DR BOBBY CHAPTER 5 BY AISHA RANO

Ranan Thursday da wuri suka shiga school sbd sunaso su zauna da group dinsu before time na presentation…tun 7 suka hadu gaba daya class suna rehearsing karatunsu…karfe 8 daidai kuma suka fara lectures dinsu…inshort basu fito daga class ba sai around 1..suna fitowa suka nufi cafeteria don cin abinci…a ciki suka hadu da Sa’eed yayi musu reserving table suka karasa suka zauna kowa ya bada ordern abinda yakeso…sunyi shiru kawai abincin sukeci don ko breakfast basuyi ba suka fito…kaman daga sama kawai suka ga mutumi yaja empty kujera dake kusa dasu ya zauna…a tare suka dago kansu duk su ukun suna kallonshi…Tajuddeen ne sanyeda uniform dinshi as always yanata kallon Lamido yana sakin murmushi…Billy taja wani tsaki tacigaba da cin abincinta…shima Sa’eed cigaba da cin nashi yayi ba tareda yace komai ba…a hankali Lamido ta ajiye spoon din hannunta tana dubanshi kaman zata sa kuka tace”what?..”kaman jira yake yace”magana nakeso muyi dake kinata min wulakanci Lamido…dan Allah ki bani dama ko Hostel ne nazo sai mu tattauna a can”…yana rufe baki tace”ba damuwa u can come to the hostel anytime u like…yanxun dai kayi hakuri ka tafi cox muna gama cin abincin nn class zamu koma”…ya danyi shiru yana kallonta kaman bai yadda da abinda ta fada ba yace”U sure?..”cikeda assurance tace”💯Sure…just go we’ll talk later”…bai sake cewa komai ba ya tashi daga wurin…sai kuma ya tsaya yana kallonta yace”i love you “…gyada mishi kai kawai tayi ya juya ya bar wurin…yana tafiya Billy kaman jira take ta dago tana hararanta tace” ki tabbata a kunnen Ammi duk wnn maganan da kukayi…shine hadda wani cewa yazo hostel ya sameki sbd tsoronshi kikeji koh?..”girgiza kai kawai tayi ta cigaba da cin abincinta as batada energy din rigima da Billy yanxu sai cikinta ya dauka…bestie dai yana zaune pretending kaman baya sauraronsu har suka kammala ya biya kudin gaba daya snn suka fita…su suka wuce female masjid dan yin sallah shi kuma ya koma class cox ya riga yayi sallah tun daxu…suna idar da sallah kiran provost ya shigo wayanta…ta dauka da sauri tana fadin”Good afternoon Sir”…yace”afternoon Lamido are you guys ready?..proprietor ya shigo tun daxu and in the next few minutes zakuzo Auditorium hope you are all set?..”tace”we are Sir “…yace” alright tell them mu hadu auditorium by 2″.. a hankali tace”toh..”suna gama mgn ta ajiye wayan a hankali cikin ranta tana nanata Auditorium kuma?…Common presentation da zasuyi shine sai an kaisu har wani auditorium sbd shegen iyayi…tasan duk wnn ba plan din kowa bane sai na wancan inyamurin mutumin…kawai presentation za’ace su tafi har auditorium sbd neman magana.

Karfe biyun kuwa cikin Auditorium din yayi musu…basu jima da zama ba malamai suka shigo su wajen 4 hadda Sir Abdool dinta inji Billy😆..sai shi proprietor din sai provost…daga dan sama kadan malaman suka zauna inda aka tanadar musu kaman high table haka…bayan gaisuwa da dogon bayani daga malaman akace the 1st group should come forward… a yanda suka tsara abun dama ba gaba daya members na kowane group zasu fito ba..each group dunyi selecting mutum uku da zasuyi representing dinsu cox idan akace gaba daya kowa sai yayi bazasu samu gamawa da wuri ba…kaman yanda yake alphabetically group din farko nasu Lamido ne dan haka ba wasting of time suka fita ita da sauran colleagues dinta…first speaker ce ta fara musu bayani tun daga introduction zuwa definition of terms haka..bayan ta gama second speaker itama tayi nata Lamido kuma itace karshe…saida duk suka kammala ta amsa markern dake hannun colleague dinta tareda karasawa jikin white board dake daga gefensu ta zana diagrams dake cikin topic din nasu tayi labelling snn ta fara explanation…sosai Audit din yayi tsit tun daga dalibai har malaman kowa ya nutsu yana sauraronta…da yawa daga cikin malaman dama sun santa tunda akwai wani end of year presentation da sukeyi duk end of session and ko na last year da akayi itace tayi winning…bayan wnn akwai wani tradition da suke dashi a school din at the end of every session ana fitar da overall student for both Nursing and Midwifery departments snn kuma a fitar da Wanda yafi kowa point a gaba daya college din as the overall student of the year…zaayi printing qaton poster mai daukeda pictures na overallers din kowa da sunanshi dana department dinshi sai kuma point dinshi…haka zaa kafe wnn postern kusada general notice board snn a sake kafe wani ta wajen admin block…so da yawa cikin malaman ko basu santa a zahirinta ba sun santa either a wancan poster tunda last year ita tayi overalling a department dinsu ko kuma a end of year presentation da akayi na last year…shi kanshi Bobby yau sai yaji wani abu daban gameda yarinyar…bama ita kadai ba gaba daya class din sun burgeshi sosai coz sunada kokari..cikin ranshi yake ayyana wai haka duk students din nashi suke da kokari ko kuwa iya class dinsu ne haka?..yana cikin tunaninshi yaji Audit din ya kaure da wani irin loud tafi yana dubawa sai yaga ashe sun gama shine ake musu tafi…babu 6ata lokaci group two suma suka fito sukayi nasu followed by group three wanda sune last group…bayan sun gama gaba daya student affairs dinsu ya tashi yana praising dinsu tareda karfafa musu gwuiwa kan karatunsu…bayan ya gama provost ma yayi nashi sai kuma mai gayya mai aiki Alhaji Dr Bobby jikan Waziri lol😃..shima praising dinsu yayi sosai snn ya fadam each group marks din da sukayi scoring wanda dashi zaayi amfani a matsayin c.a dinsu..bayan ya gama malamai suka fara fita followed by students din…kafin su karasa class kiran Sir Abdool ya shigo wayanta…ta dauka tana gaisheshi yace”Lamido can i please see you now?..”ta danyi shiru tana tunanin ne zatace mishi ya sake cewa”ba dadewa zakiyi ba Please!”…ba yanda ta iya haka nan tace mishi gata nan…ta dubi Billy da suke tafiya tare tace”kinji Sir Abdool wai inje…ni kuma na gaji wlh so nake in koma hostel in kwanta”..kar6an text book dake hannunta Bilky tayi tace”yace fa ba dadewa zakiyi ba..kiyi hakuri kije ni zan jiraki a class”..Aysha tayi murmushi tana jinjina wnn so da Billy ke mishi ta juya ta tafi…tazo daidai kofan office dinshi tana shirin budewa Bobby da Nur suka fito daga office din Nurun…ta dauje kanta da sauri sakamakon idanunshi da suka sauka a kanta…ta budr office din da sauri ta shiga su kuma suka wuce don dama tafiya gida zasuyi…tana shiga ya mike daga zaunen da yake tareda dawowa kan soafer ya zauna ya nuna mata kusa dashi itama batayi mishi musu ba  zauna…ya tsura .ata ido yana sakin wani shegen murmushi yanajin ina zai saka yarinyar nan ne tsabar son da yake mata…itadai kanta na kasa as batason wnn kallon kasa kasan da yake mata…shi kuwa rasa kalmomin da zai furta mata yayi sai kawai ya kamo both hannayenta yakai su bakinshi yayi kissing kafin ya ajiye yana fadin”i love you”…daure fuska tayi sosai tana dan turo baki ta kalleshi…yasake sakin wani murmushi yana shafa gashin kanshi yace”Ya Allah”…ganin ta sake tsuke baki ya kama ears dinshi yace”am sorry sonki ne yayi min yawa wlh Lamido..so accept my apology inshaAllah bazan kara ba”..batace mishi komai ba sai mikewa da tayi yace”please forgive me”..ta gyada kanta kawai ta fita daga office din.

Da dare Hostel suna cin abinci itada Billy kiran Daddy ya shigo wayata…tayi saurin hadiye na bakinta ta sake daidaita nutsuwarta snn ta daga tana cewa”Hello daddy barka da dare”..Daddy yace”sallamanki kenan ba?..”da sauri tace”sorry daddy..salamu alaykum barka da dare”..yace”barka dai ya studies?..hope you are doing well?..”tace”inayi daddy ya aiki”..yace”Alhamdulillah na dawo gida..ba wani matsala koh?..”tace”ba komai daddy”yace”MashaAllah bawa Bilkisu waya”..ba musu ta mikama Billy wayan..itama ta kar6a da sallama tana gaisheshi..yace”inda kika fita hankali knn?..ya karatu fatan ba wani matsala?..”tace”babu komai daddy”..yace”to Alhamdulillah aci gaba da dagewa sosai..Allah muku albarka”..Billy ta amsa da”Ameen mungode daddy Allah ya kara girma”..shima yace”Ameen”..daga haka ya kashe kiran…Aysha ta kar6i wayan tana sauke ajiyar xuciya tace”sai yanxu hankai na ya kwanta..da naga kiran nayi zaton ko wani laifin nayi”…Bilkisu ta girgiza kai tana cigaba da cin abincinta tace”bakida gaskia ne ai shiyasa”.


Bobby bai samu dawowa gida ba sai yamma likis…su Miemie ya samu a parlor suna kallo..gaba daya suka mishi sannu da zuwa ya amsa idonshi kan Sab da hankalinshi gaba daya ke ga phone dinshi yace”kai yaushe zakuyi resuming school ne?..”Sab yace”next week ne but dan Allah inaso in kara ko one week ne plss”..bai rufe baki ba Bobby yace”C’mon keep quiet..waye zai bari ka kara one week din?..you are deceiving yourself”…daga haka ya kama hanyan parlon Mummy…ga mamakinshi bai sameta a parlon ba sai ya nufi bedroom dinta yana mamakin meye sa   bedroom da wuri haka…Allah yasa dai lafiyanta qalau…yana tura kofan ya shiga sai sallaman da yake kokarin yi ya makale a bakinshi sakamakon abunda ya gani…Mummy ce zaune gefen gado tana hawaye Anty Sumy na zaune kusada ita tana hawayen itama…baisan lokacinda ya saki suit dinshi dake a hannunshi ba ya karasa cikin dakin da sauri…gefen Mummy ya zauna ya kamo hannayenta hankali tashe sosai yace”Mummy what is happening here?..why are you two crying?..”damke hannunshi Mummy tayi ta juya tana kallonshi tace”your grandfather Bobby..Waziri..idan bawan Allahn nan ya mutu baisan inda kuke ba bazan ta6a yafema kaina ba Bobby..you need to see his condition..he is seriously..”bai bari ta karasa ba ya rungumeta a jikinshi…itama saitayi lakwas a jikin nashi tana cigaba da hawaye…suka hada ido da Anty Sumy dake kallonsu tana hawaye itama..da ido ya tambayeta me yake faruwa ta buda mishi hannu alaman he has no idea…saida yaji kukan nata ya dan tsagaita snn ya sake dagota still yana rikeda hannayenta yace”Mummy kukan ya isa haka please kar bp dinki yayi rising..besides waya fada maki condition da wazirin ke ciki?..how did you know?..”tace”a news na gani wai ciwon nashi yayi worst har sun daukeshi daga Egypt zasu maidashi india..Bobby he is seriously sick inaso kuje ku dubashi idan ya dawo”..cikin 6acin rai tuno abubuwan da suka faru a baya yace”but Mummy why?..why zamuje dubashi bayan bai damu damu ba..bai damu ko muna raye ko mun mutu ba?..”yana rufe baki tace”because he is your grandfather Bobby..komai girman laifin da yayi he is still the father to your Dad and nobody can change that”..ta kamo hannunshi snn tacigaba”do you think if your Dad was alive zaiji dadin yanda kake treating mahaifinshi?..do you think he would be happy if we choose to hide ourselves from them komai girman abunda suka aikata?..”a hankali ya zame hannunshi daga nata lokaci daya idonshi sukayi jajir sbd 6acin rai yace”but Mummy we didn’t hide ourselves from them sune basuga daman su nemi inda muke ba..for five long years Mummy idan suna sonmu meyasa basu nememu ba?..”yana rufe baki tace”because he is sick Bobby..sanin kanka ne tun ranan da mahaifinku ya fadi ya mutu bai sake samun lafia ba”…cikin anger daya fara kasa controlling yace”dukda bashida lafia if he really love us..if he really want to see us he could’ve at least ask one of his selfish and wicked sons to look for us but he didn’t and do you known why?..because he hates us..he despise…”bai kai ga karasawa ba yaji saukan kyakyawan mari a cheeks dinshi…ya dafe cheek din da sauri yana duban Mummy dake kallonshi rai a 6ace itama…Anty Sumy ta taso da sauri ta kama hannun Mummy hawaye na wanke fuskanta tace”Mummy take it easy please..kinsan condition dinki Mummy kar wnn abun yasa bpnki yayi rising please”..ta karasa mgnr tana kuka sosai…Bobby da yayi suman wucin gadi sai yanxu ya dawo hayyacinshi…tun da yake zai iya counting sau nawa Mummy ta dakeshi  but now she slapped him sbd azzaluman mutanen can..wasu hawaye yaji suna cikowa idanunshi amma ya dake bai bari sun zubo ba ya dora kanshi a shoulder dinta murya can kasa yace”am sorry for hurting you Mummy amma kinsan gaskia nake fada fa..mutanen nan basu ta6a kaunarmu ba Mummy..kema basa sonki amma meyasa kikeso mu sake kai kanmu inda suke bayan duk laifukan da sukayi?..”dago kanshi tayi tareda cupping fuskanshi tace”because they are your relatives Bobby..they are your Family and Family will always be considerd as Family nor matter what..so try to understand me please”…shiru kawai yayi yana yanajin yanda maganganunta suke neman kashe mishi jiki…Anty Sumayya dai na zaune tana kallonsu..itama Mummy ganin tasirin da maganganunta sukayi ta sake yin kasa da murya tace”try and understand Bobby please..ko bamu nemesu yanxu ba dole watarana dalili zai sa mu nemesu shiyasa nakeso mu daidaita dasu tun kafin zuwan wnn lokacin..”shiru ya sakeyi idanunshi lumshe yana sauraronta…ita kuma Mummy ta dan saki murmushin cin nasara snn tacigaba”kaga watarana Aurenku ne zai taso kuma nasan kasan duk dunia babu inda mutum zaije neman aure a bashi ba tareda dangin mahaifi ba..and gaba daya ku ukun babu wanda keda aure gara Sumayya ta ta6ayi hadda yara amma kai da Sabeer baku ta6ayi ba Bobby..dole kuma watarana lokaci zaizo da zamu bukaci suzo su nema muku aure”…sake daure fuska yayi jin ta fara zancen aure yace”indai wnn mutanen ne zasu nemamin aure Mummy wlh na gwammace har in mutu banyi aure..Anty Sumy da Sab kuma duk wanda bazai kar6i aurensu a wurina ba saidai ya hakura”..ta bude baki zatayi mgn ya dora finger dinshi kan bakinta yace”enough talking about them please..yanxu ki samu ki kwanta kina bukatan hutu sbd bp dinki..maganan zuwa dubiyan Waziri kuma Allah ya dawo dashi lafia sai muje”…lokaci daya murmushi ya mamaye fuskanta tace”da gaske zakuje Bobby?..tasan indai ta samu ta shawo kanshi ragowar basuda matsala dama Bobbyn shine mai taurin kain…yace”anything for you Mummy..yanxu dai ki samu ki huta sosai”..da sauri ta shiga gyada mishi kai tace”Allah ya muku albarka”..yace”Ameen Mummy”..Anty Sumy ce ta taimaka mara ta kwanta shi kuma ya juya a hankali ya fice daga dakin zuwa nashi…a gurguje yayi wanka tareda alwala ya fito ya tayar da sallah tubda an idar a masallaci…ya dade zaune yana addu’a kan Allah ya mantar da Mummy mgnr zuwa dubiyan nan dan fa shi har yanxu baiji zai iya daukan kanshi ya kai Gombe ba..har abada gani yake bazai ta6a iya mace kalan rashin imani da suka gwada musu ba har shi wazirin daya kasance kakansu…da kyar ya samu ya mike daga wurin da yayyi sallahn ya fada kan gado ya kwanta…ya runtse idonshi da karfi yana jin duk wani abu daya faru na daow mishi kaman yanxu yake faruwa…bayason yana wnn tunanin amma ya kasa dakatar da kanshi.

ASALIN LABARI…

Lokacinda Attahir wato mahaifin Bobby yakai ma mahaifinshi Wazirin Gombe mgnr yanason Auren Nadia daya hadu da ita a kano kai tsaye yace bai amince ba sbd kasancewarta ba bahaushiya ba…hankalinshi ya tashi sosai ganin da gaske waziri naso ya rabashi da matar da yafi kauna a dunia..ya jema mahaifiyarshi da mgnr itama ta nuna batada taimakon da zata iyayi masa har tunda mahaifinshi yace ya hakura da ita kawai ya hakura…bai hakuran ba yacigaba da lalla6a waziri yana nusar dashi illar nunama wanda ba yarenku daya ba banbanci…ya kuma nusar dashi cewa har tunda ta kasance musulma kuma yar Nigeria yana ganin ko addini bai haramta mishi aurenta ba…ran waiziri ya 6aci sosai ya kuma ce matukar shi ya haifeshi bazai ta6a amince mishi ya auri inyamura ba…wnn mgn ba karamin daga hankalin Attahir yayi ba…step brothers dinshi da suke ganin waziri ya fifitashi a kansu nan suka samu damar shiga suna cigaba da ingizashi kan kar ya yadda ya amince ya hada jini da inyamurai wnn zuga kuma yayi tasiri a wurinshi sosai…Attahir da yaga bashida wani mafita kuma bazai iya hakura da Nadia ba kai tsaye yaje ya samu kakarshi mahaifiyar waziri knn yayi mata bayanin duk abunda ke faruwa nan kuma ta goyi bayan lallai sai an aura mishi matar da yakeso…hakan ba karamin 6ata ran waziri yayi ba amma ya hakura ba don yanaso ba ya tura aka nemo masa auren yarinyar har Enugu state bisa umarnin da mahaifiyarshi ta bashi kan lallai lallai ya aurama Attahir matar da yakeso idan baiyi haka ba kuma itama zata tsine masa kmr yanda yayi ikirarin zai tsinewa nashi dan.

Cikin lokaci kankani akayi bikinsu aka gama…sbd sanin da yayi cewa yan uwanshi da mahaifinshi ba son auren suke ba sai ya nema mata gida a kano ta zauna itama tacigaba da karatunta…tsakaninshi da Gombe saidai yaje ya gaisa dasu ya dawo kanon ma kuma bai cika zama ba sbd a lokacin yana aiki a Delta state…tun bayan aurensu kuma ko mutum daya baizo daga cikin ‘yan uwanshi da sunan yazo ganin matarshi ba…a haka suka dauki tsawon shekara daya bata ta6a ganin wani nashi a inda take ba..a lokacin ta damu sosai da rashin zuwan nasu shi kuma saidai ya bata hakuri yace mata komai zai wuce…ana haka ya samu kira daga waziri kan lallai ya tattaro ya dawo Gombe da zama a cewarshi wai matarshi ke hanashi zuwa ziyararsu yanda ya kamata…baiyi nasa musu ba ko kadan as baison ya sakeyin laifi a wurinshi haka ya tattarata kaman yanda wazirin yace suka koma gidanshi dake cikin Gombe…da farko Nadia taji dadin komawan nasu sbd tana ganin idan tana kusa da yan uwanshi zasufi saurin kar6anta a matsayin suruka sai kuma daga baya ta gane mutanen nan bazasu ta6a kaunarta ba…kyara da tsangwama ba kalan wanda bata gani ba a wurinsu abun har ya kai ko taro sukeyi bata isa ta shiga cikin matan brothers dinshi ba dan zasu yita jifanta da munanan kalamai suna cewa ita inyamura ce..hatta yaransu sunan da suke kiranta dashi knn inyamura…a lokacin data samu cikin Sumayya tayi farin ciki sosai sbd tana ganin kilan idan ta haihu zata iya samun soyayyar waziri dana sauran ‘ya’yanshi ko dan sbd abunda zata haifa…mahaifiyar mijinta dama bata ta6a samun matsala da ita ba hakama Munubiya..kawai dai basa iya sakewa su nuna damuwa da ita sosai sbd gudun 6acin ran waziri…duk wnn abun da ake Attahir bai ta6a daga baki yace zaiyi mgn ba sbd yasan ko yayi ba amfani zaiyi ba tunda goyon baya suka samu wajen waziri…’yan uwanshi da dama tuni yasan basa kaunarshi sbd soyayyan dake tsakaninshi da waziri shiyasa suke amfani da wnn damar suna rura wutar tsanarshi cikin zuciyar babanshi…yana sane sarai suke tunzurashi yake aikata duk abubuwan da yakeyi shiyasa bazai taba bude baki yayi complain ba fatanshi daya Allah ya rabashi da mahaifin nashi lafia.

Lokacin da aka haifi Sumayya Attahir yayi farin ciki sosai hakama qanwarshi mahaifiyarshi sun tayashi murna matuka saidai babu daman nunawa sbd waziri…lokacin da ya dauketa ya kai masa ita ko kallonta baiyi ba yace ya fitar mishi da ita a wurin…wnn abu ba karamin 6ata ranshi yayi ba…yana ganin ko arniya ya aura bai kamata ace his own father yayi treating yarinyarshi irin haka ba..abun ya 6ata ranshi matuka…wnn dalilin yasa baiyi shawara dashi kan sunan da zaa sama yarinyar ba kamar yanda sauran ‘yan uwanshi sukeyi duk wanda matarshi ta haihu shi ke za6an sunan da za’a sa…baiyi shawara da kowa ba yasa mata Sumayya sunan qanwar Nadia da bata dade da rasuwa ba a lokacin…aikam taji dadi sosai dan bata ta6a zaton zaisa sunan yar uwarta ba.

Haka rayuwa yacigaba da tafiyan musu yau dadi gobe babu har Sumayya ta fara wayo..a lokacin itama sai aka fara tsokanarta da inyamura ko kuma su kirata da ‘yar inyamura..wnn abu ba karamin daga hankalin mamanta yake ba amma ba yanda ta iya haka a koda yaushe take bata hakuri tareda fada mata cewa watarana komai zai wuce wnn dalilin yasa ko ina bata zuwa kullum tana gida nane da mamanta idan mahaifinta na gari kuma tana nane dashi…duk wnn abun dake faruwa Nadia bata nuna mishi damuwarta sbd yanda yake iya bakin kokarinshi yaga basuyi lacking komai ba itada ‘yarshi.

Bayan Sumayya saida ta dauki tsowon shekaru hudu kafin ta samu wani cikin…farin cikin da Attahir yayi da jin labarin cikin har mamaki ya bata…da dadewa tasan yanada son yara tunda tana ganin yanda yakeji da Sumayya amma yanda yake farin ciki da cikin ko wanda bai ta6a haihuwa ba sai haka…wnn dalilin yasa yake kulawa da ita yanda ya kamata…duk yake gari da kanshi yake kaita antenatal idan baya nan kuma tayi driving kanta…a kullum cikin godema Allah take sbd yanda mijinta har yanxu kiyayyan mahaifinshi dana brothers dinshi baisa ya canxa mata ba..ga kuma budi da Allah ke kara mishi a kullum.

Lokacinda haihuwa yazo mata sai akayi rashin sa’a baya gari…daga ita sai Sumy a gidan gashi tanata kiran wayanshi bai shiga as dama ya fada mata zasu shiga jeji she might not reach him sbd network issue…ba yanda ta iya haka ta kira number wani brother dinshi tayi mishi bayanin halinda take ciki yace mata baya gari saidai ta kira wani…bata hakura ba ta sake kiran wani shi kuma yace zai turo matarshi amma shiru har kusan bayan awanni bai turo kowa ba..gaba daya ta fita hayyacinta as ciwon kara gaba yakeyi sosai gashi kuma batada number wani cikin brothers din nashi sai su biyu ga kuma sumayya daketa faman kuka tun daxu ganin halinda mamanta ke ciki…tayi kokarin kiran munubiya a waya itama bata sameta ba..a karshe dai dole sai sumayya ta aika tayi mgn da wata neigbour dinta ba bata lokaci matar tazo ta taimaka mata suka tafi asibiti…lokacin wajen karfe 9 na dare…suna zuwa aka kar6eta akayi labour room da ita..midwives kusan uku ne kanta suna kokarin taimaka mata amma har gabannin asuba bata haihu ba ga dan karen wahala da takesha…sun kira doctor da yake on call sun mishi bayani yace zaizo kawai ayi masa Cs kafin doctor din yazo kuma sai ta fara fitting(jijjiga)..hankali tashe one of midwives dake kulada ita ta sake kiran doctor ta fada mishi tana fitting yace gashi nan kan hanya ya kusa zuwa…dama tunda suka fada mishi yanda blood pressure dinta yayi rising yasan da kyar idan baiyi leading to preeclampsia ba.

Doctor na karasowa basuyi wasting time ba suka shiga da ita theatre…neighbor dinta data kawota asibitin na tareda Sumayya da aka samu tayi bacci da kyar sbd jiya bata samu tayi sosai ba…before a shiga da ita theatre din kiran mijinta ya shigo wayanta dake hannun matar data kawota…nan tayi picking ta kumayi masa bayanin halinda ake ciki…hankalinshi ya tashi sosai ya kuma ce gashi nan tahowa Gombe yanxun nan…suna gama mgn ya wuce airport ya taki sa’a kuma ya samu flight din Kano nan ya sayi ticket ya zauna jiran lokacin tashi yayi.

Bai samu isowa Gombe ba sai around 10…daidai lokacin kuma ake fitowa da ita daga theatre..baisan time din da hawaye ya cika idonshi ba ganin yanda aka turota kan trolley bed an rufeta da wani green kyalle kaman babu numfashi a jikinta…shiyasa tun jiya yakejin hankalinshi ba kwance ba ashe halinda suke ciki knn.

Kai tsaye akayi moving nata Amenity dake female surgical ward…wanda suka kawota suka dagata daga kan trolley bed snn suka dorata kan bed din dakin suka fita…Nurse din da tayi resuscitating baby ta mika mishi babayn ya amsa da sauri itama ta juya ta fita..ya rage dagashi sai Sumayya a dakin dan matar data kawota kin shogowa tayi tace mishi zata koma gida…yayi mata godia tareda kyauta mai tsoka snn ta tafi…a hankali ya karasa kan wani kujera ya zauna har yanxun yana rikeda babyn a hannunshi…ya sauke idanunshi kan babyn da a kallon farko yaga tsantsan kamannin da yakeyi dashi…lokaci guda wani murmushi da bai shirya mishi ba yayi escaping lips dinshi…soyayya babyn yaji yanaji sosai har cikin jininshi..haka suka hada kai shi da little sumayya sunata kallon babyn daketa mustu mutsu abunshi.

Lokacinda Anaesthesia ya saketa ta tashi daga bacci sai yaga hawaye a idonta…hankalinshi yakai kololuwar tashi ya kuma ce dole ta sanr dashi damuwarta…itama din ba yanda ta iya duk yanda take kokarin 6oye mishi abubuwan da suka faru kasawa tayi saida ta fada mishi…6acin ran da ta gani a fuskanshi bata ta6a ganin irinshi a tattare dashi ba..yanxu kiyayyan da suke masa har yakai ga suyi abandoning matarshi tana labour wanda ba dob taimakon neighbor dinsu ba da kilan yanxu ya rasa matarshi da kuma babyn data haifa..zai iya yafe komai amma banda wnn cin kashin da sukayi masa..wnn dalilin yasa ya yanke shawaran da zaran ta warke zai daukesu su bar Gombe gaba daya tunda baiga amfanin zaman nasu ba.

Haka yake jinyar matarshi shi kadai sai neighbors dinta dake yawan xuwa kullum wasu har suyi girku su kawo…mahaifiyarshi ma bata taba zuwa ba sbd waziri daya hana amma munubiya zuwanta biyu shima duk wazirin bai sani ba take zuwa…saida ta samu sauki sosai yace ta fadi sunan da takeso a sa ma babyn nan take kuma tace sunanshi takeso yasa sbd tana ganin duk dunia yanxu batada wanda ya kaishi sai ‘ya’yanta…baiyi mata musu ba yayi mishi hudu ba da sunan Attahir tace zasu ringa kiranshi Bobby.

Daga asibiti ko gidansu basu koma ba suka wuce kano…bayan kwana biyu suka bi flight zuwa delta state inda a nan suka cigaba da rayuwa tareda yaransu.

Bayan shekara biyu suka koma Lagos sakamakon transfer da akayi mishi ya koma Lagos din da aiki…lokacin Sumy nada 6 years Bobby kuma nada 2…tsahon wadan nan shekarun kuma basu sake zuwa Gombe ba saidai yaje shi kadai ya dawo…ana haka Allah yayiwa mahaifiyarshi rasuwa…wnn karon kam gaba daya suka tafi kuma basu dawo ba sai bayan kwana bakwai…har zuwa lokacin kuma daga waziri har sauran siblings dinshi babu wanda ke kaunar matarshi da yaranshi…haka akwa kwashi tsahon shekaru babu jituwa tsakaninsu wanda hatta yaran dukda ba wasu shekaru sukeda ba sunsan akwai matsala tsakanin iyayensu da familyn babansu especially Bobby da yafi ‘yar uwarshi riko da kuma zafin zuciya.

Sbd wnn matsalan yasa ko auren qanwarshi da zaayi bai samu labari ba sai gab da bikin…yaji ciwon hakan sosai sbd ganin cewa yarinyar nan batada kowa yanxun daga wazirin sai shi da suke ciki daya da ita tunda mahaifiyarsu ta rasu…haka sukaje Gombe suka dawo bayan kammala bikin.

Bayan shekara goma Nadia da yaranta ke kira Mummy ta sake haifan namiji wnn karon yaron yaci sunan waziri Adam suke mishi laqabi da Sabeer.

Zaman Lagos na musu dadi sosai don basuda damuwan komai kuma babu wanda ke kyamansu unlike Gombe da ko zuwa basu sonyi sbd yanda ‘yan uwan Dad dinsu suke treating dinsu.

Bobby nada 17 years ya gama secndary school Sumayya kuma already ta fara karatu a University of Lagos shi kuma Sab yana primary school…zuwa wnn lokacin mahaifinsu yayi kudi sosai dan yana matakin deputy controller General na Nigerian Custom…kai tsaye ya tura Bobby America dan yacigaba da karatunshi a can.

Sumayya na kammala karatu aka aura mata isma’il da suka fara soyayya tun a university aka mikata gidanta dake Kanon dabo…unluckily itama mother inlow dinta bata sonta…dama Isma’il kadai ne danta namiji sauran duk mata ne suma kuma ba son nata suke ba…bayan shekara daya da biki ta haifi Miemie da aka sama sunan grandma dinta ta wajen uba wato Maryam ake kiranta Miemie…har zuwa wnn lokacin basa jituwa da sisters din mijinta dama mamansu gaba daya..kullum cikin nuna mata kiyayya suke kawai sbd ba ita sukeso ya auraba snn kuma da kasancewar Mum dinta igbo…wai Isma’il ya gur6ata musu family tunda ya hada musu jininsu dana inyamurai…haka aka cigaba da tafiya har ta sake haifan Ilham…ita kuma sunan Mummy aka sa mata Nadia ake ce mata ilham…wnn maida suna ba karamin tada rigima yayi tsakinshi da familynshi ba..wai don me zai sama yarinya sunan inyamurai…Sumayya da bata ta6a tanka duk abunda suke mata ba wnn karon kasa hakura tayi saida ta wanke su tatas ta kuma ce duk wanda ya sake izgili ga sunan mahaifiyarta sai sun kwashi ‘yan kallo dashi…labari na zuwa ga Isma’il mahaifiyarshi ta sanyashi gaba da kuka wai matukar yana sonta sai ya saki Sumayya tunda batasan darajanta ba tayi mara rashin kunya…da sukaga bazai saketa ba sai sukasa ya sake auran ‘yar sister din mamanshi sbd a kuntatawa Sumayyan…sunyi nasara kuma domin duk son da mijinta ke mata saida ta fara ganin canji tattare dashi…ya fara mata abubuwa wanda da ba haka yakeyi mata ba…gaba daya ma sai rayuwarshi ta koma 6angaren amaryarshi ita kuma ko oho don ko inda take bai cika zuwa ba…wnn abu yayi matukar daga hankalinta sosai tana ganin ko don yaranshi ai bai cancanci yayi abandoning dinta haka ba…daga karshe datayi kokarin nuna masa rashin dacewar abunda yakeyi sai yace taje ya saketa saki daya…bata sake wasting time ba kuwa ta hada kayanta ta wuce Abuja sbd a lokacin Daddynsu na matakin Controller General na Nigerian Custom so sun koma Abuja da zama…lokacin Ilham tana da shekara uku…haka suka cigaba da zama tareda iyayenta da kuma yaranta basu da matsalan komai…after a year Bobby ya kammala karatunshi a America lokacin shekaranshi kusan 9 a can…gaba dayansu suka shirya suka tafi America sukayi witnessing convocation dinsu snn suka dawo tareda shi Bobbyn da yakeda 27 years a lokacin…Sab kuma yanada 17 years kuma shima ya kammala secondary school.

Bayan kaman sati biyu da dawowanshi suka tafi kano wani taro da akayi inviting Daddy sai yace suje gaba daya…suka sauka nan gidanshi dake garin shi kuma ya wuce inda zasuyi taronsu…duk tsahon wnn shekarun daga Bobby har siblings dinshi babu wanda ke marmarin zuwa Gombe sbd cikinsu ba wanda baisan kalan hatred da sukeyi ma Mummynsu da su kansu ba…Bobby kuwa a lokacin ko mgnrsu ma baisonji…wani lokaci sai Daddy ya kira waziri ya waya ya hadasu su gaisa amma kowa zai kar6a shi kuma sai ya kirkiri wani abun ya tashi ya bar inda suke…Mummy duk tana lura dashi ta kuma san baya kaunarsu ne sam amma ko kusa batajin dadin hakan…tanaso ace ya samu kyakykyawan mu’ala da dangin mahaifinshi ko don sbd nan gaba ba wanda yasan me zai faru sai Allah.

A ranan bayan sun tashi daga taron shima ya wuce gida tareda zugan securities dinshi…misalin karfe 4:16 na yamma kiran wani brother dinshi ya shigo wayanshi…bayan ya dauka yake sanar dashi cewa waziri ne ba lafia kuma tun jiya yake cewa a kirashi yazo yanason mgn dashi…hankalinshi tashe sosai yace gashi nan zuwa Gomben yanxun…ba yanda Mummy batayi dashi kan ya bari da safe ba tunda yamma yayi amma yace sam bazai iya kwana while mahaifinshi nacan babu lafia kuma yana son ganinshi ba…babu yanda ta iya haka tabishi da addu’a…before ya fita ya shigo cikin gidan ya samu Miemie da Sab sai Sumayya a parlor nan yace musu zaije Gombe ya dawo suma suka mishi addu’an sauka lafia…yana shirin fita Bobby ya shigo parlorn rungume da Ilham da tayi bacci a hannunshi…shi kanshi yana ganinshi all dressed up yasan da akwai inda zaije…bayan ya fada mishi Gombe zaije  ga mamakin dukkaninsu da shi kanshi Bobbyn yace zai rakashi…Daddy yayi mamaki sosai don sarai yasan duk yaran ma babu wanda yafi tsanan Gombe kamanshi amma yau shi da bakinshi yake cewa zai rakashi…bai yadda ya bishi ba yace zai tafi da driver shi kuma yanada bukatan ya zauna ko don ya kula da Mummy da sauran yaran…haka nan ya hakura amma har cikin ranshi baiso haka ba…shi kanshi baisan dalilinda yasa yau yaji yanason bin mahaifin nashi zuwa Gombe ba…duk abunda ke faruwa Mummy na zaune tana kallonsu itama bason tafiyan nashi takeba especially da yace dagashi sai driver zasu tafi bazai tafi da securities dinshi ba…a takaice bai samu ya bar gidan ba sai around 5…kaman yanda ya fada dagashi sai driver din nashi sukashiga mota suka kama hanyan Gombe…suna dab da shiga garin dan sun wuce Azare kawai sai ganin babban mota suka from no where tayo kansu gadan gadan…a kokarin driver na ya kaucewa motan sai kan motan ya kwace daya hannunshi gaba daya…daga nan kuma basu sake sanin inda suke ba sai ganinsu sukayi a Hospital…yana bude idanunshi yaci karo da waziri dake rikeda hannunshi idonshi yayi jajawur sbd tsabar rudun da yake ciki…ga kuma wasu daga brothers dinshi suma zaune a wurin…cikin tsananin ciwon kan dake addabarshi yayi kokari ya rike hannun mahaifinshi dake rikeda nashi…idonshi na zubda hawaye yake neman mahaifin nashi da ya yafe mishi…shima kanshi wazirin kaman zaisa kukan yace ya yafe mishi dunia da lahira..shima kuma yana rokon yafiyanshi kan duk abubuwan da ya aikata wa iyalinshi…shi kanshi yasan bai kyautawa abunda yake amma sam ya kasa denawa…yanxun kuma daya ganshi kwancs cikin jini sai duk wnn tsanar da aka sa yake mishi ya 6ace 6att sai tarin kaunar da yake mishi tun can baya suka shiga dawo mishi…lokacinda su Mummy suka karaso gaba daya ba wanda ke cikin hayyacinshi…kuka kawai suke har suka karaso inda yake…idanunshi ya shiga zagayawa akansu yanajin kaman kallon karshe yake musu…ya kalli Mummy da idanunta sukayi suntum sbd kuka sai Sumayya da har yanxu bata dena kukan ba…can gefe kuma Sab ne da Miemie suma rungume da juna suna nasu kukan sai kuma Bobby dake rikeda hannun ilham idanunshi a kasa sbd bayason suga yanda idanunshi suka sauya sbd kuka…hannu kawai ya mika mashi alaman yazo gareshi…cikin karfin hali ya saki hannun ilham tareda karasawa kusa dashi ya zauna ya kama dayan hannunshi da yake free…murmushi sosai yaga yanayi dan haka shima sai shiga kakalo murmushin yana kallonshi…cikin muryanshi da ko fita baiyi sosai ya nuna su Mummy dake jere suna faman kuka yace”na bar maka su amana…inaso ka kulamin dasu fiyeda yanda nakeyi…inaso ka zama gatansu…ko kusa kar ka bari suyi kukan rashina Bobby…they are now your responsibility”…kukane sosai ya kwace ma Bobby ya kasa cewa komai sai kai kawai da yake girgiza mishi…shi kuma ya sake kallon Mummy cikeda wani irin rauni yace”Your Mom…batada kowa Bobby…banaso tayi kukan rashina make sure ka kulada ita yanda ya kamata”…wnn karon ba Bobby kadai ke kuka ba gaba daya sauran ma kukan suke wiwi…suka hada ido da Sabeer shima ya mika mashi hannu yazo nan suka hada kai da Bobby sunata kuka abunsu…waziri dake zaune yana kallonsu bai ta6a jin ya tsani kanshi ba kaman yanda yaji a yanxu…kallonsu kawai yakeyi tunda suka shigo yanda ba wanda yabi ta kanshi a cikinsu…ya fuskanci akwai soyayya sosai tsakin yaran snn kuma yayi mamakin ganin yanda sukayi girma gaba dayansu…sai yakejin wani ciwo na rashin sakewa jikokin nashi da har Sumayya tayi ‘ya’ya biyu bai taba ganinsu ba…ya kasa dauke idonshi daga kan Bobby sbd tsantsan kaman da yakeyi da Attahir dinshi…gaba dayansu ma sai yaji wani soyayyansu na daban na shiganshi…yaji gaba daya suna wani burgeshi gasu gaba dayansu tubarkallah dasu akwai kyau…hakika ya aikata kuskurenda shi kanshi baya tunanin zai iya yafema kanshi…bayan like an hour doctor yazo yace su barshi ya samu hutu…haka suka fita daga dakin sukayi cirko cirko a waje…Waziri dake waiting room yana hangosu sai ya fita daga dakin yace ace musu su shiga daka ciki su zauna…basuyi mishi musu ba suka shiga cikin dakin shi kuma ya kowa wani tareda yaranshi guda biyu da sukayi mishi rakiya…suna nan zaune akazo aka sanar dasu rasuwar drivern da suke tare dashi…hankalin kowa ya sake tashi masu kuka suka cigaba da gashi.

In summary dai shima Daddyn cikin dare Allah yayi mishi cikawa…fadan tashin hankalin da suka shiga 6ata baki ne…Mummy kuwa dama ana fada mata ta fadi wurin a sume…har wahegari bata farfadoba ga kuma bp dinta da yayi rising sosai dole aka bata alluran bacci.

Daga nan direct Gombe suka wuce dashi…lokaci daya mutuwan nashi ya watsu a gari kusan ko ina…karfe goma na safe akayi jana’izarshi aka kaishi gidanshi na gaskia(ubangiji kasa muyi kyakkyawan karshe)…shina waziri tun a wnn lokacin ya fadi dan ko jana’iza ba’ayi dashi ba…mutuwan ya dakesu ne sosai ba kadan ba…su Mummy kuwa gidanshi dake nan Gombe aka bude suka shiga itada yan uwanta da abokan arziki.

Ranan da akayi kwana bakwai rigima ya 6arke tsakaninsu brothers din Daddy suka dage kan lallai bazasu fita daga Gombe ba tareda anyi rabon gado an fiddama mahaifinsu kasonshi ba…a cewarsu tunda mahaifinsu nada gado suma suna dashi wai idan suka yadda suka bari Gombe ba’a raba ba suna iya yin sama da fadi da wasu abubuwan…kasancewar Waziri na kwance tunda akayi rasuwar sai baisan abunda yake faruwa ba…tareda Bobby sukaita yawo duk inda kadarorinshi suke ya kaisu suka gani snn aka shiga kotu akayi rabo aka fitarma waziri da rabonshi kaman yanda yake a addinance…a ranan da aka gama a ranan ya tattara su gaba daya suka bar garin ba tareda ko waziri sunje sun duba ba…duk yanda Mummy tayi dashi kan suje suga jikinshi snn suyi mish sallama kin yadda yayi dan shi gani yakeyi ma kaman da wazirin aka hada baki aka kashe musu mahaifi tunda kira akai aka ce shine bashida lafia amma da sukazo sai sukaga akasin haka.

Abuja suka koma direct sukayi parking abunda zasuyi parking…ya sai musu sabon gida a kano kuma bai yadda wani cikin ‘yan uwan Daddy sun saniba snn ya sake daukosu suka dawo…gaba daya saida yabi ya canxa musu sim card dukda dama ba wani communicating sukeyi da yan uwan daddyn ba amma still saida ya canxa musu dan kwata kwata baison sake ganin kowa a cikinsu…su barsu suji da ciwon kashe musu mahaifi ma da sukayi…ko Sab da ba wani contact dinsu yakeda ba saida Bobby ya amsa layinshi ya bashi new one…Mummy dai bada son ranta yake abubuwan nan ba amma ko yaya tayi mgn sai taga ranshi ya 6aci fiyeda tunani…da farko ma cewa yayi sai yayi bincike if ya samu da akwai sa hannun one of them a accident din Daddy then bazai ta6a hakura ba saiya mgnr court…da kyar da sidin goshi Mummy ta samu ta taushe shi ya hakura da zancen…itadai har zuciyarta bata zargin akwai sa hannun wani a cikinsu…kawai tanaga ai duk kiyayyan da suke mishi bazasu iya aikata wnn danyen aiki especially akan dan uwansu…a lokacin abokan mahaifinshi da yawa suna kokarin taimaka mishi ya samu aiki amma yace shi sam bazaiyi aikin force ba infact bazai ma iya aiki under government ba…da taimakon wani uncle din Mummy wanda ya kasance likita ya bude katon Hospital dinshi mai suna Freedom Specialist Hospital…ya dauki ma’aikata sosai kuma most of them yare ne as gaba daya yanxu ya tsani hausa fulani because yana ganin kaman duk halinsu daya da ‘yan uwan daddy…snn kuma ya tsani Gombe ya tsani duk wani abu daya fito daga garin…bayan shekara daya Allah yasa mishi albarka sosai dan ya kusan ninka abunda ya kashe a iya wnn shekaran…daga nan sai yayi tunanin ya bude Nursing and Midwifery College snn ya bude primary da secondary school duk a nan cikin kano…da yake kudi ne suke aikin in no time ya samu fili ya siya aka fara mishi aiki…a shekara na biyu ya bude Freedom College of Nursing and Midwifery Kano da kuma Freedom Science Academy Kano…nan ma yayi employing staff sosai suma kuma daga igbo sai yoruba sai kuma sauran tribes amma bai dauki bahaushe ko daya ba…a lokacin ya damqa Freedom Science Academy a hannun Aunty Sumy cox 6angaren data karanta knn shi kuma College din ya damqashi hannun abokinshi Dr.Nur…da shawarwarin Mummy dana sauran mutane abubuwa suke tafiya yanda ya kamata…cikin shekaru kalilan ya samu kudi fiyeda tunanin mai karatu…ya cire Miemie da ilham daga school da suke zuwa ya maidasu freedom shi kuma Sab ya nema mishi admission a Nigerian Police Academy Wudil as yana matukar son ya zama Police sbd it was his Dad’s ambition.

In summary cikin shekara biyar Bobby ya zama hamshakin mai kudi a kano state…tuni ya gina musu very big mansion a can airport road inda babu mutane sosai…gaba daya rayuwarshi yanxub bai cika son mu’amala da mutane ba especially hausawa cox yana ga kaman suma zasuyi treating nasu some how sbd kasancewar Mummy inyamura…gidane mai kyau da girman gaske inda babu wanda zai takurama wani a cikinsu…a takaice dai yana kulawa dasu sosai sosai kaman yanda yayima Daddy alkawari…cikin shekarun nan kuma ya sake bude another College of Nursing and midwifery a Lagos sai kuma Freedom College of Health Sciences and Technology shima a Lagos…da yake a can ya girma har yayi primary da secondary school so yanada mutane a can sosai da suke handling mishi Colleges din as bai cika samun time yana zuwa sosai ba saidai yana providing musu duk wani abu da suke bukata…bayan nan kuma ya bude Freedom Medical College Gwagwalada Abuja…itama ba karamin kawo mishi kudi takeyi ba and a wata baifi yaje sau daya ba wani lokaci ma sai yayi two months baije ba sbd aiyuka da suke mishi yawa…haka rayuwansu yacigaba da tafiya har zuwa yanxub da Mummy ke son dawo mishi da duk pain da agony da suka fuskanta a baya.

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE