DEEMAH CHAPTER 10 BY ZAHRATEEY

DEEMAH CHAPTER 10 BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A yau sati guda kenan da bikin _Kisma_, gidan shuru duk an watse, yaran ma suna gidan _Kursiyya_ jiya tazo ta tafi dasu wai zasuyi mata kwana biyu. Matan gidan mu kuma sun shiga makota jaje, yar yarinyar da bata wuce sha biyu ba kawunta ya mata fyad’e bayan ya dauketa sun fita da sunan shan ice cream, ko da ya dawo da ita saboda rashin gaskiya ya kasa shiga gida, tun fitarsu mahaifiyarta ta kasa samun natsuwa dama ita bata son yawan mu’amalsa da yarta, sai dai mijinta ke taka mata birki idan ta nuna bata son fitarsu tare, shiyasa tana ganin ta dawo ita kadai kuma ga tafiyarta ya chanja ga fuska duk a kumbure yasa ta titsiyeta shine take bada labarin abin da ya faru bayan fitansu wai gidan abokin shi ya kaita akan zasu gaishe shi ba shi da lafiya, shine ya bata wani abu kaman lemo tasha daganan barci ya dauketa bata farka ba sai bayan magriba, shine ya sata tayi wanka suka taho ya ajiyeta a bakin kofa shi kuma ya tafi yace taje zai zo, sosai mahaifiyarta ta shiga tashin hankali karshe ta yanki jiki ta fad’i daker aka shawo kanta amma har zuwa yanzu kuka kawai takeyi bata cewa komai abin gwanin ban tausayi, mahaifinta kam nadama ne karara ya bayyana a tare da shi domin bai yi tsammanin irin hakan tsakanin uba da y’a ba, shima ya yi kukan zuci ya yi na fili, sai yanzu yake ganin wautarsa na kin yarda da matarsa a duk sanda tayi kokarin jawo hankalinsa akan mu’amalar kaninsa da

y’arsu, yanzu wa gari ya waya duk ya ruguza musu farin ciki tsaban shima ya san bai kauta ba shiyasa bai sake zuwa cikin unguwar ba. (Hattara iyaye mata da maza, mutanen duniya ba abin yarda bane a cikin wannan zamanin da muke, ana samun haka tsakanin ya da kanwa da kuma kawu da yarsa kai karewarta wani mahaifin da kansa yake lalata wa yarsa rayuwa, abin sai ana takatsatsan kuma ana hadawa da addua tare da nunawa yara illar barin wani ya ta6a jikinsu tare kuma da nuna musu muhimman gurare a cikin jikinsu yadda ba zasu yarda wani ya ta6a ba, a nuna musu illar kusanci da wani namijin da abin da hakan ke haifarwa, a nuna musu cewan duk wani wanda ya musu ko wani irin wasa na banza ba wanda zasuyi tarayya bane, kuma duk wanda ya yi kokarin cin mutuncin su suyi saurin sanarwa, iyaye ku sake jiki da y’ay’anku ta yadda zaku samu damar fuskantar matsalolinsu da basu shawarwari ta yadda zasu kare kansu da kansu, dayawan yara suna tsoron tunkaran iyayensu da matsalolinsu saboda maimakon su samu sauki ko maslaha sai dai iyayen su kara musu wani damuwar, dan Allah iyaye a kiyaye a bawa yara kulawar data dace a sake musu yadda ba zasuji tsoron sanarda duk wani abin da suke ciki ba, ku tuna cewa su y’ay’annan ajiya ne kuma amanar ubangiji ne, idan kuka ci amanar Allah kuma ku zakuyi bayani, Allah yasa mu dace).

+

Fad’an su _Inna Abu_ ne ya tasheni, na lura basu da aikinyi da ya wuce su rinka fad’a suna fito na fito da juna akan abubuwan dake faruwa a rayuwarsu kowa yana bawa dan uwansa laifi, _Baba K_ haushinsa d’aya na rashin tafiya me kyau, har yanzu kafarsa bai gama mikewa ba, ita kuma _Inna Abu_ bakin cikin gidanta data rasa shine yake dawainiya da zuciyarta, tana tsananin son wannan gidan nata amma a dalilin biyewa son kud’i irin na _Baba K_ shikenan ya kaita ya baro ta komai ya kare musu, ba shagon nasa ba gidanta abin takaici ma yanzu a karkashin su _Ya Koko_ suke sai yadda akayi dasu basu da wani yancin kai. Fad’a sukayi sosai kamar zata dake shi sai faman zaginsa takeyi wai me mutuwar zuciya, yau dai zagin da akemin ya koma kan shi wai itakam anya ba musayar shi aka mata ba a lokacin data haifeshi? Dan ita kam sauran yaranta basu da mutuwar zuciya irin nasa, sai yanzu ta tuna tana da sauran yara masu mutunci ai dama in ba _Baba K_ ba bata ganin kowa da gashi, ikon Allah kenan duniya juyin waina.

Ina zaune shuru ni kad’ai babu hayaniyar yawa babu kuma _Kisma_ Allah sarki aure me raba tsakanin uwa da yarta, yar uwa da yan uwanta, Allah dai ya basu zaman lafiya ni kuma ya bayyana min _Sufyan_ a duk inda yake, ni dai na san cewa bai sakeni ba, duk da munyi akan cewa zai sakenin amma dai bai furta ba kuma banga wani alamar daya nuna hakan ba ko da a rubuce ne, kallon akwatina nayi wani abu na cewa in duba wallet dinsa, cikin bugawar zuciya na isa bakin akwatin na bude na ciro jakar laptop din na bude sannan na cire wallet din dake ciki, jiki na rawa na bude a hankali, wasu cards guda hudu ne suka zubo da wani paper guda daya, card din ATM dinsa ne guda biyu na Gtb da Unity bank sai kuma katin da aka rubuta _A&S_ wanda hakan ya tabbatarmin da harsashen _Inna Suwaiba_ sai kuma dayan ID card dinsa ne, bayan na gama gani sai na dauki wannan papern na warware a hankali sai dai ina tsoron karanta rubutun cikin.

_________________________

Samari uku ne ke zaune akan wani benci kusa da masallaci, hira sukeyi akan rayuwa da kuma tsadar aure a wannan zamanin wanda haka ke saka maza da yawa su kasa aure karshe su koma bin y’ay’an mutane, a ganinsu ma hakan na daya daga cikin abin da yasa matsalolin fyade da lalata y’ay’an mutane ya yi yawa, tunda an kasa hakuri a basu aure da irin karfinsu anfison sai sun aro rayuwar da ba tasu ba sun yafa sannan sai a basu auren, wani ma sai an gama tatse shi a lokacin biki, idan kuma aka gama hidimar biki sai ya koma hannu na dukan cinya, da zaran garan amarya ya kare sun gama cinyewa sai a barshi da cin yatsa dan babu ko kobo a tare da shi komai ya kare a gurin biki, wasu kuma zasu zo da zummar aure sai an gama komai ansa rana zasu fara lalata yarinya karshe su barta da tashin hankali su gudu, saboda iyayenta sun gama tatsar su idan kuma sukace za a yi auren a haka tabbas sune a ruwa shiyasa suke daukan wannan hanyar, matsalolin dai da yawa na kafin a yi aure da kuma bayan anyi aure.

Ganin cewa su biyu ne kawai suke hiransu shi yasa suka ta6o abokin nasu ” _Yaro_ ya dai kayi shuru baka cewa komai tun dazu?” Juyawa ya yi ta inda yakejin muryan abokin nasa yace “naku matsalar ma ba matsala nace zaku san yadda za a yi ku auru, ni kuwa sai dai in zauna in kare a gida dan ba ko wata mace ce zata auri irina ba, alal misali ma ace kudi gareni to idan mace ta aureni kudina shine jigon zaman, toh balle ina talaka gani makaho ta ina zan samu macen aure tunda ni din a gurin su abin k’i ne kuma abin kyama” ya fad’a fuskarsa na nuna damuwar dake cikin zuciyarsa.

Tausayinsa ne ya kama abokan nasa, duk sai suka zuba mishi ido, _Yaro_ kyakyawan saurayi ne kuma bak’in fata, siriri ne amma ba chan ba, yana da karatu dai-dai gwargwado dana boko dana addini, a boko ya gama secondary amma babu kud’in zuwa jami’a, a islamiya kuma ya sauke yana kan hadda, ya haddace litatafai da dama domin akwai shi da naci akan abin da yasa a gaba, shekarunsa talatin da biyu a duniya kuma shi din maraya ne yana zaune ne a gidan dan uwan mahaifinsa wanda ya kasance malamin makaranta, _Kawu Sirajo_ mutumin kirki ne kuma me son jama’a sai dai Allah ya bashi mace ne kyashi da hassada da kin mutane, sosai _Yaro_ yake shan wahala a gurinta idan kawunsa baya nan, shiyasa baya zama a gidan sai idan kawunsa yana nan dan a lokacin zai samu cin abinci, kullun ba shi da aiki sai zama tare da abokansa, ranakun kasuwa kuma suna zuwa saukewa wani mutumi kaya inda suke samun kudin dake rikesu har zuwa wani kasuwan, yanzu babban burinsu su d’an tara kud’i ne suyi aure amma abin yaki yiyuwa, nauyin iyaye da kanne duk a kansu yake har gwara _Yaro_ kawunsa baya bari yana amfani da kudinsa ko yaushe, ya kance mishi ya adana zasu mishi amfani.

A 6angaren yan mata kuwa har gwara abokansa ana dan kula su amma shikam ina yaga idon kallon yan mata balle har ya tunkaresu da zancen aure, d’iyar kawunsa ne dama ta so shi kuma ta so aurensa amma uwarta ta shiga ta fita har sai ta aurar da ita ga dan uwanta, sosai kawunsa yaji haushi daya samu labarin cewa yarinyar tana son _Yaro_ amma tsoron bakin uwa yasa ta hakura da shi, a nan kuma kawun ya yi alkawarin sama mishi mata yar gidan mutunci da karamci wadda zata so shi a mutum ba’a me nak’asa ba.Rufewa nayi saboda ina tsoron abin da zai iya faruwa, tattara komai nayi na mayar a inda nake ajiyewa, ni kam ban shirya karanta abin da ke rubuce ba, ko da abin da aka rubutan ba danni aka yi ba, ban shirya karantawa ba. Bayan na mayar ma’adanarsa na fita falo gurinsu _Baba K_ duk sunyi jugum-jugum suna tunanin kadarorin da suka rasa, _Inna Abu_ ma tafi ban dariya dan duk sanda tayi tagumi ta d’ago sai ta harari _Baba K_, kai gaskiya bai kyauta a tsohuwarsa ba. Matar da bata saba zaman a gidan wasu ba sai nata, daga gidan mijinta sai wanda yaran suka saya mata yanzu kuma sanadin _Baba K_ ta dawo zaman gidan da matansa suka saya, duk da dariyar da yake cina haka na maze na zuba musu ido kamar na samu TV…

+

Hajiya ce ta kirani akan inje in mata semosa da meatpie idan bana komai, dama gidan ya yi shuru da yawa hakan yasa na shirya na tafi gidanta, sai a lokacin na sake mata gaisuwan rashin da akayi musu, kafin in dawo aka kawo wasu yara mata tagwaye sak yarana, a lokacin na sake gaskata maganar _Inna Suwaiba_ tabbas suna da alaka da yarana. Ban bar gidan ba sai bayan la’asar dan har Vanilla cake nayi mata wanda tace za’a aikawa mahaifiyar yaran saboda ma’abociyar cin cake ne, tunani nayi akan wato a kishiyata za’a aika kenan? Rashin samun me bani amsa yasa nayi shuru, ina gamawa ta bani kudin aikina sannan na tafi gida cike da tunani irin daban-daban.

Na isa gida na samu su _Goggo Fulera_ sun dawo sai me da zancen fyaden da aka yi wa yarinyar sukeyi, kowa tana fadan albarkacin bakinta, ni ban ga yarinyar ba amma har naji tausayinta, gaskiya wasu mutane da rashin tsoron Allah suke, a bari ma akan wani na waje ne ya aikata amma kuma kai da zaka kareta kai ne ka aikata mata hakan, idan har zaka iya da yar dan uwanka ko diyar yar uwarka tabbas zaka iya da yar cikinka, tunda maraban matsayinsu kadanne kawai wannan jinika ya haifa wannan kuma kai ka haifa, wai kuma tunda ya gudu ba a sake ganinsa ba, ni zancen ma ya isheni dan takaici kawai nakeji idan ana maganar, tashi nayi na wuce daki na kira wayan _Kisma_ muka sha hira, shine take gayamin lokacin yaye dalibai ya kusa (convocation) taji ana cewa sati biyu masu zuwa, Allah ya kaimu kawai nace mata kafin mukayi sallama na ajiye wayan ina tunanin sake zuwa Sokoto da sunan yaye dalibai, ni duk kokarina bana tunanin zan samu matsayin da nake bukata, domin sai ka sha karatu har kayi ciwon kai amma kuma wani lokaci son zuciya irin na malamai ko rashin kulawa yayin makin jarabawa sai yasa ka fad’i kasa daga abin da kake bid’a, amma dai zanje kila _Kisma_ ta kar6a dan akwai ta da kokari sosai.

A cikin satinnan kuma zamu tafi gurin wannan malamin ni ban san ko zan samu zuwa gurin yaye daliban bama, dan idan mukaje bamu san ko abin zai dauki lokaci ba, nasan dai dole wata cikin matan gidan da wasu daga cikin kanne na zasuje, ko da na gaya musu _Goggo Fulera_ da _Ya Kolo_ ne suka shirya zuwa tare da _Khalifa_ da _Khalil_ sauran sunce sai _Kisma_ ta haihu zasuje su mata murna gaba daya, ni abin ma dariya ba ban wai sai ta haihu, yaushe ma akayi auren da har zaayi maganar haihuwa? Yanzu cikin satinnan za’a bude makarantu, dole ma sai na nemawa triple makarantan da zasu rinka zuwa, zuwan yayan mu ne abin ya min sauki inda yace zai hada su da yaranshi sai su rinka zuwa makaranta guda, hakan ma ni yafimin sauki idan zamu tafi zan iya barinsu ba tare da wani damuwa ba.

STORY CONTINUES BELOW

Kaya biyar na dauka sai inner wears da hijabai uku, hada komai nayi a cikin yar karamar jaka dai-dai misali, yanzu kuma da zamu tafin sai naji kwata-kwata bana son tafiya in bar yarana, dan ma sun saba da mutanen gidan ba zasu damu sosai ba musanman idan suna fita yawon shan chocolate da _Khalil_ ni yanzu ma duk tsoron fitan nasu nakeji duk da cewa ina kautata mishi zato amma shaidan mugu ne bana wasa ba, fatana dai Allah ya kare min su a duk inda sukaje. Washe gari bayan sun dawo daga gidan _Kursiyya_ na hada musu kayansu na zuwa gidan yayan mu, dan yace a kai su su rinka zuwa makaranta daga chan. Ni dai ban san meke shirin faruwa ba amma inaji ajikina akwai abin da zai iya faruwa dani wanda zai raba tsakanina da yarana abin alfaharina wadanda nake matukar so da kauna kamar rai na.

Washe gari da sassafe na tashi nayi wanka naci dumamen tuwon masara da miyar kuka, bayan na gama na d’auki wannan laptop bag din na saka a cikin kayana dan duk inda zanje in dade da shi nake zuwa bana barin shi a gida, ina gamawa naji sallamar kawunai na, da sauri na dauki jakan da wayata sannan na yafa babban mayafi na fita. A falo na same su bayan mun gaisa na gaishe da mutanen gidan dan sai a lokacin suma suka tashi daga barcin safe. Basu wani dade ba sukace mu tafi kar rana yayi mana a hanya, sallama mukayi da mutanen gidan mu suna mana adduar Allah yasa a dace ya bada sa’a sannan muka wuce tasha inda muka shiga motar Jos.

_________________________

Kamar kullun suna zaune a kan benci suna hiran duniya sai mutumin da sukewa aiki a kasuwa ya kira su akan an kawo mishi kaya, kasancewar yau din ba ranar kasuwa ba shiyasa ya kira su da kanshi tunda basu san da za’a kawo mishi kaya ba, cike farin ciki suka kama hanyar kasuwan saboda dama kudinsu ya yi kasa dayawa, suna tafiya suna hira har suka isa shagon mutumin.

Bayan sun gaishe shi ya nuna musu manyan daf guda biyu dake fake a gurin, manyan buhuhuna ne na shinkafa, masara, wake, hatsi da dai sauran su, shi dai _Yaro_ yana biye dasu amma ba ganin komai yakeyi ba duk dai inda yaji sun saka kafa shima a nan yaje sakawa, a haka har suka fara sauke kayan suna kaiwa cikin shagon. Basu suka gama ba sai bayan sallah la’asar dan kayan akwai yawa sosai dan ma basu kadai suke kwashewa ba akwai wasu maza uku dake aiki a shagonsa.

Bayan sun gama ya basu dubu biyar biyar suka tafi suna murna, sai da suka tsaya sukaci indomie da kwai harda tsire sannan sukayi sallar magriba da isha’i kafin sukayi sallama da juna kowa ya kama hanyar gidansu. A bakin kofar ya hadu da _Kawu Sirajo_ shima zai shiga gida, gaishe shi ya yi sannan suka shiga tare. Sosai _Iya Gaje_ taji haushin dawowarsu tare dan tasan cewa tare zasu ci abinci kenan, cike da bakin ciki ta kai musu abincin tanaji kamar ta murkushe wuyan _Yaro_ ya mutu ya bar mata gidanta ko zata huta da cinye musu kayan abinci da yakeyi shi ba da gadon mijinta ba…

Shikam _Yaro_ duk a tsorace yake ma, duk inda yaji muryan _Iya Gaje_ ji yakeyi kamar ya gudu ya bar gurin, ya sha jinta ita da kawarta _Iya Lantai_ da kanwarsa _Asiya_ suna maganar yadda za’ayi a kawar da shi daga doron duniya shiyasa sam yakejin tsoron cin abincin gidan, in dai ba tare da kawunsa ba sam baya cin abinci a gidan sai dai idan daya kanwar tasa ta zo ganin gida shine take saka musu abinci suci tare amma bayan haka ya gwammace ya rayu da yunwa da yaci abin da zai kashe shi, kuma da ace kawunsa ya sani da abin ba zai kai ga haka ba da kila ya koreta a gidan, hakanne ma yasa bai ta6a gigin sanar da kawunsa ba duk da cewa yana ma shakkar sanar da shi din tunda a gabansa nuna mishi so takeyi bata ta6a nuna cewa bata sonshi ba.

_________________________

Tana zaune a falon _Hajja_ taji sallamar su, amsawa tayi tana murmushi “sai yau kuka dawo kenan, ai nayi tunanin sai na roka zaku dawo” dariya _Anty Aisha_ tayi sannan tace “yi hakuri gasu nan sun dawo, dama saboda gidan ya yi min shuru da yawa shiyasa nace sai sun kara kwana” itama mayar mata da martanin dariyar tayi sannan tace “ai nima zolayar ku kawai nakeyi, nida na dauka sun koma kenan har sai babansu ya dawo zan gansu” yanayin fuskokin su ne ya canja sai dai kuma cikin lokaci kadan suka cigaba da rahansu kafin suka shiga wani hiran tare da kawar da zancen _Sufyan_ din.

Sun jima suna hira da _Hajja_ kafin suka tashi suka koma 6angarenta inda _Anty Aisha_ take sanar da ita cewa cikin shekaran za’ayi bikin yaye daliban karamar sakandiri inda yaronta _Anas_ shima yake ciki, kuma zata so ace a wannan lokacin _Hajja_ ta san da zaman shi kuma ta halarci gurin taron dan shima yaji dadi idan ba mahaifinsa akwai kakarsa. Sosai ta amince da shawaran tare da adduar Allah ya kai musu rai kuma yasa zuwa lokacin mahaifinsa ya bayyana.

Bayan tafiyar _Anty Aisha_ sai ga _Hanifa_ ta shigo cikin firgici, da sauri _Jidda_ ta tashi tana tambayarta ko lafiya ta shigo babu sallama alhali ta hane ta da irin hakan saboda babu kyau ka fadowa mutum ba tare daka nemi izini ba, ajiyar zuciya tayi sannan tace “Labari na kawo miki da dumi duminsa, Ashe _Ya Sufyan_ ya yi wani aure a inda yaje har da yara?” Kallonta _Jidda_ tayi na yan mintina sannan tace “ke to a ina kikaji wannan labarin da har kika yarda da shi?” Cike da 6acin rai da take 6oyewa tace “yanzu da zan fito naji su _Mama_ suna magana a waya wai bokansu ne ya sanar dasu wannan zancen, kuma sannan nan bada dadewa ba zai dawo gida tare da matarsa daya aura, yanzu _Anty Jidda_ shikenan na rasa _Ya Sufyan_ dina?” Wani irin abu _Jidda_ taji a kirjinta amma sai ta daure tace “kije babu damuwa idan ya dawo zanyi mishi maganarki in sha Allahu, kuma ai aure nufin Allah ne tunda har kika ga ya auro wata a tsakanin 6atan da ya yi to dama kaddaransa kenan shine kuma silar 6atar nasa” haushi ne ya kama _Hanifa_ da sauri ta fita ta barta ita kuma ta zauna dabas akan kujera tana kokarin yaki da shaidan da kuma zuciyarta, adduo’i kawai takeyi dan samun natsuwa a cikin ranta.

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE