DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 11 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE
Umma ce ta matsa mata ta shirya tasa wani simple less ta yi kyau sosai, sai dai fuskarta ba walwala ko na kwabo, tun randa suka rabu da Faruk ba ta sake ganin shi ba ko duriyarsa ba taji ba bare ta leka ko ganinsa ta yi
Maryam ce ta shigo ta katse mata tunani,
“Haba Fati, tunda aka soma sha’anin bikin nan sam ba kya walwala, kin ki ki sake ko ba kya son auren ne?” *
“Yaya Maryam ba, haka bane, ina dai tunanin rabuwa da Ummana ne, Yaya Maryam taya zan soma
fita daga gidan nan in bar Ummana?”
Ta fashe da kuka. Maryam ke rarrashin ta,
“Ki yi hakuri Pati, kowa ma da haka ya bar gidansu*
Bayan fitar ta fati tana zaune ta hada kai da gwiwa tana kuka, ta ji an dafa kanta ta dago . da sauri wanda a zatonta Faruk ne, amma ina, Amin ta gani tsaye yana doka mata murmushi ya harde hannu a Kirji, ya yi kyau sosai. Daga ganin shi ka san hankalinshi kwance yake, fuskarshi sai kyalli take, fatarshi ta kara hasko ga sajen shi kwance suna kyalli.
Gaskiya Al’amin yana da kyau na karshe, ajin farko ne a jerin kyawawa, gaskiya da kyau ke sa so da ba yadda za a yi tayar da Amin ta zabi Faruk. Amma ina so a jini yake, so wani abu ne daban wanda ba ruwan shi da kyau ko muni, Allah kadai ke hada shi.
•Ganin tana kuka Amin ya sunkuyo ya tsuguna a gabanta, “Common amaryata me yasa kike kuka? Bana son ganin hawayenki”
Nan ko ta Kara fashewa da kuka don Kara rudewa.
“Oh! No my sister why? Kiyi hakuri na san kukan rabuwa da Umma kike, na yi alkawarin kawo ki ko wani wata”
Kura mai ido ta yi kawai hawaye na zuba, hakika ta rasa masoyinta mai sonta Faruk. Ta tuna lokacin da ya ce mata, “Fati kullum zan kawo ki, ki ga Umman ki!”
Wasu hawaye suka Kara turo wasu. Nan Al’amin hankalinsa ya Kara tashi, “Wai Fati me ke faruwa ne?” *Ba komai yaya, ni dai ka tafi kawai so nake na ga Umma kusa dani”.
“Ba zan iya tafiya ba sai kin min murmushi”
Murmushin dole ta yi don tana so ya tafi ya bata guri, don bata bukatar ganin shi. Cab!
Wai taya ya za ta iya rayuwar aure da Amin ne?
Ganin ta dan saki rai ya sa Amin ya fice.
Yana fita Faruk ya danno kai zuciyarsa cike da bakin ciki wai Fati ta yiwa Amin murmushi har da zuwa ya balbale ta da masifa.lta ko kura mai ido tayi tana kallon shi zuciyarta cike da tausayin shi. Ganin surutun yaKi Karewa ta katse shi.
Wai Faruk ka manta yanzu Amin mijina ne? Ka manta cewa yanzu ni Fati mallakin wani.
Ce? Haramun ne ka shigo min daki ba tare da
Iznin mijina ba”Sakin baki kawai ya yi yana kallon ta, «Wallahi Fati baki isa ba, kika auri Amin ba ni ba dole sai an kashe auren nan kin aure ni. In ba haka ba kashe Amin din zanyi in kashe ki sai na kashe kaina” Ya damke hannunta da Karfi, “Kiz0 muje gun su Abba da suka hada aurena da Maryam suka kuma hada naki da Amin su kunce su aura minke. Wai fati ya kike so na yi? Wayyo RAYUWATA! Wallahi Fati ba ki min adalci ba kin cutar da zuciyata, wai kin san bakya sona me yasa ba ki min addu°a na mutu kafin daurin auren ba? Ga shi har an kara daura miki aure ina numfashi”
Ya kara figarta, “Muje gun su Abban”.Tsoro da tausayi, fargaba da bakin ciki sune a fuskar Fati da zuciyarta. Shakka babu Faruk ya tabu. Nan tayi ta Kokarin fisge hannunta.
“Faruk kana hauka ne? In kai baka tsoron gamon ka da Ubangiji ni ina tsoro, ka san hakkin aure kuwa? Bare ni mace, to wallahi ka sake ni ko in.
• Bata Karasa mai zata fada ba ta hango
Umma da tabarya ta nufi gun Faruk, cikin hanzari da ita kanta Fati bata san tana da shi ba ta ture Faruk ta tsaya a gabansa tace Umma ki kwada min kar ki kwadawa Faruk” «Ki matsa ko in daka ku duka”.
«Wallahi Umma sai dai ki kashe mu duka,
Umma Faruk baya da laifi, laifina ne saboda haka ki kashe ni*
Da sauri ta fisgi hannun Faruk suka yi waje. Umma ta ja dogon numfashi layi ajiyar zuciya, “Shin wannan yara wani irin soyayya suke? Kai Allah kai mana magani”.
Nan Fati ta dawo ta kwanta rub da ciki tana kuka, wanna karon Umma kasa rarrashin ta ta yi, don ita kam kalmar rarrashin Fati da Faruk sun kare a bakin ta sai addu’a.
Da dare Abba da sauran family din har da
Yaya Babba suka musu fada daidai gwargwado, ya yin da Abba ya umarci Al’amin da ya dauki matarsa su tafi, don dama shi ba al’adarsa ba ce raka amarya ko wani bidi’a.
A nan fa Fati ta rike Umma gam ta dinga ihu wai ba zata tafi ta bar Umma ba. Kowa sai da kukan Fati ya karya mai zuciya, bare gogan da ya nemi can wani bishiya nesa dasu, yasa
Hmmm