DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 8 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE

soma rawa, gumi ko ya yanko mai tako wane bangare na jikinsa. Shi dai bai san ya aka yi ba, sai ya tsinci kansa da fadin “Na taya ka murna, bari in barku ku zanta Cikin hanzari ya bar gun don gudun kar asirin shi ya tonu. Bayan tafiyarsa Amin ya kalli Fati,

“Kanwata me kika ce?”

Kanta sunkuye yake ya yin da jikinta ya yi bala’in sanyi, murmushin dole ta yi tace Yaya Bature ka san kaima abu ne mai wuyar gaske yadda na dauke ka tamkar yayana lokaci guda ka furta min kalmar so in baka amsa take. Sannan ka san komai yana buqatar nutsuwa, tunani da kuma shawara. So please ka ban dan lokaci kadan zan baka amsa

“To na gode Kanwata, plcase ki yi shawara mai kyau don wallahi Kanwata in bake ba, ba zan taba aure ba, saboda ba macen da ta dace da rayuwata. Dama ganin kina yarinya shi yasa ban gaya maki ba, amma yanzu sou are Anatured enough Murmushi kawai ta yi ta wuce, ya bita suka jera.

Sam ya kasa barin cikin falon yana jiran shigowar su Fati. Shiru, nan ya Kara jin wani bala’in kishi, wato Fatin son shi take har tana hira da shi.

Shigowar su ce ta yanke mai tunani. Kai tsaye suka shigo suka ci abinci kowa ya kama gabansa, fati da Faruk kam su kadai suka san abin da ke damun su.

Tsawon kwana uku Fati ba abin da ta yanke, ta yanke wancan ta saka wancan. Ganin Amin na matsa mata Fati ta soma neman shawarar Umma.

Umma tayi murna sai dai tana tausayin danta da fatin duka. Umma tace To Fati ai bakya ta zama haka ba, kema kin san dole ki yi aure, ya yin da kin san kin rasa Faruk tunda ya auri “yar’ uwarki, na tabbata Al’amin zai rike ki kamar yadda Faruk zai rike ki, kuma yana sonki kamar Faruk”Fati ta fashe da kuka ta ce, “Duk duniya bani da mai sona wallahi irin Faruk, ban da masoyi kamar sa. kuma bazan taba samun mai sona kamar sa ba

Umma ce ke rarrashin ta. “Ki yi hakuri kuyi fatan Allah sa haka shi ne mafi alheri a gare ki

Bayan Umma yaya Maryam ta samu, ta yi murna ta musu fatan alheri. Sannan Abida.

Abida ma dai shawarar da ta ha ta kenan

“Fati ki yi hakuri ki dasawa kanki hakuri da dangana. don ba yadda za,a yi ki zauna ba aure, kuma kinga iyayenki ma ba zasu barki ba.

Kuma kinga Amin ma na gida ne, shi ma yana sonki, Allah kadai ya san abin da ke boye da ya saukar muku da wannan Kaddarar.

Allah Fati Amin na sonki tun ba yau ba na

Lura yana sonki sosai, wanda zan iya cewa in baifi faruk sonki ba to za suzo daidai .

A fusace fatin ta kalle ta, ta buga mata Barara. Lokaci guda kuma hawaye ya biyo baya.

“Haba Abida. keda ya kamata ki bada kyakkyawar shaida a kan soyayyarmu da Faruk sai kice wai Amin ya fi sona da shi. ke kin san irin son da Faruk ke min kuwa? In baki sani ba bari in gaya miki. Faruk shine mutumin dake sona tun randa na fado daga cikin uwata, shi ne mutumin da yake sona tun ina yarinya, shi ne mutumin da yake son ganin farin cikina ko da shi yai rasa.

A dalilin sona Faruk ya canja, a dalilin sona Faruk ya shiga bacin rai, dalilin son da yake min yasa kowace magana na fada mishi zaibi ko da kowa baya so kawai don ya ganni cikin farin ciki. A dalilin son da yake mini ya yi auren da baya so, ke kanki kin san yadda auren Faruk ya kasance, ya daure ya yi auren nan tsabar sona baya iya musa duk abin da na gaya masa.

Sona ya mai da Faruk tamkar mahaukaci, sona ya hana shi aiki, sona yasa ya zauna cikin kunci da bakin ciki. sona ya mai da faruk wani iri tamkar ba shi ba.

Ki duba tsabta jan aji irin na Faruk, duk dalilina Faruk ya dawo wanka da kyar yake yi, jan aji kuma ya Kare kullum sai magiyar a aura masa ni

Faruk baya cin abinci ya rame yayi baki duk ya dawo wani iri tamkar ba shi ba, sannan ki ce wai Amin ya fi sona, yaushe Amin ya soma sona? Sai da na girma na dawo mutum ya soma sona. Za ki hada soyayyarsa da Faruk, kai in ma ya fi sona to ni Fati bana son sa, kin san ko duk kauna da so da zai nuna min a banza ne in ba zai bani soyayyar Faruk ba.

Hakika Abida ina son Amin soyayyar jini, amma batun in so shi kam babu shi, ni kam na

san soyayya da duk wani jin dadi ya Kare min tunda na rasa Faruk. Abida me zan ma Faruk in biya shi a duniya sai addu’a”Abida ta rungume ta tana kuka, “Fati ki yi

hakuri ba wai ina nufin Faruk baya son ki bane, ba wai ina so in sa miki son Amin bane ki kwantar da hankalin ki, amma kema kin san ni daya na isa shaida a kan soyayyarku. Ki yi hakuri ba wai da nufin wani abu na fada ba Ta amsa “Ba komai Abida, ni dai ki taya

ni addu’a Allah ya kashe ni kafin auren nan”

“Haba Fati, don Allah ki daina fadar haka

kar ki yi sabo”Dukkansu zaune suke a harabar gidan

iyayen sune kawai suke ciki. Al’amin ya kalli

Hmmm

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE