DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 12 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE
bakin gilas yadda ba a ganin idonsa, Allah kadai ya san me ke cikin su.
Dole Abba ya Sambaro Fati yasa a mota,
• har Al’amin ya soma jan mota ta bude ta fito da
gudu ta yi cikin gida, suka bita da ido.
Umma kam basu yi mamaki ba, Abu da
Baba Iro kam anyi iyayen kwabo, don su ma
kukan suke. Fati kam dakinta ta wuce taja
drower ta dauko agogon da Faruk ya bata ta fito,
iyayen da kówa na kallon ta.
Ta nufi gun Faruk a gindin bishiya, gilas
ne a idonshi amma Fati ta gane kuka yake.
“Yayana ka yi hakuri, don Allah ka yi
hakuri kà dau kaddara, ka yafe mini”.
Nan ta yi ta kuka. Ganin haka ya kirkiro
dariyar dole, “Ba komai kanwata ki yi ladabi ga
mijinki, Allah ba da zaman lafiya”
Ya ja hannunta tana kuka ya kaita har gindin mota ya sa ta zauna a gaba, ya ce, “Amin
ga amanar kanwa ta in ka ci amana to zamu ci
taranka”
Duka’ suka yi dariya. Hakika Faruk kadai
ke iya sa ta dariya. Nan Amin ya soma tuki, fati na kuka tana dagawa Faruk hannu shi ma haka har suka bace. Nan dai dukkan su kowa ya nufi gida.
Ya yin da Maryam ma gidansu ta nufa, kowa zuciyarsa cike da tausayi da kadaicin lafiyar Fati. Faruk dakinsa na gidansu ya nufa, nan ya dinga tuno rayuwarsu da Fati, randa ta.
Fara shigowa dakin ita da Amin ya tuno, nan ya dinga ganin lokacin data kawo masa juice da snacks, tana mika masa take yi ya mika hannu, zai karba sai ya ga wayam. Nan fa ya kifa kai da bango, duniya tai mai kunci. Dafa shi ya ji kamar anyi, ya juya Fatin yake gani lokacin da take gwada kayan da ya siyo mata
A hankali ya soma mata tafi, “Kin yi kyau
Fatina’
Yana kokarin Zuwa gunta ya ga wayam, da sauri ya bar dakin don yana zolayarsa. Amma ina, yana fitowa falo nan ma ya dinga ganin su suna cin abinci tana ba shi yana bata, kota kawo mai coffe. Faruk dai ya kamu da haukan son fati.
Sama ya nufa dakinta, komai na nan sai ita ce bata nan. Nan idon shi ya hango mishi ita tana bacci, da gudu ya nufi gun da zummar murda mata kunne, sai dai kash! Ba Fatin sai filonta.
Haka da ya juya Fati kawai yake gani tana juya mai ta ko ina, kawai sai yasa hannu aka ya fasa Kara mai firgitarwa gami da ambaton sunan Fati.
Umma ta fito da sauri, ganin halin da
Faruk yake yasa Umma ta fadi. Wannan shine musabbabin kamuwar Umma da cutar hawan jini.
Hadaddiyar Jeep BMW, Alhaji Ibrahim wato mahaifin Fati ya sayawa Al’amin mota, an yi parking a cikin harabar gidansu.
Al’amin ya fito ya yin da Fati tsabar kuka batasan ma sun iso ba sai da Amin ya ja hannunta zuwa ciki. Kimanin sati guda amma Fati jiya iyau, kullum kuka, haka dai suka yi sallama da gida su ma suka nufi Lagos.
Maryam da Faruk suka rusa musu tsawon wata ukü amma Amin bai gane kan Fati ba, Wanda hakan ya dinga dasa zargi a zuciyarsa.
Anya Fatin na son shi? To amma da ya tuna hali irin na fati sai ya daina zargin haka, don da ko makaranta zata koma da kyar take rabuwa da Umma, bare yanzu da take jin tamkar sun rabu.
Tsawon shekara amma Fati taki sakin jiki da Amin, iyakaci ta mai girki, haka nan zata karrama bakinsa, sai dai sam ba ta sakin jiki ko wani walwala, kullum fuskarta na cikin kunci da damuwa. Haka nan tun bikinsu ba ta sake sa Faruk a idota ba
Ta kan jewa Maryam wuni ko su yi waya suyita hirarsu, wanna kadai ke debo ma Fati kewa. Haka nan ta kan je gun Umma kusan duk wata. Duk abin da Amin ya san zai yi ya farantawa Fati yana yi, ko abin ban dariya, yana sayo mata comedy films wai duk don ta sake amma ina. Wannan ya yi mugun dagawa Amin
hankali, haka nan bai so ya fada a gida don tamkar ya kai karar ta ne..
Habib, Abida da Iro da matarsa suka sa Fati gaba da fada da kuma mata nasiha da wa’azi kan hakkin aure da azabar da Allah ya tanadarwa duk mace mai bijirewa mijinta, haka nan sun dada lallabar da zuciyarta da cewa.
“Shin ya ya Yaya Babba za taji in har ta ji ga halin da ‘ya’yanta duka biyu ke ciki? Maryam tana zaman hakuri, haka nan Amin ma. Kin san dai ba za taji dadi ba, kuma bai kamata ace tukuicin da za a bata na kyautatawa iyayenku da ta yi ba”kenan
Wannan ya sauko da zuciyar Fati sosai har ta sawa kanta dangana da hakuri. Amin kam ya ga canji sosai, don kuwa sun dawo tamkar da yadda suke a gida, ta sake da shi sosai, wanda har Fati ta kai ga bawa Amin kanta, ya mai data cikakkiyar mace.
Wayyo! A ranar fati tayi kukan da bata taba kamantawa a rayuwar ta ba, haka nan taji kiyayyar Amin sosai a ranta. Rufe ido kawai tayi tamkar amin na soka mata allurai, sai dai ko da wasa ba ta nuna mishi kiyayyar ba.
Faruk karami kam ya zama dan gidan
Fati, don kullum yana gida gun Fati, tana
Hmmm