DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 2 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 2 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Tallahi Mubarak dana ne, danmu ne ni da kai”.
Ya ce, “Ko? To ya aka yi muka rasa shi? Ya aka yi muka samu Mustapha?” Ta ce, “Wannan ne na rasa, amma ka
taimake ni ka dawo min da dana. Kana da kudin
da za ka karbo min dana, kana da kudin da za ka
karbo min farin ciki na. Wallahi Mubarak dankane”.
Ya ce, “Uhm, saboda ina da kudi sai in zama azzalumin attajiri? Ba na zalunci da dukiya ta, na tara dukiya da halal. To misali, yanzu asa mun karbi Mubarak, ya kike so ayi da Mustapha?”
“Duk sai mu hada mu rike”. Ya ce, “Mun zama azzalumai, mu karbi

yaro a hannun iyayen sa talakawa, sun sha wuya wajen tarbiyyar sa, sun nemi kudi da kyar sun sa shi yayi karatu, sai da ya girma mu kwace shi?” Ta ce, “Ka ki ka gane, dana ne fa, kayi bincike”.
Ya ce, “Ba zanyi ba, na taso da kaunar Mustapha, ba zan iya son kowanne da ba in ba shi ba”.
Ta ce, “To Alhaji ni zan kai abin ga hukuma, ai hukuma uwar kowa ce za ta amshi batu na”. “To in ta karbar miki kiyi masa uba, amma
zan zama uwar Mustapha kuma uban sa. Ki sani, a
duk lokacin da kika shirya yin shari’a, to lallai ki bar min gidana ki tafi can gidan iyayen ki, in kin kammala kin dawo. In kinyi nasara sai ki nemi ubansa, idan baki yi nasara ba sai ki nemi wani dan ba Mustapha ba, kin gane?”
Ta sanya masa kuka ita dai ya taimake ta, a lokacin Mustapha ya kwankwasa kofa, ya ce. “Shigo”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya gai da Momi, ya juya ya gai da Daddy,
ya ce”Ya aka yi Boy, anya ka kwantar da hankalin ka kamar yadda kayi min alkawari?”Ya yi murmushi ya ce, “Zuwa nayi in shaida maka nan zuwa jibi zan wuce Turkey”, Ya ce, “Yayi kyau, ka ci gaba da shiri ka ji dan albarka?”


Ya juyo ya kalli Momi, ya ce. “To Momi, ayi hakuri damu tunda ni dai ban san ko ni waye ba bare in gane DAN WAYE ni? Ki daure ki sanar dani asali na”.
Ta ce, “Oho, ni dai Mubarak dana ne, a shirye nake da in bar auren mahaifin ka indai zan samu cikar burina, dana Mubarak”,
Ya ce, “Momi in ba ki sona Allah (S.W.T)
Yans sona, Yana kishi na, zai bude gaskiya kowa
ya gani. Sai dai ko ba jima ko ba dade za kiji
kunyar yadda ki ka rike ni. Ni na san Allah ba Zai
kunyata ni ba”.Ya juya ya fice.
Ta saki kuka, ta ce, “Ka yafe ni Mustapha, ban yi don in tozarta ka ba, illah ina ji a jikina da zuciya ta lallai Mubarak dana ne”.
Alhaji ya ce, “Zuciyar ki ta fada miki karya, ta yaudare ki, kin siyo mana tashin hankali da hannan ki. Kiji tsoron Allah Saratu kada ki sani ni da dana a cikin wani hali”.
“To ni kuma in shiga wani halin? Ba zan iyabarin Mubarak ba, na shirya bar maka gida yanzu
ba anjima ba”. Mustapha ya ce, “Ni ya kamata in bar gidan
nan tunda tun kafin ku haife ni kuka tare, ba’zan zama sanadin rabuwar ku ba”.Cikin tsananin fada Daddy ya ce.
“Kije duk inda za ki kije, in wulakancin ki ya motsa sai a fake da mutanen ɓoye, ko ma mene ne wannan lokacin kin debo ta da zafi”.Www.bankinhausanovels.com.ng
Mustapha ya yi kuka irin kukan da bai taba yi ba, yaji sam Momi ta fice masa a rai. Yana ji ba zai iya rabuwa da Daddy ba, don shi ne mahaifin sa, hakika bashi da uban da ya fi shi. Shima kuma yana jin anya ita din uwarsa ce? Lallai shi ma ya cire ta cikin iyayen sa.
Kwankwasa kofa ake, bai damu ya share kwallar idon sa ba ya mike tare da bude kofar.
Hajiya Lami ce kakar sa ita da Hajiya Marka kanwar Mama, suka shigo.
Hajiya Marka ta ce, “Yarona, lafiyar ka? Haba, da hankalin ka da tunanin ka? Kai fa namiji ne, namiji da jarumta aka sanshi. Haba Mustapha”. Sai kawai ya rushe da kuka tamkar mace,
Haj. Lami ta kasa komai, sai kawai ta shiga taya shi.Mustapha ko ba jinin su bane suna son sa, mutum mai kyauta da taimako, wanda Allah Ya yiwa baiwa da wannan yaron ai yaji dadi.
Haj. Marka ta ce, “Haba Hajiya, ke da muka zo lallashi kuma kin sanya kuka?”
Ta ce, “Ba dole inyi kuka ba? Muna cikin kwanciyar hankali da jin dadi ta tayar mana da hankali, ta kawo mana tatsuniyar da muke so muji ance kurunkus”.
Ta sa hannu ta dafa Mustapha, ta ce. “Mustapha, kada ka fasa tafiyar ka, Allah Shi Ya halicce ka, Shi Ya Shirya maka rayuwa, komai rintsi komai wahala lallai akwai karshen abin. Kada ka damu, wallahi mu muna sonka, za mu rike ka, don ban taba jin cewa kai ba jikana bane. Ina tunanin ko mahaifiyar ka na da ciwon tabun kwakwalwa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya juyo ya ce, “Hajiya, don Allah ki sanar dani, tsinta ta aka yi?”
Ta ce, “Ko kadan, an haife ka ne a garin Gaya, kafin mahaifin ka ya dawo cikin birni, don da a garin Dum Dum yake, ai ka san Dum Dum, kuma kana zuwa?”Ya gyada kai.
Hakika shi ma yafi tunanin akwai motsuwa cikin lamarin mahaifiyar sa Kai tsaye suka shiga lallashin sa da dadadan kalamai, sannan suka fito tare.
Momi ce take ta jibge akwatunan ta a mota, wai gidansu za ta tafi, don ita da gidan sai ta karbo danta Mubarak.
Kai kawai Mustapha ya dafe saboda sara
masa da yake yi, Hajiya ta ce.Lafiya Saratu?”
Ta ce, “Zan koma gida, sai na dawo da farinciki na”.
“Ke, anya kina da hankali?Ta ce, “Hajiya ba zan zauna ba, in kuma kin
hana ni zama a gidan ki, zan samu inda zan zauna”.
Mustapha yana dafe da hannun sa ya girgizawa Hajiya kai, ta ce. “To ai sai ki shige muje, mijin ki ya san za ki tafi?”
Ta ce, “Shi ya ce in tafi”.
Weediyan tana tsaye tsakiyar falo, idanunta na tsiyayar hawaye, ta rasa ya zata yi da rayuwar ta? Tana jin haushin Momin Musty, wacce irin mutum ce mai uwar zabar kanta? Tunda maganar ta fita a dangi sai taji ta fi kowa damuwa, ta rasa
inda za ta zauna taji dadi.
Haj. Marka ta shigo ta ce”Biyulle, ba za ki cire damuwar ki ba? Kodai son Mustapha kike?”
Ta ce, “Na shiga uku Momi, ana so ya rasa rayuwar sa? Wannan wacce bahaguwar magana ce?”
Ta janyo ta a jiki, ta ce.Kiyi hakuri, shi ma ya hakura, to k
saboda me ba zaki hakura ba?” Ta harare ta, “Allah Ya kiyaye in zama A lokacin Weesal ta shigo, ta ce. “A’a, lafiya kanwa ta?”
kanwar ki”.”To naji, me ke faruwa?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Mustapha nake tausayi”. Ta ce, “Addu’a za kiyi masa Allah Zai yayyafawa abin sauki”.
Izzat na zaune tana duban Mustapha, ta ce.
“Kana tare da damuwa, duk ka yamutse, ka rame, why Musty na?”
Ta fada cikin irin yanayin maganar ta. Ya ce, “Ina cikin wani hali Sahiba ta, kiyi min addu’a”.
Ta ce, “To zanyi maka, yanzu in ka tafi sai
yaushe?”Ya ce, “Sai an kai min ke can, kin san na fada miki can zan koma, ko baza ki ba?” Ta ce, “Ai garin masoyi ba ya nisa, duk inda kake zan bi ka”.Ya yi murmushi ya ce, “Zan tafi”.
Ta ce, “Ina Mubarak?””
Ya ce, “Yana nan, kina da sako ne gurin Ta girgiza kai, ya ce.
“Okey, ki gai da min Umma”.
Ta ce, “Karfe nawa za ka tashi?”Sai da asuba”.
Ta dan yi rau-rau da ido, ya ce.
“Lafiya?”
Ta ce, “Ina ji a jikina kamar kana ɓoye min wani abu, in akwai abinda kake ɓoye min ka fada min, don ka san lallai zan sanshi”.
Yaji gaban sa ya fadi, ya yi saurin kallon
kasa yana nazarin kalaman ta. Ko ta sani? Ko taji
ance shi bashi da sali? Ko ma dan waye shi oho. Gaskiya dole ya jingine maganar aure, saboda bashi da nutsuwa. Sai dai fa akwai son Izzat a ransa, ba ya iya minti biyu ba tare da yayi tunanin ta ba, to inaga sun yi nisa?
Ta ce, “Ina sonka soyayya mai tsafta, irin soyayyar da ban taba yiwa wani da namiji ba. Ina so in zama mace ta gari a gare ka, wacce zan zamo abar alfahari a gurin ka. Ka rike ni amana, kada ka bari a shiga tsakanin mu, kada ka ya dani in kaje can”.
Ya yi murmushi, ya ce, “Kada ki damu, ke
kadai nake so, zan kuma ci gaba da son ki, da
fatan za ki rike min alkwari?”
Tayi murmushi hade da fari da idon ta, hakan kan kara mata kyau matuka, don Izzat akwai iya fari da ido.
“To shi kenan, zan wuce”.
A lokacin Surayya suka fito ita da Yaseen, Mustapha ya kalli Yaseen ya ce.
“Likita, barkan ka da yamma”. Ya ce, “Ya jikin ka?”
se Ya ce, “Ai dazu ma na je asibiti”.Lafiya?”Ya ce,Jiri ke damu na”.
Dr. Yaseen ya ce, “Kana damun kanka da tunani fa”.
Ya yi murmsuhi, “Me rai an raba shi da tunani ne?” “Haba Yallabai, bai kamata ace kana sanya damuwa ba”.
Ya ce, “Haka ne, komai lokaci ne”. Karfe biyun dare Mustapha ya daga ya bar Www.bankinhausanovels.com.ng
Nigeria, cikin zuciyar sa cike da tunanin ba zai dawo ba har abada, domin in ya tuna uwarsa ta ce ba ita ta haife shi ba, sam sai ya kasa sukuni. Ji yake tamkar ya kasa samun sukuni a rayuwar sa, ji yake ba zai sake riskar farin ciki ba, ji yake shi da farin ciki har abada.
“Haba Mustapha, sai kace ba Musulmi ba? Babu wanda zai dauwama a farin ciki har bada, haka babu mai dauwama a bakin ciki har abada. Komai ya samu bawa da sanin Allah (Subhanahu Wa Ta’ala)”.
Mubarak zaune shi da mahaifin sa, ya ce.
“Baba, na kasa yarda da halin da zulumin da ya same ni, bana son in jefa rayuwar Mustapha cikin takaici gami da bakin ciki. Duk yadda na so inyi don in ganshi abin ya ki samuwa, duka wayoyin sa a kashe, kada in zama silar wargajewar rayuwar sa? Ina laifin sa da ya janyo ni a jiki, ya tsamo ni da iyayena daga talauci?”Mal. Bala ya ce, “Kada ka damu, baka da
hannu cikin wannan matsalar, laifin uwarsa ne, kuma munga yadda aka haihu a ragaya. In ita mahaukaciya ce hukuma ai ta san komai, saboda me zamu damu kanmu? In takamar su kudi mu kuma muna tare da Ubangiji.
Tun faruwar lamarin naga Mah ta shiga tashin hankali, shi yasa nake sanya jarumta a lamari”.
Mah ta daga labule ta ce, “Dole in damu, naka gudun ka yake in baka da shi, tunda gashi ‘yar uwata tayi min na gani. Kuma shari’a sabanin hankali ce, maganar shari’a ta masu kudi ce, mu kuma talakawa ne”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mal. Bala ya ce, “Ya kike zancen shari’a ne? Sun kawo takardar sammaci ne?” “A’a, na san ko ba jima ko ba dade sai sun kai”.
Ta dubi Mubarak, “Mubarak, ka nemo min Mustapha, ya yi fushi damu”.
Ta ce, “Ka nemo shi, mu muka yi masa laifi, dole mu lallashe shi”. Ta fada cike da jin zafi.
Gidan cin abinci ne na Five Ster inda

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE