DAN WAYE? CHAPTER 8 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? CHAPTER 8 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Sun shirya zuwa gidan Baba Halima, sai da
suka biya Sahad suka dan yi mata siyayya, sannan
suka wuce kofar gidan. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wata jibgegiyar mota suka gani, Yusrah ta
Ce.
“Ko yana nan ne naga mota kofar gidan?”
Ta ce, “Yusrah kenan, ba motar sa bace,
mutumin da ke da Lifan?”
Ta dan kada kafada suka shiga ciki.
Da yake yamma ce, suna zaune tsakar gidan
kan katuwar tabarma, Mah ce ita da Mustapha da
kuma Mubarak, suna shan rake. Dai dai lokacin
suka yi sallama, suka amsa musu. Mubarak yayi
kicin-kicin har Mustapha ya fahimta, Mah ta ce.
“Sannun ku da zuwa”.
Ta nuna musu guri suka zauna.
“Ya mutanen gidan?”.
Ta ce, “Suna lafiya, sunce a gaida ke”.

Mah da kanta ta mike ta kawo musu ruwa,
ta kawo musu rake, ta ce.
“Ga rake, ku sha, kun same mu muna sha”.
Gaba daya hankalin Suhaila a tashe yake
ganin nuna halin ko in kula da Mubarak yayi mata,
ta daure ta gaida su, suka amsa.
Yusrah da tunda tazo take satar kallon
Mustapha, don ta ce ita wai dama maza suna da
kyau? Tana kallon lafiyayyar fatar jikinsa wacce ta
gogu da hutun jin dadi, ga wasu irin ido da take so
a ratyuwar ta.
Tsoro ya kama ta, Allah Yasa ba shi ne
Mubarak din ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suka hada ido da Mubarak, sai taga shi din
ma babu dama, don ya hadu.
Mustapha ya dubi Mah, ya ce.
“Mah, inaga in da anyi raken gwangwani
Allah ba karamin karbuwa zai yi ba, kinga mutum
ya huta da tauna”.
Mubarak ya ce, “Kai, ai ka tauna rake shi ne
dadin sa, amma in ka kurbe ai ya zama (juice)”.
Mah da su Suhaila suna dariya, Yusrah ta
Ce.
“Ai abu ne mai sauki, sai a ringa matse
maka”.
Mah ta ce, “Rabu da su, santi suke”.
Mustapha ya dan kara nutsuwa, ya ce.
“Mah, ba fa santi muke ba, hira ce tsakanin
mu”.


Mah ta mike tana cewa, “Suhaila, bakuwa
kuka yi ne?”
Ta ce, “Lah ba ki gane Yusrah ‘yar gidan Ya
Binta ba?
Ta ce, “Ina zan gane ta? Ai ban santa ba, ko
ba wadanda suke kasar Turawa ba?”
Ta ce, “Ita ce”.
Ta wuce daki ta barsu
Suhaila ta kashe murya ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Barek, wai me nayi maka naga kamar ba
kai murna da gani na ba?”
“Kai Mustapha ka ji abinda ta ce”.
Mustapha ya dube ta sosai, sai yaji ta bashi
tausayi, don yana tausayin duk wanda zai afka kan
zugin so, don ya shiga ya san zuciya ba ta samun
nutsuwa har sai tayi katari da abinda take so. So ba
wasa ba, don ya san ji da kai da girman kai da
akasarin yan mata suke fama da shi, amma gashi
ita ke zuwa. Lallai tana son abokin sa.
Ya dan yi murmushi, ya dubi Suhaila, ya ce.
“Madam, yayi murna da ganin ki mana
Ta dubi Mustapha ta ce, “Yanzu Barek ba
ya sona, ya sake layi saboda ni, ba ka fada masa
babu kyau yanke zumunci bane?”
“Tabbas kinyi gaskiya, saboda me ka sake
layi?”
Ya dube shi, ya ce, “Kai saboda Allah ka ga
yiwuwar soyayyar mu? Ka tuna girman mahaifa,
duk da na gari bashi da kamar su. To amma akanki an sawa mahaifiya ta damuwa, ni kuwa banga
amfanin soyayar da zanyi ta bata ran Mah ba.
Iyaye na bani da matsala da su to amma a yanzu
soyayyar ki ta kawo musu matsala. Ke. fa yar
masu kudi ce, gwanda kije ki auri dan gidan
Karuna.
Wani irin gumi ya’ dinga fesowa a jikin
Suhaila, tayi shiru uwa ruwa ya cinye ta.
Shi kuwa Mustapha sai yaji ransa ya Baci da
furucin abokinsa, ai duk wanda ya ce yana sonka
ya fi wanda ya ce yana kinka. Lallai abinda yayi
akwai wauta da karancin tunani. Ko ko tsananin
bacin ransa ya nuna akan abinda aka yiwa
mahaifiyar sa ne oho.
Yustah ta dubi Mustapha tayi wani irin
rudadden murmushi wanda tafe yake da sakon
nuna kauna, ta ce.
“Kana jin abokin ka, anya akwai adalci a
cikin furucin sa? Ina ji akwai cin fuska kwarai da
gaske ma, ganin ba mu cancanci a fada mana
haka ba”.
Sai lokacin Mubarak ya fuskanci yayi ba dai
dai ba, ya kuma kula da sauyin fuskar abokin sa.
Suhaila ta mike ta ce, “Bari in yiwa Mah
sallama”.
Ta aje mata ledar, ta ce, “Za mu tafi”
Ta ce, “Kin gai da su, amma daga zuwa
haka?”
Ta ce, “Ai sauri muke”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta fito ta ce, “Yusrah, zo mu wuce”.
Har sun kai soro Mustapha ya biyo su ya ce.
“Babu sallama za ku wuce?”
Kayi hakuri na kula abokin ka bashi da
adalci, ko kuma wata ya samu oho. Amma ni dai
na san ina son sa, zan kuma ci gaba da son sa. Ko
wani na aura wannan son yana dankare cikin
zuciya ta, amma kuma ni Suhaila ba na cikin mata
wadanda namiji zai wa gori.
Zan jure ciwon sa, daga yau ni Suhaila in
Barek ya sake gani na gidansu ya yanke min
kafafu”.
Mustapha da yasan su ke da laifi sai yace.
“Hab Suhaila, kada kiyi biyu, duk kanin ku
kunyi fushi, in daya ya hau sai daya ya sauka.
Sanin kanki ne ba halin sa bane, kiyi masa uzuri.
Mahaifi ba abin wasa bane, kin san taba mutuncin
mahaifi ai ba wasa bane, kiyi hakuri. Ku zo na kai
ku, ko da mota kuka zo?”
Yusrah ta ce, “Da mota muka zo. Sai naji ka
burge ni, kana da sanyin hali”.
Ya dube ta ya ce, “Ke ce mutum ta farko da
kika yabe ni, wala Allah don ba ki san hali na
bane. Amma ki rabu dani, bani da kyau ko nayi
wanka”.
Gaba daya suka yi murmushi, saboda ta san
raha ce.
Ta ce, “Haba, a duk kyallin fuskar ka?”
Ya shafi fuskar ya ce, “Kai, in namiji kyalli
ai abun ba zai yi kyau ba, mata Su ne aka sansu da
kyalli”.
Sai da ya ga sun shiga motar su sannan
Yusrah ta mika masa wayarta, ta ce.
“Kasa min lambar ka, kila mu kulla
Zumunci”
Ya amshi wayar ya sa mata, ta amsa tayi
(Saving), ya juya ya shiga ciki. Yana shiga
Mubarak ya ringa dariya, ya ce.
“Daga rakiya sai kuma ka dade?”
Ya sha kunu, ya suri mukullin motar sa ya
fice, shi ma ya biyo shi.
Izzatu ce a zaune a falo, yayin da Surayya
ke mata kitso. Kitson yayi kyau sosai, hannunta
anyi jan lalle, haka kafarta tayi kyau sosai.
Umman su ta shigo ta ce.
“Ke Surayya ko kishi baki yi, ki kalli Izzat
mace sosai, amma ke kafa fara sol, gashi kullum
babu kitso”
Tayi murmushi, dai dai lokacin wasu yara
suka shigo da manyan jakunkuna, suka aje.
Umma ta ce, “Ku, daga ina?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Suka ce, “Wai inji Mustapha”.
Surayya tayi saurin mikewa ta ce.
“Yana ina?”
Suka ce, “Ai yana bamu ya wuce”.
Ta ce, “Ya siffar sa take?”
Yaro daya ya ce, “Kai Surayya mai kyau ne,
gashin sa irin na Indiya, ga wani irin ido. Kada ki
ce nayi karya, ya fi Salman khan kyau”.
Daga Umma har Surayya suka dinga dariya.
To jeka mun gode”.
Suka soma zuge jakunkunan abin gwanin
sha’awa, kaya ne masu daraja da kyau.
Umma ta ce, “Izzatu, kina son sa?”
Ta rufe fuskar ta, Surayya ta ce.
Allah ko da can Izzatu bata soyayya ba
wani nan Mustapha ya samu karbuwa.
Mustapha ne cikin wata lallausar shadda
yar ubansu, dinkin ya zauna a jikinsa, aikin sama
(half gown) ne. Yanayin gyaran gashin kansa ya
dace da shi, fuskar sa cike da walwala ya fito falo
Dad dinsa na zaune ya ce
“Boy, sai ina?”
Ya yi murmushi ya ce, “Zan je filin daga
Daddy, kayi min addu’a na daina tsoro”.
Mahaifin sa ya dinga murmushi, sannan ya
Ce.
“Ina ji a hjikina za ta soka, zata yi alfahari
da samun mijin kwarai, domin kai dan albarka
ne”.
Ya shafa kansa yana mai jin dadin
kalmomin mahaifin sa, ya dubi Momi ya ce.
“Zan tafi”.
Ta ce, “Ka gai da min ita, Ubangiji ya baka
sa’a”.
Yayi addu’ar fita daga gida, haka da zai
shiga motar sa yayi addu’ar hawa abin hawa, ya
nufi unguwar su Izzatu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tafe yake yana kada kansa, yana bin wakar
mawakiyar nan Maryam Fantimoti, domin
wakokin ta da take yiwa Fiyayycn halitta babu
wacce ba shi da ita. Yayi alkawarin in bikin sa ya
zo ita ce za ta cashe masa a gurin (dinner).
Mustapha ya isa gidan, yana jingine da
motar sa, kirjin sa na dam-dam. Yan magana dai
sun ce, “fadduwar gaba asarar namiji”.
Ya dauko wayar sa ya rubuta mata.
“Gani na zo, ina kofar gidan ku. Yau nazo
mu fuskanci juna”.
Tana dubawa tayi wani irin tsalle tana kiran
Surayya, sai dai kash! Surayya na bacci, ta tura
masa gata nan zuwa, ya jira ta.
Izzatu aka shiga gyaran jiki, ta dade tana
ruwan ido akan kayan da za ta sa, sai daga can
hannunta ya dauko wata doguwar rigar ta. Shadda
ce hade da wani material wanda yanayin dinkin
kawai in ka kalla ka san ya ci kudi.
Wani shegen takalmi ne a kafarta, a kalla
kudin sa dubu sha biyu, yayi (matching) da
mayafin ta, haka da lips stick din bakinta, ban da
(shinning) babu abinda yake, ga wani mayataccen
Kamshi da take yi. Ta gama haduwa.
Umman su ta ce, “Izzat kinyi kyau”.
Ta ce, “Umma na gode. Umma Mustapha ne
ya zo zan fita”.
Ta ce, “To sai kin dawo”
Ta shige Umman, yayin da kusan ince
Umma ta fi Izzat murna, don ita kanta tana son
Mustapha duk da bata ganshi ba. Lallai tana jin sa
a cikin ranta, tana ganin ba karamin so yake yiwa
yar tata ba. Sai dai ba su san dalilin sa na boye
fuskar sa ba, ko da yake ai ta san duk daren
dadewa in dai mutum ne dole ya fito ya bayyana
kansa, don ciwon so ba abin wasa bane.
Ta fito gwadas da ita, Kofar gidan su ta
hangi lafiyayyar mota, ga wani matashi ya juya
bayan sa ba a ganin fuskar sa, saboda haka
Zuciyarta ta bata yakinin Mustaphan ta ne.
Ta karasa cikin cikin irin taku na rangwada
irn na rantsattsun yan mata, turarukan su sukaa
hadu suka ba da wani daddadan kamshi.
A hankali bakinta ya furta.
“Salamu alaikum”.
“Amin wa alaiki assalam”.
Ya juyo suka yi ido hudu, bakinta na rawa
ta furta.
“Kaine… kaine wa? Ba dai kaine Mustapha
na ba? Kai ne mutum na farko da na kasa manta
cin fuskar sa a gare ni, kaine mutum wanda ka
kasa yafiya a gare ni.
Karya kake ba ka sona, ka zo ka cuce ni ne
kawai ka cuci rayuwa ta, ta yadda ka san yamin
makauniyar soyayya ta inda na kamu da so. da
kaunar ka ba tare da na ganka ko naji sautin ka ba
Na fada maka tun farko ni din mai lalura ce, bana
ji zan iya magana ras kamar yadda ku kuke, ciwon
ya sameni ne da girma na.
Mutumin da ya kasa yin hakuri dani a
hanya taya zai aure ni? Kada ka manta shi fa aure
ana hada shi da hakuri ne, kai kuma da alama ba ku
ko hada hanya da hakurin ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dai dai nan Surayya ta fito, ta karaso cikin
fara’a da farin cikin ganin Mustapha, amma
yanayin da ta ga Izzatu sai tayi turus!
“Ki dube shi, bai ko ji kunyar yaudara ta ba
ki dube shi wai shi ne Mustapha na, bayan ya falla
min mari'”.
Ta juya gida agujwe.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE