DAN WAYE? CHAPTER 10 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? CHAPTER 10 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

Amma kuwa kin zama sauna, banda ke din
yar banza ce me zaki yi da shi? Ai komai kyan
surar ka in baka da kudi ba ka hadu ba, amma
zanyi maganin abin. Fice ki bani guri, sokuwa mai
ban haushi”
Mamie ta ci gaba da shiryawa.
Da kanta ta dauki mota ta fita, sun yi da
wata kawarta Larai za su unguwa, to sai dai ita
Laran ita ‘yar rakiya ce, kuma sai bayan ta fito take
sanar da ita yanzu haka suna hanyar Bida, sun
samu labarin wani malami mai zafi a can

Ta kunduma mata zagi, ta ce.

“Amma kin san ina da matsala da yarinyar nan shi ne kika ki gaya min?”

Ta ce, “Nima yau na samu labarin, kin san ku masu maza kuna da matsala, ba kamar mu falan daya ba”..

Ta ce, “To shi kenan, in kinje ki bashi waya zanyi masa bayani, inyaso ko ta banki sai in turo masa kudin”.

Ta ce, “Shi kenan”.

Tana kashe wayar ta kai tsaye gidan

kanwarta ta nufa.

Mubarak da Mustapha suna zaune tsakar gida, da yake lokacin zafi ne, sun fito da fanka. Mustapha ya rufe idanun sa tamkar mai bacci, shi kuma Mubarak yana yiwa Mah ɓarar gyada. Mamie tayi sallama ta shigo, tana wani taku, tana wani yiwa gidan kallon shekeke.

Halima na ganin haka gabanta ya fadi, don ta san ba da alheri ta zo ba.

“Sannu da zuwa”. Ta fada. Ta mike, “Shigo daga ciki”.

Ta yamutsa fuska, “Ba zama nazo yi a akurkin gidan naki ba”.Jin haka ya sanya Mustapha bude ido, ta ci gaba da cewa.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Na zo ne in gaya miki ki gayawa danki na yiwa ‘yata miji, babu shi babu ita. Ni bana son kwarzaba, ko dole ne hadin zumuncin? Ina dacewar kaska da gwano? Na zo in sanar miki ta samu miji wanda ko direbban ta ya fi danki matsayi”.

Ita kam tana jinta ta kasa yin komai saboda tsabar mamaki, Mubarak na kallon Mah dinsa, sai yaga ashe kuka take. Aiko ya zabura, ya ce. “Wai ni ne nace miki ina son Suhaila? Ni

ban ce ba, don Allah Mamie ki daina aibata min

uwa tunda ba ma zuwa maula”.

Tayi saroro ta kasa cewa komai, ta ce. “Kina jin danki zai min diban albarka?”

Mustapha ya ce, “Ki zo ki fita don Mah ta haifi karfi, yanzu za mu iya gwab-gwabje ki, ba a son ‘yar taki, in kin isa ki aure ta. Mara zumunci da zarmewar zuciya”.

Mamaki da tsoro duk sun dirarwa Mamie, ta

“To kai kuma awa?””kare min kallo daga sama har kasa, ba karamin mutum bane, ba alfahari ba gidanki akurki ne akan gidanmu”.

Ya nuna Mah, “Kinga wannan, yanzu nake jin sonta da kaunarta a cikin zuciya ta, ko bayan ran Mubarak zan kular masa da mahaifiyar sa, kuma ko bata haifi Mubarka ba a yadda take da kyan zuciya lallai kowa zai amshe ta, ya kuma rike ta ba tare da ta tozarta ba. Amma ke in ba naki ‘ya’yan ba lallai kowa a duniya zai juya miki baya. Www.bankinhausanovels.com.ng

Ban taba ganin mutum mara zumuncin ki ba, kin san muhimmancin zumunci kuwa? Don Allah ina kiran ki da murya mai karfi ki san matsayin Mah a gurinki, ki san muhimmancin zumunci, domin zumunta aba ce mai matukar muhimmanci. Kina son shiga cikin hakkin Allah, domin Allah Shi Ya ce ayi zumunci, duk mai yinsa ranar kiyama duk mai yinsa zai zauna cikin inuwa wacce ba kowa ke zama ba sai mai zumunci”.

Mamie tayi shiru ta kasa tabuka komai illa ta juya a fusace tana kunkuni, wanda ko ni Maman Shuriem banji me tace ba bare inyi muku tsegumi. Mah ta dube su duka biyuu ta ce, “Kuna da

hankali kuwa? ‘Yar uwata ce fa”.Mubarak ya ce, “Mun sani, ke kike sonta ita

ba sonki take ba, don ba ki da kudi, ba ki da wata rana da zaki yi mata a ganinta. Mah, ina rokon Allah Yayi min arziki, zan jiyar dake dadi mara misaltuwa, don bana iya hada sonki da na kowa, duk wanda ba ya girmama min ke ba zan girmama shi ba. Ina son ki son da ba kowanne da ne yake yiwa mahaifiyar sa ba”.

Shi kam Mustapha yana jinsu bai iya cewa koma ba, amma yana mamakin irin son da Mubarak yake yiwa Mah dinsa.

Izzat tana zaune cikin yanayi na damuwa, yayin da Surayya ke gefenta tana kallon ta. Ta dan kai mata bugu, ta juyo ta kura mata ido suka yi (face to face), ta ce.

“Ke, me ke damun ki?”

Izzat ta ce, “Ni akwai me damuna a duniya

kamar ni?”

Ta dan harare ta, ta ce, “Meye damuwar Ta ce, “Kin san ya zanyi da son Mustapha kuwa?” cikin zuciya ta?”Ta ce, “Ki kasance mai afuwa a gare shi, Allah (S.W.T) Shi ma in muka yi masa laifi yana yafe mana, kuma Yana son bayin Sa masu yafiya”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “In na yafe masa yaya ‘yan uwansa da dangin sa za su amshe ni a matsayina na kurma nakasasshiya? Kin san ku masu kunne ba ku aje komai ba sai gulma, sai munafurci”.

Furucin bai yiwa Surayya dadi ba, amma in

da sabo ta saba da halayyar ‘Yar kurma.

Izzat ta ce, “Gulmar me muke muku?”

Ta ce, “Ato, in kunyi damu bama yi ba ai

Allah Yana jinku, kuma Zai saka mana”. Dariya ta kama Surayya, amma sai ta maze saboda tsoron fada da Izzat, don fadanta ba ya mutuwa.

Ta dube ta, ta ce, “Yanzu shawara kike

nema ko ko ya kike so ayi?”

Ta ce, “Ni na san ina son Mustapha, to abinda nake tsoro Mustapha zaman da shi ina ganin akwai matsala, domin ya kasane mutum ne mai zafin rai, ta ya zai ringa hakuri dani, amma na sani ina son sa, ina so in tursasa zuciya ta ta rabu da shi, domin sanin yadda rayuwa ta take. Ina ganin shi ne rufin asirina, domin jinin ka ma ya ki ka bare ba re”.Surayya ta ce, “Ba ki ji Hausawa sun ce dadin zama sai ba re ba? Amma kuma ranar naka sai naka”.

Hawaye ya zubowa Izzat, ta ce.

“Ban san yadda aka yi har nayi sakaci so mai zafi ya shiga zuciya ta ba, bana jin zan iya rayuwa in babu Mustapha”.

An sanya lokacin bikin Suhaila waccer har yanzu zuciyarta na ga Mubarak dinta, ta so ganinsa tun kafin faruwar haka, amma Allah Bai nufa ba. Ta tsangwami rayuwar ta, duk ta fige, ta rame ainun. Ita kanta mamie dom tata hankalin ta ya tashi, domin tana son ‘yarta sosai, ta sani in har ta amince at auri Mubarak to me na sama ya ci bare ya bawa na kasa? Karshen ta ka siyar da akuyar ka ta dawo tana ci maka danga. Www.bankinhausanovels.com.ng

Lallai abu ne da ba zai yiwu ba, me zai kawo mata? Me yake da shi? Ina zai aje ‘yarta? Ina! Ba zai yiwu ba,  lallai dole ta zage don ganin ta fatattaki duk wani abu da yake neman kawo mata matsala.

Suhaila ce zaune a cikin dakin Baba Halima, ta sunkuyar da kanta, ta ce.”Mah, den Allah kiyi hakuri akan duk abinda Mamie take miki, wallahi duk zugar kawaye ce. Duk inda naso ta gane ta ki ganewa”.

Mah ta ce, “Haba Suhaila, ai ni komai ya wuce a gurina, ni ban rike ta da komai ba. Na san Mubarak da ne na gari, ina alfahari da tarbiyyar da nayi masa. Na san bamu da komai, amma tarbiyyar sa zai sa ya shiga cikin kowacce al’umma, ni na san idan halayya ce to lallai duk inda Mubarak ya nemi aure za a bashi. Ke kuma

hakuri da shi, domin aure dake da shi ba zai

Yiwuba, kibi son ran mahaifiyar ki, shi ne abu mai muhimmanci. In kin yi mata biyayya na san zaki ji dadi gaba, ki sa a ranki dama Mubarak ba mijin ki bane”. Ban da kuka ba abinda Suhaila take, take

“Mah na hakura, amma ban jin dadin yadda Barek ya tsane ni, ya ki jini na. In na tuna ina damuwa, saboda ni ‘yar uwarsa ce, zan yi zumunta da ku, ba ruwana da lamarin Mamie, itama na san akwai ranar kin dillanci, dole ne za ta gane dan uwa ba abin banza bane”.

Mubarak ya shigo, ganinta yasa ya bata rai tare da shan kunu, ya juya ba tare da ya ce komai ba.Suhaila ta kalli Mah ta ce, “Kin gani ko

Mah”.

Tayi murmushi ta ce, “Mubarak”. Ya dawo ya daga labule ba tare da ya shigo

ba, ya ce.

“Mah, gani”. Www.bankinhausanovels.com.ng

Ta ce, “Shigowa zaka yi”. Bai yi msuu ba ya shigo, ya samu guri ya zauna, ta ce.

“Mubarak, a tunani na namiji ya fi mace hankali da hangen nesa. Ba dabi’ar ka bace riko, ina ganin lokaci yayi da za ka hakura tunda komai ya zo karshe, ma’ana ita Suhaila aurenta ya zo”.

Har cikin zuciyar sa bai ji dadi ba, zuciyar

sa ta ringa zafi, ya dinga jin kunci, domin yana son

Suhaila. To ya zai yi tunda tsohuwar ta mai idon

cin Naira ce?

Ita kam Mah ta gano sauyawar da yayi, ta san an cuci danta don yana son Suhaila, sai ta ce.

“Ka hakura, kuyi zumuncin ku. Bai kyautu ka dinga nuna kyamatar Suhaila ba, domin ba laifin ta bane”.

Ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai,

Suhaila ta ce.”Ka yi hakuri Barek, duk wanda zan aura ba

na sonsa dole Mamie tayi min, in kana gaba dani kana wahalar da zuciya ta, ka yafe min Barek ka daina zargina”.

Ya ce, “Shi kenan, ya wuce”.

Ya mike, ya dube ta, ya ce, “Allah Ya sanyawa auren ki albarka”. Ya fita.

Ita kam Mah tana mamakin halin ‘yar uwarta, ita dai kudi, ba ta duba yadda zaman aure yake a yanzu, an buga soyayya ma ya ake karewa balle anyi auren kudi?

Masu irin halim Mamie suna dan yawa, don sam ba sa duba ya rayuwar gaba za ta kasance? Su kam in burin su ya cika shi kenan. Lallai akwai matsala a rayuwar irin wadannan iyaye, ya kamata su daina. Shi fa aure har abada ana yinsa ne  zama ne na din din din, ma’ana babu mahalukin da yake aure ya sa ran rabu da matar.

Ana yin aure ne mutu ka raba, to ya za a yi ace an gina aure babu so da kauna, ko tausayi? Ko a gina aure don neman kudi? Ton in aka gina aure saboda wani dalili in ba ka samu cikar burin ba lallai akwai gundumeren bacin rai, a irin haka ne aure babu inda yake zuwa, domin ita rayuwar aure ta sha bamban da rayuwar samartaka.Rayuwar aure akasari tana zuwar maka ne ba yadda kake zaton ta ba. Www.bankinhausanovels.com.ng

Mustapha da Mubarak sanye cikin wata lallausar shadda wacce ta ci aikin Senegal, sun masifar haduwa. Suna cikin mota ash kala, shaddar tasu ma ash ce, suna taye bakin get din gidan su Izzat. Izzta sanye da hijab mai hannu, ita kuma Surayya tana sanye da riga da siket, ta dora (after dress) akai. Sun zo sun shige su kadan, Mustapha ya ce.

“Sannun ku”.

Jin muryar sa yasa Surayya juyowa, tayi

murmushi ta ce.

“A’a ku ne?”  Ya gyada kai tamkar marayan da yake neman agaji, tayi murmushi. Ya tsira mata ido, ya ce.

“Ki rarrasar min rayuwa ta tayi murmushi”. Taji ta amince da son da yake yiwa lazzat, lallai duk ajinsa da girman kansa yayi sanyi. Shi kuwa Mubarak ya tsaya da Izzat, ta

kalle shi cike da hargagi irin na kurame ta ce. “Me ka rako shi yayi a gurina? Ko kun zo ya rufe ni da duka ne? Na kula ku masu kunne ba ku

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE