DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 7 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 7 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng Mun tsaya 

Alkali i ya ce, “Kotu ta baka dama”.Mal. Bala, zan so ka fadawa kotu cikakken
sunan ka”. Ya ce, “Suna na Saminu, amma kowa ya fi sani na da Bala”.
“Ina so inji ka rike shekarar da aka haifa maka Mubarak, da rana da wata?”Ya ce, “Ehy, zan iya tuna an haifi Mubarak
shekarar 1987, ranar Litinin, wanda ya zo dai dai da watan Dicember, goma ga wata”. Barrister Sunusi ya ce, “Malam Bala, ya kaji lokacin da ka haifi Mubarak?”

Ya ce, “Nayi farin ciki mai yawa, shi yasa ma na sanya masa suna Mubarak. Shi kadai ne dana a duniya, bayan shi ban kara haihuwa ba”.
Barrister ya kalli Alkali, ya ce. “Ya mai shari’a, iyakar tambayoyi na kenan,
amma ina son ganin Alh. Abdulmajid. Alhaji Majid ya fito, koshasshen mutum, wanda kana gani ka san Naira da hutu sun zauna, ya tsaya,
Barrister ya ce, “Zan so jin cikakken sunan ka”.
Ya ce, “Suna na Alh. Abdulmajid”. Ya ce, “Alhaji, wai ya abin yake ne? Ma’ana kai ma ba ka yarda danka Mustapha ba danka bane?”
“Bani da wani da a duniya in ba Mustapha ba,shi ne da na guda daya a duniya. Mubarak ba dana
bane, in danta ne ita sai ta nema masa uba”.
Lauyan ya ce, “To iyakar tambayar da zan yi
maka kenanm, sai in hali yayi zan sake tambayar ka.
Amma ina son ganin Mustapha Abdulmajid”. Ya fito sanye da shigar shadda lallausa, ta sha aikin zamani, da ganinsa ka san kamammen matashi

Www.bankinhausanovels.com.ng
ne dan da aka yiwa riko da addini. Barrister Sunusi Baba ya kalle shi cike da tausayawa, ya ce.
“Ya sunan ka?”
“Meye aikin ka?”
Ya ce, “Ni ne (manager) din mahaifina, ina kula da kamfanin sa na gida da na waje”.
“Ka ji abinda mahaifiyar ka ta ce”.”Na ji”.Me za ka ce?”
Ya ce, “Bani abin cewa har sai inda bincike ya gabatar, sai kuma inda shari’a ta yanke”. “To shi kenan iyakacin tambaya ta a gare shi. Ina son ganin Mubarak Bala”.
Shi ma ya fito, matashi ne shi ma nutsatstse,
ya tsaya, aka tambaye shi ya sunan sa?Ya ce, “Mubarak M. Bala”.
Ya ce, “Ka ji rigimar da ake akan ka?” Ya ce, “Na ji”.
“Me za ka ce?”
Ya ce, “Ni ba danta bane, bani da uwar da ta fi Mah (ya nuna mahaifiyar sa) so take ta samu a wahala don ta san mu talakawa ne. Inaga tana da wata nufaka akaina, ni ba danta bane”.
Lauya ya ce, “Iyakar shima tambayar da zan yi masa kenan, Ya mai shari’a. Ina son kotu ta bani lokaci don yin bincike don in kawo karshen shari’ar nan ba tare da kotu ta sha wuya wajen fitowa da duniya a cikin su shin DAN WAYE? A bawa mai
Da Dansa”.
Alkali ya ci gaba da rubutun sa, daga karshe ya daga shari’ar zuwa ashirin da daya ga watan shida, wanda yayi dai dai da watan uku cif  kenan, kotu ta tashi.
Abinka da babban mutum, nan da nan labarin
murdaddiyar shari’ar ya karade ko ina, kowa da
yadda yake tofa albarkacin bakin sa. Mubarak ya tari Mustapha da fara’a, ya ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Barka da safiya, sai ka tafi ba tare da kayi min sallama ba? Kana fushi dani ko?”
Ya ce, “Ko kadan, ina tausayin ka ne, don na san na janyo maka tashin hankali, kunyar ka nake ji”. A dai dai lokacin Mah ta karaso, gabanta ya
fadi da suka hada ido, ta ce. “Dana, ina ka shige?”
Ya ce, “Mah, ina Turkiyya ne, kin san ni dama na fi zaman can”.
Ta ce, “Don Allah kada ka sanya damuwa”.
Ya ce, “To Mah, kinyi ciwo ne?”
Ta ce, “Tashin hankalin da mahaifiyar ka ta
samu ne, ko ina za ta da hakkin mu?” Ya yi murmushi a loakcin Weediya da
Weesal suka karaso, ta ce. “Musty, ashe ka dawo?”  Ya ce, “Um”.
“Okey tana ina?” Ta ce, “Gata can tare da Maman ka”.
Ya ce, “To ina zuwa”.
Sai ya share ya bi motar baban sa.
Weediyan ta tsinci kanta cikin tashin hankali lokacin da aka ce Mustapha ya kai kudin zance, amma da ta tuna karshe za ta iya auren wanda ya kowa kudi a kasar nan, sai ta share, tayi kwafa.
Kai yanzu da tana da kudi ba sai ta taimaki Mah ba, duk da haka sai ta nufi wani gdian rediyo da yake tashe a kasar nan, ta nufi office din wata ma’aikaciya da take wani shiri. Ita kanta Weediyan karatun jarida tayi, don tayi (attachment) a can, sun shaku da ita, duk mai sauraron gidan rediyon ya san muryar ta.
Futuhatulkhar Ahmad, wacce ta amince ita mabudin alheri ce, ga jama’ar ta talaka da mai kudi, domin ta sha fafutukar kwato hakkin mara gata, don takan yayatawa duniya har a samu wanda zai sama maka.
ta kalli Weediyan ta ce.
Kwana biyu?” Ta ce, “Lafiya, wani taimako na zo nema gurin ki”.
Ta warware mata koma, ta ce, “Nima shigowa ta kenan daga kotun”. “To Futuha wanne irin alheri za kiyi musu?”
Ta ce, “Kada ki damu, ki kawo matar za muji yadda zamu yi da kungiyoyi masu kare hakkin talaka, don a yanzu haka munyi waya da lauyoyi sun kai uku, shari’a ce mai sarkakiya, dole sai anyi bincike”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Okey, ni fa ban san gidansu ba, amma zan je gurin Musty”.
Ta ce, “Okey Weediyan, sai na ganku”.
Ko da ta fita bata zame ko ina ba sai gidan su Mustapha, suna farfajiyar gidan shi da abokan sa,yana ganin ta ya ce.
“Kaga matar manya”.
Tayi murmushi, ya mike suka yi cikin gida.
Ta zauna yana zaune, ya ce.
“Ya aka yi matar manya?” Ta ce, “Na zo in nuna alhini na da damuwa ta
akan abinda ya faru da kai ne
Ya ce, “Kada ki damu, komai mujarrabi ne daga Allah”.
Ta matso kwalla, ta ce.
“Kada kaji haushi na, ina jin haushin Momin ka, wallahi duk da yar mahaifiya ta ce ban ji dadin abinda tayi ba, kuma na fi tausayin iyayen su Mubarak, don an cutar da su, an tayar musu da hankali”.
Ta ce, “Ka ga ranar kudi ko, wallahi da ace zan iya yi mata komai sai na tsaya mata”.
Ya ce, “Za ki iya, ina Dr. Aliyu? Ina Alh. S K money?”
Ta ce, “Duk ba irin su ake so ba, mutumin da ba zai yi maka kyautar miliyan hamsin lokaci daya ba ai ba mai kudi bane, ka share su kawai”.
Ta ce, “Ka bani lambar Mubarak”.
Ya ce, “Me zakiyi da ita?”
Ta ce, “Taimakon su zanyi, in kuma baka so
zan fasa, bana son bacin ranka, bana son sanya ka a damuwa”.
Ya bata lambar, ta sanya ta kalle shi.
“Ina amaryar ka?”
“Ko itama in baki lambar ta?”Ta ce, “A’a”.
Ya ce, “Saboda me?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Kawai bana bukata, yanzu ba ita ce a gabana ba”.
Ta mike ta ce, “In an jima ka zo nayi ma masa mai dadi”.
Ya ce, “Zan shigo, amma sai dare”.
Tun a mota ta kira Mubarak, ta ce Weediyan ce, tana son ganin sa su hadu a gidan Hajiya.Ya ce, “Lafiya?
Ta ce, “Lafiya kalau”.
Ya ce, “Sai yamma”. Ta ce, “To, Allah Ya kaimu”. Sannan tayi
gida.Haj. Saratu yadda ‘yan uwanta suka juya mata baya har mijin ta hakan bai karyar mata da zuciya ba, ita dai abinda take ji a zuciyar ta Mubarak danta ne, kuma sai ta karbi danta.
Sun yi (meeting) akan ta, sun nuna mata bata sunan mijinta da take son yi, ta ce ita fa kowa ya kyale ta, ba ta bukatar taimakon kowa. Suka kyale ta, don basu san abin yi ba.
Haj. Hadiza ce ita da Haj. Marka suka isa
gidan Mah, wato Baba Halima, tana kwance. Tana
ganin su ta mike, ta ce.Sannun ku da zuwa”.
Ta kawo muasu ruwa suka sha, Haj. Marka tace.
“Na zo unyi miki jaje, mu kuma taushi zuciyar ki, kada ki damu, ke dai tunda kin san danki ne to me zai daga miki hankali? Duk mu ‘yan uwan Haj. Saratu bamu goya mata baya ba, don mun san bata da gaskiya”.Mah ta ce, “Kin santa?”
Ta ce, “Yaya tace, uwar mu daya uban mu daya”.Ta ce, “To”.
Haj. Hadiza ta ce, “Batun lauya ne, mun yi magana da wani, ku turo min Mubarak. Ta ce, “Na gode, zan fada masa insha Allahu,
zan kuma kwantar da hankali na”. Sun jima suna yi mata nasiha.
Bayan sallar isha Mubarak ya iso kofar gidan
Haj. Lami, ya yi kiran Weediyan a waya, ta ce. “Mubarak, nayi zaton ba zaka zo ba har na taho gidan mu, me zai hana ka karaso?” Ya ce, “Okey, yi min kwatance”.
Ta yi masa, sai ya gano sun taba zuwa da Mustapha, ya iso ya ce ya iso. Ta fito da kanta ta shiga da shi falo, sun zauna sun gaisa, ta kira Weesal a waya ta ce ta kawo wa bako kayan motsa baki, Weesal ta shigo sanye da bakar doguwar riga, tayi nadin Arab, tayi masifar kyau, kyawun su iri daya, kai da ka gansu ka san ‘yan biyu ne.Ta ce, “Lah, kaine?”
Ya ce, “Ni ne”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ajiye masa, ta bashi ruwa, suka gaisa, tace.
“Bari in karasa abincin Daddy, zan dawo”. Ya yi murmushi, haka kawai shaidan yana yawan son tuno Weesal, ta yi masa, tunda ya rasa Suhaila bai taba son kowa ba, amma tun ran da yaga Weesal yaji tayi masa sosai. Ya ce, “Matar manya, lafiya kike nema na?
Ko kin kira ni cika min alkawari?”
Tayi murmushi ta ce, “Kai ma matar manyan
kake kira na?”
Ta ce, “Na kira ka ne akan shari’ar da ake, dama so nake in baka shawara. Idan kun ce za ku dauki lauya akwai kashe kudi, sannan ba lallai ka dauki kwararre ba, akwai hanya da zamu bi a samu lauya wanda zai tsaya Fisabilillahi, ma’ana za muje gurin Futuhatul khair da mahaifiyar ka, inda za ta sanar da abinda ya faru, za mu samu wadanda za su tsaya mana, lauyoyin da suka fi Barrister Sunusi Baba, don gaskiya ya san aikin sa sosai”.
“To ya kike ganin za’a yi?” Ta ce, “Na je munyi magana da ita, sai muje mu kaita ko?”
Ya dago ya kalle ta ya gyada kai, ya ce. “Na gode”.
Ta ce, “Burina in taimaki duk wanda yake cikin damuwa, ban taba ajiye kudi ba wani yana bukata. Bana tara abin duniya don inji dadi, burina bai wuce inga wanda zan taimaka ba. Ina bakin cikin inga babu ko bani da abinda zan bashi, kai ni duk sanda na fita unguwa ba na dawowa da kudi a jaka ta”.
Ya yi murmushi ya ce, “Shi kenan Weediyan, Allah Ya cika miki burin ki”. Ta ce, “Amin”. Washe gari shi ya zo suka fita a motar ta,
suka je gidan Mah, dama Mubarak ya sanar mata. Da fara’arta ta karbi Weediyan, suka gaisa, tayi mata bayani, suka dauki hanyar gidan radio. Weediyan ke tuki, Mubarak yana gefe, Mah tana baya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Duk abinda yake faruwa Weesal bata sani ba, don halayyar Weediyan sai tayi abinta za ra sanar, ba ta neman shawara.
Da suka je office din Futuha ba ta nan, taje gidan yari dauko rahoto, sai da suka yi jiranta.
Da fara’arta ta shigo, ta ce, “A’a, Haj. Weediyan”.
Ta ce, “Hajiya Futuha, mun jima muna jiran
ki”. Ta dubi Mah suka gaisa, ta dan yi mata tambayoyi, ta bata amsa, sannan ta soma daukar Mah, ta ce.
“Suna na Halima, na haifi dana guda daya, mu talakawa ne, bamu da komai, don takamar su basuda kudi take son kwace min dana. Ni ba zan iya rabuwa da dana ba, bamu da komai, bamu da gata,

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE