DEEMAH CHAPTER 12 BY ZAHRATEEY
DEEMAH CHAPTER 12 BY ZAHRATEEY
Wani irin ciwon kai ne da faduwar gaba yake kai kawo a tare dashi a cikin yan kwanakinnan. Tuna cewa _Baffa_ ya aiko a kirasa shiyasa ya tashi ya chanja kaya sannan ya fita bayan ya yi mata sallama. Kasancewar basu da wani nisa cikin mintina biyu ya isa gida. Jiri ne ya kwashe shi ya fad’a a dai-dai k’ofar gidan, cikin sauri _Baffa_ da bakinsa sukayi kansa suna kokarin d’ago shi zuwa kan tabarma, suna ajiye shi d’ayan mutumin ya yi sauri ya mike yana cewa ” _Sufyan_ nake gani ko kuma me kama dashi?”.
+
Shuru sukayi na mintina biyar kafin _Baffa_ ya fara mishi bayanin yadda ya tsinci _Sufyan_ da kuma zaman da sukayi har ma da auren yarsa da yakeyi da yara uku a tsakaninsu. Sosai mutumin ya jinjina al’amarin, ikon ubangiji kenan aure harda yara uku kuma har yanzu bai dawo cikin tunaninsa ya tuna komai a kansa ba?” Cikin sauri ya d’auki waya ya kira mahaifin _Sufyan_ ya mishi bayanin inda yake kuma yace suzo tare da iyalansa cikin gaggawa, ba tare da 6ata lokaci ba kuwa _Daddy_ ya sanar da iyalansa tafiyar gaggawa daya kamasu, cikin mintina talatin suka gama shiri har da _Anty Aisha_ da mijinta.
STORY CONTINUES BELOW
Ita dai _Jidda_ duk ta rasa sukuni ta rasa natsuwarta, gabanta sai faduwa yakeyi tana son gaskata cewa mijinta zata gani amma wani zuciya na kwa6arta akan karta saka rai kuma yazo ya zama ba hakan bane, addua kawai ta koma yi tana neman sauki akan lamuranta, karshe barci ya d’auketa bata farka ba sai da suka isa _Forest_ inda kauyen su _Baffa_ yake, a nan suka tsaya jiran abokin _Daddy_ yazo ya musu iso zuwa cikin kauyen da kuma gurin da yake so suje.
_Sufyan_ bai farka ba har zuwa lokacin hakan yasa suka shigar dashi d’akin dake cikin zauren gidan sannan suka aika _Bibalo_ tazo tare da yaran dan ta kula dashi kafin ya farka. Su kuma sukayi zaman jiran isowar su _Daddy_. Shi abokin _Daddy_ rakiya yayi wa abokinsa gurin _Baffa_ inda suka kawo matsalar d’ansa wanda yake fama da bakin aljanu, suma kwatancen inda _Baffa_ yake aka musu shine suka zo su fara ganawa kafin su kawo yaron ko kuma idan shi zai iya zuwa sai a saka rana suzo su tafi dashi. Toh cikin ikon Allah kuma sai al’amarin ya kara juyewa suka ga _Sufyan_ wanda akayi shekaru da shekaru ana nemansa amma babu labari shine cikin azama suka sanar da iyalansa.
Daf da magriba suka isa gidan, matan suka shiga su kuma mazan suka wuce masallaci, tunda _Jidda_ ta shiga gidan faduwar gabanta ya karu har wani zazza6i takeji kamar yakeson kamata, addua kawai takeyi a cikin ranta Allah ya kawo mata koma meye ne da sauki kuma Allah ya bata ikon cinye duk wani jarabawa da zai riske ta. Wasunsu alwala sukayi suka fara gabatar da salla a babban tabarman da aka shimfid’a musu, ita kam kwanciya tayi a gefen tabarman tana ajiyar zuciya a kai a kai. Sai bayan da suka idar da salla sannan akayiwa su _Daddy_ iso zuwa cikin gidan aka shimfid’a musu tabarma. _Bibalo_ duk hankalinta ya kasa kwanciya ganin masu kama da mijinta dan ma yaran duk suna barci shiyasa ta samu natsuwa.
Bayan sun zauna suka gaisa a tsakaninsu, a sannan ne abokin _Daddy_ ya fara musu bayanin dalilin kiran gaggawan daya musu, ya kuma gabatar musu da _Baffa_ da matarsa da kuma _Bibalo_ a matsayin matar _Sufyan_ har da yara uku a tsakanin su, _Baffa_ ya d’ora da nashi bayanin daga tsintar _Sufyan_ har rayuwar da sukayi dashi har ya samu lafiya da kuma auren da sukayi da _Bibalo_ bisa yardan junansu. Sosai kowa ya jinjina al’amarin kafin _Daddy_ ya musu bayanin rabuwansu da _Sufyan_ da kuma tsawon lokacin da suka d’auka gurin nemansa tare da gabatar musu da _Jidda_ a matsayin matarsa ta farko. Wani irin abu ne ya tsayawa _Jidda_ a cikin mak’ogoronta kokari takeyi karta karaya duk wani adduar daya zo bakinta shi takeyi, kirjinta ya yi nauyi kanta na sarawa duk ta rasa matsaya guda d’aya. _Bibalo_ kuwa kuka ne ya kubce mata ganin cewa mijinta da aurensa harda yara musanman labarin soyayyarsu da taji a bakin _Anty Aisha_ shi yafi komai tarwatsa mata zuciya.
Kamar a mafarki _Sufyan_ yakejin muryan mutane a tsakar gidan, a hankali ya tashi yana takawa cikin sanyin jiki, da _Jidda_ suka had’a ido yana fitowa wanda hakan yasa ya zaro ido yana son tunowa da wacece ita a gurinsa, matar da kullun yake mafarkinta tana kuka tana cewa ya dawo gareta, kallonta ya cigaba dayi kafin lokaci d’aya idonsa ya sauka cikin na _Hajja_ wani irin jiri ne ya sake d’ibarsa ya kwala kiran sunan _Jidda_ sannan ya sulale a gurin, kukan da take rikewa ne ya kubce mata cikin sauri ta k’arasa inda yake ta d’aura kansa bisa cinyarta tana kuka tana cewa dan Allah karya sake tafiya ya barta, kowa ya matukar tausaya mata harda _Baffa_ dake kokarin kwantar mata da hankali _Bibalo_ ce kawai ta k’au da kai tana jinyar zuciyarta.
Kusan mintina goma suna zaune a haka babu wanda ya motsa haka zalika shima _Sufyan_ bai farfad’o ba, sai da aka shafe mintina ishirin sannan ya fara bud’e idonsa inda ya sauke su fes akan fuskar _Jidda_ hawayenta ne ya d’iga a saman fuskarsa lumshe ido yayi ya kara bud’ewa kafin ya fara kokarin tashi, kallon kowa ya yi d’aya bayan d’aya kafin ya sake juyawa ya kalli _Jidda_ sannan ya juya ya kalli _Bibalo_ da har zuwa lokacin bata bar kuka ba, ajiyar zuciya ya yi sannan yace ” _Jidda_ Allah ya yi zamu sake ganawa, har na cire ran sake tuna komai game da rayuwata, a kullun sai nayi mafarkinki amma na kasa tuna dangatakar mu dake, ko yaushe ina kokarin tuna koni waye ko daga ina nazo amma abin yaki yiyuwa, nagode wa Allah daya had’amu a yau kuma ina matukar farin ciki, damuwata d’aya nayi aure ba tare da saninki ba nayi aure ba tare da ganin farin cikinki a kan lamarin ba, na san cewa kina da sanin ina da ra’ayin zama da mata biyu ko sama da haka, amma babu dadi ace kinji zancen daga sama har da zuri’a ma kafin kisan da auren mijinki, kiyi hakuri ki kar6i _Habiba_ a matsayin yar uwa yaranta kuma a matsayin yaranki”. Ya fad’a yana kallon cikin idonta, kallonsa itama takeyi tana tunani kala-kala, kaddara ya riga fata kuma ko da ace dama chan da sanin ta dole hakan zai faru a cikin rayuwarsu, ita wacece ne ma da har zata hana abin da Allah ya kaddara? Ita wacce da zatayi jayayya da hukuncin ubangiji? “Allah ya baka ikon adalci a tsakanin matanka da y’ay’anka” cike da burgewa kowa yake kallonta har da _Bibalo_ da takejin haushita da fari a matsayin matar mijinta kuma take tsoron karta rabata da _Sufyan_.
Tunowa da _Khadeemah_ yasa _Sufyan_ ya sake matsa hannunta a cikin nashi sannan yace “bayan wannan akwai abin da keda _Habiba_ ya kamata ku sani” dan jim ya yi kafin ya sake kallon su dukansu sannan ya maida hankali kan _Jidda_ “kafin aurena da _Habiba_ kafin tsintata da _Baffa_ ya yi nayi wani auren inda na auri wata yar garin _Bauchi_ sunanta _Khadeemah_” zuciyoyinsu ne suka buga a tare, sake matsa hannunta ya yi sannan ya cigaba da cewa “a lokacin dana gama aikina a _Abuja_ bayan na shiga mota zan dawo _Bauchi_ naji na kasa tafiya, wani irin ciwon mara ne ya kamani wanda idan har ban samu biyan bukata a lokacin ba inajin zan iya rasa rayuwata, abokina _Usman_ nayiwa bayanin matsalata shine ya kaini wani gida inda na had’u da yarinyar, bayan na d’auketa mun isa inda zamuje ta nemi alfarman inyi hakuri in nemi wata dan ita kam bazata iya ba, yanzun ma ta yarda ta biyo ni ne saboda kar madam din ta tursasa ta ko tayi mata wani abin na daban, ganin bata da tsumi ko dabara yasa ta hakura, ni kuma na fita na samu _Usman_ na nuna mishi cewa sai dai in aure ta amma ba zan iya kusantar zina ba dan ban ta6ayi ba kuma ba zan aikata a yanzu ba, ganin yadda na rikice yasa ya amince da bukatata, bayan na koma na sanar da ita abin da na aikata da kuma abin da nakeji a raina, ba tare da jayayya ba ta amince duk da cewa akwai tsoron a tare da ita, daga nan bayan komai ya afku na rubuta mata address din gidan mu saboda yadda nakeji a lokacin bana bukatan komawa gida, ban sani ba ko taje muku ko bataje ba” ya fad’a yana d’auke kansa daga kallon _Jidda_ sai a lokacin _Anty Aisha_ take sanar dasu cewa tabbas ta san yarinyar saboda ambaton sunanta da ya yi kuma a halin yanzu ba’a san inda take ba dan 6arayi sun saceta, abin da yasa ta gaskata kuma saboda yaranta data gani a ranar da taje musu jaje ta had’u dasu suna shirin komawa _Sokoto_ tare da kanwar mahaifiyarsu, kaman yaran shine yasa ta dasa ayar tambaya domin ta san cewa kwanaki mahaifanta sun koreta da sunan tayi cikin shege bayan dawowarta daga _Abuja_ shine ta koma gurin wata kakarta sai bayan rasuwan mijin kakar ta dawo, anan ne watarana bayan tazo gidan _Anty Aisha_ da tayi mata maganan aure shine take bata labarin abinda _Sufyan_ ya fad’a yanzu, sai dai ta amince ne saboda ganin cewa tabbas sai hakan ya faru a cikin idanunsa, har auren da zaiyi da ita kafin komai ya faru a tsakaninsu shiyasa kawai ta kwantar da hankalinta, kuma ta fada mata cewa akwai sihiri a tare dashi a lokacin sannan kuma ta sanar da ita tun daga lokacin abubuwan dake damunta suka ragu, bayan haka kuma dalilin tafiyarsu har ya kai ga 6atanta shine zuwa ganin _Baffa_ sai dai Allah ya yi bazasu gama da _Sufyan_ a yanzu ba kila shiyasa hakan ya faru.
Anan ta basu labarin _Khadeemah_ da kuma sanadin haduwarsu na farko dana biyu harma dana uku wanda shine lokacin da aka damfari _Baba K_, sannan ta kara da cewa tabbas yaransa yan ukun data gani a gidansu _Khadeemah_ domin kamannin ahalinsu ne a tare da yaran, sannan kuma ta sanar dasu cewa babu wanda ya san da zancen aure akan _Khadeemah_ sai ita kad’ai kuma tabbas ta san yarda da amana yasa ta sanar da ita, dan haka Idan sun koma dole zasuje su kar6o yaran tare da sanar dasu duk wani abin da ya dace su sani game da aurensa da yarsu. A wannan karon _Habiba_ bata kai _Jidda_ shiga tashin hankali ba, mata har biyu mijinta ya aure kuma ko wacce sai data haifa masa yara, duk jikinta ya yi sanyi, wani irin zazza6i takeji ga kishin mijinta daya cika ranta, tashin hankali da ba’a sa masa rana, sai a yanzu ta fahinci cewa sai tayi da gaske zata iya zama da kishiya wato idan ta ka6e zuciyarta akan aikata ba dai-dai ba ta tsarkake tare da zato me kyau ga abokan zamanta shine zata samu salama, bata ta6a hango cewan tashin hankalin da zata shiga zai kai hakan ba idan ya yi auren, addua kawai ta cigaba dayi a ranta tana fatan Allah ya bata ikon cinye jarabawanta tare da kautata wa mijinta da kuma d’auke kai daga kan duk wani abin da zai kai ta gayin dana sani. Bayan sallan ishai duk aka watse akan washe gari duk tare zasu tafi _Bauchin_ harda _Baffa_ daga nan zai duba yaron da zasu kawo kawai a chan. Tashin hankali _Sufyan_ shine ganin har aka watse _Jidda_ bata sake magana ba duk da cewa babu wani alamun da zai nuna abin da yake ranta duk yaji ya rasa natsuwarsa dan shurun ba karamin illa yake da shi a tare dashi ba. Duk _Bibalo_ tana lura dashi hakan yasa taji ranta ya 6aci sosai har taso taki kula shi amma ganin cewa hakan bai dace ba kuma tabbas _Jidda_ tafi su shiga tashin hankali a yadda komai yazo mata a ba zata shiyasa ta cire komai a ranta da karfin addua ta yaki shedan daga zuciyarta ta rarrashi mijinta akan ya yi hakuri ya bawa _Jidda_ lokaci domin tana cikin tashin hankali da take bukatan fili dan ta samu natsuwa sosai, hakan ya d’an rage mishi wani abin kuma ya kara mishi so da kaunar matarsa.