sanya ba ya ga muciji shi da shugaban garin, domin suna ganin ya zo ya kawo musu wani addini na daban. Shi yasa sam ba ya shiga harkokin fada, babu ruwansa da su illa iyaka yana fadar kalmar Allah, kuma Alhamdu lillah ya samu shiga gurin matasan garin, don da wuya kaje gida babu Musulmi a cikin gidan.
Wannan dalili yasa Sarkin garin ya kira kakana ya yi masa kashedi akan babu wani abin bauta da yafi Kamarku, shi kuwa Mal. Yusufa ya ce babu abin bauta da gaskiya sai Allah, Shi ya fi cancanta a bauta Masa, don Shi Ya halicce mu, Shi Ya busa mana rai, Ya bamu lafiya, Ubangijin Aljanu da Mutane. “Kuma Allah Shi ne Abin bauta ta, kuma Annabi Muhammadu Shi ne Ma’aikin Allah, kuma Manzon Allah”. Saboda haka shi ba zai bi wani Kumarku ba, sannan ba zai daina yada kalmar Allah ba.
Sarki ya fusata, yasa a tsare Mal. Yusufa.
Page daya ya bata ayi haquri
Shi kansa Sarki ya’san rigima ce babba in har zai ja da mahaifina, don Rarshe a zub da jinin al’umma. Wannan dalili ne ya sanya suka yi sulhu a tsakanin su, duk wanda yake garin Kaltingo kowa yayı addinin da yake so.
Haka abin yake har a yanzu, don sai ka ga jama’ar gida daya uwa daya uba daya, amma kowa da abin bautar sa.
Mutanen Kaltingo kyawawa ne, suna da hakora ruwan zuma, duk dan asalin garin Kaltingo namiji’ko mace ba zaka same shi da farin hakori ba, sai dai ruwan zuma, wannan ita ce alamar ‘yan garin Kaltingo.
Mahaifina matan sa biyu da Inna Ladidi da Inna ta, ita kuma ana ce mata Inna Tabawa.
Inna Ladidi mace ce ‘yar sababi, mafadiya, wacce ko me Innata tayi mata ba ta burge ta, ita ko Inna ta Allah Ya dora mata tsoro, tsoron Inna Ladidi take. Sam ba ta barinta ta huta, surfe, daka, rainon yaranta duk ita ce, taqi barin Innata ta huta. Shi yasa da ta samu ciki babu kwanciyar hankali, sai ya zube saboda cikin wahala.
Shi kuma mahaifina sam ba ya kula da rayuwar gidan, komai ya damkawa Inna ladidi, shi yasa tamaida Inna ta kamar ‘yar aiki take a cikin gidan. Sai dai Inna ta mace ce mai ibada, haka suka
rayu.
Inna Ladidi tana da ‘ya’ya hudu, Sallau shi.ne na fari, sai Salisu, sai Sale, sai Sambo. Haka suke duk sunyi wayo, sannan Innata ta samu cikina. Babu wanda yasan da shi, ko ita batagane dashi ba, don babu laulayi komai. Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokacin da Inna Ladidi ta kula da cikin hankalin ta ya tashi, wai za a kawo mata ‘yan uba. Duk hanyar da taga za ta bi don kada a haife ni, amma Allah Ya nufa sai na shaki iskar duniyar. Har dukan Innata take, amma da yake tana da hakuri haka ta hakura har lokacin da cikinta ya isa haihuwa.
Ita kadai tayi nakauda ta haihu cikin dare, kukan jaririyar ya tallasa ta, Inna Ladidi ta fito aguje, cewa take.
“Tabawa, haihuwa kika yi don mugun hali baza ki sanar ba? Salon ace kina kula da ‘ya’yana ni na gaza kula dake?”
Tana shigowa cewa tayi, “To me kika haifa?” Ta ce, “Yaya ki duba ki geni”.
Tana dubawa sai ta fashe da dariya, ta ce.
“Ai budurwa ce”.
Dadi ya cika ta mace aka haifa, ganin mace ce sai take ta murna dama ai ba su da mace, amma. kuma tana murna ne don ba namiji ta haifa ba, ita take da maza hudu, ita ko mace kwalli daya.
Anyi suna an sanya min Fatima, tunda Innata ta haife ni ba ta sake haihuwa ba, kuma haka ta ci gaba da wahala a gidan har na girma nima na ci gaba da bautar cikin gida kamar mahaifiya ta.
An sani a boko kamar ‘yan uwana, don zuwa wannan lokaci garin Kaltingo ya ci gaba sosai, don har kirari ake masa garin Malam da Malama, in kaga jahili bako ne. Don jama’ar mu muna da ilimi kowanne
Ina  J.S.S 3 na hadu da Musbahu, ya nuna min kauna, sanin yadda muke a dosa ne ni da mahaifiya ta ban taba bashi damar ya zo gidan mu ba, sai dai mu hadu a gidan su kawata Safara’u. Hakika mun shirya da Musbahu, don yana Www.bankinhausanovels.com.ng
karatu a A B U Zaria ne a lokacin. Musbahu dan sarkin Kaltingo ne, har zuwa wannan lokacin akwai ‘yan addinin gargajiya a gidansu, don mahaifin sa ma Kamarku yake bautawa, amma shi Musulmi ne.
Mun yi shakuwar da nake ganin babu wanda ya isa ya raba mu. Innata ta sani, tun farko ta so ta raba mu da shi, don tana ganin ta ya mahaifin sa yasa a kashe kakan mu, kuma zan aure shi? Ta ce abu ne wanda ba zai yiwa ba, amma ina naki, domin soyayyar sa ta shiga raina, kuma har yanzu da nake baki labari ban taba son wani namiji kamar Musbahu

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE