DEEMAH CHAPTER 13 BY ZAHRATEEY
DEEMAH CHAPTER 13 BY ZAHRATEEY
Har zuwa yau da suka d’au hanyar _Bauchi_ babu abin da _Jidda_ tace, komai tana yinsa kamar yadda ta saba, duk wani me son sanin meke ranta ya kasa fahimtar komai, fuskarta fayau babu wani abin da zaka iya karanta a tare da ita. Duk _Sufyan_ ya takura da wannan sauyi dan shurunta ba karamin illa bane a gareshi, ya sani ba’a komai take yawan magana ba sai akan abin da zai zama illa a rayuwarsa misali rashin bawa addininsa mahinmanci wanda ya kaishi halin daya shiga a baya, bayan haka ita ba mace me yawan korafi ko mita bace, tana da d’auke kai akan abin da zai iya sanyata wani hali shiyasa yake matukar so da kaunarta, kamar yadda yake ko mata dari kake dasu dole akwai wacce kafi so har cikin ranka wacce ba zaka iya had’ata da kowa ba a cikin ranka wacce tayi wa mata yan uwanta nisa a cikin ranka ta yadda ba zasu iya kawo matsayin ta ba hakan ya kasance akan _Jidda_ macece d’aya tamkar dubu wacce ba zai iya had’a soyayyarta da ko wace mace ba domin itan ta musanmance. Ba wai kyau ko kyaun jiki ko nasaba ke daga darajar mace a gurin mijinta ba a’a akwai mace me shiga rai da yawan kwarjini wacce kuma idan sonta ya yi wa mijinta yawa sai ya yi wa sauran yan uwan ta fintinkau, ta iya yiyuwa macen farko ce kota biyu kota uku kota hudu, babu wacce hakan ba zai iya fad’awa a kanta ba, hakan shine gaskiyar magana akwai wacce sonta da kaunarta ba’a iya had’a shi dana kowa sai dai miji me sanin yakamata shike iya boyewa dan zaman lafiyan gidansa da kwanciyar hankalin matansa.
+
Har suka isa _Bauchi_ ko wani mota shuru kakeji sai dai idan amsa waya sukayi, direct gidansu _Khadeemah_ na yanzu suka nufa. Suna zuwa _Anty Aisha_ ta shiga ta sanar da zuwansu, kafin ta fita ta shigo dasu har da mijinta daya iso a lokacin. D’aya bayan d’aya suka shiga suka zauna akan babban tabarman da aka shimfid’a musu, dan ma tsakar gidan nada fad’i da kuma girma, bayan sun gaigaisa a tsakanin su _Anty Aisha_ ta fara musu bayanin komai daga farko har karshe harda tattaunawar su da _Khadeemah_ karshen zuwanta gidanta. Anan _Inna Suwaiba_ take cewa ai itama tun zuwan su ta’aziyyan rasuwan da akayi a gidansu _Anty Aisha_ ta sa ayar tambaya akan kamannin yaran da yan gidansu, karshe data tuntu6i _Khadeemah_ shine take bata labari tare da sanar da ita cewa ai _Sufyan_ din d’an gidansu _Anty Aisha_ ne saboda sunan family dinsu data gani a jikin wani kati dake cikin wallet dinsa daya bari a gurinta da kuma kama da ta gani a tsakanin sa da _Anty Aisha_ da yaran data gani a gidan karshen zuwan.
Mamakin irin wannan juyayyen lamari me hade da kaddara kawai sukeyi ashe yaran ba yan gaba da fatiya bane da ubansu da gatansu da nasabarsu me kyau, y’ay’an manyan mutane ne kuma jikokin manyan mutane, lailai sun tafka babban kuskure da suka so wofintar da rayuwar yarsu dana yaranta alhalin komai a tsaftace yake a tare dasu, tattaunawa sukayi cike da fahimtar juna tare da neman yafiyar juna bisa abinda ya faru a rashin sani da kuma jajantawa akan 6atan _Khadeemah_ kuma sunyi alkawarin sake tsaurara bincike, abu da manyan mutane da akeji dasu surakar gida ta 6ata ai abin ba kanta, nan danan aka fara yad’awa a k’afafen labarai aka fara sabuwan bincike na musanman. Kafin su tafi sai da _Jidda_ ta nemi alfarman a dawo mata da yaran domin su had’u da yan uwansu su san junansu, sosai kowa ya yaba da tunaninta akan hakan duk da cewa dama suna da niyar kar6an yaran amma jin maganar ya fito daga gurinta shi yafi komai sanyaya ransu, ya za’a yi da kaddaran dake tattare da rayuwar dan adam da so samu ne ai baza su so lamarin ya juye ta hakan ba, sai dai Allah ne ya san dalilinsa na sanya abubuwan suka faru a juye. Sun yanke shawaran a cikin satin yayansu _Khadeemah_ zai je ya d’auko yaran. Duk kowa a gurin ganin mutuncin _Jidda_ yakeyi tare da kunyar idanun mace kamarta me hakuri da kawaici da iya zama da mutane, uban gayyan Allah Allah yakeyi su isa gida ko zai samu ke6ewa da matarsa domin ya yi matukar kewarta kuma yana son cike mata duk wani shakku dake cikin zuciyarta. Da ace ta san matsayinta a ransa data ajiye duk wata damuwa duk da cewa babu abin da ya nuna meke yawo a zuciyarta amma kowa ya san cewa dauriya ne da kuma karfin addua yasa ta iya wanzar da farin ciki da natsuwa a saman fuskarta. _Habiba_ kuwa mamakin shin wace irin macece kishiyarta shine kawai ke d’awainiya a cikin ranka, tabbas zata so Allah ya bata irin hakuri da juriyarta. Duk da cewa itama ta san a fannin halayyan kwarai itama ba baya nace amma kuma gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta tabbas _Jidda_ abar koyi ce ga duk wata macen da ta san kanta kuma take son samun zuciyar mijinta.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan sun baro gidansu _Khadeemah_ sai _Anty Aisha_ ta nemi alfarman su wuce gidansu _Jidda_ domin akwai abin da take son su sani wanda suka dad’e suna 6oyewa, duk ta saka su a duhu amma duk suka yi shuru suka wuce gidan _Hajy Naja_ kanwar _Daddy_ matar baban _Jidda_. Bayan isansu 6angaren me gidan mazan suka nufa sukayi sallah, matan kuma 6angaren _Hajy Naja_. Bayan sun idar duk suka hallara a 6angaren mahaifinsu _Jidda_ a nan aka sake mai da zancen kafin _Anty Aisha_ tasa aka shigo dasu _Anas_ ta gabatar dasu ga dangi tare da fayyace musu komai game da 6oyesu da akayi na tsawon wannan lokacin. Ita dai _Jidda_ kanta a k’asa tana tunan ko ransu zai 6aci akan al’amarin amma sai ta ga ak’asin hakan kowa na farin cikin ganinsu tare da jinjinawa hakurinta bisa dauriya data nuna akan rashin y’ay’anta a tare da ita duk da cewa ta san waye silar rugujewan farin cikin ta amma tayi hakuri ta bar komai a ranta. Hakuri suka bawa mahaifinta akan wannan cin mutunci da _Mama_ tayi musu da cin zarafin sirikarsu harya kaita ga rasa y’ay’anta da kuma 6oye wasu saboda kare lafiyarsu. sannan itama _Jidda_ suka bata hakuri tare da neman hadin kanta akan a hukunta _Mama_ dai-dai da laifin ta dan sun santa da taushin zuciya da hakuri yanzu zatace a bari ta yafe. Hakan kuwa ya faru tace ta barsu da Allah hukuncinsa shine dai-dai, alfarman d’aya take nema yaran su cigaba da zama a gurin _Hajy Naja_ na d’an wani lokaci kafin su dawo cikin yan uwansu. Kafin lokacin da sannu halayyarsu _Mama_ zai bayyana inda tabbas ta san watarana za’a kama su dumu-dumu tunda har _Sufyan_ ya dawo dole zasu sake gwada wani abin musanmance a kansa ko a kan d’an _Habiba_ tunda yara maza sune suka tsole musu ido. Sosai suka amince da shawaranta kafin abokin _Daddy_ dasu _Baffa_ suka musu sallama suka wuce suma kuma suka wuce nasu gidan cike da tunanin rayuwa da abubuwan dake cikin ta na dadi da akasinsa.
Duk wannan bidirin da akeyi su _Mama_ basa nan sunyi tafiya zuwa bikin kawarta a garin _Kano_ da ita da _Hanifa_ da mahaifiyar _Hanifa_. Hakan ya kara kwantar da hankalin mutanen gidan, masu mugun zuciya ma duk suka ajiye makamansu domin _Mama_ ta zarce inda suke tunani ba karamar yar ta’adda bace tunda har abin nata harda kisan kai yaran da basuji ba basu gani ba basu da laifin komai jarirai. Sosai sukayi ta jinjina lamarinta kuma kowa anja mishi kunnen rufa bakinsa karma maganar ya fita dan ana son aga gudun ruwanta idan ta dawo ko wani irin abu zata sake shiryawa. Hakan yasa _Daddy_ yasa aka dasa CCTV camera a 6angarenta ta ko wani lungu da sak’o amma banda cikin kewaye.
Basu k’ara tsinkewa da lamarin _Jidda_ ba sai da suka isa suka taras har an gyarawa _Habiba_ 6angarenta, kuma abokin _Sufyan_ ta bawa contract din komai na kayan gida irin nata sai dai kala daban wanda ta ga kamar _Habiban_ take so saboda shine a jikin marfin wayarta. Sosai ta shammace su ta basu mamaki dan komai anyi an gama a tsakanin jiya da yau abu da harkan kudi a hannu babu 6ata lokaci tunda ba gini bane kawai fenti ne da kayan gado da kujeru da kayan kitchen. Abokin _Sufyan_ ke musu bayanin cewa jiya da dare ta kirashi take mishi bayanin komai tare da neman alfarman idan zai yiyu ayi daga tsakanin jiya zuwa yau sai ayi, shine yace mata zai yiyu daganan ya kira masu decoration na gida wanda ainihi su sukeyi a gidansu _Sufyan_ din ya musu bayanin komai, a daren akayi fenti zuwa rana kuma akayi fixing kayan d’aki da sauransu, sai da suka gama suka saka labulen, basu dad’e da tafiya ba su _Jidda_ suka isa gidan, shi kuma yana kokarin tafiya ya had’u dasu shine yake musu bayani bayan ya mik’a mata key din. Rasa ma abin cewa sukayi kawai sai sanya mata albarka sukeyi _Sufyan_ kam zuba mata ido ya yi yana jin kimarta da darajanta suna karuwa a zuciyarsa. _Bibalo_ ita kam har ta fara tunanin ko dai tana yi ne saboda saye zuciyar mijinta, daga baya kuma ta cire komai a ranta tare da fatan Allah ya basu zaman lafiya kawai. Daular dake tattare da gidan shi yafi komai bata mamaki dama Ashe dan binni dan masu kudine yaranta y’ay’an manya ne ikon Allah lailai Allah ya kashe ya bata ita kam sai dai godiyar ubangiji tare da fatan Allah ya kau da idon makiya ya kuma wanzar da zaman lafiya a tsakanin su.
Iyayensu mazan ko wanne 6angarensa ya tafi yayinda matan suka dunguma 6angaren _Habiba_ suna kallon ikon Allah tare da adduar dacewa duniya da lahira ga _Jidda_ da kuma fatan Allah yasa zaman su ya d’ore a haka ya kuma kawar da fitina a tsakanin su. Bayan duk sun watse _Anty Aisha_ da _Jidda_ suka koma 6angaren _Jiddan_ anan ne take cewa meyasa _Jidda_ bazata bari shi _Sufyan_ din ya yi komai da kansa ba, wai ita bataji haushin auren daya kara bane har guda biyu kuma harda rabon y’ay’a shida a tsakanin su. Murmushi kawai _Jidda_ tayi tana kallonta kafin tace ” _Anty Aisha_ yanzu idan nace zan tashi hankali in tashi na mijina meye ribana to? Sanin kanki ne yana sona sosai so na tsakani da Allah kuma yana kaunata fiye da tunanina, duk wani abin da zai 6atamin rai yana kokarin kaucewa sam-sam baya son ya ganni cikin damuwa ko tashin hankali to me kuma nake nema, miji me sona, ga y’ay’a kuma Allah ya bamu masu natsuwa da baiwa na musanman, ga uwar miji me sona da yar uwar miji me sona uban miji me sona dangin miji masu sona matar uba wacce take dangin miji me sona, nayi karatu ina da ilimi ya budemin asibi ya mallakamin abubuwa da yawa me kuma nake bukata _Anty Aisha_ a duniya duk wani farin ciki ya bani sai nice zan kasa bashi farin cikin daya dace? Ina matukar son mijina ina kishinsa inaji kamar ba zan sake bari ma ya ra6eni ba saboda kishinsa dake cin zuciya ta amma idan nayi haka meye ribana, iyakaci dai ya bani hakuri kuma ya fara jin haushina kuma yaje ga d’ayar mayarsa, idan na kwantar da hankalina na kwantar da nashi na bashi natsuwa sai kimata da darajata da soyayyata a gareshi ya kara ninkuwa kinga kuwa a wannan ga6ar naci riba bama kad’an ba. Dan haka tashin hankali ba nawa bane idan nayi tamkar nayi butulci ne ga ubangiji daya sanyani a cikin ni’imarsa kuma ya jarrabeni na kasa cinyewa. Dole sai muna sara muna duban bakin gatari dole sai muna takatsatsan muna bin dokokin ubangiji shine zamu samu ribar zaman duniya kuma mu samu dacewa a lahira, _Anty Aisha_ idan nace zan tashi hankalin kaninki keda kanki bazaki yarda ba kuma bazakiji dadi ba, dan haka mu fuskanci gaskiya sai mu zauna lafiya” Matse hannuna dake cikin nata tayi tare da share hawayen daya zubo a fuskarta da dayan hannun sannan tace “kiyi hakuri _Jidda_ tabbas bai dace ince hakan ba dan hakan dai-dai ne da son rushe alkairinki, Allah ya baku zaman lafiya tare da hakuri a cikin tarayyarku. Tabbas ke alkairi ce acikin ahalin mu kuma muna alfahari dake” ta fad’a tana murmushi har zuciyarta tana jin dadin samun _Jidda_ a matsayin matar kaninta.Har nayi barci zancen gaisuwar shine a raina kuma har washe gari ina nan ina hadawa na kasa, karshe dai kawai na share zancen na cigaba da hidimomi na. Sau uku muna zuwa gaisuwan gayyar sodi na karshen ma harda _Asiya_ akaje shima acewar _Ummulu_ wai dan saboda tana son mijin matar da muke zuwa yiwa ta’aziyyar rasuwan kanwar mijin kanwar nata ne shiyasa taje kila ko dan ta ganshi ne waya sani. _Alhaji me gwanjo_ shima har yanzu yaki kama gabansa yaje ya yi abinda zai taimake shi, kullun sai zarya yake mana a kofar gida kamar me gadi _Mama_ kuma arzikin da yake kawowa shine ya tsole mata ido take ganin cewa bada ni ya dace ba da _Ummulu_ wai ya dace, a 6angaren _Ummulu_ kuwa zuciyar ta naga _Yaro_ yayinda na _Yaro_ yake gareni ni kuma nawa ban san ina ya dosa ba amma bana sha’awar sanya wani ma acikinsa.
Ana cikin haka wata rana munje kaiwa _Yaro_ abinci shine _Ummulu_ ta tsaya gaisawa da wata kawarta ni kuma naje na mik’a mishi, kasancewar ina zuwa ne daga bayan su shiyasa basu ganni ba, a nan nake jin cewa wai ni _Yaro_ yake so har cikin ransa, sosai hankali na ya tashi har zan juya in koma sai kuma nayi tunanin me zan cewa _Ummulu_ idan ta ganni na koma da abincin? Daurewa nayi na k’arasa tare dayi musu sallama muka gaisa sannan na bashi. Yau bana jin karfin zuwa mike kafan duk jiki na ya yi sanyi son maso wani koshin wahala, wani irin tausayin _Ummulu_ ne ya kamani na rasa ma meye mafita a cikin lamarin, shin zanje ince mishi _Ummulu_ na son shine ko dan ya cire sona ya kama yar uwarsa ko kuma dai zan amince ne kawai da auren _Alhaji me gwanjo_ ta yadda ita kuma _Ummulu_ zata samu biyan bukata? Wani hanzari ba gudu ba shin _Mama_ zata ta6a amincewa da tarayyan _Yaro_ da _Ummulu_? Ni duk kaina ya kulle na rasa mafita guda daya dan duk inda na 6ullo sai naga matsala ta wani 6angaren.
Gabadaya ranan haka na yini ina ta sake-sake da warwara duk na rasa inda ya dace in bi, duk nacin _Ummulu_ haka ta hakura ta barni har tayi barci idona biyu ina ta tunani. Washe gari ya kama _Litinin_ kuma yau su _Ummulu_ zasu fara zana jarabawan fita daga makarantar sakandiri. Sai murna takeyi ta hana kowa sukuni da zancen gama makaranta, ni abin ma dariya yake ta bani duk da cewa wani 6angarin tausayinta ne a zuciyata ya yin da wani 6angaren kuma ke bani shawaran tunkaran _Malam_ da maganar ta yadda idan har ya yarda _Mama_ bata isa ta hana faruwar komai ba, sai dai laifi daya zanyiwa _Yaro_ zan nuna cewa suna son junansu sai dai tsoron _Mama_ ne yasa suke 6oyewa dan karta hana su auren juna. Idan har _Ummulu_ ta samu _Yaro_ shikenan nima na hutawa kaina da auren _Alhaji me gwanjo_ dan dama saboda kar _Yaro_ yace ni yake so kuma _Mama_ ta samu daman makalawa _Ummulu_ _Alhaji me gwanjo_ shiyasa nayi tunanin aurensa amma tunda yanzu na samu wani mafitan zan gwada in gani ko za’a dace. Hakan ne ya bani karfin gwiwa na cigaba da hidimomi na ina jiran dawowan _Malam_.
Cikin ikon Allah a ranar sai su _Mama_ suka fita wani guri da yamma har zuwa dawowan _Malam_ basu dawo ba, ita kuma _Asiya_ sun fita da wani saurayinta naji dai tana cewa _Ummulu_ kila sai gobe zata dawo. Muna zaune a saman tabarma kamar ko yaushe muna hira tana bani labarin jarabawanta _Malam_ ya shigo, bayan mun gaisa ta shiga kitchen ta dauko mishi abinci da ruwan sha, anan yake tambayar _Mama_ muka ce bata dawo ba tukunna, _Asiya_ kam bai ma tambaye ta ba. Bayan ya gama cin abincin nace mishi dama akwai abin da nake son sanar dashi, _Ummulu_ duk tunaninta na amince da auren _me gwanjo_ ne shiyasa nake son magana da _Malam_ sai da taji zancen nata ne sai kuma ta sunkuyar da kai a dai-dai lokacin _Yaro_ ya shigo shine _Malam_ yake sanar da shi abinda na fad’a kuma ya nuna jindadinsa sosai ya rinka zuba musu addua inaga hakan shine dalilin daya sa _Yaro_ ya kasa musawa ya kasa cewa ba haka zancen yake ba, tabbas kunyar idon _Malam_ takeyi ba zai ita kin jininsa ba, sai kuma a lokacin naji shima ya bani tausayi matuka duk abin da yake so sai ya rasa a cikin rayuwarsa, amma ina da yakinin cewa _Ummulu_ zata zame mishi alkairi kuma mata ta gari wacce zata so shi a duk yadda yake tunda babu wanda yasa ta son shi kuma tafi kowa sanin cewa bai da komai balle ace dukiya ta gani kuma tun farko ta san cewa yanada nakasa amma ta so shi dan haka banyi nadamar hada wannan abin ba, kuma da sannu zai gode min idan tafiya tayi tafiya.
A chan inda sukaje kuwa gurin wani malamin tsubbu, inda kawarta ta sha janta akan suje dan wani biyan bukatarta amma taki amincewa sai a wannan karon da take son hada iri da me kudi irin _Alhaji me gwanjo_ shine ta amince da zuwa gurin malamin tsubbun. Mutumin da yake aiki da aljanu kam ai dama dole ya san zaku zo kuma ya san dame kuma zo din. Sanin abinda ya kawo su shiyasa _Mama_ ta sake amincewa da aikinsa zai zama kamar yankan wuka a yadda take jin labarinsa. (Shirka shima yanzu ya zama ruwan dare a cikin al umma, had’a Allah da waninsa baya yiwa mutane wuya a wannan zamanin da muke ciki har ma da wanda suka gabata. Shiyasa da yawan mutane al’amuransu yake ta6ewa amma basa gane daga ina matsalar take, shirka ba karamin laifi bane wanda yake lalata rayuwar dan adam musanman mata 80% dinsu sunfi kowa iya dogaro ga wanin Allah. Mutane sun kasa tsayawa su yarda da kaddara me kyau ko mara kyau, sun kasa tsayawa suga hukuncin ubangiji akan duk wani roko da zasuyi a garesa, gajen hakuri yasa suna tafka kura-kurai wanda yake kaisu ga halaka yake kaisu ga dana sani kuma yake kaisu wuta. Gaggawa fa aikin shaidan ne kuma baya ta6a zanewa alkairi, dan haka mu gyara mu koma ga Allah domin babu wani abin da mutum zai mana wanda Allah bai riga ya mana ba kuma sannan yake kanyi mana, kuma duk wani jinkiri alkairi ne ga rayuwar mu, Allah ya shige mana gaba ya kuma shirya mana zuqatan mu) duk wani karya da gaskiya ya sanar dasu akan abin da zai faru wanda ya basu yakinin cewa suje kawai aiki zaiyi yadda ake so kuma su zuba ido kar suce zasuyi jayayya da komai, a zahirin gaskiya ya riga ya gani cewan abin da suke so ba zai yiyu ba, _Alhaji me gwanjo_ _Asiya_ zai aura a nan gaba ba _Ummulu_ ba kuma bani ba. Sannan kuma auren _Ummulu_ da _Yaro_ babu fashi sai anyi harda rabon y’ay’a, idan yace zai fara musu gaskiya zasuce ya yi kokari ya musu wani abin a kai shi kuma babu abin zai zai iya kuma bai da lokacin 6atawa a kansu shiyasa ya chaje su kudi me yawa da sunan aikin nada wahala amma kar su damu komai zai tafi yadda suke bukata. A haka suka dawo gida suna jin dadi tare da kwantar da hankalinsu kamar tsumma a randa.
Tunda muka koma daki _Ummulu_ tayi shuru sai murmushi takeyi “ke wai lafiyarki ko dai in koma ince wa _Malam_ kince ayi sauri asa auren nan kusa ne?” Cikin sauri ta dago kai ta kalleni tana dariya “kai _Anty_ ke koh, yanzu dan Allah waya ce miki wai _Ya Yaro_ yana sona? Nikam bana ganin cewa yana sona nama fi tunanin cewa akwai wanda yake so amma bani ba, kuma na san cewa ya amsawa _Baba_ ne saboda yana jin nauyin musa zancen, duk da haka kuma ina fatan Allah yasa ya soni din da gaske” ni dukansu ma tausayinsu nakeji, kuma sunfi da cewa da zama da juna dan duk sun san halayyar junansu, idan yace ni yake so shin ya san daga ina nake kuma wacece ni a rayuwata na baya? Bai san komai a kaina ba, bashi da yakinin cewa ni din ta kwarai ce kawai ganina ya yi kamar tsuntsu daga sama gashashe wanda ba’a san ta inda ta fito ba kuma ina ta nufa, zancen gani ma babu tunda dai babu idanun ganin nawa, idan zai yi wa rayuwarsa adalci _Ummulu_ tafini dacewa da shi saboda sun san kansu sosai sun san halayyar junansu. Ni kuma koba dade koba jima wataran zan iya tafiya in koma cikin dangina wanda nake fatan Allah ya bani ikon tunowa da koni wacece ba lailai in dawwama a tare dasu ba, kuma ni banyi dadewar da har zan amince da auren soyayya ba auren ma da wanda yar gidan da nake zaune a gurin su take matukar so, sam ba zai yiyu ba adalci shine su auri junansu zumuncinsu ya kara karko.
Haka muka kwana duk cikin tunani kala-kala da kuma fargaban kar wani abu ya rushe al’amarin, ita _Ummulu_ tunaninta _Mama_ ne karta rushe mata farin cikinta, bata tunanin rushewan ta 6angaren _Yaro_ dan ta san cewa ba zai ta6a nuna rashin son had’a zuria da _Malam_ ba. Ni kuma a nawa 6angaren tunanin kar _Yaro_ ya chanja ra’ayinsa yace zai bawa kansa farin ciki a wannan karon ba zai iya sadaukar da farin cikinsa ga wani ba shine yake ta dawainiya da raina. Ni kawai ina ga zan amince da zancen auren _Alhaji me gwanjo_ wannan kawai shine mafita idan _Yaro_ yaji labari dole zai hakura ya cire ni daga ransa baki daya ya maye gurbina da yar uwarsa masoyiyarsa ta tsakani da Allah. Amincewa da auren _Alhaji me gwanjo_ ba wai yana nufin cewa aurensa zanyi ba, ana zaune kalau daga 6ata sai aure kuma 6atan ma ba wai dadewa ya yi ba, idan misali nayi shekaru biyu zuwa uku ne sai in amince da auren wani amma ko shekara ban rufa ba zanyi aure ai ba zai yiyu ba, ko da yake sha’anin ubangiji kana naka shima yana na shi kuma nashin shine dai-dai kuma mafi alkairi. Zan amince ne saboda aurensu _Ummulu_ ya faru cikin sauki kuma zanyi ta jan lamarin auren har sai anyi auren su _Ummulu_ sai ince na fasa auren kafin nan ma nasan kila _Mama_ ta saukakemin wahalar dan na san da wuya idan bata juye auren kan _Asiya_ ba shikenan komai zai zomin cikin sauki.Tana zaune a saman sallaya tayi zurfi cikin tunani taji shigowarsu, sallaman _Bibalo_ ne yasa ta tashi ta nad’e sallayan sannan ta fito. Da gudu su _Afifa_ suka zo suna murnan ganinta dama kwana biyu basa gidan suna gidan yayan babanta yanzu kuma ta san cewa dawowarsa ne yasa aka dawo dasu dan sugan shi suma hankalin su ya kwanta. ” _Ammi_ mun dawo _Abby_ ne ya d’auko mu da kanshi tare da yan uwan mu, _Abby_ yace wai su kannen mu ne kuma wannan _Mom_ din mu ce ita ma” suka fad’a suna nuna _Bibalo_ murmushi _Jidda_ tayi tace “eh _Mom_ dinku ce suma kuma kannenku ne dama bana ce muku zai dawo muku da surprise ba shiyasa bai dawo da wuri ba? Toh sune ai sai ku rinka wasa dasu koh yanzu ma haka sauran kannen ku suna zuwa kunga muma gidan mu zai cika” tsalle suka fara suna murnan suma zasu zama suna da yawa a cikin gidan su.
+
Yaran _Bibalo_ ta nuna tace suzo, kyawawan yara ne masu kama da _Sufyan_ “lailai jikinka na da karfi” ta fad’a a ranta dan ta lura yaransa duk da shi suke kama idan aka cire yaranta da suka rasu sauran duk da shi suke kama, ga wannan ma da shi suke kama da an gansu an san jiki daya ne. “Meye sunanku?” Ta farkon data fi baki kamar _Anisa_ tace _Zainab_ sai dayan tace _Halima_ sai ta kalli kaninsu tace shi kuma _Abdallah_. _Bibalo_ ce tace _Zainab_ me sunan mamana ne muma kiranta da _Ilham_ sai _Halima_ muna ce mata _Ihsan_ ita kuma kawai sunan ne ya fad’o a ransa shine yasa mata sai _Abdallah_ me sunan _Baffana_ muna kiransa _Amir_” kar6an yaron tayi tace “masha Allah ga shi kamansu _Shureim_ da _Muslim_ yayyinsa dan _Anas_ yafi su hasken fata sosai, Allah ya raya mana su, sauran yaran _Khadeemah_ yan uku ko suma duk ya kwance mana kamannin” ta fad’a tana kallon _Sufyan_ duk sukayi dariya a lokaci guda wanda hakan ya sanyaya ransa yana ganin cewa kika ta sauko daga fushin nata.
Kallon _Bibalo_ tayi tace “ita _Haliman_ kika ce ba sunan kowa taci ba, ai kuwa ita taci sunan me sunanta dan sunan _Hajja_ take dashi wato sirikarmu mahaifiyar _Sufyan_ kuma kakar yara, lailai sunan yazo dai-dai sanda ake bukatansa” kallon _Jidda_ tayi tace “kai haba lailai ashe gwara da ban musa ba dan naso ya saka _Zulaihat_ sunan kakarmu amma ganin yace _Halima_ shine kawai nayi shuru, lailai dana aikata laifi sunan uwa guda” murmushi sukayi _Jidda_ ta cigaba dayi wa yaron wasa yana dariya suma yaran suna chan suna ta wasan su a d’akin su _Anisa_ dan sun san cewa _Ammi_ bata son suna zama a cikin manya. ” _Anty Jidda_ bari muje mu kwanta mun gaisheki kuma mun gode matuka da tarban da muka samu Allah ya saka miki da alkairi ya kuma had’a kan mu ya kare mu daga sharrin mutum da aljan harma da sharrin zuciya” suma amsa da “Amin” sannan ta kar6i _Amir_ _Jidda_ tace “ki barsu kawai su kwana anan tunda naga basu damu ba, _Anisa_ kuzo” ta fad’a da d’an karfi, bayan sun fito ta kalle su “zamu kwana anan ko _Ihsan_” cikin sauri suka gyad’a kai sunawa _Bibalo_ bye bye sannan suka d’akin da gudu su _Anisa_ kuma ganin idon _Jidda_ yasa suke tafiya a hankali suna isa kofan suka shiga da gudu, dariya _Sufyan_ ya yi yace “har yanzu baki bar takuramin _Queens_ dina bako? Dan gudun ma da zasuyi kin kasa kin tsare wannan idan sukace sport zasuyi sunan son zama yan kwallon kafa ko hannun ko dai wani abu daya had’a da gudu ai an shiga uku” ya fad’a cike da zolaya _Bibalo_ na taya shi dariya tana cewa “seda safe _Anty Jidda_” _Jidda_ tace “Allah ya tashi mu lafiya” shi kuma _Sufyan_ ya fita raka _Bibalo_ bai wani dade ba ya dawo angaren _Jidda_.
STORY CONTINUES BELOW
D’akin yaran ya fara shiga anan ta sameta, wanka tasa su sukayi bayan sun fito tasa ko wacce tayi wa kanwarta wanka sai da suka fito suka chanja kaya zuwa na barci kafin sukayi adduar barci ko wani gado mutum biyu _Anisa_ da _Ilham_ yan kaud’i sai _Afifa_ da _Ihsan_ masu sanyin hali, bargo taja musu ta d’an rufe su sannan ta kashe Ac ta kunna fanka shima bata cika musu sanyin ba ta rage zuwa d’an dai dai yadda zasuji dadin barci. A bakin k’ofa suka ci karo ita bata san ma ya dade a gurin ba, d’auke kai tayi ta wuce ta barshi a gurin, janyo musu kofan ya yi kafin yabi bayanta. Ban daki ta shiga tayi wanka tana fitowa shima ya shiga cikin sauri ta shirya cikin doguwar rigar barci tayi addua ta kwanta. Yana fitowa ya ganta a kwance ta juya baya, murmushi ya yi dama ya san za’a rina duk karfin hali ne irin na _Jidda_ da dakewar zuciya akwaita da kokari ta wannan fannin. Sai da yasa kaya shima sannan ya haura gadon, juyo da ita ya yi da karfi yana kare mata kallo, ta rame tayi duhu kad’an ya san duk damuwa ce tayi mata yawa, “kiyi hakuri kinji _Jiddatulkhair_ macen kwarai _JiddanSufyan_ mace d’aya tamkar dubu, dan Allah kiyi hakuri ki kulani karki min wannan horon domin zuciyata ba zata iya d’auka ba kinji” kuka ta fashe dashi wanda ya sanyaya ransa dama abin da yake son tayi kenan matukar tayi d’in zataji saukin damuwarta kuma komai zai wuce a gurinta, sosai tayi kuka sai da tayi harya wuce yadda yake zato kafin ya fara rarrashinta, sai da yaga ta natsu kafin ya chanja salo zuwa nuna mata yadda ya yi kewar ta tun tana nokewa harta biye mishi ya mantar da ita cewa akwai ma wata bayan ita a cikin gidansa.
Washe gari da safe ta tashi da zazza6i saboda kukan da tayi dak’er ya samu zafin jikin nata ya ragu dan akwaita da wani irin zafin jiki idan tana zazza6i abin har tsoron yake bashi wani lokaci duk sai ta fita hayyacinta haka zai yi ta gasa mata jiki da ruwan sanyi harse zafin ya ragu sai ya shafa mata man kad’ai da man alayyadi kuma ya bata man alayyadin ta sha ta kwanta daga nan idan tayi barci shikenan zata tashi jikin da sauki. Sai da ya tabbatar tayi barci kafin ya fita daga d’akin zuwa d’akin su _Afifa_ ya samu har sunyi wanka sunyi wa kannensu, sosai yaji dadin hakan a ransa tabbas _Jidda_ tayi musu tarbiyya ne kyau da ace wasu ne da ko Kansu ma basu gyara ba balle har su gyara wasu a iya shekarunsu ” _Abby_ ina kwana” duk suka fad’a a tare su a yaran sukayi yadda suka ga sunyi din, ya amsa cike da fara’a _Afifa_ tace ” _Abby_ bari muje mu gaisheki da _Ammi_ sai mu kar6o kayansu _Ihsan_” kallon su ya yi kafin yace “toh kuzo muje nima can zanje amma _Amminku_ tana barci ku bari anjima sai kuje ku gaisheta idan ta tashi” a tare sukace “to” sannan ko wacce ta d’auko kanwarta guda suka bi bayansa.
A 6angaren _Bibalo_ dama daker tayi barci jiya sai da ta had’a da sallan dare da karatun alkurani sannan ta samu sa’ida a cikin zuciyarta ta kuma samu natsuwa. Ta kuma yi alkawarin cewa ba zata ta6a bari kyaun _Jidda_ da matsayinta a zuciyar mijinsu _Sufyan_ yasa ta gaza samawa kanta matsayin na musanman a gurin mijinta ba. Idan tace zata tsaya kishin banza da wofi tabbas itace a lura domin ta lura _Jidda_ ta san me takeyi macece ne ilimi da wayo kuma mace ce wayayyiya wacce ta san kanta kuma tayi takunta. Dole ita ma ta d’aura d’amaran samun zuciyar mijinta ta hanyar yin kishi me tsafta me cike da ilimi da basira ba kishi irin na jahilan mata ba. Ta san cewa ilimin addini tana dashi sosai sai dai ilimin boko shine abin da bata samu ba kuma zata bada himma wurin samun hakan. Abin da aka haifi mutum da baiwarsa shine kawai duk kokarinka zaka gaza kamo kafarsa amma abin da mutum ya koya idan ka bada himma kai ka zaka zama gwani a naka fannin. (Mata da yawa sune suke lalata aurensu da kansu ba wai wani ke lalata musu ba. Idan ita macece kema macece ai, idan zuciyar mijinki yana gareta kema sai kiyi aiki da hankali ki samu zuciyarsa ta yadda ko da ance ya za6i d’aya a tsakanin ku biyun ba zai ta6a yarda ya rabu dake ba yadda ba zai yarda ya rabu da wacce yafi so din ba. Idan ita ta taso da baiwar iya girki kema zaki iya koya kuma idan kika saka zuciyarki akan koyan kema zaki iya ta yadda duk wanda ya d’and’ana ya san kema gwana ce gwargwadon nakii iyawan. Idan ita Allah ya yi ta da ni’ima mara gushewa har ta fiki ta wannan fannin gurin kula da miji kema idan kika saka kai gurin shan kayan itatuwa da natural abubuwan da basu da illa wanda iyayenmu da kaka da kakanni sukayi amfani dashi sai kiga kema kin samun damar sanyawa mijinki natsuwa dai-dai gwargwado. Idan ita tana da dauriya gurin tarban mijinta a gurin shimfida ke meye naki matsalar da bazaki iya daurewa ki bawa mijinki farin ciki ba, kila itama irinki ce amma saboda son farantawa mijinta take daurewa tare dayiwa kanta gyara marasa illa, amma ke kin zauna kin zama sauna karshe kice ta asirce shi, ke meyasa ba zaki tashi tsaye kiyi aiki da hankali ba kiyi abin da ya dace wanda bashi da illa. Akwai abubuwa da yawa da mata keyi tsaban lalaci da sakaci wanda shine silar rushewan aurensu. Idan ita ta iya ke meye matsalarki kiyi aiki da hankali mana ki samu mafita, idan ita tana tashi sallar dare kullun ko lokaci zuwa lokaci kuma tana karatun alkurani ko wace safiya ko kuma ko wani bayan sallar da zatayi ke meye matsalarki, ki zauna kiyi tunani ki gyara rayuwarki domin rayuwar aurenki tayi karko, dan Allah mata mu gyara, Allah yasa mu dace).
Da sassafe tayiwa _Amir_ wanka itama tayi ta tsara kwalliyarta dai dai yadda zata iya kuma tayi wanda ya dace da shigarta ba kuma wanda zai lalata mata fuska ba. Tana zaune a falo tana cin bredi da shayi suka shigo da gudu tare da sallama, amsawa tayi tana murmushi “yarana har an tashi kenan” karasawa suka gurinta sukayi hugging dinta yadda sukeyi wa _Jidda_ sannan suka gaisheta, cike da fara’a ta amsa gaisuwar da sukayi mata sannan tace waya musu wanka, sukace su sukayi kuma sukayiwa su _Ilham_ sosai tayi mamaki tana kuma kara yabawa tarbiyyan _Jidda_ da kuma kokarin ta duk da kasancewarta ma’aikaciyar asibiti amma ko me aiki bata dashi komai ita takeyi abinta. Gaishe da _Sufyan_ tayi tare da tambayan _Jidda_ ya amsa yana d’aukan _Amir_ tare da cewa “kinyi kuka ko?” a saitin kunnenta, dariya kawai tayi a hankali sannan ta cewa su _Afifa_ suje d’akin zasu ga kayansu _Ihsan_ din sai su saka musu, da gudu sukayi d’akin data nuna musu, “da _Anty Jidda_ na nan ba zasuyi wannan gudun ba” murmushi ya yi yace “ai sun sani bata san ta ga mace na gudu sai tace ai wannan aikin maza ne bana mata ba” zama ya yi a kusa da ita ya sanya hannunta a na shi ya yi kissing sannan yace “kin tashi lafiya farin cikin raina” sosai taji dadin hakan ta amsa da “lafiya kalau annurin raina” sukayi dariya a tare “nayi kewansu _Baffa_” cire hannunsa ya yi daga nashi jin motsin fitowarsu “nima nayi kewarsu sosai, ki d’an basu shayi ko taliyar yara basuyi karyawa ba _Amminsu_ ta kwana da zazza6i” sai da taji wani iri a zuciyarta dan ta san mijin nasu ba sauki amma ta daure ta yaki shedan daga zuciyarta tare da cewa “ayya Allah ya bata lafiya, bari a dafa harda kai itama sai inyi mata abin da marasa lafiya zasu so” ta fad’a tana shiga kitchen din, sosai yaji dadin hakan data ce dama baya son yace tayiwa _Jiddan_ wani abu taji ba dadi shiyasa ya yi shuru. Ita kuma ta san abin da yake ransa kenan amma adalci irin nasa yasa baiyi magana ba, wani irin matsayin ya kara samu a ranta domin ya cika mijin kwarai me kiyaye dokokin Allah akan hakkin iyalansa.