DEEMAH CHAPTER 1 BY ZAHRATEEY
DEEMAH CHAPTER 1 BY ZAHRATEEY
Time of death 3:15pm”… Shine abin da ya fara yawo a kwakwalwata, kallon hagu da dama nayi sannan na kalli gadon da nake kwance, abin da zan iya tunawa shine “ina tsaye a bakin _Emergency unit_ din naga wata nurse biye da wani Likita sun fito daga cikin d’akin cikin sauri, sai kuma naji Likitan yana cewa _Time of death 3:15pm_ ita kuma Nurse din tana rubutawa a wani folder daga nan naji jiri ya fara d’aukata kafin na tallafi kaina har na kai kasa, ina jin sanda _Baba K_ yake cewa _Khadeemah! Khadeemah_ ki tashi sai dai kafin ya sake magana naji kaina yayi nauyi duhu ya mamaye idanuna daga nan ban sake sanin mai ke faruwa ba sai yanzu” _Mamita_ “oh Its just a dream” na dinga maimaitawa a cikin raina, domin bana son na yarda da abin da yake yawo a cikin kaina.
+
Bud’e k’ofar da akayi ne ya dawo dani daga duniyar kokonton dana shiga ” _Khadeemah_ kin tashi? _Kursiyya_ shiga ki taimaka mata ku fito mu wuce gida, kinga lokaci na wucewa” duk yanda naso naga fuskar _Khalil_ k’in yarda yayi, da sauri na mai da kaina a kan _Kursiyya_ ita ma sam-sam taki yarda mu had’a ido, a haka har ta taimaka min na sauka daga gadon tare da zura takalmina kafin muka fara takawa a hankali saboda rashin kuzarin dake tattare damu duka.
STORY CONTINUES BELOW
Sam_sam na kasa tsayar da hankalina guri d’aya, tafiya muke yi shuru ba mai cewa dan uwansa wani abin, kuma duk yanda naso na kalli cikin idanunsu abin yaki yuyuwa, a haka har muka isa gida.
Wani irin fad’uwar gaba naji ganin _Kawu Ade_ kanin _Mama Qudi_ “tabbas ta faru ta kare, _Mamita_ ta tafi ta barni, _Mamita_ mai sona mai kaunata, ita kad’ai ta yarda cewa ni mutum ce kamar kowa kuma ko wani bawa zai iya samun irin nawa kaddaran, baiwa ce kawai da sai wanda Allah ya nufa da samu zai samu”.
Dak’er na iya d’aga kafa ta nabi bayan _Kursiyya_ dake tsaye a jikin k’ofa tana jirana, duk da cewa taki yarda mu had’a ido har yanzu amma na riga na gano abin da basu so in sanin, _Kawu Ade_ ya fallasa komai, naga duk abin da ya faru da a cikin idanunsa “Kashe _Mamita_ akayi, kisan gilla, wuk’a aka da6a mata a ciki har sai daya fito ta bayanta” rintsa ido na nayi cike da takaicin masifan da _Baba K_ ya kunso mana, gashi ana ta mana d’auki d’aid’ai tun daga kan k’anwata _Kabira_ aka fara sannan _Kubra_ sai _Kule_ kafin _Khadija_ wato _Mamita_ Allah ne kad’ai ya san wa kuma suke hari a halin yanzu.
Tunda nasa k’afana a cikin gidan nake jin kunjin kuka daga 6angarori mabanbanta, kasancewar gidan mu gidan yawa ne mai d’auke da sashi daban-daban shiyasa yanayin kukan ke fita da sauti iri-iri wani daga nesa sosai zaka ji wani a kusa wani a d’an nesa kad’an haka dai kamar gidan koyon kuka, side d’in Maman mu na nufa wato _Mama Qudi_ duk yadda mutane suka so in tanka musu kin yarda nayi, ina jin yadda wasu ke zagi na, yayin da wasu ke tsinemin wasu kuma suke bina da kallon tausayi, inajin _Inna Abu_ kakarmu tana cewa “ai dama duk wanda bai ji bari ba zai ji hoho, tunda _Baba K_ ya auro kabila ai dama dole ya rinka shiga halin ni’asu, kuma tun ina ciki ta ba shi shawaran a 6arar dani saboda yanda ya samu karayar arziki a lokacin amma dake kunnen k’ashi gareshi sai yaki ji, to yanzu wa gari ya waya ai gashinan bala’i sai kara shiga zuri’arsu yake” da sauri na shiga falon _Mama Qudi_ saboda yadda raina ya 6aci tsaf zan iya yiwa _Inna Abu_ dukan tsiya domin rashin kunya gaba na bashi ba baya ba.
A zaune na taras da _Mama Qudi_ tana jan charbi, fuskarta fayau babu wani alamu da zai nuna yanayin da take ciki, sai dai minti minti take ajiyar zuciya, duk yadda naso kallon cikin idonta abin yaki yuyuwa sai d’auke kai takeyi, _Mama Qudi_ naji an kira sunanta daga bakin k’ofa, kamar jira take yi naga tayi saurin mik’ewa tana cewa “Khadeemah kije ki chanja kayanki ki sanyo hijabi ki sameni a falon _Babanki_” to kawai nace sannan na wuce d’akina dake kallon na _Mamita_ ina jin kuna a cikin raina, tabbas wadanda suka kashemin _Mamita_ sun tsokala tsuliyar dodo, dan ba zan kyalesu ba sai na d’au fansar jinin yar uwata _Khadija_.
Wanka nayi sama-sama sannan na sanya riga da skirt yar kanti, kafin na d’au himar dina na saka sannan na fita. A bakin k’ofan _Baba K_ na hadu da _Kabiru_ da _Karima_ suna k’ok’arin shiga, kafin inyi musu magana suka yi saurin shigewa cikin falon, kad’a kaina kawai nayi sannan na shiga tare da sallama, d’ai-d’ai ku ne suka amsamin, wasu na min kallon banza, wasu kuma ko kallo ban ishesu ba, yayin da wasu ke zagina kasa-kasa.
D’auke kaina nayi daga kansu na mayar a kan gawar _Mamita_ dake shinfid’e a tsakiyar d’akin, ido na k’urawa gawar kamar mai neman gano ko mutuwar gaske ne ko na wasa irin na cikin film. Maganar da _Inna Abu_ tayi ne ya dawo da hankalina gurinta, sosai nayi mamakin abin da tace ” _Mayya_ ko jinin nata zaki idasa shanyewa? Munafuka, kekam badan dai ina da shaidun da suka sheda haihuwarki ba da zanci musanyaki akayi, badan kuma zato zunubi ba da sai ince cikin bana _Kari_ bane awani waje uwarki ta kunso dan ko ba komai da uwarki kikayi kama gadon tsiya gadon bakin hali da bakin jini” duk abin da _Inna Abu_ takemin nida yan uwana da mahaifiyata ban ta6a jin 6acin rai da bakin ciki ba kamar na yau ” wajen gawan na k’arasa, sai da na mata addua sannan na juyo ” _Zainabu_ kike kowa, koma dai menene ki tsaya a iya sauran zagin banda shegantani, wallahi sa’a kikaci halin _Mama Qudi_ daban da nawa da ace nice ita da tuni na saita miki hanya kin bat cikin rayuwarmu, tsohuwar banza kawai, sa’arki d’aya ke uwar _Baba K_ ne wallahi da yanzu na miki dukan mutuwa banza ballagazar uwa” ina gama fad’a na cikawa rigata iska nayi gaba cikin kunan zuciya.
Shuru kake ji a cikin falon babu wanda yayi gigin magana harna fita, dayawa sunji dadin abin da nayi yayin da wasu suka yi bakin cikin hakan musanman da _Baba K_ yayi shuru hankalinsa na kan _Mamita_ ko nuna cewa yaji abin da ya faru bai yi ba, a hankali _Inna Abu_ ta sulale daga falon saboda kunyan abin da na mata kuma aka rasa mai shiga mata cikin ‘ya’yanta da jikokinta, tana fita bata tsaya a ko ina ba sai gidanta, sosai tayi kukan bakin ciki ta koshi kafin barci ya d’auke ta.
Bayan sallar la’asar aka kai _Mamita_ gidanta na gaskiya, sai a lokacin naji hawaye ya fara tsere daga idanuna, sosai nayi kuka na gode Allah. Ina zaune na had’a kai da gwiwa _Mama Qudi_ ta shigo d’akin “tarbiyyan dana baki kenan ko, ni har na miki tarbiyyan da zaki zaqi babba irin haka? babban ma uwar mijin kuma kakarki eh _Khadeemah_! Kin kyauta na gode sosai da tozartani da kikayi a gaban makiya da masoya nagode sosai Allah ya miki albarka”.
Jin shuru yasa na d’ago kaina, kuka naji tanayi shiyasa naki kallonta, to in kalleta ince mata me, nida nayi dan kwato mata yanci kuma taga bak’i na to ai gwara dai in yi shuru kafin abin ya kai ga duka, duk da nasan cewa _Mama Qudi_ bata da saurin hannu amma yadda naji muryanta to tabbas akwai matsala, nifa ko a kolar rigata banyi nadamar abin da nayiwa _Inna Abu_ ba mutuniyar kawai, haka kurum zata shegantani lallai ta taro match.Yunwa ne ya tasheni yau da safe, tunawa da nayi da layin kar6an abinci kamar makarantar bodin yasa na d’anja tsaki ” ina zuwa” shine abin dana fad’a a lokacin da naji _Kursiyya_ na kirana wai an fara raba abinci “gidan _Baba K_ gidan gayu ko da me kazo an fika” toh ko da me kazo an fika mana in dai fannin iya shege ne kowa dan iskan kansa ne.
Adduar tashi a barci nayi sannan na mik’e daga kwanciyar da nayi, na sauka daga kan gadon, slippers dina na saka saboda a ka’ida _Mama Qudi_ ba’a mata yawo a cikin 6angarenta ba tare da takalmi ba, k’aramin mayafi na yafa sannan na shiga kitchen na d’au kwano na fita.
As usual kowa na layi kamar _assembly_ ido na dinga wurgawa tsakanin yan gidan mu, chan na hango _Mama Qudi_ a tsakanin kishiyoyinta kamar zasu maida ita cikin gwangwani kifi saboda yanda suke ta mammatseta a tsakiyan su da gangan, yanzu inyi magana ace nafi kowa iya rashin kunya, ko da yake ita ta jiyo nawa dai ido idan abin ya isheni inyi rashin mutunci.
Tafiya nayi zuwa gun _Baba K_ daya dage yana rabon abinci, shi bada girkawa ba shida rabiya, abin ma abin takaici abin dariya, yayi nashe-nashe a gaban kosai da kunu, idan ka bada kwano a zuba maka kosai kunu kuma a kulle yake a leda, duk kuma na kudi ne iya kudinka iya shagalinka, ni dama na fito da y’ar naira dari da hamsin dina dan saboda sanin halin _Baba K_ babu mutunci a harkar naira, shekaru ishirin da uku kenan daya samu karayar arziki tun daga lokacin abincin gida ya koma na sayarwa, iya kud’inka iya shagalinka.
Yau kwanaki bakwai kenan da rasuwan yar uwata _Mamita_ har an manta da ita an shiga hidimar yau da kullun, dama dai a gidan mu sati guda ake zaman makoki daganan wanda abin ya shafa sune da jimami, kwanaki bakwai dinnan sune ranakun da ake ba da abinci kyauta a gidan _Baba K_ shiyasa na lura wasu har addua suke irin hakan ya faru ko zasu samu sukunin adana yan kud’ad’ansu. Mutuniya _Inna Abu_ kuwa har yau babu labarinta dan tun ranar bata sake l’ekowa ba, dayawa sunji dadin rashin zuwanta dan da ace ta zo da cikin kwana bakwai dinnan sun samu nasu rabon.
Ina zuwa kusa dashi na bada kud’ina “kosan dari da ishirin, kunun talatin” abin da na fad’a kenan ina mik’a kwano, yadda naga _Baba K_ na bud’e hakora na fahimci lailai nice na bada kud’i mai yawa gurin mishi ciniki, ina kallo ya karamin rabin kosai kamar zuciyar mara wadatar zuci, mik’o min yayi na kar6a tare da bin gurin _Mama Qudi_ na janyo hannunta muka nufi 6angaren mu, babu wanda na kula yo nida ban gaishe da _Baba K_ bama wa ya isa kuma in gaisheshi a gurin, _Mama Qudi_ ce kawai bana iya fashin gaisheta a cikin gidan mu, itama saboda matsayinta na wacce ta tsuguna ta haifeni.
Muna shiga na wuce kitchen na d’auko kofi da sugar, bayan na zuba kunun na bude kwanon kosan na ajiye mata a gabanta ” _Mama Qudi_ kici wannan, bari in dafa mana taliyar yara nida sauran yaran” bata ce komai ba ta janyo ta fara ci tare da d’auke kanta daga kaina. Murmushi nayi sannan na l’eka waje na kira sauran kannena _Kursiyya_, _Khalimah_, _Khalil_, _Khalifa_, sai auta _Kisma_ sosai naga _Baba K_ ya had’e rai dan yaga zan rusa mishi yar kasuwar cikin gidansa, d’auke kaina nayi sai da naga shigowarsu kafin na rife k’ofan nace su jirani ina zuwa.
Kitchen na shiga na d’aura ruwa a wuta bayan daya tafasa nasa taliyar yara manya guda hudu sannan na rufe, albasa da attarugu na yanka yan kananu sannan na jira ya dahu, sai da ruwan ya kusa shanyewa sannan na zuba mai kad’an da kuma magin cikin taliyar sai kayan miya dana yanka na juya sosai na k’ara ruwa kad’an na rufe. Bayan mintina biyar na d’auko babban tray na d’auraye kafin na sauke taliyar na juye a kai. Wani tukunya na dora na zuba citta, kanumfari, na’a na’a da lipton guda biyu ban saka sugar ba dan ba kowa ke son sugar me yawa ba, taliyar na d’auka na kai mana falo na ajiye sannan na kira _Kursiyya_ muka koma tare ta kwaso kofuna ni kuma na sauke shayin na juye a babban flask, kasancewar da electric cooker nayi shiyasa yayi saurin tafarfasa.
Falo muka koma muka bararraje kowa ya zuba shayinsa muka fara cin abinci cikin natsuwa, duk abin da mukeyi _Mama Qudi_ na kallon mu tana murmushi duk da cewa da mun had’a ido take had’e rai sam bai dameni ba, dan na riga na saba da halayyar mahaifiyata na nuna kamar bata sona, nasan fushin nata baya wuce kan abin da ya faru kwanaki tsakanina da _Inna Abu_ tsohuwar _Baba K_ tsaki naja a raina dana tuna shegantani da tayi “kila ma itace shegiyar waya sani ko kuma _Baba K_ ne ta haifa a waje oho dai” ganin yanda suka zubamin ido yasa nasan cewa a fili nayi maganar, ai da sauri na kwashi jiki na wuce d’aki dan yanda naga idanun _Mama Qudi_ yau Allah ne zai ceceni.
Wanka nayi na shirya cikin doguwar rigi yar kanti, kwalliya nayi dai-dai wanda ya kar6i fuskata, domin yawan kwalliya da yawa baya tsarina, mutum ya fita kamar dodo, mayafi na sanya na rufe jikina dashi sannan na d’auki karamar jaka na sanya wayata da kud’i a ciki na fita, a falo na samu _Khalil_ na tambayeshi _Mama Qudi_ yace tana barci, tunda akayi rasuwa bata samu barci ba dan haka ban tasheta ba nace wa _Khalil_ idan ta farka yace mata na d’an fita ina dawowa.
Kasancewar gidanmu babu nisa da bakin hanya yasa nayi saurin samun abin hawa, shagon _Iya Loja_ na nufa, babban shagone na cin abinci kuma anan nake aiki ranakun juma’a asabar da lahadi, aiki da biya ne dan haka tana bani dubu daya da dari biyar, a sati ina samun dubu hudu da dari biyar inda nake dan adana dubu biyu a cikin asusu sauran kuma na kashewa tunda abinci ma sai mun saya a cikin gidan uban mu da ransa da lafiyarsa.
Sauka nayi daga napep din na bashi kudinshi sannan na shiga ciki, tun daga bakin kofa nakejin masifar _Iya Loja_ kuma ko a jikina, tafiya nakeyi cikin isa da gadara, ina zuwa na gaisheta a tsaye kamar yanda na saba domin ni _Mama Qudi_ kawai nake gaisarwa a tsugune, bayan ta amsa ta min gaisuwar rashin da akayi na _Mamita_ na amsa ina share kwallar dake kokarin zubowa, wasu cikin ma’aikatan suka gaisheni cike da tausayawa saboda sanin yanda _Mamita_ take a guruna yayin da wasu suka gaisheni ba dan ransu yaso ba sai dan ganin idon _Iya Loja_.
Bayan an gama gaishe gaishen, _Iya Loja_ take sanar dani dalilin masifar ta a safiyar yau wai an sace mata kud’i naira dubu dari biyu da hamsin, “eh dole kiyi masifa Madam ai baki mayi ba tukunna wannan wasa kikeyi” nace a cikin raina, kallona tayi tace ” _Khadeemah_ please help me figure out the munafiki wey steal my money abeg, du Allah du Annabi ki temakeni” shuru nayi kafin nace “Madam ko kuma ince _Iya Loja_ tunda kinfi son mu kiraki da hakan, zan duba miki amma dole ne inji dumus nima dole in samu kaso mai tsoka” kallona tayi tana nazari sannan tace “shikenan i will give you 20 thousand, zani baki dubu ishirin ai yayi maki ba” wani irin kallon tara saura kwata na bata kafin nayi dariyar rainin hankali nace mata “dubu hamsin shine price, in kina so in kuma baki so shikenan kece da asara ba niba” da sauri ta bud’e jakarta ta kirgo dubu hamsin, kar6a nayi na sake kirgawa sannan na bud’e jakata na saka a ciki kafin nace mata “ga ajiyar jakata idan na tashi zan kar6a saboda tsaro ba tsoro ba” cikin rawar jiki ta kar6a ta adana min tare da nata.
Juyawa nayi na kallesu tuni mutabe biyu sun tonawa kansu asiri tun kafin in duba in gani, jikinsu tuni ya fara rawa sai zuba sukeyi yayin da sauran suke natse saboda sanin cewa suna da gaskiya ” _Lami_ da _Ifoema_ ne suka d’auka a lokacin da kika aiki _Tonny_ ya kai miki bank shine ya shiga kewaye tare da ajiye kud’in a kasan microwave, su kuma suna biye dashi shine sukayi saurin d’auka kafin ya fito, ki duba kasan kujeran da kike zama anan suka ajiye dan sunsan ko da an shiga nema ba za’a duba gurin ba” na k’arashe ina wucewa gurin aikina, wato fannin girke-girke na zamani da gargajiya.
________________________