DEEMAH CHAPTER 5 BY ZAHRATEEY
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sosai yan gidan mu suka shiga tashin hankali ba dare ba rana suna aikin nema na, har report suka kai a police station amma babu wani ci gaba da aka samu, _Baba K_ kuma har zuwa yanzu babu abin da yace musu, ko da ya bani labarin halin da suke ciki sosai na shiga damuwa amma kuma naji dadi da suka nuja damuwarsu a kaina, ashe dai suna sona sosai kuma sun damu dani, babban abin farin cikin shine yau zasu gan ni zuciyarsu ya samu sukuni nima nawa ya samu tare kuma da kyakyawar labari wanda na san zai sanyaya zukatansu.
+
Muna isa garin _Bauchi_ naji wani irin natsuwa da kwanciyar hankali a tare dani, duk da cewa akwai wani yar damuwa dake makale da zuciya ta, “ina zan ganshi?” Nayi wa kai na tambayar da bani da amsa, saurin goge ruwan hawayen daya zubomin nayi sannan na mayar da kaina jikin window har muka isa tasha, bayan mun sauka na biya mana kudin motar sannan muka tari napep zuwa gida.
Anguwar shuru kamar ko yaushe ba kamar wanda muka bari ba a da, dan wancan anguwar cike yake da yan sa ido da yan zaman kashe wando, sa6anin wannan da zai yi wahala kagansu a waje sun buga taro kamar gurin zaman makoki. mikawa me napep din kudinsa nayi sannan muka taka zuwa kofar gida, _Baba K_ ne ya fara shiga sannan nabi shi a baya, suna zazzaune a tsakar gidan wasu sun zabga tagumi wasu kuma suna d’an hira jefi jefi, ” _Yaya Khadeemah_!” _Kisma_ ta fad’a daga bakin kofar falon kayan abinci data dauko suka zube a gurin baki daya, sake da baki kowa yake kallon mu, ita kuma ta rugo da gudu ta rungume ni tana kuka.
Kasa daurewa nayi nima na fashe da kuka, bama mu kadai ba kanne na da yayyina mata duk sai da sukayi kukan farin ciki, sai da komai ya lafa sannan _Baba K_ ya sanar dasu duk abin da ya faru, a lokacin ne har mazan sai da sukayi kwallar tausayina, basu ta6a tunanin zan aikata hakan ba, nan fa kowa ya shiga tarairaya ta da nuna min kauna, mutane sai zuwa sukeyi taya yan gidan mu murna, yan uwa da abokan arziki duk sun zo, wadanda suka san kan maganar su aka sanar da dalilin 6atan nawa, wanda kuma basu sani ba aka barsu da cewa yan garkuwa da mutane ne suka sace ni, dayawa sunyi farin cikin dawowa ta, yayin da wasu suke bakin cikin dawowar tawa har suka kasa 6oyewa, _Inna Abu_ ko da taji na dawo bata zo ba sai bayan kusan wata guda sannan ta shigo mana.
Ina zaune a kujeran roba a tsakar gida na gama yiwa _Kisma_ kitso kenan zan tashi naji wani irin jiri kaman zan kife a k’asa, da sauri na koma na zauna ina rike kaina, a yan kwana kinnan idan nayi zama sosai ko nayi tafiya me nisa ko aiki me yawa sai in farajin jiri yana d’iba na, ga kuma yawan barci da yake damuna ko da a wajen aiki ne kawai dai dauriya nakeyi na rasa menene matsalar tawa.
Sallamar _Inna Abu_ ne yasa na d’aga kai na kalli k’ofar zauren, tana shigowa taja tsaki a lokacin matan gidan mu duk suka fito “an dawo daga yawon ta zubar din kenan? Sai dai ki raina wa iyayenki amma banda ni _Zainabu_ kin tafi yawon gantali za’a fake da kinje kawo karshen mugaye! Har me zaki iya da zaki tunkare su? Naji wannan, shi kuma haske da cikan da naga kinayi menene ya faru ko kin chanja mai ne ko kuma anyi miki 6arin madara a inda kika je din? Ai dama ba zaki samu amsar bani ba, yar iska, yar gaba da fatiya kede anyi asaran haihuwa anan” wani irin zuciya ne ya ciyoni nayi kan _Inna Abu_ ban sani ba ko me ya faru amma dai ganina nayi a d’akin asibiti an jona min alluran drip, _Inna Abu_ kuma a d’aya gadon ta sha bandeji a fuska irin goggoron _Baba K_ na rannan, duk jikinta ya kunkunbura ta ko ina, ga kafarta d’aya da hannu duk a d’aure alamun karaya, kenan duka na mata na musanman? Lailai nayi aika-aika.
Satin mu guda a cikin asibitin ana kulawa da mu, abu d’aya ne ya d’auremin kai, yadda naga wasu nayi min kallon banza, hatta _Mama Qudi_ sai dai ta zo ta duba _Inna Abu_ wacce babu bakin magana sai ido, ni kuma _Inna Suwaiba_ ce kawai da _Kisma_ suke bani kulawa sosai da kuma kannena na gurin uwa, sauran duk sun maidani ba abakin komai ba, ko kallona na lura basa son yi, idan _Inna Suwaiba_ ta tsawatar nema ake min sannu.
A yau aka sallame mu, muna isa gida muka samu duk yan gidan mu a tsakar gida sunyi cirko-cirko, ga kayana a zube a k’asa duk an had’e min a akwati da Ghana must go, da gani dai an san komai nawa aka had’a, kallonsu nayi d’aya bayan d’aya _Inna Abu_ ce kawai bata gurin an shiga da ita cikin gida “ga kayanki nan sai ki nemi gurin zuwa domin ba za’a haifamin d’an gaba da fatiya a cikin gida na ba” _Baba K_ ya fad’a yana muzurai, ni duk bangane me hakan yake nufi ba duk da cewa hausa ya yi min, kawai kunnena ya kasa d’aukar maganar ne, sai da _Mama Qudi_ tace “Allah ya isa tsakanina dake _Khadeemah_ kin cuceni kin cuci zuri’a ta, kin shafa mana bakin fenti, kin tozarta mu, kin yaye mana rigar mutunci, yanzu abin da zaki saka min dashi kenan, ki yo ciki a waje, Cikin shege _Khadeemah_? Ashe gaskiyar _Inna Abu_ da take cewa gantali kike zuwa tunda kika ki aure, kije na cireki a cikin yarana ki nemi wata uwar” tana gama fad’a tayi gaba kamar zata tashi sama dan bacin rai, kallon kowa na cigaba dayi, wasu namin kallon tsana yayin da wasu kemin kallon tausayi.
Kasa ta6uka komai nayi kawai na sulale a k’asa, ciki wani irin ciki kuma ana zaune kalau, ni sam na manta abin da ya faru tsakanina da wannan bawan Allah na gidan Felicia, gaba daya kaina ya d’aure, zancen _Mama Qudi_ yafi komai warwaremin lissafi, _Baba K_ kuwa tunda ya gama furta nashi kalaman yayi waje kuma ya jaddada musu cewa duk wacce ta barni na zauna a gidan a bakin auren ta, yan uwana kuma duk wanda ya tanka min ya cire shi a cikin y’ay’ansa kuma ba zai yafe mishi ba, sosai kalaman suka girgiza su shiyasa babu wanda yayi gigin ta6ani sai _Kisma_.
Ina zaune a gurin ta shiga d’aki ta had’o kayanta tace min in tashi mu tafi koma ina ne mu bar musu gidan su dafa su cinye, ai batasan duk basu da imani da tausayi ba sai yau, ashe duk basu yarda da kaddara ba, yanzu basa tunanin kila a gurin ceto nasu rayuwar ne nawa ya fada halaka? Kawai zasu yanke hukuncin korata, haka tayi ta masifa ina binta da idanu, karshe bayan ta taro me napep ta kwashe mana kayan mu ta kai ciki sannan tazo ta taimakamin na tashi, muna fita wasu suka fashe da kuka musanman matan da suke da rauni domin tabbas maganar _Kisma_ ya ta6a zukatan su har sunji cewa basu kyauta min ba, kalaman _Baba K_ ne ya lalata komai duk ya tsorata su.
Muna shiga napep sai ga _Inna Suwaiba_ itama da kayanta, ta saka kayan a gefe sannan ta shiga duk da cewa bata san inda zamuje ba, tasha _Kisma_ tace ya kaimu, muna zuwa tace motar _Kano_ babu 6ata lokaci muka samu muka shiga kowa da abin da yake sakawa a ransa, ni sai a lokacin na tuna da waye uban abin da yake cikina, tabbas Felicia ta cuce ni cuta mafi muni, kuma duk ta sanadin kar a cutar da mahaifiyata da mahaifina na yarda amma sai ga shi sune sukayi watsi dani suka juya min baya, anya zan ta6a yafe musu kuwa? Na tambayi kaina ina share hawaye.
Muna isa kano ta sake cewa motar sokoto mu dai kawai da ido muke bin ta babu wanda yace mata wani abun, kafin mu shiga mota haka nayi ta amai saboda tashin zuciya, na rasa ma inda zansa rayuwa ta, na dade ina yi kafin ya lafa, _Inna Suwaiba_ nata jeromin sannu, sai da na gama ta bani ruwa na wanke baki na sannan _Kisma_ ta rufe gurin da k’asa, mota muka shiga nida _Inna Suwaiba_ ita kuma _Kisma_ ta tsaya ta sayo doya da kwai wanda ta lura tun zuwan mu idona na kai, bayan ta dawo ta bawa _Inna Suwaiba_ leda d’aya da maltina a cikin da tsire sai ta ajiye mana d’aya muka fara ci nida ita, ni duk doyan yafi komai armashi a gurina.
Mun isa sokoto lafiya cikin koshin lafiya, sai dai ni duk nafisu gajiya dan ba k’aramin zama muka sha ba, ga shi ni yanzu bana son doguwar zama ko tafiya. napep _Kisma_ ta tare mana zuwa GRA, sai da muka isa gidan na tuna cewa akwai kanwar mahaifiyar _Mama Qudi_ a garin, aiki ya kai mijinta sokoto dan shima d’an lagos ne bayerabe, kuma Allah bai basu haihuwa ba har zuwa yanzu.
+
_Inna Suwaiba_ dama bata damu ba, ita dai ba zata iya bari mu tafi wata uwa duniya mu biyu ba a matsayin mu na mata, a ganinta bai dace iyayen mu su yanke wannan irin hukuncin ba, shiyasa ta biyo mu, kuma tunda ta ga munyi hanyar sokoto ta gane inda muka nufa, nice dai na manta cewa muna da kaka a garin saboda tashin hankalin daya riskeni.
Bayan _Kisma_ ta biya me napep din suka d’au kayan mu ita da _Inna Suwaiba_ naso in d’auka amma ta hanani wai jiki na ba kwari, ni dai kawai jin ta nakeyi, ni mamaki ma abin yake bani, wai mutum ke kwance a mara ta, wannan wani irin sarkakiya ce, na kasa auruwa amma gani da ciki, meyasa kaddara tayi min haka? Ga shi yanzu dalilin haka na bar cikin dangina, duk da cewa a cikin wasu dangin nawa zan zauna amma da ace a gaban mahaifiya ta nake da nafi samun natsuwa da sukuni, duk da cewa _Mama Qudi_ bata ta6a nuna min soyayya ba amma banyi tunanin cewa zatayi watsi dani ba, tabbas abin da ciwo amma koran ba shi da amfani, domin bakasan halin da yaro zai shiga ba.
Bud’e k’ofar da akayi ne ya dawo dani daga tunanin dana tafi, wata mata ce kusan sa’ar babban yayan mu, gaishe da _Inna Suwaiba_ tayi, _Kisma_ ta gaisheta ni kuma nace mata sannu, da mamaki ta kalleni sai dai bata ce komai ba, _Kisma_ ce tayi mata bayanin ko mu su waye, tana jin haka ta bamu hanya muka shiga, a cikin falon muka zauna ita kuma ta shiga kiran _Alaja Tahira_, ni kam barci ne ya fara kwasa na, ba tare da jinkiri ba na gyara kwanciyata da kyau barci yayi awun gaba dani.
Duk suna zaune _Alaja Tahira_ ta fito wacce suke kusan sa’anni da _Inna Suwaiba_ domin idan har d’aya ta girmi d’aya toh sai dai da watanni. _Alaja Tahira_ ita ce auta a gidan su kakarmu kuma mijinta me kud’i ne sosai kuma d’an sarauta, sai dai Allah bai azurta su da samun haihuwa ba sannan mijin bai ta6a gwada kara aure ba har zuwa yanzu da suka tsufa. Tana sauko wa daga matakalan benin ta kwalawa me aikinta kira “Ya zaki bar baki babu kayan motsa baki? Maza kije ki kawo musu abin ta6awa kafin suyi wanka su huta suci abinci” ta fad’a tana zama a kusa da _Inna Suwaiba_ fuskarta da alamun murmushi da nuna jin dadin ganin mu, duk da cewa hankalinta ba’a kwance yake ba ganin mu uku kachal kuma tafiya ba sanarwa amma ba tace komai ba har suka gama gaisawa suka haura sama inda ta nuna musu d’akuna biyu d’aya a _Inna Suwaiba_ sai d’aya nida _Kisma_ tace su shiga suyi wanka su huta, nikam dama ba’a tasheni ba dan _Inna Suwaiba_ yace a barni kawai barcin gajiya ne.
STORY CONTINUES BELOW
Sai da suka gama komai har sukayi salla sukaci abinci sannan na tashi, _Kisma_ na gani tana danna waya “kin tashi?” Ta tambaya, na bata amsa ta hanyar d’aga kaina, bayan wasu mintina tace in tashi muje ciki. Wanka na farayi sannan nayi salla, naci abinci kad’an dan saboda yanda nakejin tashin zuciya daganan na sake kwanciya wani barcin ya d’aukeni. Bani na farka ba sai wajen isha’i, ina tashi na sake wanka dan jikina duk ciwo kamar anyimin duka, bayan na fito nayi salla sannan na sauka k’asa dan duba _Alaja Tahira_.
A zaune na same su a falon sun bararraje sai hira sukeyi dama yaya lafiyar kura balle tayi hauka, duk sammakal da _Inna Suwaiba_ da _Alaja Tahira_ shegen surutu ne a cikin su, idan suka samu hira har sai kun gaji da sauraro abin harda maimaici kamar TV. Zama nayi a gefen _Alaji Tahira_ duk jikina a sanyaye saboda yanda ta tsuramin ido tun farkon fitowa ta har na k’araso inda suke, kwarjinin matar yasa na gaisheta ba shiri, amsawa tayi cike da kulawa “Qudirat bata kyauta mana ba jikata, kuma sai sunyi nadama ba kad’an ba, wasu suna neman yara basu samu ba su sun samu amma sun kasa daukan kaddaran su, a gaskiya banji dadi ba sam-sam raina ya 6aci, tabbas _Suwaiba_ mutuniyar kwarai ce kuma uwa ta gari wanda ba zamu ta6a mantawa da alkairinta a garemu ba domin uwa ta gari ce kawai zatayi abin da tayi muku, Allah kuma ya saka mata da alkairi ya shirya mata zuria” duk muka amsa da “amin” sosai girma da matsayin _Inna Suwaiba_ ya k’aru a zuciyata babu abin da nakeyi a face adduar Allah ya bata gidan aljanna akan wannan abin da tayi mana.
Zaman gidan _Alaja Tahira_ zama ne me dadi, abinci sai wanda ka za6a ga shi sam ta hana mu aikin komai da sunan tana da me aiki, duk da cewa ba muji dadin zama a hakan ba amma ya muka iya tunda gidan hutu ne. Haka mijinta shima babu ruwan shi, mutum ne me barkwanci da son jama’a, kusan duk sanda ya samu lokaci ya kan fita damu mu zaga gari. Komai kuma nace ina so ko sha’awar ci zan samu cikin kankanin lokaci.
A yanzu ciki na yana wata na biyar, mu kuma watan mu uku a gidan _Alaja Tahira_ sati guda da zuwan mu ta kaini asibiti aka duba lafiyata dana abin da ke ciki na, sai da taji cewa babu wani matsala sannan hankalinta ya kwanta. _Kisma_ ma ta koma makaranta suna shirin rubuta ssce.
Cikin riga da zani na shirya zan tafi asibiti gurin awo, _Kisma_ sai masifa takeyi wai nace ta jirani amma naki yin abu da jiki ga shi yanzu zatayi latti, “Washh ciki na wayyo zan mut…” Da sauri ta dakata daga masifan tayi gurina cikin tashin hankali tana yimin sannu, a haka dai har na gama shiryawa ina gimtse dariyar dake cina, dama ni masifar nata ne bana so, yarinya sai zafin ran tsiya abu kadan sai ta hau kamar farashi, tun rasuwan _Harun_ na fara fahimtar wannan sabon yanayin nata amma ban ta6a ce mata uffan ba, sai dai zan mata magana duk randa ta sake domin banga amfanin yawan masifar ba, idan har yabi jikinta shikenan baza ta iya dainawa ba.
Muna fita aka fara sauketa a makaranta sannan muka wuce asibitin, guri dreban ya samu daga nisa yayi zaman jira na kamar dai yanda ya saba a duk sanda muka zo, ni kuma na k’arasa ciki. As usual na samu malamar asibiti tana tsaye yayin da matan suke zaune tana sake wayar musu da kai akan yanda zasu kula da lafiyarsu da kuma na abin da yake cikinsu, abubuwa dai masu mahinmanci wanda wasu matan suke ganin kawai zaman 6ata lokaci ne da surutan banza, sai dai a kullun akwai salon jan hankali da shawarwari masu amfani.
Bayan na dawo na samu su _Inna Suwaiba_ a falo suna cin yalo, agwaluman da na gani a gefe shi yafi jan hankali na, babu 6ata lokaci na shiga kitchen na wanko hannu na sannan na dawo na zauna na fara sha ina lumshe ido, sai da na sha guda shida sannan na koma kan yalon da suka kwad’a da kuli kuli da tumatir da albasa, haka suma naci sai da naji na koshi na hakura, _Alaja Tahira_ tace “yanzu ga abinci amma sai da kika cika ciki da kayan kwad’ayi, to idan kin huta kin farajin yunwa ga chan alalen gwangwanin anyi miki sai kici” ni nama manta da cewa nace ina son alalen gwangwani, ai da tuni shi na fara ci, amma ba damuwa a kula yake ba zai yi sanyi ba, tashi nayi na shiga d’aki nayi wanka, ina fitowa _Kisma_ ta shigo, salla nayi nace mata barci zanyi k’arta tasheni, har zan kwanta kuma tace min “wani suna za’a sawa babyn idan macece?” Ba tare da tunanin komai ba nace “Suwaiba” sai mu rinka kiranta “Ummita” fuske d’auke da murmushi tace “abin da yake raina kenan kuma abin da _Alaja_ tace take so kiyi kenan jiya bayan mun fita”.
_____________________
A 6angarensu _Baba K_ cike da tashin hankali yan uwana suka koma gidajensu, ta wani gefen hankalinsu a d’an kwance saboda _Inna Suwaiba_ tana tare damu amma ta wani gefen suna cikin damuwa domin sam basuji dadin hukuncin da _Baba K_ da _Mama Qudi_ suka yanke ba, tabbas irin haka ba dadi suma sunji rashin jin dadin faruwar lamarin amma kuma _Kisma_ ta tunatar dasu abubuwa da yawa wanda ya sanyaya ga6o6insu kuma sukaji duk haushina da sukeji ya tafi ya koma kan _Baba K_ domin da ace bai koreni ba babu wanda ya isa ya hanani zaman gidan mu ko da kuwa _Mama Qudi_ ce.
Sosai yan uwana suka d’auke k’afa daga zuwa gida suka share iyayen namu, domin sunajin cewa duk laifinsu ne da suka bari muka tafi, ga shi basu san ta inda zasu fara neman mu ba, kuma duk wayoyin mu a kashe yake sun kasa samun ko na mutum daya, sosai matan sukayi kuka har suka gode Allah suka koma adduar Allah ya kare mu kuma yasa muna cikin kwanciyar hankalina duk inda muke, babban fatansu ma Allah ya raba ni lafiya da abin da ke ciki na.
A gida kuma _Ya Kolo_ da _Goggo Fulera_ suma sun d’auki fushi dasu _Baba K_ dan sam yanzu basa kulasu sun fita harkarsu domin basuji dadin abin da suka aikata ba, ko ba komai nima yarsu ce tunda mun hada jini da yaransu, kuma da dai na kowa ne baka san wanda zai jikanka ba, kuma suma hakan befi karfin faruwa akan yaransu ba, kaddarana yana kan kowa sai dai mutum yayi fatan cin jarabawan, dadin su d’aya _Inna Suwaiba_ na tare damu sun san ba zamu tagayyara ba.Rayuwa yana tafiya a yadda Allah ya tsara shi, kuma ko wani rana da irin na shi jarabawar, ko wani bawa da yadda aka tsara mishi rayuwa, wani rayuwar farin ciki har ya koma ga Allah bai san wani abu wai shi bakin ciki ba, haka wani har ya koma ga Allah ba zai ta6a fahimtar menene farin ciki ba, wani kuma da bakin cikin da farin cikin duk ya sansu, kuma duk wadannan yanayin jarabawa ne ga dan adam, sai dai shi me hankali da ilimi shike gane hanyar tsira tare da rungumar komai yadda yazo. Kwanaki sun wuce, satittika sun shige, haka ma watanni sun shud’e, a yanzu ciki na ya shiga watan haihuwarsa, wanda ake saka ran a ko yaushe ubangiji yaso ikonsa to komai zai tabbata babu tsimi babu dabara.
+
Sosai _Inna Suwaiba_ da _Alaja Tahira_ suke bani kulawa na musanman, haka shima me gidan ba’a barshi a baya ba, ko yaushe cikin kwantarmin da hankali sukeyi akan Allah zai kawo min da sauki, duk wani kayan buk’ata sun sayo masu yawan gaske, kayan sakawa unisex suka jibgo mana haka nima sun dinka min sabbin zannuwa masu tsada, kowa a gidan tarairayata yakeyi duk da cewa sun san ta hanyar da aka samu cikin, ni dai babu abin da zan iya saka musu da shi baki dayansu sai addua da neman dacewa duniya da lahira.
Abu d’aya me yake tsayamin a rai kuma yake sanyani damuwa wato rashin mahaifiyata alhali tana raye tana kuma da yadda zatayi domin taimakona amma ta watsar da lamarina, wacce ban ta6a d’auka a uwar da zata jikai na ta bani kulawa ba ita ce take tare dani a wannan yanayin. Ina kwance a gado kamar ko yaushe ina aikin tunani, wani irin ciwo ne ya taso min wanda ban ta6a jin irinsa ba kai ni ban ta6a sanin akwai irin wannan azabar a duniyar ba, salati na farayi a raina ina tunanin karshena yazo shikenan ban nemi gafaran iyaye na ba, shigowar _Kisma_ ne yasa nayi wani irin ihu wanda ya janyo hankalin mutanen gidan, cikin sauri suka taimakamin muka shirya zuwa asibiti.
Ko da muka isa cikin gaggawa aka kar6emu dan na riga da nafara labour, tashin hankali da ba’a sa mishi rana ni dai ina duniyar ne kawai sai dai nafi tunanin dama ace lahiran na tafi kawai dan sai wanda ya ta6a zai fahimci azabar da nake ciki, kuka nakeyi ina salati ina adduo’in da duk yazo bakina musaman wanda _Inna Suwaiba_ ta koyar dani, sosai na zubar da jini wanda hakan yasa sai da aka k’aramin dana _Kisma_.
Cikin ikon Allah na haifi yarana guda uku, maza biyu na mace d’aya, ko kad’an babu wanda yayi tsammanin ganin yara uku har dani kaina, dan likitar dake dubani bata ta6a yimin wannan bayanin ba, sosai tayi mamaki ita da kanta da ta ga yara uku dan har ga Allah itama bata ta6a ganin alamun hakan ba, cikin mintina kad’an aka gyara yaran aka mik’a wasu _Alaja Tahira_ wanda bakinsu yaki rufuwa dan murna, ni kuma aka gyarani kafin wani lokaci barcin wuya ya kwasheni.
A hankali nake bud’e ido na, da sauri na bud’e gabadaya tunowa da wai na haihu kuma wai yara har uku, ni har yanzu a wai kawai nake ganin komai, abu kamar almara babu wanda ya shaida an yi aure sai dai ganin yara har uku, ba zanyi butulci ga Allah ba tabbas ya bani kyauta irin wanda ba kowa ke samu ba, ya bani kyautar da wasu suke nema da kud’i bani da abin cewa sai “godiya ta tabbata ga Allah mai ji mai gani mai kyauta mai yafiya mai azurtawa mai jink’ai, Allah yayi dadin tsira ga shugaban mu annabi muhammad, amincin Allah ya tabbata ga annabin tsira da ahalinsa da sahabbansa da sauran mutane baki daya, Allah kuma ya rayamin su cikin imani da wadatar zuciya”.
STORY CONTINUES BELOW
“Kin tashi ashe, _Kisma_ mik’o mata kunun da kuma tuwo ta samu ta dumama cikinta” d’auke kaina nayi da ga kallon yaran wanda aka sanya musu kaya aka rufe su da abin rufuwa me kyau, mazan nasu blue macen kuma pink, sai wusul wusul sukeyi gwanin ban sha’awa, murmushi nayi ina tunanin wai fa duk wadannan kyawawan halittar yarana ne. Duk da cewa ba wani kallon Sufyan nayi ba amma tabbas da shi din suke kama farin fatansa da kyaun fuskarsa “Sufyan ina zan ganka” na fad’a k’asa-k’asa ina d’an share hawaye, tabbas a yanayin da abubuwan suka kasance ba’a hayyacinsa yake ba ni shaida ce ba’ason ransa komai ya faru ba, sihiri ne ajikinsa na riga da na fahimci komai, shiyasa ban kullace shi ba, fatana Allah ya yaye mishi matsalolin shi kuma ya bayyana shi ga y’ay’ansa.
Kwanan biyu aka sallame mu daga asibitin, yaran kuma anyi musu hud’u ba da _Suhail, Sudais_ da _Sawaiba_ muna kiransu da _Abbati, Abbey_ da _Ummita_. Sosai muke samun kulawa da soyayya daga 6angarori daban-daban babu wani abu da za’a yiwa yara masu gata da ba’ayi musu ba, ranar suna kuwa taro akayi na ban mamaki tamkar ubansu yana tare dasu, sosai nayi kukan farin ciki har na rasa wani kalma zanyi amfani da shi gurin gode musu, tabbas sud’in sun cika mutane na gari masu alkairai ga duk wanda ya ra6esu.
Gagarimin walima aka shirya wanda mutanen _Alaja Tahira_ da _Prof Suhail_ suka halatta, anci ansha an wa’azantar dan wata shahararriyar malama aka d’auko tayi wa’azi na musaman wanda ya sanyaya zuqatan mu ya kuma kara mana tsoron Allah. Yara sun samu alkairi da dama daga kayan sawa zuwa kud’ad’e har da fili, domin ba’a ta6a shagali a gidan ba sai wannan karon, hakan yasa mutane da dama suka karrama gayyatar dasu _Alaja_ suka musu, daga ni har su kaya kamar zamu bud’e kanti abin dai sai wanda ya gani, chan na hango masoyan _Deemah_ a babban canopy sunata bawa cikin su abinci, wasu ma harda sawa a jaka wata na hango ta d’auki wanda zata aika wa _Baba K_ ta faki idon masoyan _Deemah_ dan karsu suburbudeta.
Anyi suna lafiya an watse lafiya, kowa ya tafi cikin farin cikin karramawar daya samu a gurin bayin Allah nan, domin komai a wadace akayi kuma aka raba komai cikin tsari. _Suhail_ yaci sunan mijin _Alaja Tahira_ _Sudais_ kuma sunan kakansu, dan haka na gani a jikin wallet dinsa daya manta _Dr Sufyan Sudais_ ita kuma _Suwaiba_ sunan _Inna Suwaiba_ sosai naji dadi da babu wanda ya tambayi sunan waye _Sudais_ yaci domin ban da niyar bayyana wa kowa komai game da 6oyayyan lamarin y’ay’ana.
Bayan sati guda da suna su _Kisma_ suka gama jarabawansu na _Waec_ da _Neco_. Muna zaune a falon sama nida _Kisma_, _Inna Suwaiba_ da _Alaja Tahira_ muna ta hiran abubuwan da yaran suka samu, inda _Inna Suwaiba_ tace a sayar da filayen da suka samu a had’a musu da kud’insu a barshi a cikin account din, sosai _Alaja Tahira_ ta amince ta shawaran kuma tace zata yiwa mijinta magana duk yadda yace zata sanar mana. Wayarta ne yayi ringing, yanda naga fuskarta ya sauya daga farin ciki zuwa ak’asinsa yasa nima na damu, har wayar ya tsinke bata d’auka ba, sai da aka kira kusan sau uku sannan ta d’auka ta kuma saka a speaker.
Wani irin bugawa kirjina yayi “Mama Qudi_ ce, bayan sun gaisa ta fashe mata da kuka, dakewa tayi taki tace mata komai har sai da tayi me isarta ta tsaya sannan tace “_Alaja_ _Khadeemah_ ta 6ata ita da yar uwarta da matar babansu, har yau babu su babu labarinsu, mun zagaye ko ina nida yan uwana amma babu wanda yace mana ya gansu, yau kusan wata bakwai da sati biyu kenan amma shuru, baban su kuma bai damu ba hasali ma yace ko an gansu kar wanda ta dawo mishi gida, duk gurin yan uwa na bincika babu su babu labarinsu, shine na kira inji ko suna gurinki ko kuma sunyi miki waya dan wayarsu ma baya shiga kwata kwata” ta karashe cikin rawar murya da alamun kuka zata zakeyi, tashi nayi na wuce d’akin mu domin ba zan iya sauraron kukan ta ba, Allah ya so yaran ma suna barci a d’aki da sun tona mana asiri ta hanyar kukansu da baya isarsu.
Ban san dai yadda suka kare ba amma ganin _Kisma_ nayi ta shigo tana dariya tana taka rawa, ni nasan tabbas _Alaja Tahira_ ta gaya mata ba dadi shiyasa yar rainin wayonnan ta shigo tana taka rawa, nasan _Kisma_ da shegen mugunta musanman idan akace mutum yayi laifi kuma Allah yana hukunta shi ta hanyar azabtar da shi da wani abu, tsaki kawai naja nace mata dan Allah ta fita ta bani guri kaina na ciwo, “yanzu ke saboda kukan _Mama Qudi_ kike 6ata rai da shiga kunci? Kin manta abin da tace miki da wanda tayi miki? Toh idan kin manta ni kam ban manta ba kuma dai-dai kenan wallahi ina son irin hakan, Allah ya cigaba da azabtar da zuciyarta kamar yadda ta azabtar da na…” kafin ta k’arasa na isa inda take na zabga mata mari “baki da hankali ko _Kisma_ mahaifiyarki ce fa, kome tayi miki kalmar nan bai dace da ita ba, ki tuna cewa ita ta d’auke ki a cikinta wata tara, kullun da irin wahala da azabar da take sha har zuwa haihuwarki, kinsan irin rad’ad’in dake cikin haihuwa? Kinsan irin wahalar da tasha? Kafarta daya yana duniya daya yana lahira amma a haka cikin wahala da azaba ta haifeki tana me fatan ke ki rayu ita ko da ta mutu ba zai yi mata ciwo kamar ace ke kika tafi kika barta ba, shine zaki saka mata da haka, kome iyaye zasu mana basu cancanci mu furta musu wasu kalaman ba _Kisma_ ki lura kuma ki kula” sosai nayi ta mata fad’a har sai da naga jikinta yayi sanyi ta fara kuka sannan na janyo ta jikina ina rarrashinta tare da mata nasiha me ratsa zuciya, a yanzu ni uwace na kuma fuskanci irin abin da mahaifiyata ta fuskanta a kaina, kome zata yimin nikam na yafe mata domin mahaifiya tafi karfin a rainata ita din abar girmamawa ce.