DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 9 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE
Amin yace wato kanwata kinki bani amsa har yanzu ko tace a,a yayana zan baka amsa ai yanzu nayi shawara da kowa sauran babban yaya ne kawai bamuyi shawara dashi ba
Dukkan su sukai mata caa akai wallahi fati baki kyauta ba nazaci shine mutum na farko da zakiyi shawara dashi to meye amfanin fada miki din da nayi a gabanshi
Tace yaya amin ba haka bane ganinshi nakeyi wani idi ba kamar yaddah na saba ba duk yana min wani iri
Maryam tayi murmushi, “Kar ki damu Fati bake kadai yake ma haka ba, wannan shi ne halin da Faruk ya tsinci kanshi tun gabannin auren mu, ni dai iya fahimta ta akwai wadda Faruk ke so su Abba suka hana shi. Don Allah sister ki gaya mashi ko wace ce ya auro ta, indai zamu ga sakin fuska ni da Faruk junior”
Jikin fati ya yi sanyi, ta kalli Faruk ya kau da kai. Tace “Yaya Maryam wannan ai tsakanin kune ke ya kamata ki fada masa ni dai yanzu
damuwata mu yi shawara. Shin babban yaya me kace game da aure na da Amin?Cikin bacin rai take magana. don gaskiya ranta ya baci kan maganar Maryam. Amin yace, “Haba fati sauran da kika yi shawara dasu in public kika yi ne’?
“Barta Amin ba sai ayi shawarar mu gani ba
Nan ta tashi tace To muje nan small
falo”Kallon shi take idonta cike da bacin rai,
Yaya Faruk na yanke shawarar auren Amin
“Me kika ce?Abin da kunnen ka ya ji
“To ba sai ki aure shi mu gani ba”Sai ka hana
“Ai wato fati dama Amin kike so shi yasa
k. “
Saurara Faruk, ai dama na gaya maka
bana sonka. kaje ka samu matarka ku daidaita ya fi maka, kai ko gudun daukan hakki kakayi Kallon ta kawai yake har ta gama surutunta. “Ai dama na gaya miki tun farko ko kin manta, to bari kiji. Faruk din ma a Kaddara aka same shi. Dole ki min rashin kunya tunda kinga ina biye miki. Ai a tunanina in mutum yana son mutum baya nufin yana Kin ka.
Fati kin mai dani tamkar makiyinki, Fati ai ko darajar zumunci ya ci ki daina min rashin kunya da magana ta ganin dama. Yanzu kin tabbatar zaki yiwa Amin din naki haka? Ko don ni bakya sona ne kike min haka?
Ba komai Fati na gode tunda sakayyar da zakimin dashi kenan. Allah baku zaman lafiya”. Ya mike ya bar gurin. Kiran shi ta dinga yi tana kuka amma ina ko juyowa bai yi ba. Lallai yau Fati ta kai shi makura.
Satinsu biyu a London suka soma shirin komawa gida. Fati kam sam taqi dole aka shirya tafiyar da ita tunda taqi karatu kuma zamu iya cewa ya kare. Al’amin ne ya samu Abba yake sanar da shi. “Abba dama dai ina son gaya maka Fati nake so da aure Abba ya ce, “To ita Fatin tana sonka?”Eh, Abba dama sai da”Sai da ya
sunkuyar da kai alamun jin kunya.
Abba ya ce, “To Allah sanya alhori, amma dai zan tuntube ta na ji Cikin kwanaki kadan koya ya san da soyayyar Amin da Fati da kuma zancen aurensu.
Yaya Babba kam ba wanda ya kaita mura, ita bata Ki suyi ta auren dangi ba.
Har ana washegari daurin aure amma ita
Fati ba ta amincewa zuciyarta har yanzu wai
Amin za ta aura ba, ya yin da ba ta sake ganin Faruk ba tun ranar,
Zamu iya cewa Abida ce ta yi komai na bikin. Ta nemi sauran kawayensu suka raba cads da sauransu.
Kwance take rub da ciki, ko shakka babu kuka take. Umma ta shigo, “Taba Fati, tace mutum kullum ba shi da aiki sai kuka? Wai ku wasu irin mutane ne ba za kuyi hakuri ba? Kin Ki ki yi komai, auren nan fa ba dole aka miki ba ke kika zaba, kin bar yarinyar nan ita ke komai, ita ma yanzu abun sun mata yawa.
Saboda haka yanzu ki tashi ki shirya kuje direba na jiranki ku dauko dinkunan ki’
Dole ta tashi ta shirya ta fito. Umma kam har ga Allah tana tausayin Fati, sai dai in ba jan ido ta mata ba, ba za ta tashi ta dan dinga shiga jama’a ba.
Tafiya take a hankali idonta ko ya ci kuka ya gaji, ta bude motar ta shiga, har yanzu shesshekar kuka take. Ba Karamin mamaki ta yi ba gain har yanzu basu yanki hanyar Central ba, sai suka mike kofar Gombe suka nufa, sai gasu a hanyar Kirfi.
Da karfi ta kira shi, “Malam Isa lafiya?”
Ba Karamin firgita ta yi ba da ta juyo ta ga
Faruk.
Parkin ya yi gefen hanya ya fito ya jingina jikin motar, ita ma ta fito.Yaya Faruk lafiya?”
“Lafiya lau Fati, dama dai sallama zamu yi shi yasa na dauko ki. Fati Allah ya baki zaman lafiya da mijinki, ga gudunmawata
Hmmm