DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE
DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE
Ya ja hannun Fatin suka tafi, ya yin da aka
barshi tsaye yana fidda hawayen bakin ciki. Shi
kam yau ya tabbatar Abba ba ya son shi.
Umma ce ta zo’tana ba shi baki da su Baba
Iro. Ba don Umma ta so ba ta tafi ta bar danta
cikin wannan yanayin, dan ta san yanzu ma
Allah ne kadai ya kawo shi lafiya.
Har sun kusa shigewa Fati ta juyo ta
ganshi tsaye yana hawaye, wannan ya sa ita ma
ta fashe da kuka, ya yin da ta yi niyyar komawa
gunshi Umma ta rike ta, don kuwa in ta barta
jirgin sai ya tashi ya barsu, Nan ta dinga kwala mai kira tana daga mai hannu, shi ma ya dinga daga mata har suka tafi. Lokacin da su Fati suka isa London, gidan abokin Abba suka wuce, wanda dama kasuwanci ne ya kai su ‘yan Najeriya ne musulmai. Alhaji Mohammed da matarsa Hajiya Aisha sun karbe su hannu, bibbiyu gami da musu alkawarin rike Fati hannu bibbiyu, dama Allah bai taba basu haihuwa ba.
Bayan an gama mata komai suka yi shriin
dawowa, ya yin da suka ce mata duk lokacin da
aka yi hutun za a mata biza ta taho. Amma Fatin
sai ta ce ba za ta dawo ba sai ta gama karatu, wai in tana zuwa hutu kullum in za ta dawo za ta yita tunani. Abba da Umma suka ce za su ringa
kawo mata ziyara akai-akai, da kyar Fati da
Umma suka rabu da kuka da rarrashi Fati ta
hakura.
****
Maryam na zaune a falo ta buga tagumi,
tunda Faruk ya tafì ya barta zaune a gun ba ta
motsa ba, Kwakwalwarta ke juyi, shin meye
tsakanin Fati da Faruk? Ta bawa kanta amsa,
“Ba komai, ai dama tun tana karama yake sonta, ya ma za a yi haka nan ta bawa kanta amsa saboda shakuwar da suka yi tun suna kanana wannan yasa Faruk baya so ya yi ne sai da ita.
Faruk ya shigo ta tare shi,Yaya Faruk
sun tafi?Sun tafi”.Allah sarki na yi missing my sister'” In ji Maryam.Maryam ai da kina son Fati da baza ki bari ta tafì ba”To yaya Faruk ya zan yi?”Me yasa baki gaya min ba?”Ai na dauka ka sani, to me yasa su Abban suka ki tafiya
Ya za a yi ita daya ta tafi wani duniya
karatu tana mace haka ne, amma na san Fati very well. insha Allah ba komai”Dama ai ban ce da komai ba, ke dai you will not understand”. Nan ya tashi ya yi ciki yabarta.
**
Faruk ya kulla a ranshi zaibi Fati, sai dai
kuma ba zai je nan kusa ba, saboda tabbas ya san tana son shi, ta dandana ciwon da shima yake ji, sai dai ya tabbatar son da yake mata ba ta mai rabin shi, don kuwa Faruk a duniya kam duk wani abu da yake so, to yana bayan Fati. Yana sonta SO,So I don’t even know
how to explain”. Baki ba zai fada ba, biro ba zai
rubutawa ba, ido da zuciyar Faruk ne kadai za su
iya sanin irin jarababben son da Faruk kewa Fati,
sai kuma Allah.Cikin kwanaki kadan Faruk ya canza ya dawo ko in kula da aikinsa. Duk tsananin tsabta da gaye irin na Faruk ya ajiye su, in ya yi kokari ya yi wanka to shi kenan, ga wasu kananan gemu da gashin baki da suka fito masa ba ruwansu da shaving, ko wani gyaran jiki. Sam
abun bai damu Maryam ba, don ta san mijin nata
da murdadden ra’ayi.Tsawon wata hudu Faruk bai koma gun aikinsa ba, ga shi suna ta aiko mai gabo da suna tsananin bukatarsa, amma fir ya ki.
Ganin haka yasa Habib ya kai kararsa gun
iyayensa. Abba ne ya kira shi ya yi mai fada mai
tsanani.Wai Faruk me yake damun ka ne kake
son kashe rayuwarka? To ko ka fada ko kar ka
fada, wannan ba ruwana bane, amma abu na
Karshe da zan gaya maka shine, ka wuce ka tafi
gun aikinka kar na sake ganin ka a gida, in ba haka ba to bani ba kai, kuma na yafeka cikin
“ya yana”Nan ya tashi ya barshi. Alh. Ibrahim ne ya taso ya yi ta rarrashin, haka nan Umma, suka yita tausasa shi don yanzu ita ta daina mai fada,
saboda sanin halin da yake ciki.
Dole yasa suka soma shirin barin Bauchi
zuwa birin Ikko. Maryam tana ta faman shirin
‘abu ya gagara, jiri ya dinga dibarta, dole ta cije
ta ci gaba.Amma sai me, murdawa cikinta ya dingayi, kan ka ce kwabo amai ya kece tamkar za ta yi aman hanjin cikinta. A wanna halin su Umma da Umma Aysha suka same ta, ya yin da take numfashi sama-sama. Ciki ta rike tana
“Umma cikina!Umma cikina!!” Nan suka rude. Abba ne ya kira Faruk don duba Maryam. Ganin yadda take rike ciki yasa Farum yai mata scaning, a nan asibitin dake cikin gidansu,
Umma dai kura mata ido ta yi alamar
kamar ta san cutar Maryam din. Ya yin da
sauran kowa ya yi tagumi cikin damuwa.