DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 8 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 8 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Da suka je office din Futuha ba ta nan, taje gidan yari dauko rahoto, sai da suka yi jiranta.
Da fara’arta ta shigo, ta ce, “A’a, Haj. Weediyan”.
Ta ce, “Hajiya Futuha, mun jima muna jiran
ki”. Ta dubi Mah suka gaisa, ta dan yi mata tambayoyi, ta bata amsa, sannan ta soma daukar Mah, ta ce.
“Suna na Halima, na haifi dana guda daya, mu talakawa ne, bamu da komai, don takamar su basuda kudi take son kwace min dana. Ni ba zan iya rabuwa da dana ba, bamu da komai, bamu da gata,

bamu da wanda zai tsaya mana”.
Sai ta sanya kuka, ta ci gaba da cewa. “Ku taimake ni kada ta raba ni da dana”.
Kukan Mah ya sa ba a jin abinda take cewa, Futuhaltulkhair ta ci gaba da cewa.
“Wannan muryar wata baiwar Allah ce da ta zo cikin mummunan hali, saboda yadda ake so a raba ta da danta dan shekara 27 da haihuwa, kuma shi daya tal ta haifa. Za mu ci gaba da kawo muku yadda shari’ar take tafiya.
A ranar aka sanya shrii, kasancewar shirin na da farin jini, kuma dama duk yawanci al’umma na saurarar gidan rediyon. Nan da nan masu hannu kan lamarin suka riga kawo taimako, kafin lokaci an samu kwararan lauyoyin da suka san aikin su har mutum uku, kawai ranar shiga kotu ake jira.
Mustapha shi da Ahmed da yake tare suka iso Nigeria, suka isa gidan su Izzat, yayi mata (tex) gashi nan, aka ‘shiga da su har falo. Www.bankinhausanovels.com.ng
Riga da siket ne na atamfa a jikinta, dinkin ya yi mata kyau sosai, ta sa katon mayafi. An shirya musu çima iri-iri, Surayya ta shigo, ta ce.
“Ah, yau ga angon Ya Izzat”. Ya yi murmushi, ta ce, “Sannu da sauka”.
Ya ce, “Ya muka same ku?”
Ta ce, “Lafiya”.


Ta mike ta fita, Izzat ta zame ta gai da Mustapha, sannan ta gai da abokin sa, bai jin Hausa, amma don gaisawa yana fahimta.
Ta ce, “Sannu, dama za ka zo baka fada min
Ya kalle ta tana duban bakin sa, ya ce.
“Wani dalili ne mai karfi ya taso mu”.Ta ce, “Uh”.
Ahmed cikin yaren su ya ce. “Wannan yarinya ina ganin akwai yiwuwar in anyi mata aiki ta warke, tunda gashi tana iya “Nima ina da wannan tunanin, nayi magana”.da  wani likitan kunne a can kasar ku”.Ya ce, “Yauwa”.
Bata san me suke cewa, ga kurma da zargin masu kunne, saboda haka sai zuciyarta ta jagula, sai taji bata ji dadi ba sam, ta ce.
“Mustapha, me kuke cewa? In bana jin ku Allah Yana jin ku, zance na ake?”
Ya yi dariya ya ce, “A’a, cewa yayi bayan bikin mu in kaiki asibiti, yana ganin kila ki ji nan gaba”.
Ta ce, “In jirgi ya shige ina jin karar sa”. Ya ce, “To kinji ma”.
Sai tayi murmushi.
Hira suka yi sosai, Ahmed ya zama dan kallo, don gaba daya kallon su yake har suka yi sallama suka kawo mata tsaraba. Ahmed ya yi mata kyautar kudi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da daddare Umma ta fitar da tsarabar da Mustapha ya bawa Izzatu, tana nuna masa ya kalli kayan shekeke, ya ce.
“Bana jin auren su zai yiwu”. Ta ce, “Saboda me?”
“Saboda naji ance mahaifiyar sa ta ce ba danta bane, shi kuma uban ya ce bashi da dan da ya fi shi. Ta ya za mu bawa ‘yarmu dan da bashi da asali?”
Umma ta ce, “A ina kaji zancen? Karya ne
irin na masu kushe, aure ne ni ina ganin Izzatu da shi
ta dace”.”Kamar ya?”
Ta kalle shi, “Ka san komai”.
Ya zaro ido waje, ya ce, “Ban aminta da maganar nan ba”.
Ta ce, “Bana so a wulakanta dan mutum, ina jin haushi, hakika ba zan iya hana shi ‘yata ba ko a bola aka tsince shi”.
“Saboda me? To ni ban yarda ba, matukar kinga na bashi yarinyar nan, sai an kammala shari’arna gano shi din DAN WAYE?” Ya fice. A zaune take tana tunani, Surayya ta kunna
radio aka soma shirin da take son ji. Ai kam sai ga magana, Umma tayi salati, ta ce.
“Oh, ashe gaske ne?”
Anan takes ta sanar da Surayya ta ce. “Oh, naji zancen ban yi tunanin Mustaphan Izzar bane”.
Suka zauna suna mai da maganar.
Mustapha ya shiga damuwa fiye da ta da, domin kowa zancen yake. Ya samu Daddy ya ce. “Ni fa zan koma, in lokaci yayi zan dawo”.
Ya ce, “Dama zaman naka bashi da armashi, ya kamata ace ka tafin ko hankalin ka ya fi kwanciya”, Mustapha da Alpha da Ahmed suna shirin
fita, sai ga mota. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haj. Lami ce Weediyan ta kawo ta, tace “Mustapha, na ce ka zo ka ki, wato fushi kake
damu? Kana so ka datse zumuntar mu? Wallahi Tallahi har yanzu ba a yi jikan da nake so kamar ka ba, ko ba jinin mu bane kai mu muna son ka, kuma ba zamu bari ka kufce mana ba”.
Weediyan ta ce, “Musty, wallahi muna sonka, kai jinin mu ne, kawai rudin shaidan ne, ko ince kururuwar shaidan. Duk hanyar da zanyi don ganin muna tare”.
Ta ce, “Wallahio ba zan iya misalta maka yadda nake jin abin nan ba, amma na barwa zuciya ta”.
Ya ce, “Hajiya, ba naki zuwa wajen ki bane, maganar gaskiya ke mahaifiyar Mamie ce, ni kuma ta ce ni ba d’anta bane, to ame zan je inda kuke? Ai in na danganta kaina da ku ban cika dan halak ba. Kiyi hakuri, so nake in san ni DAN WAYE? in bata fada min ba yadda ta gano ni ba danta bane haka za ta nuna min iyayena”.Kuka sosai Haj. Lami take yi, ta ce.
“Shi kenan Saratu ta janyo min masifa, don in na rasa ka zan iya rasa raina. Wallahi ina son ka, domin ban taba son jika kamar ka ba”. Ya ce, “Hajiya, wallahi nima ina son ku, don da ku na bude ido. Saboda haka kada ki damu, ni
jikan ki ne”.
Ta ji dadi har cikin ranta, ta ce. “Na san halinka, kana da fushi, don Allah
kada ka dauki hukunci a hannun ka, kullum addu’a nake Allah Ya fidda mana gaskiya”. Ya ce, “Amin”. Da yamma ya isa gidan su Izzat, saboda ta ce
ya zo tana neman sa sakamakon dokar da Abban su
yaba ta, na ta janye soyayyar sa, inda ta nemi ta san dalili, ya ce saboda wai bashi da asali.
Hankalin ta a tashe ta tuno itama bata da tushe, don har yanzu bata da tartibin uba, wannan dalilin yasa ta cikin damuwa, ta nunawa Abba tana son Mustapha za ta aure shi haka, don da shi da ita sun dace.
Lokacin da ta fito ya kalli tashin hankali a kwayar idon ta, falo ta kaishi, ta durkushe kasan kafet ta soma rusa kuka.
Ya dube ta ya dan bigi kafadar ta, ta dago ido, ya ce.
“Lafiya kike kuka?” Ta ce, “Ina kuka saboda tausayin ka, da gaske
ba dan Momie bane kai? Shin kai DAN WAYE?” Ya ce, “Wannan maganar na gaban Alkali, ba Www.bankinhausanovels.com.ng
zan ce komai ba, amma yanzu waye ya fada miki?” Ta ce, “Abbana, ya kuma ce maganar auren mu babu ita, an jingines ta har sai sanda alkali ya kare shari’a”.Ta dube shi hawaye na zuba cikin idanunta, tace.
“Ka taimake ni, ina ji a raina in na rasa ka zan iya rasa rayuwa ta, Mustapha ina sonka, son da ba zan iya rabuwa da kai ba. Ina so ka sani Izzat na sonka, irin son da ba zan iya kwatanta shi ba, ni zan iya mayar maka madadin iyayen da ka rasa. Ba zan iya rabuwa da kai ba, zan zama bango abin jinginar ka. Ni babu ruwa na, ina sonka haka ko daga sama ka fado, ballantana na san cewa kai ma da ne kamar kowa”.
Ta gyara zama, ta ce, “Haba Mustapha, watanni nawa ka dauka cikin wannan bacin ran, amma ba ka gaya min ba? Ka sanar daniba ba a boyewa abokin kuka mutuwa, ina son ka haka Mustapha, saboda na san irin ciwon da mutum kan ji a lokacin da aka ce bashi da wani bangare na iyaye, domin nima ina da irin wannan matsala wacce har yanzu ba ai min maganin ta ba”. Ta sake rushewa da kuka.
Shi kam yayi shiru ya kasa cewa komai, idanun sa sun kada sunyi jajir saboda ɓacin rai. Tayi kuka sosai, ya kalle ta yana motsa bakin
sa inda za ta gano me yake cewa, ya ce.
“Kada ki damu, ki koyi hakuri ga kaddara, komai na Allah Yana da iyaka kinji mata ta?” Duk da kuka take sai da tayi dariya, ya ce. “Yauwa tawan, ki daina kuka. Ki sa a ranki,
wata daukakar ce, kuma wami alheri ne. Ke dai ba
kina sona ba?” Ta ce cikin muryar kurmantaka, ta ce.
“Ko kai DAN WAYE ina son ka haka, zan
zauna da kai, in haifa maka kyawawan yara irin ka,
wanda za suyi alfahari da samun uba na gari. Mijina
kada ka damu, na yarda da kaddara, na san hakuri haske ne, na sani wata rana sai labari”.
Ya kalli agogo ya ce. “Gobe za mu wuce kinji my wife?”
Ta kalle shi kallo mai dauke da tsantsar so da tausayi, ta cė.
“Umma na son magana da kai”. Ya ce, “To je ki kice gani”.
Ta fice, can ta dawo ta ce, “Zo mu shiga”. A zaune yake kasan kafet kansa na kasa, ya zame ya gai da ita cikin girmamawa, inda aka san siriki kan yi a kasar Hausa.
Ta ce, “Na kira ka ne Mustapha saboda in jajanta maka abinda ya same ka, ina so kada ka damu zuciyar ka bares ciwon damuwa ya kama ka. Hakika babu wani bawa madaukaki da ya wuce jarrabawa a rayuwar sa, don Allah ka dauke ni matsayin uwa ba suruka ba. Izzatu ita ce babbar ‘yata, ni ce uwar ta kuma uban ta, na baka ita, kuma zan rike ku kai da ita a matsayin ‘ya’ya. Kayi hakuri Mustapha, komai zai wuce, komai ya samu bawa da sanin Allah.
A lokacin da naji labarin hankali na ya tashi, wanda sai da ya dawo min da tsohon bikin dake jikina”.
Sai hawaye ya sirnano mata, ta goge su da hijabin ta, ta ce.
“Mustapha, kayi amfani da shawarwari na”.
Ya ce, “Na gode Umma”. “Bikin ka kamar yadda aka ce ba za a fasa ba,
saboda haka ka ci gaba da shiri”.
Ya ce, “Ai gwanda a bari in hankali na ya kwanta sai ayi komai cikin kwanciyar hankali”. Ta ce, “Shi kenan, na gode”.
Ya yi sallama da ita ya fito, Izzatu tayi masa
rakiya har gurin mota. Www.bankinhausanovels.com.ng
A zaune Alhaji Abdulmajid yake rike da jarida a hannun sa yana dubawa, a lokacin Mustapha ya shigo. Ya ajiye jaridar ya ce.
“Boy, dama neman ka nake”.
Ya zauna yana fuskantar Daddy, ya ce. “Lafiya Daddy?”
Ya ce, “Ina so zanyi bincike akan yarinyar da kake nema, labari ya zo min cewa shegiya ce bata da uba, saboda haka zanyi bincike akan lamarin, don ba zan cakuda jinin ka da gurbataccen jini mai dauda ba. Bata dace da kai ba, domin kai da ne wankakke, na ciyar da kai da halak, na shayar da kai da halak, saboda haka ina bukatar jikoki tsarkaka daga gare ka”.
Ya muskuta cikin jin furucin mahaifin sa, yace
“Daddy, wa ya fada maka?”
Ya ce, “Yan sa ido, ‘yan gaza gani. Wani ne ya zo wai shi Mal. Sallau na Kaltingo ya ce yayan mahaifiyar ta ne, ya ce ganin girma na da yake shi ya sanya ya fada min cewar Izzatu shegiya ce, bata da cikakken uba, ya ce inyi bincike, kuma ince ta san Sallau Kaltingo? Zan ji me zata ce min”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya girgiza kai, lallai biri yayi kama da mutum, sai dai a yadda yake jin son Izzatu shi ba zai fasa aurenta ba, don da ita da shi dan juma ne da dan jummai.
“Ka ji abinda na ce?”
Ya ce, “Naji Daddy, wannan ba shi ne abinda ke gaba na ba, ni duk nafi son inga karshen shari’ar mu”.Alhajin ya yi murmushi ya shafa kan sa, yace.
“Boy, kada ka damu, tatsuniya ce kawai Haj. Saratu take, kurunkus kawai nake jira inji”. Ya ce, “Daddy, ni kuma na yarda ba ita ce uwa ta ba”.
Wata irin zabura Alhaji yayi, ya ce. “Saboda me?”
Ya ce, “Saboda uwa mace ta fi kowa nuna kauna da tausayi akan abinda ya samu danta, ni

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE