DAN WAYE? CHAPTER 7 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
DAN WAYE? CHAPTER 7 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Mun tsaya
Kamar an jehota ta shigo,
mahaifiyar
Suhaila ce, ta ce.
“Halima, Suhaila dai ‘yata ce, ba zan bawa
danki ba, domin ba zan sai da akuya ta dawo tana
ci min danga ba, ki fada masa ya rabu da ‘yata”.
Mah ta ce, “Haba Yaya, nayi zaton duk
daya ne”
Ta ce, “A’a biyu ne, kwarya tabi kwarya”.
Ran Mah ya gama baci, ta ce.
“Shi kenan yaya kije ki aurawa Suhaila
karuna”.
“Ke Ni za ki fadawa magana?”
Ta ce, “An fada miki, in wata tsiyar kike
min daga yau ki daina. Don kinga ana girmama ki
sai kiga kamar tsoron ki nake ji? In kawayen naki
ne suka turo ki kije su nuna miki wanda ya fi
dacewa da Suhaila”
“Amma kin san ‘yata ba matar talaka bace”.
“Baki ji abinda na ce ba? Cewa nayi taje ta
auri Karuna”.
Malam Bala ya shigo, “A’a Hajiya Hadiza,
lafiya?”
Ta ce, “Ka yiwa matar ka da đanka magana,
su bar min yata”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tabdijan! Amma duniya ta allace,
Hadiza kinyi faduwar bakar tasa. Ashe bayan babu
Halima ba za ki rike Mubarak ba? Dan dan
uwanka? Kai wannan abu da ban mamaki yake”.
Kawai sai Mah ta sanya kuka, yayin da
Hajiya Hadiza ta fice daga gidan.
don
Mubarak dai har akai aka gama bai tanka
ba, amma yana jin radadin abinda Hajiya Hadiza
tayi masa.Suhaila Ce
zaune(office)din Mubarak hawaye wani na bin wani akan yayi
hakuri akan abinda Mami dinta tayi masa.
Ya ce, “Kiyi hakuri Suhaila, ina sonki ba
wai bana son ki ba, aurena dake akwai matsala, ki
auri irin wanda mahaifiyar ki take so.
Ina son Mah fiye da komai, bana son a
bakanta mata, domin ni daya Allah Ya basu, ni
zan zame musu hasken idaniya, gaskiya in ana
taba min su tabbas akwai matsala. Abinda nake so
dake Suhaila, maganar soyayya tsakani na dake ya
wuce, sai dai zumunci”.
Ta share hawayenta ta ce, “Shi kenan Mami
tayi nasarar raba kaunar mu wacce muka gina tun
kuruciya? Anyi zalunci a tsakanin mu”.
Ta mike a zuciye ta fita.
Surayyah da izzatu da mahaifiyarsu suna hira (text) ya shigo wayar Izzatu.
Salam. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dazu na ganki ke da Surayya kin saka
doguwar riga, kunyi shiga tamkar Arab, kun shiga
Sahad Ko in lissafa miki abubuwan da kika siyo?
Gabanta ya fadi, a yanzu ta soma tsorata,
anya ba da Aljani take soyayya ba? Komai nata ya
sani, duk inda za ta ya sani. Anya kuwa mutum
ne?Bata san sanda ta ce, “Umma, anya ba da
Aljani na hadu ba?”
Suka fashe mata da dariya.
Ku daina dariya, lamarin nan akwai ban
tsoro”.
Surayya ta karbi wayar ta kira shi, yana
dagawa ya ce.
“Hello Surayya”.
Gaban Surayya ya fadi, ta ce, “Waye kai?”
Ya ce, “Masoyin Izzat ne ni”.
“Me zai hana ka bayyana kanka a gare ta”.
Ya ce, “Lokaci bai yi ba”.
Ta ce, “Ya sunan ka’?”
“Masoyin Izzat”.
“Wa ya baka lambar ta? Kuma in tambaye
ka mana”.
Ya ce, “Ina jinki”.
“Kai mutum ne ko Aljani?”
“Ni mutum ne kamar ke”.
Mustapha yakan turo mata da kudi a waya,
in ya bushi iska ya aiko da (shopping) da kayan
kwalliya. Sun damu da su ganshi su san ko waye,
don Izzat ta damu da shi sosai, tana son sa, amma
bata taba ganin sa ba.
Wai dama ana haka? Zuciya takan kamu da
son abinda bata sanshi ba? Www.bankinhausanovels.com.ng
Tafiya ce ta kama Mustapha zuwa Cairo, ya
so a tura Mubarak don yanzu Mubarak shi ma na
keta hazo, don yanzu ya sai filin sa ana yi masa
gini, gashi ya mallaki Lifan dinsa, a yanzu yay
shar da shi.
Izzat ce suna tsaye bakin titi za ta tsallaka
ita da Surayya, sai taga Mubarak yayi parking),
bata manta shi ba, ta saki murmushi ta ce.
“Kai, dama kana gari?”
Ya ce, “Ke zan tambaya, ya hutu?”
Ta ce, “Yana gurin ku, ina mutumin ki
wanda ya mare ki?”
Ta dan sha kunu, “Kai za a tambaya”.
Ya ce, “Y ace in gaida ke, kuma ya ce in
baki hakuri”.
Ta ce, “Ta sai anjima, da alama ba ka so mu
gaisa”.
Ta ce, “surayya, wAnnan shi ne mụtumin
Dana baki labari”.
Allah da gaske nake za mu z0 ai da shi mu
baki haquri”.
Ta ce, “Bari mu shige kada mai gidana ya
ganmu ni da kai, damin yana da kishi”,
Suka tsallalke,
Suhaila rayuwarta ta shiga kunci, don ta
daina ci da sha yadda ya kamata, duk ta rame
Domin Mubarak ya sake layin wayar kuma in
taje gurin Baba Halima bata ganinsa, ita kum
tana jin lunyar ta tambaye shi.
Wata irin makauniyar soyayya ake tsakanin
Mustapha da Izzatu, don ita bAta sanshi ba, illa
siffanta shi a zuciyarta. Shi kam duk wani
shige da fice na Izzatu zatai akan idon sa take yi.
Tafiyar da yayi yana dawowa wanka kawai yayi
Don ko abinci bai ci ba ya ja mota zuwa kofar gidansu
Kamar ta san da zuwansa ta fito cikin kwalliya
Riga da wando ne a jikinta dinkin
Pakistan kalar (pupple), ya amshe ta. Gashin kanta
tufki daya tayi. masa, ya sakko a dokin wuyanta
kanta babu dan kwali. Mayafinta shara-shara ne,
fuskar ta a sake.
Yana mota yana kallon ta, taji haushin
rashin dankwalin da bata sa ba, duk kowa kallon
kyakkyawan gashin kanta yake.
Ya ringa siffanta laushin gashin, a zuciyar
sa ya ringa jin dama ya fito ya bayyana mata kansa.
Ya lumshe idanunsą, budewar da zai yi ya
bangota ta nufi lifan din wani matashi, fụskar ta
Cike da fara’a.
Yana kallonsu kishi ya kama shi, yaji ba
zai iya jurewa ba, A hankali ya sanke gilashin
motar ya kira wani yaro ya ce.
“Kai, .zo
Ya samu takarda ya rubuta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Waye wannan? Me kuke cewa? Na dawo saukata kenan nazo ina farin ciki na ganki da wani na fada miki ni mai sonki mai kishinki ne mustaphan ki
Ya ce, “Maza kaiwa lzzat”.
Yaron yace””Yar kụrma?”
YAce eh
Yana kallo ya mika mata yana mai yi mata
nuni da kyakkyawar motar. Kamshin takardar ya
doki hancin ta, a gaggauce ta karanta, shi kuma
tuni ya bar wajen.
Kai tsaye ta juya ta nufi cikin gida tana jin
haushin Saddik. Abokinta ne shi ma, kuma yana
sonta sosai, ita kuma ta dauke shi a aboki, don ita
da ta ce ta hakura da yin soyayya, amma ta rasa
yadda aka yi son Mustapha ya shiga cikin zuciyar.
ta.
Ta ji haushin kanta, don da yau taga sanyin
idanunta.
Tana shiga daki ta dauki wayarta ta tura
masa (text), ta ce.
Barkan ka da sauka cikin kasa mai ni’ima.
Zuciya ta tayi nisa wajen begen ka, kada kayi
tunanin komai, an halicce ni saboda kai ne, ko wa
zaka ganni da shi kar kayi shakka, kai kadai ne
cikin zuciya ba Wani sai kai. Ka daure ka da wo
ko na samu nutsuwa.Izzat.
Yana gama karantawa ya ji wani dadi ya
lullube shi, ya dinga (kissing) wayar aboda jin
dadin kalaman ta.
Zahra’u Baba Yakasal
Wai rai dangin goro, ashe itama “Yar kurma
ta iya soyayya?
Ya koma gida ya shiga suka hadu da
mahaifin sa, ya ce.
“Ina kaje ne haka daga dawowar ka, ko
gurin Mubarak kaje?
Ya yi murmushi da tsallen sa ya fada kan
kujera, ya lumshe ido yana mai ajiyar zuciya, Dad
dinsa yana kallon sa, ya ce.
“Ko ta mafarkin aka gani a ido biyu?”
Ya yi murmushi ya ce, “Daddy, ka taya ni
da addu’a, na kusa cimma burina, addu’ar ka nake
bukata”
Momi ta karaso tana fara’a, ta ce, “Wani
lokacin Alhaji in kana yi min fada akan yaron nan
sai in sha mamaki, ji fa dadewar da yayi amma
wanka yayi ya fice, ai ya zauna mu sake gaisawa”.
Ya ce, “Afuwa Mamni, gani na dawo”.
Daddy ya kalle ta, “Ke anje an gano surukar
ki za kiyi korafi”.
Mustapha ya ce, “Daddy wa ya ce maka can
naje?”
“Ai ni na sani, naga yanzu ta daina zuwa a
mafarki, da alama an ganta a ido biyu. Sai ka zo ga
Alpha sun shigo ka
bani labarin yadda ku ka sasanta tunda ka bata
mari”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ringa dariya yana shafa surmar kansa.
“A’a Daddy, na kasa bayyana kaina, ina dai
zuwa ina kallon ta a kofar gidansu”.
Daga Daddy har Mami dariya suke suma.
“Ka zama gwarzo, ka yarda kai namiji ne.
Ka fita filin daga, namiji baya tsoro”.
Sai yaji sun kara masa kwarin gwiwa, har
yana jin zai iya tunkarar ta.
Suhaila ce kwance falön gidan su suna
hiram da Umma kishiyar mamin ta sallamar
Yusrah taji, da tsallenta ta mike ta rungume ta, ta
ce.
“Yusrah, sannu da zuwa”.
Murna suke, Yuşrah yar babbar yarsu ce da
suke Abuja, tayi karatu ne a London, dan à can
aka haife ta har ta girma, shekarüñ su biyü dà
dawowa Nigeria.
Yusrah bata karasa Suhaila ba, anma kuma
Jinin su ya masifar haduwa, don sun kulle, babu
Wanda yasan tsakanin su sai Allah.
Suhaila ta sauki Yusrah yadda ya kamata,
sun kulle kansu đakin Suhaila, ta bayyana mata
halin da ciki, ta ce.
“Kinga ki bini mu wuce Abuja, sai mu nemi
inda yake aiki”.
Hakan ce ta faru, sun kulla, don Suhaila har
ta tambayi Abbanta ya kuma barta.
Sun shirya zuwa gidan Baba Halima, sai da
suka biya Sahad suka dan yi mata siyayya, sannan
suka wuce kofar gidan. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wata jibgegiyar mota suka gani, Yusrah ta
Ce.
“Ko yana nan ne naga mota kofar gidan?”
Ta ce, “Yusrah kenan, ba motar sa bace,
mutumin da ke da Lifan?”
Ta dan kada kafada suka shiga ciki.
Da yake yamma ce, suna zaune tsakar gidan
kan katuwar tabarma, Mah ce ita da Mustapha da
kuma Mubarak, suna shan rake. Dai dai lokacin
suka yi sallama, suka amsa musu. Mubarak yayi
kicin-kicin har Mustapha ya fahimta, Mah ta ce.
“Sannun ku da zuwa”.
Ta nuna musu guri suka zauna.
“Ya mutanen gidan?”.
Ta ce, “Suna lafiya, sunce a gaida ke”.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG