DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 13 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE

son shi da sakalta shi, wasa gaske sai ga shi ya dawo gidan, wanda ita ma in baya nan sam sai taji duk wani kunci ya dawo mata, amma in yana nan ya kan debe mata kewa.

Al’amarin Faruk kam sai addu’a, don ramu iya cewa Lagos ma yana zaune ne don Fati, duk da ba ganin ta yake ba amma kullum yana nan manne da hotunanta da yake manne ta ko ina a dakinsa.

Shi ma dai su habeeb sun mishi nasiha  kamar yadda su kai wa Fati, amma Faruk ta bayan kunnensa ya bi. Ko da yake shi ma baya da laifi, duk yadda ya yi ya danne zuciyarsa ya kasa.

Habib gaskiya so bala’i ne, na yi iya Kokarina in manta Fati na kasa”. Nan ya kwanta ya yi ta kuka sosai. Habib ya tausaya masa bai

Kara ce mai komai ba ya tafi ya barshi.

Yana zaune ya kurawa hoton Fatin ido, yanzu tana can tana wani rayuwa can da Al’amin, ko tana son shi har yanzu oho? Allah ka kashe ni in huta da ciwon son Fati da zunubin da nake kwasa. Ya Allah ka yafe min.

Wayarsa ta yi Kara, bai dai san wayeba amma ya daure ya dauka. Ko a mafarki bai zaci wannan muryar ba, Fati ce

“Fatina ke ce? Kece  Fatina? Kina sona za ki fito ki aure ni?”Yaya Faruk wannan ba ita ce damuwa ta ba, abin da zan gaya maka shi ne, ka gyara zaman gidanka in ba haka ba wallahi son da nake ma zai dawo tsana. Faruk ka yi kokari ka roki

• Maryam gafara ku yi zaman lafiya, ka ba ta farin ciki. Hakika ni na mika rayuwata ga mijina Al’amin wanda bana jin yanzu zan iya rayuwar aure da kowa sai shi.

Faruk idan kana sona da gaske ka bawa

Maryam farin ciki. Yaya Faruk ina tabbatar maka da cewa bana sonka yanzu mijina Amin nake so, ya rage naka ko ka so matarka, ko kar ka so. Sai anjima”

. Ta ajiye wayar.

Ya yin da Faruk ya dinga jin tamkar an watsa mai garwashin wuta. Ya kalli hotonta,

“Wallahi karya kike kina sona, wallahi na san Fatina kina sona, ni na tabbata Fati dan ni aka yi ki, nima dan ke aka yi ni na tabbatar ba za ki daina sona ba har abada”

*

*

Faruk dai ya canzawa Maryam da sauki za a ce ba kamar da ba, in mun yi la’akari da mugun son da yake ma Fati, yana amfani da maganar ta. Yanzu komai ya dan yi sauki, hankalin su Umma ya kwanta ganin yanzu komai da dan sauki ba kamar da ba.

Wani abin mamaki wai Maryam wani cikin take da shi tsawon wata uku, ya yin da

Faruk yanzu shekarunsa kusan

takwas,

kamanninsa da babansa ko sai karuwa yake.

Tamkar dai Faruk din aka sake haifowa yake

Kara girma.

Fati na kwance kan makeken gadonta ta

Kurawa silin ido, rayuwarta kawai take mamaki yadda abubuwa ke juyawa. Amin ne ya shigo ya katse ta, ta kalle shi ta yi murmushin dole, don duk wani abu da Fati ke wa Amin dole take tilasta kanta ta yi.

Ta ce, “Sannu da dawowa yaya” “Yauwa my sister”

“Ina Junior?” Ta tambaya.

“Na barshi can sai anima in dauko shi”

“Haba yaya ka san bana son ya yi nosa dani shi ne ka barshi”

Nan ya make murya yana kwaikwayon ta, ta juya baya wai ta yi fushi.

Ya ce, “Kin san ko me Maryam ta ban in kawo miki?”

Ta juyo da sauri, “Meye ne?”

Langa ya mika mata, ta bude farfesun kifi ne ya ji attarugu sai kamshi yake. Nan da nan ta hau ci.

“Ba tayi ne?”

Ta ce, “Kwalele, da ban karba ba asha wannan kuma after ta sha shi”Ta ci gaba da

shan farfesu, nan take ta shanye har da sude

kwano.

Shi ko ya zuba mata ido, nan ta bar lashe kwanon ta ce, “Meye kake kallona?”

“Ina kallon baiwar mata da Allah ya min da ba kowane namiji ke da kamar sa ba. Kin san kina da kyau Fati?” Murmushi ta yi tace” haba Yaya duk kyauna ina tafin Kafarka, ka san ni ban taba ganin namiji mai kyau irin ka ba. Allah ya ma baiwa da yawa, ga kyau ga hakuri ga kirki ga addini. Ka san ba kowa ke da abin da kake da shi ba. Matsalarka daya”meye?” Ya lambaya.

Sai tayi nesa da shi ta soma dariya sannan ta daga hannu sama wato alamar bai da tsayi sosal.

“Ni kike cowa bani da tsayi?”

Nan ya bita ta kwasa da gudu suka yi ta zagaya falon wai shi dole sai ya kama ta ya ja gashinta. Tana cikin gudu hajijiya ta debe ta sai gata a kasa, tuni amai ya kawo kai.

Duk Al”‘amin ya rude ya rasa abin yi, gaba daya ta wanke su da kifin da taci. Amai ya Ki karewa har ya tausayawa Fatin, nan da nan ya kira wayar Faruk amma tana rufe, dole ya kira

Dr. Zainab makwabciyar su ta duba ta.

Da kyar la samu aman ya tsaya, Fatin ta dinga mai da numfashi a hankali, ya yin da Amin yake fadin sannu yafi sau dubu.

Hmmm

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE