DR BOBBY CHAPTER 7 BY AYSHAT RANO

Basu suka baro hall din nan ba sai after seven…lokacin duk an gaji su hajia Aysha a gajiye aka dawo gida sbd rawa da aka tika wajen…kai tsaye ta fada bayi ta watsa ruwa a jikinta snn ta fito tasa kayan bacci tareda hayewa gado ta nade kaman wanda zatayi bacci…sai yanxu ta tunada wayanta data bari a school bag din daxun…shaf ta mance data dawo bata fito dashi ba ta mike da sauri zuwa inda ta ajiye jakan ta zaro wayan snn ta sake komawa gado…missed calls ta tarar guda 46 aikuwa ta wara ido sosai tana kallonsu..biyu daga ciki na Billy ne sai guda hudu na Besty sai kuma wata bakuwar Number mai sauran 40 din…ta danyi shiru tana nazarin number lokaci daya kuma sai ta wara ido tana sakin murmushi data tuna mai number…wnn sugar daddyn ne da suka hadu a Chicken Republic ranan…Allah sarki bawan Allah shine yayita jera mata missed calls haka?..tayi mamaki ma da bai ta6a kiranta ba sai yanxu…har ta danna zatayi dialing number dinshi sai kuma taga bari ta fara kiran Billy da bsty tukun dan kar ta fara kiranshi ya cinye mata time bata kirasu ba…Billy ta fara kira suka gaisa tareda yima juna ban gajia snn Billy ta jaddada mata tana nan zuwa gobe inshaAllah…suna gamawa ta kura bsty shi kuma korafi yaketa yi wai basu tsaya sunyi sallama dashi ba suka wuce ita kuma tayita aikin bada hakuri har ya hakura…bayan sun gama ta wani sake lafewa kan pillown da take kwance tana lumshe idanu tayi dialing number dinshi da yanxun nn tayi saving as Prof…yana shiga kaman jira yake ya dauka sai ya sauke wani wawan ajiyan zuciya before saying”baiwar Allah laifin me nayi ake ignoring calls dina haka?..”tana smiling tace”sorry bana tareda wayan ne”..yace”hankalina duk ya tashi na fara tunanin kodai ban samu kar6uwa bane”..murmushin ta kara saki tace”sam ba haka bane..bikin cousin dina akeyi shine na manta ban tafi da wayan ba”…yace”to shiknn hope ban takura maki ba?..”tace”not at all”..tana jiyo sautin smile dinshi kafin yace”to yanxu ya zakiyi dani?..inaso in ganki gaskia”..tace”bana Kano yanxu..na dawo gida”..yace”ohh ba kano kikeba?..”tace”yea Gombe”..ya wara idanunshi da kyau kafin yace”no wonder kikeda kyau..dama an fadamin gaba daya ‘yan Gombe kyawawa ne”..tayi murmushi kawai..shi kuma ya sake yin kasa da murya yace”to nidai inason ganinki and if kin bani dama har Gomben zan iya zuwa”..tace”haba da akwai nisa fa”…yace”bakiji ance garin masoyi bai nisa ba?..nifa da gaske nake sonki Aysha bada wasa ba..ban ta6a tunanin zan iya auren karamar yarinya ba sai a kanki..so please inaso a bani dama”…shiru tayi tana tunanin me zatace mishi…tadai san ko ta fara shaye shaye bazata fara kawoshi gidansu ba dan Lamido najin labari zaice ta fito da miji a nata aure tunda tara samari take..besides shi kanshi daddy won’t take it likely idan yaji ta kawo saurayi gida ba tareda ya nemi izini ba snn Ammi ma ba rufa mata asiri zatayi ba dan bakinsu daya itada daddyn..amma yanxu ya zatayi da wnn bawan Allah data farajin itama kaman tana sonshi…idea ne ya fado mata dan haka da sauri tace”to ka bari mu gama biki zuwa Sunday sai mu hadu a Bauchi”…yace”but why Bauchi?..ba kince Gombe ne garinku ba?..”tace”nan ne garinmu amma bazan iya kawoka gidaba sbd mahaifina zaiyi fada”..yace”zan iya turowa a nemi permission dinshi if kin amince cox banso da girmana in hadu da yarinha baa gidan iyayenta ba..it’s not proper ko ‘yata aka yima haka bazanji dadi ba”…ta dan shagwabe muryanta tace”nidai banaso kazo yanxu plss and Bauchin fa ba gidan wani zamu hadu ba gidan small mom dita ne..qanwar mamana”…shiru taji yayi for a while da alama yana tunanin yiwuwar hakan ne…kafin yayi mgn ta sake narke murya kaman wadda ke shirin fashewa da kuka tace”shikenan dama nasan ba damuwa kayi dani ba”…da sauri yace”subhanallah baby why zakice haka?..”tace”gashi nan sbd nace mu hadu a Bauchi kanaso kace ka fasa zuwa”..yace”alright ok don’t cry plss…kawai ina ganin rashin dacewar hakan ne a matsayina na babba bai kamata na biye miki ba amma zanzo kinji?..zanzo inshaAllah”…lokaci daya ta saki smile tanajin dadin yanda yake mata tace”shknn Allah ya kaimu…ranan sunday inshaAllah”..yace”no problem Allah ya kaimu i can’t wait to see you”..tayi daria tana feeling kanta kaman a sararin samaniya..wnn shine exactly dalinda yasa take son sugar daddies…tayi shagwa6arta son ranta babu wanda zaice don me..dan Allah ya sani tana son taga ana pampering dinta ita dai sai kuma Allah bai bata irin wann parents din ba don daga Ammi har daddy ba masu sangarta yara bane..itama din da takeyi kawai don abun yana jininta ne amma ba shagwa6ata suke ba shiyasa wani lokaci Ammi takan ce”wnn yarinya da shagwa6aki muke Allah kadai yasan iskancin sa zaki mana a cikin gidan nan”…sun dauki lokaci mai tsayi suna waya tanata zuba shagwa6arta yana biye mata aikam farin ciki kaman ta zuba ruwa kasa tasha to dama abun nema ne ya samu wai matar driver ta haifi mota😂.

Washegari around 11 Billy ta karaso gidan…if u see yanda suka rungume juna sunata murna zakayi tunanin dadewa sukayi basu hadu ba nan kuwa jiya jiyan nn suka rabu…bayan sun gama hoge hogensu suka je ta gaisa da daddy da Ammi snn suka shiga daki…Billy take bala labarin yanda sukai da Sir Abdool wai ya kai karanta ta dena daukan wayanshi…Aysha ta wani cunno baki tace”wai bama fada miki abunda yayimin ba?..”Billy tace”and so what dan yayi pecking hannunki?..Lamido nifa banga wani abu a nan ba kawai kina nema kiyi complicating abubuwa”…da mamaki tace”seriously?..yanxu ke a wurinki ba komai bane namiji ya kama hannunki yayi kissing?..”Billy tace”of course ba wani abu bane mana indai da soyayya…kema fa da kina sonshi nasan wlh bazaki damu da hakan ba kawai dan bakya sonshi ne”…tace”Alhamdulillah da kika gane bana sonshi…ke ban fada miki ba jiya bakiga wayan da mukasha da wnn mutumin ba wlh..Billy he is so romantic nima harna fara sonshi wlh..gobe ma zaizo mu a hadu gidan Aunty fiddausi”…harara Billy ta buga mata tace”au yanxu har daman zuwa zance ma kika bashi mutumin da bakisan halinshi ba Lamido?..ba gara Sir Abdool din ba tunda shi munsan wayeshi?..”Aysha ta ta6e baki tace”ba dama ayi mgnr arziki sai kice Sir Abdool…nidai dan Allah ki taimaka ki roki Ammi kice zan rakaki gida sai muje tare plss”…a kufule Billy tace”bazanyi ba”..tace”C’mon Billy dan Allah fa nace?..”Billy tayi mata banza bata kulata ba.

Da yake event din ranar na dare ne basu suka fara shiri ba sai after magrib…yauma kaman jiya har gida make up artist tazo tayi musu wnn karon hadda Billy…Lace ne a jikinsu yellow da black flowers a jiki sai aka daura musu black head dinkin straight gown daya zauna jikin kowaccen su…karfe takwas da wani abu Hamma Najeeb ya kwashesu zuwa hall da zaayi event din…wurin yayi kyau sosai hakama Amarya da maids dinta tamkar a sacesu a gudu sbd kyau…Amminsu ma yau ba’a barta a baya ba dan make up akayi mata light wanda baikai nasu ba sai ta fito tayi das abunsa kamar yammata…biki dai yayi biki domin anci ansha anyi ruwan kudi snn an dirki rawa kaman ba gobe…su Aysha basu koma gidaba sai after twelve..wanka kawai sukayi suka kwanta bacci.

The next day ringing din wayanya ya tadata daga bacci…ta mike zaune a hankali tana murza ido takai hannu ta dakko wayan nata..Prof taga ke kira kaman yanda tayi saving dinshi..ta saki smile sai a lokacin ta lura duk su Billy ashe sun rigata tashi sun ma fita daga dakin…tayi picking da sallama..a daya 6angaren yace”my beautiful baby girl..hope bani ma tasheki a bacci ba”..ta wani narke tace”ka tasheni mana”..yace”eyya am sorry baby pardon me plss..am eager inji voice dinki ne that’s why amma am sorry kinji?..”tana murmushi tace”baka laifi ai”..cikin excitement yace”Really?..”tace”Sure..”yace”baby gaskia inason ganinki sosai..i feel like coming to Gombe right now”..tayi kasa da murya sosai tace”no ka bari yanda muka tsara plss..anjima kadan zamu wuce Bauchi inshaAllah”..yace”shknn sai anjima..i have to barki kiyi wanka kiyi breakfast koh?..”tace”yea..ba bye”..shima yace”bye”..snn suka ajiye waya…ta sauka daga gadon tana sakin murmushi one after the other ta shiga bathroom…brush kadai tayi snn ta fita zuwa parlor…a dinning ta iskesu gaba daya suna breakfast except daddy da Ammi da normally sukafi yin breakfast dinsu a parlon daddyn…karasawa tayi taja kujera ta zauna tace”shine duk kuka fita baku tasheni ba”…Billy tace”yo kina can kin wurgar da bakinki akan me zamu tasheki?..”Husna tasa daria tace”kai Adda Billy meye wurgar da baki kuma?..”Billy tace”mutum ya kwanta yana bacci mana”…Husna ta sake sa daria…itadai Aysha bata kulasu ba ta fara serving kanta…saida suka gama Hamma Najeeb ya shigo yace suyi serving dinshi…Husna ce tayi serving su kuma sauran suka koma parlor.

karfe hudu da mintina aka fito da amarya zaa kaita gidanta dake Bauchi…hajia Aysha dai ta samu da kyar da sidin goshi Ammi ta barta zuwa kai amaryan tace daga nan ma ta biya gidan Fiddausi ta duba mata jikin Mufid idan tazo gobe saisu dawo tare…murna wurinta kaman bata ta6a zuwa Bauchi ba har saida Ammi tayi zaton ko wani abun zai kaita sai kuma ta waske tacema Ammin ba komai…basubi motan kai amarya ba Ammi ta hadasu da driver ya tafi dasu…kai tsaye gidan aunty Fiddausi ta nufa ko hanyan gidan amarya basu nema ba…lokacin karfe biyar ya kusa…suna shiga ciki suka gaisa da Auntyn nata dake nan mai kamada Ammi sak snn Aysha tayi mata bayanin zatayi bako dan yanxu haka ma yana kan hanya…kallonta ta shiga yi tace”Adda bata saniba koh?..”da sauri Aysha tace”Aunty kinsan idan na fada mata bazata barni inzo ba..tama ce gobe idan tazo duba Mufid sai mu wuce tare..Aunty ya jikin nashi kuwa?..”tace”yaji sauki dama malaria ne yake fama dashi amma yanxu ya warke yana ciki yana bacci”..tace”to Allah kara sauki amma ya banga Mufida ba”..”Mufida na islamiyya..yanxu me za’a dafama bakon naki?..”Aunty ta tambayeta kai tsaye…ta danyi shiru tana nazari kafin tace”kawai Aunty a dafa mishi koma menene..nasan ya kusa karasowa yanxu haka”..mikewa auntyn tayi ta nufi kitchen tace”to bari in fada musu suyi mishi abu mai sauri tunda lokaci ya kure”…cikin jin dadi tace”yauwa Aunty na”…Billy dai na sauraranta ko uffan batace ba as haushinta takeji for accepting wnn mutumin kuma wai harda bashi dama yazo su hadu…da farko ma cewa tayi ita gida zata tafi sai da kyar ta samu ta shawo kanta kan ta bari su tafi tare gobe.

Prof bai samu shigowa Bauchi ba sai after five…yabi address data tura mishi sai gashi kofar gidan Aunty Fiddausi…ya kirata a waya yace mata ya iso ita kuma tacema nai gadi ya bude mishi ya shigo…tana tsaye jikin window tana ganin shigowanshi…da kanta ta fito cikin black abaya da yayi nata kya sosai ta shiga dashi dakin baqi…ko zama ya kasayi kallonta kawai yake yanajin tamkar ya dagata yayita juyi da ita cikib parlon sbd tsabar kyau da tayi mashi…duk yasa ta farajin wani iri wlh..da kyar ta samu ya zauna itama ta zauna suja fara gaisawa…ya kasa dauke idonshi daga kanta kona second daya…mikewa tayi ta shiga ciki ta kawo mishi drinks da snacks kafin a gama abinci…har ta zuba lemo ta mika mashi bai bar kallonta ba..ta dan daure face tana turo baki tace”Prof mana…banason kallon nan wlh”..a hankali ya dauke idonshi yana sauke wani gwauron ajiyan zuciya yace”na dena my baby..just know that i love u so much”…dan murmushi ta saki for the first time itama tac mishi”i love u too”…ya wara idanu sosai yana kallonta full of excitement yace”Really?..da gaske kina sona baby?..thank u so much baby Allah ya miki albarka”…ta wani sake karya muryanta tace”Ameen Ameen my Baby Boo”…wani irin dadi yaji ya sake lullu6eshi…shikam baisan inda zaisa kanshi ba duk ranan da akace ya mallaki wnn zandadediyar yarinya..she’s like 100 percent kaman ita tayi kanta..she’s like a complete package da kowane namiji zaiso samunta as his wife…hira sosai suka shigayi irin na masoya inda mutumiyarku keta zu6a shagwa6a shi kuma yana tarairayarta…bayan an gama girki Billy ta kawo mishi snn ta zauna suka gaisa…Aysha tayi introducing nata as her best friend shima tayi introducing nashi as her baby boo…wani takaici Bilky taji ya isheta jin wai wnn tsohon take kirada baby boo..bata wani jima suna hira ba tayi excusing kanta ta fita su kuma suka dora daga inda suka tsaya…har akai sallahn magrib basu gajiba yaje sallah ya dawo suka cigaba da gashi…in short Professor bai bar gidan nan ba sai da aka kira sallahn isha..ta rakoshi har mota suna jin kaman bazasu rabu ba sukayi sallama ta kima ciki shi kuma ya tada mota ya wuce yasan kwanan Bauchi ya kamashi dole tunda dare yayi saidai da safe ya koma…a labarin da sujayi ne ya sanar da ita bashida mata domin tun bayan rasuwar matarshi tsahon 3 years bai sake aure ba amma yanada yara uku mata biyu namiji daya…babbar macen tana aure a Abuja with a son mai binta kyma ba’a dade da bikinta ba ita kuma tana kd sai karamin cikinsu Muslim yana karatu a Malaysia.

Washegari wajen 10 suka tafi gidansu Billy kafin Ammi ta karaso…ta gaisa da Ummansu Billy da abbansu sai wajen 12 ta koma gidan Aunty…lokacin kuma su Ammi sun jima da zuwa tareda Yusra da Husna…nan suka zauna sunata faman hira amma koda wasa Aunty Fiddausi batayi mentioning zuwan bakon Aysha wa yayar tata ba dan tasan idan ta sani har ita kanta zata hada ta wankesu tatas shiyasa tayi shiru da bakinta..wnn dalilin yasa kullum Ammin ke cewa bakinsu daya da Aysha dan nasu yazo daya sosai zaiyi wahala aji kansu snn kuma Aysha bata ta6a zuwa hutu ta koma ba tareda tazo Bauchi gidan Auntyn nata ba…suna shiri sosai da ita unlike Husna da basa jituwa kwata kwata…saida sukayi sallahn asr snn suka nata sallama suja tafi…Aysha duk sai tajita wani iri ita dama su barta ko sati ne tayi a Bauchin.

Kano…

Yana kwance cikin dakinshi yayi wani coiling a kan gado yana bacci Ilham ta shigo…tun daya gama gymming dinshi yayi wanka ya kwanta shine har yanxun bai tashi ba don sai yamma zai shiga Hospital…ta karasa kan gadon tana hargitsa uban gashin kanshi mai santsi takai bakinta saitin kunnenshi tace”Uncle Bobby wake up”…a hankali ya bude ido snn ya sake maidasu ya rufe…Ilham ta sake hargitsa gashin nashi tace”Uncle Bobby wake up mana..Mummy said i should call u”..wnn karon gaba daya ya bude idanun nashi yana kallonta…sai kuma ya mike zaune yana gyara gashinshi data hargitsa yace”Ilham bakida hankali kou?..”tace”Sorry Uncle Bobby Mummy tace a kiraka”..sauka yayi daga gadon snn yace mata”kice am coming”..Ilham bata sake mgn ba ta mike ta fita..shi kuma ya shiga bathroom yana jin haushin katse mishi bacci da akayi…ya tabbata da ba Ilham din suka turo ba duk wanda yazo ya tadashi a baccin nan sai anji kansu dashi amma Ilham favorite dinshi ce shiyasa ko fada bai fiye yi mata ba…brush yayi ya wanko face dinshi ya fito don bai dade da yin wanka ba…ya dauki wayanshi kan mirror snn ya fita…a Central parlor ya samesu zazzaune…Mummy ce da Aunty Sumy sai wata mata da bai gane wace ba…ya karasa kusada Mummy ya zauna snn yace”Mummy gani…lafia dai koh?..”da igbo tace mishi”lafia ka gane wnn?..”ta nuna matar dake zaune…ya girgiza kai alaman aah…tace”Sunanta Hafsa kuma qanwar Isma’il ce”..ai tun kafin ta rufe baki ya wara ido sosai yana kallonta fuskanshi har ya sauya sbd 6acin rai…bata damu da sauyin face din nashi ba tacigaba”zuwa tayi tanaso ta tafi dasu Miemie su dubo grandmum dinsu da batada lafia”…bata rufe baki ba cikin zafin rai still da igbo yace”babu inda zasuje Mummy…basu bukatan wayan nan mutanen a rayuwarsu”…shiru Mummy tana ganin yanda yakeson kunyata ta gaban baiwar Allahn nan..dukda bada hausa yayi mgn ba tasan zata iya fahimta sbd yanda ranshi ya 6aci all of a sudden…Aunty Sumy kam dama she expect this to happen shiyasa she’s not surprised…ita kuma bakuwa Hafsa kanta na kasa tana sauraronsu…dukda bata gane me yake cewa ba har ga Allah ko hanata daukan yaran sukayi bazatayi blaming dinsu ba tunda tasan duk wulakancin da sukama uwar yaran har ma dasu kansu yaran a baya so bazataji haushinsu ba ko kadan…Bobby da yaji zuciyarshi na kara haurowa sama mikewa kawai yayi ya fita daga parlon cox idan yaci gaba da zama zai iya causing scene din da he might end up regretting dan haka yake ganin it’s better he leaves…Mummy da taji kunyan abunda ya fada ta bishi da kallo kawai har ya shige flat dinshi snn ta dawo da kallonta ga Hafsa tace”don’t mind him Hafsa inshaAllah tare zaki tafi dasu..amma ayi kokari a dawo dasu gobe sbd kar suyi missing school”…da sauri Hafsa tace”in Allah yadda za’a dawo dasu Mummy…nagode sosai Allah ya saka da alkhairi”…Mummy ta amsa da Ameen snn ta juya ga Aunty Sumy da ita kanta bataji dadin hukuncin da Mummyn ta yanke ba tace taje ta hada kayan Ilham ta kawo itama Miemie ace ta shirya nata kayan ta fito…haka ta mike jiki ba dadi ta shiga flat dinta…dakin Miemie ta fara tsayawa ta fada mata ta dauki kaya set daya zasuje gidan grandma dinsu da Aunty Hafsa…itama ranta baiso ba amma ba yanda ta iya ta dauki set dayan kaman yanda tace ta saka a jaka snn ta fita…itama Aunty ta fito da na Ilham a hannunta.

Miemie ta amsa kayan ilham din ta hadashi da nata cikin bag din data dauko snn ta samu wuri ta zauna…Hafsa ta mike tana duban Mummy tace”Mummy to bari muje in Allah ya kaimu gobe da kaina zan dawo dasu..nagode sosai da sasai Allah ya saka da alkhairi ya kara girma”…Mummy tace”ba komai Hafsa Allah ya bata lafia”..ta amsa da Ameen snn ta rike hannun Ilham zasu fita Mummy tace”Ilham ba sallama?..”juyowa tayi tana murmushi tace”ba bye Mummy mun tafi yawo”…murmushi na daria tace”to a dawo lafia”..daga haka suka fita Aunty Sumy da Miemie sukabi bayansu…kafin su karaso har ta bude mota sun shiga..suna zuwa Miemie ma ta bude ta shiga ita kuma Aunty Sumy tace”to shknn Hafsa sai goben koh?..”Hafsa tace”eh inshaAllah…ina godia fa Maman Miemie Allah ya bar zumunci”..Aunty Sumy tace”Ameen”..snn ta dagama ilham hannu alama bye itama ta daga mata…Miemie dai na zaune back seat duk rai a 6ace..sam batason zuwan inda matar nan wlh..dukda ba wani girma gareta ba time din she can still remember yanda sukayi treating nasu kaman ba family dinsu ba…bayan sun gama sallama Hafsa taja mota ta tafi ita kuma Aunty Sumy ta koma gida.

Basu zarce ko ina ba sai gidan kakarsu dake Kabuga…tana gama parking ta bude motar ta fita tareda kama hannunsu gaba daya su biyun suka shiga cikin gidan a haka…kakarsu na kwance parlor tana jiran karasowarsu…tana ganinsu ta mike zaune da kyar ta kama hannayensu kawai sai ta rushe da kuka..ba ita kadai ba hatta Hafsa saida ta tayata kukan…ko baa fada ba tasan tanajin ciwon raba Sumayya da Isma’il tunda gashi nan tun bayan rabuwarsu ta kasa gane kan danta…matar data aura mishi ma bai dade da rabuwa da Sumayyan ba ya saketa shi kuma ya tattara ya koma London da zama sbd baqin cikin rashin Sumy…kuka takeyi sosai tana cewa su taimaka su yafe mata snn su roki mamansu ma ta yafe mata…Ilham dai tayi tsuru as kwata kwata bata san inda zancen ya dosa ba…Miemie kuwa sarai ta fahimci me take nufi amma tayi gum da bakinta dan bataji zata iya yafewa ba itadai…ta dauki tsohon lokaci tana kuka tana su yafe mata ganin kamar numfashinta zai dauke suka rabata da hannuwan yaran da kyar snn suka dauketa suka maidata daki itada autarsu mai suna Safiyya…Hafsa na fitowa daga dakin ta dannama dan uwanta video call don yace tana daukosu ta kirashi vid call yanaso ya gansu…yana ganin kiran nata ya dauka tana murmushi tace mishi”to Yaya ga ‘ya’yanka dai yau na kawosu wajen Umma”…yace”kin kyauta sosai Hafsa..dan banisu mu gaisa plss”…ba musu ta mika musu wayan tace”speak to ur Dad”..Miemie ta wani hade rai snn ta karbi wayan…kallonsu ya shigayi sosai idonshi na cikowa da hawaye…it’s been six long years rabonshi da ganinsu..yanxun kuma daya gansu sai yakejin wani irin kewa da sonsu na sake shiganshi…murya can kasa yace”Mamana”…Miemie ta dan tsuke baki kafin tace”na’am ina yini”…yace”lafia mamana ya school?..”a takaice tace dashi”fine..”kallonshi ya maida ga Ilham da tayi tsit tana kallonshi dan ba  saninshi tayi ba…shima saida yaji wani kuka ya taho mishi da yaga kallon da take masa…ko ba’a faa ba yasan kallon rashin sani ne wnn..wai ace yana matsayin mahaifinta amma ta tashi bata sanshi ba…shi kam ina zaikai zunubin yaran nan dana uwarsu?..itama murya a sarke yace mata”Maman Aunty”…ta sake yin zuru tana kallonshi dan bata gane me yake nufi ba..Miemie dai ta gane don bazata manta ba lokacin tana jaririya haka yake kiranta Maman Aunty ita kuma Miemien ya kirata da Mamana..itama Aunty tacema Miemie Maman daddy snn tacema Ilham Mamana…yayi kokari ya maida hawayen dake idonshi yace”baki sanni ba right?..”da sauri ta daga mishi kai…yace”i am ur father”..yarinyar ta wara ido sosai hadda su rufe baki tace”Uncle Bobby ne babanmu ai”…yace”yea he is ur dad but ni na haifeku”…idon ta sake budewa cikeda mamakin abunda ya fada tace” dama maza suna haihuwa ne?..”diff yayi kamar ruwa ya cinyeshi..sai can kuma yace”sunayi mana kinga ni din nan nine babanku..shi kuma Uncle Bobby uncle dinku ne shiyasa kuke kiranshi da uncle”…kafin Ilham ta sake mgn Miemie tace”sai anjima”…tana kokarin kashe kiran yace”don’t hang up plss..i missed u guys alot ko ganinku bazaki bari nayi ba?..”tayi shiru ba mgn shi kuma yace”ya Mamanku?..”ta sake cewa”she is fine..”shima ya danyi shiru na tsahon lokaci kafin yace”i know u are upset with me Miemie but believe me wlh nayi regretting komai dana aikata dan haka please inaso ki yafemin snn ki tayani rokon mamanki ma ta yafemin”…kallonshi Miemie tayi for like two minutes snn tace”toh..”daga haka bata jira me zaice ba ta kashe kiran..sam ta gaji da jin wnn maganganun nashi…ita har taso ta manta kamanninshi ma wlh..ilham kuwa dama bata sanshi ba so bata dauki abunda ya fada serious ba…haka suka kwana gidan duk basu wani sakewa dasu duk kuwa da yanda yan gidan suke kokarin jansu a jiki kin sakewa sukayi.

A can gida kuwa Bobby baisan tare dasu Hafsa ta tafi ba saida ya dawo daga Hospital around 9 na dare ya tambayesu Aunty Sumy tace sun tafi da Hafsa…wani hadadden kunchi yaji yana sauko mashi..yanxu knn Mummy saida ta tura yaran nan suka tafi?..bayan duk abubuwan da suka aikata a baya still take kokarin patching things up dasu?..ranshi gaba daya yaji ya 6aci..kawai ya wuce Flat dinshi…karfe goma da wani abu Mummy ta zuba abinci ta dauka da kanta ta nufi Flat din nashi…yana kwancen can kuryar gado ya juyama kofa baya..ta karasa ta ajiye abincin hannunta kan table snn ta isa gefen gadon nashi ta zauna…a hankali takai hannu ta zare hannunshi daya rufe fuskanshi dashi…ha dago yana kallonta snn ya mike zaune da kyar kaman mara lafia…sake kama hannun nashi tayi ta rike tana kallonshi da igbo tace mishi”so u are upset with me right?..”a hankali ya girgiza kai alaman aah…tace”you are lying nasan fushi kakeyi…kana jin haushi sbd na bari Hafsa ta tafi dasu koh?.”kasa yayi da kanshi baice komai ba…Mummy tace”Bobby you won’t understand..bansan ya zanyi maka bayani ba..kawai dai banaso ka nesantasu da yan uwan mahaifinsu kaman yanda ka nesanta mu da gaba daya yan uwan mahaifinku..ni kadai nasan how am feeling duk na tuna cewa grandfather dinku na nan da rai amma baisan inda kukeba tsawon shekara biyar…inaji a jikina bamu kyauta ba sam kuma nasan Allah bazai yafe mana…”bata karasa ba ya rufe bakinta tareda matsowa sosai ya rike hannayenta…idan ya bari tacigaba da magan nn tsaf zata kashe mishi jiki tasa ya farajin kaman shima bai kyauta din ba…ga kuma jininta da zai iya hawa idan bata bar wnn damuwan ba…yana kallon cikin idonta yace”Mummy ba laifi bane…ba laifinmu bane…laifinsu ne da basu ta6a yunkurin nemanmu ba…su kuma su Ilham nasan ke da kanki kinsan meyasa banso suje inda mutanen nan sbd ba sonsu sukeyi ba”…hawaye suka shiga sauka fuskanta tace”duk abunda in the past bai  kamata mu bari yayi affecting future dinmu ba…we are all Humans Bobby and we all make mistakes…nasan abunda da sukayi is uncalled for amma ya zamuyi?..dole haka zamuyi hakuri dasu tunda sunyi nadama…zumunchi ba karamin abu bane Bobby banaso Allah ya kamamu da laifin yanke zumunta a ranar gobe kiyama”…tana karasawa wasu tawagar hawaye suka sake biyo fuskanta Bobby baisan sanda ya matsa tareda rungumota jikinshi ba…kuka takeyi sosai da alama dama ta jima tana neman inda zatayi kukan…bai hanata ba saida ta dakata dan kanta snn yace”Mummy to kukan ya isa haka plss and we shouldn’t talk about them again..am not angry anymore”…ta saki dan murmushi tana share hawayenta tace”then tashi muje kaci abinci”…baiyi musu ya mike ya koma kan sofa ya zauna snn ya janyo table data ajiye abincin akai ya fara cin kayanshi…itama mikewan tayi ta dawo kusa dashi ta zauna snn tace”and mgnr zuwa duba Waziri”…a takaice yace”yana nan Mummy..idan ya dawo zamuje gaba daya mu dubashi..are you happy now?..”sake gyada mishi kai tayi tana murmushi…shi kuma yacigaba da cin abincinshi amma deep down yasan abunda ya fada karya yake…ko kusa baijin zuciyarshi zai iya mance tarin munanan abubuwanda Waziri da iyalanshi suka aikata musu har yaje inda suke..sam hakan ba mai yiwuwa bane ya fada mata ne kawai dan ta dena damuwa amma baida intension din zuwa ko ina..shi a yanda yakeji mafa ko rasuwa waziri yayi saidai suje za’aziyya kawai su dawo amma ba wani zaman makoki da zasuyi tunda bai ta6a daukansu a matsayin Family ba.

Gombe…

Tsaye take a kitchen tana suyan Pancake fuskan nan a tamke kaman wanda aka aikoma da sakon mutuwa…daga gefe kuma Ammi ce tana kokarin hadama Daddy breakfast dinshi a kan tray sai kuma mai aikinsu dake juya pepper soup a kan gas…bayan ta gama hadawa ta dauki tray din kafin ta fita ta dubi Aysha dake faman tura baki tace”kuma wlh idan bakiyi sauri kin gama ba har Lamido ya fita bakuje kun gaisheshi ba zakiga yanda zanyi dake a gidan nan”..mai aikinsu mai suna Asabe tace”da kin barta hajia zan karasa wlh..ita taje tayi shiryawanta”…Ammi tace”bazan barta ba Asabe na lura tunda ta dawo gidan daga kallo sai chatting ta iya bata tsinana uwar komai ko dakinsu saidai Husna ta share..anjima ma ita zaku bawa suyan fried rice tayi ai ba bayi ta ajiye dan sunayi mata girki ba”…tana gama fadin haka ta fita daga kitchen din…ita dai Aysha na tsaye tana aikin gabanta ko juyawa batayi ba amma fuskan nan kaman zatasa kuka…ko Allah yasan ba mai son girki bace ita…gara a bata duk wani aikin gida zatayi amma ta tsani girki shiyasa ko a makaranta Billy keyi musu girki…Asabe na ganin Ammi ta fita ta kashe gas din gabanta snn ta matso inda Aysha take tana amsan spoon din hannunta tace”kawo in karasa kinji indo…ki tsaya daga nan ki huta idan mukaji zata dawo saiki kar6a kicigaba”…nan da nan kuwa ta sakin mata shi tareda matsawa gefe tace”nagode Baaba”…Asabe tacigaba da suyan Pancake ita kuma ta rungume hannu tana kallonta…wayanta dake aljihun jean dinta ne ya fara ringing…ta zaroshi da sauri tana sakin wani smile ganin Prof ke kira tasan yanxu zaiyi flushing wnn 6acin ran da take ciki…saida ta gama kwa6e fuskanta tayi readyn shagwa6a snn tayi picking…a daya 6angaren Professor yace”my baby girl”…ta wani cunno baki sai kace yana ganinta tace”umhhm”…yanajin yanda tayi replying yasan akwai matsala…if u see yanda ya gigice zakasha namaki…fadi yake”my baby please what happened…waya ta6amin ke?..”ta sake narkewa tana tale baki tace”baby Ammi ne”…yace”Subhanallah me Ammi tayi maki?..hope ba dukanki tayi ba?..”tace”cewa tayi sai nayi suyan Pancake…kuma ni baby banason girki fa”…tana iya jiyo sautin dariyarshi kafin yace”eyya sorry my baby gaskia Ammi bata kyautamin ba..why zata turamin mata kitchen?..”tana sake narkewa tace”shi na gani nima baby..aidai in munyi aure bazaka na sani girki ba koh?..”yace”wane ni in saka princess dina girki…duk abunda mukeso ordering zamu dingayi ko mu dauko chefs su dafa mana”…lokaci daya ta wage baki tana smiling tace”yauwa my Professor..my very own baby durling”…saida ya lumshe ido daga can inda yake ya wani dora hannu kan chest dinshi yace”ohhh that sounds sweet baby…i love u”…tace”i love u more baby”…mai aiki dai na aikinta tana sauraron yanda take zuba shagwa6a tana murmushi…ko su da suke aiki gidan sun san Aysha mai son shagwa6a ce duk kuwa da cewa iyayen nata ba shagwa6ata suke ba…haka taciga da wayanta har aka gama suyan Pancakes din snn ta dora wormern da aka zuba kan tray ta fita dashi parlor…dining ta karasa ta ajiye snn ta nufi parlorn daddy…as usual suna zaune dinning suna karyawa shida Ammi…ta karasa ciki bayan ta nutsu snn ta gaisheshi ta bar parlon…tana fita ta samu su Husna a dinning itama ta karasa ta zauna suka fara breakfast…Ammi da daddy suka fito tare bayan sun kammala suma…Ammi na rikeda briefcase dinshi zasuje gaida Lamido shi da yaran daga can kuma zai wuce Abuja wurin aikinshi…su Aysha na zaune parlor suma sun gama nasu breakfast din kowacce sanyeda katoton hijab sbd zaaje gaida Lamido…Daddy ya kalli yanda sukayi reras a parlon kowa tasha hijab kawai ya girgiza kai yasa daria…ya lura har wani nutsuwa na musamman sukeyi duk zasuje wajen Lamido snn kaf jikokinshi ba wadda take zuwa mishi ba tareda hijab ba dan fada yake sosai…bayan ya gama dariyan ya kallesu one by one yace”are we good to go?..”suka hada baki wajen fadin”yes daddy”..snn yace”to ku tashi muje”…gaba daya suka mike suka fita…shima suka fita tareda Ammi…har jikin mota ta rakashi ta bude mishi kofa da kanta ya shiga snn ta ajiye briefcase dinshi..suma su Aysha nasu motan suka shiga tana kallon Ammi tana sallama da mijinta cikin ranta tace” muma dai muzo muyi auren nan wlh..haka zanje inta yima babyna yana lalla6ani”…Yusra dake jikinta tace”Adda me kika ce?..”ta saki murmushi tana shafa kan Yusra tace”ba komai habibty…bance komai ba”…motan daddy ne ya fara fita daga gidan snn nasu.

Kofar gidan Lamido motocinsu sukayi parking…daddy ya fara fitowa suna biye dashi zuwa ciki…katoton parlon Lamido dake daukeda two sets of kujeru suka shiga…yana zaune kan one of kujerun sai wasu mutane biyu zaune a kasa suna gaisheshi…karasawa ciki sukayi daddy ya zauna kasa ta right side dinshi su kuma suka zauna his left side…kyakkyawan bafulatani da a kallon farko da kayi masa zaka gane attajiri ne snn kuma yanada dattako…kamanninsu daya da daddy saidai haske da daddy zai nuna masa shima ba sosai ba…bayan ya sallami mutum biyu dake zaune ya juya yana duban daddy yace”Ahmad har an fito?..”cikeda respect daddy yace”na samu fitowa Baffa…barka da safiya”..yace”barka dai ya iyalin?..”kai a kasa yace”suna nan lafia Baffa…tace a mika mata gaisuwa kafin ta shigo”..gyada kanshi yayi yace”to mashaAllah”…sai kuma ya juya ga su Aysha ya dan saki murmushi yace”mutanen Lamido”…da ladabi suma suka dukar da kai suka gaisheshi…ya amsa tareda tambayansu makaranta sukace Alhamdulillah…idonshi ya tsayar kan Aysha kafin yace”ke saura wata nawa ki gama karatun ne Aisha?..”tace”ba watanni bane Lamido saura shekara daya da rabi”..gyada kai yayi yace”to ba laifi Allah ya kaimu..Allah yasa a gama lafia”..sukace” Ameen Ameen”…sun dan jima suna hira har wani qanin daddy ya shigo shima da ‘ya’yanshi…suka gaisa dashi snn daddy yayi salama da mahaifin nasa suka fita…kai tsaye ya shiga motanshi suma suka shiga nasu bayan ya sallamesu suka koma gida shi kuma suka fita daga Estate din.

Kwanci tashi abun ba wuya har sun cinye sati biyunsu cif sun fara shirin komawa makaranta…tunda satin komawa ya shigo Aysha take kunci tana baqin ciki sam batason komawa wlh especially idan ta tuna wnn dan rainin hankalin inyamurim Proprietorn nasu…sam bata kaunarshi wlh…neman hanyan da zata sanar da Ammi kawa take amma ta rasa dan haka ta tsiri 6ace 6acen rai sai ta zauna a parlor da gayya tayi tagumi wai tanaso Ammo ta tambayeta abunda ke damunta ta fada mata amma Ammi tayi biris da ita kaman batasan tanayi ba…abu daya dake dan yaye mata wnn damuwan shine Prof dinta…zuwa yanxu soyayya sukeyi sosai sai kace wanda sukayi shekara da shekaru a tare…yana mugun shagwa6ata kaman yanda takeso ita kuma tana sake falling mishi.

Kaman kullum yau ma tana zaune ta buga uban tagumi a parlor wai ko Allah zaisa Ammi ta tambeyi meke damunta saidai abunda bata sani ba shine Ammi ta rigada ta ganota tasan duk wnn attitude da take displaying kilan sbd komawa makaranta ne shi yasa taki kulata…Ammi ta shigo parlon waya kare a kunneta tana mgn da Aunty Fiddausi…bayan ta gama ta dauki remote tana kokarin kunna tv Aysha da taga still bazatayi mata mgn ba ta dan marairaice tana dubanta tace”Ammi..”ba tareda ta bata attension dinta ba tace”na’am”…sake narkewa tayi tace”Ammi bazaki tambayi meke damuna ba?..”dan juyawa Ammi tayi tana kallonta kafin yace”what’s wrong..are u sick?..”sake marairaicewa tayi ta koma kalar tausayi tace”Ammi dan girman Allah ki cema daddy bazan koma makaranta ba plsss”…fuska daure Ammi tace”sbd me?..”tace”bana sonta wlh kuma yanxu ba wani karatu akeyi ba sai shegen takurawa mutane”…gyada kai Ammi ta shiga yi tace”dama nasan karshen zancen knn…kilan kinje kinyi laifi anyi miki fada shine zakizo kice mana bazaki komaba kuma kike tunanin zamu yadda dake kaman bamusan halinki ba koh?..to bari kiji in fada maki babu fashi komawa makarantanki gobe idan kuma kika sake kika sake min mgnr nan sai kinci ubanki wlh…daidai nake dake ai kinsani”…nan da nan ta fara hawaye tana cewa”nifa Ammi Allah na gaji da Kano inaso in dawo gida…kuma Proprietor dinmj inyamuri bashida mutunci wlh”…Ammi mikewa tayi zata bar parlon tace”ur problem not mine..nidai na gama mgn kuma Allah yasa kar ki dena kukan nan kiga yanda zanyi dake a gidan nan…shashasha kawai”…daga haka Ammi ta wuce dakinta…ita kuma hajia indo ta rungumi pillow tana sake rushewa da kuka.

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE