DAN WAYE CHAPTER 1 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? CHAPTER 1 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

hankali yake tafiya cikin sanyin
jiki, da alama ya sha wuya,
zai sanya ka san
yanayin sa nutsatstsen matashi ne.
A nutse ya karya lumgun da ya shiga, a
dai dai lokacin wata fitinanniyar mota ta sako kai
cikin lungun. Yanayin yadda ake jan motar da
yadda sauti yake tashi shi ya tabbatar masa da
cewa matashi ne dan uwan sa, da yake kallo
Daya ya yiwa motar ya mai da kansa, ya ci gaba
Da tafiya.
(Horn) din da motar take yi ya sanya shi
kallon me ake wa hon din? Ai kuwa wata
matashiya ya gani tana tafiya a nutse, don yadda
ta nuna sam ba ta ma san matashin na yi mata
horn ba.Can sai ya ga matashin ya fito a zafafe ya wanke
mata fuska, ta kuwa dafe fuskar ta tana mai
kallon sa. Ta zuba masa ido, ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Me na yi maka ina cikin tafiya za ka
mare ni?”Tuni idanun ta Sun sonma tsiyayar hawaye,
kan ka ce meye wannan duk mutane sun kewa
su.
Dai dai lokacin da ya soma masifa, ya ce.
Shegiya, da na sani ma in take ki in taka
banza, shashasha kawai”.
Ta ce, “Oho, ni ban san abinda kake cewa
ba, illah iyaka na san ka zalunce ni, don ban san
me nayi maka ba. Ina da matsala a kunne na don
bana ji sam”
“Ka ji ‘yar rainin hankali, za ki ce wai ba
kya ji, gashi nan kina magana rambadadau”.
Mubarak dake tsaye yana kallon su ya
taka ya ce.
“Abokina ba haka ake yi ba, saurin hannu
yakan kawo da na sani, bai kyautu ba”.
Ya kafa mata idanunsa yana kallon ta, ya
Soma magana yadda za ta
fahimta, ya ce.
“Ke kin san kina da matsala me ya sanya
kika fito ke daya?”
Ta ce, “Nayi jiran Surayya ba ta zo ba, ni
kuma na tafi. Wannan ba shi ne karon farko ba,
amma ya zalunce ni, domin marin mace
kaskanci ne. A ka’idar Musulunci ba a marin
fuskar mace, jikin ma ba don duka aka yi shi ba,
sai dai na barshi da Allah”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wancan mutumin ya ce, “In ba ki barni da
Allah ba ya zakiyi? Yar rainin hankali”.
Ya dawo da hankalin sa kan Mubarak, yace
“Malam ba a yi min irin abinda ka yi min
yanzu, don na tsani shisshigi. Ke kuma ki kiyaye
ni, wallahi na sa mota na tattaka ki”.
Mubarak ya kalle shi cikin mamakin
furucin sa, yace


“Kayi hakuri, ban san abin zai bata maka
rai ba. Ke kuma maza muje in raka ki, saboda
gudun faruwar irin haka”.
Suka juya, mutumin ya ce.
Nonsence) dama kana son sa kai ne, me
zaka yi da musaka yadda Allah Ya yika da kyau
haka?”
Mubarak da Izzatu suka ci gaba da tafiya,
zuciyar ta na suya saboda takaicin abinda aka yi
mata.
Sun yi tafiya mai nisa suka karaso wani
tafkeken gida, ta juyo ta ce.
“Na gode, na Allah ba sa karewa, gashi ka
kawo ni har gidanmu”.
Ya ce, “To sai anjima”.
Har ta shige ta juyo ta ce.
“Kai wanne irin mutum ne? Ba za ka fada
min sunanka ba?”
Ya ce, “Ni suna na Mubarak”.
Ta ce, “To Mubarak, sai anjima”.
Ta juya ba tare da ya tambayi sunan ta ba,
ta shiga gida da sauri. Tana shiga ta fadawa
Ummanta, ta ce.
“Kinga yau ma na sha mari”.
Ta ce, “Kiyi hakuri, ita rayuwa haka take
“Amma Umma mutane basu da adalci..
Nan ta fadawa Ummanta abinda ya faru,
Surayya ta shigo ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Izzatu.
Ta ce, “Kinga kyale ni, ai kin san zan fita
ki ka fice”
Ta ce, “Kai, kin manta ina da (text) yau?
Kiyi hakuri, afuwan kinji ‘yar uwa”.
Ta mike tayi falo, don duk suna tsakar
gidan.
Mubarak yaro ne matashi, dan shekaru
ishrin da bakwai. Yaro ne salihi, na gari, wanda
a duk fadin unguwar su in za a fadi matashin
mutumin kirki za,a bashi na farko ba to zai
shiga na biyu. Ya samu tarbiyya gurin iyayen sa,
wanda suka dauki so da kauna suka dora masa,
ko don shi daya suka haifa ne? oho.
Iyayen Mübarak ba masu kudi bane, masu
rufin asiri ne, don Mubarak yayi (digree) dinsa,
don mahaifin sa mutum ne me son sai ya ga
Mubarak din yayi ilimi sosai, an kuma yi sa’a
Mubarak din mai kwakwalwa ne.
Sallamar da yayı ya sanya mahaifiyar Sa
wacce mutanen ungwuwar suke kira da Marmo
Mubarak, shi kuma Mubarak din yana ce mata
Mah. Ta taso tana cewa.
“Kai yaron nan kayi nisan kiwo, ina ka
shiga ka sanya zuciyata ta kasa zama guri daya?”
Ya kwashe da dariya, ya ce.
“Mah, sannu da gida”.
Yai dariya ya ce, “Na girma fa yanzu Mah,
a yanzu na kai munzalin da zan kula da ku”
Ta washe baki ta ce, “To Mubarak. Yaya
an dace?”
Ya dan yi jimm, sannan ya ce.
Kaiya Mah, rayuwar kasar nan na bani
mamaki. Ki duba kiga kyau irin na sakamako na,
wai amma na rasa aiki. A Nigeria ba a duba
cancanta illah a duba wa ka sani, wanda yake ya
san wani”
Mah, ta ce, “Uhm, kai dai dan nan bari
Insha Allahu sai ka sami albarkacin Annabin
Rahma”.
Ya ce, “Amin”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Bari in kawo maka abinci”.
Ya mike, “A’ah Ma, bari in dauko da
kaina, ai yanzu ni ya kamata kuma na dinga yi
miki kina zaune. Ke dai Allah Ya bamu kudi in
kai ki Makkah, har Madina'”
Ta ce, “Allah Ya nuna min”
Shigowaar Malam Bala ta sa suka amsa
sallamar sa, ya shiga. Mah tai saurin dauko
da sabuwar tabarmarta ta shimfida masa ya zauna,
ya cire babbar rigar sa, Mubarak ya karba ya kasha
ciki. Ita ko Mah ta soma yi masa fifita.
Malam Bala ya dubi Mubarak ya ce.
“Mutumina ya aka yi? Ina fatan an dace?”
Mubarak ya kada kai, ya ce.
“Uhm Baba, yau da kaga wuyar da na sha
wallahi da ka tausaya min. Tun kokon safe
cikina bai ga komai ba sai yanzu nake niyyar ci”.
Malam Bala ya dubi matar sa ya ce.
“Halima sarkin kokari, har kin dafa”.
Ta sunkuyar da kai tana dariya, yayin da
ya ci gaba da sa mata albarka.
Ya ce, “Na fita ban bar komai ba ina
tunanin ya za a yi, sai gashi har kinyi”.
To Malam meye amfanin neman da
nake? Dama don kai da wannan dan nake yi”.
Ya ce, “Allah Ya biya ki”.
Ta ce, “Amin”.
Shi kuwa Mubarak addu’ar sa daya, Allah lin
Ya bashi aiki ya sanya iyayen sa suji dadi.
Mah ta tashi ta kawo wa malam’ abinci.
tare da Mubarak suka ci suka koshi, suka kuma
kama hira.
Hakika iyayen Mubarak suna Son sa
soyayya mai zafi, don ko zarzabi in Mubarak
yayi duk sai sun rame. Allah kuma Ya taimake
su yaro ne nutsatstse, don ba ya son yaga abinda
zai taba mutuncin iyayen sa.
Sun jima suna tattaunawa akan neman Www.bankinhausanovels.com.ng
aikin da Mubarak din yake yi, har yanzu shiru.
A firgice ya farka daga baccin da yake yi,
ya tofa addu’ar da Annabi Yai umarni da ayi idan
kayi mummunan mafarki, don mafarkin da yayi
dole ne ya kira shi da mummunan mafarki.
Ya zuba kafafun sa kasa yayin da yake
zaune a bakin gado, ya dafe fuskar sa da hannun
sa. Abinda ya gani a mafarkin ya ringa dawo
masa kamar dai a gaske.

HMMM SHIN ME YA GANI KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE