DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 11 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 11 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 




Mun tsaya 

karatu a A B U Zaria ne a lokacin. Musbahu dan sarkin Kaltingo ne, har zuwa wannan lokacin akwai ‘yan addinin gargajiya a gidansu, don mahaifin sa ma Kamarku yake bautawa, amma shi Musulmi ne.
Mun yi shakuwar da nake ganin babu wanda ya isa ya raba mu. Innata ta sani, tun farko ta so ta raba mu da shi, don tana ganin ta ya mahaifin sa yasa a kashe kakan mu, kuma zan aure shi? Ta ce abu ne wanda ba zai yiwa ba, amma ina naki, domin soyayyar sa ta shiga raina, kuma har yanzu da nake baki labari ban taba son wani namiji kamar Musbahu

ba, don son gaskiya nake masa. Ina aji huda Allah Ya yiwa Inna rasuwa, lokacin damuna shekarar anyi rusau, to itama gini ya fado mana muna bacci, abin ya zo da karar kwana ta rasu, ni kuma na sha wuya na warke.
To sai me? Gaba daya aikin da Innata ke yiwa Inna Ladidi duk ya dawo kaina, bani da lokacin kaina, makaranta ma bani da lokacin zuwa, duk na rame, na jeme, na zama tamkar almajira.
A lokacin mahaifina ya kula da wahalar, sai yayi nufin ya aurar dani, don shi ma kamar tsoron Inna yake ji. To akwai abokin yayana Sallau Lawandi, ya ce yana sona, ni kuma na ki jinin sa, saboda Yaya Sallau ya fi ‘yan uwana mugun hali, don har ya fi mahaifiyar sa mugunta, ita kanta tsoron sa take. Sam ya ki karatu sai sace-sace da tare ‘ya’yan mutane a hanya, wannan ya sanya sam naki abokin sa. Shi ma ba shiga shirgin sa nake ba, don ba mutumin kirki bane.
Iyayen Lawandi sun zo gurin mahaifina ya tambaye ni na ce bana son sa, ya ce ni daya ce ‘yarsa mace, ba zai yi min auren dole ba, wanda nake so zai bani.
Ganin ya fadi haka na ce ai Musbahu nake so,ya ce.”Waye haka? Dan waye?”


Www.bankinhausanovels.com.ng
Na ce, “Dan sarki ne”.Ya ce, “Dama yan zuwa gurin ki?”Na ce, “Eh”.Ya ce, “To zai yi tunani”.
Sallau ya same ni yana fada, ya ce don abokinsa zai rufa min asiri ko nayi zaton duk abinda muke da Musbahu ba a sani ba? Nan dai ya kama ni
da duka. Ko da Inna taji ba’asi sai ta ce, “Lallai kwadayi, ina ke ina auren dan wanda ya kashe kakan
ki?”Nan da nan ta tantsama maganar cikin dangi, ai ko aka yi min ca tamkar a cinye ni ko a kashe ni. Ni ba uwa ce dani ba, kuma ni asalin mahaifiya ta Bakanuwa ce.
A lokacin Musbahu shi ma ya ta da maganar,da yake da ne wanda mahaifin sa yake son sa.
Musbahu dan gayu, ba shi da hayaniya, yana da mutunci kwarai.
Mahaifin sa ya ki mahaifina fada aka sanar da su ga abinda suke so, ya ce sai yayi tunani. Ko da ya zowa da dangin sa maganar sai aka ce lallai ba ya kishin mahaifin sa.
Rigima tayi tsanani, ni kuma na ce indai ba Musbahu ba lallai babu ni babu aure. An jima ana rigima wacce daga baya ‘yan uwa suka ce za su bani
Www.bankinhausanovels.com.ng
shi amma kada in fidda ran zan iya haifar da mai bautar Kamarku.
Na ce ni dai ina son shi, suka ce komai ya same ni babu ruwan su, na ce na yarda, aka ce shi kenan. Inna Ladidi bakin cikin duniya ya ishe ta zan
je gidan da zan huta, bata so ba. Ta so in auri
Lawandi mashayi, amma bata yi nasara ba.
Maganar aurena da Musbahu ta kan kama, lokacin ya kammala (digree) dinsa, har yana aiki a garin Gombe. Ko da aka yi bikina Gombe aka kaini.
Rayuwa ta da Musbahu rayuwar jin dadi ce, don ya mai dani makaranta. Ina son Musbahu, don shi bawan mace ne, mutum ne mai tattalin iyalin sa, don Allah Ya yi shi da tausayi, gashi dan sarki kuma babban maaikaci, amma haka zai zage muyi aikin gida ni da shi.
Wata na biyu da aure na soma zazzabi mai zafi, muka je asibiti gwajin farko aka gano cikin da nake dauke da shi. Murna Musbahu yake, ni ma kunya ce ta hana ni nuna tawa, amma duk da haka ina muna cewa zan haifawa wanda nafi so ‘ya.
Mukan je garin Kaltingo, haka ina yiwa mahaifina alheri, don in na tara kudina in nazo zan bashi, haka Musbahu zai hado kayan abinci ya kai. Tabbas ita kanta Inna Ladidi ta san haihuwar ‘ya’ya munyi missing page daya ayi haquri
Washe gari ta koma Kaltingo ta je har gidan Sarki ta kai tsegumi, Sallau shi ya fara bi na da kazafi wai ai dama ina yawo na, ai ya sani kyale ni yayi, amma yanzu tunda Allah Ya toni asirina, shi kenan.
Aka je Gombe aka taho damu, Sarki ya ce wannan ba jinin sa bace, ba zai karba ba. Musbahu na kuka ya ce, “Wallahi ‘yata ce, ni
ne namiji na farko da na kadaice da Fatima”. Amma ina! Mahaifina yace
“Ya bata Musbahu ce, don ko da wata shida tayi ta haihu bare wata bakwai, kuma likitoci sun tabbatar bakwaini ce, don har sun shimfida dokoki kan jaririyar”.
Sarki ya ce, “Ni ba Musulmi bane, in ka yarda
za a kai yarinya ga abin bauta Kumarku, shi zai nuna
mana gaskiya”.
Mahaifi na ya ce bai yarda ba, shi ma Sarki ya ce bai amince da ace ke din jikar sa bace. Mahaifina ya ce aje ayi gwajin jini, Sarki yace shi fa akai ta ga abin bauta, shi ne ma Mahaifina ya ce girman yarinya halittar jiki ne,” yana da girma wani ba ya da girma, amma ya tabbatar wannan yarinyar ‘yar Musbahu ce.
Musbahu ya ce da mahaifin sa, “To a bari in
Www.bankinhausanovels.com.ng
karbiyata, wallahi yarinya amman inaa Sarki ya kore mu ni da mahaifina  ya ce ya kuma bata Musbahu bace. Muka taso muka  dawo gida, Inna Ladidi dadi ya cika mata ciki, ta ce, “Ai dama duk wanda ya shiga motar kwadayi lallai zai sauka a tashar wulakanci”,  mahaifina yace kada in damu, komai mujarrabi ne, zai rike min ke, zai kula dake har zuwa lokacin da Allah Zai baiyana gaskiya  Ita ko Inna Ladidi ta ringa talla dani a garin Kaltingo, ake zuwa ganin ki wai na haife ki shegiya. Har cewa tayi ina ma Tabawa ba ta mutu ba taga abin takaici. Musbahu ya zo gidan mu ya kawo riguna da kayan bacci, duk abinda uba yake wa ‘ya Musbahu
yayi miki, shi ya yi miki huduba da Izzatu  Mahaifin ki yana son ki, nima ina son ki,ba kawai haka Allah Ya shirya rayuwar ki, ba”Duk yadda Musbahu ya so ya maida ni daki
na ya karbe ki iyayen sa sun ki, duk wannan ya faru ne saboda sharrin matar uba, bata sona, bata son ci gaba na.  Haka muke rayuwa komai Musbahu na yi mana, ya ce da mahaifina ya bashi mu ya gudu muyita wanı garin mu rayu, mahaifina ya ce a’a, kawai ya
Www.bankinhausanovels.com.ng
bani takarda ta.
Musbahu ya ce, shi ba zai iya ba. Mahaifina ya ce dole kuwa sai ya bani. Mahai fina ya kai maganar kotu ya bani
takardar saki, dole ya sakeni
Ya ce da Alkali, “Izzatu ‘yata ce, ka rubuta ka ajiye, duk daren dadewa zan karbi ‘yata Izzatu Musbahu”.
Tun daga wannan lokacin Musbahu ya soma rashin lafiya, saboda damuwa, daga karshe mahaifinsa ya sa shi ya bar kasar don ya koma London ya ci gaba da karatu.
Wannan shi ne rabuwa ta da mahaifin ki, har yanzu ban sake dora idona akansa ba”. Sai ta fashe da kuka.
“Ya manta dake, kiyi hakuri Izzatu, ki jure,
komai mujarrabi ne”.
Izzatu tana sharar hawaye ta ce.
“To saboda me Kawu Sallau yake so ya hana ni aure? Duk wanda ya zo maganar aurena zai ce ni bani da uba, Umma ta,
Ta tsare ta da ido, “Zan samu kawu Sallau, ba zan kyale shi ba”. Surayya ta ce, “Ki bari ta karasa mana labarin
muji ya aka yi har ta auri Babana”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Umma ta ci gaba da labarin ta, ta ce.
Rashin Musbahu ya haifar min da damuwa, abin ya zamar min zafi biyu, na farko rashin masoyi, na biyu sheganta min ‘yata.
Inna Ladidi ta takura min, ta hana ni sakewa sam, wannan dalilin yasa babana ya sake ta. Kwana biyu da sakin Inna Ladidi ya auri Inna Rabi, mace mai kirki, ta rikemu ni da ‘yata tare tausayawa da kauna.
Su Sallau kuwa ko kula ta basa yi, a lokacin aka yi auren Sallau da Sale, iyayen Inna suna ta rokon babana ya dawo da ita, amma ya ce zaman su shi da ita ya kare, dole suka hakura.
Lokacin da na yaye ki manema suka fito neman aure na, ke ko yarinya ce mai girman jiki, gaki da shiga rai. A lokacin na shirya zuwa Kano ganin dangin Inna ta, sai Inna Rabi ta ce in bar mata ke saboda dama a gurinta kike, komai ita take miki.
Haka muka shirya da babana, shi ya kaini har muka zo Kano unguwar Gabari.
‘Yan uwa sun yi murna, tun ba kaka ta ba. Washegari baba ya koma da cewar zanyi wata daya.
Na ga kara da karamci, anan na sanar da kaka
ta komai, taji haushi ta ce me yasa ban zo da Izzatu ba?
Na cc, “Inna Rabi ta ce abar mata ita”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kaka ta ce, na zo kenan. Nan take satina daya ta sani makarantar (Liberary) dake Kofar Nassarawa, ta kuma tashi yayan mahaifiya ta ta ce tana neman alfarma ya barni a hannun su, su ba da Izzatu in sun yarda.
Ya ce babu komai, amma a barwa Inna Rabi Izzatu, don sun saba. Ganin irin kulawar da take mata aka bar mata ita, ni kuma na ci geba da aji hudu na sakandire, har na gama.
Na soma zuwa F C E. A nan na hadu da mahaifin su Surayya, mutumin kirki ne, ban boye masa komai na taba aure, ina da ‘ya daya. Shi kuma a lokacin saurayi ne, bai taba aure ba, ya ce babu komai.
Anyi neman aurena cikin jin dadi da kwanciyar hankali, a Kano aka daura min aure, babana da ‘yan uwana mota daya suka zo Kano, aka daura aurena, aka yi bikina na tare gidan mijina Alh. Habib Salga, yana aiki a kamfanin robobi.
Yana kula dani, na cire Musbahu a zuciya ta.
Na haifi Surayya, daga nan na haifi Habib, a lokacin Allah Ya yiwa mahaifina rasuwa.
Inna Ladidi daga zuwa gaisuwa tayi zaman ta, wai ita ke da gida tunda duk ‘ya’yansa nata ne. Rigima aka yi sosai, Inna Rabi iyayen ta manoma ne masu arziki, da aka bata tumunin takaba sai ta ce ta
Www.bankinhausanovels.com.ng bawa Izzatu kyautan. Rabin gidan mu na Kaltingo naki ne.
Kaka ta ce ta dauko Izzatu ta dawo da ita hannun ta, ta sanya ki a makarantar boko da Islamiyya. Kina da kokari, kowa yana son ki.
Shekarar ki goma sha biyu, kina J.s 1 kika yi sankarau, shi ne dalilin da kika samu matsalar kurumancewa, don da farko ba a gano ba kya ji ba, sai ai tayi miki magana amma ba kya ji, a dake ki, a zage ki. Sai daga baya aka gano kin zama kurma, kina iya magana amma ba kya ji, amma a duk sanda jirgi zai shige za kiji rugugin jirgi
Kin rayu a hannun kaka ta, ta rike ki ke da Izaddeen dan wan Inna ta, wanda kun shaku da shi sosai. Kin san abinda ya hana auren ku da shi? Mahaifiyar sa ta ce ba zai auri kurma ba”.
Izzatu ta mike, “Umma na gano ko ni din ‘yar
waye, ni ‘ya ce ga Musbahu Kaltingo. Zan nemi uba
na, ba zan yarda a sake kirana da shegiya ba”. Ta mike, “Naji abinda nake son ji”. Surayya ta biyo bayan ta, ta ce. “Ni kin katse min labarin da nake so inji”. “To ai an gama, me yai saura da ba ki saniba?”
Ta janyo wayar ta don ta turawa masoyants (text), sai ko taga sako, ta soma karantawa.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE