DEEMAH CHAPTER 8 BY ZAHRATEEY
DEEMAH CHAPTER 8 BY ZAHRATEEY
Cikin ikon Allah muka gama jarabawar mu lafiya, yanzu ma shirye shiryen komawa _Bauchi_ mukeyi, _Alaja_ kuma tana shirin tafiya _Lagos_, _Hindatu_ kuma an riga an sallame ta, a ranar da zamu tafi itama zata wuce garinsu.
+
Sati guda muka kara a cikin garin _Sokoto_ kafin jirgin mu ya d’aga zuwa _Bauchi_, _Alaja_ ce ta biya mana tace muma mu d’ana, sosai munaji dadin hakan kuma muka mata godiya. Tunda muka shiga jirgin yaran sukayi tsit cike da tsoro dama daker suka shiga dan kuka sukayi tayi wai ba zasu shiga ba. Shuru nayi ina tunanin zuwan mu wanda ya kasance kowa na cikin kunci, sai ga shi yau zamu koma cikin nasara da farin ciki.
Ban san cewa nayi barci ba sai da _Kisma_ ta tashe ni tana cewa mun iso, kallon ko ina nayi naga mutane sai fita sukeyi, nima cikin sauri na d’auki jakata na rataya sannan nabi bayan _Kisma_. Ina zuwa na samu har yayan mu ya iso d’aukarmu da motan daya saya kwanan nan, sienna ce me kyau kalar ruwan toka, cike da murna muka zuba kayan mu a bayan motar kafin muka shiga ciki ya tuka zuwa gida.
Komai lafiya muka samu a cikin gidan, su _Ya Kolo_ sunyi kokari gida ne me kyau suka saya dai-dai talaka, d’akunan zaure na yara mazan ne sai kuma cikin gidan kitchen dinsu a waje haka band’aki shima a waje sai babban falo da d’akuna biyar a jere da juna, d’akin _Mama Qudi_ muka ajiye kayan mu, bayan an gama gaisuwa anci abinci shine _Inna Suwaiba_ tace zata wuce, da sauri su _Ya Kolo_ suka ce babu inda zata ko da ace ba’a mai da auren su da _Baba K_ ba, ba zasu bari ta tafi ba balle kuma an riga da an maida auren, sosai nida _Kisma_ mukaji dadin hakan sa6anin _Inna Suwaiba_ data 6ata rai tace zata zauna ne dan su amma ba sai dan ita d’in tana da auren ba dan bata san me zata zauna yi tare da wanda bai san daraja da kimar iyalansa ba, sosai tayi masifa san ranta ta gaggayawa _Baba K_ maganganu masu zafi a matsayinta na yar uwarsa ba wai a matarsa ba, mu dai namu ido, bayan komai ya kara suka shiga bada hakuri har da kuka shi da _Inna Abu_ ni dai kawai ina jinsu ne domin nasan tabbas idan da zasu sake samun guri tsaf zasu koma gidan jiya…
_Kisma_ d’akin _Ya Kolo_ ta maida kayanta kamar yadda ta umurceta, sai yaran suka zauna gurin _Inna Suwaiba_ ni kuma ina d’akin _Mama Qudi_ _Inna Abu_ kuma tana tare da _Goggo Fulera_ sai d’aki guda na _Baba K_, wai su baban mu anji duniya duk ya lalace ya rame ya zama gwanin ban tausayi ga wani gashi daya tara a fuska kamar tsohon mahaukaci, idan da ace _Baba K_ ba irin mutanen dake d’aukan wanka suna buga gayu bane da tuni anyi ram da shi zuwa gidan mahaukata a yadda yake dinnan, ni tunda muka zo kawai sai kallonsa nakeyi, ni dai dama na yafe musu tun tuni ban rikesu a zuciya ba, _Kisma_ irin mutanen dake rike mutum a zuciya ko da ba’a ita akayi wa laifi ba matukar ya shafi wani nata, har zuwa yanzu ina kokarin ganin cewa na cire mata wannan akidar domin ba abu ne me kyau ba amma abin yaki yuyuwa, ba laifi ta rage zafin zuciya amma fannin riko sai abin da ya yi gaba dan ko gaishe da _Baba K_ na lura batayi ba balle su _Inna Abu_.
STORY CONTINUES BELOW
Washe gari da safe yan uwan mu sukayi ta zuwa da yan cikin _Bauchi_ da yan _Kari_ sosai mukaji dadin ganinsu masu min kallon banzan ma duk sun rusuna kowa sai haba-haba yakeyi da yarana, abin kuwa yamin dadi dan babu abin da nake so kamar a nuna so da kulawa ga yarana, a haka har suka watse bayan sallar la’asar, muma mukayi musu alkawarin zuwa idan mun huta, na lura yanzu cewa yawancin abubuwan cikin rayuwata sun sauya, musanman kalle-kallen da nakeyi sai yanzu na k’ara yarda cewa akwai aikin aljanu a tare dani, dama kanin _Baba K_ yace zamuje a dubani a cikin satin nan domin akwai abubuwa da yawa dake damun rayuwata, nima kaina yanzu ina son zuwa dan in san ko kawai shafar aljannun ne ko kuma da hannun wani nawa a cikin durkushewar rayuwata.
Bayan kwana uku da zuwan mu kannen _Baba K_ biyu suka zo muka tafi _Kari_ domin ganawa da wani malami, ko da muka je mun samu ba kowa sai almajiransa, bayan yasa anyi mana shinfidin tabarma a cikin gidansa sai muka shiga, gaisuwa sukayi da kawunai na, daga nan nima na gaishe shi, kallona yayi yace “Tabbas akwai mutanen 6oye a tare da ita sai dai kuma irin wad’annan aljannun akwai malamai na musanman masu iyawa dasu, zan baku adireshin wani malamina a wani karamin kauyen dake hanyar _Jos_ da izinin Allah idan har kuka samu zuwa gurinsa komai zai zo karshe. Bayanai yayi musu da dama akan aljanu iri daban daban wanda ko wani irin malami yake ji da irinsu da kuma irin wanda sai malamai na musanman sune suke iya kawar dasu da izinin ubangiji, mun dad’e sosai sannan ya bamu adireshin muka tafi, ni motar _Bauchi_ na shiga su kuma suka koma gida akan sati me zuwa zasu zo sai mu shirya mu tafi, sosai na musu godiya sannan na shiga motar.
Cikin lokaci kad’an muka shiga _Bauchi_ daga tasha na hau napep zuwa gida duk da cewa sai da na kira _Kisma_ aka sakemin kwatance dan gidan akwai lunguna da yawa kuma gidajen kusan gini d’aya ne, ina zuwa nayi wanka nayi salla sannan na musu bayanin duk abin da ake ciki, addua sukayi akan Allah yasa a dace idan munje chan din. Shuru gidan banji hayaniyar yaran ba sai chan gasu sun dawo tare da _Khalil_ wai sunje sayan cakuleti.
_________________________
_Asalin su_
_Malam Madu Mahmud_ da _Malam Ilu Mahmud_ yan asalin garin _Bauchi_ ne kabilar _Gerawa_ tun asalin kaka da kakanni gidansu an sansu da kasuwanci, kuma sosai suke samu a kan hakan domin Allah ya albarkaci kasuwancin nasu. _Malam Madu_ da d’an uwansa _Malam Ilu_ sun kasance tagwaye ne haka zalika matansu yan uwa juna ne kuma tagwaye wanda suke yan wa da kani, babansu _Malam Madu_ shine babba sai baban matayen su shine karami kuma sun kasance su kad’ai Allah ya azurta iya yensu da samu. Matar _Malam Madu_ sunanta _Khadija_ suna kiranta da _Inna Dija_, na _Malam Ilu_ kuma _Zuwaira_ ana kiranta _Inna Zuwai_.
_Malam Madu_ Allah ya azurtashi da samun yara biyu _Muhammad Sudais_ da kuma _Naja’atu_ sai _Malam Ilu_ Allah ya azurtashi da yara uku _Sadis, Samir_ da _Salman_. Sun taso cikin so da kaunar juna, ko me suke so iyayen su suna iya bakin kokarinsu gurin sama musu shi, duk sunyi karatun bako daga matakin farko zuwa jami’a amma banda Naja’atu wacce a iya karamar secondary ta tsaya sannan aka mata aure, ta auri wani dan kabilar shuwa arab kuma makaniki da matarsa d’aya _Rahima_ wacce ta rasu gurin haihuwa bayan auren da watanni biyar, sosai _Naja’atu_ tayi kuka saboda shakuwar da sukayi da matar dan akwaita da saukin kai da son jama’a, shiyasa duk wani na kusa dana nesa sunji mutuwarta sosai.
Cikin ikon Allah, Allah ya bud’a musu har suka sayi gidan kansu suka koma inda anan Naja’atu ta haifi diyarta mace ta had’a da yaran marigayiya su uku maza biyu da mace d’aya duk ta rikesu. Bayan haihuwarta akayi bikin Yayyinta biyu da _Sudais_ da _Sadis_. Bayan watanni tara matar _Sadis_ ta haifa d’iyarta mace ita kuma matar _Sudais_ ko 6atan wata ba tayi ba, a haka har matar _Sadis_ ta sake haihuwan d’iya mace a lokacin kuma _Samir_ shima yayi aure bayan auren da wata biyu _Sudais_ da _Sadis_ suka kara aure, matar _Sudais_ yar _Niger_ banufiya ita kuma matar _Sadis_ yar _Nasarawa_ kabilar gwandarawa, cikin shekaran matar _Samir_ ta haihu bai dade ba amare suma suka haihu duk y’ay’a mata, bayan shekaru biyu _Salman_ shima yayi aure inda aka had’a dana yayansa _Samir_ shima ya kara mata yar _Kogi_ ibira, daganan akayi ta gasar haihuwa amma banda _Lami_ da batada ko d’aya da kuma _Maryam_ da take da _Aisha_, bayan shekara shida _Salman_ shima ya kara aure ya auri yar _Kano_ bahaushiya, a lokacin ne aka haifi _Sufyan_ sai kannensa hudu a d’akin _Anty amarya_ daganan babu wacce ta sake haihuwa.Bayan auren _Samir_ iyayensu maza suka rasu, bayan an raba gado shine suka yanke shawaran sayan fili babba sukayi gini me kyau da tsari wanda kowa aka mishi side dinsa daban, _Sadis_ likitane yana aiki a wani babban asibiti dake cikin garin _Bauchi_ shi kuma _Samir_ Babban lauya ne me zaman kansa, _Salman_ kuma manager ne a wani banki sa6anin _Sudais_ daya cigaba da harkan kasuwanci kuma sosai harkan ya kar6eshi har ya gina masana’antu da gurin wasan yara. Cikin ikon Allah arzikinsa ya dinga ha6aka a lokacin ne aka haifi _Sufyan_.
Cikin shekaru goma suka tara yara mata guda ishirin da biyar sai d’a namiji d’aya, a 6angaren _Naja’atu_ kuma ta haifi yara uku bayan na farkon da yan biyu mata da kuma namiji d’aya, bayan haka bata sake haihuwa ba, a lokacin mijinta ya kara aure, ya aro babarbariya, tunda tazo ko 6atan wata bata ta6ayi ba sai bayan kusan shekaru bakwai a sannan ne ta haifi d’iya mace me suna _Hauwa Jidda_ daga nan kuma kofa ya bude mata ta haifi yara hud’u mata maza biyu, a haihuwarta na karshe Allah ya kar6i ranta sosai sukayi jimamin rashinta ko ba komai mutum rahama ne ko da zaman babu dadi, daganan yaran suka koma hannun _Hajy Naja_ inda ta had’a duka da yaranta ta rike cikin so da kauna ba tare da nuna banbanci ba, bayan rasuwan amarya suka tare a sabon gidansu dake GRA, dama Allah ya yi baza’a shiga da Amarya ba.