DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 6 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 6 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
Ya je gurin Jasnen family, su da yake duk
‘yan kasar kowa da sunan family dinsa a karshen
sunan sa. Babban family ne, kuma tare suke
kasuwanci shi da mahaifin Ahmet, wato Ahmet Jasnen.
Hakika mutanen Turkey mutane ne masu karamci da nuna soyayya, haka nan mutane ne masu masifar son ‘ya’ya, shi yasa da Mutsapha ya sanar da Ahmet matsalar sa abin ya girmama, don sam kwakwalwar sa ta kasa daukar zancen.
Muhammed Jasnen ya rike mukamai da dama cikin kasar Turkey, duk da dai ita kasa ce ta hadin giwa, ma’ana dauloli da yawa sun mallake ta, kamar Girkawa, Rumawa, Usman em rope. Yawanci a al’adar Turawa su ke da ta mutanen Asia.
Muhammed yana ganin aminin sa ya rungume shi suka yi gaisuwar nan irin ta mutanen kasar, jikin sa a kasalance da bujen wando da jar hula, ya yi dai shigar gargajiya irin ta kasar.
Sun hau bene na 20, don kasar ta samy ci zgaba, don ginin su irin na zamani ne, benaye ne. Wani irin kayataccen falo suka zauna, don dama su mutanen Turkey sun shahara a (furnitures).
Mohammed ya ce, “Amma ba ka sanar dani zuwan ka ba? Kuma gobe akwai (meeting) da zamuyi da ma’aikatan kamfanin (furnitures)”. mu
Ya ce, “Okey, gashi na zo a dai dai”. Ya ce, “Eh, ai da Mert ne zai wakilce ka”.
(Yana nufin Mustapha). Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ai dani da shi duk daya”. Sun jima suna hira, don sai da aka shirya
musu shan (tea) don karramawa. Da daddare suna zaune Mustapha yana kan
kafet dadin sa na kan kujera, Mustapha ya ce.
“Ashe Momi da gaske take cewar ni ba danta bane? Tunda gashi ta kaini kara”. Ya ce, “A’a, ba kai kadai takai kara ba, akwai dai
mamaki”.Ya ce, “Nima abinda yake damu na, nima kotu ta kawo min takarda in bayyana ni da kai, wannan shi ne makasudin zuwa na. Kada ka damu, amma ko kai danta ne, ko ba danta bane na yanke igiyar aurena akan ta”.
Mustapha ya yi saurin kallon baban nasa, yace.
“Daddy, bai kamata kayi haka ba, kana so na, nima yanzu na soma shakka akan Komi, don Allah tunda ba ta sani ba ka bar maganar saki. Tun kafin a haife ni fa ku ke tare, ka rabu da ita”.
“To Mustapha naji, yanzu za mu koma tare
ni da kai”.Ya ce, “Ina da muhimman abubuwan ci gaban mu anan, kayi hakuri zan halacci zaman, amma ba tare za mu koma ba, tunda akwai lokaci”. “Shi kenan, Allah Ya kaimu”.
Washe gari sun zaga kamfanonin can, sun halacci (meeting), kai tsaye suka nufi Zafer, wajen shakatawa ne.
Suna zaune Dadddy ya ce. “Af na manta ban sanar da kai ba, an baka Izzatu”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya rungume Daddy, ya ce. “Har mun sanya rana, watanni biyar”.
Ya yi murna sosai, har farin ciki na neman ya mantar da shi a matsayin da yake. Tunanin sa daya kada iyayen Izzat suji su sauya bashi, tunda takamaimai shi an rasa ko DAN WAYE?
Mah gaba daya hankalin ta ya tashi, don abinci ta kasa ci. Shi kansa Mubarak ya kode, ya jeme, in ka ganshi kamar korarre, don zai baka tausayi. Ga zance ya cika gari ko ina maganar ake.
Mah ta dubi Mal. Bala cikin kuka, ta ce. “Da na san dawowar mu cikin birni zai kawo min matsala da ban dawo ba Malam, ko mu gudu?”
Ya ce, “Ya zamu gudu? Mun zama marasa gaskiya kenan”.
Ta ce, “Ina jin tsoron shari’a da mai arziki, ka kalli shigar ta da kallon da take min, ina jin tsoron ta, wallahi ina tsoron in ta raba ni da dana zan mutu, wallahi rasa ni zaka yi, zan iya mutuwa”.
A lokacin Mubarak ya shigo ya ce. “Mah, kin taba ganin yadda aka raba jini da
tsoka? Ni da ke ba zamu rabu ba kinji Mah dina?” Ta kalle shi, sai tayi shiru tana tuna yadda ta ga shigar Haj. Saratu, da motar da ta zo. Sai ta ci gaba da kuka, tana cewa.
“Allah bani da kowa, bani da komai. Na kama kafa da soyayyar da kake yiwa masoyin Ka, Annabin mu Annabin da babu kamar sa, Allah Ka bayyana gaskiya cikin kankanin lokaci, don na san ni za a zalunta. Allah kada Ka barsu su zalunce ni, Kada ka basu ikon rabani da gudan jini na dana”. Sai ta fashe da kuka.
Mal. Bala ya ce, “Ai kin kai kukan ki ga Mai kowa Mai komai, kada ki damu. Mu tsaya muga yadda Allah Zai yi mana hukunci, domin duk abinda Ya zartar dole mu hakura”.
Weesal na kallon Weediyan yadda jikinta ke tsuma, ta ce.
“Ke ‘yar uwa ta, ya za ki takura rayuwar ki akan wani?”
Ta ce, “Ina kaunar sa, akida ta ce kawai ta in auri mai bala’in kudi, amma son gaskiya nake masa. Ina son sa, da ace shi ne mai kudi ba baban sa ba, to da tuni ina gidan sa. Sai dai kash! Da ace na auri dan masu kudi, gwanda na auri mai kudin ko?”
Ta ce, “Um, ke ni na fasa aure a nan kasar, mazan kasar mu sun fi na nan iya tattalin mace”. “Oh, yanzu da ace Musty zai aure ki kin fasa?”
Ta ce, “Ina son sa so ba na wasa ba, don dai me bala’in Naira nake so, kuma shi ma Mustapha ya jima yana fadin ba zai yi soyayya ba, kin san yadda yake gwara kan mata, shi yasa naji me zan ce masa? Ya zo ya ce baya sona in shiga uku, in ya ce baya sona zan mutu ne kawai”.Ta ce, “To Allah Ya kyauta”. Www.bankinhausanovels.com.ng
A haka Haj. Marka ta shigo, ta ce.Biyulle, yaya ne?”
Cikin shagwaba ta ce. “Mamie, kuna ji kuna gani Mamien Musty
za ta tozarta shi?”
Ta ce, “To ya za’a yi mata? Mu duk mun zuba mata ido muga karshen hauka tunda ita bata da kan gado”.
Izzat zaune gaban Computer suna ta hira da Mustapha, ya ce.
“Ina Surayya?”
Ta ce, “Ita da Umma duk suna gaida kai”.
Ya ce, “Kina lissafa ranar auren mu?” Kamar yana gurin ta rufe fuska, ya rubuto.
“Kin yi shiru, to shi kenan tunda kunya kike ji bari in sauka. Ko kin san muna tare da Daddy?” Ta rubutu, “Lah, ya zo gurin ka?”
Ya ce, “Eh, amma duk ya ganni a rame, da ya nemi dalili sai na ce masa tunaninki ne”.Kai masoyi na!”.
“Uhm, ke ya kika gani Sahiba ta?” Ta ce, “Uh, tunda kuna tare da Daddy mu kwana lafiya”.Ya ce, “Dama kin gaji, ki ce za ki gudu”.
Ta ce, “A’a”.
Ya ce, “To ya ne?”
Ta ce, “Kun jima ba ku hadu ba, na san zakuyi hira”.
Ya ce, “Na gano ki, tunda nayi maganar bikin mu ki ke neman hanyar zillewa.
Ahmed ya ce sai ya shirya mana bikin gargajiyar kasar Turkey”.
Ta rubuta masa murmushi, ya ce.”Au ba ki da abin cewa”.
Ta ce, “Sun yi daya, haka Surayya ta ce itama za ta yi (traditional party)”.Ya ce, “Kai mu ‘yan gata ne”.gargajiya”.
Ta ce, “Kaga mu ma garin mu suna bikin Ya ce, “Can Gombe? Au
Ta ce, “Ai ni garin mu sunan sa Kaltingo, cikin Gomben ne”.
Ya ce, “Oh, kice za muyi kallo”.
Ta rubuta dariya, shigowar Daddy ya yi mata sallama. Sanye yake da kananan kaya, amma ya sanya hula tashi ka fiya naci, alama ce ta yayi shirin zuwa masallaci, domin ‘yan kasar Turkiyya
indai za su masallaci to lallai sai sun shiga da hula.
Hakika Mustapha ba haifaffen kasar bane, amma ba ya da bambanci da ‘yan kasar, domin ya shiga cikin su tun yana karami, yana da takardun zama na kasar. A yanzu haka ma babban limamin masallacin juma’a ne, don yana da ilimi na addini sosai, don a nan kasar Turkey ya samu ilimin.
Yau Juma’a, shi ne limamin da zai gabatar da sallah, sanye yake da alkyabba wacce al’adar kasar ne duk limami sai ya sanya.
Ya huduba sannan ya gabatar da sallah,
bayan ya idar ya cire alkyabbar ya rataye wanda su a can haka suke, al’adar su ce rataye alkyabba a masallacin. Haka ya fito ana girmama shi, ya nufi motar sa shi da Sheikh Amert, suka nufi gida.
Hakika ya mayar da lamarin sa ga Ubangiji, ya sanya dangana, haka yana yawan sadaka da kyauta, don duk Ubangiji Ya nuna gaskiya, ya kuma amince duk abinda Allah Ya hukunta shi kenan.
Yau ce rana ta biyu a zaman kotu, tunda suka nufi kotu Mah ke zubar da kwalla, wannan ya ta da hankalin Mubarak, ya ji ya tsani duk wanda ya danganci Haj. Saratu, balles ita kanta. Bai taba tsanar mutum kamar ta ba, don suna zaman su lafiya ta sanya su a ukuba, don ta janyo musu salalan tsiya.
Kamar yadda alkali ya shigo an mike don girmamawa, bayan ya zauna kotu tayi shiru, alkali ya yi murmushi ganin yadda kotun tashi ta cika. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shari’ar farko ta wata mata ce wadda ta – kawo mijin ta akan ba ya ciyar da su ita da ‘ya’yanta, sannan ga fada da duka gami da cin mutunci. A fadar matar ta ce mijin nata ba ya iya zama da kowa lafiya, wannan dalili yasa ta kawo shi kotu don alkali ya raba auren. Bayan kammala wannan shari’ar sai kotu ta
kira Haj. Saratu da Malama Halima da maigidan ta Malam Bala.Alkali ya yi gyaran murya, ya ce. “Malama Halima, kina da lauyan da zai kareki?”
Ta girgiza kai, ta ce.”Bani da shi Ya mai shari’a”.
Ya juya ga Haj. Saratu, ta ce ita tana da lauyan ta Barr. Sunusi Baba Yakasai, nan ya mike. “Ya mai girma mai shari’a, ni lauya ne mai zaman kansa, wanda ofishi na yake cikin garin Kano Zoo road”.Ya kalli Baba Halima ya ce.
“Zan so sanin cikakken sunan ki”.
Cikin muryar kuka ta ce, “Suna na Halima, amma an fi kirana da Mah, shi ne sunan da dana
Mubarak yake kira na”. “Okey, waye baban sa?”Ta ce, “Mai gidana Mal. Bala”.
Ya ce, “Shin za ki iya tuna lokacin da ki ka samu cikin sa?”
Ta yi shiru, can ta ce..
“Shekara ta biyar da aure sannan na tsinci
kaina da samun juna biyu”.
“Kina zuwa asibiti awo?”
Ta ce, “Eh, lokacin ba a damu da awon ba, amma saboda mai gidana yana cikin farin cikin samun cikin sai ya ce zan je asibiti don a kula da cikin, har iyayena suka ki, to da ya dage sai suka ce bamu da kunya. Nayi awo a asibitin Wudil”.
Lauyan ya girgiza kai, ya ce. “To kina nufin a gida ki ka haife shi ko a asibiti?”Ta ce, “A asibitin garin Wudil”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya girgiza kaí, ya ce, “Na gama da ita Ya mai shari’a, ina neman kotu ta bani dama zan kuma yiwa Mal. Bala wasu tambayoyi”.
Alkali i ya ce, “Kotu ta baka dama”.Mal. Bala, zan so ka fadawa kotu cikakken
sunan ka”. Ya ce, “Suna na Saminu, amma kowa ya fi sani na da Bala”.
“Ina so inji ka rike shekarar da aka haifa maka Mubarak, da rana da wata?”Ya ce, “Ehy, zan iya tuna an haifi Mubarak
shekarar 1987, ranar Litinin, wanda ya zo dai dai da watan Dicember, goma ga wata”. Barrister Sunusi ya ce, “Malam Bala, ya kaji lokacin da ka haifi Mubarak?”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG