DEEMAH CHAPTER 15 BY ZAHRATEEY

DEEMAH CHAPTER 15 BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tana zaune a kan kujera tana kallonsu cike da tausayawa, wasa sukeyi amma minti minti suke sako zancen mamansu, yau satinsu biyu kenan da zuwa gidan ita kuma watansu guda da zuwa _Bauchi_  sosai yaran suke da wayo ga rigima da kuma surutu, duk cikin yaransu ta lura _Anas_, _Afifa_ da _Ihsan_ sune masu sanyi amma sauran duk yan kaud’i ne musanman _Anisa_, _Ilham_ da _Ummita_ duk sunfi kowa kokari. Tashi tayi ta shiga kitchen dan duba girkin data d’aura, yau gidan shuru _Abby_ da _Ammi_ duk sun tafi aiki daga ita sai yaranta. Tana shiga ta samu ruwan shikafan ya shanye haka zalika miyan shima ya yi dan duk mai ya gama fitowa ruwan ciki ya shanye, kula ta samu ta zuba nasu ita da _Jidda_ da _Sufyan_ yaran kuma ta zuba musu a babban tray dan a ka’ida tare suke cin abinci domin hakan na kara dankon zumunci.

_Afifa_ da _Anisa_ ta kira suka d’auka musu, _Afifa_ ta d’auki abincin _Anisa_ ta d’auki zobo da kofuna, babban ledan cin abinci ta shimfid’a musu a gurin dinning sannan suna ajiye, bayan ta zubawa kowa zobon a cup ta kirasu suka zo suka zazzauna sukayi bismillah kafin suka fara ci. Madaran yara ta dama wa _Amir_ dai-dai yadda zai iya sha, sai da ya shanye sannan ta ajiye shi a gurinsu tare da kayan wasa ita kuma ta shiga wanka. Bata wani d’au lokaci ba ta fito dai-dai lokacin taji karan motarau _Sufyan_ cikin sauri ta k’arasa shiryawa tana cikin d’aura d’ankali ya shigo dama yau ranar girkinta ne.

Sannu da zuwa tayi mishi wannan ta kar6i kayan hannunsa ta adana su a guri guda, ruwan wanka ta had’a mishi tare da taimaka mishi gurin cikin kayan. Rigima yaso mata akan dole sai dai suyi wankan tare ita kuma tace ba zai 6ata mata kwalliya ba haka kawai zai maida ita kifi yanzu fa ta gama wanka, sai da sukayi drama kafin ta amince aka sake wanka, kallon agogon dake jikin bango tayi taga sun 6ata lokaci sosai ” _Abby_ kalli fa gaskiya mun 6atawa _Anty Jidda_ lokaci baka kyauta ba” dariya ya yi cikin sauri ya k’arasa shiryawa suka fito a dai-dai lokacin ita ma _Jidda_ ta shigo “dama ashe had’in baki ne abin shine kukayi anko kuka barni” sai a lokacin suka kalli junansu dariya sukayi a tare _Bibalo_ tace “lailai kam munyi maka wayo, _Anty_ kayan sunyi miki kyau sosai” murmushi _Jidda_ tayi tace “kema naki sunyi miki kyau, kuyi hakuri na tsaya waya da _Anty Aisha_ ne shiyasa ban fito da wuri ba” ta fad’a tana zama a kujeran dinning din “babu komai _Anty_ yaushe zamuje gidanta ne?” _Bibalo_ ta fad’a tana zuba musu abincin “Ko gobe ma tunda weekend ne sai muje ko _Abby_” kallon _Jiddan_ ya yi cikin tsigar zolaya yace “ba komai ni da yaran kuma zamu fita yawo ko _Maman yan 4_” bata kulashi ba ta fara cin abincin ta tana yaba wa _Bibalo_ shi kuma ya rinka dariya kasa-kasa dama ya san ba zata ce komai ba. Sai data gama cin abincin sannan tace “ai ni na gama haihuwa na sai dai _Habiba_ da _Khadeemah_ suyi nikam naci girma”.

Har zata tashi sai kuma ta juyo tace “ni kam wai _Abby_ ya batun cigiyar _Khadeeman_ ne, anya suna wani abu a kai kuwa? gaskiya ya dace a k’ara takura musu domin su tsaurara bincike” ajiye cokalinsa ya yi “wallahi sunayi kawai an kasa tracing dinsu ne, alamu sun nuna cewa kwararru ne 6arayin, amma dai su jami’an tsaron sunce zasu kara tsaurarawa in sha Allahu za’a sameta” a tare sukace “Allah yasa hakan” yace “Amin” tashi _Jidda_ tayi ta taimaka mata suka kwashe komai suka kai kitchen sannan ta musu sallama ta koma 6angarenta, gurin motsa jikin dake cikin 6angarenta ta nufa, sai da tayi zufa sosai sannan ta hakura ta wuce d’aki tayi wanka ta kwanta dan huta gajiya kafin su koma gurin aiki anjima.

STORY CONTINUES BELOW

Karfe uku ta tashi ta shirya tana saukowa daga stairs sukayi kicibus da juna “barci kikayi ko? Naga har yanzu idonki bai gama bud’ewa ba” murmushi tayi wanda ya zame mata jiki “eh yanzu ma na tashi shine na shirya na fito ashe kaima har ka gama shiryawa?” Yace “eh muje ko” ya fad’a yana kar6an jakarta suka jera tare, suna zuwa gurin motar ya ajiye jakar a baya inda nashi brief case din yake sannan ya bud’e mata mota ta shiga shima ya zagaya ya shiga 6angaren direba sannan ya tada motar suka tafi. Kasancewar babu nisa sosai cikin mintina biyar suka isa, jakarta ta d’auka tare da brief case din shi, suna zuwa office dinsu ta ajiye kayan hannun nata ta shiga wani d’an d’aki ta chanja kaya shima ya shiga ya chanja nashi sannan suka wuce d’akin tiyata inda zasuyiwa wata mata aiki a zuciyarta.

Basu suka dawo gida ba ranar sai guraren karfe goma, sun samu har yaran sunyi barci ma, sai daya rakata 6angarenta ya tabbatar taci abincin da _Bibalo_ ta ajiye mata dan ya santa sarai idan har sukayi dare irin haka bata zama taci abinci kawai kwanciya takeyi dan gajiya shiyasa ya zauna ya tabbatar taci ta koshi kafin ya mata sai da safe ya tafi 6angaren _Bibalo_, itama ya samu harta fara barci sai da yaci abinci ya yi wanka sannan ya tasheta ya sanar da ita dawowansa, tashi tayi da niyyar dauko mishi abinci yace mata ai ya riga yaci har ya yi wanka karta damu, har zatayi mitan meyasa bai tasheta ba ya wahalar da kansa sai kuma kukan _Amir_ yasa tayi shuru ta d’auke shi ta shayar da shi, sai da ya koshi kafin ta jijjiga shi harya koma barci sannan ta kwantar dashi, itama ta kwanta tana cewa “idan ba wai rashin lafiya ba duk dare idan ka dawo ka rinka tashi na” yace “shikenan yi hakura ba za’a sake hakan ba” sannan ya yi addua kafin ya jawo ta jikinshi suka kwanta.

Washe gari ya kama weekend, _Jidda_ da _Bibalo_ da _Amir_ suka wuce gidan _Anty Aisha_ su _Sufyan_ da yaransa kuma suka tafi park kala kala karshe suka yada zango a park din gidan su. Basu dawo gida ba sai kusan magriba dan sai da suka biya gidan _Hajy Naja_ suka ajiye su _Anas_ sannan suka wuce gida. Su _Jidda_ kuwa sun dawo da wuri dan ana la’asar suka dawo, _Jidda_ ce da girki hakan yasa bata huta ba ta shiga kitchen. Kafin magriba ta gama komai tuwon alkama da miyan kubewa daya sha man shanu sai kuma kunun tsamiya da tayi wanda _Sufyan_ yake matukar so. Ana kiran sallan magriba suna shigowa gida, matan suka wuco 6angarenta sukayi salla mazan kuma suka wuce masallaci tare da _Abby_ bayan sun idar suka wuce 6angaren _Bibalo_ dan cin abinci ita kuma _Jidda_ da mijinta suka ci nasu tare.

A 6angaren su _Mama_ sunyi sabon aiki ne akan _Khadeemah_ dan karta bayyana balle har ta sake haihuwa, boka ya sanar dasu komai a kanta har da mantuwan da tayi na ko ita wacece wanda shi ne silar rashin dawowar ta, haka yasa suka bashi kud’i me tsoka akan ya yi aiki a kanta ta hanyar nisantar da ita daga garin _Bauchi_ ita kuma _Bibalo_ sun batta ne tukunna ta mori dukiya wai acewarsu kafin suyi aiki akanta ita ma, yanzu sun gwammace _Hanifa_ ta auri _Sufyan_ akan ya rinka auren wasu suna zazzaga mishi y’ay’a ko ba komai idan _Hanifa_ ce a matsayin matarsa kuma take haifa masa y’ay’a su zasu mori dukiya. Na _Jidda_ ba matsala bane ko kashe ta suka soyi ta hanyar _Hanifa_ tsaf zasu iya cikin sauki amma na zasuyi hakan ba sai sun samu cikar burinsu _Sufyan_ ya auri _Hanifa_ domin itace garkuwarsu ta wannan 6angaren.

A 6angaren _Hanifa_ kuwa burinta shine ta fara sanin wacece ainihin mahaifiyarta a tsakanin yan uwa biyun shiyasa a yanzu take bibiyar ko wani motsinsu, tana sane da cewa suna harin _Jidda_ da _Bibalo_ a yanzu kuma ta fahimci cewa sun amince da aurenta da _Sufyan_ a wannan lokacin, sannan kuma taji batun aikin da sukayi akan _Khadeemah_, yanzu tana tunanin yadda zata tunkari _Jidda_ da batun aurenta da _Sufyan_ amma tana so sai taje _Kano_ gurin mahaifinta ta samu bayanan da take bukata kafin ta dawo ta tunkari zancen aurenta sannan kuma taci mutuncin su _Mama_ kafin ta kawar dasu _Jidda_ su zama tarihi.

_________________________

Ina zaune a bakin rafi ina jiran _Ummulu_ munje tsinko wa _Malam_ wasu ganyayyaki na magani kasancewar bayajin dadi kwana biyu, shuru nayi na tsurawa ruwan idon a raina so nake in shiga ruwan saboda yadda yake wani ruwan bula bula me haske da kuma fari ruwan gwanin ban sha’awa, “ba dai shiga zakiyi ba? Shine fa ruwan da _Malam_ ya tsintoki daga ciki kuma ruwa ne me cike da hatsari kala kala dan haka karki soma wallahi” ta fad’a cike da tsoron a idanunta.

Murmushi nayi ina kallon ruwan sannan na tashi ina cewa “da dai naso in shiga din kafin ki dawo saboda kyaun da ruwan ya yi min, amma tunda kin tsorata na fasa muje amaryan _Yaro_” rufe fuska tayi wai ita kunya sai kace ba ita bace ta gama nuna alamun tsoro saboda nace zan shiga ruwa, kama hannunta nayi nace “muje to” tafiya muke muna hira jefi-jefi musanman akan lamarin _Asiya_ da _Mama_ a haka har muka isa gida.

A kan tabarma muka same su sunyi jugum jugum hankali a tashe ga _Yaro_ shima a tsugune ni duk sai na fara tunanin ko ya shaida musu cewa baya son _Ummulu_ ne ni yake so, tunani kala kala dai babu wanda banyi ba karshe naji _Ummulu_ na tambayan ko lafiya shine _Mama_ take bayanin cewa wai _Asiya_ ce tayi ciki, har kusan watansa biyar babu wanda ya farga sai yanzu take sanarwa dan kar a saka bikinsu da _Alhaji me gwanjo_ a bari sai ta haihu tukunna, zaman yan bori _Ummulu_ tayi a kasa ta fara rera kuka ni kuma na zauna a saman wani dakali na zuba tagumi.

Muna zaune cikin tashin hankali sai gata ta fito cikin kwanciyar hankali tasha kwalliya fukarnan kamar anyi 6arin hoda da kallo muka bita har da _Ummulu_ dake rera kukan bakin ciki “sai dai hakuri fa aikin gama ya gama babu yadda za’a yi sai dai idan Allah bai yi za’a haifi cikin ba, amma idan akwai kaddaran haifar cikin sai dai a rungumi kaddara a rike hannu bibbiyu, ni hakan ma be dameni ba yanzu ma fita zanyi wani na waje yana jirana, kuma kila bazan samu dawowa yau ba dan haka ku rufe kofar gida idan dare ya yi idan har na samu dawo wa kuma zan kiraki a waya” ta fad’a tana nuni da _Mama_ baki sake muke kallon ikon Allah, _Malam_ kuwa tuni ya sume saboda tashin hankali ga zazza6i ga damuwa, daker aka shawo kansa ya dawo dai-dai nan ya zauna ya yi ta shirgan kuka yana tsinewa _Mama_ da tayi silar lalacewar _Asiya_ acewarsa fa kenan shi sam bai ga nashi laifin ba sai nata.

________________________Babban kasuwa ne dake cikin garin _Bauchi_ , kowa yana sana’arsa cikin kwanciyar hankali ba tare da hayaniya ba, da yawa suna saida kaya ba tare da ha’inci ba ya yin da wasun su suke saida wa cike da ha’inci domin sai ka sayi kayan abinci misali shinkafa ko hatsi kaje gida ka samu duk datti ne ya cika, ko kuma ka sayi tumatur da sauran kayan miya kaje ka samu mafi yawanci ru6a66u ne, shiyasa wasu zasu ga suna samun kudin amma sai su rasa ina yake karewa saboda babu albarka a tare da kudin nasu ya yin da wasu kuma duk rashin yawa ko kankantar kudin saboda albarkan dake ciki sai ya wadace su yadda suke so.

+

Wasu shagunan kansu ne wasu kuma shagunan haya ne, wasu manyan shaguna ke garesu wasu kuma k’ananan shaguna, wasu na yar rumfa kawai suke dashi yayin da wasu ko yar rumfar ma basu da shi, wasu na sayarda kayan abinci, wasu kayan sawa, wasu kayan aikin gona, wasu kuma kayan kwalliya da dai sauransu, a ya yin da wasu abincin a dafe ma suke saya dan sanyawa bakin salati musanman ma’aikatan cikin kasuwan wadanda basa samun wanda zai aika musu daga gidajen su, da yawa sun fito aiki tare da tunatarwa daga matayensu akan adalci wanda hakan yake sawa suke saida kaya tsakanin su da Allah, ya yin da dayawa suka fito babu wani tunatarwa wanda zai sa suji suna son yin abu tsakani da Allah, wasu kuma Allah ya tsarkake musu zuciya basa bukatar tunatarwan domin sun san abin da ya dace.

A cikin wad’annan yan kasuwa akwai _Baba K_ wanda ya warke sumul ya fara sayarda shinkafa da wake da miya har da kabeji da salad, da kuma dambun shinkafa, zobo da kunun aya me sanyi wanda dai duk kake so acikin su, babban Rumfa ya kama inda yake yin sana’ar tasa, duk daga gida ake d’ora mishi a babur dinsa da d’ansa ya saya mishi, _Inna Abu_ itace ta bashi wannan shawaran kuma tare suke zuwa duk da cewa yaransa basu so wannan sana’ar tasa ba aganinsu suma sun isa suyi mishi duk wani abin da yake da bukata ba sai ya fita nema ba, amma mai hali dai baya fasawa yace ba zai yiyu ya zauna a gidan mata ba zai fita nema domin ya kama na shi hayan idan so samu ne ma ya saya gidan kansa su koma ciki hakan shine dai-dai ba wai ya zauna a gidan mata da mataccen zuciya ba, _Inna Abu_ data bashi shawaran ita ta samo mishi bashin kudi a hannun kannensa da zummar idan sana’ar ta samu kar6uwa zai mayar musu da kudin su amma sai kuma aka samu sun bar mishi a kyauta ba sai ya biya din ba.

Su _Mama Qudi_ sun karo sabon walakanci dan ba dafawa sukeyi a kyauta ba biyan kudin aiki yakeyi ko wani rana dubu hudu ko wacce dubu d’aya d’aya, shi yake tafiya da kayan abincin _Inna Abu_ kuma da kayan sanyi da kuma kwanuka, yanzu kashi hamsin na damuwarsu ya ragu tunda har suka san mahaifin yaran _Khadeemah_ kuma suka tabbatar ba shegu bane, damuwar daya rage musu shine 6atan _Khadeemah_ amma tunda sarakunanta sun kar6i ragamar sawa a tsaurara bincike sai suka d’an sawa zuciyarsu salama.

Kamar kullun yau ma sun dawo gida a gajiye, sai dai matsala d’aya da aka samu _Inna Abu_ daker take iya takawa ko da aka bincika sai aka ga ashe halin rashin kirki irin nata tayiwa wata Igbo shine tayi mata shegen duka ga _Baba K_ dama ba karfi ne dashi ba sai dai iya cika baki, sa’arsa d’aya sun gama sayarda komai nasu suna shirin dawowa gida shine _Inna Abu_ taji ana hayaniya da matar, tsaban shishshigi sai ta shiga ta goyawa bafulatanan baya wai a dole musulma yar uwarta ita kuma bafulatana data samu mabiya sai ta gudu karshe dai inyamura ta harzuka ta kai iya wuya ta lakad’awa _Inna Abu_ duka abin haushi sai dai jama’a ne suka ceceta tare da nunawa inyamura rashin kyautuwar hakan samari yan zaman banza dake gurin sun so suyiwa inyamuran nan duka ita ma amma dattawa suka hana su domin hakan zai iya zama wani babban matsala tsakanin kirista da musulmai, daker aka saka _Inna Abu_ a napep dan bakinta yaki mutuwa sai da mijin matar yazo ya bada hakuri kuma ya mata fada akan abin da tayi bai dace ba ko ba komai ai ita kasa take da _Inna Abu_ kuma ma ai ta haifi irin ta tunda ga _Baba K_ nan misali.

STORY CONTINUES BELOW

Su _Inna Suwaiba_ sun samu abin labari haka suka maida zancen abin dariya tare da Allah kara ai alhakinsu ne yake ta bibiyarta, _Baba K_ shuru ya yi ya zauna a can gefe yana kirga kudi, bayan da ya gama yace mata gobe sai ta huta shi kad’ai zai fita abinsa. Sau biyu tana wanka da ruwan zafi dan samun saukin ciwon jikin da yake damunta, karshe dai sai da aka dunduma mata jikin tare da shafa mata mantalita shine ta samu sauki taci abinci ta sha magani ta kwanta barci. Abu d’aya ne ya 6atawa _Baba K_ rai zaginsa da yan kasuwa sukayi tayi akan ya kasa taimakon _Inna Abu_ ya zuba ido anata narkanta kamar kayan wanki sai kace ba uwarsa ba, shi kuma a ganinsa idan har yace zai shiga sai dai a jibgesu tare, tsakani da Allah kuma ita ta nemi maganar har ta sha duka to idan duk aka hadasu aka jibga wa zai taimaka wa wani gurin dawowa gida?…

Karfe sha d’aya kamar kullun suka kammala abincin suka had’a mishi a kula sannan suka had’a mishi kayan sanyin suma a wani guri daban, suna gamawa ya mika musu kudin su, su kuma suka zuba a asusunsu, _Khalil_ ne ya raka shi yau domin kai mishi sauran kayan nashi, yana ajiye mishi ya juya ya koma gida da zummar idan ya gama zai kira shi sai ya dawo ya taya shi kwashewa. Ba laifi an sayi abincin sosai sai dai wadanda sukejin haushinsa na abin da ya faru jiya sune basu kula shi ba, ganin shi zai cutu hakan yasa ya shiga basu hakuri tare da sanar dasu cewan ai yana da aljanu ne wanda basa son hayaniya komai kankantarsa kuma idan da ya shiga da abubuwa duk zasu rikice, ba tare da dogon nazari ba suka yarda da shi suka fara tausaya mishi, karshe dai duka abincin ya kare aka daina ganin laifinsa sai ma addua tare da fatan Allah ya bashi lafiya ya raba shi da mugayen aljanun dake tare dashi.

Haka ya dawo gida cikin fara’a yanata wage baki duk yadda mutanen gidan suka so suji meke faruwa kin fada ya yi, sai a lokacin _Khalil_ dake biye dashi yace “Allah sarki _Khadeemah_ da ace tana nan data sanar kana abin da yake faruwa” nan kuma aka koma jimamin rashinta wanda hakan ya yi sanadin kukan _Mama Qudi_ shi kuma _Baba K_ ya fallasa kansa ya shiga basu labarin abin da ya yi tare da cewa tabbas da ace tana nan data fayyace musu komai ba tare da ya yi magana ba. _Inna Abu_ kuwa jiki yaki dadi dama ga tsufa ga kuma an sha duka abin sai ya had’e mata goma da ashirin sai tsinewa inyamura takeyi kuma tace ba zata sake zuwa kasuwan ba ya isa haka.

Ko da yaranta suka zo sam sam basuji dadin abin da ya faru ba, kuma sunji haushin _Baba K_ da yaki taimaka mata ya bari aka jibge ta, hakan yasa sukace zasu tafi da ita kauye su aganinsu sunyi gwaninta ai kuwa ta hayayyako musu tace ba inda zataje tana nan a gidan _Baba K_ har sai ya yi kudi suji dadinsu tare duk ne bakin ciki sai dai ya mutu amma tana cikin birni ita da kauye sai dai ziyara ai wuce nan. Duk mamaki ta basu da irin kalmomin data jefe su dashi tana nuna cewa su din matsiyata ne _Baba K_ ke da k’ashin arziki tunda ga shi tun ba’aje ko ina ba har ya fara tara yan kudadensa, sosai ta 6ata musu rai amma babu wanda ya tanka saboda matsayinta na mahaifiyarsu, rufin asiri dai suna dashi dai-dai gwargwado babu me nuna su da yatsa yace basa neman na kai kuma sunfi karfin bukatunsu na yau da kullun babu ne kukan babu a cikin ahalin su kuma ko banza arzikin da take takama zaiyin da arzikinsu ya samu tunda su suka bashi jari, kafin nan kuma duk wani abin da ya jaji6o a gurin su yake samun na rufin asiri dan haka bai isa ya nuna musu komai ba, tunda har ya kasa komawa ga Allah daman tuban muzuru ya yi daga shi har _Inna Abun_ babu inda zasuje ko sunje zasu kara durkushewa ne tunda babu Allah a ran su burinsu kawai abin duniya basa tunanin kowa balle su gode wa wanda ya musu rana, ko da yake duniya ce ta ishesu wando da riga har da zanin daurawa.

Sosai yan gidan sukaji kunyan abin da _Inna Abu_ da _Baba K_ suka musu domin basuyi tsammani ba, tabbas tuban muzuru ne _Inna Suwaiba_ data karo rashin mutunci dama yanzu bata shuru komai akayi sai ta tanka itace ta nuna musu cewa basu kyauta ba, ai ko ba komai sai su duba irin karamci da mutuncin da suka musu ko wani wahalar su karshe su suke taimaka musu akan fitintinun da suke 6ullowa a garesu amma sai su maida musu da kalamai marasa dadi “a dai juri zuwa rafi domin wata rana tulun zai fashe, kuyi hattara wallahi _Inna_ domin duk mutum me hakuri bai iya zuciya ba, idan nasu fushin ya motso ina tausaya muku, duk cikin matansa nice dolenku tunda nice jininku amma duk da haka wannan karan ba zan ta6a taimakon ku dako sisi ba idan kuka 6allo wani ruwan, balle kuma wanda suke bare aure ya had’a kuma aka samu zuria su din ma zasu iya tafiya su kyaleku domin su din ba dolenku bane idan zalincin ya yi yawa, y’ay’ansu sune dolenku, gwara ku sake tunani wallahi domin sam baku kyauta musu ba ni kaina banji dadi ba balle su da kukayiwa, sai ki rinka abu kamar ba y’ay’anki na cikin ki ba, wallahi _Inna_ ba dan ni jininku bane na san komai dake wakana a cikin dangin mu da sai ince y’ay’an kishiya ne kila shiyasa kike walakanta su, kuma d’a na kowa ne ko da bai kasance naka ba domin baka san wanda zai jikanka ba balle kuma naka ai ya wuce walakanci a gurinka dan kai ka san zafinsa” tana gama zazzaga musu tayi shigewanta d’aki cikin kunan zuciya, sauran matan gidan suma suka mara mata baya, su _Inna Abu_ kuwa duk bakin su ya mutu tabbas sun san basuyi dai dai ba kuma basa kyautawa amma girman kai din fa idan suka ajiye wa zai taya su dauka?…

Sai kallon yadda take karkad’a k’afa yakeyi alamun ta gaji da jira, murmushin gefen baki ya yi sannan ya tashi ya shiga wani d’aki dake cikin falo, mintina goma ya yi sannan ya fito ya na cewa “yace wai ki shiga” bata tsaya 6ata lokaci ba ta shige cikin d’akin cikin zak’uwa, tana zama tace da shi “Hoton nake so da kuma address dinsa dan bana son binciken da zan yi ya d’au lokaci” bud’e drawer mutumin ya yi sannan ya fito da wani envelop “kud’i kafin aiki” fahimtar abin da yake nufi yasa ta yi saurin fito da kud’i masu kauri daga jakarta ta mik’a mishi, sai da ya kirga yaga sun cika dai-dai yadda ya bukata sannan ya mik’a mata ya na cewa “ba’a garin nan mahaifin ki yake ba, a garin _Bauchi_ yake, abin da yasa _Baushe_ yace miki shine mahaifin ki a lokacin saboda yana so ki sake dawowa _Kano_ domin ku gana, sai kuma akayi rashin sa’a kin dawo baya nan, sai dai wani lokacin kenan”.
+
Godiya kawai tayi kafin ta sa envelop din a jaka ta sa kai ta fita, ta kuwa yi sa’a taxi din da tayi shata bai tafi ba yana zaman jiranta, shiga tayi tace mishi su juya su koma _Bauchi_, ba tare da jayayya ba ya juya kan motar zuwa hanyar fita daga cikin garin _Kano_ ya d’auki hanyar _Bauchi_ tunani ne kala-kala a ran ta, envelop din ta bud’e ta fito da hoton dake ciki, wani kyakyawan mutumi ta gani, fari, dogo, siriri, a zuciyarta ji tayi ina ma da dashi tayi kama dan yafi su _Mama_ kyau, ita kuma dasu take kama, juya bayan hoton tayi ta ga an rubuta address d’in gidansa wanda sunan ya mata yanayi da sunan unguwannin talakawa, a can k’asa kuma aka rubuta _Khamisu Kabir Kari K³_ a cikin bracket kuma akasa _Ba.._ wayar ta ne ya katse ta daga karanta sunan…
_________________________
Safa da marwa takeyi a cikin ofis din, shigowar sa ne yasa tayi hanyar kewayen dake cikin ofis din, tana shiga ta kunna famfo ta fashe da kuka me ta6a zuciya, “ya Allah ka yafemin kuskuren da naso aikatawa, lahaula wala kuwwata illa billa, inna lillahi wa inna ilaihi rajiun astagfirullah wa a tubu ilaik” shine abin da take ta maimaitawa a cikin zuciyarta, sai da ya kwankwasa mata k’ofa sannan ta bar kukan ta wanke fuskarta ta fito sai dai taki yarda su had’a ido da shi, kallonta ya tsayayi, karantar yanayin ta yake son ya yi, ya san dai sun fito daga d’akin operation lafiya komai ya tafi dai-dai, tunowa da mace guda d’aya data rasa y’ar da ta haifa a karo na takwas shine yasa ya yi tunanin kila dalilin da yasa hankalinta ya tashi kenan dan yasan _Jidda_ akwai tausayi da shegen d’aukan matsalar kowa ya koma nata.
Kafin ya isa inda take tuni ta fice daga office din, kewayen ya shiga ya yi alwala ya fita zuwa masallaci, ita kuma tana fita ta wuce d’akin da aka ajiye matar, a zaune ta sameta ta zubawa cikin ta ido hawaye na zarya a kumatunta, zama tayi a kusa da ita sannan ta kama hannayenta duka biyu “kin tunatar dani abin da na manta duk da cewa ina da sani a kan hakan amma damuwar rayuwar da nayi a baya shine silar laifin da naso aikatawa sai dai Allah ya nuna ikonsa a kai abin da naso yi din yaki faruwa” shuru tayi na wasu yan mintina kafin ta bawa matar labarin rayuwarta da kuma tsoron da takeji akan sake haihuwar d’a namiji a wannan gidan, sosai matar ta tausaya mata kuma ta nuna mata cewa duk wanda yake cikin yanayinta dole ya kasa tunani dai-dai ya kuma yanke irin hukuncin data yanke wa kanta “ni kin ganni nan kece dai shaida haihuwa takwas nayi biyar da kaina uku kuma aka tsaga ni aka cire su daga cikina duk kuma basu zo da rai ba sai dai ban cire rai daga rahamar ubangiji ba balle inyi tunanin kila daina haihuwa shine maslaha a gareni saboda na san ko ba jima ko ba dade da yardan ubangijina zanga me tsawon rayuwa acikin su. Kuma ina fatan Allah yasa wadanda na rasa su zama alkairi a rayuwarta, idan zan fada miki wani abu ki yarda to ni da kike gani uwar mijina ce silar rashin y’ay’ana domin a rayuwarta bata son haihu wata da danta, sai dai kuma Allah yana bani haihuwar amma burinta na cika saboda basa zuwa da rai, sai dai na barta da Allah domin shine me sakayya, kuma ya sakamin din domin y’ay’an ta mata biyu duk basa haihuwa sannan su na can suna shan wahala a gidan mazajensu kuma ko wacce da muguwar kishiya Allah ya hadata, ko a haka Allah ya barsu ni kan ya sakamin tunda har dasu ake k’ina da k’in y’ayana agidan. A Labarin rayuwarki na fahimci ke mutuniyar kirki ce kuma ta kwarai wanda a halin yanzu ajizanci irin na dan adam yasa kika so tafka kuskeren zubar da cikin jikinki saboda tsoron kar ki rasa abinda yake cikin ki ta silar wata shine ya sa kikayi hakan sai dai laifinki daya, da kika manta cewa duk da ita ce silar rasa su amma Allah shine yake kar6an rayuwar dan Adam, dama Allah yayi ba rayayyu bane kuma ta silarta zaki rasa su kinsan yawanci silar shine abin da yake 6atawa ko gyarawa, na kuma ji dadi da kikayi sauri dawowa hayyacinki kika fahimci kinyi ba dai-dai ba Allah ya kara ganar damu gaskiya ya shiga tsakanin mu da makiyan mu” amin suka amsa ita da kanwar matar dake gurin, sai da ta kar6i lambar matan da address dinta wannan ta musu sallama ta koma office dinta ranta fes ko ba komai ta taimaketa data tuna mata abin da ta so mantawa, shafa cikin ta tayi ” _Sufyan_ baka da dama, ko yara nawa kake son tarawa ? Allah dai ya yi musu albarka tunda kana da halin ciyar dasu da kuma ilimantar dasu an wuce waje” Ta fada a zuciyarta tana murmushi…
STORY CONTINUES BELOW
Shigowa ya yi ya same ta tana ta murmushi “wai ni yau juju ne dake ko kuma menene matsalar, jiya da dare duk hankalinki ba’a jikinki yake ba, yau kuma fuskarki fayau  kamar ba wani abu, dazu kuma na ga kamar dai kinyi kuka yanzu kuma na samu kina murmushi?” Cire hannunta tayi daga cikin nata dan bata son na ya san tana da ciki, duk da cewa kwana biyunnan ya isheta da zancen lailai fa ciki take dashi ita kuma tace sam bata dashi har yace sai anyi gwaji tayi mishi bori shine ya barta ba dan ya hakura ba dan ta san zai sake mata wani wayon “kawai dai yanayi ne ba wani abu ba, ka gama ne mu wuce ko kuma baka gama ba?” Key din motar ya d’auka yana cewa “na gama ina ga anjima ma ba zamu dawo ba kawai sai zuwa gobe, muje yunwa nakeji ma wallahi” tattara musu kayansu tayi wanda zasu bari a ofis ta ajiye su a ma’adanar su wanda zasu tafi dashi kuma ta d’auka suka fita, sai da suka tsaya a wani gurin cin abinci sukayi take away dan yau sun fito da wuri bata samu tayi girki ba duk da ta san kila _Bibalo_ ta riga ta taimaka mata amma jiki da jini kar bata samu damar yi ba, dan ma yaran suna makaranta sai uku suke dawowa gida. Ai kuwa kamar ta sani sunyi take away din a dai-dai dan sun samu _Bibalo_ tsautsayi yasa santsi ya kwashe ta har tayi targad’e a k’afarta shine _Hajja_ ta kira aka gyara mata _Amir_ ma yana 6angaren _Hajjan_ dan kar ya dame ta, ita kuma sun samu tana barci wahala.
_Hanifa_ bata iso _Bauchi_ da wuri ba hakan yasa ta wuce gida direct akan sai washe gari zata bazama neman mahaifin ta, ko da ta isa gida a falo ta same su suna hira kuma tsaban rashin sanin darajan y’ay’a da rashin sanin cewon kai ko tambayar daga ina take basuyi ba, zunubi kan zunubi yar zina kuma an kasa bata tarbiyyan data dace sai garari takeyi a gari tana abin da ta ga dama babu me kwa6arta, gari ya gari take yawo babu me nuna mata rashin dacewar hakan an barta kara zube tayi abin da take so, sai dai taji iyaye na gari na yiwa y’ay’ansu fad’a akan gaskiya amma ita babu wanda ya tsaya mata, ko kallon su batayi ba tayi wucewarta zuwa d’aki sai da tayi wanka sannan ta sauko ta bada umarnin a dafa mata indomie, kwai da kuma ginger drink, fita tayi zuwa 6angaren _Jidda_ anan take jin labarin abin da ya samu _Bibalo_ addua ta rinka yi Allah yasa kafar ta ru6e, har ta gama zamanta bata ga _Sufyan_ ba kasa hakuri tayi cikin dabara ta fara tambayar yaran sannan ta tambayi shi, shine  _Jidda_ take fad’a mata yana 6angaren _Bibalo_ yaje ya sake duba ko ta tashi, yaran kuma suna 6angaren _Hajja_ basu dad’e da dawowa daga makaranta ba. Cike da bakin ciki tayi wa _Jidda_ sallama ta tafi itama _Jidda_ ta bi bayan mijinta dan duba jikin abokiyar zamanta.
Washe gari da safe _Hanifa_ ta shirya taje gurin _Dr Nasir_ dan tare zasuje, tana nuna mishi address din ya yi dariyar muguntan daya saba “ai unguwar talakawa ne wannan lailai _Mama_ bata kyauta miki ba, ni so nake ma in san yadda akayi tayi cikin harta haifeki kuma da aurenta, sannan suka juye zance da cewa d’iyar yar uwar tace ke din, gaskiya sun iya drama bari dai muje mu same shi ko zamuji cikekken labari daga gurinsa, babban abin da ya d’aure min kai shine me _Mama_ zatayi da talaka irin wannan har ma da y’a a tsakaninsu?” sai a lokacin _Hanifa_ tayi magana “nima dai shine abin da har yanzu na kasa fahimta menene had’inta da talaka kamar _babana_ dan daganin sunan anguwar an san na talakawa ne” tana gama rufe baki suna isa anguwar, a dai-dai wani majalisa suka tsaya, sauke glass din motar ya yi ya musu sallama sannan ya nuna musu hoton kafin ya tambaya ko sun sanshi? D’aya daga cikin su ne yace musu ya san shi amma mota ba zai shiga lungun gidan ba sai dai idan zasuyi parking a gurin masallaci suje su dawo. Hakan kuwa sukayi bayan sunyi parking ya raka su har kofar gidan, godiya suka mishi tare da bashi dubu daya sannan ya tafi shima yana musu godiya, yaro suka aikata dan ya musu sallama dame gidan, bai dade ba ya fito yace wai me gidan bayanan ya tafi gurin sana’arsa.
Har zasu tafi wani yaro ya fito bayan sun gaisa yake tambayar ko sune suke neman me gidan sukace eh yace idan dai sauri suke yi zai iya kai su idan kuma basu sauri sai su dawo da yamma zuwa lokacin ya dawo gida, cikin sauri _Hanifa_ tace dan Allah ya kai su, ba tare da 6ata lokaci ba yabi bayansu. Basu wani d’au lokaci ba suka isa, a gurin da ake ajiye mota suka ajiye nasu bayan sun biya kudi, tafiya sukayi me d’an nisa kafin suka isa kwanar inda yake sana’ar nasa, tun daga nesa _Hanifa_ ta gane shi sai dai d’an tsufa da ya yi amma haskensa yana nan yadda yake a hoto, _Dr Nasir_ kuwa sai kunshe dariyarsa yakeyi dan shima ya gane mutumin daga nesa, duniya kenan wai wannan mutumin shine mahaifin _Hanifa_? Abin kunya wai abinci ma yake saidawa a cikin kasuwa, tun kafin su isa _Hanifa_ tayi ta yiwa su _Mama_ Allah ya isa da suka rasa wanda zasuyi shashanci da shi sai wannan dan ita tama rasa wacece uwarta a cikin su.
Yaron daya kawo su kuma yana nuna musu shi yace musu zai wuce sauri yakeyi akwai inda zashi, godiya suka mishi shima suka bashi naira dubu kafin suka k’arasa gurin da mutumin yake sai faman raba abinci yakeyi yasha manyan kaya ya daura babban riga a kugu sai hankici a kai kamar wani dan daudu yasa waka a waya sai taka rawa yakeyi yana mik’a abinci ana bashi kudi yana cokewa a hulla, sallama suka mishi yana amsawa ya d’ago dan ganin ko waye ido hudu sukayi da yarinyar dake tsaye tana kallonsa cike da tashin hankali ya nuna ta yana cewa ” _Lami_? Kai ba dai _Lami_ bace sai dai yarta, yarinya meya kawo ki inda nake” ya fad’a yana zare ido alamun rashin gaskiya duk kan sa ya d’aure baya son abin da yake tunani ya zama gaskiya…

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE