DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 9 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

 DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 9 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

Ka ji abinda na ce?”
Ya ce, “Naji Daddy, wannan ba shi ne abinda ke gaba na ba, ni duk nafi son inga karshen shari’ar mu”.Alhajin ya yi murmushi ya shafa kan sa, yace.
“Boy, kada ka damu, tatsuniya ce kawai Haj. Saratu take, kurunkus kawai nake jira inji”. Ya ce, “Daddy, ni kuma na yarda ba ita ce uwa ta ba”.
Wata irin zabura Alhaji yayi, ya ce. “Saboda me?”
Ya ce, “Saboda uwa mace ta fi kowa nuna kauna da tausayi akan abinda ya samu danta, ni

kuwa na rasa wadannan abubuwa guda biyu a gare ta, amma na kai lamarina hannun Allah Buwayi Gagara misali”.
Ya ce, “Kai dai kayi addu’a,
Mubarak ya mai da gidan su Weediyan gidan hirar sa, domin sun shakau da Weesal, don a yadda ya kula kamar ta amince da shi, duk da dai bai wani fito ya ce yana sonta ba, itama kuma haka, amma suna yin zanen su cikin hikima da iya taku. Weediyan kuwa ta mai da hankalin ta kacokan kan lamarin shari’a, domin har sun saba da Mah, haka nan jinin su ya hadu, don in tazo zasu yi hira sosai.
Weediyan yarinya ce ‘yar gayu, gata da son kyautatawa wanda ta fi. Haduwar su da Mah tayi mata alheri mai yawa, haka Mal. Bala, ita haka Allah Yayi ta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mustapha ya kasa bacci sai juyi yake, har Ahmed dake gefe ya ja tsaki, ya ce.
“Ni fa ka hana ni bacci, meye matsalar ka?” Ya ce, “Babu”.


Ya janyo wayar sa ya soma matse-matse, sai
ga (text) ya shigo. Amincin Allah Ya tabbata ga masoyi na, na
kasa bacci, ina ji a zuciya ta kana cikin damuwa,
kuma ba ka yi bacci ba. Murmushi yayi ya rubuta. Ban yi bacci ba, tunanin ki nake. Ta ya kika ta yaya
gane ban yi bacci ba? Tana  karantawa da a kwance take, sai ta mike zaune, ta rubuta.
Ka san soyayyar gaskiya ba ta buya, ni da kai mun zama jini da tsoka. Ina ji a jikina wani abu ya hana ka bacci, domin nima na kasa bacci. A duk lokacin da kake bacci jikina yana bani miji na bacci yake.
Lokacin da ya bude (text) din yana
karantawa, dariya yayi, ya ce. Na ji, gobe zan fada miki me ya hana ni bacci, yanzu in na gaya miki za muyi,,,,, saboda haka mu kwana lafiya”.Sai ya kashe wayar sa.
Haj. Saratu tana zaune a falo ita da lauyanta
suna tattaunawa, ya ce. “Hajiya, a gaskiya wannan shari’ar tamu tadan rikita ni, saoda ke baki da takardun haihuwar Mustapha, baki da (date) din akan ki, akwai tarin kalu bale”.
Ta ce, “Ba za a rasa ba, sai dai yana gurin Www.bankinhausanovels.com.ng
Alhaji, shi kuma ba zai taba bani duk abinda ya zama zan samu nasara ba, saboda idonsa ya rufe da so da kaunar Mustapha. Ya ce, “Ai ba komai, zan tambaye shi a kotu,
kuma Alkali yasa ya kawo dole”. Tayi murmushi ta ce, “Na gode Barrister”.
Ya mike yayi mata sallama, ta raka shi har gaban motar sa, a lokacin ta ajiye masa rafar kudi, ta ce. “Ka sha mai, kai dai ka tsawaita bincike,Allah Ya taimake ni”.
Ya ce, “Amin Hajiya”.
Da safe Izzat na bude wayar ta (text) din Mustapha ne ya shigo, inda ya rubuta. “Kin san malam Sallau na Kaltingo?”
Ai ko tana mikewa ta karasa da gudu ta ce.
“Umma, shi ma za a hana shi ya aure ni, anzo an fada masa”.
Ta ce, “Allah Umma in ban auri Mustapha ba mutuwa zanyi wallahi, wayyo Umma ta, me yasa dan uwanki yake min haka? Saboda me? Da wanne dalilin?”
Ta ce, “Kiyi hakuri, shi aure nufin Allah ne, matar mutum kabarin sa. Na san ‘yan ubanki ne da kwadayin abin duniya yasa shi yake haka, babukomai, bani wayar ki in kira Mustapha”. Ta jima tana (ringing), ya san kila Surayya
ce, saboda haka a lokacin ya dauka, ya ce. “Ya aka yi Surayya?”
Ta ce, “Ba ita bace, ina son ka zo za muyi magana”.
Ya ce, “Kash! Umma, gani a filin jirgi mun wuce Lagos, saboda ta can zan tashi. Lafiya?” Ta ce, “Shi kenan, Allah Ya sauke ku lafiya”.Ya ce, “Amin”.
Ta kalli Izzatu ta ce, “Ya tafi can Turkey, yanzu jirgi zai hau ya tafi Lagos, daga can za su tafi”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Umma na rasa shi, kila ba zai aure ni
ba shima, shi yasa. Na tsani yin soyayya, don Allah
Umma ki ki taimake ni kada shima ya subuce min”.
“Kada ki damu, ba za ki rasa shi ba, zan sanar da shi gaskiya. Kada ki damu, yana sonki, insha Allahu za ki sadu da mahaifin ki, bana so ki dawo min da bara bana, kiyi hakuri, domin hakuri magani ne”.
Izzat ta juya zuwa dakinta zuciyar ta tana zafi, ba zata iya rabuwa da Mustapha ba, don tana jin sonsa na kara shiga zuciyar ta, rabata da shi yana nufin rabuwar ta da numfashin ta. Ta sani ta so Izuddeen, amma ba kamar yadda take son Mustapha ba, balle Sufyan da taso shi son kuruciya. Hakika za ta jingine soyayya, za ta nufi garin su, za kuma taje gidan yayan Umman ta, tana so ta san gaskiyar lamari, ita din ‘yar waye?
Ta kwanta a gado idanunta na zubar hawaye, a haka Surayya ta shigo ta ce.”Lafiya?”
Izzatu ta girgiza kai ta ce.
“Fada min matsalar ki”.
Ta ce, “Mustapha, shi ma zan rasa shi, anje an
fada masa bani da asali”.
Cikin tsananin fusata ta ce, “To shi ma da ake tababa akan asalin sa ai sai ki fada masa ke da shi kun dace, akan sa za ki zubar da hawaye? Kada ki damu yaya ta”.
Ta ce, “Dole in damu, ana nufin ba zanyi aure
a duniya ba saboda kawai bani da tartibin uba? Ku
kunji dadin ku, to ni me na yiwa Umma ta haife ni?”
Kuka take sosai, hankalin Surayya ya tashi, tace.
“Wallahi na yarda da Umman mu, ta haife ki da aure, kuma ke ‘ya ce da take so, don ta sha fada min ta fi sonki da kowa”.
“Eh, tunda ta yiwa rayuwa ta illah dole ta fi sona”. Ta fada cikin yanayi na kuna da damuwa. Surayya ta kama hannun ta suka yi (pacing) juna, ta ce.
“Yar uwa ta”.
Tana duban bakinta, ta ce.”Kiyi hakuri, kiyi tawakkali, domin in Mustapha mijin ki ne ruwa da iska, mutum ko aljan babu wanda ya isa ya hana. Don Allah kiyi hakuri”.
Ta dube ta ta ce, “Allah, Allah ba zan hakura ba in shegiya ce ni, ta fada min ko ma mece ni. Na kai munzalin da zan yarda da kaddara walau mai kyau ko mara kyau”.
“Haka ne, amma ko ma dai meye hakuri halin Ma’aiki ne, in kinyi shi za ki tsince shi a gaba”. Ta kau da kai ba tare da ta ce komai ba.
Mustapha da Ahmed sun sauka babban filin jirhin kasar Turkey, suna saukawa daga jirgi suka tarar Muret ya zo daukar su. Cike da doki suka yi gaisuwar su ta gwara kai, ta dauke su kai tsaye gidan su Ahmed suka isa. Mahaifiyar sa Mefva ta tare su tana nuna farin cikin ganin su. Www.bankinhausanovels.com.ng
An zagaye su ana murna tare da tambayar su sun iso lafiya?
Kanwar Ahmed Mai suna Zaynap ta shirya musu abinci, sai da suka ci suka koshi suka huta, sannan suka nufi gidan Mustapha. Gidan a share yake kamar yana ciki, masu yi  masa aiki suka tare shi da murna. An shirya komai, wanka yayi ya kwanta, duk kwakwalwar sa ta toshe, ya ma rasa yadda zai yi. Amma ya san komai na rayuwa Allah Shi Yake tsara maka, ya sani yana son Izzat, to amma in har Daddy ya hana shi zai hanu.
Shi ke nan rayuwar sa ta lalace, to ya zai yi? Sai ya ji zuciyar sa ta karye, yana jin tsanar Momi, har abada ya rabu da îta, ina za ta taba daraja a idon sa?
Hakika ya ma rasa inda zai aje kansa, shin shi DAN WAYE? Kawai sai kuka, ya jima yana zubar da hawaye, ya san tun yana yaro yake cikin kyara da tsanar mahaifiyar sa,  bai taba -zaton za ta ita tozarta shi ba.
Lokaci daya ya soma tunanin irin matsanancin halin da ya tsinci kansa a ciki, tun lokacin da ya tsinci kansa a mutum ba ya jin dadin zama da ita, farin cikin sa yana tare da mahaifin sa ko kakar sa.
Ya taso ya san mahaifiyar sa na fama da matsalar ciwon damuwa ko shafar aljanu ne bai sani ba, hakika in aljanu ke kanta to tabbas ba sa jituwa da shi.
Kyarar da take masa da tsangwama, shi yasa ya taso zuciyar sa a bushe, sam ba ya iya dagawa kowa kafa, ya taso da fada da zafin zuciya, saboda yadda ake kyarar sa.
Lallai shi ma ya amince Momi ba mahaifiyar sa bace, to wace ce mahaifiyar sa?
“Allah Ka sada ni da iyaye na ko da sun fi kowa talauci ina son su, kuma zan kaunace su”. Ita ko Momi kallon ta ya dinga yi ita da shi har abada.
“Izzatu zaune jikin Umma, idanunta jajir, ta ce cikin muryar kurumta. “Umma, ki taimake ni ki sanar dani wace ce
ni? Kinga dan uwanki shi yake so ya hana ni aure
ke kinyi auren ki ni yana son kassara rayuwa ta. Dan
uwanki ne Umma, kiyi masa magana ya fita daga
harka ta, in ba haka ba zan bushe masa kyandir”.
Umma ta dube ta fuska a bace, ta ce..
“Ke Izzatu, kina da hankali? Ni na haife ki ko ke kika haife ni?”
“Ke ce kika haife ni kike so ki tozarta ni, kin haife ni ba tare da aure ba. Na kai munzalin aure yaki samuwa, shin ba ki tausayi na? Ga nakasa ga rashin miji?
Ba wai masoyi na rasa ba illa bakin cikin dan uwanki da yake son ganin baya na. Na fada miki dole in san ni din ‘yar waye? In kin haife ni ta hanyar banza ko ta hanyar tsautsayi duk ba wani
sabon abu bane, amma ya zama dole in san waye baba na? Don komai ya same ka a duniya ba akan ka aka fara ba, saboda haka ni ba zan damu da yadda nazo ba. Kice wane ne baban ki ni zan je gare shi, ki taimake ni”.
Umma ta rasa bakin magana, amma ya zama yau ta warware mata komai, amma kuma kuka dole take tana takaici yau Izzatu ta turke ta.
Izzatu ta ce, “Umma ta, in kinyi min haka kin
danne min hakki, ki taimake ni”. “Zan sanar dake, amma yanzu zuciya ta tana zafi, ki bari da daddare ki same ni, zan sanar dake asalin ki, kinji?”
Suhaila hankalin ta ya kwanta, domin mijinta mutumin kirki ne, ya kuma san mutuncin dan Adam, damuwar ta daya tana da zargin yana fama da damuwa sosai.
Sanye take da kananan kaya, tai masifar haduwa. Ta janyo jiki jikisa ta sanya dan yatsanta daya ta dago fuskar sa, ta ce.
“Dear, me ke faruwa da kai?”
Ya kakalo murmushi ya ce, “Ba damuwa”.
Ta ce, “A’a Dear, jiya mun je asibiti likita yace kana saka damuwa”.
Duk yadda ya so ya boye ya ki boyuwa, sai
ya runtse ido yace
“Kiyi min addu’a mata ta, addu’ar ki kaifiyyan ce, amma ina damuwa, ina rasa jin dadi na”. Ta ce, “Dear, me ke faruwa da kai? Damuwar ka tawa ce”.
Ya ce, “Ina damuwa fiye da shekaru ishirin, Allah Ya san damuwa ta tana da yawa, amma kullum addu’a ta Allah Ya yaye min damuuwa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Haba Dear, shekaru da yawa haka, tun kan a haife ni fa? Haba, kada ka damu, komai ya samu bawa da sanin Allah”.
Ya ce, “Haka ne”.
Ta shiga inganta masa rayuwar don ta
mantar dashi abinda yake damun sa.
Weediyan ita da Mah suna hira Mubarak ya
shigo da rake a leda an yanko shi, ya ce.
“Mah, ga rake”.
Tayi murmushi ta ce, “Allah Sarki Mustapha, shi ne mai son rake”.
Weediyan ta ce, “Shan rake ne da shi Mah?” Tayi murmushi ta ce, “Ai wato idan suka hadu su biyun suna sha cikin ki sai yayi ciwo”.
Mubarak ya ce, “Mah, ai ni na daina shan rake saboda na rasa kaunar amini na wanda yaso ni don Allah, ina takaici ina jin haushin Momi da ta

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE