DIYAM CHAPTER 21 KARSHE

DIYAM CHAPTER 21 KARSHE

A Perfectly Perfect Night4 I was thinking about covid-19. Sai nake ganin da ace al’ummar duniya duk sun sani kuma sun bi umarnin fiyayyen halitta (S.A.W) a inda yake cewa idan annoba tazo guri, wanda yake ciki kar ya fita wanda kuma yake waje kar ya shiga, da an bi haka da cutar bata kai matsayin da take a yanzu ba.9 Chinese basu san wannan umarnin na annabi ba, amma mu munsani dan haka me yasa mu ba zamu bi ba dan dakushe yaduwar cutar? Stay safe Stay at home2 Hannatu Sokoto da muka yi magana a last episode wata member ce ta group dina na WhatsApp, amma bata gyaran jiki, na saka sunanta ne kawai to honor her and for fun. But Maman Fareeda is real, duk mai so zata iya kiranta.2 Ta dora wayar a kirjinta ta lumshe idonta taba jin hawaye yana taruwa a idonta, sai data fahimci da gaske kukan zata yi sai ta mike da sauri zata shiga toilet sai suka hadu da Humairah tana fitowa ita kuma, ta tsaya tana kallon ta tace “wai kuka kike yi?” Sai Diyam taji sauran kukan data rike ya taho gabaki daga, ta juya bayanta tayi facing bango tana kokarin share hawayenta. Humairah ta fara dariya, abinda ya jawo hankalin yammatan da suke dakin suka taso suna tambayar abinda ya faru. Hannatu Sokoto ta shigo lokacin da Diyam take kokarin ture Humairah zata shiga toilet sai Hannatu tace “wai shiga kike so kiyi ki zauna a kan sassanyan tiles kiyi kuka zaki a toilet din? To dakata, bara in kawo miki garwashin wuta in dumama miki tiles din sai ki zauna kiyi ta kukan” duk suka kwashe da dariya, tace “a to, ni ba kukan ne damuwata ba, ni damuwata shine zama a sassanyan guri”. Da Diyam taga sun mayar da ita abar tsokana sai ta fice ta bar musu dakin. Daya dakin da yake kusa da inda suke ta shiga, wanda a da shine a matsayin dakin Sadauki sanda suna yara. Ta shiga ta rufe kofa ta jingina a jikin kofar tana kallon dakin da yanzu yaje a gyare tas amma babu komai a cikinsa sai carpet da akwatunan su Murjanatu da aka kawo dakin dan kar wancan ya cika da kaya. Ta rufe idonta hawayen yana cigaba da zarya a kuncinta, hawayen da ita kanta tasan na murna ne ba wai na bakin ciki ba. Sai yau ta tabbatar da cewa ana iya yin kukan dadi.+ Ta bide idonta tana tuno lokacin da take shigowa dakin tayiwa Sadauki kaca-kaca dashi, ta yayyaga masa takardun sa ta hargitsa masa shinfidar sa, ko kuma tazo ta kwanta a shimfidar tayi ta baccin ta, amma bai taba ko daga mata murya da sunan fada ba. Da kuma sanda take zuwa ta saka shi a gaba yayi mata homework ko da kuwa shi baiyi nasa ba. She never thought da gaske one day zai zama mijint, duk kuwa da cewa tun kafin tasan ma’anar kalmar miji take cewa shine mijinta. Anan dakin ta kwanta akan carpet. Ta lumshe idonta sai kuma tayi murmushi tana jin duk sauran problems dinta na rayuwa suna melting away. Ta zama matar Sadauki. Tana nan kwance Rumaisa tazo gidan, ita ta shigo har dakin ta fita da ita palo sannan suka kafa tsokanar ta wai tayi kukan aure, sai kuma Falmata tayi mata kwalliya ta musamman aka shirya ta cikin tsadadden farin lace din da ta tanada saboda yau wanda tayi musu anko ita da Subay’a. Sannan suka fara daukan pictures, suka dauka anan sannan ta shiga part din Inna can ma suka daddauka da mutane ana ta taya ta murna da kuma yaba kyawun da tayi. Masu selfie nayi a waya, cameraman ma yana yin nasa. Sai kuma ga sanarwar cewa ango yazo zasuyi pictures da amarya, nan kuma Diyam taji ita duniya babu wanda take kunya kamar Sadauki, ita sam bata dauka zaizo yin wani hoto da ita ba. Sai ta wayance ta koma part din Umma tayi zamanta amma tana jin alamar ya shigo kuma sai ta mike ta tsaya daga bakin kofa tana lekensa, yayi kyau sosai, a idon Diyam sai taga bata taba ganin mutum mai kyau irinsa ba a rayuwar ta, yayi shigar farin yadi kal dashi tun daga hula har zuwa takalmi fuskarsa dauke da annuri wanda yake bayyanar da farin cikin da zuciyarsa take ciki. STORY CONTINUES BELOW  Tana kallo ya shiga gurin Inna, da alama gaisheta yaje yayi sai kuma gasu sun fito tare hannunsa rike da Subay’a, suka tsaya a tsakar gida suka yi pictures sai kuma Inna ta sa baki ta kira ta amma sai ta makale taki tafiya, sai Subay’a ta taho part din da sauri “mommy kizo kiga yadda uncle Sadauki yayi kyau, kizo kuyi hoto kafin ya tafi” Sa’adatu tayi dariya tace “chafdi, mai fitar da yaya Aliyu daga gidan nan ba tare da yaga Diyam ba ai babu shi a duniya”. Diyam ta kama hannun Subay’a amma kafin tayi magana sai gashi a tsaye a bakin kofa yana kallon ta, tayi saurin sunkuyar da idonta tana mamakin rashin kunya irin ta Sadauki da har ya keto mutane ya taho gurinta. Sai ya tako cikin tafiyar kasaita ya zo har gabanta ya tsaya yace “my wife” sai ta saki hannun Subay’a ta rufe fuskarta da sauri tana murmushi, taji yammatan gurin sun dauki shewa sannan kuma wata mata a tsakar gidan ta rangada guda.3 Sai kawai ji tayi ya kama hannunta ya fara jan ta zuwa waje, a dole ta nutsu ta bishi amma fukarta a kasa, ta kasa daga ido ta kalle shi duk da yadda zuciyarta take son ganin cikin idonsa, balle kuma ta kalli sauran jama’ar gurin. A kayi ta hotuna, suna tsaye wannan yazo a dauka wancan ma yazo a dauka har saida aka gama sannan ya kuma jan hannunta zuwa dakin daya dauko ta ya zaunar da ita yace da Murjanatu “kar kuda ya taba ta” sannan ya juya ya fita, sai a lokacin ta dago kanta ta bi bayansa da kallo, tana kallon yadda yake taking steps one after the other. Sai da ya fita sannan kuma suka zo suka zagaye ta suna tsokana ‘mai tsoron miji’ ‘ta kasa kallon mijinta’ ‘dama fulani haka kuke?’ ita dai bata kula suba sai ta karbi wayar Asma’u wadda ta lura tana ta daukan pictures “kawo inga pictures din da kika dauka” ta bude hotunan da sauri tana scrolling tana neman wanda yafi fitowa sosai har ta samu, sai ta kwanta ta dunkule a guri daya ta zuba wa fuskarsa ido tana murmushi. Humairah ce ta katse mata daydreaming dinta, tace “Bassam yazo fa, yana waje” sai ta ajiye wayar ta mike da sauri, ta kira Asma’u “akwai bako a waje, ki bude masa dakin baki ki kai shi can, sai kizo ki kai masa abinci da ruwa” sai Asma’u ta saka mayafin ta ta fita, amma kuma wajen a cike take da mutane maza da mata na ta gaggaisawa, sai kawai ta tsaya tana bin su da kallo tana son ta gani ko zata iya gane waye jikan sarkin Abuja a cikin su. Yana cikin mota ya hango ta fito daga gidan da yake tunanin nan ne gidan su Diyam, farko ya dauka Diyam din ce amma kuma yasan Diyam ba zata fito kofar gida cikin mutane ba tunda yau aka daura mata aure, sai kuma ya lura wannan bata kai Diyam maturity ba amma suna kama sosai sai fari da Diyam ta fita. Yana ganin yadda take yamutsa fuska, dafa dukkan alama zata yi tsiwa. Nan sai zuviyar shi ta bashi cewa wannan Asma’u ce, only sister din Diyam. Sai ya bude kofar motar ya fita yana kallon ta, sai yaga ta juyo ta kalle shi kamar wadda aka kira, suka tsaya suna kallon kallo sannan sai yaga ta doso shi. He likes yadda take tafiya, ya tabbatar bashi kadai ba sauran mazan da suke gurin ma ta ja hankalinsu. Ta tsaya dan nesa dashi kadan tace “Bassam?” Ya gyada kai yace “Asma’u ko?” Bata amsa ba sai tace “Adda tace ka shigo ciki” muryarta tayi masa dadi, sautin fulani. Sai ta juya tayi gaba. A zuciyarsa baya son shiga dan shi da a son ransa ne daga gurin daurin auren zai komawarsa dan dai Humairah ta nace sai yazo yayi wa Diyam Allah ya sanya alkhairi “dan ita kazo fa, ai ya kamata ku gaisa ko minti daya ne”. Amma yanzu da Asma’u take gabansa tana tafiya sai yaji cewa binta a baya ya zama wajibi a gare shi. Ya zare key din motar ya bita cikin gidan yaga ta tura kofar wani daki kafin a karasa shiga cikin gidan ta ce masa “Bismillah” sai ya shafa kai yana kallonta, shi ai ya dauka tare zasu shiga amma sai yaga ta juya ta shiga cikin gida ta barshi a tsaye. Wannan yasa dole ya shiga dakin ya zauna ya kama daddanna phone dinsa. Amma zuciyarsa tana tunanin ko zata dawo?1 Bai jima ba sai gata ta shigo da sallama, tayi masa shimfidar abinci can gefe kadan sannan ta fara jera masa kayan ciye ciye iri iri har ta gama amma shi idanunsa a kanta suke ba wai a kan abinda take yi ba. Itama kuma tana jin idanuwan nasa akanta, dan kada ne ya rage bata yi barin abincin da take shiryawa ba. Sai data gama sannan ta mike, yayi saurin pretending kamar wayarsa yake dannawa tace masa “Bismillah, ga abinci. Adda zata fito ku gaisa” ya ajiye wayar sai kuma yace “thank you. Amma ki zauna mana kafin tazo din ko. Kinga ai sai ki tayani hira ko?” Sai ta dauke kanta, wannan mutumin neman magana yake yi kuma. Shi baisan zuciyarta bugawa take yi da wannan kallon nasa ba? Ga shi ya cika kyau da yawa.7 STORY CONTINUES BELOW  Ta girgiza kai tace “ina yin wani abu ne a cikin gidan” yace “Please, minti uku fa kawai. Kinga ni ban iya cin abinci ni kadai ba” he is a playboy, tayi deciding a zuciyarta, sai ta doshi kofa ba tare da ta kuma ce masa komai ba, har ta daga labule sai taji yace “an a lobbo sanne, Asma’u” sai ta juyo tana kallon sa, bata taba tsammanin bafulatani bane ba, mix din shi yayi yawa. Sai ta samu kanta da yin murmushi tace “miyetti” amma duk da haka bata zauna ba ta fita. Bata shirya yin wasa da zuciyarta ba. Bai ci abincin ba tunda yaci a reception din da suka wuce daga gurin daurin aure. Aliyu ya gane shi kuma ya karbe shi sosai. Sai ya zuba juice ya sha, sannan ya koma ya zauna ana fatan Asma’u ta biyo yayarta su dawo tare. Amma sai ga Diyam tazo sanye da hijab tare da Humairah, suka gaisa tayi masa godiya shi kuma yayi mata fatan alkhairi sannan yace zai tafi. Yace “Asma’u tazo ta kwashe kayan abincin nan mana” Diyam tace “no, kar ka damu kayi tafiyar ka kawai, an jima za’a kwashe su” yace “a dauke dai yanzun ai sai yafi ko?” Ta tsaya kawai tana kallon sa sai yayi murmushi, ta daga gira tace “Asma’un?” Yace “sallama kawai zamuyi ba wani abu ba, dan Allah ki turo ta” Humairah tace “kar ka damu kani na, har phone number dinta zan karbo maka” yace “kash, shi yasa nake yinki over yayata”. Suna shiga ciki Humairah ta kwalla kiran Asma’u “kije kuyi sallama da kani na” sai Asma’u ta tura baki tana kallon Diyam, Diyam ta daga kafada tace “ina ruwa na, in kina son zuwa kije mana” kamar ba zata je ba, sai kuma ta zari mayafi ta tafi.1 Bayan sallar azahar sai ga yan kawo lefe. Anan gida ya hargitse gaba daya ashe wai al’adar bare bari ne sai an daura aure ake kawo lefe. Akwatuna akwatuna, ga kuma wasu kayan a jakankuna. Lefen yakunshi akwatunan amarya set biyar, akwatin maman amarya (inna), akwatin kannen maman amarya(innaso), akwatin yan uwan baban amarya (bawaso), sai sisters (Asma’u) sai na kawayen innarta (ya samma soye) sai na matan waliyinta (su Hajiya Babba da yalwati), sai matan kawunnanta (kamu rawaye. Matar kawu isa da kuma su Hajiya Babba again)sai na yan bayarwa (na rabo) sune a jakankuna, sai na wadda tayi mata kiso (Hannatu Sokoto) an bata atampopi da kudi. Tun a kofar gida aka fara nunawa maza tukunna aka shiga dashi cikin gida gurin su Inna. Wannan duk al’ada ce ta barebari. Fulani sai suka tsaya kallo da mamaki, wanda baya kusa ma sai da aka kira shi a waya yazo ya kashe kwarkwatar idonsa masu video coverage suna yi masu dauka a hotuna suna yi.1 Diyam kuwa tana cikin daki ta rufe kanta, ita kunyar yan uwan Sadauki take ji gashi taji ance gar da Yaya Ladi da yan’uwanta aka zo. Ana cikin haka sai ga Fauziyya ta shigo gidan tana rarraba idanu, da goyon yarinya a bayanta. Irin yadda gidan ya chanza rake kalla ga kuma uban kayan data gani mutane suna ta gani wanda ko ba’a fada ba tasan lefen Diyam ne. Amma data tuna wanda aka ce shi ya auri Diyam din sai taga wannan ba komai bane ba. Ta tambaya aka raka ta har dakin da Diyam take. Diyam tana zaune da waya a hannunta tana kallon kiran Sadauki yana shigowa one after the other amma ta kasa dauka. Sai ganin shigowar Fauziyya tayi, ta tare ta da fara’a sosai sai Fauziyya tace “fushi nake yi fa, kin manta dani kuma wayar ki bata shiga kwata kwata” Diyam tace “Allah sarki, ba haka bane ba wallahi. Bana kasar ne ina UK ina karatu” Fauziyya ta gyada kai kawai. Ta tuna lokacin da Saghir ya fita da ita honeymoon America, a lokacin tana jin kamar duk duniya babu ya ita, tana yiwa Diyam dariya a ranta tana ganin cewa Diyam din tayi asara ashe ita asara zata samu. Rayuwa ta juya mata baya gabaki daya, komai ya tsaya mata. Dama a gurin maza take karbar yan kudade tana biyan buƙatar ta yanzu kuma tunda tayi deciding haifar cikin Saghir shikenan ta rasa costumers, bayan ta haihu kuma tana kallon fuskar jaririyar ta taji cewa ta gama yawon ta zubar kenan. Yan uwan Saghir sam basa taimaka mata kuma ta fahimci suma kansu taimakon suke nema, sun dai je sunga baby sanda ta haihu sai kuma Hajiya da take dan kiran ta tana tambayar lafiyar Anisa. Jin dadin ta daya ta samu aikin koyarwa a wata private school anan layin su. Diyam ta karbi Anisa tace “Masha Allah. Kinga dai yaran nan gaba ki dayan su kamar baban su suke yi”. Fauziyya tayi murmushi jin an yabi hasken rayuwarta, tace “ni fa bansan ma zakiyi aure ba, Hajiya Babba ta gaya min ana bikin kannen Saghir shine na shigar musu to a can ne nake ji ashe tare da naki ake yi” Diyam tayi murmushi kawai. Fauziyya tace “Allah ya sanya alkhairi” Diyam tace “ameen”. STORY CONTINUES BELOW  Ta dauko wayarta a karo na ba adadi tana kallon kiran Sadauki yana shigowa. Sai daya katse sannan tayi murmushi. Sai kuma ga Murjanatu ta shigo ta mika mata waya tace “yaya Aliyu yana kira” Diyam ta ture wayar tayi mata sighing “kunya” sai Murjanatu tayi dariya ta fita tana masa magana. Diyam ta kuma daukan wayarta sai sakon shi ya shigo. Tunda Sadauki ya fita daga gidan yake kokarin ganin yayi waya da Diyam, yana so yaji muryarta. Da farko mutane ne suka hanashi samun sukunin yin hakan, daga baya kuma da ya samu ya kira sai taki dauka. Yayi yayi amma sai dai tayi ta ringing ta katse ba zata dauka ba. Da farko ya dauka bata kusa da wayar ne dan haka ya kira Murjanatu ya ce ta bata, amma sai taki karba, yana jin Murjanatu tana yi mata dariya sannan tace masa “yaya Aliyu kunyar ka fa take ji wai” sai yayi murmushi ya samu secluded guri ya zauna ya shiga WhatsApp ya tura mata “ke fillo” shiru at first, sai later kuma ta aiko masa da reply na emoji na harara. Yayi dariya shi kadai ya rubuta “wai da gaske kunyata kike ji? Tun yanzu?” “Kunya kuma? Wacce irin kunya?” “Hmmm, really? So tell me, me yasa kika rufe idonki da na shigo gida? Me yasa kika ki yi min magana kuma me yasa kika ki daukan phone dina?” “Bafa kunyarka nake ji ba. Fushi nake yi” “Poor me, laifin me nayi?” “Ba kai bane ba ka hanani rawa a gurin wushe-wushe” (imojin shagwaba) Dariya “okay, yanzu dai rawa kike so ko?” “Uhmmmm” “Shikenan. Kina bina bashin rawa” “Da gaske?” “Yes, but just me and you. Tonight.” Tayi logging out da sauri. Feeling very nervous. Ina ma dai za’a daga kai amaryar nan zuwa gobe? Ko jibi? Babu abinda aka fasa. Magrib tana yi aka saka ta ta sake wani wankan, wannan karon babu kwalliyar da aka yi mata sai atamfar da ta saka blue mai adon pink and white flowers. Sannan aka nada mata laffaya fara mai shara shara da adon blue and pink flowers. Humairah da Murjanatu ne suka shirya ta tsaf, sannan suka kamo hannunta suka taho da ita dakin Inna inda anan iyaye suke, Mama, Inna, Hajiya Rabi (matar Kawu Isa) sai kuma step sisters din su Inna su biyu. Ta zauna a tsakiyar su ta nannade kafafuwanta suka fara yi mata nasiha, idan waccan tayi ta gama sai waccan ta dauka itama tayi nata. Suka gama sannan suka yi doguwar addu’a suka shafa. Lokacin masu daukan amarya suka zo, yaya ladi, Mama (matar baban Sadauki) sai kannen Papa mata su biyu. Suna zuwa aka fara nuna musu kayan garar da aka hadawa Diyam. Komai da komai na kayan abinci an siya in abundance, ga kuma kayan gara dangin su alkaki, nakiya dubulan, gireba, cincin da sauran su komai a cikin manyan containers. Sai daaka nuna musu kayan suka gani suka saka albarka sannan aka zuba su a mota aka tafi dasu gidan Alhaji Bukar. Diyam tana jinsu suka zauna suna ta barkwanci dasu Mama, sai taji dadin yadda taji ana magana tsakanin Inna da yaya ladi. Sai da suka gama sannan aka sake feshe ta da turare sannan maman su Murjanatu ta kama hannunta ta mike. A lokacin Subay’a ta shigo “mommy! Mommy wai aunty Asma’u tace tafiya zaki yi ki barni, Mommy ai tare zamu tafi ko?” Mama tayi saurin dauke ta ta fita da ita daga dakin tana ta rusa kuka, wannan shi ya kawo hawaye idon Diyam. Tun sanda za’a kai kayanta gidan Sadauki ta fara hada na Subay’a amma Inna tace “ba ki da hankali. In ma zaki tafi da ita ba yanzu ba. Kuma ke da zaki koma karatu menene amfanin tafiya da ita?” Ta fara kuka a hankali maman su Murjanatu tana tsokanar ta. Ita kuma tsokanar kara mata jin kunya take yi. A haka suka fita tana jiyo kukan Subay’a suka shiga mota ita da maman su Murjanatu da Mama, almustapha kuma yana driving suka tafi, sannan sauran motocin daukan amarya suka biyo bayan su.2 Duk da fuskar ta tana rufe amma tana gane inda suke har suka je, a lokacin ta daina kukan Subay’a, suka fito aka saka ta tayi basmala ta kuma shiga gate din gidan da kafar dama sannan ta sake repeating sanda zata shiga cikin gidan. Tana shiga kamshi ya kaiwa hancinta ziyara, kamshi mai dadi, kamshin Maiduguri. Sama suka hau da ita suka kaita har cikin bedroom din da yake nata suka zaunar da ita, suka sake yi mata nasiha sannan suka tafi. Sanda Mama zata tafi sai tace “Diyam yau ba zaki rike hannuna kice kar in tafi in barki ba?” Sai Diyam ta samu kanta da yin murmushi tare kuma da jin kunya.2 STORY CONTINUES BELOW Humairah ce ta fara zuwa tayi mata sallama saboda a daren zata bi flight zuwa Abuja, daga nan kuma mutane suka fara watsewa a hankali gidan ya fara yin shiru. Su Murjanatu, Rumaisa da Asma’u ne karshen tafiya, sai da suka gyara mata duk inda aka bata suka kara tabbatar wa ko ina na gidan yana kamshi sannan suka yi mata sallama. Murjanatu tace “wato ko dan tayin nan ba zaki yi mana ba ko? Irin ki dan ce ‘ku zauna ku kwana mana tunda dare yayi?” Diyam ta matsa mata guri tace “Bismillah, zo ki kwanta a kusa dani” Rumaisa tace “har na tausaya miki Murjanatu. Ni dai kunga tafiya ta maigidana yana waje yana jirana tun dazu” Adama tace “kunsan wani abu? Yaya Aliyu fa yana cikin gidan nan duk wannan abin da ake yi. Naje part dinsa naji kofa a rufe kuma an bar key a jiki ta ciki” Murjanatu ta mike da sauri ta dauki handbag dinta “Allah ya bamu alkhairi” duk suka yi mata dariyar ta fiya tsoron Sadauki sannan suka fita gabaki dayan su a tare. Tunda Diyam taji cewa Sadauki yana cikin gidan sai taji duk nervousness dinta ya dawo. Wayar ta har zamewa take yi daga hannunta tana faduwa kasa. Ta mike daga kan gadon tana karewa dakin kallo sannan ta kalli kanta a madubi kawai sai taga tayi wani irin kyau har kyalli fatarta take yi duk kuwa da cewa babu ko digon kwalliya a fuskarta. Ta gyara zaman laffayar ta sannan ta bude kofar balcony din daya ke cikin bedroom dinta ta fita tana kallon yadda sama tayi tas sannan taurari suka cika ta. Sai tayi murmushi tana jin wani irin farin ciki a zuciyarta sannan ta koma cikin dakin ta murda kofar fita waje ta leka empty corridor sannan ta fita da sanda kamar marar gaskiya ta bude dakin da yake opposite nata taga shima irin nata ne sai girma da wancan dakin yafi wannan sai kuma banbancin colors. Shirun da gidan yayi ne yasa ta jiyo kamar motsin takun mutum yana tahowa inda take, sai tayi sauri ta karasa shiga cikin dakin ta haye can karshen gado ta rufe fuskarta da laffayar jikinta. Taji an bude kofar corridorn an shigo, sannan heavy footsteps suka taho zuwa dakin da take yayinda bugun zuciyarta ya karu, taji shigowarsa sannan taji kamshinsa. Ya dan jima a tsaye yana kallonta sannan ya karasa shigowa ya hawo kan gadon ya zauna akan kafafuwansa a gabanta yana kallon fuskarta ta cikin shara sharan laffayar ta sannan murya can kasa yace “Sadiyam” Ta saka hannayenta da sauri ta kara rufe fuskarta tana murmushi. Sai ya saka nasa hannayen a saman nata yana shafa wa yace “hannayenki suna da kyau, kunshin yayi musu kyau sosai”. Tayi sauri ta juya tana kallon side. Sai yayi dariya yace “yanzu ni fuskar matar tawa ba za’a barni in gani ba?” Tace “sai ka biya tukunna” yayi murmushi ya jawo rose flower da ya shigo da ita a soke a bayan wandonsa a jikin rapping din an rubuta “loving you is all I ever know” ya mika mata ta karba da hannun dama, sai kuma ta miko masa hannun hagu tana murmushi, sai ya tuna lokacin da suna yara in ya bata sweet a hannu daya sai ta miko masa daya hannun shima ya bata. Sai ya saka hannu a aljihu ya dauko chocolate din twix ya saka mata a hannun. Yace “shikenan na biya?” Bata ce komai ba sai ya saka hannu biyu ya bude fuskarta ya sauke laffayar har kafadun ta. Ta dago kai a hankali suka hada ido yayi mata murmushi mai kyau sai ta kuma sunkuyar da idonta kasa itama tana murmushi ta fara bude chocolate din daya bata amma maimakon ta kai bakin ta sai ta kai nasa bakin. Ya rike hannunta a cikin nasa ya juyar dashi zuwa bakin ta ta fara gutsira sannan ya juyo da hannun zuwa nasa bakin shima ya gutsira.2 Sai da suka gama cin chocolate din su sannan ya jata suka mike a tare yace “let’s pray”. Dakin da aka kaita suka koma, shi ya fara shiga toilet yayo alwala sannan itama ta shiga. Sai ya ja musu jam’i a gurin da aka tanada a dakinta musamman dan sallah. Sukayi sallar isha’i tunda duk su biyun basu yi ba, sannan kuma suka yi sallar raka’a biyu ta godiya ga ubangiji a bisa cikar burinsu sannan ya juyo yana kallonta suka fara jero adduoi. Farko sun fara gabatar da godiya ga Allah sannan suka yi salati ga fiyayyen halitta (S.A.W) sai kuma sukayi addu’a ga mahaifansu da suka riga mu gidan gaskiya, Baffa da Ummah, suka roka musu gafara da ragamar ubangiji, sannan kuma suka yi addu’a ga mahaifansu da suke a raye tare da fatan tsahon rai a cikin kyakykyawar rayuwa. Sai kuma sukayi wa kansu addu’a, suka roki tabbatar alkhairin dake cikin auren su sannan suka roki tsari daga sharrin dake cikinsa. Suka yi addu’a ga yayan su, twins da suka rasu da fatan su zamo masu ceton mahaifansu sukayi addu’ar rayuwa mai kyau ga Subay’a sannan sukayi doguwar addu’ar a kan neman zuri’a ta gari mai albarka a tsakanin su.1 In Sadauki ya dauko addu’a Diyam tana amsa masa da ameen in ya gaji sai ita kuma ta karba ta cigaba shi kuma yana amsa mata. A haka har suka kammala suka shafa.1 Kanta yana kasa tana kallon hannunta amma tasan ita yake kallo duk da bata kallonsa, sai ta murguda masa baki, yace “ni ko?” Ta daga gira. Ya mike tsaye yana cewa “zakiyi bayani ne yarinya” sai ya zauna a kan gado sannan kuma ya tafi da baya ya kwanta rigingine ya lumshe idonsa, tana zaune still a inda ya barta tana kallon sa ya jima a haka sannan ya juyo inda take ya bude idonsa a cikin nata yace “na gama komai ko?” Ta mike tsaye tace “sauranka kaza” yayi kamar zaiyi kuka “Please ni kam a yafe min kazar nan mana. Kinga na gaji fa, ga kuma dare yayi” ta makale kafada tana kallon sa. Ya mike zaune sannan ya mike tsaye yace “shikenan, in na fita waje aka sace ni kar kiyi kuka” ya juya ya fita ya barta ita kadai. Kayan jikinta ta cire, ta shiga toilet tayi refreshing sannan ta fito ta zauna tana shafa mai me sassanyan kamshi a duk ilahirin jikinta, tana yi tana kallon kofa a tsorace har ta gama ta saka underwears dinta ta kuma saka riga da dogon wando na bacci, rigar a sake take sosai amma ta tsaya ne a saman cibiya, wandon kuma dogo ne har kasa sai dai ya kama saman sosai ya kuma bude sosai daga kasa, sannan ta hau kan gado ta dauko wayarta tana duba pictures. A lokacin ne sakon Sadauki ya shigo wayarta. “I owe you a dance, da kuma kazar amarci. Meet me in the garden please” Ta rufe idonta ta bude tana jin kamar zatayi zazzaɓi. Sai kuma ta mike ya dauki hijab ta saka masa turare ta saka sannan ta fita a nutse. Ta sauka kasa ta cikin corridorn daya raba palonsa na kasa da nata, inda anan ne stairs din hawa sama suke kuma anan ne front door da back door na gidan suke. Ta murda back door din ta fita doguwar veranda sannan ta sauka daga kan steps guda uku ta shiga garden. A tsaye ta hango shi, ya chanza dogayen kayan jikinsa zuwa shirt da wandon. Yayi shimfidar karamin carpet akan grass carpet din gurin ya zuba throw pillows akan carpet din sannan ya zagaye shinfidar da candles masu kyalkyali, a gefe kuma ga food warmers guda biyu da fruits da aka yi arranging dinsu a shape din heart. Ya taho ya tarye ta yana murmushi, ya jawo ta zuwa jikinsa ya rungume ta ta baya yana saka fuskarsa a ramin wuyanta yace “ga kaza an siyo, sai me kuma?” Ta juyo tana kallonsa tace “saura rawa ta” yace “with pleasure” sai ya zare hijab din jikinta ya ajiye a gefe ya juyo yana kallonta lokaci daya ya dauke numfashi saboda abinda ya gani, ya sani cewa tana da good figure but bai san cewa it is this good ba, ya jima tsaye yana jin tamkar ya samu paralises ita kuma tana ta sussunne kai, sai ya saka hannunsa na dama a waist dinta ya jawo ta sosai ya hade jikin su, daya hannun kuma yana shafo tun daga kan kananan kitsonta zuwa gadon bayan ta zuwa hips dinta, ta kwantar da kanta a tsakiyar kirjinsa tana jin cewa tamkar a nan ne aka halicceta, ta zagaye shi da hannayenta, tare suka sauke ajjiyar zuciya. Sai ya fara taking steps tare da ita a jikinsa, tamkar jikin nasu guda daya ne, three steps forward, two steps back.2 Ta lumshe idonta tana jinta kamar tana floating a cikin iska, kakkarfan jikinsa like a shield to her, his heart beat like a music to her ear. And he sang to her a cikin kunnen ta: I found a love for me, Darling just dive right in, And follow my lead, Well I found a girl beautiful and sweet, I always knew you will be the someone waiting for me…… ‘Cause we were just kids when we fell in love, Not knowing what it was, I will not give you up this time…. But darling, just kiss me slow, your heart is all I own, And in your eyes you’re holding mine…… Well I found a woman, stronger than anyone I know, She shares my dreams, I hope that someday I’ll share her home, I found a love, to carry more than just my secrets, To carry love, to carry children of our own We are still kids, but we’re so in love, Fighting against all odds, I know we’ll be alright this time… Darling, just hold my hand, Be my girl, I’ll be your man, I see my future in your eyes Baby, I’m dancing in the dark, with you between my arms, Barefoot on the grass, listening to our favorite song, When I saw you in that dress, looking so beautiful I don’t deserve this, darling, you look perfect tonight. Songwriters: Edward Christopher Sheeran.9 Lokaci daya ya tsaya, ya saka hannayensa biyu ya dago fuskarta daga kirjinta suna kallon juna for some seconds sannan ya sunkuya a hankali ya dora lips dinsa akan nata. Very slowly at first, very lightly that she hardly felt it, then it grows and it sends shiver data fara tun daga yatsun kafarta zuwa kwakwalwar ta tayi blocking dukkan tunanin ta, and she opens up to him, inviting him further in. A hankali hannayenta da suke sarke da juna a bayansa suka fara journey upward, daga bayansa zuwa wuyansa sannan zuwa kansa suna kara jawo shi closer, giving him more, accepting more. Ga masu tambayar abinda Bassam ya gayawa Asma’u. Fulatanci ne, amma kunsan kamar kowanne yare fulatanci ma yana da dialect da yawa. Yayi mata magana ne da dialect din fulanin yalleman. Idan bamu manta ba Maimoon mahaifiyar Bassam yar yalleman ce dan haka dialect dinsu ya iya. Abinda yace mata shine “you are so beautiful” ita kuma tace masa “thank you”.5 Diyam………… Wani irin feeling na emptiness ne ya farkar da Diyam daga bacci. Tana jin tamkar jikinta ne a kwance a kan gadon amma ruhinta is somewhere else. Ta bude idonta a hankali tana kallon bedside lamp din take ajjiye a gefen gadon feeling so lonely tamkar ita kadai ta rage a duniyar. Sai kuma tayi murmushi tana lumshe ido yayin da tayi realizing abinda yasa take jin wannan feeling din shine saboda babu hannayen Sadauki a rungume da ita. Sai ta mike zaune da sauri tana kallon tafkeken bedroom din daya ninka nata a girma, sai kuma tayi sauri taja sheet ta rufe jikinta saboda tunawa da tayi babu komai a jikin nata, ta kama rarraba ido kamar wadda tayi wa sarki karya sannan ta jiyo motsin ruwa daga toilet, sai ta koma da baya ta fada kan gadon tana yar karamar dariya ita kadai kamar sabuwar shiga a gidan tababbu.3 But she is not sure ko ta tabu din ne dan bata da tabbas din cewa abinda take feeling yanzu da abinda tayi feeling jiya da daddare is possible. Can it really be this good? Can one night really be worth a lifetime?5 It had started with a kiss, a kiss that lasted for like an hour a tunanin Diyam dan lokaci ya tsaya mata ne tamkar yadda tunanin ta ya tsaya. A kiss that loosen up everything na Sadauki, his heart, his brain and his entire body har ya sashi yayi realizing cewa ashe dai shi ba Sadaukin bane ba.4 But suddenly sai tayi breaking up the kiss, wai kazar ta zata ci, tana so ne taja ajinta for as long as she can. Ji yayi shi haushin kazar ma yake ji, haushin dukkan kajin duniya yake ji. Ina ma dai bai siyo ba? But dole ya barta ta zauna cin kazarta amma kuma bai fi loma biyu ta samu tayi ba saboda ko da second daya hannunsa bai bar jikinta ba, nema yake yi yayi mata kuka dan haka dole ta hakura da kazar amma sai da yayi alƙawarin biyanta wata.6 Ta rufe fuskarta cikin jin kunya sanda ta tuna cewa she lost some of her clothing a garden din, shima kuma haka. Tayi addu’ar Allah yasa ya fita ya dauke musu kar masu aikin gidan su zagaya su gani.4 Daga garden suka fara slow journey dinsu zuwa daki, branching a palo wanda ba zata iya tunawa wanne palon bane ba kamar yadda ba zata iya tuna yadda akayi suka shigo dakin ba, amma abinda take da tabbas akai shine she didn’t come in with any of her clothing, except for ribbon din data daure kitson kanta dashi.8 Ya rikirkice mata ya susuce mata acting as if cinye ta zaiyi gabaki dayanta, burinsa kawai ya samu ya kai inda yake son kaiwa amma ita kuma ta hana shi, making him beg, har sai da ta tabbatar he can no longer take it ita ma kuma haka sannan ta sakar masa.1 The first round was wow, and it fused not only their hearts but their souls together. A gurin Sadauki it was mind-blowing and was much more than what he expected. Ya tuna da duk wahalar da yasha kafin ya samu abinda ya samu din, sai yaga cewa ashe bai ma wani sha wahala da yawa ba, ashe prize dinsa yafi wahalar da yasha yawa. He used to call her his heart, yanzu sai yaga cewa that is an understatement, kamar ya rage mata daraja ne dan ita zuciya ai a jikin mutum kawai take, ita kuwa ai ta hada ne da jikinsa da ruhinsa da kuma duk abinda ya mallaka a duniya. And then he called her his world.4 A gurin Diyam mamaki abin ya barta a ciki. Dama haka abin yake? Dama haka ake ji? Can this really be possible ko kuma imagination dinta ne kawai. In haka feeling din yake me yasa ita bata taba ji ba sai yau? Bata taba jin koda kashi daya cikin goma na abinda taji yau ba. Duk rayuwar aurenta na baya ba zata taba iya tuna ranar da taje shimfidar mijinta ba tare da hawaye ya zuba daga idanuwanta ba saboda zuciyarta bata son abin. Saboda jikinta baya son abin. With every touch daya taba ta ji take kamar naman jikinta yake yanka and it hurts duk sanda ya kusanceta. Wannan yasa a lokacin take mamakin matan da suke neman mazajensu su makale musu kamar chewing gum saboda ita ta dauka yadda take ji din haka kowacce mace take ji. But now she knows better.1 STORY CONTINUES BELOW  The second round was wow wow, much better than the first, after which bacci mai nauyi ya dauke Sadauki. Sai Diyam ta tashi ta tafi toilet da niyyar tsaftace jikinta, tana jin cinyoyinta kamar tayi tsallen kwado. Ta fara wanka kenan ya murdo kofa ya shigo, tayi saurin rufe idonta ta durkushe a gurin tana jin wata irin kunyarsa wadda dazun duk bata ji ba, ko dan yanzu ta dawo sense dinta? Baice mata komai ba sai ya sunkuya da dagata chalak ya mayar da ita daki ya dora ta a gado daga ita har ruwan jikinta sannan ya dora daga inda ya tsaya tamkar zakin daya kwana bai ci abinci ba, and she found out ita din ma ashe yunwar take ji.5 Jin heavy footsteps dinsa ya katse mata tunanin ta, tayi saurin jan abin rufa ta lullube har kanta dan tana jin kamar ba zata iya hada ido dashi ba. Tana jinsa yazo ya tsaya a kanta sai kuma tayi sautin murmushin sa. Ya saka hannu ya gogo ruwa a jikin gashin sa sannan ya daga abin rufar ta ya goga mata a tsakiyar naked bayanta. Ta danyi kara tana matsawa tare da kara chukuikuyewa a guri daya. Ya zauna a bakin gadon yace “ko ki bude rufar nan ko kuma in shigo nima mu lulluba tare” tayi saurin girgiza kanta, yace “to bude in gani” ta sake girgiza kai, yace “Please, fuskarki kawai zan gani” ta fara bubbuga kafafuwanta a kan gadon cikin yana yi na shagwaba sai yace “hmmmm, baki san wannan abin da kike yi tamkar gayyata ta kike yi ba?” Sai ta daina sannan tace “ka tashi ka tafi” yace “ina zani? Dakina ne fa wannan. Ke ki tashi ki tafi” tace “dan Allah ka tashi. Na roke ka” yace “okay zan tashi amma sai naga fuskarki tukunna. Please just a glimpse” kamar ba zata bude ba kuma dai sai ta bude iyakacin fuskarta amma idonta a rufe gam. Ya jima yana kallon fuskarta sai kuma yasa hannu ya shafa doguwar jelar kitsonta and then bai san yadda akayi ba sai ganin fuskarsa yayi akan tata, hannunsa kuma yana cire abin rufar ta. Tayi saurin bude ido tana kwace bakinta daga cikin nasa “kai ba kayi wanka bane ba?” Yace da dasashshiyar murya “ban fita ba, wani wankan zan sake”. Sai da kuwa ya sake din. Yana tayar da sallah ta mike ta nannade jikinta da bedsheet sannan ta fita da sauri ta tafi dakinta. Toilet ta zarce tayi wanka a gaggauce sannan ta fito ta saka doguwar riga da hijab tayi sallah. Tana son ta koma bacci amma kuma yunwa take ji sosai dan jin cikinta take yi kamar anyi mata yasa. Ta duba agogo taga karfe bakwai, a lokacin kira ya shigo wayarta daga Murjanatu. Ta dauka da sallama Murjanatu tace “amarya, wannan saurin daukan waya haka kamar wadda ta kwana ba tayi bacci ba?” Sai kuma ta kyalkyale da dariya. Diyam tayi rolling eyes dinta tace “kina da abin cewa ne ko kuma kirana kikayi saboda credit yayi miki yawa?” Murjanatu ta daina dariyar tace “Mama ce tace in kira ki in tuna miki cewa karfe goma jirgin mu zai tashi, ki shirya zamu biyo mu dauke ki” Diyam ta dafe kanta, shaf ta manta akwai mother’s eve da Maman su Murjanatu ta shirya musu yau a Maiduguri. Lallai Sadauki ba karamin formatting kwakwalwar ta yayi ba. Murjanatu tace “kin manta ko?” Diyam tayi saurin cewa “no no no, ban manta ba, baki ji har na tashi na fara shiryawa ba?”……..1 Ta cire rigar da tayi sallah da ita ta mayar da wata doguwar rigar wadda bata karasa har kasa ba amma ta kama ta tsam-tsam like a second skin. Yadin rigar mai layi layi ne na kalolin black, dark ash, ligh ash da white. Wuyan rigar ya bude sosai har Diyam tayi tunanin ya zama too reveling, wannan yasa maimakon ta daura dan kwalin sai ta nade shi a wuyanta stylishly yadda ya rufe kirjinta. Ta bude kofa ta fito daga dakinta a dai dai lokacin da taji kara kamar ta faduwar wani abu, followed by another sound kamar ana ɓari. Ta dan kara sauri zuwa inda take jiyo sound din sai ta ga daga mini kitchen dinsu ne da yake a sama. Ta tsaya a bakin kofa leka ciki, abinda ta gani shi ya saka ta rufe bakinta tana hana dariya fitowa. Sadauki ne daga shi sai singlet da short, kusan duk cabinet din kitchen din a bude su ke ga kasan tiles kaca kaca da egg shells da kuma ɓawon dankali, ga mai cikin kasko a kan wuta shi kuma yana tsaye like three meters away from kaskon hannunsa da spatula yana leka cikin man. Sai kuma taga ya dauko wasu bowls guda biyu, daya ruwan kwai ne a ciki kusan rabin crete, dayan kuma danyan dankali ne guda gudan sa. Sai taga ya dauko dankali guda daya ya saka a cikin ruwan kwan sannan ya dauka da spatula ya jefa a cikin man daya riga yayi over heating.2 Dariyar da take rikewa ce ta kwace mata lokacin da yayi wani tsalle zuwa karshen kitchen din. Dariyar ta ce ta juyo hankalinsa gurinta. Yayi kamar zai yar da bowl din kwan da take hannunsa amma sai yayi saurin ajiyewa ya taho gurinta yana kallon ta tun daga kasa har zuwa sama. Ta rufe fuskarta cikin jin kunya sannan ta juya masa baya, not realizing cewa ta juyo masa daya daga cikin abinda yake so a jikinta. Yana zuwa inda take sai ya jawo ta ya hada bayanta da jikinsa, ya saka fuskarsa a wuyanta yana shakar kamshinta mai dadi sannan yace “good morning Sadiyam” bata amsa ba sai yace “wai kunyar ce har yanzu? I tot na cire ta tun jiya ashe da akwai sauranta. Ki gayawa kunyar nan ko ta rabu dake ko kuma inyi maganin ta” ta kara narkewa a jikinsa tana lumshe idonta. Ya kai baki dai dai kunnenta yace “na dauka kunyar ta tafi lokacin da naji kina cewa ‘sadauki more please” ya fada yana kwaikwayon muryar ta. Tayi saurin kokarin janye jikinta daga nasa tana bubbuga kafa tace “lahh! Ni wallahi ban fadi haka ba” yana dariya yace “nayi recording fa, in baki yarda ba mu koma dakina in kunna miki kiji” kamar zata yi kuka tace “ni bana son ji, ni ban fada ba” ya dawo da ita jikinsa yace “I had the greatest night of my life yesterday. And I had the greatest birthday gift. Yanzu wish dina guda daya a rayuwa shine every night na sauran rayuwa ta ya cigaba da kasance wa like yesterday night” ta juyo tana facing dinsa tace “lallai ma. To yau ma ba anan zan kwana ba” ya bata rai yace “ban gane ba” ta saka hannu tana gyara masa hannun rigarsa tace “biki zanje” ya sake bata rai “biki kuma? Bikin wa?” Tana murmushin fahimtar ba ita kadai ta manta ba tace “bikin mu ni da kai. Ka manta yau za’ayi event a Maiduguri? Mama har ta saka a kira ni a tuna min karfe goma jirgin mu zai tashi. Kuma nasan ba zan dawo yau ba, maybe sai jibi”. Ta fada da yanayin tsokana. Ya kife kansa a kafadarta yace “bara inje in hada kayana nima” ta ture shi tace “ba fa a gayyace ka ba” yace “duk wanda ya gayyaci matata to kuwa tabbas ya gayyace ni. Anywhere you go I will also go”.4 Ta kalli kaskon da yake kan wuta tace “me kake dafa mana ne?” Ya kalli kaskon shima, har ya manta ma da cewa girki yake yi, sai yace “dankali da kwai” tayi murmushi kawai sai ya dan ja da baya yana kara kallon shigar jikinta, ya daga gira yace “if you want to wear a dress like this, wear it with confidence” sai ya saka hannu ya zare dakwalin da ta rufe wuyanta da kirjinta da shi. Ta danji kunya ta sunne kai a kirjinsa sai shi kuma ya daga ta chak ya dora akan worktop, ta karbi dankwalin a hannun sa ta nada masa shi a nasa wuyan tana dariya, yace “ki zauna anan. Let me cook for you” sai ya koma ya leka cikin man sa, ya juyo yana kallon ta fuskarsa abin tausayi yace “ya kone” tayi dariya shi kuma ya harare ta ya dauko dankalin da ya zama kamar gawayi ya jefa a waste basket ya dawo gurinta ya zagaye ta da hannayensa ya dora kansa a kirjinta yace “ban iya girkin ba. I wanted to cook for you” tace “ka iya mana. Let me tell you what to do. Shi wannan dankalin you boil it first with a little bit of salt, sai ka yayyanka shi a kwance yayi shape din circles, shi kuma kwan sai ka zuba masa attaruhu da albasa da spices, sai ka juye dankalin a cikin kwan ka juya su sosai sannan ka dora frying pan akan wuta ka zuba mai kadan sannan ka juye dankalin da kwan ka soya su together on a very low heat, in side daya yayi ka juya dayan side din shima yayi, shikenan” sai ta sauko taje ta kashe wutar da har yanzu man yake kanta yana konewa. Tace “yanzu bara in hada mana, in ka gani yadda nayi kaga watarana kai ma sai kayi mana” sai ya sake daukanta ya mayar da ita kan worktop yace “you seat here, ni zanyi mana, ai na gane”. Har ya koma gaban cooker din sai kuma ya dawo gurinta yana langwabe kai yace “energy na ya kare. I need a refill” ta turo baki tana magana kasa kasa, yace “me kike cewa?” Tace “bayan yunwa nake ji tun jiya banci komai ba kuma kazar ma baka barni naci ba” yace “to ba nace zan biya ki ba, please” ya fara koma mata Sadaukin jiya, tayi kokarin ture shi “kitchen ne fa” yace “kitchen din waye? Gidan waye? Matar waye?” Ta sake makale kafada sai yace “okay, just a kiss then” ya fada yana kawo fuskarsa kusa da tata, ta saka fingers dinta tana tracing gashin girarsa ta zagayo har zuwa sajen sa, ya lumshe ido sai tayi sauri ta juya fuskarsa side tayi kissing cheek dinsa. Ya bude idonsa ya bata rai ita kuma tana dariya yace “gaskiya ban yarda ba. Ni bana son wannan” ta miko hannunta tace “bani kaya na to tunda baka so” yayi mata murmushin mugunta yace “with pleasure” sannan ya dora lips dinsa akan nata. Hmmmm. Naga wadannan ba yunwar suke ji da gaske ba, kuma na fahimci basu da niyyar zuwa Maiduguri. Gwara in tafi kar jirgi ya tafi ya barni. Diyam bata samu shiryawa ba har sai data ji horn din mota a waje, sannan ta ruga daki da gudu tayi refreshing. Tana cikin saka kaya Murjanatu ta shigo dakin tana kallon ta tace “wai sai yanzu kike shiryawa?” Diyam tace “da wannan complain din da kike yi dama jakar da zan tafi da ita kika dauko min a closet. Na riga na hada kayan da zanyi amfani dasu tun a gida” Murjanatu ta shiga ta fito da karamar jaka a hannun ta, lokacin Diyam har ya dauko hijab dinta tana checking contents din handbag dinta sannan ta kara abinda zata kara tayi zipping dinta ta rataya. Suna saukowa Murjanatu tace “baku da abinci a gidan nan? Ki zubo min dan Allah ko a mota ne sai inci yunwa nake ji” Diyam tace “nima yunwar nake ji, in kin samu nima ina so”.1 A waje Sadauki ne a tsaye tare da Al-mustapha wanda yake cousin din su Sadauki kuma daya daga cikin maneman Murjanatu suna magana, ya dora jallabiya akan shorts din dake jikinsa. Su Diyam suna fitowa Al-mustapha yazo ya karbi jakar hannun Murjanatu ya je ya saka a mota, Murjanatu tana kallon Sadauki tayi wa Diyam rada tace “baiwar Allah me kika yiwa yaya na? Na ga ya zama fari cikin dare daya. Ko dai man bleaching kika shafa masa?” Diyam tana dariya tace “kakan bleaching ba bleaching ba” amma ita ma sai ta lura fatar Sadaukin tayi haske sosai, wani annuri a kwance a fuskarsa and he seems kamar ya kasa daina murmushi.4 Al-mustapha ya dawo suka gaisa da Diyam yana kallon Sadauki, Sadauki ya lura tsokanar sa yake son yi sai yace “to ya isa haka, shiga mota” ya nuna Murjanatu yace “kema shiga, ko a gaban ku zanyi sallama da mata ta?” Almustapha yace “kaji masu mata, muma dai mun kusa zuwa gurin” Sadauki yace “kun kusa, amma baku zo ba. Ka bari sai kazo gurin sannan sai kazo mu jera, amma yanzu kana baya na” duk suka yi dariya, sannan su biyun suka shiga mota.2 Ya karaso gaban Diyam yana kallon ta, kanta a kasa tana wasa da fingers dinta, sai ya mika hannu ya kama nata, tace “zamu tafi” yace “Allah ya kiyaye hanya. I will be on the next flight insha Allah. Take care of yourself for me kinji? Sai nazo anjima” tayi murmushi tana gyada kai, sai kuma tayi ɗage on her toes tayi kissing beard dinsa. Ya bude mata kofa, ta shiga sannan ya gyara mata hijab dinta ya manna mata kiss a palm dinta sannan ya rufe mata kofa.3 Suna jan mota Murjanatu tace “I will pretend kamar banga komai ba” Diyam ta harare ta tace “to ai dama babu abinda kika gani yarinya. Ni yunwa nake ji wallahi”. Suna zuwa airport suka wuce VIP lounge. A can suka tarar dasu Mama already har sun isa, sai a nan Diyam ta samu tayi breakfast kafin su tafi. A lokacin ne kuma ta yi studying maman su Murjanatu sosai, sai ta ga cewa akwai tsantsar ilimi da wayewa a tare da ita wanda Diyam ta fahimci cewa shine dalilin da yasa bata daukan Sadauki a matsayin abin ki sai dai abin so, dan jahilci da rashin aikin yi suna playing role sosai akan wadannan abubuwa.4 Kafin 11 na safe sun sauka a Maiduguri. Tun daga yadda akayi musu a airport, tun daga motocin da Diyam taga sun zo daukan su harda motar security, Diyam ta kara tabbatar wa lallai ɗan Umar Mustapha Abatcha ta aura. Gidan da suka je kuwa ba gida bane ba, Diyam ta fahimci kamar wani estate ne amma family estate mai dauke da gidajen kakanni, iyaye da ya’ya. Gidan baban Sadauki a ciki yake, uncles uncles dinsa duk suna ciki, da kuma cousins dinsa da sukayi aure. Ko wanne gida ka gani a cikin estate din abin kallo ne, amma babban abin kallon shine gidan Umar Abatcha, tsarin gidan, motocin da suke gidan, kayan alatun da aka kawata gidan dasu, su suka saka Diyam ta fahimci dalilin da yasa Sadauki baya jin fitar kudi daga aljihunsa dan akwai su din.1 Yadda ake tayi mata ya saka take ta jin kunya, abincin da aka sauke su dashi ma takasa ci sai da Murjanatu ta ja ta suka tafi part dinsu su yammatan gidan wanda shi a kansa ma gida guda ne. Murjanatu tana ta tsokanar ta “wallahi in kika ce kunya zaki ringa ji ko? To wallahi a gidan nan sai an kusa mayar dake tababbiya” Diyam tayi murmushi, amma ita tasan ba zata iya cire kunya daga ranta ba kamar yadda ba zata iya cire jini daga jijiyoyin ta ba.2 Anan ta samu taci abinci sosai tare da sauran yammatan, sai kuma duk suka yi wanka har ita suka fara shiryawa, ta jawo jakar kayanta zata saka sai Sa’adatu tace “Mama fa ta bayar anyi miki dinkin da zaki saka yau, sai dai ki gwada abinda baiyi ba aje yanzu ayi miki adjusting” Diyam tayi godiya, amma kuma ta so saka nata kayan data tanada musamman saboda yau din sai dai kuma hausawa sunce yaba kyauta tukuici, in bata saka kayan ba Mama ba zata ji dadi ba. Dan haka sai ta yanke shawarar zata saka yanzu in yaso in an jima sai ta saka nata. Aka kawo mata kayan ta saka, komai yayi mata sai hips ne da za’a dan buda mata. Nan take Sa’adatu tayi waya aka zo aka karba kuma suna cikin yin kwalliya sai gashi an dawo dashi. Farar shadda ce da akayi mata wani irin stone work da golden brown stones a gaban rigar da kuma hannayenta, in ka gani zaka dauka aikin sirfani ne amma stones ne kawai aka jera su, Falmata tayi mata dauri mai kyau da dankwalin shaddar sannan ta saka bungles na danyen gold wanda ta dauko daga kayan lefenta, ta saka takalmi ta rike clutch golden brown nan take ta fito a matsayin Mrs Aliyu Abatcha. Bayan suma su Murjanatu sun gama shiryawa sai suka fita babban palon gidan, aka zaunar da Diyam a kan kujera kusa da Mama wadda Diyam tana zama ta rike hannunta tana yaba kyawun da Diyam din tayi.1 STORY CONTINUES BELOW  Already mutane sun fara zuwa gidan, yanuwan Sadauki, kannen babansa mata da matan kawun nan sa, matan abokan babansa, abokan arziki da sauran matan manyan gari. Duk wadda tazo zata zo su gaisa da Mama sannan Diyam ta gaishe ta, Mama kuma tayi introducing dinsu, kuma duk sai sun yaba kyawun Diyam sannan suyi mata wasa saboda kasancewar su barebari ita kuma sai dai tayi murmushi kawai dan ba zata iya mayarwa ba. Wasa wasa gida ya fara cika, duk girman palon sai Diyam taga mutane suna neman cika shi. Kowa kuma tazo zata kawo mata gift ta karba tayi godiya sannan sai Mama ta saka a shiga dashi ciki. Sai a lokacin ta fahimci ma ashe ba wai anan ne za’ayi taron ba, akwai hall da suke dashi a gidan wanda suke amfani dashi dan gudanar da tarurruka ko kuma family meetings. Sai da akayi la’asar sannan aka fara kai mutane can gurin taron, Diyam kuma ta koma daki dan shiryawa. Tana shiga sallah ta fara yi sannan ta dauko kayan da ta taho dasu ta ajiye akan gado a lokacin da Sa’adatu ta shigo dakin tana kallon kayan tace “wow” Diyam tayi murmushi. Kayan Fulani ne na saki complete set din da abin wuya da hannu da kafa da komai. A gaggauce tayi wanka, sannan ta danci abinci kadan kafin ta shirya tsaf ta fito a cikakkiyar bafulatanar ta. Nan take ta dauki kanta a hoto ta turawa Sadauki wanda tun dazu da suka tare da su Mama yake ta kiranta a waya amma ta kasa daukan wayarsa a gabansu. Yana gani yayo reply “Diyam, na taba gaya miki kuwa cewa ke din kyakykyawa ce?” “Really? Ba zan iya tunawa ba. Maybe ka taba fada but not directly” “To yanzu zan fada directly din. You are very beautiful Halima. Kina da beauty na fuska, na jiki dana zuciya. Ki godewa Allah Diyam dan yayi miki komai” “Anya kuwa na kaika kyau Aliyu? Ni in ina kallonka har mamakin kyawunka nake yi. Komai naka tamkar kai ka zabar wa kanka. Komai ya dace da komai a fuskarka wadda ita kuma ta dace da jikin ka. Jikinka kuma ya dace da sunanka, Aliyu Sadauki. Strong in the heart and the body. Imojin heart mai beating “I love you so much my husband” “I love you more, my wife”.3 Dakin taron ya cika sosai da manyan mata, ga makada nan suna ta aikin su mata ana ta cashewa ana barin kudi. Diyam tana zuwa aka saka ta a tsakiyar fage aka fara yi mata ruwan kudin da har sai da ta fara tunanin anya wannan ba almubazzaranci bane ba? Ba’a tashi daga event din ba sai daaka fara kiran magrib. Karshen gajiya Diyam ta gaji, jikinta gabaki daya ciwo yake yi mata dan haka akan sallayar da tayi magrib anan ta zame ta kwanta sai bacci. Cikin baccin aka zo aka tasheta wai taje su gaisa da matar governor wadda bata samu zuwa dazu ba sai yanzu. Can palon Mama aka kaita ta tarar dasu suna ta hirar su suna dariya, ta gaishe su suka amsa mata da fara’a suka yi ta tsokanar ta tana rufe fuska sannan matar ta dauko wani set din scent burner mai kyau ta bata a matsayin gift sannan tayi musu sallama Mama ta tafi ta raka ta. Bayan Mama ta dawo ne sai kuma ta zauna tana ta yiwa Diyam nasiha da kuma dabaru irin na zaman aure, wadansu maganar sai Diyam taji sunyi mata nauyi da yawa amma kuma duk tana ganewa kuma tana dauka. In dai Sadauki ne, she can and will do anything for him.2 Suna tare su Murjanatu suka shigo, sannan aka gabatar musu da abinci suka hadu a dining din Mama suka ci tare sannan suka dawo palo suka cigaba da hira, Diyam tana ta mamakin yadda Mama take yi da yayanta kamar kawayenta. Suna nan tare Sadauki ya shigo, Diyam ta kalleshi sau daya suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ya je ya gaida Mama sannan ya samu guri ya zauna yana amsa gaisuwar kannensa, Diyam ma ta gaishe shi ya amsa yana danna phone dinsa, Murjanatu tayi dariya Diyam ta harare ta. Mama tace “kaje gurin babanka kuwa?” Yace “eh, muna tare dashi ai tunda nazo, sai daya shiga ciki sannan na shigo”. Ya turo wa Diyam text “ki taso mu tafi” ta karanta sai ta dago kai ta harare shi. Ya hade hannunsa alamar roko sai ta gyara zamanta yadda bama zata ke kallon sa ba. Sai kawai suka cigaba da hirar su shida Mama, tana bashi labarin taron da irin matan da suka zo da kuma gifts din da Diyam ta samu. Sai yayi mata godiya sosai sannan ya mike tsaye yana cewa “Fanna kawo min abinci daki na Please” Mama tayi sauri tace “wacce Fanna kuma? Mu ai mun yaye ka yanzu. Halima tashi maza ki hada abinci ki bishi ki kai masa” bai ce komai ba yayi hanyar waje sannan ya juyo a wayence yana kallon Diyam, yayi mata gwalo.2 STORY CONTINUES BELOW Ta tashi ta hada masa duk abinda tasan zai so ta zuba a basket sannan tace da Murjanatu “tashi ki rakani” Murjanatu ta harare ta “kinga in kika fita daga gidan nan ki kalli gabas, gini na farko da kika gani a gurin shine part dinsa” Adama tayi dariya tace ” me dakin gabas kenan, shi yasa mu a gidan nan bamu fiye kallon gabas ba sai in zamuyi sallah” Falmata tace “to ai dan kar mu kalla ace harara mukayi” Mama ta jefi Fanna da remote tayi mata magana da barbarci sai ta mike suka fita tare da Diyam.1 Suna fita Diyam tace “kun takurawa bawan Allah nan. Mutum mai hakuri da kawaici irinsa, mutumin da ko hannu aka saka masa a baki ba lallai ya ciza ba” Murjanatu tace “waye hakan? Lallai so hana ganin laifi. To in gaya miki saboda muguntar sa kwanan baya sai da ya saka ni Murjanatu na share gidan nan gabaki daya, tun daga sama har kasa” Diyam tayi dariya tace “daga ji wani babban laifi kika yi masa, shi bawan Allah ne mai sanyin zuciya mai kuma hakuri da yafiya idan aka bata masa” a lokacin suka zo kofar part din Sadauki. Murjanatu ta bude kofa ta tsaya a gefe tace “wacce take fadar maganar tafi wacce ake fadawa sanin cewa ba gaskiya take fada ba. Good night friend” Diyam tayi dariya tace “yanzu zan dawo ai” Murjanatu tace “we will see about that”.2 Ta ajiye abincin a palo tana studying kyawun gurin, sai ta tafi kofar da jikinta ya bata yana ciki tayi knocking ta tura kofa, yana kwance a kan gado da yawa a hannunsa, dakin cike da sanyin ac da kuma kamshin sa, ya ajiye wayar yayi mata murmushi yana folding hannayensa yace “welcome wife” tace “ga abincin” ya dan bara rai “waye yace miki yunwa nake ji? Ni matata nake so” ya karasa maganar yana langwabe kai, ta fara bubbuga kafa a kasa “ni wallahi bacci nake ji, ni wallahi na gaji jikina ciwo yake yi min” ya mike zaune yace “good. Kinga sai inyi miki massage” ya fada yana tattare hannun rigarsa. Ya nuna gefensa akan gadon yace “come and lay down here inyi miki tausa. You will thank me tomorrow”. Ta yi kamar zata yi kuka, ya miko mata hannunsa yana kara marairaice wa sai kuma tayi murmushi ta tafi tasa ka nata hannun cikin nasa.2 Da safe sai da kowa ya tashi a gidan aka kuma gama komai har breakfast an gama shiryawa amma babu Diyam babu Sadauki babu kuma labarin su. Anyi ta kiran wayoyinsu kuma da suna shiga amma daga baya switched off. Sai da aka zo yin breakfast sannan Papa yace aje a kirawo su, yana son suci abinci tare gabaki dayansu saboda a yau yake son komawa Canada.7 Cikin bacci Diyam taji kamar ana knocking kofa, ta bude ido da kyar saboda nauyin bacci, ta hannun Sadauki daga jikinta sannan ta juya tana kallon fuskarsa so deep in his sleep sai kawai ta dulmiya wajen kare masa kallo tana murmushi. Wani bugun kofar da aka sake yi shi ya dawo da ita daga duniyar kallon Sadauki. Ta mike tana gyara kayan jikinta sannan ta dauki hijab dinta ta saka still cikin baccin ta fita palo ta bude kofa. Murjanatu ta gani a tsaye, ta harare ta tace “kika ce min ba kwana zaki yi ba” Diyam tace “wannan ne dalilin da yasa kika dame mu muna bacci? To bara inje in kira wo shi sai ki maimaita a gaban sa” ta daga hannu tace “Papa ne yake kira, in kuma inje in gaya masa kunce kar a dame ku ne to?” Diyam bata ce komai ba ta koma da sauri ta tashi Sadauki ta gaya masa sakon kira sannan ta fita da sauri a ranta tana cewa “wannan wanne irin abin kunya ne nayi ni Halima”.3 Da sauri Diyam tayi brush ta wanke fuskarta ta chanza kaya sannan suka tafi part din Papa inda anan ake neman nasu. Tana shiga Sadauki shima yana shigowa, fatar idonsa a dan kumbure alamar bacci bai ishe shi ba. Shi ya fara zuwa ya durkusa ya gaida mahaifinsa sai bayan da ya zauna sannan Diyam itama ta karasa for the first time ta gaishe da surukinta. Ya amsa da madaukakiyar fara’a “Halima, ance min jira kinyi kyalliya da kayan fulani, ni kuma sai nace to lallai zamu yi miki zanen barebari dan mu tabbatar miki kin zama tamu yanzu” duk suka yi dariya har Diyam data rufe fuskarta da hijab dinta. Sai data zauna sannan ta samu damar ganin fuskarsa. Sai a lokacin tayi mamakin yadda akayi duk ganin da take yi masa a hotuna bata fahimci suna kama sosai da Sadauki ba sai data gan shi ido da ido tukuna. Bayan shekaru, banbancin fuskarsa data Sadauki shine hancin Sadauki yafi nasa tsaho sai kuma sumar Fulani da Sadaukin yake da ita.1 Suna zama masu aiki suka matso suna tambayar kowa abinda za’a zuba masa daga cikin menu, kowa ya fada aka fara saving, Sadauki kuma ya fadi nasa dana Diyam dan yasan ba zata yi magana a gaban su Papa ba. Sai da suka gama cin abincin sannan Mama ta sake yiwa Diyam barka da zuwa family. Papa kuma ya dora da cewa “ina so Halima ki saka a ranki cewa nan gidan ku ne ba wai gidan surukan ki ba, ki dauke ni a matsayin baban ki ba wai baban Aliyu ba. Saboda baffanki, malam Usman yayi min halaccin da babu wanda ya taba yi min irinsa a duniya. Ya rike min Aliyu tamkar shi ya haife shi dan haka nima zan rike ki tamkar ni na haife ki insha Allah. Wannan shine abinda zanyi in kwatanta abinda Usman yayi min”.2 “Nasan Aliyu ya baki labarin dana bashi akan rabuwata da mahaifiyar sa amma ban gaya masa dalilin da yasa bayan nayi bincike na gano wanda yake neman halaka su kuma na dauki mataki akan sa ban koma na dawo dashi gida gurina ba. Na barshi ya cigaba da zama a hannun Usman ba tare da yasan nine mahaifinsa ba saboda a lokaci nayi tunanin hakan shine dai dai a gurinsa, maybe I was selfish, but I wanted what is best for my son. Ni mutum ne mai harkoki da yawa wanda ban fiya samun lokacin kaina ba ballantana na iyali na, tarbiyya, nuna soyayya, nuna kulawa ga dan karamin yaro bayan kuma bana tare da mahaifiyar sa ba abu ne da zai samu a gurina ba. Wannan ne yasa na bar shi a hannun Usman da Zainab. Na kuma boye kaina daga gare shi ne saboda ina son ya zama strong, bana son yasan nine mahaifinsa ballantana ya dora wani abu a ransa ko kuma ya raina marikansa. Sai na nemi alfarmar Usman nace ya koya masa neman na kansa tun yana karami. I used to go to the garage duk sanda na samu dama, I used to watch him work, drenched in oil and sweet, na kan ce a raina “good, yanzu zaka san darajar kowacce kwandala da ka samu”. Usman kuma bai taba neman ko kwandala daga wajena ba saboda kula da Aliyu, sai lokacin daya kasa samun admission ne ya nemi in taimaka masa ni kuma nace ya barshi ya sha wahala ya samu da kansa, har yayi fushi dani a lokacin yana ganin kamar nayi tsauri da yawa. Amma yanzu gashi naga result din abinda nayi din, Aliyu yayi turning into more than yadda na saka rai. Yes, na bashi kudi nace ya juya, shekaru biyu bayan nan dana bincika sai naga already yayi doubling kudin da na bashi. A yanzu haka bansan adadin me yake dashi ba. Allah ne kadai yasan me ya tsara wa rayuwar sa amma ni ina saka ran cewa this is just the beginning for him. Allah yayi muku albarka gabaki dayan ku, Allah kuma ya baku zaman lafiya da zuriya mai albarka”.2 Duk suka amsa da ameen. Diyam ta saci kallon Sadauki sai taga kansa a kasa amma fuskarsa tana nuna tsantsar farin ciki. Mama tace “a matsayin wedding gift, Papa and I decided to give you two, Aliyu da Halima, gidan mu na Oxford, mun bar muku shi duniya da lahira. Allah ya baku zaman lafiya” nan take gurin ya kaure da murna, siblings din Sadauki duk suka taho suka ringume Diyam suna taya su murna. Ta gefen idonta taga Sadauki ya durkusa gaban mahaifinsa yana godiya, sai taga ya dago shi ya rungume shi a jikinsa yana bubbuga bayan sa. Food for thought: Mun tuna da hadisin da Annabi (SAW) yake mana bayani akan healing power da take cikin habbatus sauda? Sannan da hadisin da yake gaya mana cewa nemon tsami yana maganin cututtukan annoba? Zam zam fa? Mun tuna cewa yana maganin duk wata cuta da aka sha shi da niyyar neman waraka daga gareta? Add that to bin ka’idodin kare ka kai daga wannan cutar, kar ki/ka fita daga gida indai bada wani kwakwkwaran dalili ba, in za’a fita din kuma a saka face mask da hand gloves. A guji taba mutane, doorknobs, railers etc a lokacin da ake waje, kar kuma aci ko a sha wani abu, a kuma guji taba fuska, in an dawo gida kuma a cire kayan da aka fita dasu a shanya su a rana sannan ayi wanka kafin a taba komai na gidan.7 Don’t forget your morning and afternoon azkar. Insha Allah we will get through this together. #Don’t panic #Stay safe #Stay at home5 A ranar da yamma su Diyam suka dawo Kano. Tun a jirgi Diyam take ramuwar baccin ta, sai Sadauki ya daga armrest din tsakanin kujerun su ta kwanta ta dora kanta a cinyarsa shi gyara mata hijab dinta ya rufe mata har kafafunta. Sai da zasu sauka sannan ya tashe ta, suna fitowa already daya daga cikin office drivers dinsa yana jiransu ya dauke su ya kaisu gida. A gidan ma Diyam baccin ta ta cigaba, dan sai yau take huce gajiyar biki, Sadauki bai dame ta ba ya batta tayi baccin ta shi kuma yayi musu order ta abinci aka kawo musu har gida saboda ya tabbatar wa kansa cewa bai iya girki ba.1 Sati daya bayan tariyar Diyam Asma’u tazo ita da Subay’a, ranar Subay’a kamar zata zuba ruwa a kasa ta sha dan dadi musamman saboda ganin dakin da aka ware a gidan saboda ita. Diyam kuma sai ta dauko gift din data samu a Maiduguri ta ware wadanda take so sannan sauran ta hada da wasu daga cikin kayan lefen ta ta bawa Asma’u tace ta kaiwa Inna a raba wa yan’uwa, cousins dinta duk kowa sai daya samu wani abu. Asma’u kam sai data debi rabonta dama tun kafin a fara tabon. A lokacin ne Diyam ta fahimci cewa Asma’u suna waya da Bassam, she did not comment, idan hakan suke so to ita kam sai dai ta taya su da fatan alkhairi.1 Sati biyu bayan bikinsu hutun su Diyam ya kare, ta dauka zasu yi drama da Sadauki akan komawarta amma sai taga shine ma mai taya ta lissafi. Da lokaci ya matso sai taga ya fara hada nasa kayan shima. Tace “aikin fa? In ka bini wa zai kular maka da companyn ka?” Yace “my dear Halima. Kin manta I managed my company for the five years din da nake karatu? Ko kin dauka zan barki tafi ki barni ne?” Tayi dariyar yadda ya fadi maganar kamar wani yaro. Amma kuma tana jin dadi a ranta dan ba karamin faduwar gaba take yi ba a duk lokacin da ta tuna cewa zata koma England school ta bar Sadauki a Nigeria.1 Ta zo ta zauna akan cinyarsa ta zagaye wuyansa da hannayenta ta saka fuskarta a wuyansa tana dan bubbaga bayansa tace “kar kayi kuka, bazan tafi in barka ba kaji habibi” ya shafa mararta yace “habibi yana cikin nan gurin a kwance” ta zaro ido tace “ba wani nan” yace “to ni dai banga kinyi period ba” tace “sati biyu ne fa kadai” yace “koma kwana biyu ne, ni ai nasan irin shukar da nayi kuma nake yi so nake inga na fara girbi” ta boye fuskarta a wuyansa tace “kai dan Allah, sai kace wata gona? Ni bani da komai Allah. Kuma ma ai kaga karatu nake yi yanzu ko? Ko so kake in ke faduwa exams dina?” ya dago fuskarta yace “tare zamuyi karatun ai, muna yi kuma muna cigaba da planting seeds din mu, kafin mu gama in Allah ya taimake mu sai mu girbi ko da biyar ne” ta zaro ido “biyar fa kace? Sai kace kaza?” Sukayi dariya tare. Yace “biyar din ma rage miki nayi ai dan kar ki sha wahala da yawa, in za’a bani zabi twins nake so duk shekara. In akayi twin boys sai ayi girls, sai a sake boys a sake girls, kinga a shekara hudu anyi takwas kenan” ta mike da sauri tana cewa “in yaso a shekara ta biyar sai inga an shigo min da amarya ko” ya jawo ta ta fado jikinsa, ya gyara mata zama tana facing dinsa yana tracing jawline dinta da finger dinsa yace “kina so ta mutu ne amaryar saboda bakin ciki? Ko kuma kina so ranar lahira in tashi da shanyayyen barin jiki saboda na kasa adalci? Kina ganin zan iya jera wata dake a zuciyata Halima?” Ta turo baki tace “daɗin baki” yace “au baki na yana da dadi dama? Ai ban sani ba nasan dai naki yana da mugun dadi. Let’s taste and find out na waye yafi dadi”.1 STORY CONTINUES BELOW  Tafiyar su tazo dai dai da hutun su Subay’a. Dan haka Sadauki yace zasu tafi da ita da Asma’u suyi musu hutu a can kuma su taimaka musu gurin settling a sabon gidan su. Murna gurin Asma’u kamar zata tashi sama dan dadi, Diyam tana kallonta tace “kina murnar zaki je England ne ko kuma kina murnar zaki je gurinsa?” Asma’u tayi saurin yi mata signing akan tayi shiru kar Sadauki yaji. Diyam ta daga murya tace “eh, Bassam da kuke waya dashi Asma’u nace kinga kuwa a can yake karatu, nasan zaku ke haduwa in kinje” Sadauki yayi saurin juyowa daga kallon news yana kallon su yace “Bassam, menene hadin Yar asama da Bassam?” Diyam ta nuna ta tace “gata nan, tayi maka bayani”. Asma’u ta fara kame kame tana rarraba ido, ya kalle ta strictly yace “bana son shashanci, idan yana sonki da gaske yazo ya same ni first kafin ya cigaba da neman ki. I know his family, amma shi din zan saka a bincika min halayensa in kuma basu yi min ba kin gama ganin sa kenan. Kinji abinda nace?” da sauri Asma’u ta gyada kai.4 Ranar dasu Diyam suka sauka a ranar ne suma su Murjanatu suka zo. Sun taho gabaki dayansu tare da sisters dinta dan su taya su Diyam tarewa a sabon gidan su. Gidan da Diyam taga kamar yayi musu girma dan haka ta saka aka rufe part din matar gida suka zuba kayansu a part din maigida ita da Sadauki. Sai bangaren yara kuma anan Murjanatu zata zauna tare da Judith din da Diyam ta kuma gayyatowa. Daga nan kuma sai gurin ma’aikatan gidan wadanda dama suna nan already, masu kula da tsaftar gidan, masu abinci da masu gadi. A cikin kwana biyu aka gama settling komai, a ranar suna zaune gabaki dayansu matan a palo suna hira sai Sa’adatu take basu labarin abinda Papa ya gaya musu kafin su taho daga Canada, cikin kwaikwayon muryarsa tace “ke Sa’adatu dake Falmata, ku fito da miji ayi muku aure hakanan, tunda naga karatun nan naku ba karewa zaiyi ba” duk suka kwashe da dariyar yadda tayi maganar, Diyam ta harare ta tace “yanzu haka baban nawa yake magana?” Falmata ta bude hannu tace “yanzu fi sabilillahi ni ina naga mijin da zan fitar? Ni ina naga saurayin ma? Samari fa basa kula yayan masu kudi” Murjanatu ta gyara zama tace “basa kula ku dai, ku da kuke musu girman kai, ki zo in koya miki yadda ake jawo hankalin maza” anan Sadauki ya bude kofar bedroom ya fito ya tsaya yana kallon su, duk sunyi tsuru tsuru saboda basu san yana cikin daki ba sai Diyam ce kawai ta sani. Bai ce musu komai ba sai ya dauko wayarsa yayi dialing sannan yace “hello Papa” ya gaishe shi yace “maganar nan da ka yiwa su Sa’adatu, ina ganin a hada harda fanna saboda duk tafi su samari. Okay. Insha Allah. Thank you Papa. Love you too” ya juyo yana kallon fanna yace “ke ma ki fito da naki. Gaba daya guri na zasu fara zuwa First, sai nayi approving sannan zasu je gida” bai sake cewa komai ba ya saka hannayensa a aljihu yayi tafiyar sa.1 Murjanatu ta zamo daga kan kujera ta fado kasa tana birgima dramatically, tace “wallahi yau na kuma tabbatar wa yaya Aliyu baya so na” su kuma duk suna tayi mata dariya. Diyam tace “alhamdulillah. Zuciyata fess yau. Karyar tara samari ta kare. Satin su Sa’adatu daya suka koma. Su kuma su Asma’u sai da sukayi wata daya sai da hutun su ya kare sannan suka koma gida. Washegarin da suka tafi ne da assuba Diyam tana karatun Alkur’ani akan sallaya sai ga Sadauki ya dawo daga masjid. Ya zauna akan gado yana kallonta har ta idar sannan ta mike ta hawo kan gadon ta kwanta tana lulluba yace “ni fa har yanzu banga tazo ba” bata kalle shi ba tace “wacece zata zo? Bakuwa zaka yi?” Ya yaye rufar yace “yau ba zaki yi baccin nan ba sai kin gaya min akwai ko babu” ta fara yi masa shagwaba “ni me zan gaya maka. Ni babu abinda zan gaya maka” ya cire rigar da yaje masjid da ita yayi astriding dinta yace “ko ki gaya min ta lallami da lumana ko kuma ki gaya min in kinji wuya” ta fara dariya, ya sakar mata nauyinsa shima yana dariya, tayi kokarin ture shi ta kasa sai ya rike hannayenta duk biyun da hannunsa daya, yace “akwai ko babu?” Tace “to ni yanzu me kake so ince maka” yace “cewa zaki yi ‘sadauki kayi min ciki” ta kwace hannunta da sauri ta rufe fuskarta tace “la ila, wai kai baka jin kunya ne?” Yana dariya yace “ina ji mana, ina jin kunyar mutane amma bana jin kunyar matata” tace “ni dai bazan iya fada ba” yace “to kinga, in akwai ki gyada kanki, in babu ki girgiza kanki” tayi shiru, yace “akwai ko babu?” Ta bude ido tana kwallon sa ta miko masa hannu tace “kawo tukuici” yace “say it, duk abinda kike so, anything” ta rufe hannun tace “in ka kawo tukuici sai kazo a gaya maka” yace “a bani bashi zan biya” ta turo baki “har yau fa baka biya ni bashin kaza ta ba kuma kake neman a kara maka wani bashin?” Ya dafe kai “wannan kaza, wannan kaza. Yanzu duk kajin gidan nan amma ban biya ba?” Tace “waccan special ce” ya mike yana saka rigarsa. “Zan siyo miki kaza yanzu, zan kuma kawo miki tukuicin ki”. STORY CONTINUES BELOW  Sai daya loda rigunan sanyi a jikinsa saboda sanyin da ake yi a waje, gashi kuma gari bai ko gama wayewa ba amma haka ya fita, da kyar ya samu kazar saboda duk eateries din kusa dasu basu fito ba sai da ya shiga cikin gari sosai sannan ya samu, ya siyo mata chocolates duk wadanda yasan tana so leda guda sannan ya dawo gida. A gado ya same ta har lokacin ta lulluba tana baccinta. Ya zauna a gaban gadon ya bude ledar gasassun kajin ya yanko cinya daya ya bude fuskarta ya kai naman kusada fuskata, ta motsa idonta sannan ta bude idon cikin nauyin bacci tana kallon naman sai kuma ta kai hannu da sauri zata karba sai ya janye yace “kwadayayyiya. In kina so sai kin fada min abinda nake son ji, akwai ko babu?” Ta tashi zaune ta leko tana kallon naman kajin daya bude ya cika dakin da kamshi ga kuma chocolates din daya zube a kasa suma. Sai ta kalleshi ta gyada kai da sauri ta koma ta kwanta ta rufe fuskarta. Wannan ciki na Diyam ya sha gata, gayu da soyayya a gurin sabon shiga Sadauki. Rigimar da tayi tunanin zasu yi akan komawarta school basu yi ba sai yanzu akan zuwa school da ciki. “Idan kuma kika fara rashin lafiya a can fa? Ko kuma in kina son ki kwanta ki huta babu gurin kwanciya? In zaki yi amai fa? Ko kuma kina sauri kin makara ki gurde ki fadi” tana dariya tace “baban baby kenan” yace “babies, kar ki rage min daraja mana” tace “okay Baban babies. Wannan cikin fa ba me laulayi bane ba, dame laulayi ne da ni da kaina zan nemi hutu. Ka barni in cigaba da zuwa please kaga yafi inyi ta zama a gida ko?” Amma fir Sadauki yaki, sai yayi enrolling dinta a online classes yadda zata zauna a gida tayi connecting da class dinsu online, duk abinda suke yi ko suke cewa tana ji kuma tana gani a screen din computer dinta, za kuma ta iya yin question a amsa mata, in bata kusa kuma zata iya saving lecture din sanda take free ta bude ta gani. Sai Murjanatu ta koma ita kadai take tafiya school sai Judith, dan ma dai ta samu at last ta koyi driving an kuma bata mota tana zuwa da ita.2 Diyam babu abinda take yi sai dai taci ta sha ta kwanta tayi bacci sannan ta kula da mijinta, wanda sun rasa gane a cikinsu waye yafi kula da danuwansa. Kullum tamkar kara wa musu kaunar junansu ake yi. A lokacin ne kuma ya bayyana mata abinda yake shiryawa. “Branch nake so in bude na Abatcha Motors anan kasar, kinga sai inke siyan motocin daga nan ina aikawa dasu Nigeria kuwa zanke siyarwa anan din ma. Tunda muka zo nake processing abin amma saboda kasancewar ni ba dan kasa bane ba sai na kasa samun permit na bude Company, but alhamdulillah yanzu na samu” ya dauko takardar ya nuna mata, ta karba tana karantawa yace “har na sayi fili ma, yanzu zan fara gina gurin tukunna sai in dauki ma’aikata insha Allah” ta rungume shi cikin jin dadi tace “congratulations darling. Allah ya cigaba dayi maka jagora mijina” ya zagayo da ita gabansa yace “ameen. Yanzu problem din shine, bana son harkar bude wannan branch din ta saka ni in kasa saka ido akan wancan, though lafiya lau komai yake tafiya a can din but I need an assistant, someone that I can trust” tayi shiru tana tunani sai tace “Alhaji Bukar bashi da ya’ya? Kayi masa magana mana ya hada ka da mafi aminci a cikin yayansa kaga shima zaiji dadin ka karrama shi” yayi murmushi mai kyau sannan yayi kissing forehead dinta yace “that is one of the reasons I love you, saboda kina da tunani mai kyau. You know what? Kema na baki aiki” ta bata rai tace “wanne aiki kuma bayan wanda already nake dashi?, na matarka?” Yace “you are now my special advisor” tace “duk ka dai part of my job ne as your wife”.1 Koda yaushe Diyam tana lissafin Saghir a ranta, amma bata taba yiwa Sadauki maganar ba saboda bata son taba masa zuciya, duk kuma sanda suka yi waya da Subay’a sai tayi mata maganar sa, duk da cewa Inna tana yawan kaita ta ganshi. Shima Sadauki bai taba yiwa Diyam maganar Saghir din ba amma shima Subay’a bata barshi gurin tambaya ba. A lokacin dasu Diyam suka kammala second semester dinsu a lokacin cikinta yana da watanni biyar, a lokacin kuma Sadauki har ya kammala ginin sabon branch din Abatcha Motors. Cikin Diyam ya dan fito kadan amma baiyi girma sosai ba, abinda ya fito sosai shine kyawunta, dan sanda suka fito daga jirgi a malam Aminu Kano international airport ita da Sadauki hannayensu rike dana juna, duk wanda ya kalle su sai ya sake kalla. Gidan Inna suka fara zuwa, a can suka ci abinci suka huta Diyam tana ta jin kunyar cikin jikinta, anan Sadauki ya barta sai dare yazo ya dauke ta duk da tayi ta rokonsa ya barta ta kwana biyu a nan. Yace “ina garin zaki kwana gida? Ki bari in nayi tafiya sai kiyi zauna ko kwana nawa ne kiyi musu”. A week after that, ya dawo daga office sai taga mood dinsa ba shi da kyau, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya zauna akan kujera tare da lunshe idonsa. Ta zauna a hannun kujerar tana shafa fuskarsa tace “wanka ko abinci?” Ya dan bude ido ya kalleta yace “bara in dan huta tukunna” sai ta sauka ta durkusa a gabansa ta cire masa takalmi ta hada da briefcase dinsa ta kai sama ta dawo ta sake zama a gabansa ta cire masa safar kafa ta dora kafafun a kan cinyarta tana mammatsa masa ita, tana jan yatsun kafar. Ya dan janye kafar yana cewa “ke! Chakulkuli fa kike min” ta sake jawo kafar tace “tausa fa nake yi maka, haka ake chakulkulin?” Sai tayi masa chakulkulin gaskiya a tafin kafarsa, Yayi dariya yana tashi zaune sosai ya janye kafarsa, sai ta mike tayi kneel down tana murmushi ta faki idonsa ta saka hannunta cikin rigarsa tayi masa chakulkuli tana cewa “gana gaskiyar nan nayi maka to” ya kama dariya har da zamowa kasa ya jawo ta suka fadi tare, sai shima ya yi mata yana cewa “sai na rama wallahi” ta kama kyalkyata dariya tace “wayyo zan mutu, ka bari wallahi, chakulkuli fa kanin mutuwa ne” ya sake ta ta janye daga jikinsa tana dariya, yace “kinci sa’a bake kadai bace ba” ta murguda masa baki sannan ta dawo kusa da fuskarsa tace “wanne mai tsautsayin ne ya taba min lion dina” ya danyi tsaki yace “mutane, yanayin rayuwa, cin amana. Babu abinda wasu mutanen ba zasuyi saboda kudi ba. Babu wanda ba zasu ci amana ba akan kudi. I don’t know mai mutanen mu suka mayar da kudi, abinda zaka iya samu yau gobe ka rasa, abinda zakayi bayani a lahira dalla dallar yadda akayi ka samu” tace “me ya faru?” Yace “Saghir zai fito next week insha Allah” taji dadi har cikin ranta amma sai ta boye ta danyi murmushi tace “alhamdulillah. An samu Kabir din kenan?”. Yace “tun kafin ku koma school ake neman Kabir an kasa kama shi, iyayensa sunki bada hadin kai dan haka ba’a san sanda yake shigowa gari ba ballantana sanda yake fita, nayi nayi abu ya gagara, daga baya ma sai na samu labarin wai ya kwashe iyalansa daga kano sun koma kaduna da zama baki daya. I told Ahmad amma sai yace ba zai iya kama shi a kaduna ba saboda kaduna ba a ikonsa take ba, in dai zai kama shi a can sai yana da arrest motive da zai nuna wa commissioner of police na kaduna, kuma a lokacin babu wani motive na kama kabir tunda zargi kawai akeyi babu shaida. Sai nayi tunani a kan wani abu, Nayi tunanin yadda son kudi ya kai Saghir inda yake a yanzu, na kuma tuna yadda son kudi ya saka abokinsa yayi framing dinsa, sai na tuna maganar hausawa da suke cewa sai hali yazo daya ake abota, da kuma maganar bature da yace birds of the same feathers flock together, sai na saka aka bincika min wanene next friend dinsu su biyun, sai aka hada ni da wani Bashir, kin sanshi?” Diyam ta gyada kai, yace “ranar da muka zo gari na kira shi nace ya same ni a office dina, and he came, na gaya masa abinda Kabir yayi wa Saghir ba kuma nemi ya taimaka mana mu kama Kabir din, farko sai yaki, but then as I expected sai ya fara bargaining, ya fadi kudin da yake so in bashi in ina so ya fada mana sanda Kabir zai shigo gari da kuma inda za’a same shi. I told him in yana so in bashi kudi sai dai yayi making Kabir yayi confessing cewa shi yayi framing Saghir and he agreed. I gave him some money. Yau sai gashi ya dawo, can You believe ge got Kabir drunk ya ringa yi masa questions yana amsawa shi kuma yana recording? It hurts me cewa duniya tayi lalacewar da friend zai iya yiwa friend dinsa haka, but considering abinda shima kabir din yayi sai naga yayi deserving shima ayi betraying dinsa”2 “Nayi submitting record din to Ahmad, yanzu zasu iya shiga har Kaduna su kama kabir, and Saghir is coming out latest next week”. Sai da Diyam ta gama da Sadauki sannan ta zauna ta kira Inna ta gaya mata labarin zancen fitowar Saghir. Inna tayi murna sosai tace “Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah yasa karshen wahalar sa kenan shi kuma Sadauki Allah ya saka masa da alkhairi” Diyam tace “ameen Inna” tace “bari in kira gidan Alhaji Babba inyi masu albishir”. A ranar zance ya zagaya family, zuwa washegari yab uwa suka fara kiran Diyam suna confirming “da gaske Saghir zai fito?”. Ranar da aka kama Kabir kuwa Hajiya Babba har gidan Diyam ta zo tayi mata godiya ita da sister dinta, hawaye fal idonta, tana ta bata hakuri dan gane da rashin kyautawar da suka yi mata a baya. Diyam ta cika su da abin arziki kuma ta nuna musu babu komai ai yiwa kai ne. Sun so ganin Sadauki suyi masa godiya amma yaki fitowa yace ace musu babu komai.+ Ranar da Saghir zai fito, Friday kenan, a ranar Sadauki yace da Diyam ta shirya tare zasu je. Daga gidan su gidan Inna suka fara zuwa suka dauki Subay’a sannan sannan suka tafi prison din. Suka yi packing a tsallake, Sadauki yace musu su zauna a mota ya shiga shi kadai. Bayan ya tafi Subay’a tace “Mommy nan prison ce ai” Diyam tace “eh” “inda Daddy na yake” “eh” “to Mommy mu shiga mana muhe mu ganshi” “a’a ba shiga zamuyi ba Subay’a” “to Mommy mai uncle ya shiga zaiyi a ciki?” Sai kuma ta bude ido ta ja numfashi tace “zuwa yayi ya fito dashi, dama ya gaya min zai fito dashi, Mommy ki bude min kofa inje gurin su” Diyam ta rike hannunta, sai kuma tayi murmushi tace “Subay’a uncle zuwa yayi ya fito da Daddy, amma kiyi zamanki a mota tunda uncle bai ce ki fito ba, yanzu zaki gansu sun fito tare”. Subay’a ta hakura bata fita daga mota ba amma kuma bata zauna ba, in ta leka ta waccan window din sai ta dawo ta leka ta wannan, in kuma taga motsi a bakin kofar gurin sai ta fara tsalle sai taga basu bane ba. Daga baya data gaji sai ta kwanta a backseat tana kuka wai sunki fitowa. At last sai gasu sun fito. Sadauki ne fara fitowa tare da wadansu mutum biyu wadanda Diyam ta gane a matsayin lawyers dinsa. Sai kuma Saghir ya fito tare da wani wanda ya tsaya yana ta yi masa bayanai har su Sadauki suka karaso mota. Mutanen suka yi masa sallama suka tafi sannan wancan ma yayi wa Saghir sallama ya tafi. Diyam ta zauna tana kallon shi ta cikin motar. Yayi baki sosai, ya kuma rame sosai, amma wannan kyawun yana nan sai dai babu gayun, kuma shekaru sun fito sosai a fuskarsa harda strings of furfura a gashin sa. Ta gane kayan jikinsa, sune kayan da yake sanye dasu ranar da aka kamashi a airport, she can remember yadda ya fito daga arrivals cikin yana taku dai dai yana jin duniya duk a tafin kafarsa ga kyakykyawar Fauziyya a gefensa but yanzu da ta kalle shi bata ga komai daga cikin characters din wancan Saghir din ba. He looked calm and very different. Sadauki ne yayi knocking a tagar da Subay’a take, ta dago tana kallonsa sai yace “Subis ga Daddy nan” ta mike da sauri ta kalli kofar prison din, tana hangoshi sai ta kama kokawa da handle din motar sai Diyam ta bude mata central lock tana dariya. Ai kuwa nan take ta bude ta fice daga motar a guje, Diyam ma ta bude ta fito tana cewa “careful Subay’a akwai titi fa”. Daga tsallake Saghir ya hango fitowar ta, ya kuma lura da yadda tayo kan titi da gudu dan haka sai shima ya taho da sauri gurin ta zuciyarsa tana bugawa. A tsakiyar titi suka hadu, ya daga ta sama amma sai ya kasa juyi da ita ya sauke ta yana haki yace “kinyi girma Subay’a, Daddy kuma bashi da karfi” sai ta rungume ƙafafuwan sa tana murmushi. Ya kamo hannunta suka karasa tsallako titin zuwa inda su Diyam suke a tsaye. Unintentionally hannun Diyam ya sauka akan cikinta tana kallon Saghir, sai taga ya kalli cikin sai kuma tayi sauri ta dauke hannun tana sunkuyar da kanta. Yayi murmushin takaici Yace “amarya” sai ta gaishe shi ya amsa yace “a sake min godiya gurin Mr Abatcha. Na goge sosai Allah ya bar zumunci” ta gyada kai a hankali tace ameen tana kallon Sadauki wanda yake ta danne danne a waya kamar baya jin me suke cewa. Sai ta kalli Saghir tace “congratulations. Allah ya kiyaye gaba” daga haka ta bude mota ta koma ciki. Sadauki ya dago kansa yana kallon Saghir ya nuna masa mota yace “Bismillah, sai mu ajiye ka a gida ko?” Sai Saghir ya kalli Diyam, ya hadiye wani daci a ransa ya girgiza kai yace “no, thank you. Kar in takura muku maybe akwai inda zaku je. Bara in hau napep kawai” Sadauki ya daga kafada kawai, sai ya tare masa napep din ya kuma biya kudi sannan ya yi wa mai adaidaitan kwatancen sabon gidan Alhaji Babba, tunda Saghir din bai sani ba.1 STORY CONTINUES BELOW  Saghir yace da Subay’a “zaki bini gidan Alhaji?” Ga mamakin su sai ta kalli su Diyam ta kuma kallonsa sannan ta girgiza kai tace “no, Aunty Asma’u tace yau Uncle Bassam zai zo, kuma na bashi sakon abubuwan da zai taho min dasu in zai zo, ka ga kar yazo bai same ni ba” Sadauki ya bude ido yace “Subis akwai zarar magana sai kace wata babba” Saghir yayi murmushi yana kallon inda Diyam take yace “gado tayi ai”. Har adaidaitan zai ja sai Subay’a tace “Daddy zan kawo maka ziyara gidan ka”. In silence suka bar gurin kowa yana lissafe lissafe a zuciyarsa. Sai can sannan Sadauki yace “ba zan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata. Bana son drama, nafi sonsa a nesa damu” bata ce komai ba, ya cigaba “amma zanyi masa komari ya samu kudin sa na gurin Kabir” Diyam tayi sauri ta kalle shi tace “kudin ka dai, ai kudinka ne” ya girgiza kai yace “nayi signing takarda cewa na bar masa kudina daya dauka, so legally yanzu kudin sa ne ba nawa ba. I have already talk to my lawyers, za’a siyar da kadarorin Kabir maybe za’a samu part of kudin amma nasan ba za’a samu gaba daya ba” Diyam taji dadi sosai a ranta tana yabawa kyawun zuciyar Sadauki, kamar yadda ya taba fada mata shi fire ne da ice, duk da wadda kazo dashi za’a tarye ka. Tayi masa godiya sosai sannan yace “kin san wani abu? Ni da Saghir are alot alike” ta bude ido dan ita bata ga hadin su ba bayan kasancewar su musulmai kuma half fulani tace “ta yaya?” Yace “kinga ni da shi duk only sons ne a gurin iyayen mu. Kuma iyayen mu suna son mu sosai sannan sun nuna mana soyayya in their own different ways. Duk kanin mu iyayen mu sun bamu kudi, the only difference is yadda muka yi da kudin da suka bamu. Sannan kuma duk muna sonki” ya fada yana kallon ta, tayi saurin girgiza kanta tace “he doesn’t” yace “he does. I saw it in his eyes yanzu da yana kallon ki” Tayi saurin kawar da maganar ta hanyar cewa “kuma duk ku biyun kuna da kanwa mai suna Murja” yayi dariya yace “ni kanwa ta Murjanatu sunan ta ba Murja ba, kuma ni nafi shi son kanwa ta” tace “ita kuma duk duniya gani take yi kafi kowa kinta” and they laughed together. ************************* Saghir ya juyo yana kallon Subay’a, yana kallo Sadauki ya kama hannunta ya bude mata kofa ta shiga mota sannan shi kuma ya zagaya ya zauna kusa da pregnant Diyam. Yayi sauri ya rintse idonsa tare da dafe kansa yana jin hawaye yana zuwa idonsa. Bai dauka har yanzu Diyam tana da gurbi a zuciyarsa irin haka ba, ya dauka ba zaiji komai ba inya ganta musamman saboda kokarin da mr Abatcha yayi masa, amma ita zuciya bata da linzami dole ya ja baya dasu ya daina ganinsu, ko kuma abinda yaji din yana da alaka da yadda Diyam din ta zama? Irin kyawu da cikar halittar da tayi? Wai hakan na nufin da ace ya kula da ita tsahon shekarun da suka yi a tare da irin haka zata zama kuma maybe da zata so shi? Lallai gaskiyar hausawa da suka ce tun ranar gini tun ranar zane, shi kuwa nasan ginin ya bushe dole sai dai ya hakura da zanen ko kuma ta sake sabon gini, sabon ginin wata rayuwar. But with who? Wannan wata tambaya ce for another time. Maganar da Subay’a ta fada ta dawo masa zuciyarsa “zan kawo maka ziyara gidan ka” wanne gidan? Shi fa yanzu ko gidan kansa ba shi da shi, wayake ma maganar gida, shi ko kwandala bashi da ita. Bashi da komai sai freedom dinsa, kuma ya dauki freedom din nasa ya zama another chance at life. Chance din kuma da insha Allah zai yi amfani dashi sosai yadda har sai mutane sunyi mamakinsa. Yadda har sai iyayensa sunyi alfahari da shi. Iyayen da a wancan lokacin ya wofantar ya wulakanta, abinda yake tunanin shine dalilin zuwansa inda yaje ba wai Diyam ba. Maganar mai napep ce ta dawo dashi hankalinsa, yace “yallabai munzo” ya leko dakansa yana kallon gurin yace “nan ne?” Mai napep yace “nan dai yayi min kwatance, yace jaen layin shago tara, gashi nan kuma har mun kusa fita daga layin tunda mun fara hango diga. Sai dai ka sauka ka tambaya” Saghir ya sauka yana kallon gurin, not that bad. Mai adaidaitan ya miko masa dari biyar yace “dubu biyu ya bani, ga dari biyar ka sha ruwa kai ma” Saghir ya karba harda yi masa godiya sannan ya tafi gurin wasu mutane su uku da ya hango a kasan bishiya ya gaishe su yace “dan Allah tambaya nake yi, gidan Alhaji Babba, bai dade da dawowa unguwar nan ba” duk suka ce basu sani ba, yayi gaba ya cigaba da tambaya amma babu wanda ya sani sai ya juyo ya fara retracing ta inda suka shigo yana yi yana tambaya, ga rana gashi dama jikin sa duk babu karfi. STORY CONTINUES BELOW  Da kyar ya samu wanda yace “inda akayi biki watannin baya?” Da sauri Saghir yace “eh” sai aka hada shi da yaro suka koma can inda ya baro, suka je har gaban wani gida sannan yaron ya nuna masa ya juya. Ya tsaya yana kallon gidan, a tsahon rayuwarsa bai taba tsammanin duniya zata yi juyawar da har nan gidan zai koma shine gidan baban shi ba, gidan ma kuma gidan haya, gidan hayar ma kuma Diyam ce ta ke biya masa. Ya shiga soro yayi sallama, Hajiya ya hango ta fito daga wani guri daya ga kamar kitchen tana amsa sallamar hannunta rike da wuka tana goye da wani yaron da bai sani ba a bayanta. Ta yarda wukar tana kiran sunan Alhaji, Alhaji ya fito, Hajiya yalwati ta fito, sai ga yaran gidan suma sun fito daga wani daki duk suna binsa da ido. Shi ya karasa shigowa, ya tafi gaban mahaifinsa ya durkusa amma sai ya kasa gaishe shi sai kuka ya kwace masa. Alhaji ya sunkuya gabansa ya jawo shi jikinsa ya rungume shi shima yana hawayen yace “bansan yau zasu fito da kai ba Saghir, da ko ba zan iya zuwa da kaina ba da sai in gaya wa mahaifiyarka ta je ko ta tura aje a taho da kai” Saghir ya goge hawayen sa yace “Mr Abatcha ne yaje ai, dashi da Diyam da Subay’a” ya fada yana jin dacin zuciyar dazu yana dawo masa. Alhaji yace “madallah dasu. Allah yayi musu albarka ya jikan Usman”. Nan fa gida ya rude da murnar dawowar Saghir, dan ma yanzu duk yaran babu saura kadan. Hajiya Babba ce ta kama shi ta kaishi daki, Hajiya yalwati kuma ta dora masa ruwan wanka, alhaji kuma ya aika a siyo masa nama da lemo kafin a gama abinci. Babu laifi suna cikin rufin asirin su duk da cewa alhaji har yau bai kuma gwada kasuwanci ba amma matansa suna yan sana’o’in su sannan yayansa mata da suke aikin gwamnati suna kokari gurin taimaka musu sosai, haka ma surukan gidan lokaci zuwa lokaci suna aiko musu da kayan abinci ko kuma suttura. A dakin Hajiya ya huta, naman da Alhaji ya siyo masa sannan yayi wanka ya chanja kaya zuwa wanda Hajiya ta ajiye masa akan gado. Sai ta kunto yaron bayanta ta mika masa. Kallo daya yayi masa yasan waye, sai kawai ya ajiye shi a gabansa ya sunkuyar da kai, tace “sunan babanku ne dashi, Jawad ake ce masa” yaron ya rarrafa da sauri yabi bayan Hajiya yana kuka alamar bai san shi ba.2 Dakin da yake soro, wanda kuma yake da kofa a waje shi dama Alh yasa aka gyara tun sanda yaji labarin dawowar Saghir gida. Aka shimfida carpet aka saka katifa, wardrobe, da kuma standing pan. Nan ne ya koma dakin Saghir. Kwanan Saghir biyar ya warware, duk da dai babu inda yake fita sai yan’uwa da suke ta zuwa yi masa murna. Inna ma tazo ita da Asma’u da Subay’a, suka kuma bar Subay’a anan tayi weekend tare da mahaifinta da kakannin ta. A ranar ne Alhaji ya kira shi dakinsa. Suka zauna sai ya dauko wata leda ya miko masa, Saghir ya karba ya bude sai yaga kudi a ciki, ya zaro ido “Alhaji kudi ai, kudin menene wannan?” Alhaji yace “kudi na ne, sauran kudin gida na ne da kuma abinda na samu daga gadon Usman, su nake ta ajjiye dasu da niyyar duk ranar da ubangiji ya sake baka dama a rayuwa ya saka ka fito daga prison nima zan sake baka dama in baka su kayi jari” Saghir yayi saurin girgiza kansa hawaye yana bin idonsa yace “Alhaji kar kayi haka, ka bani kudi sau ba adadi ina salwantar wa, kai ma kana bukatar kudin nan alhaji, kana da iyali kaima. Ka rike kudinka alhaji ka kula da kanka da matanka da kanne na” Alhaji yace “da wanne karfin Saghir? Ni ai tawa ta kare, karfi na ya kare, dan haka kai na dora wa wannan nauyin ka juya wannan kudin ka kula da kanka sannan ka kula dani da iyayenka da kannenka, kuma ka cigaba da kula dasu ko bayan rai na ne”. Saghir ya karbi kudin ya rike yana jin nauyi a zuciyarsa “anya kuwa akwai soyayya sama data iyaye?”2 Alhaji yace “akwai kuma wata magana da nake so muyi. Ina so ka kawo karshen rashin jituwar da take tsakani na da danuwana, ina son ka auri Suwaiba” ya dago kai yana kallonsa, Alhaji ya gyada kai yace “ta inda ake hawa tanan ake sauka. Tunda kuka bata dan haka ku zaku gyara”. Sai Saghir yaji Fauziyya ta fado masa a ransa. Bayan ya bata takardarta sun rabu, daga baya sai ta koma tana gaya masa cewa tana da cikinsa, ta kuma ce zata haifi cikin za kuma ta jira shi as long as bata samu miji ba har ya fito sannan kuma yana da sha’awar mayar da ita. Bayan ta haihu kuma ta kai masa babyn ya gani. And after seeing Subay’a rike da hannun Sadauki, baya jin zai kuma barin wata yar tasa a wani gidan. Dan haka indai Fauziyya bata yi aure ba to sai dai ya hada su ita da Suwaiba. STORY CONTINUES BELOW  Wata daya bayan nan Diyam tazo yi musu sallama zata koma Oxford, England. Washegarin zuwanta kuma alert ya shigo masa. Ya bude ido yana kallon kudin cike da mamaki ya tafi da sauri ya nunawa Alhaji. Alhaji yayi murmushi yace “Diyam ta gaya min jiya, kudin da Kabir ya gudu dasu ne aka dawo maka dasu. Zabi kuma ya rage naka kasan me zaka yi dasu”. Abinda Saghir ya fara yi shine ya dauki kudin da Alhaji ya bashi ya sayi gida madaidaici amma me kyau. Ba shine ya tare a gidan ba, Alhaji Babba da iyalin sa ne suka tare. Sai kuma ya sayi karamin fili a kusa da gidan a matsayin nasa “sai in zauna a kusa daku yadda zanfi jin dadin kulawa daku” next sai yaje har gidan Kawu Isa ya durkusa ya bashi hakuri sannan ya nemi ya bashi auren Suwaiba. Sai kuma ya tafi gidan su Fauziyya itama ya nemi auren ta. Amma duk kan su yace sai shekara mai zuwa idan ya samu nutsuwa sosai. Daga nan sai ya tafi kantin kwari, tsofaffin shagunan Alhaji wadanda wuta ta cinye babu komai sai ginin, shima ginin duk ya mutu an sace kwanukan. Cikin kwanaki kadan ya tayar da ginin su, yayi komai ya saro kayan duk da yasan Alhaji yana siyarwa ada da kuma kayan da yasan zamani ya zo dasu ya zuba a ciki. Sannan ya nemo tsofaffin yaran Alhaji wadanda suke kular masa da shagunan a da ya dawo dasu dan su suka san kan kasuwa, shi kuma ya zauna cikinsu dan shima ya fahimci harkar. Watanni kadan abubuwa suka warware wa Saghir, ya hada kudin neman aure ya kai gida biyu aka saka masa rana watanni takwas masu zuwa za’ayi duk a tare, sannan kuma ya fara ginin gidan sa a hankali. Gidan da yake da yakinin zai zamanto tushen sabuwar rayuwa a gurin sa. **************************** A lissafin Sadauki so yayi in sun bar Nigeria su fara tafiya Canada suyi kwana biyu tukunna, amma Diyam ta tubure masa ita bata son zuwa, ya gane abinda yasa bata so, ita kunya take ji ake ganin ta da ciki. Yayi dariya “to wai ke banda abinki, ni fa banga abin kunya anan ba, kowa ma fa yana yi” ta juya masa baya tana kallon Subay’a a cikin swimming pool tace “kuma kawai sai in je gidan inyi ta yawo da ciki suna kallona?” yace “baiwar Allah, idan baki je da ciki ba in kika haihu dai ai dole zasu ganki da dan ko? Ko shima cewa zaki yi ba ke kika haifa ba?” Tace “ai kuwa in naje gidan da baby to har in bar garin ba zan dauke shi ba” ya rike baki “to waye zaiyi feeding dinsa?” Tace “sai ya sha madara” ya kwanta akan camp bed din da yake zaune akai ya rufe ido yace “you are impossible Diyam, ke fulatancin kamar a kanki ya kare” ya sake cewa “kiyi addu’a to, kar a saka bikin su fanna kafin ki haihu, sai muga yadda zakiyi da cikin a gurin biki” tayi saurin cewa “Allah ya kiyaye, insha Allah sai na haihu”. Sai ta jawo kujerar da take kai kusa dashi tayi tagumi tana kallon sa, ya bude ido yana kallon ta yace “what?” A hankali tace “I want to kiss you, kuma Subay’a tana kallon mu” yace “ohh, a wannan bangaren kam kin ajiye fulatancin ko?” Sai kuma ta rufe ido tana dariya. Addu’ar Diyam dai bata karbu ba, dan suna komawa makaranta aka saka ranar bikin su Sa’adatu kuma wata biyu kadai aka saka, meaning cikin Diyam yana da wata takwas kenan za’ayi bikin. A dole Diyam ta taho Maiduguri lokacin bikin da katoton cikinta, Sadauki yana ta yi mata dariya amma sai ta maze da shiga harkokin bikinta sosai ta rike role dinta na matsayin babbar yaya. Da ita akayi shawarar komai, da ita aka sayi komai, wani abun ma in ana nema sai Mama tace azo wajen Diyam. Su Inna da Mama da Asma’u ma duk sunzo gurin bikin sun kuma Kawo wa amaren gift sosai har sai da Maman su Murjanatu tace “kayan nan anya basu yi yawa ba Amina?” Aka daura aure aka kai amare gidajen su. Sa’adatu ta auri Aminu an kaita Abuja. Falmata kuma Saifullahi mutumin Kano amma mazaunin Canada dan haka can zasu koma, Fanna kuma ta auri cousin dinta Al-mustapha zasu zauna anan Maiduguri amma zata zauna a gurin su Diyam ta karasa karatun ta. Bayan su Diyam sun koma England sai hankalinsu kuma ya koma kan haihuwa, Sadauki yana ta rawar kai, duk zuwa asibiti tare suke yi idan kuwa yaga namiji ne zai duba ta sai ya ja abarsa su bar asibitin. Twins ne kamar yadda Sadauki yake ta addu’a. Diyam tayi tunani sai taga cewa ba zata iya tuno yadda haihuwa take ba tunda bata yi labor a haihuwar Subay’a ba, haihuwar twins kuwa ba zata iya tuna yadda abin ya kasance ba dan haka sai ta shiga maternity classes, anan ta fahimci komai ta kuma yi browsing wasu abubuwan ta sake fahimta. Abinda take tsoro guda daya shine shigar Sadauki gurinta in tana labor, tasan kuma za’a bashi option din shiga kuma tasan zai shiga din. Sannan tasan in dai ya shiga sai ya hargitsa daga ita har me karbar haihuwar kuma in yaga wahalar da ake sha a gurin haihuwa sai sunyi rigima kafin ya barta ta samu wani cikin. Ta kuma san yadda yake son yaya, dan haka ta yanke shawarar yi masa dabara yadda ba zata haihu a gabansa ba saboda ta haifa masa yaya as many as yadda Allah ya basu.2 Ranar data fara jin alamar labor da daddare sai taki nunawa Sadauki, da safe kuma sai tayi pretending as if bacci take yi har ya gama shiryawa a hankali dan kar ya tashe ta, ya zo yayi mata kiss ya fita. Sai bayan fitarsa sannan ta tashi ta dauko jakar tafiya asibitin ta wadda already ta riga ta shirya ta ta kuma yi driving kanta zuwa asibitin. Sai da taje suka aunata suka kuma tabbatar mata da cewa haihuwa zata yi sannan suka bata daki suka kuma nemi su kira mijinta amma ta hana su tace sai ta haihu tukuna. Ta sha wahala ba kadan ba, Sadauki ya sha kira kamar sunan sa zai kare ta kuma yi nadamar kin gaya masa dan da yana kusa ko ganin sa in tayi zata ji dadi. A haka har Allah ya sauke ta lafiya ta haifi namiji first, sai data huta sannan labor ya sake dawowa ta haifi mace. Ana miko mata su taga fuskar babansu amma fatarta, sai dai namijin bai kai macen haske ba. Sai da aka gama garata aka kuma gyara babies din ta kuma danyi bacci kadan ta huta sannan tace su kira shi. 30 minutes after kiran nasa sai gashi ya shigo asibitin hakan yasa Diyam ta tabbatar da cewa yayi breaking every traffic rule a hanya saboda sanin nisan asibitin daga office dinsa. A rikice ya bude kofar dakin da aka nuna masa ya shiga. A tsaye ya ganta a gaban window ta juya masa baya. T-shirt dinsa ce a jikinta, wadda ta kawo mata har zuwa rabin cinyarta, gashin kanta a barbaje wani ya sauka a bayanta wasu akan kafadun ta wasu kuma sun zubo kan kirjinta. “Diyam” ya fada cikin sarkewar murya. Ta juyo tana kallonsa, hannunta rike da jariri tana rocking a hankali, fuskarta da faffadan murmushi. Ya karaso cikin sassarfa ya jawo ta jikinsa ya rungume ta yace “don’t you ever do that to me again” ta kwantar da kanta akan kirjinsa tace “am sorry my Lion. Bana son in tayar maka da hankali ne” yace “kinsan tashin hankali da naji kuwa? Kinsan da yadda nazo asibitin nan kuwa? I tot karya suke yi min da suka ce lafiyar ki kalau, I tot ba zaki iya haihuwa ba tare da ni ba” tace “I missed you sosai, nayi ta kiran sunanka” ya danyi dariya yana dago fuskarta da hannun sa daya, taji kunya ta mayar da fuskar kasa. Ta zaunar dashi akan kujerar da take dakin ta mika masa babyn hannunta, ya dan leka cikin diaper dinsa fuskarsa kamar zata yage dan murmushi. Ta dauko dayar da take bacci a kan gadon su ta mika masa itama. Ya rike su hannu bibbiyu inya kalli wannan sai ya juya ya kalli wannan ya kasa tantance wanne yafi kyau a cikin su. Yayi musu addu’a. Tana tsaye a gabansu tana kallon su sai ta fara buga kafa cikin shagwaba, ya dago kai yana kallon ta cikin alamar tambaya sai tace “ni a ina zan zauna, sun tare min gurin zama na” ya daga babies din da sauri yace “zo ki zauna akan cinya” ta tafi ta zauna tana karbar daya, ta rike ta da hannun ta daya dayan hannun kuma ta zagayo wuyansa dashi. Sun jima a haka suna kallon kyautar da Allah yayi musu sannan yace “Baffa ne da Ummah. Baki ga yadda suke ta kokarin rike hannun juna ba?” Diyam tayi dariya tace “babu ruwana sai na gaya wa Inna” yayi murmushi yace “so kike ta biyo ni da muciya?” Sukayi dariya a tare. Sai ta kwantar da kanta a wuyansa shi kuma yayi kissing forehead dinta tare da sauke ajjiyar zuciya. A hankali yace “ALHAMDULILLAH”11 Godiya ta tabbata ga Allah da ya bani ikon kammala wannan littafi lafiya. Allah ya kara salati ga fiyayyen halitta (SAW) Allah kuma yasa muna da rabon ganin sa baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE