DAN WAYE? CHAPTER 14 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
DAN WAYE? CHAPTER 14 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Mun tsaya
Kowa ya gyara ya sani, kowa ya bata ya sani. Kanwar taki guda daya in baki yi mata ba kiyiwa wa? Duk wanda za kiyiwa ba burge su zaki yi ba. Shi dan nata da kika hana kin san me zai zama?””To ki dauki ‘ya’yanki ki bashi”.
Tayi dariya, ta ce, “To inama ace Allah (S.W.T) Ya amsa bakin ki, kuma ya hadu da Weesal ko Weediyan, da na bashi”.”Wadannan yaran ‘yan feleke?”
Ta ce, “Cewa kika yi in bashi, ni kuma na ce Allahumma amin”. Hajiya Laure ta ce, “Ke kin bawa Suhaila abin nan?”
“Wallahi na manta”.
“To dai kin san budurwa ce, kada ku bata abinda zai cuce ta, kin san ba sonsa take ba”.
“Wani hadi ne na mallaka, aka ce lallai
yau tayi amfani da shi, dole za ta ba da kai, kuma sai ya zama kamar rakumi da akala”. “To Allah Ya taimaka”. Suka rangada guda, Hajiya Laure ta nufi
inda dakin amarya yake, taje ta tare ta. Sai da
taga ta shanye tas ta juya zuwa ɓangaren da aka sauke su.
Dr. Yassen ke rubutawa Mustapha wasu magunguna, saboda an sallame shi, kuma cikin asibitin basu da shi, inyaso ya siya a (chemist).Wayar sa ta dauki kara, yayi murmushi ya
dauka, ya ce.Da gaske kin shigo?” “Ina duba wani (patient) ne amma ki jira”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “To ki iso daki mai lamba (5) za ki same ni”. Ya kashen wayar ya ci gaba da yiwa
Mustapha bayani. Aka yi kwankwasa kofar aka shigo, Dr.
Yaseen ya juya yana murmushi, ya ce. “Surayya, au ke daya ce? Ina Izzat din?”
Ta ce, “Ita muka kawo ni da Umma”.
Jin an ambaci sunan Izzat ya dago kai
suka yi ido biyu da Surayya, ta ce. “Mustapha, dama ba ka da lafiya? Nayi kiran wayar ka a kashe”.
Ya ja aji sosai har sai da taji haushin yanayin da yayi, ya sake murmushi, mulkin yamotsa, ta ce.
“Ai ance dama mai hali ba ya fasa halin sa”. Ta fada a zuciyar ta. A lokacin Alpha da Mubarak suka shigo,
Mubarak ya ce. “Dama kun san bashi da lafiya?”
Ta ce, “A’a, nima Izzat muka kawo, bata da lafiya, am ma naga abokin naka ya yi fushi, ko kulani bai yi ba. Ai laifin wani ba ya shafar wani, ina maka fatan samun lafiya”.Ta ce, “Dr, zo muje kaduba min ‘yar uwa Suka juya suka fita, Alpha da Mubarak
suka mutumin me yasa kayi haka?”murmushi yayi Ya ce, “Ina so in cire duk wata mace a rayuwata ne, ku kyale ni. Ina ji a zuciya ta zan rabu da Izzat ko da rabuwar mu zai haddasa mutuwa ta, ba shi kenan ba. In kuma bai kai ba lallai ba zan yi aure ba, zan kuma bar kasar nan, Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokaci daya suka kalli juna, Alpha ya soma hada kaya, yayin da Mubarak ya bisu ya ga jikin Izzat. Har an dora ta a gado yana kokarin daura mata ruwa, ta kalle shi ta ce. dan Allah”Mubarak, ina Mustapha?” Ta fada cikin muryar kuramé da magagin bacci, a hankali ta rufe idonta. Ya tsuguna gaban Umman su, ta ce.
“Ina Mustapha?” Ance, Ba ya jin dadi tun ran da kuka je gurin Izzat, amma yanzu an sallame shi”.. Shigowar sa shi da Alpha wani daddadan kamshi ya gauraye dakin, hankalin sa gaba daya ya koma kan Izzat, ta rame sosai. Ya mai da hankalin sa kan Dr. Yaseen, ya ce.
“Me ke damun ta likita?”Ya ce, “Bincike muke, ba mu tabbatar ba,sai mun gama gwaje-gwajen mu”.Sai a lokacin ya kula da Umma, ya risina ya gaida ita, ta amsa.”Ya jiki?”
Ya ce, ai ya warware, yanzu ma an sallame su.
Ta ce, “To Allah Ya kara lafiya”. Ya ce, “Amin”.
Suka fice zuwa motar Alpha, kai tsaye gida suka nufa, dakinsa a share Bello ya gyara masa, shi ne mai kula da sashin sa. Ya yi wanka ya hada (tea) ya sha, bacci mai nauyi ya dauke shi, ganin haka yasa suka fita.
Bayan ya farka ya tarar da dinning area an shirya masa abinci, ruwa ya sake watsawa. Ya jima yana murzawa kansa kalolin turaruka, don Allah Ya yi shi dan kwalisa ne sosai. Ya gyara gashin sa da wani mai da yake sake nade masa sumar sa tayi luf-luf gwanin sha’awa.Ya taso a lokacin ya kunna wayar sa ya ajiye. Yana jin shogowar (text) ya zauna yana cin abinci, ya kammala ya shiga cikin gidan.
Hajiya Saratu na hamshakin falon ta, sanye take da doguwar riga (pink colour), tayi mata kyau, hakoran Makkan ta guda biyu masu matukar sheki. Ya shaki kamshin falon ta, ya ji sanyi har cikin ransa.
Ya tsuguna jikin kujerar da take zaune, yace.
“Momie, barka da gida”.Ta ce, “Barka ka dai, ya jikin naka?”
Ya ce, “Na warware”.Ya zauna, ya ce, “Momie, nakan yi mamaki da har na gama zama na a asibiti baki zo ba, na rasa gano dalilin da kika dasa kiyayya ta a zuciyar ki, saboda me? Ki fada min laifina na daina, ba na shaye-shaye, ba na neman mata, ba na neman maza, Momie ba na sata. Na rasa me yasa kike kina, in kuma ba ke kika haife ni ba ki sanar min in nemi uwata, don Daddy shi ne ubana”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tana jin tausayin sa, amma tana jin wani abu game da shi cikin ranta, ta ce. “Mustapha kayi hakuri, haka Allah Ya yi ni, kullum ina addu’a akan lamari na, nima abin yana damuna…”
Sai ta sanya kuka. Tun”Kana karami ka kamu da hawan jini, nima ina dashi”,
Ya zaro ido, “Kema kina da shi?”
Ta ce, “Eh Mustapha, zan yi shekaru sha biyar tare da hawan jini. Ka yafe ni, nima bana so nake maka haka, ni da zan mutu ma da na huta”.
“Momi mutuwa fa kika ce?”
Ta ce, “Eh mana, to mene ne amfanin
uwar dake azabtar da danta?” Shi ma yanzu ya yarda da maganar mahaifin sa, Momi na da aljanu.
“Kada ki damu”.
Ta ce, “Na damu, kuma zan ci gaba da damuwa ko da damuwar za tayi sanadin mutuwa ta”.
Ya zuba mata ido yana nazarin ta, ya ce. “Momie, ina son ki ko da za ki ringa redar naman jikina kina ci, ni zan zama mai biyayya a gare ki”.Ta shafi kansa, tayi murmushi ta ce.
“Boy dan gidan Daddy, ina mai zuwar naka a barci?”
Ya ce, “Ta ce bata sona, saidai banji haushi ba tunda wacce ta haife ni ma ba ta sona”.
Ta kalle shi, ta ce, “Ina son ka Mustapha, kada ka tsani ‘yar mutane. Duk wanda ba yama sonka ba na kaunar sa, na ce maka kai namiji ne, ko a kuruciyar ka kai ba rago bane, bana kai kara sai dai a kawo min. Maza Boy din Daddy ka je ka nemi soyayyar ta”.”Momie, sai dai fa kurma ce”.Ta ce, “Kur me?”
Ya ce, “Tana iya magana, sai dai ba ta ji, ya same ta da girman ta (may be) in anyi mata aiki kunnen zai bude”.Ta ce, “Anya kuwa?”
“Iyayen ta naga suna da wadata”.
Ta ce, “Ai shi kenan, ai kurma mutum ce, don tana kurma sai ince ba zaka aureta ba? In nayi haka na yiwa Allah shisshigo, ai kai za ka zauna da ita, kana da ikon ka auri mace hudu fa”. A lokacin Alhaji Abdulmajid ya shigo, ganin su suna hira ya bashi jin dadi, ya ce.”Ikon Allah, nan da anjima sai ta ce ita ba ta son ganin sa. Allah dai Ya kawo karshen abin”.
Ya ce, “A’a Momie ce da Boy dina?”
“Hirar surukar ka muke yi, kaji kurma ce”. Ya yi murmushi ya ce, “Wacce zaka yi ta
masifa ba ta san kana yi ba””Oh ni Mustapha na ga takaina, Allah Www.bankinhausanovels.com.ng
Daddy bani da fada”. Kai kai! Ka dai fadi gaskiya”.
Suka fashe da dariya, hira suke cike da so da kaunar juna.
*******
“Amarya ba kya laifi ko kin kashe ‘yar masu gida”.
Wannan shi ne taken duk wata amarya a kasar Hausa, ko ince kirari.
To Suhaila dai amarci ya tabbata, don bayan abokan ango sun zo sun sai baki tare da dire mata manyan akwatina hade da kudin da bata san iyakar su ba.
Musbahu shi ma yasan ba ta sonsa, don ta sha fada masa ita Allah Ya halicce ta don Mubarak. Shi kansa shakkun yanda zai kadaita da amaryar yake. Ya so ya share ta sai bakin sun koma, amma da ya tuna faduwar gaba asarar namiji, sai ya sa kai.
Tana zaune har a lokacin tsakiyar gado, ya ja jiki ya ce.
“Suhaila, ya gajiyar biki?”
Ba ta tanka masa ba, don jinta take cikin wani yanayi, ga tunanin Barek dinta. Ta so ace ita da Barek suka zama ma’aurata, amma ga yanda Allah Ya hukunta.
Cikin yanayin salon wanda ya saba da mace ya ringa tarairayar ta, tun tana gocewa, ga kuma karfin magungunan da aka turka mata. Mijin ta ya same ta kamammiyar budurwa, wadda a tunanin sa yadda take son Barek ya gama da ita tuni, ashe abin ba haka yake ba.
Ta samu albarka daga bakin mijinta, tayi kuka na takaicin halin da ta tsinci kanta a kirjin wani ba Mubarak ba.
Kwana tayi tana kuka har asubahi, Musbahu shi ne ya taimaka mata tayi wanka, tashirya, tayi sallah.
Sai sha daya su Hajiya Hadiza suka shiga, har zuwa lokacin sharbe Suhaila take. Kawayen ta ganin da iyayen ta a gurin babu wanda ya tambayi dalilin kukan, su kuwa da yake manya ne sun ranfe ta. Suka yi dan gyare-gyaren su, sannan suka yi shirin tasowa. Haka aka bar ta daga ita sai dangin mijinta.
Mutanen Gombe su ma washe gari suka wuce gida, daga ita sai dan mijinta Khalid dan shekara goma. Yaro ne mai kazar-kazar, wayayye, gashi da girmama manya, shi yasa ya shiga ranta sosai, tana son Khalid.
*******
Misalin karfe takwas suka iso asibitin kaf ‘yan (group) din su, Dr. Shuriem ya kalle su ya zo shigowa, ya ce.”Ku ba an sallame ku ba?”Mubarak ya ce, “Likita korar mu ake?” Ya ce, “No ba wai korar ku nake ba, ku Www.bankinhausanovels.com.ng
din ne akwai cafta”. Suka ce, “To ai ba cinya ba kafar baya”.
Ya ce, “Ni fa ban gane ba”.”To ka sallami Musty kun rike mai dakinsa”.
“Oh! Ai ban sani ba, yaushe aka kawo ta? Yau ina AKTH ban jima da shigowa ba”.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG