DIYAM CHAPTER 19

DIYAM CHAPTER 19

Inna ce ta yi magana “au biye mata zakayi? Wani irin karatu zata tafi har wata kasa tayi? Ba gwara ayi auren ba in yaso in ma alhuda huda zata zama sai tayi ta zama ba?” Na kalleta nace “Akwai wanda yazo yace yana son aure na ne Inna?” Sai tayi min dakuwa tace “ku raba ke da yan gidan ku, yanzu zama kike so yayi tayi yana jiranki har ki gama wani karatu? Ko wanne karatu ne ai za’a iya yinsa a gidan miji” sai ya mike yana kallon Inna, ban kalle shi ba but I sensed cewa ransa a bace yake, yace “in karatu take so Inna ki barta tayi karatun ta, in zata je Oxford din ta fada and I will take her there. In kuma bata son ta ta fadi duk wadda take so in dai ina da dama zan kaita” sai ya juya ya fita. Na mike da sauri nabi bayansa kamar wadda ake fusga ta zuwa gare shi na same shi a gareji nace “Aliyu” ya juyo da sauri yace “what?” Ina kallon yadda idonsa yayi ja nace “kar kayi fushi dani please” ya dawo gabana ya tsaya yace “nasan abinda kike trying to do, kinsan ina sonki da yawa ina son aurenki shi yasa kika yi shawarar tafiya karatu a tunanin ki hakan zai saka na fito miki da Saghir dinki, which I will never do. Na gaya miki kuma nace bazanyi ba, the more you keep mentioning him and showing that you care about him, the more zuciyata take gaya min in barshi yayi rotting there. In da kinsan kina son sa sanda na tambaye ki ko kina son komawa gidan sa sai ki gaya min, I would have supported you, kamar yadda a yanzu zanyi supporting dinki through karatun da kika ce zaki yi. You know why? Because I love you, and to me that’s what true love is. In kana son mutum soyayya ta gaskiya shine you care about him and support him, you put his happiness a saman naka, you sacrifice everything just for him”+ Naji bacin rai nace “how can you accuse me of that? I don’t love Saghir kuma ka sani, ka sani kai nake so, kuma…” Yace “ni kike so? Na dai ji a baki kin fada kin ce kina sona. But am not so sure about that. Saboda duk abinda kike yi is total opposite of abinda na fahimta a matsayin so. Yes, kin soni a da na sani, but yanzu ban sani ba because a yanzu Saghir dinki shine a gabanki, dashi kadai kika damu” nace “ka daina cewa Saghir dina, ba nawa bane ba, bana son Saghir kuma ban taba son Saghir ba kuma bana jin zan taba sonsa tunda har na zauna dashi a matsayin mijina for years amma ban so shi ba. Kai na so, kai nake so kuma kai zan cigaba da so. Son da nake maka ne kuma ya saka nake so ka fito dashi din for your own good, for peace a cikin rayuwar da nake mana burin shinfida wa dani da kai har mutuwa, and that’s my version of true love. In jawo ka kan gaskiya even if that will hurt you and me”. Sai naga idanunsa sunyi softening, yana girgiza kansa yace “I can’t, na gaya miki I can’t”. Raina a bace na koma cikin gida. Why is he so stubborn? Amma ina zuwa gida na tarar inna ta na tsarawa Murjanatu dalilin rigimar mu ni da Sadauki, sai ta juyo tana kallona tace “why are you so stubborn?” Nace “ni? Au nice ma mai taurin kan bashi ba?” Inna tace “ke ce fa. Kuma ke zakiyi wa kanki, dan ni bazan goyi bayan yayi ta zama yana jiranki ba har zuwa sanda zaku gama rigingimun ku wadanda babu rana. Ke fa kece baki da gaskiya, shi waye yace ya daukar masa kudi? Ita kuma Subay’a ai ba’a kanta aka fara rufe uba ba, wasu ma uban nasu mutuwa yake yi ya bar su kuma haka suke hakura. Wadansu ma basu san iyayen nasu ba uwa da uba gabaki daya. Kowa da kaddarar sa”. Ni dai bance mata komai ba saboda nasan ba fahimta ta zata yi ba. Sai naga ta saka mayafin ta tace mana ta tafi unguwa. Sai bayan ta tafi sai sannan na zauna nayi wa Murjanatu bayanin irin yadda Sadauki intentionally ya shirya wa Saghir trap din daya kai shi prison. Maimakon inga ta fahimce ni sai naga tayi dariya tace “kadan da aikin yaya na wallahi, Aliyu Haidar sadaukin sadaukai” na bude baki ina kallonta da mamaki “wato ke burge ki yayi ko?” Tace “waye yace ya daukar masa kudi? Ai kamar yadda ya fada ne shi ba shi yayi forcing hannunsa ba, ba kuma bindiga ya saka masa a kai ba, ya dai haka masa rami amma shi yayi deciding ya dauka dan haka shi ya jefa kansa cikin ramin”. Sai dare sannan Inna ta dawo daga unguwar tata. Lokacin kwanciya bacci yayi muka je muka kwanta ni da Murjanatu dan tun zuwanta na mayar da Subay’a dakin su Inna. Muna kwance Murjanatu tana ta chatting da sisters dinta da samarinta. Na dauki wayata ina ta jujjuyawa a hannu na. Sam bana jin dadin rabuwar da mukayi da Sadauki dazu, amma kuma banji dadin abinda ya gaya min ba akan wai ina son fito da Saghir ne saboda ina so sa. Zuciyata tana son in kira shi in ji muryarsa kuma in bashi hakuri amma kuma wani barin yana nuna min cewa shi me yasa ba zai kira ni ba? Na ajiye wayar nayi tsaki na kwanta na juya bayana, kusan awa daya ina kwance babu bacci babu dalilinsa, har Murjanatu ta gama yin wayoyinta da chatting dinta naji tayi addu’a ta kwanta. Sai na kuma dauko wayata na nemo number dinsa nayi dialing a raina ina cewa ba lallai ne ta shiga ba, amma sai ta shiga din, bugu dayakuma ya dauka sai kuma muka yi shiru gabaki daga muna sauraron numfashin juna. STORY CONTINUES BELOW Nace “I tot ba zaka dauka ba” yayi ajjiya zuciya yace “ni na isa. Bayan kin hana ni bacci” nace “ta yaya zan hana ka bacci ina miles away from you” yace “yes, miles away but so close” sai na lumshe ido na ina jin dadi a raina, naji duk bacin raina yana gushe wa zuciyata tayi fes. Nayi murmushi nace “ko?” Yace “ke ma kin sani ai, ko sai na maimaita miki. Haliman nan dai ita ce a kirjin Aliyu. Itace a jininsa ita ce a tsokar jikinsa. Bana jin akwai abinda zakiyi min in ki daukan wayarki” a hankali nace “kayi hakuri. Na bata maka rai na sani amma tawa zuciyar tafi bakanta a kan taka” yace “nima na bata miki ai. I shouldn’t have said what I said about Saghir. Matsalata ina kishinki da yawa Diyam” nace “Amma ka yarda cewa bana sonsa kai nake so?” Yayi dariya yace “kara fada min inji?”2 Mun jima muna hira har credit din yawa ta ya kare. Sai ya kira muka cigaba. Yana ta bani labarin rayuwar sa a Canada da University din da yayi. Sanyin da naji gari yayi yasa na fahimci dare ya ja sosai. Da kyar nayi masa sallama. “Zaka je office fa gobe” sannan dai yayi min sallama ya kashe. Ina yin addu’a ko minti daya ban kara ba nayi bacci. Da safe Murjanatu ta tashi tana ta jera hamma. “An hana ni bacci jiya da I love You I Love You” na jefa mata pillow nace “zaki koma kwana a palo” tayi dariya tace “wai su yaya Aliyu an iya soyayya. Lallai in na koma gida akwai labari” sai na tambayeta in tana ganin Papa zai amince, ta bata rai tace “why not?” Nace “ni na taba aure. Aliyu kuma bai taba yi ba” tace “and so what?” Bazan iya miki describing Papa ba, but duk randa kuka hadu you will feel ashamed in kika tuna cewa kinyi min wannan tambayar”. Ranar ma inna ta sake fita unguwa. And I stated to suspect something. Har yamma bata dawo ba, a lokacin ne kuma Sadauki yazo. Na bude masa palon da yake a matsayin na baki muka zauna a ciki. Sai a lokacin na samu courage din yi masa tambayar da take raina nace “Sadauki baka gaya min labarin yaya ladi ba” yayi murmushi yace “sai yanzu kika tuna da ita? Na gaya mata ai nace kin manta da ita gashi kuma kin kwace mata miji” na zaro ido nace “tana raye? Tana ina? I tot ta rasu ne kuma bana son tuno maka da old painful memory, you are already bitter ba sai na kara maa wani ciwon ba” yace “tana nan. Tana damagun gurin wata cousin dinta. Bayan na tafi Canada ta tafi can ita kuma, kuma tunda na dawo taki dawowa gurina tana can sai dai inje in ganta, one day zamu je tare as a couple” na ture maganar gefe nace “baka kuma fada min ba, tuwo na na ranar nan, ka ci? Na jima ina son inji ko kaci ko baka ci ba” sai naga ya bata rai kamar ba zaiyi magana ba sannan yace “naci, sai da safe amma. I drove throughout the night” Muna cikin hira aka kira shi da kamar ba zai dauka ba kuma sai ya dauka yana cewa “Inna ce” naji sun gaisa sai yace “ina gidan ma. Okay bara in fito sai inzo” na yi masa alamar tambaya da hannuna sai yace “Inna ce tace inje in same ta a gidan Kawu Isa” ina jin haka nasan magana tace, amma ya inna zata yi min haka bayan mun gama magana da ita na roke ta kar ta shiga maganar? Sai dare inna ta dawo. Bata ce min komai ba sai ta shiga harkokin ta nima kuma ban tambaye ta ba amma sai na kira Sadauki na tambayeshi. Ya kukayi a gidan Kawu Isan?” Yace “babu komai. In tayi tsami zakiji ne ai” amma ni kuma ai bana son tayi tsamin. Nafi so in samu maganar a fresh dinta yadda zan iya tackling dinta. Amma Sadauki yaki gaya min. Da weekend Murjanatu ta koma gida. Sai naji duk babu dadi saboda na saba da ita a kwanakin da tayi a tare damu. Bayan tafiyar Murjanatu kamar yadda nayi wa Subay’a alkawari na shirya ta muka tafi central prison gurin Saghir. Amma sai da muka samu ganin sa sannan nayi nadamar zuwa gurin cos it really broke my heart to see him a wannan condition din. Ya rame sosai fatarsa tayi baki ta lalace. Yayi datti. Uniform dinsa na prisoners wandon ya yage daga gwuiwa. Sai na tuno wancan Saghir din dan gayu mai iya daukar wanka da kwalliya yana kyalli kamar tarwada.1 Ya dauki Subay’a ya daga ta sama ya rungume a jikinsa irin yadda yakeyi mata a gida. Sai ta kankame shi tana cewa “Daddy ka dawo gida gurin mu dan Allah” ya sauke ta yana lakuce mata hanci yace “Daddy zai dawo gida kinji princess, ki ringa yiwa Daddy addu’a kullum in kika yi sallah” sai ya juyo yana kallona yace “look at you. Kinyi wata kiba kamar wata Hajiya. Me Inna take baki kike ci ne?”2 STORY CONTINUES BELOW Sun jima suna hira shida yarsa, tana bashi labarin sabuwar makarantar ta da sababbin kawayenta. Sai da zamu taho yace “Diyam ya labarin alkawarin mu? Wannan alkawarin da kika yi min shi kadai ne yake keeping dina going a gurin nan. The hope that one day zan fita shi yasa har yanzu banyi loosing sanity dina ba”. Na dauka Subay’a zatayi kuka amma sai naga bata yi ba. Muna zuwa gida tace min “Daddy yace zaki saka uncle Sadauki ya fito dashi ko?” Nace “mommy da uncle Sadauki zasuyi iyakacin kokarin su, amma sai kinyi min alkawarin kin daina maganar, ba zaki kara yiwa kowa maganar ba kuma ba zaki kara yin kuka ba”. Da yammacin ranar nayi baki. Kawu Isa aunty Fatima da Mama. Ina ganinsu naji hankalina ya tashi dan nayi guessing maganar data kawo su. Basu jima da zama ba sai ga Sadauki shima yazo, naji haushinsa for not telling me abinda ake shiryawa. A gaishe su, shima ya gaishe su sannan sai na gaishe shi sama sama. Kawu Isa ya fara magana. “Diyam innarki ta same ni da maganar ki da yaron nan. Tace yazo yana neman aurenki amma ke kin dauko wasu sharadai marasa tushe kin gindaya masa. Menene dalilinki nayin hakan?” Na dago kai ina son hada ido da Sadauki amma ya sunkuyar da kansa. Na fahimci lallai ni ake jira inyi magana amma kuma ban fahimci me ake so ince din ba. Shin wai su basa ganin abinda nake gani? Sai dai na fahimci akwai banbanci a tsakani na dasu, su basu san gadar zaren da Sadauki ya saka wa Saghir ba, su basu san maganar siyan gida da motar Saghir da Sadauki yayi dan ya taimaka wa Kabir wajen guduwa da kudin da Saghir ya sata ba. Nace “ni ba cewa nayi bazan aure shi ba Kawu. Ni cewa nayi ya yafewa Saghir kuma ya taimaka masa yayi clearing case din drugs dinsa” Mama ta kara da cewa “Sannan kuma ya bashi aiki ko?” Sadauki yayi sauri ya dago kai ya kalle ni, shi baisan da wannan part din ba ma. Nayi niyya ne sai Saghir ya fito sannan zan gabatar masa da wannan kudirin. Na dauke kaina daga kallonsa yayinda Kawu Isa ya rufe ni da fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Ni mamaki yake bani sosai musamman saboda nasan ba wai dan zumunci yake yin wannan abin ba, yana yi ne dan ya batawa Alhaji Babba rai kuma dan ya tabbatar da zaman Saghir a prison saboda abinda yayi wa suwaiba. Sai na tambayi kaina “anya kuwa akwai family din daya kai namu lalacewa?”2 Sai daya gama yi min fadan sannan yace “kuma yaron nan yana iyakacin kokarin sa gurin ganin an fito da Saghir, jiya ma sai da muka je tare dashi har ofishin commissioner of police, kuma sun gaya mana suna iyakacin kokarin su akan maganar amma akwai rudani a cikin maganar sosai. Sunce zai fito amma sai ya dauki lokaci” Ya juya yana kallon Sadauki yace “shekara nawa ma suka ce mana?” Sadauki yayi gyaran murya yace “drug case is complicated. Kamar five years haka zuwa sama. Amma zai fito”. Mama tace “to alhamdulillah. Wanda ake tunanin ya tafi kenan kuma aka zo aka samu sassaucin da har za’a saka ran fitowarsa? Ai babu abinda zamuyi sai godiya ga Allah. Kai kuma Sadauki Allah ya biya ka” suka ce ameen. Aunty Fatima tace “ai wannan commissioner Ahmad Muhammad yana kokari sosai” suka ci-gaba da hirarrakin su yayinda ni kuma hankali na ya tafi wani gurin daban. “Ahmad Muhammad” a ina nasan wannan sunan? Na dago kai muka hada ido da Sadauki sai na tuno inda nasan sunan and everything become clear to me. Ahmad Muhammad shine babban abokin Sadauki wanda suka taba zuwa min visiting makaranta tare, Ahmad Muhammad da yace bashi da buri irin yaga ya zama commissioner of police dan ya kama yan iskan gari ya rufe su a cell. That Ahmad Muhammad. Sai na tuno da kamun Saghir na farko, lokacin da aka je bail dinsa akace wai commissioner yace kar a bada bail dinsa. Sai nayi realising cewa Sadauki yana playing Kawu Isa ne, wato ya dauke shi ya kaishi office din abokin sa sun hadu sun ninke shi a bai bai da maganar cewa suna iyakacin kokarin su bayan kuma babu wani kokarin da suke yi. And I realized with a sinking feeling that Sadauki bashi da niyyar fito da Saghir. “Ahmad Muhammad” na maimaita a fili. Duk suka juyo suna kallona sai muka hada ido da Sadauki a take kuma na fahimci cewa ya gane cewa na gane abokin sa ne. Nace “shekara biyar ko? Allah ya nuna mana shekara biyar din. Kawu kuyi hakuri kuyi min afuwa ku barni in tafi karatu, kafin shekara biyar din na dawo insha Allah. A lokacin in Saghir din ya fito sai ayi maganar auren”.7 STORY CONTINUES BELOW Gaba-daya suka yo kaina da fada, har bama na jin abinda suke cewa ni kuwa na sunkuyar da kaina. Su basu san cewa decision din yafi yi min zafi a kansu ba amma dole ce ra saka ni. Sadauki bashi da niyyar fito Saghir bana jin kyma zai fito dashi ko da kuwa bayan na aure shi dinne. Option dina daya a lokacin shine inyi relying da son da yake min in hana shi cikar burinsa na aure na har sai ya warware daurin dayi da hannunsa.7 Fada suke tayi min har saida Sadauki ya koma basu hakuri, inna kamar zata dake ni tana cewa “ya fasa auren naki to, aurensa zaiyi ya rabu dake. Yarinya sai shegen taurin kai” Aunty Fatima tace “ikon Allah, wai kamar ba Diyam din da take ta kuka an raba ta da Sadauki ba ce ba, yanzu kuma ita ake cewa ta auri Sadauki tana ki” Ni kuma bana son in bayyana musu gaskiyar laifuffukan Sadauki saboda bana son in bata shi a wajensu. Gwara ni in dauki laifin shi kuma ya zauna fes. Washegari da safe Sadauki ya kira ni a waya. Da kamar ba zan dauka ba kuma sai na dauka dan inji me zai ce min sai yace “Oxford din ce kenan” na danyi tunani. I need a break gaskiya, from Sadauki and from my family. Maybe in nayi nesa da Sadauki zaifi tabbatar wa cewa da gaske nake maybe rashina yayi breaking dinsa. Sadauki loves me, and that love shi nake relying on. Nace “Yes, Oxford din ce” ya danyi shiru sannan yace “na gaya miki tuntuni, I can’t do abinda kike fada. Ki bar maganar Saghir, he deserves halin da yake ciki” nace “deserves? Sadauki Allah ne fa kadai yasan waye yayi deserving kaza wate baiyi ba, Allah ne kadai yake judging mutane akan laifuffukan su ba wai mu bil’adama masu tarin laifuffuka ba, Saghir yayi laifuffuka na sani, Alhaji Babba ma haka, amma Allah shi zaiyi judging dinsu bamu ba. Me yasa ba zamu zamanto masu yafiya ba saboda muma Allah ya yafe mana?” Sai yace “Allah yana judging wadansu ta hanyar wadansu. Wanne department din za’ayi miki applying for?” Nayi shiru. I had been thinking about that for years na kasa tsayar da shawara sai a ranar da Saghir ya bani takarda ta, a ranar da na samu freedom dina, a ranar ne na yanke shawarar abinda zan karanta. Law.1 “Law” na fada masa. Yace “wow. But why law” nace “nayi tunani, kusan duk abinda ya same ni a rayuwa, tun daga auren dolen da akayi min har zamana a gidan sa da rabuwar mu ta farko da karbar Subay’a da yayi da farko. Duk wadannan sun faru ne saboda abu guda daya. Saboda rashin sanin yancin kaina da banyi ba. Alhaji Babba a both musulunci da kuma a dokar kasa bashi da right din yi min auren dole. Ko da mahaifin daya haife ni ne bashi da wannan right din sai dai zan iya yi masa biyayya dan in samu lada amma ina da option din cewa ‘no’. Zaman da nayi a gidan Saghir, wahalhalun da nasha wadanda suka yi kokarin lalata both rayuwata ta duniya da kuma ta lahira duk sun faru ne a saboda bansan yancin kai na ba balle in nemi rabuwa da Saghir, both matsayi na na musulma da kuma matsayina na yar Nigeria sun bani yancin zabin wanda nake so in zauna dashi a matsayin mijina, na tuna rabuwar mu ta farko lokacin da ya dauke Subay’a ya tafi da ita da irin halin dana tsinci kaina a ciki saboda rashinta, shima wannan duk ya faru ne saboda bansan yancina ba, ba kuma ni da courage din fighting for my right dan shari’a ni ta bawa rikon ƴata, ko da mutuwa nayi rikon Subay’a baya hannun Saghir sai dai a bawa Inna, wannan itace Shari’a ta gaskiya. Amma rashin sanin yancin kai da matan hausawan mu suke fama dashi shi yasa ake tauye musu islamic and constitutional rights dinsu”3 “Wannan shi yasa nayi deciding in karanta law, dan in samu damar tsayawa duk wata yarinyar da iyayenta ko marikanta zasu tursasa ta gurin auren wanda bata so, dan in tsayawa duk wata matar auren da take zaune da abusive husband kuma take son rabuwa dashi, dan in tsaya in tabbatar iyaye mata sun samu right dinsu da ubangiji da kansa ya basu na karbar rikon yayayensu a lokacin rabuwar aure ko kuma lokacin mutuwar miji. Wannan shine zai zama role dina a society” Yace “Masha Allah. I am very proud of you Diyam. Kuma ki sani ina tare dake tun daga farko har karshe”.1 Na fahimci cewa Sadauki shi ko a jikinsa da nayi suspending auren mu nace sai na gama karatu. Shi dai kawai in dai Saghir zai cigaba da zama a prison shikenan. Da nayi kokarin yi masa complain cewa bama so nake tunda bai damu da aurena ko rashin aurena ba sai yace “you have no idea how much I want to marry you. This is just a phase we are going through. Am sure zaki chanja mind dinki along the way, in ma baki chanja ba I will wait har ki gama din ki dawo”. Wato ni ina depending on son da yake yi min cewa zai sauko ya chanja shawara ya fito da Saghir saboda muyi aure shi kuma yana depending on son da nakeyi masa yana saka ran zan sauko in bar maganar Saghir muyi aure. Ni dashi aga wanda zai fasa. Ya gama nema mana admission, kuma mun samu successfully. Anan na fahimci cewa su ba yearly suke bada admission ba kamar in batches suke yi kuma mu namu session din zai fara ne January. Daga nan kuma sai ya shirya ya tafi yaje yayi one week a can ya dawo yace “all set, an samo muku apartment a kusa da school din an kuma ajiye muku mota saboda zirga-zirga. Abinda ya rage miki shine koyan driving” shi ya koya min, ya ajiye duk harkokinsa yake zuwa yana dauka na muna fita koyon mota kuma cikin kankanin lokaci na iya sosai. Zamu yi ta hirar mu amma da zarar nayi masa maganar Saghir zai dauke wuta in ba hakuri na bayar da kuma to sai dai mu dawo gida ranar ba za’ayi koyon motar ba. Shi yayi min komai na harkar student’s visa, muka je Abuja ni da shi da Asma’u. A embassy na UK na hadu da Judith itama tana neman student’s visa, daga gaisawa naji yarinyar ta kwanta min muka yi ta hira har na fahimci scholarship ta samu daga program na African Initiative for Governance kuma session din karatun mu zai fara tare ne. Sai na roki Sadauki ya karbar mana visar tare da ita sannan kuma nace mata in mun hadu a can tazo mu zauna tare a apartment din mu. Bayan everything ya zama set kuma sai na ji duk jikina yayi sanyi. Naji bana son rabuwa da gida, da Inna da Subay’a da Asma’u. Bana son rabuwa da Sadauki. Inna nasamu wadda har lokacin bata daina fushi dani ba akan kin auren Sadauki, nayi mata bayanin manufa ta akan hakan, na nuna mata nima bawai hakan naso ba sai dai hakan nake ganin shine dai dai, sai ta dan sauko, ta saka min albarka sannan tayi min nasiha a game da zaman da zanyi a can. Ranar tafiya Sadauki ne yazo ya dauke ni muka tafi airport, su kuma yan rakiya ta suka biyo mu a mota daban. A hanya babu wanda yayi wa wani magana a cikin mu har muka je muka yi packing sai kuma muka ci gaba da zama a motar. Can ya juyo yana kallona yace “can you promise me something?” Nima ina kallonsa nace “what?” Sai kuma yayi shiru kamar ba zai yi magana ba sannan yace cikin rikakkiyar murya “zaki tafi jami’a, Oxford, akwai mutane da yawa a can, maza, and you are very beautiful am sure some of them will ……. God, bazan ma iya fadar kalmar ba” nayi murmushi nace “soyayya? I won’t. Nayi maka alkawarin Halima ta Aliyu ce. In ba Aliyu ba kuma to babu wani namiji a gaba na” yayi dan murmushi yace “Allah yasa ki rike alkawarin nan. Dan ni yanzu am not sure about you anymore. Tsoro nake ji. Gani nake anya kuwa zan iya wannan zaman jiran kar inje fa zuciyata ta buga” sai nayi dariya nace “tsoro da girmanka” ya juyo and for the first time ya kama hannuna a cikin nasa ya rike yana kallona yace “let’s play a little game da zai making everything easier for everyone. Let’s make a bet” na girgiza kaina nace “ni kasan bana son wadannan games din naka fa” yayi dariya yace “tsoro kike ji? Tsoro kike ji kar kiyi failing?” Nace “kaima kasan ko sanda muke games din bana faduwa” yace “yes, kina winning, saboda ina barin ki kiyi winning dan kar kiyi kuka” sai muka fara musun cewa ba barina yake ba ni nake winning da kaina sai yace4 “let’s do this one mu gani. Yanzu in muka rabu a airport din nan in kika sauka a UK, through out your stay har zuwa sanda zakuyi hutu in dai har kika dauki wayarki kika kirani da kanki then nayi winning and I got to decide whether or not zan saki Saghir. In kuma baki kira ni ba har kukayi hutu kika zo gida then kinyi winning kuma zanyi duk abinda kika ce” Na dan tsaya ina kallonsa ina assessing maganarsa, yana kallona with a broad smile a fuskarsa, na dauke kai ina lissafi, yes it will make everything easy amma anya zan iya kuwa? Not talking to him for months bayan a yanzu bana iya kwana daya ba tare dana yi magana dashi ba? But the result is really worth it, amma kuma in na fadi fa? In na kira shi fa?. Na sake kallonsa naga har yanzu ni yake kallo yana murmushi with an unreadable expression a fuskarsa. Na girgiza kaina, it is too risky gaskiya. Sai ya langwabe kai gefe kamar abin tausayi, yana robbing palm dinsa a nawa yace “Please Diyam, shekara biyar tayi yawa. Ba kya tausayina wai ke?” Nayi saurin zare hannuna daga nasa ina yarfarwa kamar wadda wuta ta kona saboda wani blood rush da naji ya taso daga hannun nawa cikin seconds ya zagaye duk jikina. Cikin sarkewar murya nace “okay, okay. Na yarda. It is a deal” ya lumshe idonsa ya bude yana kallon yadda nake yarfe hannuna sai ya miko min nasa hannun yace “let’s shake on that” na boye nawa hannun a cikin hijab dina nace “nace na yarda ai, no need to shake kuma” ya daga gira yace “tsoro kike ji?” Sai na dauki handbag dina nace masa “goodbye Aliyu” yayi murmushi yace “till we meet again Halima”. Na fita da sauri daga motar ina harhada hanya, but I felt as if gangar jikina ce ta fito ta bar zuciyata a cikin motar. Nayi kokarin calming down kafin in karasa inda Asma’u take jirana rike da sobbing Subay’a. Na durkusa na rungume ta ina jin tafiyar duk ta fita daga zuciyata, tausayinta naje ji sosai zata zauna without uwa da uba kuma bayan duk suna raye. Sai da muka je bakin departure hall sannan na juya na kalli inda motar Sadauki take, har yanzu yana nan a zaune, bana iya hangoshi amma ina hango duhunsa. A smiled at him, waved my hand sannan na shige.+ Murjanatu ce ta tare ni a airport a Oxford. Muka tafi gida tare da ita, sannan washegari ita ta fara kaini school duk da dai itama bakuwar ce amma kasancewar ta fini wayewa da sanin kan al’amurra sai ya kasance ita tayi guiding dina har na kammala duk abinda ake bukata cikin nasara. I tot about Sadauki alot, tun a jirgi nake nadamar taking wannan bet din nasa but what is done has already been done, sai kuma naja damarar ganin cewa nayi winning dan mu samu nutsuwa gabaki daya ni dashi. Nasan shima burinsa shine yaci, kuma yana ganin kamar zaici din saboda yana ganin rauni na, and I decided to show him am strong. At first abin da wahala, musamman in naga kiransa ya shigo sai inji kamar in dauka amma nasan halinsa in na dauka zai iya cewa duk is part of the deal dan haka kiran nasa ma bana dauka. And it really hurts. Kullum babu fashi zai kira ni first thing in the morning, sannan ina dawowa daga school zai sake kira sai dai in naki dauka ya kira Murjanatu ya tambaye ta lafiyar mu ko kuma in muna bukatar wani abu. Kudi kuwa kamar ruwa haka ya sakar mana su, ina so in masa complain ince kudin sunyi yawa amma ina tsoron kar yace yayi winning. Most of the times in suna waya da Murjanatu sai in yi ta straining kunnena wai dan in jiyo muryarsa, wani lokacin kuma shi da kansa zai ce ta saka a handsfree yayi ta yi min magana amma sai in ki yin maganar duk a tsoron kar yace yayi winning “please Diyam, please, please kiyi min magana” amma na daure na cije na cigaba da ignoring dinsa hoping wannan ta zama karshen wahala ta. Gani nake yi taimaka wa Saghir da nake so yayi shine zai gyara image dinsa a gurin family dina, kuma ina hopping hakan ya zamanto sanadiyyar daidaituwar al’amura a cikin family din. And Subay’a. Ina so in aure na ya kasance Sadauki Subay’a ta rike shi a matsayin uba ba wai matsayin enemy ba, wannan shine zai tabbatar da zaman lafiya a tsakani na da shi. Sannan taimaka Saghir zaiyi softening heart dinsa ya zamanto mai yafiya ga wanda ya munana masa sannan mai tausayi ga na kasa dashi, wannan kuma zai kara kusantashi da mahaliccin mu. Dan haka ni a ganina duk abinda nake yi ina yinsa ne domin Sadauki. And then he tricked me into calling him and also found out about Bassam. And now he is angry. Nasan kishi yakeyi dan nasan yana da kishi sosai, ni kuma har cikin zuciyata ba wai ina kula Bassam bane saboda wata alaka ta soyayya, na fara kula shi saboda in goge haushina da yake ji, and we became friends, sai kuma na lura cewa shi Bassam din ya fara developing feelings for me wannan shi yasa nayi deciding in yanke alakar mu tun kafin abin yayi nisa but the decision was made late, dan already Sadauki yasan maganar Bassam ba kuma na son yazo yayi wani abinda ba dai dai ba. Ban kashe wata wutar ba bana son a kunno min wata. STORY CONTINUES BELOW Wannan ne yasa na yanke shawarar bawa Bassam labari ne dan ya fahimci dalilin yanke alaka ta dashi, dan yasan waye Sadauki da kuma alaka ta dashi, sannan kuma ina hoping labari na zai taimaka masa wajen solving family issue dinsa kuma maybe zai iya bani shawarar yadda zan bullowa crises din Sadauki da Saghir. (Now, some people need to re-read episodes 1-10. Diyam is in love with wanda yake kiranta. Kuma ba labari take bawa Bassam ba, she is going over the story a kanta kafin ta bashi. Lol)7 Bassam yace “ina jinki. Ina so inji labarin naki” ta dauke idonta daga kallon ruwan da yake tsiri a fountain, sai ta samu kanta da yin murmushi ganin yadda ya nutsu yana kallonta, tace “ba labari ne mai dadi sosai ba, and get your hanky ready cos you might cry at some point” yayi murmushi amma baice komai ba sai ta bashi labarin ta in summary, asalinta, soyayyar su da Sadauki, mutuwar su Baffa, aurenta da Saghir da yadda sukayi rayuwar auren tsahon shekaru, dawowar Sadauki cikin rayuwarta da kuma mutuwar aurenta ta farko data biyu. Ta bashi labarin a takaice but without missing all the main points da zasu saka ya gane manufarta sosai. Sai kuma ta gaya masa winning din da Sadauki yayi da kuma text din da yayi mata dazu akan Bassam din. Tana bashi labarin yana yi mata tambayoyi a gurin Baiyi kukan ba kamar yadda ta tsokane shi da, amma idonsa yayi ja fuskarsa ta nuna bacin ransa akan abinda ya faru da ita, abinda bai taba tsammanin yana faruwa a kasar sa har a yanzu ba. Ya kuma jinjinawa jarumtarta dan he can’t even imagine a girl of 14 years going through what she went through. But his heart breaks daya fahimci karfin soyayyar da take tsakanin ta da Sadauki. Yes, da gaske ya fara jinta a zuciyarsa har yana hoping alakarsu will lead to something da zai fitar da khausar daga zuciyarsa. But daga labarin ta ya fahimci cewa cigaba da rike soyayyar ta a ransa will be a wrong move. She is already in love, deeply in love with someone else, just like Khausar. Ta katse masa tunanin sa ta hanyar cewa “ina fatan ka fahimci duk abinda nake so ka fahimta” ya gyada kai yace “na gane, sosai. Kuma bana jin da akwai wata kalma da zan iya furta miki wadda zata nuna how sorry I am akan abinda kika yi passing through a rayuwarki. It was unfortunate. Kuma bazan iya misalta miki how happy and how important I feel right now da har kika zaunar dani kika bani wannan labarin. Naji dadi sosai, na karu sosai, nayi wa rayuwa kallon da ada ban taba yi mata irinsa ba” tace “thank you, thank you for understanding Bassam” ya sake murmushi yace “nine da godiya, you have no idea how this is going to change my life. My family, I have been taking them for granted duk da irin kauna da kulawar da suka yi kokarin gina min rayuwata a kai, a lokacin dani nayi watsi da supportive family dina nayi kokarin rusa zumuncin dake tsakanin mu saboda budurwar da bama ta sona a lokacin ke kuma kike against mutumin da ya ke miki soyayya ta gaskiya irin aliyu saboda family din da suka yi everything possible dan ganin sun rusa rayuwar ki. You truly are an angel. I now understand the real value of my family, kuma zanyi iyakacin kokari na inga na gyara kuskure na. And like you said, story dinki ya kara nuna min ma’anar true love, it is not feelings like I said. It is much more than that, true love means sacrifice. Kayi sacrificing happiness dinka dan wanda kake so yaji dadi, ka sa farin cikin wanda kake so a sama da naka. Na koyi wannan daga Aliyun ki kuma nima zanyi applying dinsa a case dina da khausar, ina sonta dan haka zan dora happiness dinta a saman nawa, happiness dinta kuma shine kasancewa tare da wanda take so. Am going to let them be, and hope to find my one true love nima watarana”. Tayi murmushi tana jin tausayinsa a ranta, tasan so tasan zafinsa dan haka tasan decision din nasa is not an easy one. But it is for the best. Tayi ajjiyar zuciya tare da gyara zamanta tace “to saura ni. Ina so inji menene view dinka a game da sharadin dana kafawa Sadauki” ya girgiza kai yace “ni a fahimta ta, daga ke har Aliyu kuna kan gaskiyar kune, dan haka sharadin da kika kafa masa from your point of view dai dai ne. But where you are wrong is on the approach, hanyar da kike bi wajen ganin yayi abinda kike so ne ba tayi dai dai ba. Mu maza a yadda Allah ya halicce mu shine bama son ake directing din mu, do this, do that. Wannan hikima ce ta ubangiji sai ya saka mu as heads of the family mata kuma yace kuyi submitting to us. Amma inda hikimar take shine indai mace tabi namiji sau da kafa yi nayi bari na bari to zata juya shi ba tare da shi yasan tana juya shi din ba. Musamman ace idan yana sonta. Duk mijin da zaki ji ance mijin tace to shi bai san ma yana yin abinda mutane suke tsegumin ba. Irin son da Aliyu yake miki if you submit to him ba fito da Saghir kadai ba, in yana da dama zai iya fito da duk mutanen prison for you”.6 Ta jinjina maganar sa, Mama ta taba fada mata something similar to this, tace in ta nuna wa Sadauki soyayya zaiyi duk abinda tace but ita a ganinta ai tayi ta fada masa tana maimaita masa cewa tana sonsa kuma gashi nan har yanzu baiyi abinda take so din ba. Sai tace “yanzu me kake ganin ya kamata inyi?” Ya daga kafada yace “Marry him. Aurensa kawai zakiyi to make him feel loved, pamper him, take good care of him, ki tabbatar masa da cewa you are his and his alone kuma ki daina o da mentioning sunan Saghir then shi da kansa zai dubi yarinyar da take tsakani ya sake shi ba tare da kin furta hakan ba”.3 Ayi hakuri da wannan. A kuma yi hakuri da jina shiru kwana biyu, abubuwa ne suka cushe min but insha Allah in komai ya warware za’a cigaba da jina akan kari. Ta tsaya tana kallon sa for some seconds. Sai kuma tayi murmushi very brightly sannan tayi dariya, shima dariyar yayi and they laughed together sannan tace “thank you Bassam. Nagode sosai” yace “no, thank you. Nine da godiya” wayarsa tayi kara ya dauko ta yana duba prayer alarm dinsa, lokacin magrib yayi. Suka mike a tare sannan suka jera suna tafiya suka bar garden din, taking their steps together kamar yadda suka shigo but unlike yadda suka shigo kowa rai a bace yanzu da zasu fita kowa a cikinsu murmushi yake yi. A bakin kofa ya tsaya yace “wait a minute, naji kince Umar Mustapha Abatcha, Umar Abatchan dana sani kike nufi ko kuma wani daban?” Tayi murmushi tace “shi din dai da ka sani, do you know him personally?” Ya girgiza kai yace “sunanshi dai na sani. But the son, ya taba zuwa gidan mu ones. Last year lokacin auren Ya Ameen Daddyn mu ya gayyaci father din sai bai samu damar zuwa ba but he sent the son to represent him. Ko gaisawa ba muyi ba amma zanso mu gaisa wata rana” Diyam tace “am sure shima zai so haduwa da kai” sai kuma tayi murmushi ta kara da “idan ya huce”. Yayi murmushi yana kallonta yace “goodbye Halima” tayi murmushi tace “see you soon Sadiq”. Sai ta juya ta tafi shi kuma ya tsaya yana kallon bayanta, sai kuma yayi murmushi yana girgiza kansa yana tunanin irony din rayuwa.+ Duk wanda ya shigo rayuwarka da akwai dalilin shigowarsa, some enter your life to teach you a lesson, some to take lessons from you, some enter to help you and some to accept a help from you. Duk wanda ka hadu dashi to ya shigo rayuwar ka ne for a reason. Da akwai point din da zaka hadu da mutum akwai kuma point din da zaka rabu dashi bawai lallai dan bakwason juna ba sai dan role dinku to each other ya kare. The only person that will stay from start to finish in your life is YOU and YOU are the only person responsible for your happiness.2 People are not perfect, nobody is, so if you truly love a person you just have to accept him/her the way s/he is, accept both the good and the bad sides of them and together you can bring out the best in each other.2 Ya juya da sauri ya koma cikin hotel din sannan ya hau zuwa dakinsa. Yana zuwa ya fara gabatar da sallah sannan ya jawo jakarsa ya fara zuba kayansa a ciki. It is time for a change a rayuwarsa, Nigeria zai tafi ya gyara rayuwarsa but before that he have to pay a visit to his Aunt first, yasan haduwarsu ba zatayi masa dadi ba but dole yayi clearing mess din da yayi creating da kansa. Diyam tana zuwa gida itama sallar ta gabatar sannan ta tsaya a gaban mudubi tana practicing yadda zata fuskanci Sadauki gobe. Tasan akwai battle a tsakanin su dan ta tabbatar da daurarriyar fuska zai sauko daga jirgi. Sai ta fara making faces a mudubi tana zabar wacce zata fi melting frozen heart dinsa. Ta gwada fuskar tausayi, ta gwada fuskar shagwaba ta kuma gwada serious face amma duk sai taga basu yi mata ba. Ta binciko kaya tana zaben wadanda zata saka saka suma kuma taga duk basu yi mata ba, ta tuna ranar nan a Kano da Murjanatu tayi mata kwalliya ya yaba sosai dan haka gobe ma zata saka ta tayi mata. And she is going to wear dogon hijab kamar yadda yake so. Ta ajiye kayan ta fita da sauri zuwa dakin Murjanatu, ta tarar da ita tana waya sai ta tsaya har ta gama sannan tace “Murjanatu Please zo ki taya ni zaben kayan da zan zaka” Murjanatu ta ajiye wayar tana kallonta, sai kuma tayi murmushi tace “kayan da zaki saka yaushe? Biki zaki je?” Diyam ta harare ta tace “kakan biki ba biki ba. Malama ni fa yayarki ce kuma am ordering you to do something for me” Murjanatu ta hade hannayenta tace “to babbar yaya tuba nake yi, tunda yaya na za’ayi wa kwalliya dole in tashi”. Haka sukayi spending the night preparing. Har takalmi da sarka sai da aka ware. Sannan suka yi plan din abincin da zasu dafa masa. Tuwo dai yafi so miyar yauki amma basu san inda zasu samo ingredients din ba dan haka Diyam ta yanke shawarar dafa masa farin couscous garnished with vegetables sannan kuma suyi masa farfesun kifi sai kuma suyi pepper meat. Drink tasan yana son kunun aya amma bata da aya dan haka zata yi masa banana smoothie. STORY CONTINUES BELOW Ta kira shi da niyyar tambayarsa sanda jirgin su zai sauka amma kamar yadda tayi tunani sai yaki picking, tayi masa text babu reply. Ta saka Murjanatu ta kira shi itama yaki dagawa duk sai taji babu dadi, shi wannan zuciyar tasa ce problem dinsa, yana da saurin hawa amma kuma yana da saurin saukowa dan haka ta shirya sauko dashi goben in yazo. Ta lura Murjanatu duk ta daga hankalinta sai ta zaunar da ita tace “kar ki wani damu kanki da fushinsa, zai sauko na gaya miki ki barni da shi kawai” Murjanatu tace “baki san halinsa ba, zai iya raba ni da makarantar nan fa wallahi. Akwai abinda ya taba yi min a gida Canada akan wani saurayi na an gaya masa bad abubuwa akan sa sai yace min kar in kara kula shi ni kuma na cigaba da kulashin. Ashe yasa a saka masa ido a kaina sai gashi an tura masa da videon mu tare a gurin cin abinci. Ba wani abin muke ba kawai muna hirar mu muna dariya. Akan haka ya karbe wayata kuma yayi grounding dina a gida for three months ko kofar gida bana fita. Papa da Mama kuma suka biye masa yanzu ma kuma nasan duk abinda yace biye masa zasuyi” Diyam tace “ba zai ce komai ba, ki barni dashi”. Suka duba suka tabbatar suna da abubuwan da suke bukata, abinda basu da shi kuma sai sukayi order online da niyyar a kawo musu da sassafe. Sai kuma suka shiga website din airport suka duba flights schedules na gobe, anan suka ga time din da jirgi zai sauka from Nigeria. Sai yamma. Wannan yasa suka yi baccinsu sosai sannan suka tashi a tsakane suka yi komai tare har da Judith itama ta taya su, suka ci abincin su sannan suka yi wanka aka zauna kuma yin kwalliya a shafa wancan a goga wannan a ja wancan suna ta rigima har aka gama sannan aka yi dressing aka kuma bi da turare. Murjanatu ce ta dauko hijab da kanta ta bawa Diyam tace “gwara ki saka tun kafin yayi ball damu tun daga airport har gida”. Tare suka tafi airport din a mota, suka bar Judith a gida tana gyara musu gidan. A hanya duk sukayi shiru kowa tana lissafe lissafen ta sannan Diyam tace “Murjanatu a tunanin ki ta yaya Aliyu yasan ina kula Bassam?” Murjanatu ta daga kafada tace “yaya Aliyu ne fa, ya iya bincike ta karkashin kasa I guess wani ya saka ya saka masa ido akan mu. The guy might have saw you two together and reported to him” Diyam tayi shiru tana tunani, she will have to talk to him about that, hakan kamar rashin yarda ne. Murjanatu ta katse mata tunanin ta ta hanyar cewa “there is nothing between the two of you, is there?” Diyam ta harare ta tace “in kina son shi just say so, sai in hada ku” Murjanatu ta tabe baki tace “bai yi min ba, he is definitely not my type. Daga ganin sa nasan lady’s man ne, Allah kadai yasan yawan yammatan sa” Diyam tayi dariya tace “wai dama kura tana iya cewa da kare maye? Ke ma Allah ne kadai yasan yawan samarinki” Murjanatu ta yi murmushi ta fara bata labarin new catch din da tayi a school last week. Suna tsaye suna jira jirgin ya iso, Diyam tana ta jujjuya hannun ta feeling nervous dan bata san da wacce zai zo ba sannan kuma ga zuciyarta da take neman betraying dinta saboda dokan tuwa da tayi gurin son ganinsa after almost three months of not seeing him. And then suddenly sai idonta ya sauka a kansa, yayi kyau sosai fuskarsa tayi fes gashinsa na fulani da sajensa sun kwanta lufluf suna daukan ido. The freshness of his dark skin alone zai tabbatar maka da cewa he is taking good care of his body, yanayin takunsa kuma da posture dinsa sun nuna yawan ziyarar da yake kaiwa gym. Their eyes locked, and everything in her stopped except bugun zuciyarta da yayi doubling. He walk straight to gabanta ya tsaya one hand inside pocket, his expression unreadable yace “hello Madam”. Ta bude baki zatayi magana amma sai taji duk rehearsal din da tayi na abinda zata ce masa ya gudu ya barta. Yayi mata kwarjini da yawa, and the fact that he called her madam have added to that. Sai ya dauke idonsa daga kanta ya mayar da dubansa kan Murjanatu da take kusa da ita tana mishi murmushin dole, suna hada ido tace “sannu da zuwa yaya, ya flight din?” “Fine” yace mata in short sannan ya zagaye su yayi hanyar fita, Murjanatu taja hannun Diyam da sauri suka bishi a baya. Suna fita suka ga cab tayi packing a gabansa Murjanatu tayi saurin cewa “ga mota munzo da ita fa” ya juyo yana kallon Diyam yace “thank you” sai ya shige suka ja suka barsu a wajen. STORY CONTINUES BELOW Murjanatu ta juyo tana kallon Diyam tace “you kept quiet, me yasa zaki yi shiru?” Diyam tace “he called me Madam. Kin san kuwa yadda nake jin haushi in yace min Madam?” Murjanatu tayi dariya tace “to menene na jin haushi? In yace miki Madam sai kice masa Sir, ba shi kenan ba? Now we have to follow him kuma” suka shiga mota suka bi bayan cab din data dauke shi but sai suka ga sunyi wata hanyar daban ba hanyar gidan su ba, Diyam zata yi magana Murjanatu tace “gidan Papa zashi. Inda muke sauka in munzo gari” sai Diyam ta juya kan motar suka yi hanyar gidansu. Murjanatu tace “ba binsa zamuyi ba?” Diyam tace “we cooked for him, dole kuma yaci abincin da muka dafa”. Suna zuwa gidan Murjanatu ta shiga ta hado kan girkin da suka yi masa ta jera a babban basket sannan ta dawo motar suka kama hanyar wajen gari inda anan ne gidan yake. Suna packing Diyam ta tsaya tana kallon gidan a ranta tace “wow, da gaske dai Umar Mustapha Abatcha ne ya haifi Sadauki” ba mutane a gidan sai security daya bude musu gate suka shigo, amma komai na gidan tsaf yake daga alama ana zuwa aba gyaran gidan akan kari. Kofar da suka hango a bude suka dosa, suka shiga wani palo madaidaici Diyam tana iyakacin kokarinta na ganin bata yi kauyanci ba. A kan dining suka hango shi yana zaune yana kallon kofar da suka shigo. He kept his eyes on them har suka karaso Murjanatu ta ajiye basket din hannunta ta gaishe shi ya amsa tare da tambayarta karatu, sai kuma tace da Diyam bara taje ta dubo wani abu a cikin gidan. Sai data fita sannan Diyam ta dauke idonta daga kansa ta sauke kan wata baturiya sanye da apron da hular cooks tana ta jera abinci akan dining table din gabansa. Diyam ta tako ta karaso gurin tana kallon baturiyar tace “thank you, I will take it from here” sai matar ta juya tana kallon Sadauki shi kuma ya yi mata alamar ta tafi da hannunsa sai ta juya ta bar gurin. Diyam tabi bayanta da kallo tana jin haushinta ba tare da matar tayi mata komai ba. Sai kuma ta fara tattare abincin kan table din tana ajiyewa gefe sannan ta dauko basket din da suka shigo dashi ta dora akan table din ta fito da abincin ciki ta jejjera sannan ta jawo kujera kusa dashi ta zauna. Tunda ta fara yayi folding hannayensa yake kallonta har ta gama ta zauna sannan ta jawo plate gabanta tace “banyi maka tuwon da kake so ba saboda bani da kayan hadi. Amma nayi maka something da nake tunanin zaka so” still idonsa akanta yace “how is he” ta gane maganar da yake amma sai ta cigaba da hada abincin ta, carelessly tace “how is who?” Sai ta debo abincin a spoon ta kawo bakinsa tace “ha” and she saw his lips curved in a smile amma sai ya juya fuskarsa gefe kar ta gani sai ta sake bin bakinsa da spoon din tace “ha muga ni” sai ya langwabar da kai sannan a hankali ya bude mata bakin ta saka masa abincin a ciki sai ta zauna tana kallon sa with wide opened eyes shi kuma yana taunawa a hankali sannan tace “please tell me yayi dadi. I spent hours ina shirya maka abincin nan kamar yadda nayi spending hour ina yi maka kwalliya amma gashi nan ko yaba wa ba kayi ba” ta karashe maganar kamar zata yi kuka. A hankali yace “waye yace miki ban yaba ba?” Ta turo baki tace “you called me Madam, kuma kaki shiga mota ta” ya danyi murmushin daya tsaya a iyakacin idonsa yace “to ba Madam din bace ba ke?” Tace “I am not Madam, in ka kara gaya min kuma nima Sir zan ke ce maka” and his smile widen to his lips. Ta sake dauko wata lomar ta kuma cewa “ha” ya bude ta saka masa yana ci ya kuma cewa “how is he?” Ta gyara fuskarta zuwa serious one tace “kana magana akan Bassam ko?” Ya daga kafada yace “bansan sunansa ba and I don’t want to know” tace “he was fine as of yesterday, bansan ya yake yau ba. Kamar yadda bansan me yasa kake wani tunani akan sa ba. He is just my friend, department din mu daya muna lectures tare and he is a Nigerian” ya bata fuska yace “shi yasa kuke cin abinci tare?” Ta saka masa wata lomar a baki sannan tace “and how do you know that? Wani ka saka yake spying on me? Baka yarda dani ba?” Yace “babu wanda na saka yayi spying on you. Akwai mutumin da muka yi harkar admission da registration dinku tare. He saw your pictures then. A lokacin kuma na gaya masa ke matata ce then he saw you with that boy and thought ya kamata in sani. I told him bake bace ba cos I thought you would never do it sai ya tura min da picture of you two together” ta ajiye spoon din hannunta tana kallon yadda fuskarsa take nuna bacin rai, yace “do you like him?” Ta dafe kanta tace “I just told you, Bassam is my friend. Na bashi labarin ka ma na gaya masa zaka zo yau kuma har cewa yayi zai so ku hadu. There is nothing there. Please stop looking for something that isn’t there” she saw him relax a little yana kallonta yace “he is handsome” tace “really? Ni ban gani ba. He may be one of the thousands of stars in the sky amma ni duk bana ganinsu, only one star shines brightly a ido na, you. Kai kadai nake gani a matsayin mai kyau sauran duk dusudusu nake ganin su. You are the only star in my sky”. And he smiled. This time genuine smile yayi mata ya lumshe idonsa ya bude yace “I always remember that night duk sanda naga starry sky” ta sunkuyar da kanta kasa tace “me too”.2 Sai ya saka dogayen fingers dinsa guda biyu ya dago fuskarta yana kallon cikin idonta yace “feed me” ta hadiye wani abu a makogwaron ta amma taji yaki tafiya, sai ta yi sauri ta dauke idonta daga cikin nasa ta dauki spoon with shaking hand ta cigaba da bashi abinci. Bai kuma magana ba sai ido daya tsare ta dasu har sai da ta tabbatar ya koshi sannan ta bashi drink ya sha sai kuma yace “thank you, this is the best food I have tasted for a while. Ko kuma yadda aka bani abincin ne ya saka naji yafi kowanne dadi?” Sai kuma ta danji kunya ta rufe fuskarta da bakin hijab dinta, suddenly sai taji babu abinda take so irin ta kuma jin wannan kalmar daga bakinsa but as her husband yadda zata ji dadi fiye da na yanzu kuma ta samu lada mai yawa. Sai ta zame daga kujerar da take zaune ta durkusa a gabansa tana kallon yadda yake kallonta da mamaki tace “Aliyu Umar Abatcha. Will you do me the honor of marrying me?”For two seconds ya zauna yana kallonta da tsantsar mamaki a fuskarsa sai kuma yayi sauri ya mike tsaye ya kamo hannayenta duk biyun ya mikar da ita tsaye yana kallonta tana murmushin ganin duk yadda yabi ya rude sai yace cikin saurin murya “No! No”. Ta bude ido da mamaki tace “no?” Sai ya saki hannunta da sauri ya dafe kansa yace “ba wannan no din ba, I mean no karki durkusa please, karki bata kayanki” ya fada yana ciwo hanky da sauri ya kama goge mata hijab dinta, sai daya dago sannan ta daga gira tace “so? Yes ne ko No?” Maimakon ya bata amsa sai ya dora goshinsa a kafadarta, tana jin yadda ya sauke wata nannauyar ajjiyar zuciya wadda tasa hawaye ya gangaro daga idon Diyam sannan yace can kasan makoshinsa “Yes Diyam. Of cause I will marry you. You have no idea how much I want to marry you”5 Murjanatu ta bude kofa ta shigo, sai kuma ta tsaya tana kallon su sannan tace “wrong room. Ba nan zan shigo ba” sai ta kalli kofa tace “Na’am!” Ta juyo tace “they are calling me so I gotta go” sai ta juya da sauri ta fita. Diyam tayi dariya tana share kwallar idonta tace “she is funny. Babu wanda yake kiranta” ya danyi dariyar da Diyam taji vibration dinta a kirjinta yace “kika sani ko aljanun gidan ne suke kiranta?” Ta dan matsa baya forcing him to raise his head from her shoulder. Sai ya kalle ta da idon da suka fara chanja color yace “yaushe kika chanja shawara kuma? What about Saghir? Kin fasa fitar dashi din?” Ta zauna a kujera tayi dagumi but fuskarta da murmushi tace “you won the bet, I can’t continue to deny myself freedom. Nayi kokari ai ko?” Ta fada da sanyin murya. Ya zauna opposite dinta yace “Subay’a fa?” Tace “in muka yi aure Subay’a ta zama yarka. And I trust you will do everything in your power to make your daughter happy” ya gyada kai yace “you bet. She is going to be the happiest girl ever”. Matar dazu ce ta shigo ta fara gyaran dining table sannan ta zo gurin su tana tambayar Sadauki in akwai abinda yake bukata in babu tana son tafiya. Ya sallameta ta tafi ya juyo yana kallon Diyam da take bin bayan matar da harara yayi murmushi yace “what?” Tace “fire her. Ita da wannan secretary din taka ta Kano” ya bude ido da mamaki yace “why?” Ta turo baki “ni bana son su” yayi dariya yana shafa kansa yace “and you accuse me of being heartless” ta bude hannu tace “sai ka basu wani aikin ai. Kai kuma ka samu maza suke yi maka irin wadannan aiyukan” yayi tagumi da hannu daya yana kallonta yace “yarinyar nan anya kuwa Baffa bada A’isha yayi miki huduba ba? Kishinki yayi yawa. Yanzu suna min aiki kince ba kya so, so tell me idan kuma kika gan mu tare muna cin abinci a cafeteria mai zaki yi? Hmm?” Ta gane inda ya dosa sai tayi saurin cewa “kayi hakuri, an gama ba za’a kuma sakewa ba” bai ce komai ba sai kallonta da yake tayi fuskarsa da murmushi. Ta jawo fuskar hijab dinta ta rufe fuskarta tace “ni kunya kake saka ni in kana kallona” sai ya koma ya jingina a jikin kujerar yace “kinsan tunanin me nake yi?” Ta bude fuskar ta tace “no” yace “tunani nake yi in koma airport a yau in koma Nigeria, gobe inga Kawu Isa jibi a daura mana aure in dawo gurin amaryata a jibin” tayi saurin mayar da fuskarta ta rufe tace “kai dan Allah. Ka dai bani lokaci in shirya dai ko?” Yace “wacce shiryawa kuma? Nasan a gida zasu ce zasu shirya wani abu amma koma menene sai dai su jira sai bayan na tare da amarya ta” sai ta mike da sauri tayi hanyar waje tana hada hanya tace “sai dai ka tare kai kadai” ya biyo bayanta yana cewa “dama ai ni kadai nake tarewa ta kullum on my empty cold bed, it is about time I get some warmth” ta karasa kofar da sauri tana hoping ba irin ta office dinsa bace ba. Tana murdawa taji ta bude ta fita tana raba idon inda zata hango Murjanatu, sai gashi nan ya fito shima ya rufe kofar ya jingina da jikin kofar ya harde hannayensa da kafafuwansa yace “run run little girl. Duk inda zaki je you will come back here” ya fada yana nuna kirjinsa yace “cos that’s where you belong. A heart belongs to the chest”.1 Ta juya suka hada ido, feeling like yau ta fara ganin sa. She couldn’t help but look at chest din daya nuna, very broad and very strong, sai taji babu abinda take so irin ta jita a gurin feeling the warmth and the strength that she so much miss. Ta hadiye wani abu tare da saurin girgiza kanta a kokarin ta na goge image din daga kanta tace masa “uhmmm. Lokacin Sallah. Murjanatu” yayi mata murmushin gefen baki sai ya nuna mata wata kofa da hannu” ta juya da sauri ta tafi can. Sai data bude kofar ta shiga sannan ta rufo kofar ta jingina da jikinta ta yi ajjiyar zuciya. Sai kuma tayi murmushi tana girgiza kanta. STORY CONTINUES BELOW Daga gefenta taji ance “hmmm. Wato da can anaso ana kaiwa kasuwa akeyi ko?” Ta juyo ta harari Murjanatu tace “ke nifa yayarki ce, bana son rashin kunya”. Anan tare sukayi sallah tare sannan suka fita Murjanatu tana zagayawa da ita gidan Diyam tana ta kashe kwarkwatar idonta. Komai na gidan abin kallo ne, exact lissafin da Diyam take yi na abinda ake cewa aljannar duniya. Suna cikin zagayen suka hadu dashi, yace da Murjanatu “thank you Fanna, zaki iya komawa daki” ta turo baki tana buga kafa amma yana yi mata wani kallo ta juya ta koma. Diyam tace “kai kuwa ka barta mana mu karasa” yace “a gabanta zanyi hira dake? Kina sone ma ta raina ni kenan” suka jera suka cigaba da tafiya tare, but ba kallon gida sukeyi ba hirar su kawai suke yi suna jin dadin iskar da take kadasu. Ta rungume hannunta tana jin sanyi amma bata son nunawa dan tana jin dadin hirar da yake yi mata, sai ya cire top dinsa ya saka mata, ya cigaba da bata labarin irin yadda ya yi ta kokarin ganin ta kira shi dan yayi wining amma taki. Yace “har halucination fa nake yi. In wani ya kira ni sai inga kamar ke. It was hectic. I almost lost it” tayi murmushi tace “kasan me? Wani lokacin sawa nake Murjanatu ta saka min kai a handsfree” ta fada tana rufe fuskarta, yace “laaa ila, that was cheating” ta bude fuskarta tana hararar sa tace “har zaka yi maganar cheating?” Yayi dariya yace “bature yace ‘nothing is fair in love and war”. A lokacin suka kai karshen gidan sai suka juyo suna retracing steps dinsu sai yace “sanda zaku taho Papa cewa yayi ku zauna a nan gidan, but sai na nuna masa cewa yayi nisa zaku ke shan wahalar transportation. But ni personally ba wai dan haka na samo muku wancan gidan ba, ni a ganina you are my responsibility kuma nan ba gida na bane ba bana son matar gidan ko sauran siblings dina suzo gidan suyi miki wani kallo, gwara can nawa ne babu mai daga miki kai” tayi murmushi tace “bansan sauran ba amma Murjanatu tana da kirki sosai” ya gyada kai yace “tana da kirki, suma duk basu da problem amma hausawa sunce maganin kar ayi kar a fara”. Sai da sukayi sallar isha sannan suka bar gidan. Zuciyoyin su tas kamar takarda. Suna zuwa gida sukayi wanka suka yi shirin kwanciya saboda duk sun gaji. Diyam ta kwanta tana bitar maganganun su da Sadauki. Yes, ta karbi shawarar Bassam, Sadauki baya son tana maganar Saghir dan haka ta daina amma bawai ta bar maganar bane ba, zata jira taga if he will come around and do the right thing da kansa. Watarta tayi kara ta dauka tana murmushi. Bai gaji da hirar ba kenan. Ta dauka da sallama yace “so nake in taho nan kin yarda?” Tace “nan kuma? Me zaka yi anan din?” Yace “hira zan yi miki kadai” tace “to kayi min a wayar mana, ai ina jinka a haka” yace “nafi son inke ganin ki as ina miki maganar. Nafi son in yi miki joke kiyi min murmushi in gani. Nafi son in tsokane ki ki harare ni in gani. Nafi son in fada miki sweet sweet words inga kin rufe fuskarki kina jin kunyata” sai taja abin rufa ta rufe fuskarta. Tace “ni dai kar kazo zuwa zakayi kayi ta sakani jin kunya” sai kuma tace “amma bada gaske kake ba zancen daurin aure jibi ba ko?” Yace “in da zan samu yadda nake so da ko gobe nema ina so. But nasan ba zan samu ba, Papa zai ce abokansa da sauran mutanen sa, Mama zata ce zasuyi biki, and you, I want you to have all the wedding things da baki samu ba ada. So, I will wait. Kinsan ni am a patient bird. Yanzu ki gaya min duk abubuwan da kike so for the wedding” ta lumshe ido tana tunanin childhood dreams dinta, but those are only dreams kuma yanzu sun zama past, dan haka tace “ni bana son komai fa. Sai dai ko in kai kana son wani abu” yace “ni ke nake so. I want only you, and that’s the only thing that matters” taji ta tamkar tana narkewa tana shigewa cikin katifar da take kwance. Is it possible to love someone this much?3 Suka cigaba da hirarsu mai ratsa zuciya, tana bashi labarin makaranta da yadda tayi adapting, shima yana bata labarin lokacin da yake tasa makarantar. She told him about Bassam abinda ya hada su da yadda rayuwar su ta kasance tare but sai taki gaya masa cewa Bassam ya fara sonta. She told him yace ya taba ganinsa yaje daurin auren brother dinsa. Sai a lokacin yace “Abuja? Last year you said?” Tace “eh” ya danyi tunani yace “naje daurin auren gidan sarki. Maybe can yake”. Sai da yaji alamar ta fara jin bacci sannan yace “kiyi addu’a ki rufe idonki. I will talk to you sai kinyi bacci saboda ina son kiyi mafarki na” Took my hand, Touched my heart, Held me close. You were always there, By my side. Night and day, Through it all. Baby, come what may. Swept away on a wave of emotion, Oh, we’re caught in the eye of the storm. And whenever you smile, I can hardly believe that you’re mine, Believe that you’re mine. This love is unbreakable. It’s unmistakable. And each time I look in your eyes, I know why.This love is untouchable. A feeling my heart just can’t deny. Each time I look in your eyes, Oh, baby, I know why This love is unbreakable. Shared the laughter, Shared the tears. We both know We’ll go on from here. ‘Cause together we are strong. In my arms: That’s where you belong. I’ve been touched by the hands of an angel. I’ve been blessed by the power of love. And whenever you smile, I can hardly believe that you’re mine. This love is unbreakable. Through fire and flame. When all this is over, Our love still remains. This love is unbreakable. (Lyrics by Westlife) Washegari Sunday, Diyam tayi baccin safenta sosai sannan ta tashi. Tana mikewa ta jawo wayarta ta tura masa message cewa tana gayyatarsa breakfast. Ta fita ta tarar duk su Murjanatu suma babu wanda ya tashi dan haka ta zarce kitchen ta fara shirya abinci. Tana cikin aikin Judith ta shigo suka cigaba tare har suka kammala sannan ta tafi ta tashi Murjanatu ita kuma ta shiga tayi wanka ta shirya sannan suka fito kusan a tare da Murjanatu. A palo suka hadu suka baje kayan breakfast suna yi sai gashi ya shigo. Suka gaishe shi gaba-daya ya amsa da sakakkiyar fuska tana bude warmers din gurin. “Me aka shirya mana ne?” Murjanatu ta tashi tana serving dinsa yayinda Judith tayi musu sallama ta fita. Ya jingina da kujera yana shan tea yana kallon Diyam yace “kin yi kyau sosai” ta sunkuyar da kanta tace “thank you”. Ranar wuni sukayi tare, ya dauke su a motar Diyam suka fita yawon zaga gari. Sai dare suka gama suka dawo gida ya ajiye su shi kuma ya tafi da motar. A daren Diyam ta kira Inna dan rabon da suyi waya tun sanda ta kira ta suna tare da Bassam. Inna ta dauka suka gaisa suka kuma gaisa da Asma’u da Subay’a. Sannan Inna ta karba tace mata “ya bakon naku?” Diyam tace “lafiya lau Inna” Inna tace “ya gaya miki abinda yayi? Naji bakiyi mana magana ba” Diyam taji gabanta ya fadi, me kuma yayi? Sai ta dake tace “me yayi kuma Inna? Ni bai gaya min komai ba” Inna tace “nasan dama bai gaya miki ba, na dauka zai gaya miki yanzu da yazo. Ya kwashe dabbobin nan daga gidan Alhaji Babba ya mayar dasu bayan gari tun kusan sati biyu da suka wuce. An buge katangar tsakiyar gidan Alhaji yace ya bar masa gurin kyauta”.

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE