DAN WAYE? CHAPTER 2 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
DAN WAYE? CHAPTER 2 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Mun tsaya
Shi kuwa Mubarak addu’ar sa daya, Allah lin
Ya bashi aiki ya sanya iyayen sa suji dadi.
Mah ta tashi ta kawo wa malam’ abinci.
tare da Mubarak suka ci suka koshi, suka kuma
kama hira.
Hakika iyayen Mubarak suna Son sa
soyayya mai zafi, don ko zarzabi in Mubarak
yayi duk sai sun rame. Allah kuma Ya taimake
su yaro ne nutsatstse, don ba ya son yaga abinda
zai taba mutuncin iyayen sa.
Sun jima suna tattaunawa akan neman Www.bankinhausanovels.com.ng
aikin da Mubarak din yake yi, har yanzu shiru.
A firgice ya farka daga baccin da yake yi,
ya tofa addu’ar da Annabi Yai umarni da ayi idan
kayi mummunan mafarki, don mafarkin da yayi
dole ne ya kira shi da mummunan mafarki.
Ya zuba kafafun sa kasa yayin da yake
zaune a bakin gado, ya dafe fuskar sa da hannun
sa. Abinda ya gani a mafarkin ya ringa dawo
masa kamar dai a gaske.
Ya ce, “Oh! Ni fa kada na je na mari Aljana, yarinya kin fitine ni, kullum na kwanta
sai nayi mafarkin ki, anya za a kwashe da
gaskiya? Ai babu shiri yayi alwala ya dauko
Alkur’ani ya soma karatu har sai da yaji mahaifin
sa na buga masa kofa ya tashi su tafi masallaci
Ya fita suka tafi tare da mahaifin sa.
Mustapha záune ya yi tagumi cikin falon
mahaifiyar sa ta fito, irin manyan Hajiyoyin nan
ne, amma fa kyakkyawa ce ajin karshe.
Ta ce, “Lafiya kake my boy
Ya kada kafada, “Momi na debo ruwan
dafa kaina”.
Ta ce, “Kamar yaya?”
Ya ce, “Uhm, zauna ki sha labari
Ta zauna a nutse ta shafi kan dan nata, ta
ce”Ina jinka”Mustapha ya ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Wata yarinya ce kyakkyawa Momi
Ta san halin wautar Mustapha, ko kuma-
ince shagwaba. Ta sanshi yanzu zai yi kwaba,
don haka tai saurin cewa.
“Ita kyakkyawar sonta kake?”Ya ce, “No Momi, yana zuwar min a mafarki…”Dai dai nan Alh. Majid ya shigo, yana
takawa a hankali. Ba wani tsoho bane, don yan
matan zamani za su s0 ace ya aure su. Sai dai shi
mutum ne mai kamun kai, ba kamar yadda masu
kudin yanzu suke ba. Domin a zahiri masu kudin ,
yanzu za su hana ya yansu yawo, amma ‘ya ‘yan
talakawa suke tarawa cikin (guest house) na su. abinda ba zaka so ayi da yarka ba shi
kake yi da ‘yar wani.
To shi Alh. Majid baba ruwansa da kula
mata in ba matar sa ba Hajiya Saratu, mace ce
yar kwalisa, wacce ta san yadda za ta kula da
mijinta.Ya shigo da sallama, ta kalle shi a matukar
kaikaice ta ce.Au, har ka tashi a baccin?”
Ya harare ta, ya mai da hankalin sa kan
Mustapha ya mika masa hannu, Mustapha ya
noke.Ka gani za mu bata”
Ya ce, “Allah Abba in ka miko min hannu
sai inji duk duniyar ta yi min kadan, sai inji wani
bambarakwai”.Ya kamata ace ka saba Mustapha nawa,
da ai kana bani hannu, yanzu ka daina”
Hajiya Saratu ta ce, “Ya yi hankali ne, ya
ga rashin dacewar hakan” s”Wai ko lafiya kake?”
Ya girgiza kai ya ce, “Abba, wallahi wata
kyakkyawa ce take zuwar min a bacci, anya ba
aljana na mara ba?”
Su Abban ya dube shi ya ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Meye labarin fa har ka mare ta?
Bai boye ba ya tada musu, cikin tsananin
Bacin rai Hajiya Saratu ta ce.
“Wai Boy yaushe za ka daina hauka ne?
Kullums ai nayi ta fama da kai anmma kamar ina
Rara zuga ka? To yanzu in Aljana ce ai ka jaza
mani”Abban sa mutum ne mai sanyin hali, bashi
da zafin Mami, saboda haka sai ya lallashe ta
tare da cewar Mustapha yaro ne, zai daina.
Ta ce, “Har yaushe? Saurin hannu bashi da
dadi”.
Ya shafi kan Mustapha da ya bata ransa,ya ce.
Boy, bana son saurin hannu ka ji? Bare
dukan mace, wacce aka fi son a tausaya mata
Domin mace daraja ce da ita, ka ji Boy?
Ya gyada kai, ya ce.
“Abbana yarinyar yar rainin hankali ce, ce
min tayi bata ji, kuma magana radau tsabar
iskanci ne’.
Hajiya Saratu ta harare shi, ta ce.
“Ai yanzu gashi nan hakkin ta ya kamna
ka, daga mafarki sai so kuma”
Alh. Majid ya ce, “A’a, kada kiyi masa
baki”Gaba daya suka yi dariya.
“”Ba ma sonta nake ba, me zanyi da
dunkum? Can dai”.Daga nan suka ci gaba da hirarsu Hajiya
Saratu ta gayyace su cin abinci, don ko kusan an
shirya tebir, shi ake jira kuma ya fito.
Sallamar Suhaila Maman Mubarak ta ji, ta
ce”A’a, yau a gari?”
Tana dariya ta ce, “Mah, ni ce”
Ta shigo ta tadda Mah din tana shara, take
ta karbi tsintsiyar, ta ci gaba da yin shara, ta ce.
“Daga zuwa?”In da sabo Mah ta saba.
Tana gama shara ta shiga ciki ta dauro
zani, ta hau wanke-wanke suna hira. Bayan ta
gama ta shige dakin Mah, can Mah ta ji shirunn
yayi yawa, ta shigo a zaton ta bacci take, amma
sai ta tara ta tsaftace dakin fiye da da, don Mah
tsafta ce da ita, gashi ta hado kayan wanki ta ce.
“Uh, nayi zaton kwanciya kika yi, shi ke
kika hado wanki. Ke ba kya son hutu? To bani
da sabulu, sai ki ajiye”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tayi dariya, “Na zo da sabulu na”. i
Mah ta bi Suhaila da kallo, ta ce.
Ni kam wallahi bana son in ganki kin Zo
kina aikin wahala”.
Suhaila ta ce, “Mah, meye abin wahala? A
gida ma aiki nake, ni babu ruwana da masu aiki”
Dole dai Mah ta rabu da ita, ta sanya
sanwar abinci.
Tana cikin yin wankin Mubarak ya shigo,
ya ce.
“:Wai! Wata sabon gani.
Ta ci na Khamis, ma’anata sha kunu.
Ya ce, “Haba ‘yar kanwa ta, yaushe kika zo
Tayi banza da shi ta ci gaba da aikinta, ita
kuwa Mah tayi musu banza uwa ba ta jisu ba.
Ya ce, “Ai wahala ba naki bane, bari
inzo in taya ki”.
Nan ma ba ta tanka ba.
Ya ce, “Ki fada min laifina sai in gyara
kinji Sister? Amma in kika yi min shiru sai inga
kamar ban cancanci haka ba”.
Ta saci kallon Mah, sai ta ga ma ashe ba ta
wajen, hakan ne ya bata damar wurga masa wani
irin kallo, sannan ta ce.
“Barek, kana bani mamaki”,Ya dan sha kunu, ya ce. “Na fada miki bana son kina jibga min
sunan katon arne”. Ta ce, “To ni ba don shi nake kiran ka da
haka ba”Ta kalle shi, ta ce, “To na ce yayana ka ce
baka so, wai in na ce maka yaya na sanya ka a
kwalba, to me kake so ace?”
Ya ce, “To ga irin su Honey, Dear, my
love da dai sauran su. Ko ban cancanci a kira ni
da wadannan sunayen ba?”
Tayi dariya mai kara mata annurin kyau,
ta ce. eh To ai sai ka zabi wända kake so”. Ya ce, “Ke ya kamata ki zaba min”.
“Shi kenan”. Ta ce.
To fada min inji”.
Ta ce, “Ka ji sanda na kira”, Mah ta fito ta ce, “Ka zo ka cika ta da
magana, ba ka barta tayi aikin ta ba”Ya ce, “Mah, taya ta zanyi”
Ta dan zaro ido kadan tare da girgiza kai.
“Um-um na gode, zanyi abina ni daya”. Ya ce, “Na kula ba kya so mu samu ladan Www.bankinhausanovels.com.ng
mu biyú ko?” Ta murmusa ta ce, “Ai ka san da wankin
ba ka yi ba sai da nazo ina yi”.”
Mah ta ce, “Yauwa Suhaila, fada masa
gaskiya”.
Ya ce, “Jiya nayi na Baba, kema Mah
zanyi miki. Ita da bata iya ba, wankin nata jika
jika”
Mah ta ce, “Ya fi min naka”.
Suhaila cikin jin dadi tayi masa gwalo, shi
ne yayi nmurmushi ya ce.
“Zan rama ne”.
A dai dai lokacin da Suhaila ta soma
shanya. Ranar a gidan Suhaila ta wuni, sai dare
direba ya zo ya dauke su, yinin ranar sunyi shi a
cikin farin ciki.Suhaila Saddik Fillo ‘ya ce ga wani
hamshakin attajiri wai shi Alhaji Abubakar
Saddik Fillo, yana da matan aure uku.
Hajiya Hadiza ita ce matar sa ta lalle, ita
ce uwar Suhaila. Duk ‘ya ‘yanta maza ne su shida
ras, ita ta bakwai.
Suhaila ita kadai ce mace cikin dakin su,
saboda haka duk son duniya Hajiya Hadiza ta
dora shi akan Suhaila, don yanda ta ci burin irin
mijin da Suhaila za ta aura. Kun san abin kishi,
su abokan zaman ta duk sun aurar da ya ya
mata, ita dai sai mazan ne suka yi aure, yanzu
kuwa ta sa ido ta ga wanne irin miji Suhailan za
ta fito da shi.
Halima mahaifiyar Mubarak da Hajiya
Hadiza uwar su daya uban su daya.
Hajiya Halima tana da zumunci, don tana
masifar son yayar ta, itama Hajiya Hadizan babu
laifi, don tana taimakon ta da abubuwa. Misali
takan aiko Suhaila ta kawo mata shinkafa,
dankali, doya, taliya har makaroni, ga kwancen
kaya, wani lokacin ma har da sabo. Kuma ‘ya
yanta ta nuna musu girman kanwar ta a gurinta,
don haka sun tashi suna son Baba Halima kamar
yadda suke kiranta. Sai dazi tunda ta haifi
Mubarak ya soma ce mata Mah, su ma sai suka
koma gaya mata Mah din. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiya Hadiza ba ta damu da shakuwar
Mubarak da Suhaila ba, don ta san dole su so
juna tunda yan uwa ne. Amma tunda suka girma
sai ta soma tsorata da yadda Suhaila ta damu da
shi, don ita Hajiya Hadiza ta fi son Suhaila ta
auri miji mai: arziki, don itama ta ce wane
sirikinta ne. Shi yasa sam yanzu ba ta sakarwa
Mubarak fuska, tunda ta fahimci yadda ya sa
gaba Suhaila Saddik yarinya ce mai matukar
kirki da karamci, gata da mutunta mutane.Halinta ya sha bamban da mahaitiyar ta, don
wani lokacin ma ita ke sanya Ummanta ta yiwa
yar uwarta hidima, musamman ganin su biyu ne
rak, kuma tuni iyayen nasu sun rasu. Sai dai Hajiya. Hadiza ta fi mu’amala da
kawaye fiye da kanwar tata, sai dai duk da haka
ba ta bawa yayan ta fuskar da za su raina
kanwarta ta ba, amma sai ta shekara ba ta je
gidan yar uwar ta ta ba. Ita kuwa Halima tana yawan zuwa, da taga Www.bankinhausanovels.com.ng
kamar yar uwar tata na nuna gajiyawar ta, sai
itama ta janye. Don a yanzu danta Abbas bai
dade da aure ba, sam ba ta san komai akai ba, sai
satin bikin ta aiko mata, ita kuma ranar bikin duk
da bata ji dadi ba haka ta daure ta je, kuma danta
da mijinta sun halarci daurin auren.
Sam ba ta yi mata shisshigi ba wajen
bikin, saboda komai na ‘yan gayu ne, kawayenta
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG