DAN WAYE? CHAPTER 9 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? CHAPTER 9 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mu tsaya 

Na fada maka tun farko ni din mai lalura ce, bana
ji zan iya magana ras kamar yadda ku kuke, ciwon
ya sameni ne da girma na.
Mutumin da ya kasa yin hakuri dani a
hanya taya zai aure ni? Kada ka manta shi fa aure
ana hada shi da hakuri ne, kai kuma da alama ba ku
ko hada hanya da hakurin ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dai dai nan Surayya ta fito, ta karaso cikin
fara’a da farin cikin ganin Mustapha, amma
yanayin da ta ga Izzatu sai tayi turus!
“Ki dube shi, bai ko ji kunyar yaudara ta ba
ki dube shi wai shi ne Mustapha na, bayan ya falla
min mari'”.
Ta juya gida aguje.

Surayya ta dubi Mustapha suka yi cakare-
cakare da su uwa wasu zakaru, ta ce.
“Sannu”.
Ya murmusa idanunsa sunyi jawur, ya dube
ta ya ce.
“Zan so ace kin fuskance ni, domin ki
fahimci makomar rayuwa ta. So daya ne tak,
wallahi Izzatu na bawa, na san a farkon gani na da
ita ban kyauta mata ba. Ina so a matsayin ki na yar
uwarta ki wayar mata da kai.
A tun sa’ar da na mari abar sona, hasken
Rayuwa ta na gaza samun farin cikin rayuwa,
gaba daya na kasa sukuni sai da na binciko
Inda Izzat take Ina sonta, ina kaunar ta, ita ce farin
cikin rayuwa ta, ita ce jin dadina. Ina son ta, zan
iya hakuri da ita a duk irin yanayinta, ina son ta so
mai yawa, ba wai so kadan ba. Idan ta ce ba ta
sona lallai ne rayuwata ta tashi daga aiki”.
Surayya ta dubi aji da ji da kai irin na
Mustapha, sai taji tausayin sa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Waii Zafi biyu kenan, sunan wani littafi.
Ta san abin ya zamar mata biyu, don ga so na
Mustapha, ga kuma kinsa a cikin zuciyar ta.
Mutum daya? To wanne ne zai rinjayi wani?
Ta murmusa ta ce, “Kaje, duk halin da ake
ciki zan kira ka a waya ta”
“Uhm, ba zan iya tafiya ba, don ban san
halin da Izzat take ciki ba, kije ki gan0 min irin
halin da take ciki, ki kuma kamanta adalci, kada ki
fada min karya, Surayya baki yi kama da mutanen
banza ba”.
Ta ce, “To”. Tajuya.
Izzat da kuka ta shiga falo ta fadawa
Umma, tsoro da fargaba suka cika zuciya
Umman, tana tambayar ta lafiya? Sai kuka, shi ne
amsar har lokacin da Surayya ta shigo.
Umma ta dubeta ta ce, “Me yake faruwa?”
Tayi murmushi ta ce, “Ba kowa bane
Mustapha illa wanda ya mari Izzatu”.
Umma ta zabura, don babu ranar da ba zata
yi zancen marin ba duk da ba shi bane na farko,
amma tana yi masa kallon mugu, azzalumi, kuma
mara hakuri.


Umman su ta ce, “Ikon Allah, amma ai ance
in zaka yi so kayi don Allah, in zaka yi ki kayi shi
don Allah. Makiyi na iya rikida ya zama masoyi,
haka masoyi na zama makiyi”.
Ta kama kan ‘yartata tana girgizawa, yayin
da ta dago tana mai furtawa a hankalı, Ita kuma ta
nutsu tana kallon bakinta.
“Kiyi hakuri, ki bi komai cikin nutsuwa, ta
yiwu Mustapha alheri ne a tare dake. Ki tuna
komai mukaddari ne, ki sanya haka Allah Ya tsara
haduwar ku ta farko”.”
Ta ce, “Umma, bashi da tausayi, babu
ruwana da Mustapha, zan yakice shi cikin raina”.
Ta mike zuwa dakinta, ita kuma Surayya ta
sanar da Umma yadda suka yi, ta ce.
“Je ki ce masa an rarrashe ta, yaje abinsa”.
Ta mike, inda ta barshi anan ta same shi.
Kafin ta iso shi ya karaso, ya ce.
“Yaya? Meye ne labari?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Uhm, Ummna ta rarrashe ta”.
Ya ce, “Godiya nake yiwa Umma, zan tafi,
sai gobe. Ki kular min da ita, ki daure ki sake
rarrashin ta”.
Yajuya ya tafi, kai tsaye gida ya isa, a falon
mom ya yada zango, ya kwanta. Ya fita masallaci,
bai shigo ba sai da aka yi sallar isha.
A farfajiyar gidan su ya hadu da Alpha, yaCe.
“Oh mutumina”.
Ya ce, “Ya garı?”
Ya ce, “Kai dai bari, an doka min guduma
aka”
Sun zauna gefen dakin Mustapha, Alpha ya
“Me ke faruwa ne?”
Ya ce, “Alpha, dama na ce ba zata so ni ba.
To tace ni din mara hakuri ne, to wai ya zanyi ne”
“Kunyi (facing) juna ne?”
Ya ce, “Kwarai”.
Ya ce, “To gobe in za ka zanje in ganta”.
Ya ce, “Ai, ayi haka kuwa? Uhm Allah Ya
hada ni da mugun ciwo”.
Alpha yayi murmushi ya mike ya ce.
“Zan wuce gida inje inci abinci, za ka fita
majalisa?
Ya kada kai, “Au na manta, yau fa mutanen
ka ne zasu yi wasa”.
Ya shafa kansa ya ce, “Kai ana ta kai wa
yake ta kaya?”
Alpha ya fashe da dariya, ya ce.
“Mata masu gari”.
Ya ce, “Af, ka manta Dr. Yakasai ya ce
mace’yar kunama ce?”
Ya sake fashewa da dariyar mugunta yana
cewa abokin nasa.
“ka zo hannu, indai mace ce”
Cikin jin haushi Mustapha ya ce.
“jeka gida ka ci abincin ka dawo”.
Alpha ya ce, “Sai na dawo”.
Mustapha yayi gabá yana
mamakin al’amuran
Izzatu a yanzu duhun da take ciki ya yaye,
don ta gano da wa take soyayya, sai dai har yanzu
tana jin Mustapha a ranta. Matsayi biyu ya hau,
ana kinsa domin ya kasa gano matsalar ta ko ko
ya gano jin kai da izza ya sanya shi ya bata mari.
Lallai akwai artabu sosai.
Ta tashi zaune tsakiyar gado ta ringa tariyo
abubuwan da suka faru suka wuce, lallai rayuwa
akwai artabu a cikin ta. Sai ta sanya kuka har ta
bani tausayi.
Tana son sa, Mustapha kam ya shigar mata
Zuciya, sai dai har yanzu akwai haushin marin da
ya falla mata.
Suhaila ta shiga damuwa na rashin samun
kulawa daga Barek dinta, wai dama akwai ranar da
Barek zai iya nuna mata halin ko in kula? To
ma namiji ya bi maganar. mahaifiyar sa bare ita
mace? Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta san Mubarak ya fita gaskiya, anya za ta
iya hakuri da shi?
Maminta ta same ta tayi nisa cikin tunani
tana ta yi mata magana amma ba ta jita ba, saboda
haka sai ta ce.
“Ke, lafiyar ki kuwa?”
Ta dago a razane ta ce, “Mami babu
komai”.
Ta ce, “Da komai, ke banda tsiyar ki ba dai
kina batawa kanki lokaci kan matsiyacin yaron
nan ba?”
Ta zubawa mahaifiyar ta ido tana mamakin
furucin ta, sai kace ba dan yar uwarta ba.
Ta ce, “Ki tashi ki shirya kina da bako,
kuma ki ka sake naji wani abu sai ranki ya baci
sOsai. Sha sha sha, ana nuna miki inda za ki huta
kina janyo wa kanki wanda bai da shi, bashi da
kuma hanyar samu. Ko kina tunanin dan abinda ya
samu zai sa in amince? Ni fa bani da ra’ayin
wannan auren, gwanda ki fidda ranki akai, kin
gane?”
Ta gyada kai, ta fita.
Suhaila tayi da na sanin zuwanta Abuja,
saboda wani makocin gidan su Yusrah ne tunda ya
kyalla ido ya ganta shi kenan ya rikice, domin
matar sa ta rasu sakamakon hadarin mota, yaron su
daya. Khalid Musbahu Muhammad dan asalin
garin Gombe ne, Bafillatani, yana da uku-uku a
fuskar sa. Mutum ne mai fara’a, kuma ya dan
manyanta.
Ta shirya ta same shi a falo an cika shi da
kayan cima iri-ini. Bata yi mamaki ba, aboda sanin
halin Maminta
Ta ringa watsa masa kallon raini da
wulakanci, shi kuma yana yi mata kallon kasan
ido. Ya gani, amma da yake yana sonta sai bai
nuna ya gani ba, ya ce.
“Ranki ya dade, barkan ki da yini”.
Ta share,  tayi shiru kamar bata ji ba,
ya sake maimaitawa, sannan ta amsa.
“Ina ta zumudin ki amma sai naga kamar
baki yi murnar gani na ba”.
Ta yamutsa fuska, ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kusan haka din kenan”.
Ya ji zafin maganar sosai, wayar sa ta soma
(ringing) ya dauka, ya ce.
“Hello my boy, na sauka”.
Ya ce, “Yanzu haka ina tare da Auntyn
naka”
Ya dube ta ya ce, “Khalid ke gaida ke, ya ce
in baki”.
Ta amsa ba don ta so ba, yaron ya gayar da
ita, yace
“(Next) in Daddy zai zo Kano zan biyo shi
in ganki. Ina son ki, saboda Daddy ya ce kina da
kirki, kina da kyau, za ki kula dani”.
Ta ce, “To shi kenan Khalid, sai kunzo din”
Ta bawa mahaifin nasa, suka ci gaba da
hira, har suka kammala.
Bayan ya kashe wayar ya ce, “Kai Khalid na
sonki sosai”.
Ta ce, “Uh”.
Ya ce, “Ina son Khalid saboda yaron na da
hankali, ga hakuri, ga kokari. Kin san bayan
rasuwar Marwa nayi aureta wahalar da shi, duk
sanda ya ji ance zanyi aure sai ya ce shi kam in
mayar da shi Gombe.
Musbahu sai da ya ja ra’ayinta sukai ta yin
hira akan Khalid.
Musbahu ya sämu karbuwa gurin Mamee,ne ta
inda yayi la barin abin duniya, har ta kai iyayen sa
Sun zo tambaya.
Suhaila ta samu mahailiyar ta a cikin
(bedroom) dinta, tace
“Mami”.
Ta dube ta yayin da take kokarin rufe sif
din kayanta, ta aje kayan da ta dauko kan gado, ta
mayar da hankalin ta kan Suhaila, tace
“Ina jinki, kinyi shinu, ke nake sauraro”.
Ta ce, “Mamie, gaskiya bana son Musbahu,
Barak nakeso. Kin san ba zan iya rayuwar aure
Inba dashi ba Www.bankinhausanovels.com.ng
Tace “Ko? To bani kiji, ko uban ki a tafn
hannu na yake bare ke, aure in kinga an fasa kece
baki da rai. Ke din kwalli daya mace inga samu
inga rashi? Wallahi ba ki isa ba, kada in kara jin
kina yi min maganar Mubarak dan matsiyata, me
suke da shi?”
Ta ce, “Mamie a tunani na dan yar uwarki
danki ne
“Da kenan, amma a yanzu muna zamani
daga kauri sai gwiwa”.
Ta ci gaba da shirinta, ta ce.
Zan yi maganin halima ba Mubarak ba
don na san ita ke sanya shi, saboda kwadayi. Ina
so ke kuma daga yau ki sa wa ranki kin zama
matar Musbahu”.
Ta dan karyar da kai, ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Mamie, na yarda zan auri Musbahu. a
dalilin inyi miki biyayya, amma bana son sa. Ina
rokon alfarma a gareki, ki taimake ni ki hakura
kada kije gidan Baba Halima, domin za ki sake sa
masoyina ya tsaneni. Kin san Mubarak ba ya son
damuwar mahaifiyar sa, tuni shi ya fita daga harka
ta, ni ce na nace”.
Ta harare ta kamar. ta rufe ta da duka don
haushi, ta ce.
“Amma kuwa kin zama sauna, banda ke din
yar banza ce me zaki yi da shi? Ai komai kyan
surar ka in baka da kudi ba ka hadu ba, amma
zanyi maganin abin. Fice ki bani guri, sokuwa mai
ban haushi”
Mamie ta ci gaba da shiryawa.
Da kanta ta dauki mota ta fita, sun yi da
wata kawarta Larai za su unguwa, to sai dai ita
Laran ita ‘yar rakiya ce, kuma sai bayan ta fito take
sanar da ita yanzu haka suna hanyar Bida, sun
samu labarin wani malami mai zafi a can

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE