FARAR WUTA CHAPTER 3 BY AISHA MAHMOOD
FARAR WUTA CHAPTER 3 BY AISHA MAHMOOD
Ana gobe sallah ne ranar, ita da Maryam sun je kasuwa siyayar mayafai da takalmi, tun kusan sha biyu suka fita har mutane suka fara alwalar sallar la’asar basu gama siyayyar ba.+
Maryam dake riƙe da ledar kayan da suka siyo kalli tsinken kwakwar da suka auno tsawon kafar Hafsa dashi tace.
“Ai wallahi dama na san takalmin yarinyar nan shi zai bamu wuya, kafa kamar ba ta mutane ba ƴar firit da ita.”
Amina ta share gumi a gefen fuskarta tace.
Har tunani nake ko ba daidai na auno ba wallahi gashi mun kusa gama siyen komai…”
Bata karasa ba ta tuno da sakon garin da Amma tace su siyo zata yi teba dashi da daddare.
“Kin san na manta da garin Amma… zo muje wancan layin na san zamu samu.”
Maryam ta girgiza kanta.
“Mu raba tafiyar kawai lokaci ƙara wucewa yake, ga wani kantin takalma can, bari naje na duba idan ma ban samu ba zan jira ki sai kizo ki same ni anan.”
Da haka suka raba tafiyar, Maryam ta tsallaka ta cikin cunkoson mutanen ta nufi kantin ita kuma tabi layin gefensu inda nan ɗin ma turuwar mutanen ce wadda dama sun riga sun shirya mata, don tun ana saura sati ɗaya sallar suka so zuwa kasuwar amma rashin haɗuwar kudin yasa dole sai yau suka samu suka fito.
Ga rana, ga azumi amma yadda mutane suka hargitse baza kace kowa a gajiye yake ba. Da kyar ta samu ta ɓulla layin da masu garin suke, kuma akan ragin naira hamsin ɗin da zasu yi kuɗin mota dashi, sai da ta kusan shanye layin tana tambaya da ƙyar ta samu wani acan ƙarshe yace zai rage mata.
Tana tsaye yana ƙoƙarin auna mata, wani yaron shagon nasa ya shigo, irin samarin nan ne masu magana, yana shigowa ya haye kan ɗaya daga kantocin shagon yana fadin.
“Allah na tuba a yadda ake wannan ranar ga azumi ai wallahi komai talauci na ba zanyi aikin sauke gari ba, don mugunta kaga yadda suke jefo musu buhun nan daga sama, wani har sai ya kai ƙasa wallahi kafin ya ɗago.”
Maganar ta ɗauki hankalinta, tana hango yadda nauyin buhun gari yake ace mutum ya dauka a wannan ranar.
“Yau ma mota ta sauka ne?”
Mai shagon ya tambaya yana miko mata ledar garin.
“Gata can yanzu ta tsaya, ka san shi Auwalu ko da goma yaga sunyi ƙasa sai yayi aike.”
Ta miƙa masa kuɗin tana faɗin ta gode, amma kafin ya karba saurayin yayi saurin miƙo hannu ya karba sannan ya miƙo mata yana mata murmushi, irin halin ƴan kasuwa.
A kofar shagon kuwa tana fita taga motar ana ta sauke garin, tausayin masu yin dakon ya tafi har cikin ranta ganin yadda ko a ido buhun ke da nauyi, tana tafe tana ganin fuskokinsu lokacin da idonta ya kai kan fuskar da ta sa ba shiri hannunta ya saki ledar garin nan… Mahaifinta ta gani dauke da wani katon buhu yana ƙoƙarin kaiwa inda sauran ke saukewa, mahaifinta dai Baba, Baban daya shirya tsaf a yau ya fita suna yi masa a dawo lafiya.1
A wannan lokacin yana gaɓar farfaɗo wa daga karayar arzikinsa ne, don duk da kokarinsa wajen yi musu kayan sallah, har saida aka haɗa da kuɗin Aminu kafin komai ya isa, bata san lokacin da hawaye ya fara biyo kuncinta ba, taga ya sauke ya koma sake ɗauko wani… Baba mutum ne mai tsananin son dogaro da kansa kowa ya sani, yayyensa duka sunyi kokarinsu wajen tallafa musu tunda al’amarin ya faru, amma babu wanda ya isa ya ɗauke maka cin yau da gobe sai Allah, don haka ta san nauyin ya cigaba da tambayarsu ne yasa har ya kawo kansa yin wannan aikin don kula dasu.
STORY CONTINUES BELOW
Hawayen ya cigaba da bin fuskarta yayin da zuciyarta ke rawa a kirjinta, tunanin ta ɗaya ne a lokacin, idan har mahaifinta zai iya sadaukar da girmansa yayi wannan aikin don kawai ya fita kunyarsu meye su baza suyi don fita tasa kunyar a duniya da kuma lahira ba?
Ta share hawayenta lokacin da wani mai wulbaro ke miko mata ledar garin da Allah yaso bata fashe ba. Kuma bata fadawa Maryam abinda ta gani ba, bata fadawa Amma ba, bata fadawa kowa ba, don ta san hakan wani abu ne da Baban ba zai taɓa so waninsu ya sani ba.
Kuma a wannan daren sai gashi ya dawo da ledar kaza har guda biyu ta miyar sallah, su Hafsa suka yi ta tsallen murna yana binsu da nasa murmushin shima.
Wajen karfe biyun dare bayan kowa ya kwanta, ta hango shi ta ƙofar ɗakinsu a wajen banɗaki yana miƙe bayansa, kukan da tayi a cikin filonta a wannan daren Allah kaɗai ya san yawansa, abu ɗaya kawai ta sani shine tayi wa kanta alƙawari a wannan ranar cewa ko abinda yafi rayuwarta ne zata sadaukar a duniya don farantawa mahaifinta.1
*
“Wallahi gani nake yi kamar zaki ƙyalƙyale da dariya ki gaya min wasa kike yi.”
Fatima ta faɗa tana kallon Amina data idar da sallah a gabanta.
“Ke ma kin san ai ban taɓa miki irin wannan wasan ba, da gaske nake Fatee, don yanzu haka ma Baba ya tafi gidan Kawu Mallam ya faɗa masa.”
“Ya fada masa cewa kin yarda zaki auri wanda yake da matsalar ƙwaƙwalwa Amina…? inalillahi wa’inna ilaihir raji’un Amina kin san Allah ko da nake cewa ki rabu da Abdallah ki samu wanda yafi shi ba irin haka nake nufi ba, ya za’ayi kiyi irin auren da ake bada labarin ire-iren sa a sigogi mara sa daɗi?”
Fatiman ta ƙarashe muryarta na karyewa. Amina ta cire hijabin sallar tana kallonta,
“Ban gane me kike nufi ba?” Ta tambaya tana kallonta. Fatima ta girgiza kai kafin ta gyara zamanta.
“Amina duk wanda yaji batun auren wallahi shaidar da zaiyi miki daban, kowa cewa zaiyi auren kuɗi zaki yi, musamman ƴan unguwar nan da kin san daman ƙiris suke jira akanki.”
Amina ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, abinda Fatiman ta faɗa gaskiya ne ta sani, kuma maganar iri ɗaya ce da maganganun Amma na jiya, duka su biyun ƴancinta suke nemar mata, amma a wajenta darajar mahaifinta itace a gaba da ita kanta don haka ta riga ta gama yankewa kanta hukunci, ta gayawa zuciyarta cewa zata tsaya tare da mahaifinta koda zata mutu sau biyu idan ana yi.
“Fatee na tabbata ba fa ba wai matsala ce sosai ba, kawai sun faɗa ne saboda kinga a aure ba’a ɓoye komai, kuma ma Baba yace baza’a bari maganar ta fita ba, kema kin san ba zan iya ɓoye miki bane.”
Ta faɗi hakan yayin da idanunta ke hango takardar data cusa cikin kayanta a jiya, babu wanda ya san da ita, babu wanda ta gayawa hatta Amma kuwa duk yadda kowanne abu mai hankali a cikin kanta ya tsorata da maganar dake rubuce, amma ta sani cewar in har iyayenta suka ji hakan dole zai iya sake zama wani ƙalubale musamman ma a wajen Amma don haka ta yanke hukuncin ɓoyewa tunda ba zata taba fatan abinda zai hadassa mahaifinta yaji kunya ta dalilinta ba.
Kuma kafin Fatiman ta sake cewa wani abu suka tsinci sallamar Ummi daga tsakar gida, ƴar Kawu mallam wadda suke kusan sa’anni da Aminan.
“Ina amaryar take?” Muryarta ta fito da fara’a bayan ta gaisa da Amma da kuma Maryam wadanda suke kitchen, ta karaso ya ɗage labulen ɗakin tana kallon Amina bakinta a washe.
“Yarinyar nan da tsinannen wayo, sai dai muji kawai wai zaki yi aure?”
Sai dai Amina tayi wani guntun murmushi kafin tayi mata sannu da zuwa.
STORY CONTINUES BELOW
“Ni ba zan amsa ba wallahi, tunda sai da muka ga meeting ɗin su Kawu yayi tsawo sannan da kyar muka san me ake ciki, da ake ɓoye mana naga wanda zai raka ki siyayyar kayan bikin ai.”
A cikin maganar ta Amina ta tsinci wani abu, cewa da gaske Baba yake a ɗazu daya shaida mata cewar kowa zai ji maganar auren ne ta fuskar alkhairi, babu wanda zai san me ake ciki, gashi kuwa ko iyalan Kawu Mallam ɗin da ake taruwa a gidansa basu san komai ba, zurfin maganar ya tsaya a iyakar Baba da yayyensa ne sai kuma Amma, Fatima, Maryam da Aminu da suka sani a yau. Ance zancen duniya baya ɓuya, amma har cikin ranta tana fatan zancen ya tsaya a iya wadannan mutanen kawai.
“Ai ni ban yi zaton har ɗan bokon naki ya gama makaranta ya shirya ba, shi yasa wallahi abun ya bamu mamaki sosai, har su Umma ma cewa suka yi koda wasa Amma bata yi musu zancen a kurkusa ba.”
Amina ta girgiza kanta.
“Ai ba shi bane Ummi, wani ne daban.”
Sai da Ummin tayi shewa kafin tace.
“Gaskiya ne yarinyar nan, kice da karfinki kika taso, Fatima bani labari don na san zanfi ji a wajenki, wane ne sabon kamun?”
Fatima tana take tace.
“Wallahi kin san al’amarin Allah ai, kawai komai a lokaci guda yazo.”
“Eh, amma dai da maiƙon sa ko? Yadda komai ya taso a lokaci gudan ai na san a shirye yazo ko?”
Kawu malam mutum ne malami mai sauƙin sha’ani, amman sai Allah ya bashi matansu duka ukun masu azabar son kuɗi, kuma suka taso da ƴaƴansu ma gabaɗaya akan hakan, gashi mata sunfi yawa a ciki don haka a zaune yake cewa basa auren kowa sai mai abin hannunsa ire-iren ƴan kasuwa, gasu da surutu da kuma kauɗi, hakan yasa duk kusancinsu dasu Amina basu fiye shiga cikinsu sosai ba don halayensu sun banbanta duk kuwa da cewa suna da mutukar kirki.
“Ai kuwa dai yana da kuɗi gidansu ma haka.”
Fatima ta bawa Ummin amsa har a lokacin tana murmushin yaƙe.
“Kice dole ne mu raƙashe a bikin nan, wallahi azo a saka mana rana ma nan kusa Momi tazo mu fara shirye-shirye, zaki yi anko?”
Amina taji wani abu ya tokare mata a maƙoshi, don ita har ta yanke hukunci bai taɓa zuwa kanta cewar ma biki za’ayi ba, gani take kamar jana’iza kawai za’ayi akaita, kuma sai Allah ya taimake ta kiran Amma yazo a daidai lokacin don bata san amsar da zata bawa Ummin ba.
Amma ta kalle ta bayan ta isa kitchen din, fuskarta fayau tace.
“Kizo ki zuba muku abinci gashi nan an sauke.”
Ta haɗiye yawu a hankali tana ƙarasawa ciki, lokacin da flask ɗin ruwan zafin nan ya faɗi daga hannun Amma, sai ya zama kar ya fashe da dukkan irin hukuncin da take tunanin Amman zata dauka akan ƙin bin maganarta da tayi, don a lokacin bata ce komai ba, juyawa tayi kawai ta bar wajen yayin da Baba ke saka mata albarka, kuma bayan taje ta same ta a ɗaki, abu daya kawai tace.
“Rayuwarki ce dama Amina, na nuna miki kuskuren dake ciki ne kamar yadda yake alhaki na a matsayin uwa, kuma tunda har kinga zaki iya dauka, ga fili ga maidoki nan, zuciyata ba zata riƙe ki da komai ba, Allah ya baki sa’a.”
Daga haka bata ƙara cewa komai ba, kuma bata yi fushin da Amina tayi zato ba, harkokinta ta cigaba da yi a gidan kamar dama maganar bata taso ba, kamar dai shekaranjiya da Baba bai ko ziyarci gidan Hajiya Kilishi ba, balle su san da komai.
Ta zuba abincin ta kai musu, suna ci Ummi na daɗa bada bayanin yadda abubuwa zasu kasance wanda daga ita har Fatiman yaƙe kawai suke suna amsa mata, wajen la’asar ta tafi, lokacin ma Fatima ta daɗe da tafiya asibiti inda tace yau za’a sallamo kakarta.
STORY CONTINUES BELOW
Wajen ƙarfe biyar, Aminu ya shigo gidan riƙe da wani flask lokacin da take wanke-wanke ita kaɗai a gidan, don Amma ma ta shirya ta tafi gidan wata ƴaruwarta a Goron dutse ta shaida mata al’amarin.
“Ina yarinyar nan take?”
Ta san Maryam yake nema don haka tace.
“Ta tafi makaranta tun ɗazu.”
Sai ya ajiye flask ɗin a ƙofar kitchen sannan ya ƙaraso ya tsugunna a kusa da ita, muryarsa ɗauke da nutsuwar da zaka shafe rabin rayuwarka kafin kaji ta a wajen Aminu yace.
“Hukuncin da kika yanke yayi daidai Amina, ba don Amma ba daidai ta faɗa ba, sai don kare mutuncin Baba da kika yi, kuma na tabbata Allah zai duba hakan ya kyautata rayuwarki.”
Kwalla ta taru a idonta lokaci guda, don haka ta gyada kai kawai ba tare da tace komai ba. Wucewar wasu ƴan sakanni shima yana tsugunee kamar yana sake biya abinda ya fada a zuciyarsa, sai kuma yayi gyaran murya sannan ya koma Aminun da yake.
“Kin gayawa Malam ne?”
Ta san Abdallah yake nufi don dama haka yake kiransa, saboda haka ya girgiza kanta tace.
“Na san dai zai zo anjima.”
“Kice yau Malam zai danɗani baƙin cikin latecomer kenan.”
Bata san lokacin da ta watso masa ruwan wanke-wanken ba tana jin wani abu a zuciyarta na fadawa, ya kauce shima yana dariya sannan yayi hanyar fita yana faɗin.
“Idan wannan ƙwalamammiyar ta dawo kice mata ga wainar masar da take ƙalata nan na samo mata.”
Bayan ta gama wake-wanken ta koma ɗakinsu har a lokacin ƴan islamiyar basu dawo ba balle kuma Amma, a ƙasan kayanta ta sake ɗauko wannan takardar tana karantawa, idanta suka tsaya akan sunan yayin da a yanzu bayan tsoron ma’anar rubutu wani sabon tsoro daban ke shigarta.
Ma’aruf B.
Ta karanta sunan tana jin yadda tsoron harafan kadai ke zanuwa a zuciyarta, ba wai don ta sanshi ta gane waye ba sai don zuciyarta bata cika manta fuskokin mutane ba koda kuwa sau ɗaya ta taba arba dasu, kamar dai shi rana guda ta taɓa ganinsa a rayuwarta kuma bata ƙara ba daga sannan.
Ranar ɗaurin aurensa, ranar da Baba yasa suka tafi tunda sassafe ita da Amma don wai suyi yinin bikin da gaske kamar yadda aka rubuta, a lokacin da ya shigo gidan shi da abokansa da ƴanuwansa bayan ɗaurin auren, ita da Amman suna rakuɓe daga can jikin wata kujerar a falon Hajiya Kilishin, kuma duk da tarin ƴan bikin mata da suka yanyame shi da tsokanar ‘ango kasha ƙamshi…’ sai da idanunta suka iya hango mata shi yasha farar shaddar dake ƙyalli kamar murmushinsa, yana tsaye daga tsakiyar mutane yayin da masu hoto ke ta yi musu kala-kala.
A wannan lokacin gani take kamar bambancin su ita da Amma da mutanen gidan ya zarta na mutum-mutum, don bayan Hajiya Kilishin da ta amsa gaisuwar su cike da fara’a ta kuma sa aka kawo musu abinci babu wanda ya ƙara lura dasu a gidan, sai wata mace guda ɗaya da tace Amma ta ara mata hijabinta lokacin sallar azahar, itama da alama irinsu ce don ta ɗebo tarin ƴaƴan da ta cika musu faranti taf da abinci suna ta ci. Daga baya ma dole suka bar cikin falon suka zagaya baya can wajen ɗakunan masu aiki, inda anan ne suka ɗan sake har Amma ma taga wata ƴar ajinsu ta sakandire a ƴaƴan dattijan da sune manya-manyan masu aikin gidan.
Don haka kwatanta tsoron cewar a wannan karon ita zata maye gurbin wannan kyakkyawar amaryar da aka shigo da ita gidan wajen yamma abu ne da ta tabbata babu wanda zai iya kwatanta shi a duniyar nan.
Tsaya ma tukunna… Ina matar tasa take??
*****
“Baffa ya gaya maka komai ko?”
STORY CONTINUES BELOW
Hajiya Kilishi ta tambaya tana kallon Ma’aruf ɗin dake zaune a gabanta, a cikin falon ɓangarenta suke su biyu sai Surayya dake can wajen dining tana danne-danne a wayarta, yana zaune a kujerar dake kallon Tv yana kokarin canja channel daga ta india zuwa wata channel da ya san a lokacin ana wani Tv show na likitoci mai suna ‘Code Black’.
Sai da ya kai tashar ya karo volume sannan hankalinsa a kwance ba kamar yadda ta zata ba ya juyo ya kalle ta.
“Ya gaya min, and I was surprised har dake Mami.”
Tayi murmushi tana kallonsa daɗi na cika kowanne lungu da saƙo na zuciyarta na ganinsa a gabanta, zata rantse da alƙur’ani ko ya’yan da suka fito daga cikinta basa ƙarasawa inda Ma’aruf ke kaiwa a zuciyarta, matsalar ɗaya ce kawai… duk wani ado da zai ƙawata kusancinsu dole ana kaiwa gabar da za’a yaye cewar shi ba mallakinta bane, kuma tana jin cewa da zata iya samun mai gyara mata hakan babu makawa zata bada komai na duniyarta don kawai a wayi gari duniya ta shaida cewa shi nata ne.
“Baffa ya riga ya gama yanke hukuncinsa shi da Alhaji Baba, daga ƙarshe kawai suka tuntubeni Mai gaskiya kuma ka san ba zan iya cewa Baffa A’a ba, shi yasa sai na bada tawa gudunmawar ta hanyar zaɓo maka yarinyar da na san zata dace da yanayinka. Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma’aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata.”
Wani murmushi yayi kaɗan sannan yace.
“Na dade ina gaya miki kulawarki kaɗai ta ishe ni in rayu Mami, tunda har Rukayya ta kasa bana tunanin akwai wadda zata iya jurewa mess ɗina a duniyar nan kuma.”
Maganganun suka taɓo wani abu a can ƙasan zuciyar Hajiya Kilishi, wani abu da sai da ta ji shi har a ƙarƙashin tafin ƙafarta musamman yadda muryarsa ta fito da wannan amon mai zurfi da kuma sanyi. Kuma sai da ta maida wata ƙaramar ƙwalla a idanunta sannan tace.
“Yanzu dai ka san baza’a fasa ba ko? Don haka zamu fara shirye-shirye, za’a kai musu lefe dole sannan idan kana so ma zaka iya zuwa ka ganta.”
Maimakon ya bata amsa, sai kawai ya juyo ya kalle ta, lumsassun idanunsa suka tsaya a nata.
“Wai zaman me Ishaq yake yi ne ma? Me yasa Baffa baice a haɗa dashi ba?”
“Sai gida ya koshi ake kallon na waje Ma’aruf, kaine damuwar mu a yanzu ba shi ba.”
Kamar bai ji dadin maganar ba, don juyawa yayi yana cigaba da kallonsa ba tare da yace komai ba. Hakan yasa tayi saurin gyara zancen ta.
“Kar ka damu amma, da an gama zancen nan ni da kaina zan saka shi a gaba sai ya motsa.”
Murmushin da ya sake yi ya sata jin wani ɗaci a zuciyarta, ba sau daya ba sau biyu ba tasha tunanin kawar da Ishaq daga hanyarta kamar yadda ta kawar da abubuwa da yawa a rayuwar Ma’aruf, don duk wani abu da zai jawo ya raba zuciyarsa da kowa bayan ita, bata ƙaunarsa sam! Amma matsalar shine Ishaq ba ƙaramin amfani yake mata ba, amfanin da shi ta lissafa har ta bada shawarar dawo dashi wajensu bayan ya rasa iyayensa ba don kyautatawar da duniya ke kallonta dashi ba.6
“Akwati nawa kake so a haɗawa yarinyar?”
Kamar bai damu ba, hankalinsa kwance yace.
“Duk yadda kika yi Mami daidai ne, ni yanzu abinda ke gabana daban harkar Office ce da zanje in gyara, Baffa yace anyi asara da yawa a wannan watan.”
Ba shiri maganar ta doka wata tsawa a cikin kan Hajiya Kilishi tana janyo ta daga ramin da zuciyarta ke shirin kai ta, taji kamar ta miƙe tsaye tana karkaɗe raunin daya baibayeta tun bayan data ɗora idanunta akan Ma’aruf ɗin.
“Shikenan, Allah ya taimaka. Ka taho min da magungunan naka?”
Wata ƴar ƙaramar jakar daya shigo da ita a gefensa ya ɗauko ya miƙa mata ba tare da ya janye idonsa daga Tvn ba, kuma da Ma’aruf ya saurara da kyau, zai ji lokacin da ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta buɗe jakar tana nazarin kayan ciki.
STORY CONTINUES BELOW
A lokacin Samirah ta shigo ɗauke da lemo mai sanyi da kuma cake a faranti, yarinya ce ita mai tsananin kula da son kyautatawa kowa, shi yasa kusan komai na gidan yanzu sai da izininta ake yi, hatta abincin Baffa ta daɗe da karɓar ragamarsa sai dai ko in tana makaranta sai wani a cikin yayyenta yayi, don su Hajiya Kilishi basa girki a gidan. Kuma ko a ɓangaren Hajiya Maimuna akayi baƙi Sameerah ita zata fara tarbarsu da waje da kuma kayan cima kafin kowa, ƙarya ne wani ya shiga gidan nan yace ya fito da yunwa in har tana nan.
“Dan Allah Yaya ka bani kwangilar sati ɗaya in cicciko maka da waɗannan kasusuwan, wallahi baka ga yadda ka rame ba.”
Ta faɗa tana ajiye masa farantin a gabansa. Ma’aruf ya ɗago ya kalle ta yana murmushi lokacin da Hajiya Kilishi ta mike riƙe da jakar magungunan tayi hanyar ɗaki. Kusa dashi ya nuna mata a kujerar yace.
“Zo ki zauna muyi ciniki Please, how much do you need? ( Nawa kike so) coz ƙarfi nake nema nima yanzu.”
Ta kuwa ƙyalƙyale da dariya daidai lokacin da Shukra (ƙanwarsa dake bi masa a wajen Hajiya Maimuna) ta shigo daga hanyar wajensu, kuma ganin Ma’aruf ɗin yasa tayi murmushin dake ƙarawa fuskarta kyau tana fadin ‘Alhmdlilah” sannan ta juya da sauri don ɗebo takardun research ɗin da ta tara zai duba mata.
Don haka Ma’aruf bai samu shiga wajen Hajiya Maimuna ba sai da yamma tayi sosai. Kuma a falo ya same ta itama, tana zaune daga kan Wheelchair ɗinta tana karatun azkar ɗin yamma, yayin da Zahra da kuma Sahla ke zaune suna kallon video ɗin wani tutorial daga labtop ɗin Munaya da suka aro.
Ya durƙusa har kasa a gabanta ya gaishe ta cike da girmamawa, girmamawar da bayan ita baya taɓa kallonta da wani abu.
“Yaya jikin naka?” Muryarta mai taushi ta tambaye shi bayan sun gama gaisuwa.
“Lafiya ƙalau Hajiya, naji sauki ai.”
“Allah ya ƙara sauki. Kaje wajen Inna ne?”
Ya girgiza kansa.
“Yanzu zan shiga idan na fita.”
Tayi shiru yayin da idanunta ke nazarinsa, ya sunkuyar da kansa ƙasa sanye da dogwayen kaya na farin yadin da ko a ido mai laushi ne don ya kwanta a jikinsa sosai ta yadda ya fito da ƙirar jikinsa mai tsari, wani abu dake ɗaya daga cikin abinda ke ƙara masa kwarjini a idon mutane.
A lokacin ne kuna maganar ƴar uwarta a kwanakin baya ta haska a cikin kanta.
‘Ban ce ki tada hankalin gidan ki ba Maimuna, amma abin yayi yawa, kin rasa Jamal kuma Ma’aruf shine Babba a gidan yanzu, ko yaya ne ya kamata ya dinga tunawa cewa ke kika haife shi ba ita ba…’
Tayi saurin kawar da wannan tunanin tana haɗiye wani abu da batasan sunan sa ba, a lokainda ƙwaƙwalwar ta ke tuno mata damagaar da Baffa ya yanke taauresa jiya da daddare, sai dai har ta buɗe baki zata yi masa magana kawai taga ya miƙe tsaye yana yi mata sallama, sai ta mayar da maganarta a hankali sannan ta amsa, kuma murmushin da yayi wa su Zahra a matsayin amsa tasu sallamar ya sake ɗago wani abu a zuciyarta da ta daɗe tana danne shi tsawon shekaru. Idanunta suka bishi da kallon da har ya rufo mata ƙofar falon hankalinta bai koma kan karatun da take yi ba.
A falon Inna Danejo Ma’aruf ya tarad da ita tana sallah daga kan sallayar ta da anan take kwana ta yini in har ba tashi ne ya kamata ba, don haka ƙafafunsa suka tako cikin falon a hankali, yana jin kamar zai nutse a sabon carpet din da aka shimfide mata falon dashi, (wall to wall). Ya karaso ya sami waje daga gefenta ya jingina da wasu ƙullin kayanta da ya san na wanki ne sannan ya zaro wayoyinsa daga aljihu.
Tarin messages ɗin da har yanzu bai duba ba suka shiga tururuwa akan screen ɗinsa, sai ya zura hannunsa ɗaya cikin gashin kansa kawai sannan ya cillar da ita a gefe ya dauko ɗayar.
STORY CONTINUES BELOW
A ciki ya lalubo nambar Faruk, aboki ɗayan da yake dashi bayan Ishaq kuma mataimakinsa a wajen aiki.
“Ka gaya min ba maganar aiki bace dan Allah B, don wallahi as we are talking now ina Coldstone ni da yara, kowa yana son hutu a rayuwarsa Ma’aruf.”
Faruk din ya faɗi hakan tun kafin yace komai, don shi kansa ya sani ba zai iya kirga adadin wayar da suka yi akan zancen Office ɗin ba tun bayan dawowarsa. Sai dai kalmar yaran da ya furta ta daki zuiyarsa da wani irin tasirin da baya taɓa sabawa dashi don haka ba shiri ya tafi kai tsaye ga abinda yake son tambayarsa.
“Account number Daniel zaka turo min.”
“Me zaka yi da ita? Na gaya maka gayen yana can har yanzu da kumburarriyar fuska wallahi.”
Ya cije leɓɓensa a hankali yana hango fuskar Daniel ɗin a idanunsa, sanda ya cakumo wuyansa yana kai masa naushin da baya ƙarewa, kuma duk da zafin dukan nan Daniel baya kare ba ko sau ɗaya, kallonsa kawai yake da idanunsa dake nuna tsantsar mamaki da kuma ruɗani har ya fita daga hayyacinsa.
Ya sake tuno yadda ya jawo shi ya fito dashi har waje ɗimbin jama’ar Office ɗin na kallonsa, da lokacin da ya saka shi a boot din motarsa ya rufe sannan yaja motar zuwa gida, yaje gidan kuma ya fito dashi dashi daga boot ɗin motar ya ja shi har falon Baffa a lokacin ma ya riga ya suma…
Sai kawai ya sake mai da kansa baya, yana motsa ytsunsa cikin gashin kansa a hankali, idonsa ya cigaba da hango masa yadda a lokacin duk da baya cikin hayyacinsa amma nauyin idanun Baffa suka sa ya durƙushe akan gwiwoyinsa sanda ya kai Daniel ɗin har gabansa, amma kuma duk da hakan bai fasa gayawa Baffan cewar wai ya kawo shi ne ne don ya kore shi daga aiki ba…
“Just send it Umar…” (Kawai ka turo min…)
Ya faɗa yana katse tunaninsa kuma bai ƙarasa abinda zai ce ba hayaniyar yaran nan ta shiga kunnensa daga cikin wayar, don haka ba shiri ya katse kiran yana ƙoƙarin ture abinda ke ƙoƙarin tasowa daga ƙasan zuciyarsa.
Ya cillar da ita gefen ɗayar itama sannan ya rufe idanunsa yana cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin nasa daidai lokacin da Inna Danejo ta idar daga sallarta.
“Wai rana kika koma bautawa ko me? Wannan wace irin sallah ce bayan la’asar?”
Inna Danejo ta kalle shi zuciyarta fara ƙal! da farin cikin ganinsa lafiya ƙalau, don a cikin addu’inta na tsukin kwanakin bata jin ko kanta ta ambata a cikin addointa banda fatan nema masa sauki, don haka da guntun murmushi a fuskarta ta kai laziminta na sallamar sallah sannan tace.
“Idan ranar na koma bautawa Muhammadu, iyayenku ai su zasu fara biyo ni kafin ku.”
Murmushi yayi a hankali sannan ya buɗe idanunsa ya juyo ya kalle ta dasu a lumshe.
“Allah yasa da kika dama furar kin rage min, tun da na shigo nake jin ƙamshinta.”
Maimakon ta bashi amsa sai tace.
“Yanzu Allah baza ka ji magana ta ka aske gashin nan ba ko? Ko iska ba ka so kaji tana ratsa ka Muhammadu?”
Ba shiri murmushinsa ya karu.
“Saboda me zan so iska ta ratsa ni? Wadda ke shiga hancina ma ta ishe ni Inna… Ki tashi ki ɗauko min furar dan Allah.”
Ai kuwa kamar ya ziga ta ne akan irin mitar da tayi a duk lokutan da baya nan a gidan, ta faro ta tunda daga farko daki-daki har tana faɗin idan ma ba zaiyi askin ba wai ya tsaya ta wanke masa da sabulun salo ta tabbata ranar sai yayi bacci mai daɗi, murmushinsa kawai yake yi yana jinta tunda dama ya riga ya shiryawa hakan.
A haka har Ishaq ya shigo ya same su, shima aka zuba masa furar sannan ta tasa su a gaba su duka biyun kuma da zancen aure. A lokacin Ishaq ke gaya mata hukuncin da Baffa ya yanke game da Ma’aruf, don haka bayan ta gama hamdala da mitar cewa Baffan bai zo ya same ta ya gaya mata ba, sai faɗan kuma ya koma kan Ishaq shi kaɗai, tana yi tana zayyano masa jikokin ƴanuwanta na ƙauye, kowacce ta faɗo Ishaq sai ya gyada kai yace “Kuma da alamun tana da hankali.”
STORY CONTINUES BELOW
Ma’aruf na jinsu bai ce komai ba, tunani da yawa ke yawo a cikin kansa game da abubuwan dake gabansa, sai dai ko kaɗan babu batun auren nan a cikinsu, don tunaninsa ya gaya masa cewa ko iyayen yarinyar nan mahaukata ne idan ta nuna musu wannan takardar dole ne auren ba zai yiwu ba.
A hankali ya sake rufe idanunsa yana tuno dukkan irin matakan dake rubuce a jikin takardun asibitinsa, Allah ya sani a baya baya taba damuwa da ciwonsa, yana ajiye shi ne a can ƙarshen lissafinsa, amma a yanzu… yanzu bai san me yake ji ba, tsoro ko kuma taraddadin cewa abubuwa zasu iya ƙwace masa kafin ya kai ga cimma manufarsa? A cikin duhun idanun nasa ya hango a inda yake manufar tasa, abinda shi kaɗai ne abu guda a duniyar nan da baya taɓa haɗawa da kowa, ɗakin bincikensa yake hangowa, tunda ya dawo bai buɗe shi ba don haka a yadda ya tafi ya barshi yake hango shi… Yadda yayi kaca-kaca da takardu cikin takaicin da shine linzamin dukan da yayi wa Daniel.
“… Kaga Rabi ma ƴar wajen Baɗɗejo, yarinya ce mai hankali, ga kyau…”
Muryar Inna ta shiga kansa da wani irin tasirin da ya doka a ƙirjinsa, tasirin da yasa ba shiri ya buɗe idanunsa yana kallon Innar da kuma Ishaq din dake cigaba da gyada kai yana shan furarsa, sai dai ba saurarar abinda suka cigaba da cewa yake ba, muryar Inna ta shekaru goma da suka wuce ce ta shiga haskawa a cikinsa, shekaru goma cikin wannan ɗakin.
Kuma bayan muryar sai hoton ma ya canja a idanunsa, yaga yadda tsufan Inna ke raguwa da shekaru goma da yadda komai na ɗakin ke canjawa da abubuwan da suke a mazauninsu a shekaru goman da suka wuce, sannan a lokaci guda Ishaq ɗin ma ya bace, siffar Jamal ta maye gurbinsa yayin da yake zaune a gaban Innar yana dariya.
“Ga Halima ma ƴar gidan Baffayo, yarinya ce mai hankali, ga kyau, ga kyau…”
Ya ga yadda Jamal ke girgiza kansa yana dariya kafin yace.
“Akwai abubuwa da yawa a gabana yanzu Inna, ki ajiye maganar yaran nan… Akwai abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan kafin ma in fuskanci aikina…”
Kuma a lokaci guda ƙwaƙwalwar Ma’aruf ta tsinto kalamai biyu a cikin zancen…
Abubuwan da nake son daidaitawa a cikin gidan nan… Abubuwan da nake son daidaitawa a gidan nan…
Tabbas! Ya akayi bai taɓa tunawa da wannan lokacin ba? Me yasa ƙwaƙwalwarsa bata taɓa hasaso masa wannan ranar ba? Babu shiri idanunsa suka shiga hasko masa tarin abubuwan dake ɓullewa ga wannan maganar, yaji su suna sauka a cikin kansa kamar zubar ruwan da aka tunkuɗo da ƙarfi.
“B, Yaushe zaka fita?”
Muryar Ishaq ta janyo shi daga tunaninsa, sai kawai ya lalubo wayoyinsa a gefe da mukullin motarsa ya mike tsaye.
“Yanzu.” Ya bashi amsa idanunsa na muna tsantsar nazarin abubuwan da shi kaɗai yake hangowa.
Kuma da haka bai jira komai ba yayi waje, yana ji Inna Danejo na ƙokarin tsaida dashi amma bai tsaya ɗin ba, ya fita yana jin tasirin idanun Ishaq da ya biyo da kallo.
A harabar gidan ya gano Munaya tsaye tana waya, duk ta rikice kamar yadda take kullum sai faman gyara glasses ɗinta take alamun bayani ake mata ta cikin wayar, don haka bata ma ganshi ba har ya buɗe motarsa ya jata ya bar cikin gidan, kuma zai iya rantsewa zuciyarsa na lissafa kowanne wucewar lokaci kafin ya isa gida.
A ƙofar gidan ya ajiye motar don ƙwaƙwalwar sa ta gaya masa cewa ba zai iya jira har maigadi ya buɗe masa gate ɗin ba.
Ya shiga har ciki zuwa ɗakinsa, ya buɗe ƙofar da ko waye ya shigo ɗakin zai ce wardrobe ce. A ciki komai yana nan kamar yadda yake hango shi kafin tafiyarsa.
Tebura ne da duruwoyi masu cike da files ɗin takardu da kuma hotuna, ga tarin printers da photocopier a gefe, sannan bayan kayan rubutu akwai allo har kala uku ɗaya na rubutu biyun kuma ya manne su da takardu da kuma hotuna. Ɗaki ne da ko makaho ya shafa zai danganta shi da kalmar binceke balle kuma ga mai ganin da kallo ɗaya da zai yi masa zai bashi amsar da ba sai ya tambaya ba.
A jikin allon nan bayanai ne da kuma hotunan mutanen da Jamal yayi mu’amala dasu tun daga lokacin da ya dawo daga karatu har zuwa ranar mutuwarsa, kuma a jikin kowacce takarda da hoto Ma’aruf ya zana tambarin × da jar marker alamun abinda yake nema bai ɓulle ga wannan hanyar ba, kusan hakan ne ma a jikin kowacce takarda dake barbaje a ɗakin har kuwa da waɗanda aka yayyaga.
A wata durowa daga can ƙarshen ɗakin ya shiga fito da duk takardun cikinta har hannunsa ya kai kan wani file daga can ƙasa.
A cikin file ɗin tarin takardun Jamal ne wanda suka haɗa da duk certificate dinsa na gama makaranta da kuma takardun ɗaukarsa aiki a matsayin sabon ma’aikaci a kamfanin Baffa, takardun ɗaukar aikin ya shiga buɗawa ɗaya bayan ɗaya idanunsa na nazarin komai sai dai har yaje ƙarshensu bai ga komai ɗin da yake nema ba, ya zauna daga tsugunnen da yake, ya sake bin komai dalla-dalla, amma har a lokacin babu komai ɗin.
Hannayensa duka biyu ya cusa cikin gashinsa yana fitar da iska ta hancinsa… Tunani da yawa ke tsere a cikin kansa, yana ji yadda yanayinsa ke ƙoƙarin canjawa, ciwo na harbawa a cikin kansa yana gaya masa cewa zai koma halin da baidade da fitowa ba.
A lokacin ne kuma idanunsa suka hango masa wata ƴar mitsitsiyar takarda da alamun ta faɗo daga cikin file ɗin ne ba tare da ya kula ba, ya miƙa hannu da sauri ya ɗauko ta…
Rubutun Jamal ne, hanwriting ɗin sa…
Mamaki ya kama shi tun kafin yafahimci me aka rubuta, don yasha buɗe file ɗin nan ya zazzage shi amma bai taba ganin takardar ba. Kuma mamakinsa bai karu ba sai da hankalinsa ya gane masa me Jamal ɗin ya rubuta a jiki.
Amina Sulaiman.
Gadon ƙaya.
***
Me kuke tunani ya haɗa marigayi Jamal da Amina?1
Me Hajiya Kilishi ke yi da magungunan Ma’aruf?
Me yasa Ma’aruf baya son hayaniyar yara?1
Me Ma’aruf yake son cimma ne game da bincikensa?5
Waye ya saka kansa a takalmin Amina?😅
Wani mai adaidaita sahu ya shigo layin har zuwa ƙofar wani gida mai baranda, kuma da tsayuwarsa Aminu ya fito daga ciki yana dariya alamun sun daɗe suna hira da saurayin dake jan adaidaita sahun wanda shima ya fito bayan ya kashe mashin ɗin, kuma a tare suka kamo wani buhun shinkafa ƙato guda suka shiga kiciniyar shiga dashi cikin gidan, inda tin daga soro ƴar hayaniyar mutanen ciki zata shaida maka cewar an samu baki fiye da mutanen gidan.+
A tsakar gidan Amma ce tare da ƴanuwanta su uku da suke uwa ɗaya uba ɗaya suke ta kiciniyar hada wasu kayayyaki a cikin kwalaye.
Yayarta mai suna Zahra’u da suke kira da Tanti wadda ke zaune a goron dutse ta kalli Amman da ta fito daga kitchen riƙe da ƙaton tire ɗin data yanko kankana tace.
“Ni kuwa Halima wai yarinyar nan kaya kala nawa ta ɗinka a cikin lefen?”
Amma ta ajiye farantin hannunta a tsakiyarsu kafin tace.
“Ina ga kusan rabi ne, ai tun zuwan su Momi ƴar gidan Kawu Mallam wancan satin suka ɗiba suka kai mata wajen mai ɗinkinsu, har da na fitar bikin.”
Tanti ta gyada kanta tana faɗin.
“Ko da naji, don na lura ita bata da wannan niyyar, a baki kawai Amina ta karɓi zancen auren nan amma banda a al’amuranta wallahi.”
“Kinga ko jiya…” Ɗaya ƙanwar Amman mai suna Ma’u ta shigo zancen.
“… Abinda nake gaya mata kenan, nace tunda dai har ta amsa, ya kamata ta saki ranta tayi komai kamar kowacce amarya a haka ne zancen zai cigaba da rufuwa, komai ya tafi daidai.”
Ɗayar da take ƴar autarsu Safiya tace.
“Ai ce miki zata yi hankalinta a kwance yake, ba irin faɗan da banyi mata ba wancan satin amma ƙiri-ƙiri ce min tayi ita ba abinda ke damunta.”
“Allah ya kyauta, yaya kuka sake yi da ita Hajiya Kilishin? Yaushe za’a fara kai kayan ne? Ya kamata ma aje a ga wajen.”
Aunty Zahra’u ta tambaya tana rufe ƙaton kwalin da ta gama tara ƴan ƙananun kayan kitchen a ciki.
Kuma tambayar ta dawowa da Amma tarin abubuwan da suka faru a cikin wucewar sati uku, yadda ka ranar da taje gidan Tantin a goron dutse, ta hau ta da fada bayan ta shaida mata komai, tace Uba yana da ikon zaɓawa ƴarsa mijin aure don haka ita bata ga aibu a cikin zancen ba, tunda a yadda ta san Baba ta ba zai aurawa ƴarsa mara hankali ba kamar yadda Amman ta kira lamarin.
Don haka babu yadda ta iya dole ta ja bakinta tayi shiru, kuma kamar wasa al’amarin auren ya cigaba gudana bi da bi, a yanzu saura sati guda bikin, an karɓi kuɗin aure hade da lefen da bai wani girgiza su ba kamar yadda take zato a gidan Kawu mallam, sannan har sau biyu Hajiya Kilishi ta kira ta a waya tana shaida mata yadda wasu daga cikin al’amarin bikin zasu kasance a wajensu da kuma cewar gidan da za’a kai Aminan a cikin gidan da suke ne.
Sannan a jiya ta aiko da ɗan aike ya kawo tulin wasu katinan ɗan aure da ba su ko san yadda zasu yi dasu ba, don haka a dole ta karɓi al’amarin itama suka fara shiri sosai, Baba yana ta fafutukar kayan katako da ƴan kudin hannunsa da kuma wanda yayyensa suka haɗa masa, yayin da ita da ƴanuwanta mata ke iya nasu ƙoƙarin na kayan kitchen da kuma sauran na amfanin gida, wanda su Aunty Safiyan ke ta sintirin zuwa kasuwa tun wancan satin.
Sai da al’amarin ya kai duk da irin halin da zuciyoyinsu ke ciki, shirye-shirye a yanzu sun kama kamar dama sunyi tanadin lokacin. Don haka kafin ta bawa Tantin amsa su Aminu suka yi sallama a lokacin suna shigowa da buhun shinkafar nan.
“Yawwa master, nagode sosai…”
Cewar Aminun bayan sun jingine buhun shi da wani saurayi daya kamo masa, saurayin yayi waje yana fadin babu komai yayin d shi kuma ya juyo ya kalli su Amma dake kallonsa suna jiran ba’asin abinda zai ce.
STORY CONTINUES BELOW
“Haba Amma ke ma fa kin san bana sata, Baba ne ya kira ni yanzu naje na karɓo a wajensa.”
Ya faɗa cikin raha yana kallon Amman. Aunty Ma’u tace.
“Na ga ranar da zaka yi al’amarin ka kai tsaye Aminu, in ma satar kake ai kowa ya san ba zaka kawo gida ba.”
“Ameen wallahi…” Cewar Aunty Safiya.
“Amma da ƙyar ne canjawar Aminu, ai hali ZANEN DUTSE ne.”
Ya ƙaraso ciki da dariyarsa yana shirin buɗe babin shafin tsokanar Aunty Safiyan da yafi rainawa, amma tun kafin ya zauna Amma ta katse shi.
“Zaka koma ne?” Ta tambaya.
“Eh yace in ɗebi kati in kai masa.”
Kai tsaye ya bada amsar da a lokaci guda ta shiga kunnen Amina wadda ta fito daga ɗakinsu a lokacin riƙe da tsintsiyar laushin da abin kwashe sharar data ɗebi abinci fal a ciki kasancewar Aunty Safiya da Aunty Ma’un duk sun zo da ƙananun ƴaƴansu, suna ta dabdala a ɗakin.
Riga ce ƴar kanti a jikinta kalar ruwan toka da wani tsohon zanin atamfa da babu mitar da Amma bata yi ba amma ta kasa rabuwa dashi saboda daɗin ɗaurawarsa, sai ta bayar da sabuwar atamfa ma amma shi yana nan, Gashinta mai laushi yana ta fitowa ta saman ɗankwalinta dake zamewa.
Tayi wajen sharar ta zubar lokacin da su Amma suka cigaba da zancensu, Aminu kuma ya dage wai sai sun yi cinikin sabuwar motar Aunty Safiyan da mijinta ya siya mata kwanakin baya kasancewar sa mai hali.
Sai ta juya ta koma ɗakin a lokacin da wata ƴar Aunty Ma’u mai suna Yusra ke janyo kaya daga cikin drawer ta.
“Me kike nema anan Yusrah?”
Yarinyar ta juyo ta kalle ta.
“Hijabi Aunty Amina, Sallah zanyi.”
“To ya zaki yi da hijabina, duka sun fiki tsawo… Kije ɗakin Amma ki ɗauko na Hafsa, me yasa ma baki bi su Hafsa aiken ba?”
Ta faɗa sanin cewar Hafsan da ƴar gidan Tanti da kuma ɗaya yayar Yusran basu daɗe da fita siyan kayan miya ba. Adam ma tunda ya samu sa’ansa ɗan gidan Tanti mai suna Mubarak suka fita filin ball shikenan sai an gansu kuma.
Ta tsugunna tana ƙoƙarin kwashe kayanta bayan fitar Yusran, yayin da hayaniyar ƴan ƙananan yaran da suka ɗane katifar Hafsa suna doki ke shiga kunnenta, tunda satin nan ya kama komai ƙara gaya mata yake yi cewar sauran wasu ƙaiyadaddun kwanaki rayuwarta ta fara daga gaɓar da zata ƙare.
Musamman wannan haɗuwar ta ƴanuwan Amman a gidansu, wani abu ne daban da basu saba ba don Tanti itace babba a cikin su Amman, don haka mafi yawanci a gidanta ake yawan haɗuwa, ko da Sallah kowa can yake tafiya su haɗu har su, shi yasa ganin yadda gidan nasu ya zama wajen haɗuwa yanzu yana ƙara tabbatar mata cewa da gaske komai ke shirin faruwa, gashi Baba ma har ya fara aiko da tanadin abincin biki duk da Amma ta daɗe da kafa layin cewa ba wani taro za’ayi mai yawa ba, ko ƴanuwansu a can Niger tace duk a waya za’a shaida musu kawai, sai dai idan maza zasu zo ɗaurin aure don ya zama shaida a wajensu.
Wani abu ya wuce ta maƙogwaronta lokacin da idonta ya kai kan tulin katinan ɗaurin auren nan, sunayen mutane takwas ne a jiki banda sauran bayanai, amma idan ta kalle shi ba abinda idonta ke gani sai nata sunan dake ƙasan rubutun Ma’aruf Mansur Bakori, sunan da ko sau nawa zata maimaita shi sai ta ji bugawar zuciyarta a cikin allon ƙirjinta.
Ta rufe idanunta ta buɗe tana jin yadda har yanzu zuciyarta ta kasa yarda cewa tana shirin buɗe shafin kaddarata ne da hannayenta. Ba lallai ne ya kashe ta kamar yadda ya rubuto a takardar nan ba ta sani, ya rubuta ne kawai don ya tsoratar da ita, amma hakan ba zai hana ta ɗanɗani gwargwadon azabar da ya tsara mata ba, tunda ta tankwabe gargaɗin da yayi mata.
STORY CONTINUES BELOW
Ta tuno shekaranjiya lokacin da Tanti ke tambayar Amma ‘yaron kuwa yazo?’ sai da ta ƙware da yawunta tsabar yadda tsoron hakan ya shige ta, ita har yanzu bata hango cewar in dai wannan Ma’aruf ɗin da ta sani ne zata ganshi a kusa da ita ma balle ƙaddara ta haɗa su. Gani take yi kamar za’ayi auren ne kawai a kaita wajen Hajiya Kilishin da sunanta ne kaɗai ke yawo a gidansu game da auren. Shi yasa bata fatan kowa ma ya ambace shi, tafi son ayi dukkan abinda za’ayi a kaita ɗin kawai, acan zata tsara matakan da watakila zasu iya siyar mata lokaci kafin dukkan abinda zai faru ya faru har Amma tazo tace.
‘Dama na gaya miki Amina’
Fatima ma tace.
‘Me yasa kika yi tunanin zaki iya Amina?’
Maryam zata dinga da binta da kallo kawai, Aminu kuma zai iya cewa.
‘Ko ba komai kin ƙoƙorta Amina.’
Baba ne kadai zai saka mata albarka ta sani, yayi mata addu’o’in da wataƙila zasu iya gyara rayuwarta a gaba, don ya san tayi komai ne don shi, don tallafar mutuncinsa.
Ta kai ƙarshen tunaninta lokacin da sallamar su Ummi da Momi ta cika tsakar gidansu, taji su suna gaisawa dasu Amma har da muryoyin wasu daban don haka ta rufe wardrobe ɗin ta juyo tana korar yaran zuwa waje. A lokacin Ummi ta ɗage labulen ɗakin ta shigo.
“To amaryar ƙulle, kina nan mu munje mun samawa kanmu mafita..”
Suka shigo suna ajiye ledojin hannayensu yayin da Momy ke cewa.
“Amina ruwa dan Allah, wallahi mun ɗebo rana.”
Da murmushi ta fita zuwa kitchen ta ɗauko jug ɗinsu na roba haɗe da kofinansa ta ɗebo musu ruwa sannan ta dawo.
“Wai daga ina kuke?” Muryarta a hankali ta tambaya tana ajiye musu ruwan.
Ummi ta miƙo mata ledar kusa da ita tace.
“Buɗa ki ga.”
Ta karɓa kuwa ta shiga zaro wasu atamfofi masu kyau kalar ruwan hoda, (pink). Wani abu ya zarce ta maƙogwaronta, tun lokacin da aka kawo kayan lefen nan su Ummi suka san zancen auren, tunda suma sun san Hajiya Kilishin a matsayin ƴar uwarsu kawai dai tafi shiri da Baba ne duk a cikin si Kawu Mallam ɗin, don haka sai rawar ƙafarsu ta ƙaru kamar me sanin cewar bikin irin wanda suke so ne.
“Kowacce dubu ɗaya kenan da ɗari biyar, jikinsu mai kyau ne baza ki taɓa cewa roba bace.”
“Wai na meye?”
Momi tace.
“Har tambaya kike? To anko ne muka fito dashi tunda ke baki da niyya, kin san mu ƴan ayi sha’ani ne babu ta yadda za’ayi muyi biki lami ko amaryar bata so.”
Amina bata ce komai ba, Momi ta sake cewa.
“Ina Fatima? Ga guda ɗaya nan ta Maryam mun siyo sai ta nunawa ƙawayenku ita, wanda yake da hali yayi tunda dai saura ƴan kwanaki, waɗannan kuma ƙawayen mu ne su ma gashi sun siyo tasu.”
Sai a lokacin ta ɗago ta kalli ƙawayen nasu da murmushi a fuskarta tace.
“Allah ya saka da alkhairi, nagode.” Ummi ta kalle ta tace.
“Su da kuɗinsu kike musu godiya? Zo muje ni kiga wani abu.”
Da haka ta ja ta suka fita daga ɗakin, a tsakar gida su Amma duk sun shige can ɗakinta suna cigaba da haɗa kayan dake ciki, sai Aminu kawai dake ta ɗaga yaran nan sama suna dariya.
A ƙofar ɗakin Baffa suka tsaya Ummin tace.
“Amina duk shiru-shirunki na san ba haka halaiyarki take ba, akwai wani abu game da auren nan da kike ɓoye mana, kin sani ni da Momi ƴanuwanki ne kuma sa’aninki da zamu iya jin irin ciwonki, idan akwai matsala ki gaya mana, wallahi in zamu iya zamu taimake ki.”
STORY CONTINUES BELOW
Amina ta haɗiye wani abu, duk kauɗin su Ummi ta sani cewa suna da zuciya mai kyau a can ƙasa, kuma ta sani cewa suna sonta fiye da yawanci daga cikin ƴan uwansu don haka zasu iya taimaka matan da komai, sai dai bata yi tunanin cewa Ummin zata iya ganin damuwarta sama da ɗokin bikin da suke yi ba. Amma duk da haka ta san babu amfani sanin nasu kamar yadda Baba ya shar’anta tun farko, musamman su biyun nan da ta san idan suka ji kamar ta saka lasifika ne a tsakar gidan Kawu mallam ta faɗawa kowa. Don haka sai kawai ta girgiza kanta.
“Wallahi ba wani abu bane Ummi, kin san ban taɓa kawowa kaina aure a yanzu ba ne kawai, kuma sai komai yazo a lokaci guda shi yasa kawai nake jin wani iri.”
Kamar Ummin bata yarda ba, amma bayan ta kalle ta na wasu sakanni sai ta gyaɗa kanta tace.
“To ai shikenan, idan wannan ne da an kai ki sati ɗaya na san zai tafi, don duk da haɗa ku akayi ke bata wasa bace Amina, kuma duk yadda yake jin kansa na san zaki iya dashi….Wai yaushe zamu ganshi ne ma? Ya bamu kuɗin walima…”
Wai me yasa kowa yake son ganin sa? Me yasa kowa yake son jawo shi da baki? Basu san a lisafin tashin hankalinta wannan shi ne a sama ba? Jin bata ce komai ba yasa ta sake cewa.
“Ko da yake da alama kema ba wani ganinsa kike ba, masu kudin nan sai a hankali, amma dai na san zaku haɗu kafin wani satin sai ki karɓo a madadinmu, idan ba haka ba kuma ni zan karɓi lambar wayarsa na tambaya da kaina.”
Jin haka yasa tayi saurin girgiza kanta tace.
“Kar ki damu baza’a kai hakan ba ma.”
Ina zata kai kanta idan har Ummi ta kira shi da wannan zancen? Ai ko a mummunan mafarki ta san wannan rashin sa’a ce babba a rayuwarta. Ummin ta kalle ta sosai.
“Amina auren masu kuɗin nan fa dama ce da kuma rabo, ki saki jikinki ki ci kuɗin gayen nan son ranki, don baki san irinsa ba, ba lallai ne in kin shiga ma ya buɗa miki ba.”
A yanzu ta dawo Ummin data santa, ƙanwar ƴanmatan Kawu mallam me cike da buri, don haka sai kawai ta faɗaɗa murmushin ta tana fadin.
“Toh shikenan.”
Da haka suka koma wajen su Momi, inda suka dasa hira su da ƙawayensu, hirar da taso tafiya da yawan tunanin zuciyarta, don hira suke har da dariyar da har ƙasa suke kaiwa wajen ƙyaƙyata ta, daga baya ta zubo musu abinci a ƙaton faranti suka zagaye shi su bakwai suka cinye tas, a lokacin su Tanti duk sun tafi kuma har Amma ta yaba da atamfar da suka siyo bayan an nuna mata.
Maryam ma ta dawo ita da ƙawayenta da suka tafi gidan wata mata tambayar Beads ɗin da zasu yi amfani dasu a bikin, kuma ganin atamfar murnarta ta ƙaru don tace tayi kalar beads ɗin da ta bayar ayi mata na atamfar da Baba yayi musu na fitar bikin. Kallonta kawai Amina take don ta lura ita mantawa ma take da zancen cewar ba auren da suke so za’ayi ba, don gabadaya ma ta manta da zancen saukarsu da suke ta shiri, yanzu bikin ne a gabanta don ko jiya tana jinta tana takurawa Aminu cewa ya ƙara mata kuɗi zata siyo kayan da zata yiwa ƙawayenta ‘takeaway’.
“Tun safe Fatee, tun ɗazu nake ta kallon hanya, baku dawo da wuri bane?”
Ta faɗa lokacin da Fatima ta shigo gidan da daddare, don tun safe tace mata zasu je bikin ƴaruwarsu.
Sai dai maimakon Fatiman tayi dariya kamar yadda ta zata sai kawai tace.
“Go slow ne wallahi ya rike mu a wajen Gandu.”
Da haka ta juya ta gaishe da Amma dake yankewa Hafsa farce anan tsakar gidan sannan a lokaci guda ta jawo hannun Aminan dake jikin durum tana kokarin ɗiɓan ruwa a buta suka yi soro.
“Amina dama wanda zaki aura da kika ce min ɗanuwanku ne shine wani Ma’aruf Bakori wanda gidansu yake a sharada?”
Sai da gaban Amina ya faɗi duk da bata san me zata ce ba, ta gyada kai tana kallonta da fararen idanunta da ake gani tar a cikin rashin hasken soron.
STORY CONTINUES BELOW
“Eh, baki gani a jikin katin? Me ya faru?”
“Bikin da muka je a sharada ne Amina, kuma a layin gidansu, ƙanwar amaryar ce take gaya min cewa ta san duka ƴan gidan kuma da gaske bashi da hankali.”
Sai ta girgiza kanta.
“Su Baba fa sun gama duk bincikensu Fatee, har ganin sa ma sunyi, sun ce ciwon ba mai yawa bane, sun ce har aiki yake yi a kamfanin babansa, ba wai bashi da hankali bane gabaɗaya.”
Fatima ta girgiza kanta.
“Amina baki san me tace min bane…”
Da sauri ta sunkuyar da kanta sannan ta shiga girgiza shi itama tana faɗin.
“Mutane sun iya yaɗa irin wannan jita-jitar Fatee, ba yau aka fara ba, musamman a sha’anin aure…”
“Yana da wa sunansa Jamal?”
Fatiman ta katse ta, ba shiri ta ɗago ta kalle ta yayin da muryar Baba ta kwanakin baya ke haskawa a cikin kanta, lokacin da Amma ke tambayarsa idan Ma’aruf ƙani ne a wajen wanda suka je bikinsa a shekarun baya.
‘A’a, shine dai wanda kuka je auren nasa, ai ya rabu da matar ne daga baya. Wa ɗaya yake dashi sunansa Jamal kuma ya rasu shekaru goma da suka wuce…’
“Ya rasu shekaru goma da suka wuce ko?” Muryar Fatiman ta tambaya tana karashewa da tunaninta.
“Me ta faɗa miki?” Bata san lokacin da bakinta yayi tambayar ba yayin da zuciyarta da abinda take tunanin ƙasusuwanta ne suka shiga rawa ba tare da kwakwaran dalili ba.
“Shi ya kashe wan nasa Amina! Shi ya kashe Jamal ɗin shekaru goma da suka wuce!”1
****
“Kar ki ɓata min rai Saratu, don me Allah ya halicce ki a mace? Me zaki yi da ƙwaƙwalwar da ake cewa ko shaiɗan na tsoron kaidin da zaki iya fitarwa ta cikinta?”
Muryar Hajiya Kilishi ta faɗa cikin shirun ɗakin yayin da wayarta ke kare a kunne. Ƙawarta da ta kira Saratun tayi ajiyar zuciya a cikin wayar kafin tace.
“Baza ki gane bane Kilishi, ba zaki gane yadda nake gaya miki cewa matar nan ta addabe ni ba, shi yasa naje wajen malamin nan, amma gashi yanzun ma kuɗin da na zuba na neman tafiya a banza.”
Wani murmushi ya suɓuce a fuskar Hajiya Kilishin yayin da fuskarta take fayau! Sai dai a cikin murmushin akwai wani ɓari na sirrin mafi yawan nasarorinta.
“Tsafi gaskiya ne Saratu, amma gaskiyar da bata ɗorewa, kuma na sha gaya miki babu amfanin mallakar abinda ba zai ɗore ba, har wani ƙato a gefe ya isa ya magance miki matsalar da ke kike cikinta?
Sau nawa zan biya miki karatun nan ne? Shekarata talatin a gidan nan kin sani amma babu rana ɗaya da na taba takaws wajen wani malami da sunan taimako. Da yatsa ɗaya nake juya kowa a gidan nan yadda nake so kuma kin san ko ƴanuwana da muke ciki ɗaya su ma basu san wata fuskata bayan wadda Iyalan gidan nan suka sani ba. Shi yasa nake son ki gaya min meye amfanin buɗe miki cikina da nake yi ke da Salamatu? Ba don mu taru akan bigire guda bane? To don me a yanzu zuciya zata ja ki ki kauce?”4
Tambaya ce, amma Hajiya Saratun bata amsa ba, don ta san halin Kilishin sarai, ranta ne ya ɓaci amma har a cikin ɓacin nata halayyar ta kan yi rinjaye a zuciyarta. Don haka tana jinta tayi ajiyar zuciya a cikin shirun sannan tace.
“Yanzu a ina kuka tsaya?”
“Yace ita zai mayar can Egypt ɗin Kilishi, ni uwar garke in zauna in kular masa da ƴaƴa.”
Ta furta hakan tana furzar da wani irin huci da Hajiya Kilishin zata rantse tana jin zafinsa tun daga nan.
“Bi shi a hakan, kar ki sake ki nuna ranki ya ɓaci, kiyi kwalliya ki tausasa muryarki, ki gaya masa zaɓin da yayi daidai ne, ya duba ɗawainiyar yaranki ya taimake ki.
STORY CONTINUES BELOW
Sannan ki faɗaɗa murmushin ki a gabanta itama, ki gaya mata ko da ke ya zaɓa ba zaki bishi ba dama. Bayan haka kiyi mata ɗawainiya a lokacin da zai gani, misali, samu yaji da irin su busashshen tattasai kice tunanin amfaninsu kika yi musu, don kwana biyu ne abincin can zai gundure su. Idan kin aikata hakan, ki kira ni sai mu ɗora.”1
“Kina ganin zan iya Kilishi? Ba kowa Allah ya halittawa irin zuciyarki ba fa?” Muryar Saratun ta tambaya ɗauke da rauni da kuma wani irin tuƙuƙin dake cin ranta.1
Sai ta sake wani guntun murmushin tana miƙewa tsaye kafin tace.
“Zuciyar da Allah ya halitta min nazo duniyar nan daban take da wadda nake da ita yanzu Saratu, ni da kaina na sami wannan zuciyar don haka kema ki tashi ki samarwa kanki abinda zai ɗore. Ki kira ni idan kin gama abinda na gada miki.”
Da haka ta katse wayar tana mai taya kawar tata jin ɗacin dake faruwa a rayuwarta, da ace tana da ikon juya zuciyar Saratu yadda taga dama, tayi rantsuwa a ciki wata daya kacal zata gyara mata komai, ta samar mata fiye da ƴancin da take dashi a wajen mijin nata tun kafin sake aurensa.
Amma zuciya ce kowa da irin tasa duk yadda ka kai ga iyawa, wani a baki kawai zaka bashi labarin dukkan nasararka amma tasa zuciyarsa ba zata taba iya ɗauka ba. Ƙawayenta biyu kenan a duniya Saratu da Salamatu, kuma bayan abotar tasu, tana zana su ne a cikin wasu mutane da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwarta, suka yi mata amfanin da zata rantse ko uwar data kawo ta duniya bata yi mata ba a wajenta, don haka su biyun ne kawai duk duniya kawai take iya buɗewa cikinta su ga ainihin kalolin da take ɗauke dashi bayan farar fatar ta.
Matsalar guda ɗaya ce a wajen kowannensu, zuciyar Saratu bata iya jajircewa abubuwa har tayi yaƙi da iyawarta kamar yadda ita kanta ta furta a yanzu, Salamatu kuma sun sha banban da abinda kowannensu ke wa kallon nasara, don ita yanzu ko aure bata dashi, tafi ganewa yawon kasuwanci ga manyan mutanen da zasu dinga bata kuɗin da suka fi ƙarfin kayan nata.
Ta ja tsaki a hankali tana nufar ƙofar wardrobe ɗin ta, yau ita ke da turakar Baffa, ta gama shiryawa tuntuni wayar Saratun ce ma ta tsaida ita, a cikin wardrobe din ta dauko wata baƙar ledar magani da kuma muƙullin ɓangaren sannan ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe, ta buɗe ta sanda hayaniya ta cika kunnenta, hayaniyar da a yanzu kullum cikinta suke saboda ƙaratowar bikin.
Mutane ne kawai ke zuwa musu Allah sanya alkhairi tun yanzu, musamman daga ɓangaren ƴanuwan su Baffan na can ƙauye, masu kwana ma babu adadinsu don wasu tun wancan satin suka taho ma da zugarsu wai sun zo taya aiki, aikin da kullum sai anyi musu bayanin babu shi.
Don daga harkar jere har harkar abincin da za’aci lokacin bikin da duk wata hidima, kuɗi suka biya a dunƙule wa mutane daban-daban da zasu ɗauki nauyin hakan.
Kamfanika biyu na interior decoration suka biya don su yi jeran gidajen amaren, kawai ƴanuwanta dana Hajiya Maimuna ne ke zuwa su sa ido akan aikin don a hada har da tunanin mata komai ya tafi daidai, don haka su ɗin da suka zo, ba abinda suke ma illa ƙara aikin, don in banda ci su da ƴaƴansu ba abinda suke yini suna yi, dadinta ɗaya kawai basu barwa ma’aikatan gidan komai ba dasu ake girkin da duk wani aikin da ya taso, shi yasa ba wanda ya kai Inna Danejo murna a gidan yanzu ganin duk inda ta juya kawai ƴanuwanta take gani.
Surayya ta fara gani a falon tana danne-danne a wayarta kafin dandazon matan da ke ta fitar da kaya daga kitchen suna yin waje.
Ta wuce Surayyan da bata ko dago ba zuwa tsakiyar falon inda suka fara ganinta.
“Hajiya sannu da fitowa.”
Wajen mutum biyar dake rike da wasu manyan fanteku tun na aurenta suka fada.
“Yawwa, waɗannan kayan fa? Ina za’a kai su?”
“Sameera ce tace a fita dasu waje Hajiya, na aikin cincin ɗin da za’a fara ne.”
STORY CONTINUES BELOW
“Cincin kuma? Ina ita Samiran take?”
Tana tambayar kuwa ta fito ita da wata sa’arta mai suna Khadija da take ƴar ƙanwar Hajiya Kilishin, suka fito suna jan ragowar wani buhun sukari da ya kusan kai kwata.
“Cincin ɗin me ake yi shirin yi a gidan nan Samirah?”
Ta tambaya tana katse dariyar da suke yi ta kasa ɗaukar buhun.
“Mama yara ne ke jin yunwa kafin a sauke abinci musamman da safe, shine nace bari ayi cincin sai ya dinga rage musu hanya.”
Girgiza kanta kawai tayi tana kallonta, kowa da irin ƙaddararsa a rayuwa, ita tata ta abinci ce, don duk da science take yi a makaranta, amma course ɗin da take son yi a University shima ɓangaren girki ne, (Nutrition and dietetics.)
“Allah ya baku sa’a, kafin ku fara ki kawowa Baffa abincinsa yanzu, can zan je.”
Ta faɗa sanda ta juya, a cikin zuciyarta tana lissafin layin da zata saka Samiran daya danganci ra’ayinta nan da shekara guda idan ƙwarya ta fashe!
Sahla ta fito daga ɗakinta a lokacin riƙe da labtop ɗin Munaya tana sake gyara gilasan idonta.
“Mami dan Allah ki bani 1000 muyi subscription, datar da muke streaming ta ƙare kuma Aunty Munaya tace mu kai mata labtop ɗin wallahi ba zata sake siya mana ba.”
“Kije ɗaki, na ajiye wasu canji akan mirror ku ɗauka.”
Ta san ita da Zahra ne don kullum suna manne da juna, shi yasa bata san me zai faru dasu ba nan da shekara ɗayan nan.1
Ta fita daga ɓangaren zuwa harabar gidan kamar wata sarauniya, don duk ɗaukacin mutane kowa tsugunnawa yake yana mata sannu da fitowa yayin take binsu da murmushin da zuciyarta ta wanke shi tsaf, ta tace shi kafin fitowarsa. Kuma ɓangaren Inna Danejo ta fara biyawa ta kai mata maganin cikin ledar nan, na ciwon ƙafa ne wanda Innan tace tana jin daɗinsa saboda haka take sawa ana kawo mata duk wata.
Kuma bayan sun yi ƴar hira da sauran tsofaffin dake wajen da kuma tarin albarkar da Innar ke sanya mata, ta fito zuwa ɓangaren Baffa, kafin ta shiga ta hango Munaya daga gefen ɓangaren tana waya, sai gyara glasses ɗinta take alamun tana sauraren wani abu, kuma fuskarta kaɗai ta kalla ta san a rikice take tunda dama ita ko doguwar magana akayi yanzu zata rikice tace bata gane ba, duk kuwa irin mahaukacin ƙoƙarin da take dashi a ɓangaren karatu, don tun suna yara Jamal ke cewa Ma’aruf da Munaya sune Geniuses (masu kokarin) ɗin gidan.
Zuciyarta ta cunkushe a lokaci guda da ambatar sunan, shekaru goma kenan da shafewarsa a doron ƙasa, amma har yanzu yaƙi barin zukata su huta, don ƙaryane a gidan nan ance an shafe sati guda na kowanne wata ba’a samu wani ya ambace shi ba, hatta ita kuwa tunaninsa na yawan wulga mata a zuciya, ta tabbata da ace Jamal na raye har yanzu to da itace a bayan ƙasa, don ta daɗe da lissafa cewa shi da ita mutane ne da baza su taba rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba.1
Ta zira muƙullin hannunta ta buɗe bangaren ta shiga. Komai yana nan kamar yadda ta sanshi, don dama ɓangaren a suna yake na Baffan amma ita ke da iko da komai na cikinsa, me ta gayawa Saratu ne ɗazu? Babu abinda ƙwaƙwalwar mace baza ta iya ba idan har ta saka kanta, ta tuno shekarun da ranta ke ɓaci idan ta ɗaga labulen ɗakinta ta hango kyakkyawar surar Hajiya Maimuna na shiga ɓangaren Baffan, idan taci kwalliyar nan tata za’a shafe tsawon dare ana musu da wani cewa bata ajiye kamar Ma’aruf balle ma wanda yafi shi a duniya ba, kuma da tayi tunanin cewa bata don ganinta a wajen lokaci yayi da zata bar mata bangaren ita kaɗai, me ya faru yanzu?1
Tayi wani guntun murmushi lokacin da take kunna turaren wuta a jikin burner, a lokacin kuma Samirah ta shigo riƙe da katon tray ɗin dake shaƙe da kayan abincin da ita kadai ta san me ta dafa.
STORY CONTINUES BELOW
Ta ajiye su daga kasa kujerar da ta san nan ne wajen zaman Baffan sannan ta juya.
“Bana jin zan fito sai gobe kuma, kar ki daɗe a waje.”
“To Mami.” Cewar Samiran tana saurin fita, sai dai tana isa bakin kofar Hajiya Kilishin ta sake kiranta.
“Da gaske nake miki magana, kar ki wuce goma a wajen mutanen nan.”
Kuma duk da ta amsa ɗin sai da taga yadda ranta ya ɗan ɓaci kafin ta fita. Dole ne ma ta ƙara dagewa wajen kokarin fara ɓanbare tarin abubuwa daga jikinsu, don komai ya kusa ƙarewa, wannan rayuwar ba dahir ɗinsu bace.
Fitar ta ke da wuya kuwa taji muryoyi daga wajen suna bin layin gaishe da Baffan da ta hango hasken fitilar motarsa da direba ya sauke shi ta labulen falon. Sai ta taho wajen kofar don ta bude, so take ya fara yin tozali da ita da kuma kwalliyarta kafin wani abu ma na ɗakin.
Sai dai kafin ta ƙarasa ɗin wayar hannunta tayi ƙara, ya kalli lambar dake kiran ke shigowa kafin ta dauka, Kuma abin da muryar cikin wayar ta faɗa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ƙirjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faɗi kasa ta tarwatse!
***
Hasken safiyar ya shigo ta tsakanin fararen labulen ɗakin yana ratsowa har ciki zuwa kan gadon da shima komai a jikinsa fari ne, Rukayya ta motsa a cikin baccinta tana ƙara binne kanta a cikin filon amma tasirin wasu dogwayen yatsu dake shiga cikin gashinta suka hana baccin nata cigaba.
“J dan Allah mana..”
Muryarta ta fito a can kasan numfashinta.
Jawad ɗin dake tsugunne a gaban gadon sanye da singlet fara ƙal da kuma wandon gogaggiyar shaddar daya sanya bayan ya fito daga wanka ya sake motsa yatsun nasa cikin gashinta yana matso da fuskarsa kusa da ita.
“Na gaya miki ina da meeting by 10 a Abuja, ko so kike in tafi in barki anan?”
Bata bude idanunta ba tace.
“And what time is it now? (Kuma yanzu karfe nawa?)
“Eight tana dab da ƙarasawa, kamar yadda zuciyata take dab da shirin fashewa akanki.”
Bata san lokacin da tayi dariya ba sannan ta bude idonta akansa.
“Sai yaushe zaka dawo?”
“Sai nayi kwanakin da kika yi Paris.”
Ta juya idanunta tana jin yadda yatsun nasa ke ƙara shiga cikin gashinta.
“Ka san bani da matsala ko zaka ninka kwanakin ne.”
Ya gyada kansa a hankali.
“Na sani Barbie, na san ni zan haukace…”
Sai kuma yayi shiru yana kallon kyawawan idanunta yayin da itama tayi shirun tana sauraren yadda sautin numfashinsa ke fitowa akan fuskarta.
“You never know what I went through da bakya nan Rukayya, zan iya tsayawa a gaban ko waye in faɗa miki ke daban ce.”
Ta lumshe idanuwan nata tana murmushi, tana da tarin hujjojin da zata yarda cewar dukkan maganganun Jawad akanta gaskiya ne, yana ƙaunarta ne da gaske, sai dai maganganun basa taba ƙarasawa har cikin zuciyarta don bata so ya tsallake huruminsa, tafi so ya tsaya a iya matsayin da tsananin kulawarsa gare ta da kuma matsayinsa na ɗan gidan minister da mahaifiyarta ke kwaɗayi yasa ta bashi kawai. Amma akwai wajajen da duk yadda ta kai ga jin sa a zuciyarsa bai isa ya tsallaka ba, Ma’aruf ne kadai mai wannan ikon akanta.
Ta tuna da text ɗin da ta tura masa a jiya ta nambar da aka tabbatar mata tasa ce, wani text layi guda kawai da ta tattara dukkan fatanta a cikinsa tana fatan ya zama silar niyya da kuma ƙudirin da ta gama tsarawa a cikin kanta har ma tayi masa ado da ƙarin wasu kyawawan abubuwan da zuciyar tata ke so.
STORY CONTINUES BELOW
‘M’aruf, Hameeda ta tambaye ka…’
Kuma sai bayan da ta tura ne sannan bangaren ƙwaƙwalwar tata mai hankali ya shiga jero mata kuskure tare da wautar ta, yana gaya mata kamar ba haka ne daidai ba, yana hasko mata tarin yarjejeniyar data yarda da ita a cikin doguwar takardar nan, lokacin da ta yarda tasa hannu akan komai yayin da zuciyarta ke cike da ɗokin rayuwa mai kyau a gaba kamar yadda mahaifiyarta tace, yana gaya mata cewa saboda ta sami saɓanin tunaninta hakan baya nifin cewa ta shirya fuskantar duk waɗannan sharaɗan?
“Jibi zan dawo, ki gaya min zan ƙara samunki dan Allah.”
Muryar Jawad ta jawo ta daga tunanin yayin da yake ƙoƙarin ƙara matsowa. Sai kawai tayi murmushi sannan a lokaci guda ta shammace shi, ta ture shi ta miƙe tsaye tana dariya, yayi ƙoƙarin kamo ta amma ta kauce saboda haka shi ya faɗa kan gadon inda ta taso.
“Zo.”
Ya faɗa daga kwancen yana kallonta, ta matse kafaɗarta ɗaya.
“Zanje in shirya ne kar kayi missing flight dinka.”
“Wani abu zan gaya miki.”
Ta ƙara matse kafaɗarta.
“Ka barshi sai na fito.”
Da haka ta shige banɗakin tana murmushi yayin da Jawad ya dafe kansa da duka hannayen sa biyu yana jin wani abu kamar taraddadi akan abinda ke shirin faruwa.
Allah ya sani da gaske yana sonta, irin son da bai san adadinsa ba kuma bai san lokacin da ya shige shi ba, abinda ya sani kawai shine a matan da yayi mu’amala dasu a rayuwarsa Rukayya daban ce, komai nata daban ne ta yadda tun daga lokacin da ya santa, sanda suka haɗu a airport zuciyarsa ke bin ta kamar raƙumi da akala. Shi yasa a yanzu da iyayensa ke damunsa da maganar aure ya ture duk wani kokwanton zuciyarsa ya tsayar da abu guda, don ya tabbata idan yayi saɓanin hakan zai zama kamar an bar baya ba zani ne.
Saboda haka a lokacin da ta fito take tsaye a gaban mudubi tana shiryawa, sai ya ture komai ya jawo ƙwarin gwiwarsa ya isa kusa da ita ya tsaya daga bayanta. Ta ƙifta masa idonta ɗaya tana murmushi ta cikin mudubin kafin ya kira sunanta.
“Ruƙayya..”
Sai ta juyo ta kalle shi amma yasa hannayensa ya komar da ita gabaɗaya, tana kallonsa ta cikin mudubin shima yana kallonta lokacin da da ya buɗe baki yace.
“Ina so zan aure ki.”
Ga mamakinsa sai kawai ta kalle shi na wasu sakanni ta cikin mudubin sannan ta ƙyalƙyale da dariya.
“Me kace?”
Ya haɗiye wani abu mai zurfi a maƙogwaronsa kafin ya saka hannayensa ya sake juyo da ita yana kallon fuskarsa.
“Wallahi da gaske nake, ina so zan aure ki Rukayya, ki bani dama ko a weekend ɗin nan zan turo iyayena, saboda na fahimci cewa I can’t live without you. (Ba zan iya rayuwa ba sai da ke)”
A lokaci guda ta shiga girgiza kanta yayin da duk wannan rahar ke barin fuskarta, kamar tana karkade ta ne tare da girgizawar kan nata.
“Ba muyi wannan alkawarin ba Jawad, saboda haka don me yasa zaka yi tunaninsa, ofcourse kana burge ni saboda wasu abubuwa a gefe, amma bana sonka, na daɗe ina gaya maka hakan, zuciyata ba taka bace.”
Tana kallon yadda dukkan wani ƙwarin gwiwar da ya tashi dashi a safiyar ke zagwanyewa daga cikin idanunsa, tana kallon yadda yanayin dake cikin idanun nasa ke juyewa zuwa wani abu da ba zata iya fassara shi ba.
“Saboda me?” Yayi tambayar kamar iyakarta zata sa ta canja ra’ayinta.
“I’m sorry J, amma saboda gidan tsohon mijina zan koma kuma na riga na tsayar da zuciyata akan hakan, idan har ba zaka iya rayuwa ba sai da ni, to ni wataƙila munyi tarayya akan hakan,
don nima ba zan iya rayuwa babu Ma’aruf ba Jawad.”
Bata san me yake tunani ba, bata san me yake lissafawa ba, kawai kallonta yake ɗauke da wannan yanayin da, da ace lokacin da ta buɗe ido daga bacci ne ta ganshi a hakan, zata rantse cewar ba shi bane.
Saboda haka tayi baya a hankali ta fita daga cikin hannayensa, kuma sai ƙarar wayarta tazo a daidai wannan lokacin don haka ta isa wajen jakarta dake yashe daga can gefen gadon ta ɗauko wayar, bata ko tsaya tantance lambar dake kiran ba, ta ɗauka ta kara a kunnenta.
Kuma abin da muryar cikin wayar ta faɗa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ƙirjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faɗo kasa ta tarwatse!
***
Ina Ma’aruf yake?
Kuna tunanin saƙon cikin wayar nan ya dangance shi?
Meye gaskiyar labarin Fatima?Mark my words, idan har wani abu ya same ta, babu wanda zan saurara Ishaq, babu wanda zan saurara.”+
Muryar Ma’aruf, ta faɗa a cikin ɗakin asibitin da misalin ƙarfe takwas na wannan daren, yana zaune daga gefen gadon ɗakin da waya kare a kunnensa yayin da daga tsakiyar gadon, wata ƙaramar yarinya ce kwance tana bacci.
Da hannunsa ɗaya ya shafo kansa sannan ya sake cewa.
“Saboda me? Shekaru biyu ta hana ni ganinta amma yau sai na tsince ta a tsakiyar wannan gidan arnan? Idan kana yiwa Allah ka gaya min cewa zan iya maka ta a kotu a hukunta ta.”
Daga cikin wayar Ishaq ya sake cewa.
“Ka taimaka ka fara kwantar da hankalinka yanzu B, ba dai yarinyar tana hannunka ba? ai anci rabin matsalar abinda zai biyo ba mai yawa bane. Sannan na tabbata shi kansa Baffan yanzu idan yaji komai, ba zai sake goyon bayanta ba, mu godewa Allah ma da ba’a dauki shekarun da suka fi haka ba.”
Baice komai ba ya cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin kansa kawai yana sauraren duk bayanin da yake yi kafin wayar tasu ta kai ƙarshe, suka yi sallama bayan Ishaq ɗin ya gaya masa cewa sai jibi zai dawo don aiki ya kaishi wani gari a can hanyar Abuja.
Ma’aruf ya sauke wayar a lokacin da idanunsa suka sake komawa kan yarinyar, Hamida ce… ƴarsa, har yanzu tunaninsa ya kasa gasgatawa, ya kasa yarda cewa ita ɗin ya gani bayan tsawon shekaru rabonsa da ita kuma a wani waje da bai taɓa zato ba.
Tsawon sati uku kenan da ya sadaukar da duk lokacinsa da komai wajen ƙoƙarin daidaita al’amarin da yake faruwa a kamfanin nasu. Wata irin asara suka yi da bata da tushe, bata da reshe kuma babu wani abu da yaja zuwanta. Dawowarsa kawai aka wayi gari da report din ɓatan maƙudan kuɗaɗen da babu ma wanda ya kula dasu sai a lokacin da aka zo fitar da wani kaso na harajin ƙarshen shekara da ake cirewa a duk ƙarshen kowanne wata.
Anyi duk wani bincike amma babu abinda aka tarar daga ƙarshe, don haka Baffa yace a rufe zancen kawai su karɓi hakan a matsayin ƙaddara,. kasuwancinsu ya cigaba da gudana, amma haka kurum sai zuciyarsa taƙi bashi cewa hakan daidai ne, wannan aiki ne da ya riga ya saka ransa akai… Ba yana yinsa don yana sonsa bane yana yinsa ne don ya zame masa dole, dolen da a cikinta ba zai taɓa bari a lissafa da wata tangarɗa ba, don haka ya bi maganar Baffan ya cigaba da gudanar da aikinsa a gefe guda kuma shi da Faruk suna cigaba da bincike akan lamarin.
A cikin binciken nasu Faruk ya samo wani mutum ne a cikin ƙananun ma’aikatan wajen da yace yana yana da wani bayani da zai iya basu, amma bayan Faruk ɗin yaje ya same shi har gida, sai ya ƙi bashi haɗin kai game da hakan duk kuwa yadda yayi dashi. Sun fahimci tsoro ne ya kama shi don haka shi yace zai je ya same shi duk kuwa da magiyar da Faruk ɗin yayi masa akan cewar kar yaje, magiyar da ya riga ya san ta mecece don dukkansu du niyun sun san cewar idan lamarin ya ɓaci babu wanda zai iya kallon Baffan a cikinsu da wani bayani.
Amma shi kansa Faruk ɗin ya san cewa tunda har ya saka ransa babu abinda zai tsaida shi don ba tun yau ya sani cewar idan har ya furta abu zai yi to tabbas zai yi ɗin, bai taɓa ganin ya sa kansa yin abu ya fasa ba.
Don haka kai tsaye bayan ya tashi daga aikin ya nufi unguwar sabongari da address ɗin da Faruk din ya turo masa don ba yadda zai yi. Ya isa da kyar bayan ya haɗa da tambaya sannan kwatancen ya tsayar dashi a daidai kofar gidan mutumin da yake nema.
Sunansa Okafor, wani dattijo ne arne daya dade yana aikin shara a kamfanin, ya san shi tun lokacin da idan sun dawo hutu daga makaranta yake zuwa kamfanin, kuma har sai bayan ya fara aiki ne sannan aka ƙara masa matsayi zuwa aikin hada takardu saboda tsufan da ya kama shi, ya kalli takurarren gidan dake gabansa, mutane ne ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, a ransa ya ayyana cewa idan har Okafor yana da sa’a watakila zaman gidan ya kusa kare masa shi da iyalansa.
STORY CONTINUES BELOW
Wani saurayi da ba ko riga a jikinsa sai gajeren wando da kuma sarƙa ya samu ya raka shi zuwa cikin gidan, kuma duk inda suka wuce juyowa ke an kallonsu da mamaki saboda manyan kayan dake jikinsa, nasa mamkin ya fara ne daga lokacin da suka shiga ciki inda yaga ashe gidan wani irin ƙato ne mai kuma tsawo, ga tarin ƙofofi birjiki daga kowanne gefe sannn da ɗimbin mutanen da ya san zasu iya tashin unguwa guda, ƙaton tsakar gidan ya cika taf da kaya da kuma igiyoyin shanya kota’ina, ga kwata layi-layi dake tashin wari kamar bola aka buɗe, sannan hayaniya kamar zata fasa kunne.
Ba shiri ya haɗiye yawu yana sake damƙe mukullin motar dake hannunsa lokacin da idonsa ya fara arba da tiƙa-tiƙan mata sanye da ƙananan kaya suna ta harkokinsu tare da maza da kuma tulin yaran dake yawo koina, daga can gaba ya hango wasu suna faɗa, mata biyu ne sai ihu-ihu da zage-zage suke cikin yarensu, yaga masu raba su basu da yawa kowa harkarsa kawai yake a wajen.
“Abeg no vex eh, this is Mr. Okafor’s room.” (Kar ka damu dasu kawai, ga ɗakin Mr. Okfor ɗin nan.)
Saurayin nan ya katse shi lokacin da suka tsaya a kofar wani ɗaki mai ɗauke da ragwajajjen ƙofar net. Sai kawai ya gyada kansa sannan cikin nasa kwantaccen turancin yace da saurayin ya fara shiga ya sanar musu zuwansa tukunna, kuma minti guda bayan tshin hayaniyar da ya jiyo a ciki sai saurayin ya fito yace zai iya shiga. Hannunsa ya zaro dubu guda a cikin aljihunsa ya miƙa masa, ai kuwa ya washe baki yana godiya gami da sake buɗa masa ƙofor ɗakin.
Da takalmansa ya shiga amma har a jikinsa yana jin dattin da yake takawa akan baƙin carpet ɗin ɗakin, kuma rashin iska da wari ko ƙansnin wani abinci ya hau kansa a take, amma yayi kokarin dannewa ta hanyar murmushi wa tarin al’ummar ciki dake ta ɗebe kaya don sama masa waje ana faɗin.
“Welcome sir.”
Shi kansa Mr. Okaforn jikinsa rawa yake yi na ganinsa balle kuma tarin ƴaƴan sa da kowannensu ya riga ya zube a ƙasa, kuma cikin gurbataccen turncinsa Mr. okaforn ya shiga faɗin.
“Ban san da kanka zaka zo ba yallabai, ai na cewa yallaɓai Faruk ne ya bari sai na dawo aiki tukunna, matata ce ba lafiya muna ta faman jinyarta.”
Ya fada yana nuna wata tsohuwa dake kwance cikin tarkacen kaya, daga nesa ƙaryane ka banbance ta ma da tarin kayan dake wajen.1
Ya amsa masa bayanin yayin da ya dawo da kallonsa daga kan matar zuwa tarin ƴaƴan da suka zube a gabansa, kusan su tara wanda da kammaninsu kaɗai ya san duka ƴaƴan Mr. Okaforn ne, yaji a ransa yana ƙudirta cewa ya riga ya gama samun bayanin da yake nema don romon da yake shirin kwaɗaitawa Mr.Okaforn wani abu ne da ko mahaukaci ba zai ƙi tayin ba.
Sai dai ɗan adam baya taɓa hango tazarar faruwar wasu al’amuran, don a lokacin da ya buɗe baki zai yi magana ne, a lokacin babbar ƴar Mr. Okaforn ta fito daga wani ɗaki ɗaya tal dake manne da falon, hannunta ɗauke da Hamidan da ta saba a kafadarta a lokaci guda kuma tana ƙoƙarin cusa wasu kaya cikin jakar data ratayo tace.
“Papa, make I run go drop their pikin that woman go eat me alive if she returned.” ( Baba zanje na kai musu ƴarsu, wannan matar zata iya cinye ji idan ta dawo.)
“Mary!” Mr. Okforn ya daka mata tsawar da lokaci guda ta dago da idanunta kuma lokacin gudan itama ta durƙushe kamar ƴanuwanta tana faɗin.
“Welcome sir.”
Ya tuna yadda ta dinga rantsuwa jikinta na rawa tana gaya masa cewa kula da yarinyar take a wajen aikinta ce ta taho da ita saboda an kira ta cewar jikin mahaifiyar tasu ya tashi, idanunsa a rufe ya cigaba da hango ta sanda ta biyo shi har bakin motarsa tana fadin yayi mata rai ya bata yarinyar, kuma ya san cewa sanin da tayi cewa shi shugaban mahaifinta ne, shine kadai abinda yasa bata yi masa ihu ba.
A hankali ya taso, ya dawo daga gefen Hamidan dake baccinta har yanzu, tun a gidan ya fahimci cewa baccin da take yi yayi nauyi, don har yazo ya sanya ta a mota, sau ɗaya ta buɗe idanunta ta koma bata sake farkawa ba, jikinsa ya bashi cewar tabbas hakan da matsala don haka kai tsaye ya wuce da ita wani asibiti mai zaman kansa inda aka karɓeta da gaggawa kafin likitoci su tabbatar cewar maganin bacci aka bata wanda da alamu ma ta daɗe tana yinsa don jikinta babu kwari sam, a take aka bata gado aka shiga ɗura mata drip mai haɗe da ruwan magani.
STORY CONTINUES BELOW
Kuma sai bayan da ya sami kansa ne sannan ya iya kiran Mami ya gaya mata dukkan abinda ya faru, bai san me ya faru lokacin da suna waya ba, amma sai a wayar Samira ta kira shi daga baya ta shaida masa cewa gata nan zuwa ta cikin hayaniyar da yake jiyowa a gidan.
Ya sake gyara zamansa a hankali yana kallon fuskar yarinyar, wani irin abu yake ji yana ratsawa har can bangon zuciyarsa, yana fito da tarin kaunar daya daɗe da binne ta, yawan ƙaunar yana sashi ganin irin ƙoƙarin da yayi a cikin shekaru biyu nayin nisa da yarinyar, yana sa shi alaƙanta abinda yake ji da cewar haka sauran iyaye ke ji idan suka kalli abinda yake gudan jininsu. A hankali ya lumshe idanunsa yana tuno kalaman Rukayya wanda su suka yi sanadin raba shi da ita.
“…bata da lafiya har yanzu Ma’aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zabi dawowarka.”
Kuma ya yarda da maganarta ne a wancan lokacin ba don komai ba sai don nauyin laifin da ya san nasa ne.
Don ranar da ya shaƙe Ruƙayya bayan ya karɓe yarinyar daga hannunta yayi wulli da ita, a wannan ranar ne kanta ya bugu da kujera, har buguwar ta haddasa wani ciwo a ƙwaƙwalwar ta wanda da duk da karancin shekarunta aka fahimci cewa bata iya gane mutane a lokacin, kuma sai likitoci suka bada shawarar cewar a ƙaiyade iya adadin mutanen da zata iya sani a ƙwaƙwalwar tata har sai ta fara wayo tukunna, don haka sanin cewar gidansu cike yake da mutane yasa Baffa ya bada umarnin cewa ko bayan an yaye ta baza su karɓe ta daga hannun Ruƙayyan ba sai tayi wayon da za’a tabbatar ciwon yayi sauƙi tukunna.
Kuma bayan hakan sai Ruƙayyan ta sanya shi cikin wannan lissafin shima, tace.
“Ka taimaka kayi nesa damu Ma’aruf, wannan rayuwar ba itace mafarkina ba, ko kaɗan ba haka nake hango abubuwa ba a lokacin kake gaya min, kuma Allah ya sani na yin dukkan ƙoƙarina wajen gyara maka rayuwar amma ka ƙi barina don ban kasa ba, don haka ina so mu ka barmu mu gyara tamu, Hameeda baƙuwa ce a duniyar nan bata san komai ba, dan Allah kar son zuciyarka ya hana ka bari ta gina tata rayuwar. Allah ya sani ina tsoron kasancewar ta kusa da kai, bata da lafiya har yanzu Ma’aruf, ƙwaƙwalwar ta bata iya gane kowa, ka matsa daga rayuwarmu na wani lokaci, watarana lokacin da kansa zai zaɓi dawowarka.”
Kuma bayan wannan ranar bai sake ganin Hamidan ba, abinda ya sani kawai shine a cikin shekaru biyun ya tura mata isassun kuɗin da ya san sunyi yawa ma wajen kula da yarinyar, kuma a watanni shida da suka wuce sanda aka ce Ruƙayyan zata yi aure ya san cewa sun kai ta wani asibiti a makkah, ba zai iya zuwa ba a lokacin don haka Baffa ya tura Hajiya Kilishi da Shukra da kuma wata ƙanwar Hajiya Maimuna suka je can suka duba ta suka dawo.
Yaji kansa yana ɗaurewa da tsananin mamakin da ya kasa lissafawa, tsawon lokaci… tsawon shekaru an hana shi da yake mahaifinta da kuma ƴanuwansa raɓarta akan dalilin da har iyayensa suka tsaya akansa, don tun su Samirah na naci da ƙorafi akan suna zuwa gidansu Rukayyan ana hana su ganinta har sai da suka daina suka cire ta a ransu, sai gashi yau ya tsince ta a irin wannan gidan, tsakiyar sabon gari zagaye da tarin arnan da bai san adadinsu ba.
A lokacin ƙofar ɗakin ta buɗe, wata Nurse ta shigo da takardar jerin magungunan da za’a siya kafin farkawarta kamar yadda likitan ta shar’anta, da yatsa daya kawai yayi mata nuni da ta ajiye akan drawer dake gefe, kuma budewar kofarta wajen fita yazo daidai da shigowar Hajiya Kilishi da kuma Samira dake bayanta riƙe da kwandon abinci, duk da halin da yake ciki sai da yaji zuciyarsa tayi fatan yarinyar nan tana tuna Allah kamar yadda take tuna abinci.
“Innalillahi wainna ilaihir raji’un, me ya faru mai gaskiya? A ina ka samo ta?”
Muryar Mamin ta faɗa, sai da ya taso ya miƙe sosai sannan ya shiga gaishe ta, ta amsa tana ƙoƙarin riƙe hannun Hamidan da ya saki.
STORY CONTINUES BELOW
Kuma sautin muryarsa a hankali ya shiga yi mata duk bayanin da zai iya a wannan lokacin yayin da take kallonsa da wannan tsananin kulawa da kuma damuwar da kullum ke ɗamfare a fuskarta game dashi.
“Kar damu, komai zai daidaita insha Allah Ma’aruf, daɗin abin komai bai ja da nisa ba, ka kwantar da hankalinka dan Allah mu bi komai a sannu kar ka damu kanka da wani tunani, Baffa ya dawo na shaida masa, shima yayi mamaki sosai amma yace a bari ta fara farfaɗowa tukunna kafin komai ya biyo baya, don haka mu tsaya anan, mu tsaya a iya nan dan Allah mai gaskiya.”
Roƙon da take ya san har da wani bari na muryar Baffa a ciki, don dukkaninsu sun san irin abinda zai iya, don haka bai ce komai ba kawai yayi shiru yana sauraren ta, sauraren da a cikinsa ta fahimci cewa ko ta cigaba da maganar ba fahimtar ta zaiyi a lokacin ba don haka sai tayi shiru kawai ta juya tana kallon fuskar Hamidan.
A lokacin Samirah ta zubo abinci a plate ta miƙo masa, kuma ganin ƙoƙarin ta ne kawai ya gaya masa cewa ya kamata yaci abincin ba wai don yaa so ba, don haka ya karɓa a lokacin da itama ta koma gefe tana kallon fuskar yarinyar.
A cikin tunaninsa yaji Samiran na waya dasu Munaya da kuma amaren da wai dawowarsu kenan daga wajen gyaran jiki suna tambayar sunan asibitin zasu zo, amma Mami ta karɓi wayar tace duk suyi zamansu don in suka ce zasu taho ɗin a yanzu ba’a san adadin wanda zasu biyo su ba kasancewar suna dab da fitowa yanzu ma wasu ƴanuwan Hajiya Maimuna ma suka sauka daga jigawa.
Ma’aruf na jinsu bai ce komai ba, wayarsa kawai yake kallo idanunsa na wasa da adadin messages ɗin dake shigowa bi da bi suna nunawa akan screen ɗin, amma a cikin zuciyarsa tunawa yake da zagayen halin da yake ciki bayan wannan, cewar wannan shirye-shiryen bikin da ake shirin farawa har dashi a lissafin.
Don tun daga lokacin da ya samu wannan takardar mai dauke da sunan Amina, kuma ya tabbatar cewa zancen auren bai lalace ba kamar yadda yayi fata a farko, sai kawai ya mayar da hankali kan aikinsa kuma yawan aikin ke sa shi sha’afa da zancen auren sai wasu abubuwa kamar wannan sun faru da zasu tuna masa cewar shima yana jiran faruwar auren ne don ya fara nasa sabon binciken da har cikin zuciyarsa yake jin cewa wannan hanyar zata iya kaishi ga nasarar da ya shafe shekaru yana lalubenta a cikin duk wani abu da ya danganci kayan Jamal.
Misali irin lokutan da Mamin ke kiransa ta bashi wasu bayanai na cewar an kai kaya gidansu yarinyar ko kuma ya turo da wani adadin kudi za’ayi abu a kaza, abubuwan da suke sa shi yana jin cewa da gaske auren zai yi don Baffa ma ya kafa sharaɗin cewa gidan zai dawo ɓangaren da Baba Alhaji ya taɓa zama, yaje kamar yadda Aa ya marta har sau biyu yaga gyaran da ake yi, amma daga haka bai kara tunawa ba ya cigaba da harkokinsa don damuwarsa ba sai ta komai yayi daidai bane, ta ya iya kammala abinda ke gabansa ne kafin lokacin don ya sami nutsuwar da zai yi dukkan bincikensa akan yarinyar.
Ya cije leɓɓensa a hankali yana tuno kalaman da Faruk ya faɗa masa kwanakin baya.
“Sake yin aurenka shawara ce mai kyau B, amma me yasa sai wannan yarinyar? Kace mahaifinta ba wani bane, kuma kaima ba saninta kayi ba balle ince kana sonta ne, beleive me akwai tarin ƴaƴan masu kuɗin da har layi zasu yi idan kace zaka zaɓa.”
Ya faɗi hakan ne ranar da Baffa yasa aka raba katin ɗaurin auren ga kowa a Office ɗin kuma mamaki ya kama su ganin cewa har da sunansa, don haka Faruk ɗin yayi wannan ƙorafin ne bayan ya shaida masa yadda al’amarin ya kasance. Kuma kallonsa kawai yayi a lokacin da dukkan tunanin da bai zo kansa ba, cewar iyayen yarinyar ba masu arziƙi bane, ya sani cewar maza irinsa basa aure a irin waɗannan gidajen, misali aurensa da Ruƙayya shine daidai, don ko irin manyan mutanen da suka halarci ɗaurin auren nasu daga bangaren mahaifinta ma wani abu ne.
Amma baya jin ko bashi da wani abu da yake nema daga yarinyar hakan zai dame shi, don ba auren ko itace a gabansa ba, kuma kuɗin mahaifinta ba abinda zasu tsinana masa kamar yadda na mahaifin Rukayya ma basu kare shi da komai ba sai abinda yake ganin yanzu har dasu a silar sa. Tuna cewar bai ma taɓa ganinta ba har yanzu yasa ya jinjina kansa a hankali, bai sani ba idan ya kamata a kira wannan al’amarin auren gaske bane wannan.
STORY CONTINUES BELOW
“Ina kika baro masu yin cin-cin ɗin ne da kika biyo ni?”
Yaji Mami na tambayar Samirah bayan ta ajiye wayar, sai dai bai bari ita ɗin ta bata amsa ba ya miƙe tsaye, muryarsa da zurfi yace.
“Zanje in dawo.”
Sai ta girgiza kanta..
“A’a, kaje ka kwanta ka huta kawai, ni zan kwana da ita anan, ka tafi da Samira ka ajiye ta a gida sai ta ɗebo min ƴan kayan kayan da zamu buƙata zuwa, zan kira Malam Sani ya kawo min.”
Ya cije leɓɓensa kaɗan yana bin maganganun nata kafin ya gyaɗa kansa sannan yayi mata sallama ya juya tare da ɗaukar hularsa da ya ajiye daga kan wata drawer a gefe.
Samiran ta biyo bayansa, kuma har ya isa waje jikin motarsa, zuciyarsa na riƙe da yadda muryar Mamin ta fito da tsantsar damuwa da kuma kulawar da ba mai iya ƙiyasta yawanta, a lokuta da yawa yasha ƙiyasta yadda zuciyarta ke iya ɗaukar damuwar tarin mutane da tarin kyautatawa ga duk wani mahuluki da zai shigo hanyarta balle kuma shi da kowa ya sani cewa matsayinsa daban ne a wajenta.
Ya san itace ja gaba akan komai na bikin nan, amma duk da wannan hadaniyar ta tsallake ta zata zauna, bai san irin son da yake yiwa Hajiya Maimuna mahaifiyarsa ba bayan tsananin girmanta da yake gani, amma Mami zai ajiye ta ne gefe ya tara dukkan ƙaunar waninta a wani gefen, don yana daga cikin abinda yasa yake son yayi tsawon rayuwa mai kyau don ya kyautata mata.
A sanda lokaci ke wucewa da wannan tunanin a zuciyarsa, a lokacin Hajiya Kilishi ke girgiza kanta daga cikin ɗakin asibitin bayan fitarsu, zuciyarta na ƙara gaya mata cewar ba haka tsarinta yake ba, ita ke da ikon ƙaiyade duk mutanen da zasu shigo rayuwar Ma’aruf, don haka bata zana cewar abubuwan da ya rasa a baya zasu waiwayo shi nan kusa ba. A tunaninta yadda yarinyar tayi masa nisa haka tayi a zuciyarsa ma, a tunaninta ko zai neme ta sai shekaru sun ja tukunna a lokacin da hakan ba zai shafi tsarinta ba, amma har me tayi a yanzu da duniyarta zata fara girgizawa?
Ta ƙara girgiza nata kan a fili tana cigaba da kallon fuskar Hamidan da kuma yadda ɗan ƙaramin ƙirjinta ke ɗagawa wajen fitar da numfashi mai nauyi, a ɗaya gefen ƙwaƙwalwar ta tana hango idanun Ma’aruf da suka tafi ɗauke da tsananin damuwa da kuma ƙaunar yarinyar dake nunawa ƙarara.
Ta kuma girgiza kanta wannan karon a hankali, ai alƙawari ne cewar ba zata taɓa iya raba zuciyar Ma’aruf tare da kowa ba, sau nawa zata zana cewar shi nata ne ita kaɗai? Ba har da tsoron wannan yasa ta haɗa aurensa da yarinyar data san ba zata taɓa tasiri akansa fiye da ita ba? Ko uwar data haife shi a yanzu ta isa ta raba soyayyar sa tare da ita ne balle kuma wannan sabuwar halittar? Ta ƙara gurgiza kanta, ba lokacinta bane yanzu, ba lokacin da zata shigo rayuwarsu bane yanzu, bata tsara mata waje ba sam.
Numfashin yarinyar har yanzu take kallo tana so ta kai karshen lissafinta… Lissafin da ta fara tun a lokacin da wayarta ta suɓuce daga hannayenta a lokacin da Ma’aruf ɗin ke mata bayanin samun yarinyar. Kuma wucewar wasu sakanni kawai, tunanin nata ya kai kan gaɓar da kwakwalwarta tayi tanadinsa tun a gida…
Gaɓar da take shirin faruwa da zaren wani makamancin tarihin da ta taɓa ja a baya, fuskar Jamal ta haska a cikin kanta a ranar da ya shiga har cikin ɗakinta ya gaya mata cewa bata isa ba, wani murmushin ya suɓuce a fuskarta cike da fatan ruhinsa ya iya ganin yadda lokaci ke bata tarin damar dake ƙaryata kalamansa, tana fatan ace kabarinsa zai buɗe don yaga sabon saƙon da zata aika masa a daren yau wanda zai ƙara ƙaryata kalamansa fiye da cikin masaki.5
Ta miƙe a hankali ta nufi wajen da ta ajiye jakarta, kan teburin da Ma’aruf ya ajiye hularsa, zata yi komai ne hankalinta a kwance don ɗakin asibitin shi zame mata mafaka mai kauri daga duk wani tunanin da zai iya taɓa farinta.
Ta gama tsara hotunan komai a cikin kanta har tayi musu fenti ma, sannan hannunta ya jawo jakar da niyyar buɗe ta….2
***
STORY CONTINUES BELOW
A cikin ɗakin, da misalin ƙarfe goma na safe, Ruƙƙaya ta kalli mahaifiyarta da fararen idanunta dake shaida tashin hankali da kuma fargaba ƙulli-ƙulli, ta girgiza kanta tana share hawaye.
“Wallahi Maamah Hanan ƙawata ce ta haɗa ni da ita, tace ta taɓa yin aiki da wata ƴaruwarta suna da ƙoƙari sosai, shi yasa banyi tunanin komai ba na ɗauke ta a lokacin, kuma itama ta taɓa fada min inda take amma na manta.”
Kukanta ya ƙaru lokacin da ta sake cewa.
“Na shiga uku Maamah, idan na rasa Hamida ya zanyi da rayuwata? Da me Ma’aruf zai sake kallona idan har babu ita?”
Hajiya Nafisa, mahaifiyar Ruƙayya na zaune a cikin ƙaton falon gidan na ƙasa, sanye take da wata doguwar riga irinta larabawan dubai, kanta daure da ƙaramin mayafin rigar yayi da wayarta ke riƙe a hannu.
Idanunta na kallon Ruƙayyan ne da tsananin takaici bayan tashin hankalin da suka tashi dashi na ɓatan Hamida, sai jiya da daddare jirginta ya sauka daga Paris, don haka ko da ta dawo ta hawo samanta bata nemi kowa ba tunda maigidan ma baya ƙasar. Sai a safiyar yau da ta tashi ne sannan ta san Ruƙayya bata gidan saboda haka ta nemi Hamida da mai aikinta Mary amma sai su Jamila da Aisha masu share-share na gidan suka shaida mata cewar ai kwana biyu kenan Mary ta fita da Hamidan kuma bata dawo ba.
Saboda haka kai tsaye ta kira Ruƙayyan ta shaida mata cewar ba’a san inda Hamida da Mary suke ba, kuma wucewar minti talatin sai gata ta ƙaraso cikin tashin hankalin da yafi nata, kuma a zaton ta da tazo kai tsaye zata kira Maryn ko kuma ta bita zuwa address ɗin gidansu ta karɓo yarinyar amma sai gashi tana gaya mata wai lambar Maryn bata shiga kuma ita bata san inda take ba.
Allah ya sani idan har tana da wata matsala a rayuwarta to akan Ruƙayya ne, don babu abinda ta nema ta rasa a duniyar nan illa haɗin kan ƴar tata, ita kaɗai ce mace kuma babba a cikin maza huɗu amma a abubuwa da yawa ta kan gwammace mu’amalarta da mazan akan ita.
Ta sani cewa tun daga lokacin da Ruƙayya ta fara hankali a duniya ta rasa ta, don daga lokacin da ta ɗauki zuciyarta ta danƙa a hannun Ma’aruf shikenan take zaune da ƙirjinta fanko, don bata kara marmarin saka wani a zuciyarta har ta kalle shi da daraja ba kamar shi, tun yana cikakkensa na mutum har ciwon da zata iya kira na hauka yazo ya same shi, haka akayi auren tana murna su suna jiye mata baƙin ciki, kuma ko kafin ta haihu takaici iri-iri sun sha shi, sai da ya juye ƙwaƙwalwar ta tsaf ya goge wannan Ruƙayyan da take a baya, ƴar gayu mai cike da izzar da ko a cikin ƴaƴan manya ake samun masu kwaikwayon ta.
Ya canja mata yarinya zuwa bagidajiya irin matan da basu san komai ba sai zaman aure, ɗaya daga cikin abubuwan da ba zata manta ba shine lokacin aurenta har Lagos tasa aka nemo mata wasu ƙwararrun chefs(masu girki) mata bama maza ba don sanin halin Ma’aruf ɗin, amma wucewar sati guda Ruƙayyan ta bugo mata waya cewa ya sallame su yace shi girkinta yake so, kuma duk ƙin Rukayyan da girki haka ta ajiye ra’ayinta pa gefe ta shiga makarantar koyon girki tsawon watanni don kawai farin cikinsa, abubuwan da ta canja a rayuwarta don Ma’aruf baza su lissafu ba, don a abubuwa ne da ko na nesa zai hango su balle na kusa.
Don haka a lokacin da ta fahimci cewa da gaske tana shirin rasa ƴar tata, a lokacin ta miƙe tsaye tayi wani yunƙuri da bai bawa Rukayyan zaɓin komai ba illa bin umarninta, kuma sa’arta ta zarce har bayan rabuwar tasu ta cigaba da jin maganganunta zuwa yardar da tayi ta auri Alhaji Ahmad, amma zata rantse cewar zamanta baiyi nisa a gidan Alhajin ba fitinanniyar zuciyarta ta sake karkatowa zuwa shafin da take zaton sun barshi kenan har abada wato Ma’aruf, don haka auren bai je koina ba ta fito.
Ƴarta Hamida bata taɓa damunta ba don a tunaninta ita ba tasu bace, da tayi wayo ne mahaifinta zai karɓe ta koma wajensa, don haka bata ko waiwayarta a al’amuranta ta Ruƙayyan take yi. Ashe duk ub*n shirin da suke yi mata ita da ƙawarta akan alaƙarta da yaron nan Jawad a banza suke kashe ƴan kudadensu, ashe har yanzu zuciyarta bata dawo daga inda ta juya ba, Tunani take zata sake komawa wajen wannan yaron da a wajenta kudin da yake dashi ne kawai banbacinsa da wani mahaukacin.
STORY CONTINUES BELOW
Har ta buɗe baki zata yi magana, Ahmad, ƙanin Ruƙayyan dake bin Ashraf (wanda yayi aure) ya hawo saman daga shi sai gajeren wando da riga.
“Wai Maamah ki dawo ƙasar nan baki gaya mana ba. Sai da na shigo wajen 12 maigadi yake ce min ai kin dawo.”
Ya faɗa yana ƙarasowa kusa da ita ya zauna, kuma sai a lokacin idonsa ya kai kan Rukayya dake kuka.
“Me ya faru?” Yayi tambayar ga dukkansu biyu.
Hajiya Nafisa ta nisa sannan ta bashi amsa.
“Hamida ce ba’a gani ba, ita da mai kula da ita.”
“What? Ta yaya? Tun yaushe?”
“Itama bata gidan ai, sai da na dawo tukunna.”
Ransa a ɓace yace.
“Me nake gaya mata a gidan nan Maamah, don me zata dauko wata ƙedara wai ita zata dinga kula da ƴarta, wai don ta iya turanci? Turancin banza su Hausawan ba su iya turancin bane?”
Hajiya Nafisa ta girgiza kanta.
“Ajiye wannan zancen Ahmad tunda komai ya faru, yanzu nemanta ne a gabanmu. Ya za’ayi?”
Kafin ya bada amsa, Ibrahim ya shigo riƙe da wayarsa a hannu yana faɗin.
“Is it true yarinyar nan ta ɓata? Umar just called me now wai ya ganki a waje ɗazu kuna tambayar Hamida.”
Hajiya Nafisa ta gyaɗa kanta don ita yake kallo sanda ya shigo yana tambayar.
“Ƴansanda ɗin dake gadi a bakin titi muka tambaya suka ce mana tun shekaranjiya Maryn ta fita da Hamidan kuma basu dawo ba.”
“Ya salam! This is bad, yanzu me ake ciki?”
Tambayar tasa Ruƙayya sake fashewa da kuka.
Ahmad yace.
“Akwai wani abokin Ashraf da ya taɓa zuwa nan yace min ya san ita mai aikin, ban ɗauko wayata daga ɗaki ba, Ibrahim kira shi.”
Ya kalle shi.
“Wa zan kira?”
“Ashraf ɗin zaka kira kace ya baka number B-man.”
Wayar Hajiya Nafisa tayi kara a lokacin, ta kalli number dake kiran nata, mahaifinsu ne don lokacin da Rukayyan ta dawo tace bata san inda Maryn take ba shi ta kira ta gaya masa halin da ake ciki. Ta ɗauki kiran ta kara a kunnenta, gaya mata yake yi cewa yasa an turo da ƴan sanda gidan zasu zo su nemi bayanai don su kamo Maryn.
Kuma bayan ta sauke wayar kallon Rukayyan ta cigaba da yi a lokacin Amir ɗan autansu ya shigo rike da kofin shayinsa ya zauna a gefenta yana bata hakuri.
Gayawa zuciyarta take yi cewa ba zata sake kuskuren rasa ƴarta ba a karo na biyu, bata son Ma’ruf amma idan har yanzu shine zaɓin Ruƙayya, shi abinda zai daidaita rayuwarta, to zata hakura kawai ta karɓi wannan ƙaddarar, zata dawo mata da Ma’aruf cikin rayuwarta ko ta wace hanya.
***
“Allah yayi miki albarka, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Allah yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin duk wani hakkinki, Allah yasa ku zamewa junaku inuwar salama har a ranar alƙiyama, Allah ya sanya albarka a zuri’ar da zaku samu, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi…”2
Duk wannan addu’ar tana fitowa ne yayin da ruwa ke sauka akan Amina daga bakin wata dattijuwa ƴaruwar Amma mai suna Gwaggo Balkisa da suka zo daga Nijar a lokacin da gidansu Amina ya cika da ɗimbin jama’ar dake shaida Kamu ko kuma wankan amarya da a ƙa’idar zuri’arsu Amma ake yinshi kwanaki kafin ɗaurin aure, al’amarin da yazo musu babu shiri don kwatsam suka samu baƙoncin ƴanuwan Amman tun daga Nijar mutane har motoci biyu.
STORY CONTINUES BELOW
“Bikin ƴarki ta fari guda kice ba sai mun zo ba Halima? Idan kince ku komai yazo muku cikin gaggawa an gaya miki mu yanzu muka fara tanadi ne? Har a aika da katinan ɗaurin aure amma ace wai iya maza ne kawai zasu taho? Yau ko Amina ba ƴarki ta sunna bace kina tunanin zamu ƙi halartar bikinta ko da kuwa tsakaninmu daku nisan bangon duniya ne?
Amina tana tuna yadda Amman ta sunkuyar da kanta tana saurare kafin tayi musu bayanin yadda al’amarin auren yazo, kuma fahimtar al’amarin ya kawo cece-kuce a tsakaninsu, waɗanda suke tsofaffi a ciki basu ga aibin komai ba don sun yarda cewa dama uba ke da ikon bada ƴarsa budurwa zamani ne kawai ya canja komai, amma sauran suma sai tunaninsu ya zama irin na Amma cewar tasirin taimakon da Hajiya Kilishi ke yiwa Baba shi ya rufe idanunsa saboda auren bai kamata ba.
Sai da aka kira Aminan ta tabbatar musu cewa ita ta amsa auren da bakinta sannan kowannensu yayi shiru. Ta faɗi hakan a lokacin da take kallon idanun Amma dake ɗauke da sauran labarin da bata ƙarasa musu ba, sauran labarin da ko ƴanuwan Baban basu sanshi ba, tana jin yadda zuciyarta ke bugu akai-akai cike da fatan kar nauyin kalaman su rinjayi zuciyar Amma a wannan lokacin, amma bata yi maganar ba, bata ce komai ba.
Kuma hakan yana tuna mata da matsayinta na Ammar su, matar da tunda suka taso a rayuwarsu babu wata rana da zasu iya ɗorar da saɓanin cewa faɗa ya shiga tsakaninta da mahaifinsu, kuma ba wai ba’ayi ba, ta tabbata ana yi ma fiye da tarin wasu gidajen auren, kawai babu ƙofar da zasu gane ne. Ta tuna watarana da taji ta tana yiwa Aunty Safiyya nasiha bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninta da mijinta.
“Sirrin mijinki sirrinki ne Safiya, idan kika buɗe kamar kin tonawa kanki asiri ne, ko wa kika budewa littafin da wannan karatun zaiyi ta kallonki koda kuwa kin cigaba da zama ko kuma kin rabu dashi, mafitar matsaloli da yawa a hannunki suke, da wuya ake kaiwa gaɓar da wani ne zai iya magance miki damuwarki…”
Zata lissafa Ammanta cikin manya-manyan jajirtattun mata a gidajensu, zata lissafa ta cikin irin mutanen da mata da yawa ya kamata su kalla suyi koyi dasu, don ita kanta babban makamin da take taƙama dashi na shirin tunakarar sabuwar rayuwar da zata yi, halayen Amman ne.
Sai dai duk yadda ta kai ga dake zuciyarta, a wannan lokacin da Gwaggo Balkisa ke mata wannan addu’ar tana zuba ruwan ɗumi daga saman kanta, kuka take sosai, kuka mai nauyi, kuka mara sauti, kuka da zata iya cewa ya zarce na amare da yawa, don nata kalolin taraddain dake cikinsa basu da adadi, ba na barin gida ne kawai ba, bana shirin fuskantar wata sabuwar rayuwa bane, wataƙila idan tace na shirin mutuwa alhali tana numfashi ne, hakan zai iya fassara rabin abinda take ji.
Tana sanye da wani farin saƙi dasu Gwaggon suka taho dashi, anyi mata ɗaurin ƙirji dashi kawai, yayin da gashinta mai laushi da yawa ke mannewa a fatar kanta da kuma wuyanta saboda ruwan dake bi ta cikinsa, tana zaune akan wani sabon turmi dasu Aunty Safiya suka siyo a cikin kayanta, yayin da sauran jama’ar bikin ke tsaitsaye zagaye da, gidan ya cika danƙam don har ƴan unguwa sun shishigo.
Taga lokacin da Tanti ta shigo cikin masu zuba ruwan ta ɗebo nata itama tana kwara mata tare da nata addu’oin dake ƙara karya zuciyarta suna saka kukanta ƙaruwa. A lokacin ne kuma fuskar Ma’aruf ta haska Idanunta, ranar da ta fara ganinsa, ranar da ta taɓa ganinsa, yana dariya a tsakanin mutanen dake taya shi murnar aurensa, babu shiri wani kukan mai ƙarfi ya sake suɓucewa a bakinta.
A haka sai da duk wani babba na danginsu da kuma dangin Baba suka zo suka yi sannan aka rufa mata wani farin saƙin, aka lulluɓeta dashi har ƙasa sannan kuma sauran ƴanuwan Amman da basu kai irinsu Gwaggo Balkisa ba suka shiga fesa mata turare ana guɗa. Al’ada ce sabuwa ga duk wanda ya halarci wajen, irin dangin Baba da kuma sauran ƴan unguwa don haka abin ya birge kuma ya ƙayatar ga duk wanda ya gani, kuma duk da cewar ba wani abinci aka raba ba, amma kowa ya tafi yana yaba abinda akayi.
STORY CONTINUES BELOW
“Na gaya miki su Nusaiba duk cewa suka yi baza su zo ba wai tunda ba ke kika fada musu ba, ba’a gaiyace su ba kenan.”
Fatima ta faɗa da daddare bayan an gama komai mutanen duk sun tafi, wadanda suka rage iya na cikin gidan ne kawai.
“To ba shikenan ba, su sha zamansu. Dasu da masu karyatawa suna cewa karyane duk su ƙarata can, ranar da suka zo nemanki akace musu kina gidanki sai su san cewar da gaske ne.”
Ummi ta faɗa tana kallon Aminar wadda a yanzu ta canja zuwa wata doguwar riga daga cikin ɗinkin kayan sallarta, har yanzu bata fara amfani da kayan lefen nan ba duk kuwa da an karbo daga dinki, gani take kawai kamar basu gama tabbata nata ba har yanzu.
Dukkaninsu suna zaune ne a cikin dakinsu tare da ƙawayen su Ummin da kuma ƙawayen Amina da basu fi biyar ba, don kamar yadda Ummin ta faɗa ne da yawansu da Fatima ta gaya musu cewa suka yi ƙarya ne basu yarda ba.
Amina bata ce komai ba saurarensu kawai take yayin da take riƙe da ƙaramar ƴar Aunty Safiyya da tayi bacci a cinyarta, daga tsakar gida hayaniya ce kawai ke tashi cikin hausa da kuma zabarmanci daga ƴanuwan Amma, ƴaƴan Baban kurn dana Kawu Malam da kuma yayyensu Ummi duk suna nan, tabarmarsu daban ana ta hirar yaushe gamo, don ma ƴaƴan su Kawu Ibrahim dana Kawu Hamza basu ƙaraso daga Abuja bane, wanda su dama ba sa’anninsu bane, su hudu ne duk sunyi aure a can Abujan ɗaya ce kawai a Kaduna, don haka ko zasu zo tabbas sai ana i gobe ɗaurin auren ne tare da iyayensu, Kawu Hamza ne kawai yake da ƴa sa’ar su Aminar amma tana Ghana ta samu scholarship tana karatu.
Amina ta sani cewar ƴanuwan mahaifinta suna da arziƙin da tun lokacin da ta gama karatu zasu iya daukar nauyin cigabanta, amma basu yi ɗin ba, don duk yadda zumuncinsu yake da karfi akwai raunin taimako a tsakaninsu, kowa yafi maida hankali kan iyalansa kawai, kuma Baba mutum ne mai son dogaro da kansa a komai shi yasa shima bai cika tambayarsu abu ba idan har ba wanda hannunsu ya miƙo masa ba.
Ta lumshe idanunta tana sauraren hirar dasu Fatima ke yi a gefenta, Baba bai ƙara yi mata maganar auren ba har yau tun daga ranar da ta shaida masa amincewarta, amma a kodayaushe ta kalli fuskarsa sai taji ƙarfin gwiwarta na ƙaruwa, taji zata iya yin abinda yafi wannan ma idan har zai umarce ta. A hankali maganganun da ta gayawa Fatima ranar da tazo mata da labarin Ma’aruf suka shiga dawowa kunnenta.
“Fatima, Baba yasha wahala akanmu a rayuwarsa, yaga tashin hankalin da ba zan iya lissafa miki ba duk saboda mu. Lokacin da nake shekara hudu, Amma tayi fama da wata irin rashin lafiya bayan haihuwar Aminu, Baba shi yayi ɗawainiyar konai damu har tsawon shekara guda kafin ta warware. Lokacin da ina aji ɗaya a sakandire nayi wata rashin lafiyar ciwon ƙafafu har bana iya tafiya, wani abokinsa ya kwantanta masa wajen wani mai magani a garin Benue, ni dashi kawai muka tafi, daren farko a hanya mota ta lalace mana gashi motocin dake wucewa basa tsayawa saboda gudun ƴan fashi, a bayansa ya goya ni Fatima, muka dinga bi ta daji tare da sauran mutanen motar har washegari kafin Allah ya taimaka mu isa wani ƙauye.
Lokacin da zanyi jarabawar shiga sakandire, Baba ya sadaukar da lokacinsa da komai wajen koya min karatu ba dare ba rana, idan ya dawo daga kasuwa yana gyangyadi yana hamma zamu yi karatun nan, ranar da sakamakon jarabawar ya fito kuma naci, ranar na fara ganin hawaye a idanun Baffa, hawayen farin ciki.
Sanda Maryam bata da lafiya kuma karayar arziƙi ta same shi, kin sani Fatima, kin san yadda Baba ya koma kamar mai roƙo yana bi kusufa-kusafa don tara adadin kudin da ake buƙata. Kullum so yake mu girma, mu zama wasu mutane da al’umma zasu amfana suyi alfahari dasu, don haka ba lallai ne mu hango fa’idar wannan hukuncin nasa a yanzu ba, amma na tabbatar miki Baba ba zai yarda da zancen auren ne haka kawai ba, yace ya amsa musu ne saboda nauyin idanunsu da yaji, amma ni na sani cewar akwai wani abu daban da yasa ya amsa wanda ba lallai ne dukkanmu mu fahimce shi yanzu ba.
Kema na yarda da maganarki kamar yadda na yarda da ta Amma, sai dai bana jin zuciyata zata dauki taku sama da tasa, don ban san wane irin butulci zanyi ba idan har na kunyata mahaifina a idon duniya, gwara ko meye ya same ni da inyi sanadin hakan.”
Kuma tun daga lokacin, shikenan ta kashe bakin Fatiman, bata kara cewa komai ba, bata ƙara ƙalubalantar ta da komai ba, ta fauwalawa ubangiji al’amarin kamar yadda itama tayi, har ta saki jikinta cikin su Ummi itama ta siya atamfar nan ta kai ɗinki.
“Gobe zanje in karbo ɗinkina, kuma zamu je ni da Maryam wajen masu sarƙar nan mu ƙara yi musu tuni.”
Fatiman ta faɗa tana katse tunaninta. Sai ta gyada kai kawai sannan tace.
“Ɗazu Maryam take gaya min, wai ta samo me zuwa ta mana ƙunshi ma.”
“Ƙunshi a ina? Me zuwa gidan ce zata miki? Ai kar ma ku fara wannan zancen, kuɗi zaki karɓo zoo road zamu tafi jibi-jibin nan, idan aka gyara miki gashin nan naki da hannayenki, ba wanda za’a sake yiwa bayanin cewa ke amarya ce.”
Ummi ta faɗa, kuma tana ƙarashewa wata ƙawarsu ma ta ɗauka da faɗin.
“Ni wallahi naga ta kara haske ma akan ranar da muka zo daga kasuwa.”
“To kina raba amare da gyare-gyaren jiki ne? Kawai ki tambaye ta sirrin tunda kema kin kusa fara naki.”
Momi ta faɗa suna ƙyalƙyalewa da dariya, Amina kuwa ta haɗiye yawu, don ita bata san wani abu gyaran jiki ba, vasiline ɗin da take shafawa kullum shine dai, robar ko ƙarewa bata yi ba balle ta canja ko kuma ta waiwayi mayukan cikin lefen nan, abinda ta sani kawai shine idan har da gaske tayi fari to kuwa tabbas na tsora ne.
Don Allah ya sani idanunsa kaɗai idan ta tuno zuciyarta na bugawa da sautin dake barazanar saka ta kuka duk da ƙwarin gwiwar da take ji, tsoron daban ne don bata san me shi da kuma zuciyarsa suka tanadar mata ba… Ta rufe nata idanun a hankali tana jiyo hayaniyar su Aunty da Aminu daga waje akan motar da zata fara ɗaukan kaya, don gobe Tanti tace ya kamata a fara jere.
Tsoro take ji da gaske,
Tana ji kamar tana faɗowa ne daga wata sama mai nisa, kamar tana tafiya cikin idanun nasa inda ruwan cikinsu zai nutsar da ita da kuma numfashinta.
Abinda bata sani ba shine har yanzu a gaɓa take, bata shiga koina ba ma balle ta fara nutsewar!