DEEMAH CHAPTER 6 BY ZAHRATEEY
Www.bankinhausanovels.com.ng
A hankali komai yake zama kamar ba’ayi ba, kullun k’ara girma suke yi kuma kamanninsu da mahaifin su na k’ara fitowa, tun bayan da suka cika wata biyar nace wa _Alaja_ ni makaranta nake so in koma, ba tare da dogon jayayya ba ta amince in da na shiga _UDUS_, _Usman dan fodio university sokoto_ nake karanta _Islamic law_, sosai na dage da karatu babu wasa duk da cewa ina fama da yara, sauki na d’aya mutanen gidan suna kula dasu sosai shiyasa bana damuwa. Ina level 2 _Kisma_ ma ta samu admission tana karanta _Islamic Studies_ sai ya zama yaran suna gurin su _Alaja_ ganin kamar kar wahala tayi musu yawa yasa na cewa _Alaja_ ta samo musu me raino, da farko taki yarda amma daga baya ta amince.
+
Kukan _Ummita_ ne ya tasheni a barci, ni kam wataran kamar in fasa ihu, sai mutum ya fara barci me dadi komai zai lalace, har gwara yan mazan kukan su baya wuce idan sunajin yunwa amma _Ummita_ kukan nata har da najin dadi kawai dai taji tana kuka ana rarrashinta, tsaki na d’an ja sannan na d’auke ta, sauran yan uwanta duk barci sukeyi, kallon agogo nayi karfe takwas na safe, _Kisma_ na kalla dake ta barci harda gyara kwanciya, sannan na kai idona kan yaran, a lokacin suma duk sun bud’e ido, idanun su ne kawai irin nawa, amma bayan haka babu wani abu nawa da suka d’auko, cizon data yimin ne yasa na fahimci ta koshi, kamar in zuba mata mari haka naji dan na lura idan ta koshi kawai sai ta cizeni, ajiye ta nayi na d’auki sauran yaran, sai da na tabbatar duk sun koshi sannan na ajiye su.
Yanzu haka shekaransu daya da wata biyar da haihuwa, duk wani kiriniya sun kware a kai, tun suna wata uku da yan kwanaki suka fara zama tare da yan kiriniya ga shi yanzu har sun fara takawa, ga kokarin cin zalin _Ummita_ dan haka kawai sai su had’u su kifar da ita ko suyita ja mata gashi tana ihu suna dariya, ita kuma babu abin data iya sai kuka da cizo idan ta samu dama. Duk wani abu da tsawon su zai kai duk mun dauke saboda rigimar su, kayan wasa ne kawai jibgi muka cika musu guri da su.
Ganin suna wasa yasa na shige wanka, ina fitowa na shirya zuwa doguwar riga yar kanti sannan na d’aura d’ankwalin na fita. Kitchen na shiga na fara taya _Uwani_ wasu ayyuka, sai da muka gama sannan na koma sama lokaci _Kisma_ ta tashi, d’akin _Inna Suwaiba_ na shiga na gaisheta muka d’an ta6a hira sannan na shiga na _Alaja_ a zaune na same su suna hira a kan carpet, har k’asa na tsuguna na gaishe su sannan nace musu an gama abinci yana dinning, albarka suka saka min kafin na fita.
D’akin na koma na samu _Hindatu_ har ta musu wanka tana chanja musu kaya, bayan sun gama suka sauko suna ta wasa a cikin falon, _Kisma_ kuma ta k’araso dinning muka ci abinci, bayan mun gama na koma d’aki na kwanta.
Karfe sha d’aya da rabi na farka, ina bud’e ido na nagan su sunyi wanka da Vaseline, daga fuskar su har jikinsu, _Kisma_ ce ta fito a ban d’aki ganin abin da sukayi yasa tayi sauri ta k’arasa gurinsu ta kwace roban duk da cewa saura kad’an nema a ciki, ni kam rasa abin cewa nayi kawai na tashi na fice na barsu, ita data ajiye musu sai ta san nayi dasu.
Kitchen na shiga na samu _Uwani_ har ta fara had’a abincin rana, sannu nayi mata sannan muka cigaba da aikin tare, sai wajen azahar muka gama, d’aki na koma na sake wanka sannan nayi sallah, ina idarwa suka shigo tare da _Kisma_ har ta musu wanka ta chanja musu kaya, hararanta nayi kawai na d’auke kai, zama suka yi kusa dani suna surutun su da ba kowanne nake fahimta ba, bance musu komai ba na had’e rai, _Kisma_ ce ta zauna a kusa damu tana cewa “ayya basu suka yi laifin bafa, mantawa nayi na ajiye a gurin bayan na gama shiryawa, toh in shiga toilet in mayar da towel shine fa na fito na samu har sun gama wanka da shi” kallon su tayi tace suce “sorry momy” kallona sukayi sunyi tsuru tsuru da ido wannan ya kalli wannan sai da ta maimaita musu sannan suka fad’a a tare, dariya ma suka bani yadda naga sunyi tsuru tsuru da ido, “shikenan amma kar ku sake kunji ko” a tare suka kad’a kai kamar kadangare.
Kasancewar yau lectures din karfe uku ne yasa nayi sauri na gama komai, na shirya cikin atamfa riga da zani, sai hijabi har kasa da safan kafa saboda lallen da nayi, _Saminu_ direba ne ya kaini muna zuwa nace mishi ya dawo karfe biyar ko kuma idan na gama kawai zan kira shi, _Nasiba_ da _Suliyat_ na samu suna jirana, bayan mun gaisa muna wuce lecture hall. _LIL 2303 Introduction to Islamic law ll_ shine abin da muke da shi, sosai muka natsu muna jotting point masu mahinmanci har matar ta gama sannan tace idan da me tambaya yayi, mutane uku ne kawai sukayi tambayi ciki harda _Nasiba_ bayan ta kara mana bayani tayi mana sallama ta tafi.
Cafeteria muka nufa dan suci abinci, bayan sun gama muka fara duba wasu takardun, muna zaune yayi mana sallama kamar ko yaushe, bayan mun amsa ya zauna a kujeran dake kallon nawa, “meyasa kike son walakantani ne _Deemah_? Idan kina tantama a kaina sai ki fara gwadani tukunna” wani irin kallo na watsa mishi sannan na tashi na fara tattare kayana ban sake minti biyu a gurin ba nayi gama bayan na musu sallama, ina zuwa kuwa sai ga motar gida, da sauri na shiga bayan mun gaisa da _Saminu_ sannan muka d’auki hanyar gida.
Nikam na rasa wani irin mara zuciya ko kuma wani irin maye ne _Faruk_ sam-sam bashida zuciya ko kad’an, tunda yake min magana ban ta6a kula shi ba, kuma dadi na d’aya kawayena biyu basu ta6a tursasani ba, shiyasa ma nake sake sakewa dasu, tsaki naja kad’an sai kuma nayi murmushi dana tuna cewa da ada ne da yanzu ya kusa margayawa, tun bayan tarayyata da baban triple babu wani wanda yazo gurina daya rasa rayuwarsa, sosai abin yake bani mamaki sai dai nayi godiya ga Allah domin dama hakan shine burina mutane su daina mutuwa a kaina.
Ina zuwa gida na samu dayan mayen wato d’an kanin mijin _Ajala_ tun bayan haihuwarsu triple daya zo shikenan ya sani a gaba da zancen soyayya, ni sam babu wanda yake raina bayan mijina kuma uban y’ay’ana _Sufyan_ tabbas na kamu da son mijina tun bayan faruwar lamarin kuma ba zan iya had’a shi da kowa ba, ina adduar Allah ya bayyana min shi mu rayu tare da yaranmu cikin aminci da kaunar juna, ba zan iya kula wani namiji ba alhali ni bansan matsayin da nake ba, _Sufyan_ be furtamin saki duk da cewa yace zai sake ni amma bana ma fatan ace ya sake ni din.
D’aki na shiga nayi wanka sannan na nufi d’akin _Inna Suwaiba_ anan kuma na same su baki d’ayansu, yanda naga ran _Alaja_ a 6ace yasa hankali na ya tashi, tambayarsu nayi ko meke faruwa, kallona _Alaja_ tayi tace “zamanki haka yana damuna, gashi kinki kula kowa har _Kisma_ ta samu saurayi amma ke shuru, a ganinki haka zamu zuba ido a kanki, d’azu yaron gurin _Atta_ ya zo kuma _Alaji_ yace yakamata ki ba shi dama ku fahimci juna, wani irin bugawa kirjina yayi, inba wa dama? Wai wannan yaron dake falo, lailai ma kuwa, ai gwarzon mijina ya riga ya tafi da zuciya ta wanda babu wani fili da zan iya amincewa da wani “ba zan iya aure akan aure ba, _Sufyan_ bai sake ni ba, yarana ta hanya me kyau aka samar dasu, da aure a kaina _Alaja_” na fad’a ina barin gurin cikin kunan zuciya, wani irin kuka ne yake cin zuciyata da sauri na wuce d’aki na fad’a kan gado.
“Tunanin me kikeyi _Khadeemah_?” _Alaja_ ta tambaya tana bawa _Ummita_ kunu, ajiyar zuciya nayi dana gane ashe wai duk tunani ne kawai, tabbas na dawo na samu mayena a falo kuma na haura sama nayi wanka na nufi d’akin _Inna Suwaiba_ kuma _Alaja_ tayi min maganar aure amma bata tursasa min ba, ta dai ce ya dace inyi tunani da kyau in fitar da mijin aure, shine ni kuma na tafi tunanin cewa har tace in gwada d’an kanin mijinta kuma har na sanar da ita cewa inada auren wani a kaina, eh tabbas inada auren wani a kaina kuma ba Iowa bane face baban triple, abubuwan a juye suka kasance kuma abin ya faru bisa kaddaran samun cikin triple, zan warware muku komai a sannu amma a yanzu ina bukatan sanin ina mijina yake!”
+
Bayan mun dan ta6a hira na wuce gurin _Uwani_ na samu ma har ta gama saura jera abinci a dining da gyaran kitchen, hannu nasa muka karasa aikin sannan muka jera abinci a dining, daganan na wuce d’aki dan yin salla, ina shiga na samu har _Hindatu_ tayi musu wanka ta chanja musu kaya, “dama kin bari sai da suka farajin barci kika musu wankan, dan yanzu kafin suyi barci sai sun gama lalata kayan, ko da yake kunfi kusa ai naga kema akwai son wasa da ruwa, sai ku sake wani wankan anjima” na fada ina shigewa toilet, ita kuma tayi murmushi kawai wanda yake al’adarta a ko da yaushe.
__________________
Zuwa yanzu duk _Mama Qudi_ ta nemi natsuwar ta ta rasa, kullun sai tayi kuka akan rashin sanin inda muke, yanzu kam su _Ya Kolo_ sun fara jin tausayinta domin duk ta rame tayi duhu kullun daga kuka sai kuka, ko abinci ma sai sunyi yar nasiha take iya ci, _Inna Abu_ kuwa tafi kowa jin dadin rashin ganin mu da akayi domin arzikin dan ta sai kara ha6aka yakeyi hakan yasa ta kara yarda da cewa tabbas nice silar karayar arzikin daya samu, yayyina da kanne na suma duk suna cikin damuwa sun kasa samun natsuwa a zuqatansu, _Baba K_ kam gaba ta kaishi dan shi bai ga abin damuwa ga yar da tayi ciki a waje ba, ya san dai bariki na koma na koma janyo yar uwata muka cigaba da Sana’a sai dai tafiyar _Inma Suwaiba_ ne kawai ya 6ata mishi rai, a ganin shi ai ita ta girme wa sana’ar karuwanci sai dai kawai kwadayin abin duniya daya mata yawa.
_Inna Abu_ itace babba a cikin dangi baki daya, dama mahaifinta ne yake tsawatar mata a lokacin yana raye, to yanzu kuma babu ke iya taka mata burki ko kuma ya fad’a mata gaskiya saboda kasancewarta babba a cikin ahalinsu, kannen _Baba K_ kuwa basu isa suyi magana ba dan zata iya sallama su wa duniya amma tabbas sunji ba dadi kuma sunzo sunyi wa yan uwana jaje tare da nasiha a _Mama Qudi_ dan aganinsu biye mishi da tayi sam babu amfani a ciki tunda ga shi yanzu itace a ruwa shi kam ko a jikinsa.
______________________
Babban gida ne wanda ya amsa sunan gida, ga kyau ga tsari, wani mota ne ya shiga gidan kirar _Toyota Benz_ wasu yara mata biyu ne suka fito tare da wata kyakyawar mata, ” _Anisa,Afifa_ ku tsaya nace ko? Na fada muku bana son yawan gudun da kukeyi” cikin sauri yaran suka bar gudun da sukeyi saboda basa son 6ata ran _Amminsu_ saboda _Ya Sayyidi_ yace babu kyau kayi abin da zai 6ata ran iyayenka, duk wanda yake sa iyayensa fushi ko 6acin rai ba zai shiga aljanna ba “Sorry Ammi” suka fad’a a tare “is okay muje kowa tayi tafiya da natsuwa” kai suka gyad’a sannan suka cigaba da tafiya, a bakin wani kofa babba suka tsaya, alarm din kofar _Ammi_ ta danna, bayan tsayuwar minti guda aka bude musu “Sannu da zuwa _Ammi_” wata mata ta fad’a bayan ta bud’e “Yauwa sannu _Atika_” _Ammi_ ta fad’a fuskar ta d’auke da murmushi.
Wata babbar mata suka samu wanda akalla zatayi shekaru sittin da biyar, fara’ar fuskarta ne ya kara “Maraba da jikoki na, sannunku da zuwa” ta fad’a tana mik’a musu hannu, cikin sauri suka isa gurinta suna murnar ganinta, sai da suka gama murnar nasu kafin _Ammi_ dake zaune a k’asan carpet din ta gaisheta, amsawa tayi cikin kulawa sannan tace wa yaran su shiga ciki akwai sabbin kayan wasan data sayo musu, har zasu fara gudu sai kuma suka tuna da fadan _Ammi_ ai da sauri suka natsu suka fara tafiya a hankali, suna haurawa sukayi d’akin da gudu.
Kad’a kai kawai tayi tana cewa “ai dama nasan sai sunyi gudun” dariya _Hajy Naja_ tayi sannan tace “ki barsu kawai lokaci ne ai kuma nasan zasu dai na” waya ta d’auka tayi kira, bayan mintina uku wasu yara maza uku suka shigo, biyun da ganinsu tagwaye ne yan shekara takwas, sai d’aya wanda yafi su natsuwa shi zai yi shekaru goma sha d’aya, bayan sunyi sallama aka amsa musu sannan suka shiga suka zauna kusa da _Ammi_ kallon su take yi cike da jin dadi yaranta sun girma, bayan sun gaisa take tambayar su batun karatunsu, suka amsa da komai lafiya, hira suka d’anyi me tsawo har sai da taga farin ciki ya bayyana sosai a tare dasu sannan tace suje sama su samu kannen su, cike da zumudi suka haura saman.
Kallonta _Hajy Naja_ tayi sannan tace “finally kin yanke shawaran barinsu suga yan uwansu kenan?” Ita kanta ba a son ranta take hana su ganin juna ba ” _Umma_ ba wai bana son su rinka ganin juna bane, kawai dai kinsan halin _Anisa_ da shegen kai rahoto, har gwara _Afifa_ bata da matsalan bada labarai, idan ba tambayarta akayi ba ba zata ta6a bayani ba, _Anty Aisha_ ce tace kuma kar in bari su san juna harse lokacin da suka dawo gida sai komai ya bayyana, nima kuma naso hakan ya kasance amma a halin yanzu da aka rasa _Sufyan_ bana tunanin zan iya cigaba da hana yan uwa sanin junansu” ta fad’a tana share kwallar dake neman zuba.
“Hakane _Jiddah_ kinyi tunani me kyau, itama _Aisha_ tayi tunani me kyau a lokacin data hana barinsu su san juna dan da ace sun san juna da sun takura akan son zama da yan uwansu, su kuma matan da zasu takura akan son ganin yayyinsu a kusa dasu, kinga kenan an gudu ba’a tsira ba domin _Lami_ zata iya komai gurin ganin ta 6atar dasu, ni sam bansan meye nata a haihuwar yara maza da _Sufyan_ yakeyi ba, tabbas kinyi hakuri iya hakuri _Jidda_ kuma ke surukar kwarai ce wanda ta san abin da takeyi, da ace wata ce da tuni ta d’au mataki, yara har hudu tayi miki sanadin su saboda kasancewarsu yan maza amma duk da kinsan gaskiya kikayi hakuri kika barta da aniyarta, tabbas _Aisha_ tayi dabara da bata ta6a bari tasan da wadannan yaran ba, shima mahaifin su gwara da ba’a bari ya sani ba, domin nasan da ya nace akan a bashi su, fatana Allah ya bayyana shi a duk inda yake, nasan kina hakuri ki cigaba da hakuri akan wanda kikeyi, Allah ya miki albarka” kukan da take rikewa ne ya kufce mata, mijinta kuma uban y’ay’anta ya 6ata babu shi babu alamunsa, a yanzu kusan shekaru biyu da wasu watanni kenan ana neman shekaru uku, tunda ya tafi Abuja wani aiki shikenan aka rasa shi sunyi neman har sun gaji amma babu wani labari. Sai da tayi kuka sosai sannan ta tashi ta shiga kewayen take cikin falon ta wanko fuskarta.
Sama ta haura inda yaran suke, ganinsu a tare ya matukar sanyaya ranta, duk da cewa tafi _Sufyan_ kyau amma idan taga fuskar shi a tare da yaran sai taji wani irin farin ciki da annashuwa a tare da ita, shekaru goma sha uku kenan da aurensu da _Sufyan_ a bad’ini yaran su tara a zahiri kuma yaran su biyar, hud’u duk sun rasu, uku kuma suna gurin kanwar kakansu, sai biyu da suke tare da ita, ukun da suke gurin kanwar kakansun ma babu wanda ya san dasu saboda miyagun mutane dake zagaye dasu, biyun kuma kasancewar su mata babu wanda yasa musu ido, ita kam bata san meyasa son zuciya yayi yawa a wannan rayuwar da muke ciki ba.
Su yan mazan sun riga da sun san yan uwansu domin duk sanda suka zo idan sukayi barci _Ammi_ ta kan kai su domin suga kannen su, amma su yan matan bata bari su gansu saboda kar suje suyi maganarsu a gida wanda hakan zai jawo musu damuwa, sai dai a wannan ga6ar tana bukatan ganin farin cikin yaranta a bayyane dan ta dade da sanin cewa suna son ganin kannensu suna son suyi wasa dasu kamar yanda kowa yake muamala da yan uwansa.Zaune suke a wani d’an karamin tabarma a gaban wani bukka ” _Isa_ gobe nefa daurin auren mu, a gaskiya ina cikin farin ciki sosai” kallonta wanda ta kira da _Isa_ ya yi fuskarsa d’auke da murmushi “tabbas ni ma ina cikin farin ciki sosai _Bibalo_, banyi tunanin cewa _Baffa_ zai bani ke ba, nayi tunani ko nace zanyi aure babu me bani y’arsa sai ga shi _Baffa_ ya bani ke, tabbas babu abin da zan iya biyansa da shi illa in rikeki bisa amana” murmushi _Bibalo_ tayi “duk da cewa mu yan kauye ne kuma kauyen ma karami irin wannan kuma a cikin daji ba’a bainan nasi ba, muna da sani dai-dai gwargwado, domin _Ilu_ d’an gidan me gari yayi karatu sosai ta fannin boko da addini shiyasa bamu sha wahala ba, bayan daya dawo daga birni sai ba bud’e mana k’aramin makaranta inda yake koyarda mu daga cikin abin da ya koyo” ta fad’a cike da alfaharin _Ilu_ shine malaminta.
+
_Tani_ da _Hansai_ ne suka shigo suna kwala mata kira, da sauri tace mishi bari suje su dawo, a bakin kofar madafin ta samesu, sannan suka fita zuwa gurin _Marka_ me gyaran jiki, tun satin daya wuce suka fara sai yau zasu gama dan gobe d’aurin auren ta da d’an binni, suna zuwa aka fara yi mata nata, sai da aka gama taja gefe tana tunanin d’an binni, yanzu k’imanin shekaru biyu da wata shida kenan _Baffa_ ya tsince shi a cikin ruwa, sosai ya galabaita dan daker aka shawo kansa, sai da yayi wata biyu ya samu dawowa hayyacinta sai dai kuma ya manta ko shi waye ba zai iya ma tuna komai ba, a haka _Baffa_ ya rikesa har zuwa wannan lokacin da zasuyi aure, sosai d’an binni yake sonta ita ma tana matukar son shi, hakan yawa _Baffa_ ya amince da aurensu nasu tunda duk suna kaunar juna.
Sai yamma lis suka gama gyaran jikin tare da lallen gargajiya da kuma na zamani, kowa ta fito shar da ita bama kamar amarya _Bibalo_ kasancewarta fara amma ba chan ba sai dai haskenta me kyau ne kuma dai-dai misali, tana da kyau dai-dai gwargwado domin babu abin kushewa a tare da ita, siririya ce me kyaun diri, sai dai bata da cikan kirji, haka kuma tana da yalwar gashi kasancewar su fulanin usuli. Tana shiga gidan ta samu har an fara cika yan uwansu dake wasu rugan duk sun k’araso, cikin sa’anninta ta shiga suna ta hira ana yaba kyaun da tayi, ita kuwa sai murna takeyi burinta bai wuce d’an binni yayi tozali da ita ba tasan dole zai yaba har da tukuici ma zai bayar, Allah-Allah takeyi gari ya waye a d’aura musu aure ko zata samu sukunin kasancewa da abin begenta zama na har abada.
______________________
Wai samun guri tusan asuba, su _Baba K_ an karo sabbin salo, wanda sabuwar amaryarsa daya yi me suna _Safara_ ta gindaya, sati biyu kenan da akayi auren, _Safara_ yar bariki ce sananniya, kuma ba komai ya kawo ta gidan ba sai ta nanike kud’in _Baba K_ saboda yanzu arzikinsa k’ara ha6aka yakeyi, ya rufe wannan shagon ya bud’e wani babba a kasuwa inda kanin amarya yake kula masa da shago.
STORY CONTINUES BELOW
Kamar kullun suna layin kar6an abincin sayarwa wanda yanzu _Safara_ ce ke sayarwa, duk da cewa iya kudin iya shagalinka ne amma yanzu wani irin zubawan walakanci ake musu wanda yake ci musu rai sosai da sosai, har gwara lokacin da _Baba K_ yake sayarwa komai cikin sauki amma wannan matar duk tasa sun muzanta a gidan mijinsu. Bayan an gama rabiyar abincin sayarwa suna zaune a falo suna ci dan kawai kar yunwa ya lahanta su, _Ya Kolo_ ce tace “a gaskiya dole ne mu had’a wasu yan k’adarorin mu, mu sayar mu fara wani sana’ar dan munaji muna gani kudin hannun zasu kare mu rasa na sayan abinci, tunda kunga ko yaran nan sun kawo mana ba bari yakeyi ba sai ya d’auke ya kai shagonsa wasu kuma ya ajiye a gurin matarsa” _Goggo Fulera_ ce tace “kina da gaskiya sosai dole ne mu tashi tsaye musan abin da ya dace kafin muzo muna kukan yunwa dan matar nan ba imani ne da ita ba” _Mama Qudi_ da ta zuba tagumi ne ta amshe tana cewa “ko da zamuyi sana’a sai dai ya zama a 6oye kar shi ko matarsa su sani, zamu iya bawa su _Khalil_ su kula mana da shi, ko da acikin kasuwa ne sai mu bud’e k’aramin shago, ko ya kuka ce? Tunda akwai yan kud’ad’en da yaran nan suke bamu kunga sai mu had’a tare da sayarda wasu k’adarorin mu domin a samu a zuba kaya masu d’an yawa da amfani” sosai sukayi na’am da shawaran data bayar. Haka suka cigaba da tattaunawa har zuwa lokacin sallar azahar suka watse domin gabatar da salla.
_____________________
“Zakuyi shuru ko sai na dake ku?” Na fada ina zare musu ido, kallo na sukayi sannan suka fashe da kuka a tare, a harzuke na tashi ina neman bulala, ai da gudu suka fice a d’akin suna k’ara sautin kukan nasu, kawai ina karatu amma na kasa gane komai dan surutun da sukeyi wanda ba komai ma ake ganewa ba, sau uku kenan ina cewa suyi shuru amma sai sunga hankali na ya koma kan karatu zasu cigaba, dan k’aramin tsaki naja kafin na cigaba da karatuna a nitse.
Bayan na gama na gyara inda suka 6ata saboda yau _Hindatu_ bata da lafiya nace ta huta, ina gamawa na ciro wannan k’aramin laptop bag din daya bari a gurina, yau dai ina sha’awar ganin abubuwan ciki, bayan na rufo kofan d’akin na dawo na baje akan gado, wallent dinsa na ajiye a gefe sannan na bud’e jakan laptop din na ciro, bayan na bud’e naga akwai password nazari na farayi akan abin da ya dace in rubuta, chan na tuno da sunan da naji yana ta maimaita wa _Jidda_ na saka ina tunanin ko ita wacece a gurinsa, sai dai bai bud’e ba, na gwada style din rubuta sunan da yawa amma yaki karshe dai nasa _JiddanSufyan_ wanda ina rubutawa zuciyata na zafi ina danna enter kuwa ya bud’e, wani hawaye masu dumi ne suka zubomin ganin hoton wata kyakyawar mace wanda ko shi _Sufyan_ din bai Isa ya nuna mata kyau ba, su hud’u ne a hoton, da shi da ita da yara biyu kyawawa masu kama da shi kuma masu kama da _Ummita_ kamar an tsaga kara, “matarsa ce ashe? shikenan na kad’e” haka na dinga maimaita wa, kashe laptop din nayi kawai na mayar da komai ma’ajiyarsa, kuka na fashe da shi, _Jidda_ na maimaita, yana da mata kamarta me zaiyi dani, shi kansa ta keresa a kyau balle suni wanda idan na jera dasu sai dai ace min yar aikinsu, ba wai na raina irin nawa tsarin bane, tabbas ba za’a cemin mummuna ba amma kuma bana sahun kyawawa sai dai ace min ina tsaka tsakiya, duk da cewa ina da jiki amma ina da k’ira me kyau kuma me ban sha’awa, gashinta na tuno mace kamar d’iyar larabawa kila ta had’a jini da _Shuwa Arab_ ni kuwa gashin ba wani chan bane amma dai yana packing me kyau kuma yana da cika da duhu, kai bafa zan iya had’a kaina da ita ba domin ba ko wata mace ke samun tsarin matar ba, tana da cikan kirji da diri sosai wanda ni ban kaita ba, kuma ita ba siririya bace kuma ba me kiba ba sannan da alamu bata da tsawo sosai, tsaki naja na tashi na shiga ban daki na dauro alwala na tada salla ko zanji sauki a raina, ina idarwa na d’auki Al qurani waraka ga dukkan damuwa dai ga shi na samu natsuwa na shiga wata sabgar, amma fa tunanin cewa mijina nada mata ya tsaya min a rai, lailai ina ruwa…
Gabad’aya ranar kawai dai gani nan gani nan ne dai, sai dai kuma wani abu dana tuna shine ya sanyaya min zuciya, ko wata mace dai macece sai dai ko wacce da irin nata baiwar, kuma wacce ta san kanta itace a gaba ba wai ina nufin wani abu na daban bane, duk kyau ko rashin kyaun mace kyaun zuciyarta shine ke rike mata gidanta tare da duk wanda take muamala dasu, bana so in karaya saboda ganin wacece kishiyata domin nima bansan wani irin baiwa Allah yayi min ba, duk da cewa ba’a shaidar d’an adam wani lokaci amma daga ganin yanayin ta na fahimci cewa zatayi saukin kai, amma lokaci shi zai fahimtar dani komai, zan so ace mutuniyar kirki ce domin muyi zama na gaskiya da gaskiya, kuma zan so ace mijin mu ya kasance mutum me adalci da sanin yakamata wanda zai iya rike gidansa ta hanyar nunawa ko wacce ita sarauniya ce kuma ta hanyar nunawa ko wacce da ita da yar uwarta duk daya suke a zuciyarsa, ta hakan ne zai nuna wa ko wacce tana da mahinmanci agaresa kuma sai a samu wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da sassautawar kishi daga zuqakata.
Gidan mata hud’u na taso, duk da cewa suma mata ne kuma suna da kishi amma na fahimci cewa suna da kyakyawar zuciya domin duk yadda suka kai ga nuna basa son junansu musanman ma _Mama Qudi_ da suka k’i tun farkon auren ta da _Baba K_ idan da ace abu mara dadi zai sameta to suna tare da ita, ko wacce ma idan abu mara dadi ya sameta suna tare da junansu suna jajantawa, ga misali nan _Inna Suwaiba_ ita da ba ita ta haifeni ba ta tsayamin kuma ta amince a bakin aurenta, da ace bata da kyaun zuciya babu abin da zai sa ta zauna dani, kishi halittace wanda yake tare da ko wace mace kuma yake tare da ko wani namiji, sai dai muna fatan Allah yasa namu ya zamo me kyau ta yadda ba zamu iya cutar da wani ba, ba’a raba mutum da kishin abin da yake so, sai dai kuma mutum na iya daurewa ya kai zuciyarsa nesa ta yadda zai samu natsuwa kuma ya samawa wasu suma natsuwar, zama da kishiya sai an kai zuciya nesa, domin wata duk yadda zata tunzuraki sai tayi wata kuma fatanta duk a zauna lafiya amma wata ita dai ta zauna lafiya amma kowa ya rasa kwanciyar hankali, ni bazance ma anyimin ba dai-dai ba dan ban san banda kishi ba tunda komai ma na a dai-dai ya tafi ba, ita matarsa ce ma zan ce anyi mata ba dai-dai ba sai dai ta ga kishiya daga sama, bana kuma fatan in zama me son kaina da yawa ina fatan Allah daya had’a ya daidaita tsakaninmu tare da hade kanmu dana y’ay’an mu idan lokacin haduwar tamu yayi…