DR BOBBY CHAPTER 6 BY AISHA RANO

Bayan sati hudu…

Yau tuesday Aysha na zaune cikin dakinsu kan study table ta dora macbook dinta akan table din tana kallon wasan Manchester United da Liverpool live…sai ihu takeyi tana nishadi duk ta cika dakin nasu da ihu sbd best player dinta Pogba gana performing well…yana ta6a ball zata hau ihu yanxu ma daddagewa tayi ta kwalla wani uban kara tana fadin”Goaal..yes yes..go on senior Man..go ahead”…Billy data fita karatu tun daxun sbd exams da suka fara jiya ta shigo dakin rungumeda katon text book dinta a kirji…ta karasa ta ajiye text book din kan shelve snn ta shiga rage kayan jikinta tana hararan Aysha tace”duk kinbi kin cikama mutane daki da ihu sai kace a kanki aka fara kallon ball”…Aysha da gaba daya hankalinta ke ga abinda take kallo ta saki wani smile tace”bazaki gane bane Billy wani hadadden ci Ronaldo yayi yanxun nan…and kinsan waye yayi assist?..”sake ta6e baki Billy tayi tana daura towel a jikinta tace”ya wuce Martial ko Rashford…ko kuma wnn gantalallen Lingard din”…tace”to duk basu bane Pogba ne..kuma gaskia kika sake cewa Lingard dinmu gantalalle za’aji kanmu dake a hostel din nan”…sake ta6e baki Billy tayi tareda shiga bathroom…har ta fito daga wanka hajia indo na nan inda take tana kallon ball dinta…ihu kuma ba fasa yinshi tayi ba saidai Pogba bai ta6a ball amma sai tayishi…Billy tayi banza da ita ta gama shiryawa abunta snn ta shiga kitchen ta hado corn flakes ta fito…tana zaune tana sha wayanta yayi kara…ta dauka ganin  one of colleagues dinsu dake cikin hostel ne…tambayanta yarinyan keyi yaushe zasu fita karatu dan duk aka fara exams suna haduwa suyi karatu gaba saya su ‘yan class dinsu dake cikin hostel din su 15…Billy ta amsa da bata sani ba su tambayo Lamido…tana tsaka da kallonta mutum biyu suka shigo dakin…daya daga cikinsu tace”Lamido ya mgnr karatun mu na yau ne?..kowa yana Common Room fa ku biyu kawai ake jira”…san juyowa tayi tayi musu kallo daya duk hankalinta naga kallon da take sam bataso a wuceta tace”safiyya dan Allah kuje ku fara da Billy ana gama wasan nan zan zo”..tana rufe baki Billy tace”babu wani farawan da zamuyi kawai idan bazaki koyawa mutane ba ki fada musu ba sai kima hanya hanya ba”…ta fada tana wani basarwa tasan tunda ta fadi bazata iya cigaba da kallon ba dan a dunia ta tsani mutum yace tayi mishi wulakanchi taki koya mishi wani abu…harara sosai ta sakarwa Billy kafin ta juya tana dubansu tace”ku bani 5 minutes plss ana tafiya half time zanzo”…Billy ta juyar da kai tana kunshe daria dama tasan maganinta knn…kaman yanda ta fada ana tafiya half time din ta mike ta fita hajia Bilkisu tabi bayanta…gaba daya sauran sun taru a Common Room din su biyu kadai ake jira…dakin yanada girma sosai snn da akwai expensive set of kujeru masu kyau a ciki hadda su tv da fridge da standard ac inshort dai babu abunda babu ciki har su curtains da center table like normal parlor dai sosai…each apartment sunada Common Room dinsu da bama wani zama ciki sukeyi ba sai idan abu ya kama irin haka…bayan sun zauna Billy tace”to yanxu da wanne ya kamata mu fara”…da sauri wata tace”mu fara complicated midwifery dan Allah…daxun dana daukoshi zan fara karatu har wani hazo hazo naga ina gani sbd tsabar bana fahimta”…gaba daya sunyi na’am da haka dan haka suka fara da shi din…course outline dinsu suke dauka sunabi one by one suna explaining snn duk wanda yakeda tambaya ya fada a amsa mashi…suna gamawa dashi sukayi other course din da shima zasuyi exam dinshi gobe snn suka watse.

Washegari bayan sun fito daga exam Aysha ta shiga kiran Sa’eed da tun safe bata ganshi ba…yana dauka tace”bestie where are you?..”yace”ina downstairs…kun fito daga exams?..”tace”eh..bari muzo downstairs din”…tana kashe wayan ta dubi Billy tace”muje yana kasa”…Billy ta wani hade rai tace”wai me zaiyi miki ne da kiketa nemanshi tun daxu?..”Aysha bata ce mata komai ba taja hannunta suka sauka kasa…can wajen wasu flowers masu kyau suka hangoshi yana zaune da wata class mate dinshi da alama yana koya mata abu ne…karasawa wurin sukayi suka zauna shi kuma ya sallami yarinyan da suke tare snn ya shiga kallonsu with a smile yace”so how was the exams?..Aysha tace”exam Alhamdulillah besty ya naka?..”yace”it was fine”…kallon Billy dake duba littafin hannunta yayi yace”so Bilkisu ya exams?..”tace”lafia lau”…ya kalli Aysha suka hada ido snn ya sske cewa”sai wani hade rai kikeyi sbd kin ganni…ki kwantar da hankalinki munayin counsil bazaki sake ganina ba”…ya karasa mgnr kaman wani abun tausayi…lokaci daya sai Billy ta dago tana kallonshi…idan akwai abunda ta tsana bai wuce yayi mentioning counsil exam ba duk sai taji jikinta yayi wani sanyi…ganin yanda ta kura mashi ido suka sake hada ido da bestyn shi sukasa daria…bayan sun gama yace” my Mom will be coming tomorrow.. hope zakuje ku gaisheta?..”da sauri Aysha tace”of course zamuje mana bestie..Allah ya kawota lafia…and yauwa bestie zaka kaimu lalle ranan Thursday idan mun fito daga exams…kasan cikin week din nan zaa fara bikin Adda Ruky”…yace”na sani besty amma baki ganin zaku samu matsala idan aka ganku da lalle?..nasan kinsan cikin ethics dinmu hadda kin applying wadan nan abubuwan”…tace”i know besty amma bansan ya zanyi bane…tun Thursday fa zaa fara bikin kuma ni bazan samu zuwa ba sai friday kaga banida time din yin lalle da sai na bari idan mun koma muyi…besides nafi son lallen kanawa yanxu..yafi namu kyau”…bai sake cewa komai ba kawai ya girgiza kai dan yasan tunda tasama ranta sai tayi lallen nan duk abunda zai fada ma ba changing mind dinta zatayi ba.

The following day kaman yanda suka tsara bayan sun fito daga exams suka koma hostel sukayi changing kaya snn ya kwashesu zuwa Tarauni gidan kakarshi…suka samu Mom dinshi zaune a parlor da Hajia sai dan autansu Mahmud…suka karasa ciki suka zauna snn suka gaisheta…ta amsa musu da fara’a tana tambayan su ya karatu…suka amsa da fine…tace”ga bestie ga Bilkisu koh?..”Sa’eed dake sauraronsu yace”Mom ashe baki manta ba”..tace”ya za’ayi na manta tunda kullum cikin zancensu kake”…Hajia tace”nima nan haka yake damuna da zancensu..magana daya biyu zaice besty tayi kaza ko kuma Billy tace kaza”…daria sukayi gaba daya jin yanda Hajia ke immitating mgnrshi…yana dan hararanta ta gefen ido yace”yanxu Hajia haka nake mgn?..”tace”oho kai ka sani”…sister dinshi ce ta fito daga daki waya kare a kunneta…tana ganinsu tayi hanging call din ta wani karasa cikin parlon da gudu ta fada jikinsu…Sa’eed yac”Lubna meye haka?..karya min su kikeso kiyi ne?..”ta daga jikin nasu tace”sorry yaya..nayi farin cikin ganin kawayena ne…kawayena da basu damu dani ba”..ta karasa mgn kaman zatai kuka…Mom tace”to sai ku shiga daki ku karasa mgn dan naga kaman they are not comfortable here”..Lubna ta mike tsaye rikeda hannayensu tace”yanxu kuwa Mommy”..daga haka 

ta jasu zuwa dakinda ta fito Sa’eed ya bisu da kallo har suka shige…Hajia dake ankare dashi tun dazu tace”mutum dai yayita yaudaran kanshi da sunan kawance..watarana kana zaune wani zaizo ya dauke ya barka da cizon yatsa”…juyawa yayi yana kallonta yace” me kike nufi?..”tace”me kuwa nake nufi daya wuce kana son mace kana yaudaran kanka wani wai kuna kawance..idan bakayi da gaske ba kana zaune zata auri wani ta barka wlh”…yace”to ke waya fada miki inason wata a cikinsu?..we are just friends “..tace” shine nace kacigaba da yaudaran kanka Sa’eedu”…bai sake mgn ba ya juya yana kallon Mom dinshi sai yaga daria take musu..zaiyi mgn tace”babu ruwana tsakaninku ne wnn”..

Suna shiga daki suka zauna suna sake gaisawa…Lubna tace”da gaske mutanen nan baku damu dani ba..ko nemana fa ba wanda yakeyi a cikinku”…Billy tace”wlh abubuwan ne sai a hankali Lubna amma inshaAllah daga yanxu zumunchi sai kince ya isheki koba hakaba Lamido?..”da sauri tace”sosai ma kuwa..daga yanxu mun kulla knn har sai mun isheki”..tace”nikam ba wani dadin baki da zakuyi min dan bazan taba yadda ba sai naga kunzo har kd bikina snn zan yadda daku”..Billy tace”u mean an kusa bikinki?..”tace”in the next three months inshaAllah”..Aysha tace”Allah ya kaimu ya sanya alkhairi…amma besty bai ta6a fada mana ba wlh”..Billy tace”shine nima nake mamaki ai..koda yake kadan knn daga aikin Sa’eed”…nan kuma hiran nasu gaba daya ya koma kan bikin Lubna da irin shirye shiryen da zasuyi…if u see yanda suka sake da juna suna labari zakayi zaton tasowa sukai tare tun kuruciya nan kuwa basu dade da sani juna ba shima ta dalilin Sa’eed wani lokaci da tazo ta dade a kano ya kaita hostel dinsu shknn suka kulla kawance…basu fito daga dakin ba saida yazo da kanshi yace su fito ya maidasu snn suka fito…sukayi sallama da Mom da Hajia da har yanxu suke parlor…Mom ta basu dambun nama da tayoma Sa’eed da Hajiyarta cikeda wani flask aikam sukaita godia snn suka tafi har Lubna data dage zatayi musu rakiya…kaman yanda ya saba duk ya fita dasu sai ya siya musu kayan kwalama yake maidasu yauma haka ya tsaya a grand square ya sai musu su chocolates da sweets snn yayi dropping nasu a hostel su kuma suka koma tareda Lubna.

Washegari Thursday suna zaune a premesis kafin time din shiga exam dinsu yayi motan Proprietor ya shigo makarantan…Ayshata wani hade rai dan tana gani ta gane motanshi ne…ko gama parking motan baiyi ba securities da some of staff da sukaga shigowanshi sukayi inda motan yake kaman yanda suka saba…tana daga zaune tana ganin yanda suka bude mishi kofa ya fito sunata wani washe mashi baki hadda masu risinawa suna gaisheshi kaman wani ubansu…Billy ce ta fara lurada ita sai tace”are you okay?..”ta saki wani tsaki tana fadin”mutanen can ne suke bani haushi wlh…dubi yanda sukema inyamurin mutumin can kaman zasuyi mishi sujada…kawai dan mutum nada kudi sai kuyita kaskantar da kanku a wurinshi da yawa daga cikinsu mafa sun girmeshi”..girgiza kai Billy tayi tace”to ke ina ruwanki…kuma an fada maki ba inyamuri bane har yanxu kin ki yadda koh?..”ta maka mata wani harara tace”wai wnn mutumin zaki kalla kice ba inyamuri bane haba Billy..”Sa’eed daketa sauraronsu yace”da gaske ba igbo bane shi besty..ance dai Mom dinshi igbo ce amma babanshi bafulatani ne fa”…da sauri Billy tace”tell her…bafulatanin ma kuma dan garinku”…da sauri ta daga kai tana kallonta tace”what do u mean?.”Billy tace”ina nufin dan Gombe ne shi mana”…tun kafin ta rufe vaki tayi spitting tana binta da wani disgusting look tace”God forbid…how could such a heartless person come from Gombe?..gaskia i doubt that kilan dai bakuji daidai ba…and wether u accept it or not mutumin can inyamuri ne kuma na tabbata yana daga cikin masu assasa yakin Biafra sbd tsabar mugun halinshi”…daria suka sa mata gaba dayansu aikuwa ta cika tayi fam har ta mike zata bar wurin Billy ta janyota da sauri tace”to shikenan Sa’ees tell her mun yadda inyamuri ne shi”..da sauri yace”eh mana kuma a cikin inyamuran ma yana daya daga cikin masu assasa yakin Biafra so are we good now?..”murguda musu baki tayi tana hararansu…ganin time din exam ya gabato duk suka mike zuwa classes dinsu.

Karfe biyu da wani abu ya daukesu suka tafi lalle kaman yanda suka tsara…Lubna ce tace tasan wani gidan lalle a Na’ibawa sun iya lalle sosai dan haka kai tsaye can ya nufa dasu.


Basu suka baro gidan lallen ba sai after six kowacce da rangadeden lallenta mai kyau har Lubna da tace bazatayi zuwan banza ba dan haka dole akayi mata itama…tun da suka fito yake yabon lallen nasu amma wai na bestynshi yafi kyau…Lubna tace”Yaya wnn dai son zuciyarka ka fada gaskia”..Billy tace”ai kadan ma kika gani daga aikin Sa’eed”…Lamido dai dariya take sai kuma ta dan rausaya kai tana dubanshi tace”yanxu besty hostel zamu koma knn?..”yace”eh mana you guys have exams tomorrow “..tace” mun riga mun gama karatu wlh besty dan Allah ka kaimu yawo kaji”…ya dan harareta yace”wani wai kun gama karatu sai kace yin karatun kike”…tace”nidai dan Allah muje yawo pllss ko Billy “..dagowa tayi ta watsa mata harara yace” then we are definitely going back to hostel tunda hajia Bilkisu bata yadda ba”…da sauri Lubna tace”Billy kice kin yadda plss”…kmr bazata ce komai ba sai can tace”shikenan amma we won’t stay long”..Aysha tace”hakanma mune da godia hajia bilkisu”…daria kawai Sa’eed yayi yace”to ina zamuje yanxu?..”da sauri Aysha tace”mu fara zuwa mudassir da akwai veils da nakeson siya”..yace”besty da shopping”…tace”ba haka bane besty kaga ko ban siya a nan dole ina sauka Gombe inje in siya kasan fa gobe ne kamun adda ruky”..jinjina kai kawai yayi sarai yasan halin kayarshi da shegen son biki…suna isa mudassir din gaba daya suka fita zuwa ciki…ta kwashi veils wajen guda four snn ta dauki shoe da bag…Billy ma ta dauki nata sai Lubna da suka tilasta mata ta dauki mayafi itama…sunzo wajen biyan kudi Aysha ta mika card dinta..Sa’eed ya watsa mata wani kallo yace”and what’s that?..”tace”besty kullum fa kai kake biya yau daya dai ka bari na biya plss”..bai sake ce mata komai ba ya amsa card dinta daga hannun mutumin snn ya bashi nashi…ana gama cire kudin suka fita daga wurin rikeda ledojin kayan da suka siya…daga nan Chicken Republic suka wuce suka samu table suka zauna snn aka kawo musu menu kowa yayi ordern abinda yakeso…suna nan zaune kafin a kawo abincin sukaji sallama kusa dasu gaba daya suka juya inda sukaji sallaman…wani mutumi ne da akalla zaikai iri 50 to above yana nuna empty seat dake wurin yace”may i?..”Sa’eed ne yace mishi”Bismillah”…a hankali yaja kujeran ya zauna snn ya mikama Sa’eed hannu suka gaisa yace”sorry i interrupt you guys…wlh tun daga kabuga na biyoku har nan wajen”…mamaki sosai ya bayyana a fuskokinsu jin tun daga kabuga yake binsu…ganin kallon da suke mishi sai ya saki murmushi ya nuna Aysha da finger dinshi yace”because of her”…wani mamakim ya sake kamasu jin abunda ya fada…shi kuma ya saki murmushi yana duban Sa’eed da yayi tunanin ko yayansu ne yace”can i please talk to her in private?..”shiru Sa’eed yayi ya juya yana kallonta sai yaga tana wani blushing kanta a kasa cikin ranshi yace”dama nasan za’ayi haka wlh..besty da shegen son sugar daddies”…jin har yanxu baiyi mgn ba mutumin ya sake fadin”only 5 minutes plsss”..yaja plss din da har saida ta dago ta kalleshi…a hankali Sa’eed yace”Sure u can”..mutumin yace”thank u so much..you are a life saver”…daga haka ya mike tsaye yana mata wani kallon kasa kasa yace”Ma’am”…batayi mgn ba ta mike tabi bayanshi zuwa wani table a can gefe…da kanshi yaja mata kujera ta zauna snn shima yaja ya zauna yana facing dinta yace”Allah yasa dai banyi laifi ba”…ta danyi murmushi hadi da girgiza mishi kai…shi kuma yayi mata kuri da ido kamab ya samu tv…saida suka hada ido ya sauke wani numfashi tareda cewa”u are very beautiful…shiyasa ina kallonki naji komai nawa ya tsaya..naji bazan iya hakuri ba har saida na biyoki…Allah yasa ban kawo kaina inda za’a wahalar dani ba”…still murmushi ta kara saki tana girgiza kai…yace”my name is professor Ahmad Abdu Kurawa and i think i have fallen for you”…shiru kawai tayi tana kallonshi sai taji ya burgeta sosai…this is exactly why she loves sugar daddies cox they are straight forward ba wani kwana kwana a tsarinsu…snn ga iya handling mace da nuna mata so da kauna…shiyasa duj ta shirya yin aure batada burin da ya wuce ta samu sugar daddynta ta aura yanda zata yita zabga shagwa6a son ranta ana lallashinta…jin batace komai ba ya wani rausaya voice dinshi yace”dan Allah say something plss..wlh i love you..i love you so so so much”…murmushi ta kara saki tana rufe fuska da hannayenta sai ya saki murmushin shima kafin yace”ohk i guess i have to give u some time to think right?..”da sauri ta gyada mishi kai..yace”alright then you take your time…amma plss kiyi min mgn inji sai in tabbatar da banyi zuwan banza ba”…still smiling tace”sunana Aysha Ahmad Lamido”…yana gyada kai yace”your name suits you…dama ina ganinki naji a jikina wnn beautiful soul din must be Aysha..thank you so much Aysha for giving me your time…yanxun zan wuce sbd na bar yaro a mota kema kuma naga ‘yan uwanki suna jiranki”..batace komai ba sai murmushi shi kuma ya zaro card dinshi ya ajiye mata yana cewa”ga card dina nan saiki kirani or better still bani number dinki cox i can’t the risk of loosing you”…batayi musu ba ta amsa wayanshi tasa number dinta…saida yayi dialing yaga ya shigo snn ya katse tareda mikewa tsaye yana kallonta yace”to ni zan wuce beautiful Aysha..zan kiraki inshaAllah and Allah yasan baza’a bani negative news ba”…tace”inshaAllah”…yace”alright bye”…itama tace mishi”bye”snn ya juya ya fita itama ta mike ta dauki card dinshi daya ajiye ta koma inda suke..Lubna tace”so har kun daidai knn?..”itadai tayi murmushi tareda fara cin abincinta…Billy tace”ai bama saikin tambaya ba Lubna wlh nasan da kyar idan batayi accepting dinshi ba..Lamido da shegen son sugar daddies”…shidai besty yana jinsu baice musu komai ba…suna gamawa suka bar wurin time din dare ya farayi sosai yayi dropping nasu a hostel su kuma suka wuce Tarauni.

Washegari Friday zasuyi final paper na first semester level two knn..zasuyi hutun two weeks snn su tafi clinical posting…tun wajen 7 suka baro hostel zuwa cikin makaranta..daga ita har Billy murna suke zasuje gida dan ko weekend sun kwana biyu basu je ba…kafin time din exam yayi provost ya kira wayanta yace tazo yanason ganinta…babu wasting of time kuwa taje office dinshi yace list din yan class dinsu yakeso ta bashi yanxun nan…ta juya zata fita ya dawo da ita ya mika mata pen da paper yace ta zauna nan ta rubutasu yasan zata iya tunda ba wani yawa garesu ba…ba musu ta amsa ta zauna ta fara rubutawa shi kuma Nur yacigaba da aiki a Laptop dinshi…a hankali Bobby ya turo office din ya shigo…idanuwanshi basu sauka ko inaba sai hannun Lamido da lallenta yayi wani moroon yanata shinning abunka da farar fata…ranshi yaji ya 6aci sosai like how dare this girl apply henna a hannunta bayan tasan baya cikin ethics… har ya karaso cikin parlon basu sani ba sai kawai sukaji yace”keh..”a gigice ta dago tana kallonshi..fuskan na sarari yace”bakuyi professional ethics bane?..”voice dinta na dan cracking tace”mun…yi”yace”then why did you apply this rubbish a hannunki?..”tayi shiru kanta kasa tana 6oye hannunta…Nur dake kallon abokin nashi da mamaki yace”C’mon Bobby ni banga wani abu anan ba..maybe kafin su tafi clinical posting ya baje so relax “…a fusace ya juya yana kallonshi yace” amma kai kanka kasan duk wayan nan abubuwan is prohibited a profession dinta koba a clinical area bane”…shiru kawai Nur yayi yana kallonshi..baisan why he easily gets angry when it comes to her ba..he remember yanda yayi acting ranan da sukaje hostel…ita kuwa Aysha daure fuskanta tayi tana dan turo baki har yanxun kanta kasa dan ko a mafarki batason sake hada idanu dashi…(note:nasan wayansunku will be like ya zaayi a hanata yin lalle sai kace a secondary school..well duk wanda yayi health institution yasan banbancinsu da secondary school dan kadan ne coz sunada strict dokoki snn kuma akwai ethics so ba yanda zaayi mutum yazo yana yin anyhow a irin wnn makarantun sbd suna dealing da lives of many people..da akwai rules da dole mutum sai yabi while in school ko kuma clinical area..na farko dai applying lalle is prohibited especially during clinical posting..snn ba’a sanya kayan ado musamman duk wabi abu da zai dauki hankalin patient ta hanyar sound dinshi ko wani abu shiyasa ake sanya uniform and ko takalmi bada kowanne ake zuwa ba dole sai preferred wanda aka za6a..irinsu zobe su agogo da sauransu suma duk are prohibited sbd suna iya daukan hankalin mara lafia shiyasa ake fara training mutum ya saba tun a school kafin ya tafi clinic..so i hope u understand dan nasan wasu zasuce wnn ta cika tsanani da yawa ko kuma ace tana rubuta abunda ba haka bane bayan haka tsarin kudan duk wani health institution yake saidai wasu sufi wasu tsanantawa)…karasawa yayi cikin office din ya tsaye nan inda take zaune snn yace”a ka’idar wnn abun da kikayi suspension za’a baki kuma bazaki dawoba har sai ya baje amma yanxu tunda you are going for holiday punishment dinki shine bazaki rubuta exams dinki na yau ba”…a rikice ta dago tana kallonshi idonta har ya ciko da hawaye…kallon nata yakeyi shima aikam nan da nan tayi kasa da nata don bazata iya daukan wnn kallon nashi ba…Nur ya taso daga seat dinshi ya zagayo inda yake yace”Bob me kakeyi ne haka pls?..meyasa bakajin mgn?..”a fusace yace mishi”ita why bazaka tambayeta meyasa batajin mgn ba?..meyasa ta cika fitina duk wani abu da tasan zai ja mata matsala bazata hakura dashi ba”…shiru gaba daya sukayi suna kallonshi…shidai Nur har yanxu bai dena mamakin wnn behaviour din nashi ba…shi kuwa ganin kallon da yake mishi ya karasa ciki ya dauki wani file akan table dinshi snn ya juya ya fita daga office tunda dama abunda ya kawoshi knn…kaman jira takeyi ya fita ta saki wani kuka mai ciwo…Nur ya dawo kusada ita da sauri yana kallonta a hankali yace”Lamido stop crying plss…dont cry”..girgiza kai kawai take as tasan idan daddy yaji an hanata rubuta exam sbd lallen da tayi applying fada ne zata sashi kilan ma saiya hada da duka..sam ba mai daukan iskanci bane shiyasa take mugun tsoronshi…ganin yanda take kuka Nur ya sake kwantar da murya yace”dan Allah stop crying kinji…duk wnn abun da kikaga yanayi baikai zuciyanshi ba…yanxun kije can office din nashi ki bashi hakuri”…yana rufe baki ta dago a razane tana kallonshi…sai kuma ta hau girgiza kanta tace”Sir bazan iya zuwa ba…inajin tsoro”…yace”don’t be..ba abunda zaiyi miki inshaAllah believe me…kawai idan kinje ki kwantar da muryanki kice yayi hakuri dan darajar Mummy da Daddy na tabbata idan kika fadi haka zai hakura”…shiru kawai tayi tana kallonshi kaman bataji me yace ba…saida ya sake mata mgn snn ta fita daga office kaman mara lafia…secretary dinshi na ganinta tace ta jira ta fara mishi mgn…landline dinshi ta kira ta fada mishi yanada bakuwa kai tsaye yace a barta ta shigo…saida ta gama goge tears dinta snn ta shiga office din kai a kasa kaman munafuka…kanshi na sunkuye yana signing wasu papers so bai ga wanda ya shigo ba…ta karasa gaban table dinshi ta tsaya gabanta sai aikin faduwa yake…batasan why take tsoron bawan Allahn nan ba dan duk yanda takai da son ta bude baki tayi mgn kasawa tayi…kawai imagining take ta koma gida daddy ya samu labarin an hanata exam sbd tayi lalle…duk wnn abun da take baisan tana tsaye kanshi ba saida ya gama signing papers din ya dago…mamaki ya kamashi sosai dan baisan itace bakuwar ba…idanunta rufe suna fitar da hawaye sai bakinta daketa motsi kaman tanaso tace wani abu…kallonta ya tsaya yayi da kyau irin kallon da bai ta6a yima wata mace a dunian nan ba…tun daga kan idonta da suke rufe har zuwa kan lips dinta dake shinning as a result of hawaye daya wankesu har yanxun kuma basu dena motsi ba…haka nan yaji wani irin sanyi na rufe mishi jikinshi…irin internal sanyi da mutum keji idan yana fever…ya dauke kanshi da sauri sai kuma yaji hadadden zafi yana maye gurbin sanyin daya faraji…ranshi ya 6aci sosai jin yanda temperature dinshi ke raina mishi hankali…yanxun nn yakejin sanyi after a minute kuma ya farajin zafi…ita kuma har yanxu taki bude ido tana tsaye tana karanta mishi Yaseen cikin zuciyarta wai ko Allah zai dorata a kanshi ya janye abunda ya fada…ganin bayan sauyin temperature har mood dinshi ma ya fara sauyawa gata kuma ta wani yi mishi tsaye a kai kaman wata soldier ya sake dinke fuskanshi tsaf snn yace mata”keh..”a hankali ta bude idonta ta dora kanshi sai kuma ta sauke da sauri tana kwa6e fuskanta irin yanda babies keyi idan zasuyi kuka ganin wnn kallon data tsana yakeyi mata…kirjinta har bugawa yakeyi dan tsoro ta rasa wane irin magic mutumin nn keyi dake sanya mata tsoronshi haka…shidai Bobby baki da hanci ya saki yana kallon ta6ara iya ta6ara…yanda tayi da face dinta dama kana gani zakasan sanrgatacciya ce ta ajin farko ma kuwa…ranshi yaji ya sake 6aci dan a dunia ya tsani shagwa6abbun yara wlh…ya tsani yaga an zubama yaro ido yana zuba iskanci son ranshi baza ayi mishi fada ba sunan wai ana sonshi…can kasan makoshi yace”spoiled brat”…a fili kuma komawa yayi yayi relaxing kan kujeranshi still yana kallonta yace”leave my office if u don’t have anything to say”…da sauri ta shiga girgiza kai cikin stammering tace”Sir…am…sorry”…wani kallo yake binta dashi before yace”what did u said?..”ta dan turo baki tace”i said am sorry”…tana rufe baki yace”sorry for yourself..now leave”…shima yana rufe bakin ta hade hannayenta alaman roko tace”Sir dan Allah…dan annabi..dan darajar Mummy da Daddy kayi hakuri”…shiru yayi yana kallonta totally speechless as ta fadi biggest weakness dinshi…in his entire life bashida weakness daya wuce parent dinshi likewise his strength especially Mummy that is still alive…ko ba’a fada ba kuma yasan aikin Nur ne wnn and he will definitely have to deal with him…ganin yanda yayi shiru ya kurama spot daya ido ta sake karya muryanta tace”Sir Please!..”wnn kallon dai data tsana ya watsa mata kafin ya nunata da finger dinshi strictly “but this should be your last…i promise duk na sake ganinki dashi you’ll face the consequences”… tun bai rufe baki ba tace” nagode Sir..thank you so much”…bai sake cewa komai ba sai kofa daya nuna mata…ta dan ta6e baki tana goge tears dinta snn ta juya ta fita cikin ranta tace”inyamurin banza”.

Taci sa’a tana zuwa aka fara raba question papers ta karasa seat dinta da sauri ta zauna…Billy daketa baza ido taga shigowanta tun daxu ta saki ajiyar zuciya dan sam hankalinta bai jikinta ganin har za’a fara bata shigo ba.

11 daidai suka fito daga exam hall…already Hamma Najeeb na zaune  cikin mota yana jiransu dan haka suna fitowa suka nufi inda suka hango motanshi…shima yana hangosu ya bude motan ya fito…suna karasowa ta wani kwa6e fuska kaman zatasa kuka snn ta kama hannunshi ta rike idonta na cikowa da hawaye…hankali a dan tashe yace”what happened again?..”ganin taki mgn ya juya yana duban Billy yace”me akai mata?..”Billy ta buda hannu alaman bata saniba…shi kuma ya kama hannunta suka kan wasu cement chairs dake gefe still hannunta cikin nashi yace”Maama plss talk mana..waya ta6amin Mamana?..”tana turo baki tace”Hamma i don’t want to come back to this college kayi mgn da daddy plss”..yace”but Maama why?..did something happen again?..”tace”Proprietor ne…Hamma wlh ya tsaneni..kawai daxu yayita min wulakanci hadda cewa bazanyi exam ba sbd nayi lalle..nidai i don’t want to come back plss”…kamo dayan hannunta yayi yana dubanta da kyau yace”Maama kinsan daddy bazai ta6a yadda ba tunda ke kika dage sai an kawoki nan…but i think i have to talk to Proprietor din naku ya bar takura maki kawai”…tana goge hawayenta tace”there is no need..idan kaje ma wulakanci zai maka na sani…Hamma inyamuri ne fa..ko cikakken hausa bai iyaba”…yace”to indai bakiso inje in sameshi ki bar kukan nan haka..yanxun ku debo kayanku mu wuce amarya nata kirana wai inyi sauri in kaiku da wuri”..da sauri ta karasa goge hawayen nan da nan kuma saiga murmushi a fuskanta tace”laaa Hamma kasan har na manta wlh…Billy taso mu tafi nasan yanxu ana can ana shirye shiryen kamu”…girgiza kai kawai Billy tayi tana mamakin halin Lamido da shegen son biki..yanxun nan fa take kuka sha6e sha6e amma daga jin mgnr biki ta wartsake…kayansu kawai suka dakko daga wani class don dama basu fito da shirin komawa hostel ba..suka zuba su cikin booth snn suma suka shiga motan Hamma yaja suka tafi…basu samu yin sallama da Sa’eed ba as har time din yana exam hall bai fito ba..dama ba lokaci daya suka shiga ba so sun rigashi fitowa.

Saida suka fara tsayawa Bauchi suka ajiye Billy snn suka wuce Gombe bayan tayima Lamido alqawarin zata zo gobe ayi bikin da ita yau dai tanaso ta huta gajiya…suna shiga cikin Gombe murnanta ya kasa 6oyuwa dan ba karamin missing gida tayi ba…kai tsaye GRA suka nufa inda a nan Estate dinsu yake…Estate ne babba inda ciki duk wani wanda ke amsa sunan Lamido yake.. a nan ciki gidansu yake tun daga kan ‘ya’ya da jikokin Lamido maza baya bari suyi nesa dashi mata ne kadai suke fita shiyasa ake yima Estate din laqabi da LAMIDO’S PALACE…horn yayi jikin tangamemen gate din shiga Estate din wanda daga can samanshi aka rubuta THE LAMIDO’S in capital letters..masu gadi sukazo suka bude mishi yasa kan motar ciki…tsayawa fadan haduwan ciki ma bata baki ne kawai dai is one of the biggest and beautiful Estate i have ever seen…ya tsaru ne iya tsaruwa snn yana daukeda gidajen da ni kaina bazance ga adadinsu ba don sunada yawa sosai…layi na uku ya shiga by his right side snn yayi parking motan a daidai kofan gidan daya kasance shine na uku layin…tun kafin ya kashe motar ta bude kofa ta fita da gudunta ta fada cikin gidan…bata ga kowa a parlor ba dan haka ta wuce zuwa dakin Ammi…a gaban madubi ta isketa zaune tana daura dankwali ta karasa da saurinta tayo hugging nata ta baya tana fadin”Ammi nayi missing diki wlh”…a hankali ta juyo ta zame hannunta daga jikinta snn ta daure fuska tana kallonta tace”bakida hankali kou?..wnn shine sallaman?..”rungume hannu tayi tana turo baki tace”Ammi nayi kewarki nefa sosai shiyasa amma kiyi hakuri”…juyawa Ammi tayi tacigaba da daurinta tace”zakici ubaki ne”…sake turo baki tayi tace”yanxu Ammi ko gaisawa fa bamuyi ba”…Ammi data gama daura dankwali tana kokarin sa wayanta cikin hand bag dake hannunta tace”ni kike jira in gaisheki ai tunda ke kika haifeni”…kaman bata son mgn tace”Ammi ina yini..ya gida”…tace”lafia lau ki wuce kije kiyi wanka ana gama ma su Husna make up kema ayi miki ku taho..tun daxun ake tafiya sbd ke nace su jira ku wuce tare”…tace”to bari inje Ammi..amma Aunty Fiddausi bata zo bane?..”tace”bazata samu zuwa ba Mufid ne ba lafia wai…yanxun mu fara zuwa ku gaisa da daddy sai kije kiyi wankan”…tare suka fita daga dakin bayan Ammi ta yafa mayafinta…tayi kyau sosai cikin coffee lace daya amshi skin clour dinta sosai snn kallo daya zaka mata kaga tsananin kamar da Lamido takeyi da ita…a zahiri kuma bazaka ta6a cewa ta haifeta ba dan yanda suka jero sai sukayi kaman kawaye…a palor suka samu daddy zaune yana yin waya…suka karasa ciki Ammi ta zauna kusa dashi ita kuma malama A’ee ta zauna a kasa tana wani irn nutsuwa kaman mutumiyar kirki…bayan ya gama wayar ya dubi Ammi da tayi mishi kyau kwarai yace”har kin gama?..”tace”na gama daddy zuwa zanyi Najeeb ya ajiyeni a hall din kafin ya fita..su kuma idan sun kammala sai Idris ya kawosu”..gyada kai yayi yana fadin”ohk”..snn ya maida kallonshi ga Aysha da take zaune tsumu a kasa kaman ba ita ba..cikin sabuwar nutsuwar data aro ta yafawa kanta tace”daddy barka da yamma”..yace”yauwa Aysha an dawo?..”tace”mun dawo daddy”…yace”Maa sha Allah ya exams?..”tace”daddy Alhamdulillah”…yace”to Alhamdulillah ya ban ganku tareda Bilkisu ba?..”tace”sai gobe zatazo daddy”..ya gyada kai yace”Allah ya kaimu..sai kije ki fara shiryawa kar suzo suna jiranki”..a hankali ta amsa da”toh..”snn ta mike ta bar parlon…itama Ammi mikewa tayi da bag dinta a hannu tace”nima bari in wuce daddy lokaci na kara tafiya”..kama hannunta yayi ya zaunar da ita yace”ki bari in kaiki da kaina mana…irin kyau da kikayi ya kamata ace sai na gama gani zaki tafi”..murmushi ta saki tana girgiza kai tace”daddy bakada dama wlh…inaga sai kaga mun aurar da Aysha snn zaka gane girma ya fara zuwan mana”…yaja dogon hancinta yace”ke girma ya fara zuwan ma bani ba..kuma ko mun aurar da Aysha ni babu abinda zai canxaki cikin zuciyata”..daria ta saki tana jin kaunar mijinta ta ko ina a jikinta snn ta sake mikewa tace”to nidai ayimin uzuri in wuce ba don ni ba..nasan yanxu ana can ana menana wlh”…bai sake yunkurin hanata ba yace”sai kin dawo Allah ya kiyaye”..ta amsa da”Ameen”..with a smile snn ta fita daga parlon…a main parlor ta samu Najeeb na jiranta dan haka yana ganinta ya mike suka fita tare..dukda cewa hall din da suke bikin cikin Estate din yake yanada nisa sosai da baza’a iya zuwa a kafa ba.

Aysha kuwa tana shiga dakinsu ta iske Husna zaune ana mata make up din Yusra kuma na kwance kan gado…saida suka gama rungume rungumesu itada Yusra as usual Husna nata faman ta6e baki tana binsu da harara snn ta fada bathroom tayo wanka sharp sharp ta fito…lokacin am gamawa Husna an farama Yusra…ita kuma ta tayar da sallah bayan ta idar ta dauki kayanta da yake iri daya dasu Husna har dinki ta saka snn ta zauna zaman jira.

Karfe biyar da wani abu suka shigo cikin hall din…dukkaninsu suna sanye cikin atampan ankonsu dark blue da adon sky blue a jikinta…kaman yanda na fada dazu hatta dinkinsu iri daya ne haka daurin dankwali da akai musu shima iri daya ne..takalmi da jakansu ne ya bambamta amma duk color daya ne…hall din ya cika makil da mutane banda sautin waka ba abunda ke tashi a ciki…amarya na zaune high table tareda angonta…Aysha na hangota ta fara zuwa inda take kawai suka rungume juna cikin rada tace”adda ruky kinga kyan da kikayi kuwa?..”amarya data kasance cousin dinta domin diyar yayan daddy ce tace”duk kyauna ban kaiki ba Lamido”..ta matsa daga jikinta tana dan turo baki tace”kema Lamidon zakice?..”itama amarya komawa tayi ta zauna snn tace”yes koba sunanki bane?..”tace”sunana ne kaman yanda kema yake sunanki..so daga yanxu duk kika kirani da Lamido kema da Lamidon zan kiraki”..murmushi kawai tayi mata ita kuma ta juya ta tafi..can inda ta hango da yawa daga cousins dinta ta nufa wanda duk yawancinsu age mates dinta ne suma duk suna sanye da anko…nan suka hau rungume rungume suna farin cikin ganinta.

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE