DEEMAH CHAPTER 18 KARSHE BY ZAHRATEEY

DEEMAH CHAPTER 18 KARSHE BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan watanni biyu da tarewata akayi bikin _Ummulu_ da _Yaro_, _Asiya_ ta haihu d’an ba rai kuma mahaifarta ta lalace sakamakon sha maganin zubarda ciki data yi tayi, sosai tayi kukan bakin ciki tayi nadamar rayuwar data za6awa kanta, abin har yaso ya ta6a kwakwalwarta, daker aka samu ta dawo dai-dai.

+

A 6angarensu _Mama_ taro _Daddy_ ya had’a na gaggawa, inda ya sanar da kowa halin da ake ciki na cewan _Hanifa_ diyar _Mama_ ce tare da gabatar shaidu kwarara na CCTV camera da yake 6angarensu, duk wani makirci nasu dana _Hanifa_ yau dai asiri ya tonu, ana cikin haka _Baba K_ da mutanen gidan mu suka zo sosai hankalin _Mama_ ya tashi, anan yake sanar da cewa ai _Hanifa_ diyarsa ce nan ya bada labarin komai kamar yadda ya sanar da _Hanifan_ kuma yace yazo ya nemi gafaran _Daddy_ ne akan abin da ya faru, yau son kudinsa ya ja mishi kunyar idon siriki haka nima ya sani cikin tashin hankali, kasancewar abin ya faru ne ba tare da _Baba K_ ya san _Mama_ tana da aure ba hakan yasa _Daddy_ ya yafe mishi, a ranar kuma ya gabatar da yaran _Jidda_ asu _Mama_, bayan an gama taro _Daddy_ ya kori _Mama_ daga gidan shi ita kuma _Hanifa_ su _Inna Suwaiba_ suka tasa kyeyarta zuwa gidan mu.

Bayan shekaru goma…

Abubuwa da yawa sun faru, ciki har da mutuwar _Hanifa_ sanadin cuta me karya garkuwar jiki, _Mama_ kuma ta kamu da cutar shanyewar 6ari guda sanadin mutuwar  _Anty Mansura_.

_Ummulu_ tayi min takwara a farkon haihuwarta, yanzu haka yaranta uku, maza biyu mace daya, _Asiya_ tana gidan _Alhaji me gwanjo_ tana shan walakanci a gurin iyalansa da shi kan shi domin ita kadai ce bataje mishi da martabarta na diya mace ba, kullun sai tayi kuka da dana sani wanda bashi da amfani.

Yanzu haka yarana shida, bayan _Triple_ na haifi yan biyu namiji da mace, macen nasa sunan _Jidda_ abin kamar hadin baki domin a rana daya muka haihu da _Bibalo_ itama yan biyu kace dana miji macen tasa _Jidda_, mazan kuma daya sunan _Baba K_ daya sunan _Daddy_  Jidda kuma tun haihuwarta na karshe bata sake haihuwa ba, inda ta samu yan uku mata biyu namiji daya namijin yaci sunan _Daddy_ matan kuma tayi mana takwara.

A yanzu haka _Bibalo_ ta kammala karatunta inda _Sufyan_ ya gina mata babban makaranta, ni kuma ya gina min babban ma’aikata wanda nayi rejistarsa na dauki ma’aikata muna aikin kare hakkin mutane marasa galihu, kuma a cikin shekarunnan akayi auren yaran mu su uku duk yan dakin _Jidda_ da babban yaya _Anas_ da _Anisa_ da _Afifa_ muma mun kusa zama kakanni.

Sannan _Sufyan_ ya sayawa _Baba K_ gida madaidaici inda suke zaune a yanzu shi da matansa domin samarin gidan duk sunyi aure, haka iyayen _Bibalo_ wato _Baffa_ suma ya gyara musu gidansu an mayar dashi na zamani sannan ya gina musu babban masallaci a cikin garin.

_Kisma_ ta haihu yara hudu, maza biyu mata biyu, dame sunan _Mama Qudi_ dame sunan maman mijinta, sai me sunan mahaifin mijinta da kuma me sunan _Baba K.

Yanzu _Baba K_ ya koma na Allah domin yana kokarin kyautatawa matansa, haka suma yan uwan sa ya jawo su a jiki tare da neman yafiyarsu. Bayan sun samu fahintar juna _Inna Abu_ tace ga garinku.

Kwanciyar hankali da fahimtar juna ke wanzuwa a cikin ahalin mu, rayuwar mu tazo a yadda bamuyi tsammani ba, mun samu nasarori masu tarin yawa wanda bamuyi tunanin samu ba. A kullun idan na tuna rayuwata na baya sai inga kamar a mafarki hakan ya faru.

Bani da abin da zancewa abokan zama na da miji na _Sufyan_ sai Allah ya saka musu da alkairi ya kuma basu farin ciki kamar yadda suka bani, ya kuma kara mana so da kaunar junan mu. Samun miji kamar _Sufyan_ da mace kamar _Jidda_ abu ne me matukar wahala amma idan aka had’a da rokon Allah sai a samu fiyema da hakan. Rayuwa mukeyi me tsafta cike da fahimtar junan mu, akwai kishi amma kishi irin na masu hankali mukeyi ba irin na jahilan mata ba…

*Alhamdulillah Tammat Billah*😍

Laifin dadi karewa Alhamdulillah ala kulli halin duk abunda yayi farko yanada karshe abunda muka fada daidai Allah ya hadamu a ladan kuskuren da mukayi kuma Allah ya yafemana baki d’aya.

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE