DAN WAYE? CHAPTER 16 BOO1 KARSHE BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
DAN WAYE? CHAPTER 16 BOO1 KARSHE BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Mun tsaya
Weesal ke da dumpil daya, yayin da Wediyan ke da biyu, shi ne bambancin su. Hatta magana, kallon su tsahon gashin su duk daya ne, daya na da yawan magana da son budawa. Indai suka zauna suka yi shiru, to babu mai gane su, ko laifi suka yi da wuya a gane, su sai su. shi yasa lamarin
Shi dama Mustapha ba ya shiga sabgar su, Weesal ce mai nacin kaunar sa, ita ko Weediyan ta ce ita ba zata auri talaka ba, sai mai kudi, mai kudin ma sai wanda yayi suna cikin jerin masu
kudin Nigeria. Kai in son samu ne sai wanda yayi suna cikin jerin masu kudin duniya.
Wannan burin nata ya sanya sam ba sa shiri ko kadan, to amma shi kansa ba ya iya gane kowacce a cikin su, don sun jima. Shekaru uku kenan suna can kasar su baban su, sai cikin satin nan suka dawo.
Suka samu gefe lokaci daya suka ce.
“Musty, da fa daga nan gidan ku za mu, munji ance ka kusa zarcewa. Ka san yanzu tazarce ake”.
Ya harare su, ya ce, “Ta Allah ba ta kuba”.
Suka bushe da dariya, Weesal ta gai da su,
Weediyan ta maze, ya kalle ta ya ce. “Dama kin gaishe su duk nan babu (choosing) dinki, matar manya”.
Ta ji dadi sosaita sake ta mazewa, Alpha dan tsokana ya ce.
“Hajja Weediyan ko ‘”.
Weesal ta mike tayi ciki cike da takaicin ‘yar uwarta, Mustapha yace Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ya kamata Hajjaju ki rage buri”.Ta ce, Wa! Ni din? Kai dai ai kudi sunyi a rayuwa, ko ya kace Alpha?”
Shi dama dan cafta ne, ya ce, “Ai abin alfahari ne ki fito a matar gwamna ko shugaban kasa, ko minister. Wayyo! Ni ko ina fasa kai, ina kanwata ce, ina yiwa mutane hayaniya, kina taimakon al’umma”.
Ta ce, “No Alpha, nafi so in auri mai bala’in Naira, bana son shiga gwamnati, da ta bare mun zama sai labari. Masu masifaffun kudi dai, ni ko in zube a falo ana yi min hidima, ina kallon mabukata sun zagaye ni ina ta rabon Naira”.
Tayi wani ihu ta mike ta ce, “Wa yaga Hajiya Weediyan, ka san Allah Mustapha, a rayuwa ina son in auri mai kudi don in ta taimakon mabukata, in ta bude asibitoci, ko ina ka ji ana fadin Hajiya Weediyan”.
Mubarak ya ce, “Allah Ya cika miki miki burin ki tunda taimako za kiyi”.
“Amin abokin Musty, na baka Weesal in kana so, ita ce kyautar addu’ar ka gare ni. Sannan zan taimaka maka da kai da iyayen ka a lokacin da bukata ta biya, sannan zan dankara maka mota mai numfashi kaji?” Mustapha ya harare ta, ya ce.
“Weediyan, ana girma ana hankali amma ke kam abin naki gaba yake”. Alpha ya ce, “Weediyan jan wuya ce ke,
sai a hankali”.
Ta dube shi ta ce, “A tarihin rayuwa ta talaka bai taba cewa yana sona ba, kuma ni ko ya zo ba zan so shi ba”.
Alpha ya ce, “Da zan shigo kice da
dagudu zan koma”. Ta harare shi ta ce, “Kai? Tab Ai ko ogan ku ba zan yi maleji da shi ba, bare kai”.
Ta dubi Mubarak ta ce, “Kai ya sunan ka?
Naga ka danfi wannan nutsuwa. Kada ka manta,
nayi alkawarin Weesal”.
Mustapha ya ce, “Da yake ke kika haife ta, ko ance miki bata da masoya da zaki yi kyautar ta?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “A’a Musty, ko kana ciki ne ban sani ba? Amma ai abinda nake so shi take so, irin mu daya, komai namu daya ne, to akan me zan zaba mata miji ta ki? Kai nice fa ogar ta”. Suka fashe da dariya, tayi ciki.
Hajiya Lami ta mike ta bi bayan su, ta ce. “Oh ni Zainabu, naga sanda Weediyan zata daina son mai Naira”.
Duka samarin suka yi dariya, tana shiga Faisal ya ce.
“Weediyan manya, ita babu ruwanta, tsakanin ta da Allah take furucin ta”. Anas ya ce, “Kai kam Barek anyi maka
kyautar mata, ga kyau ga gayu”. Mustapha ya katse shi, ya ce.
“Manta da ita, ‘yar wulakanci ce. Ita ce ta haife ta da zata yi kyautar ta?”
Weesal ce da Shuhuda suka shigo falon suna ta jera kayan abinci, sai da suka sa komai a muhallin sa, sannan Shuhuda ta ce. “To gashi nan mun kammala, sai ku zo kuci”.
“Okey, sannu”.
Suka juya, ciki ne Weediyan na kishingide tana kallon su, daga baya ta ce. “In kun gama da wadancan kartan nima ku kawo min nawa”. Suka ce, “Kin isa?”
“Kai! Hajiya ce fa ni, yanzun nan nayi kyautar ki, ‘yar rainin hankali”.
Hajiya Lami ta ce, “Kyauta kamar ya?”
Ta ce, “Mubarak abokin Mustapha, yo ni ban sanshi ba sai yau, anma dai naga yana da hankali, haka kuma zuciya ta naji ta karbe shi. Sai naga kawai tunda ni me Naira nake so, to bari in sadaukar dashi ga Weesal, amma da ba mai Naira nake so ba zan yi maleji da shi”.
Hajiya tayi dariya sosai, ta ce.
“Allah Ya kawo ni zamani, rashin kunya. Tab! Ikon Allah”.
Shuhuda ta ce, “Ke kinje da shirmen ki kindawo da tatsuniyar ki”.
Ta ce, “Ko sai ran da na ce Shuhuda fadi kasashen da kike son zuwa kiji kamar mafarki”. Hajiya Lami na kallon su cike da so da kaunar jikokin nata. ‘Ya’yanta uku, mahaifin Shuhuda shi ne babba, sai mahaifiyar Mustapha, sannan mahaifiyar su. Weesal ‘yan biyu. Tana son su sosai, suma suna sakewa da kakar su, don suna son ta fiye da kakannin su, don suna sakewa a gidanta, Mace ce wayayyiya da iya mu’amala da mutane, ta iya zama da kowa a cikin su.
Kwanan Izzat biyu aka sallame ta, Alh. Habib Salga sai yayi murna da ganin Mustapha a matsayin surukin sa, don samun matsashi mai tashen kudi ace ba ya hulda irin ta samarin yanzu. Shi dai Kyale shi akwai fada, mafadaci ma ai sai ka shiga hurumin sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Izzat zaune a farfajiyar gidan su, zaunė take da littafin Kashin tsiya, tana mamaki yadda rayuwar Muwadat take tafiya, har hawaye taji ya zubo mata.
A lokacin (text) ya shigo wayarta, ta gane haka ne ta kadawa da taga wayar nayi.
Ta bude ta ga Musty ne ya karaso, ta shiga ciki ta sake shiryawa, ta nade kanta da karamin mayafin BB, doguwar rigar tayi mata kyau, baka ce a jikin fara, ta haska ta.
Inda Kanin ta Nasir ya shigo, ya ce. “Na kaishi”.Ta mise cike da yanga da rangwada, ta iso
gare shi ta ce. “Sannu da zuwa masoyina”.
Yayi murmushi, ta zauna ta kura masa ido,
murmushi take, sannan ta zame ta ce, “Barka da yamma?”
Ya ce, “Mun yini lafiya?”
Ta ce, “Lafiya, ya Momi da Daddy?”
Ya ce, “Duk suna gaida ke”.
Tayi shiru, “To ina kannen ka?” ai”Ni kadai ne, yanzu zuwan ki muke jira ki
bawa momi yaran da za su debe mata kewa”.
Tayi murmushi ta rufe fuska alamar jin kunya, a lokacin Surayya ta karaso ta ajiye kayan cima iri-iri, ya ce.
“A’a, ni kam a koshe nake”. Ta ce, “Haba Yallabai, ai ka ci ko
kadanne”.kishirwa”.Ya ce, “Bani insha ruwa, don ina jin
Ya ce, “Surayya, a daina ce min Yallabal”. Ta ce, “Ai Abban nu haka yake ce maka”. Ya ce, “Ai ya daina, ni yanzu dansa ne”,
Suka yi murmushi dukkan su. Sun jima
suna hira, daga nan ya tafi. Alh. Abdulmajid a office dinsa shi da
lauyan Mustapha, an bashi takardu ya sanya hannu, dama shi ya rage. Bayan tafiyar lauyan Alhaji ya ce. “To yanzu batun auren ka shi ne a gabana,ya batun tafiyar Turkey?”
Ya ce, “Yana nan Daddy”. Sun yi hirar su ta da da mahaifi,
Mustapha kwance falon mahaifiyar sa suna hira, wayar sa tayi kara, ya dauka ya ce. “Mubarak, kaine? Bari in fito”.
Hajiya Saratu ta ce, “A’a, ina zaka tafi bayan ka ce yunwa kake ji?” Ya ce, “Mubarak ne ya zo”.
Ta ce, “Oh, ni ban taba ganin sa ba”. Ya ce, “To ai tsoron kawo shi nake, kuma shi din ba mai son shga cikin gida bane”.
“Ta ce, “Irin ku daya”.
Ya ce, “Momi sai kinga inda nake shiga gidan su na sake sosai, Mamar sa mace mai kirki da hakuri. Ni ina bala’in kaunar mamar sa, saboda yadda take tafiyar da rayuwar ta”.
Ta ce, “Allah Sarki, yau dai a kawo min Mubarak in ganshi. Je ka shigo da shi, insha Allahu za ka kaini gurin mahaifiyar tasa. Ai tunda naji Alhaji na yabon halin sa na san yaron kwarai ne”.
Ya mife ya fice.A zaune ya same shi, suka tafa. “Ya gida ya hidima”.Ya ce, “Mu shiga ka gaisa da Momi”.
Yaji matsanancin faduwar gaba, shi dai baya so ya shiga, barin yadda in Mustapha ba ya wajen ake labarin halin Maman sa, baya son wulakanci. Amma bai isa ya ce ba za shi, haka ya bishi suka shige ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tunda uwar sa ta kawo shi duniya bai taba zaton akwai irin wadannan falukan a Nigeria ba. Ya zauna kamshi da sanyi suka ratsa shi, ya dinga zare ido yaga ta inda Momi za ta fito, ai kam sai gata ta fito. Ta zauna ba tare da ta kalli Mubarak ba, ya tsuguna ya gai data. Ta kalle shi, gabanta yayi mummunan faduwa, har sai da ta firgita. Ta mike ta kalle shi,ta ce.
“Kaine Mubarak?”Ya ce, “Eh”.”Ina ne gidan ku?”
Ya yi mata bayani, ta kalle shi a tsanake,ta ce.
“Mubarak, kai dana ne, ni ce uwarka, ni na haife ka. Wallahi babu wanda ya isa ya raba ni da kai, sai kuma na karbe ka, don kai dana ne na cikina, ni na haife ka”.
Gaba daya suka zabura, anya kanta daya?
Mustapha ya ce, “To ni kuma DAN WAYE? Ki fada min ni din DAN WAYE? To fa, muje zuwa.
Taku
Maman Shuriem.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
MU HADU A BOOK 2