FARAR WUTA CHAPTER 4 BY AISHA MAHMOOD
FARAR WUTA CHAPTER 4 BY AISHA MAHMOOD
Ɗimbin jama’ar dake yin tururuwa suna ƙara cika kowanne ɓangare na cikin masallacin su suka shaida auren mutum takwas ɗin da aka ɗaura kowanne kan sadaki mabanbanci, motoci kawai kake gani daga koina an ajiye su yayin da wasu ke ƙara shigowa suna daɗa adadinsu. Jama’a kuwa babu wanda ya san adadinsu sai ubangijin daya tara su gurin, dattijai da samari har ma da yara masu tasowa, gasu nan kala-kala kowanne ango da ƙungiyarsa da sai faman gaisawa ake ana ɗaukar hoto.
Daga can gefe, Kawu Ibrahim ya ƙaraso inda tasu tawagar ƴanuwan take, ya tsaya a kusa da Kawu Hamza yana girgiza kansa.
“Ka san yaron nan har yanzu bai iso ba.”
“Ai ba zuwa zaiyi ba, gwara mu ma mu hanzarta mu bar wajen nan don ni jirgi na na ƙarfe uku ne ma, kuma akwai abubuwan da zanyi kafin nan.”
Kawu Ibrahim ya juya ya hango su Kawu Mallam dake tsakiyar mutanen yana gaisawa da sauran ƴanuwansu fuskarsa cike da irin kalar tasa murnan, sai kawai ya juyo da kansa yace.
“Har yanzu na kasa gano dabararsu akan auren nan, babu wani abu dake nuna min cewa ba don saboda kudin mutanen nan komai ya faru ba.”
“Koma meye dalilin nasu, a yanzu komai ya riga ya faru, kuma duk matsalar data faru daga yanzu kuma na tabbata shi ɗin yana da hannun ɗaukarta.”
Kawu Ibrahim ya girgiza kansa.
“Muyi fatan alkhairi kawai, don har cikin zuciyata ina tausayin yarinyar nan, Amina tana da hankali wallahi.”
“Hankalin da bai kamata ace an ƙuntata rayuwarta tun daga yanzu ba. Ai wallahi da nine da ikon Kawu mallam, auren nan ba zai taɓa faruwa ba.”
Kafin Hamzan ya sake magana wayarsa tayi kara don haka ya dauka yayi gefe yana ƙoƙarin amsawa. Kuma sai a lokacin idanun Ibrahim suka iya hango masa Baba (mahaifin Amina) yana daga tsakiyar mutanensa sai faman gaisawa yake dasu fuskarsa ɗauke da ɗimbin fara’ar da ya kasa auna nauyinta dana kuɗin sadakin auren dake cikin aljihunsa, dubu ɗari cif!
A cikin ƙwaƙwalwar sa lissafi yake cewar ko da kudin zasu iya ninka adadinsu sau goma baya jin zai taɓa iya bada ƴarsa aure ga mutumin da akace yana da matsalar ƙwaƙwalwa, tunda gashi tun a yanzu sun fara gani, in ba haka ba wane ango ne yake ƙin halartar wajen ɗaurin aurensa?
***
Motar ta shigo kamfanin da saurin da ya saka maigadin da ya buɗe gate ɗin juyowa yana kallonta, kuma duk saurin nata sai da ta isa ga layin da ake ajiyar motoci ta tsaya sannan ƙofar mazaunin direba ta buɗe.
Ishaq ya fito sanye da wasu kaya kalar sararin sama, wayoyinsa rike a hannu ya rufe ƙofar sannan ya tunkari cikin ginin dake kallo shi, wani gini mai hawa uku da yasha adon gilasai tun daga samansa har ƙasa. Security ɗin daya bude masa ƙofa har sunkuyawa yayi bayan ya gane shi yana fadin.
“Yallaɓai sannu da zuwa.”
Kuma maimakon ya amsa sai kawai ya tambaye shi.
“Ma’aruf yana ciki ko?”
“Eh tabbas, ai tun safe ya iso yallabai”
Jin haka yasa Ishaq ɗin yin gaba zuwa hanyar matattakalar da zata kaishi sama, wata receiptionist (mai karbar baki) a wajen mai suna Rafi’at ta shiga gaishe shi tana murmushin da ke manne cikin tsarin ayyukanta, kuma da mamakin yadda akayi bata manta fuskarsa ba duk da karancin zuwansa wajen ya ɗaga mata hannu yana zarcewa zuwa saman.
A hawa na farko can ƙarashe ofishin Ma’aruf ɗin yake, don yana tuna lokacin da yake gaya masa cewa ya canja office, ya isa ƙofar daidai lokacin da sakatariyar Ma’aruf ɗin mai suna Martha ke fitowa riƙe da wasu files a hannunsa.
STORY CONTINUES BELOW
“Sannu da zuwa yallabai, yana tare da wasu baki ne a ciki, ko zaka jira su kammala.”
Martha ta fada da murmushin dake nuna masa da gaske take, kuma ya san lallai baƙin masu muhimmanci ne don babu ta yadda za’ayi ta tsaida shi idan ha haka ba.
Gyada kansa kawai yayi alamar ya fahimta sannan ya ƙarasa kofar ya buɗe ta, idonsa ya gane masa wasu inyamurai biyu da kuma wani ɗan china, dukkansu suna zaune a kujerun dake tsallaken teburin Ma’aruf ɗin, kuma budewar kofar tasa dukkaninsu suka juyo suka kalle shi, Ma’aruf na sanye da wani bakin yadi mai sealed ɗinkin da ya fito da tsarin jikinsa, hular kansa ma baka ce data dace da shigar da ita kadai ya kamata ta tabbatarwa da Ishaq cewar abinda yake tunani tabbas haka ne, dama baiyi niyyar zuwa wajen daurin auren ba.
“Bismillah, ka shigo mana.”
Ma’aruf ɗin ya faɗa yana kallonsa, sannan a lokaci guda ya maida kansa kan takardar dake gabansa yana ƙarasa rubutun da yake yi, ya kuwa karaso cikin daidai lokacin da ya rufe takardun ya miƙowa mutanen tare da murumushin daya dace da fuskarsa.
Ɗaya daga cikin inyamuran ne ya karba tare da yin godiya kafin dukkanninsu suka mike a lokaci guda, Ma’aruf ɗin ma ya mike yana miƙa musu hannu, ɗaya bayan ɗaya suka gaisa kowanne da murmushi yayin da yake sake yi musu alkawarin cewar kar suji komai, suyi aikin da zasu yi kawai babu abinda zai gifta a tsarinsu.
Kuma watakila yanayin fuskar Ishaq ɗin suka kalla don babu wanda yayi masa magana a cikinsu suka yi hanyar kofar suka fita.
“Wanne za’a kawo? Tea ko Coffee”
Muryar Ma’aruf ɗin tasa hankalinsa dawowa daga rakiyar da yayiwa mutanen nan, ya juyo ya kalle shi.
“Kaima ka san ba abinda ya kawo ni ba kenan.”
“Na sani…” Ma’aruf ya faɗa yana komawa kan kujerarsa.
“Shi yasa na tambaye ka hakan ai, don idan ka fara muryarka zata fi fitowa idan da abu mai zafi a kusa.”
Sai kawai ya girgiza kansa, yace.
“Wane irin rashin mutunci ne wannan B? Ya za’ayi ranar da za’a ɗaura maka aure guda ka taho Office? Ka san tarin mutanen da suka neme ka a wajen nan?”
“Really? Ai da ka sani kawai su biyo bayanka ku same ni anan sai su ganni.”
Wani irin abu ya sake tasowa Ishaq, sai kawai ya karaso gaban teburin nasa ya zube wayoyinsa sannan ya kalle shi sosai yace.
“Abinda kake yi ba daidai bane Ma’aruf, me yasa ko sau ɗaya a rayuwarka ba zaka yi abu irin na mutane ba? Ka nuna baka son auren nan da farko, daga baya kazo ka nuna ka yarda saboda Baffa, to idan haka ne me yasa zaka kunyata shi a yau? Me yasa baka je wajen ba alhali ka san rashin zuwan naka zai iya haifar da wani abu?”
“Me zai haifar?” Ya tambaya alamun hankalinsa a kwance, kafin ya cigaba.
“Zai haifar da rashin faruwar auren ne? Kana tunanin akwai abinda zai saka Baffa ya canja maganarsa? Na gaya maka na yarda da auren ne saboda naga ba zan iya karewa ba, naga babu abinda zanyi wanda zai canja ra’ayinsa, yanzu ka gaya min da ban je ba ya fasa ɗaurawa?”
Ishaq yayi shiru kawai yana kallonsa, sautin numfashinsa na fita da yawan da ya zarce daidai, don akan fuskar Ma’aruf din yake gane cewa abinda ya fada ba haka bane, dole akwai wani dalili daban da yake dashi game da auren nan, saboda abinda ya faɗa da farko gaskiya ne.
Su biyun sun sani cewar wannan auren ba ƙaramin haɗari bane, abu ne da bai kamata ya faru ba, don haka ba saboda Baffa ya ture hakan ba ya sani, shi yasa babban tsoronsa shine abinda zai iya yi, don shi shaida ne akan tarin abubuwan da suka faru a baya, abubuwan da basa furtawa har yanzu balle na ukunsu ya sani, abubuwan da ba wai sunyi shawarar ɓoyewa bane kawai akwai su ne amma kamar babu su ɗin.
STORY CONTINUES BELOW
Ya haɗiye wani abu a ƙirjinsa yana jin yadda shakka da kuma tsoron abinda Ma’aruf din zai iya ke bin koina a jikinsa, bai san yarinyar nan ba, bai taɓa ganinta ba amma yana tausayinta tun yanzu, don ya san wani rauninta a rayuwa aka kalla aka haɗa wannan auren, tunda a bayyane yake ga kowa cewar ba kowanne uba ne zai iya ɗaukan ƴarsa ya bawa mutum irin Ma’aruf ba, kamar babu banbanci ne da ka tura ƴar taka cikin dokar dajin da babu ranar fitowa.
Sai kawai ya zaro wallet ɗinsa daga aljihu, kuma har a lokacin Ma’aruf ɗin na kallonsa da nasa idanun dake danne tarin abubuwan da yake dannewa, a cikin wallet din Ishaq ya zaro ID Card ɗinsa ya nuno masa shi, kuma da ganin haka Ma’aruf ya san me yake nufi, ya san cewa da gaske ransa ya ɓaci, don rana ta ƙarshe da ya fito da ID card ɗinsa yana tuna masa cewa shi lawyer ne zai iya ɗora aikinsa sama da alaƙarsu shine ranar da aka kai Baffa asibiti saboda ciwon zuciyarsa da ya tashi ta dalilinsa.
“Ban san me kake shiryawa ba Ma’aruf, amma na yarda cewa ba ka yarda da auren nan saboda Baffa ba, akwai wani abu da kake ɓoye min…”
“Jamal ya san yarinyar.”
A lokaci guda muryar Ma’aruf ɗin ta katse shi yana kallonsa.
“Me kace?” Ya tambaya idanunsa na shaida rashin ganewar.
Ma’aruf ya gyara zamansa, ya ƙifta idanunsa yana kallon Ishaq ɗin sannan ya sake maimaitawa.
“Jamal ya san yarinyar Ishaq, so nake na san yadda akayi Jamal ya san yarinyar, wataƙila hakan zai iya bani damar da zan iya gano mutanen da suka sa na kashe shi!”1
Ya rufe bakinsa daidai lokacin da Faruk ya shigo Office ɗin yasha adon wasu fararen kaya har da babar rigar, bakinsa a buɗe yace.
“Wai da gaske baka je ɗaurin auren ba?”
****
Kayan jikin Amina wani farin Lace ne wanda aka ɗinka daga cikin kayan lefen, ta yafa farin mayafin da shima a cikin kayan yake, hannayenta sun sha ƙunshin da suka je har zoo road tare dasu Ummi suka yini ana yi, ɗaurin ɗankwalin da Momi tayi mata yayi baya da yawa ta yadda hakan ya fito da gashinta ta gaba, akwai fararen awarwaro a hannyenta har da wani zobe mai kyalli ma.
Babu ko kwalli a idanunta amma ita kanta ta sani cewa kamanninta ba ɗaya suke da sauran ranaku ba, watakila suna da kuma matsayin aure yana zuwa ne da tasirin dake banbanta kowacce amarya da sauran fuskoki, don ita kanta ta sani cewar fuskarta tayi wani irin fresh da kuma kyan da kowa ke gani tare da fararen idanunta, fatar fuskarta har maiƙo take saboda yadda take tas babu ko ɗigon ƙananun ƙurajen da ta saba fama dasu.
“Fatee, ina gurasar? Jiranki fa muke yi!”
Wata Shukra ɗaya daga cikin kawayenta a islamiyya ta kwallawa Fatiman dake can cikin hayaniyar tsakar gida kira, a cikin ɗakin nasu ƴanmata me fal da suka haɗa da kusan duka ƙawayen su na islamiyya da kuma na makarantar boko wanda duk a ƙoƙarin Fatima ne ta tattaro su, sannan ga su Ummi ma da tasu tawagar ƙawayen, don haka ɗakin ya cika taf sai faman hayaniya suke wadda ke sajewa cikin tarin ta gidan gaba ɗaya.
Don ko’ina a cike yake taf da mutane sai faman rabon abinci kawai ake, babu wanda yayi tunanin za’ayi wannan taron, Amma bata taba lissafa cewa yawan waɗannan mutanen zasu taru ba, amma ance wai biki dama ba’a masa gayya da kansa yake fallasa kansa, musamman ga su ɗin da kusan duk wanda suka mu’amalanta yana jin daɗin zama dasu.
A lokacin Maryam ta shigo ɗakin riƙe da wani faranti da aka cika da ƙullin zobo. Ummi da tasha kwalliya cikin ankon atamfar nan tace.
“Yawwa Mary, matso ta nan, tun dazu dama Aunty Safiyya ke cewa mu jira a kawo.”
“Taɓ! Wallahi na wannan ƙawaye na ne suna can a dakin Aminu, plate nazo nema idan kun gama zan zuba gurasa.”
“Au ba zaki bamu ba?”
STORY CONTINUES BELOW
“Waashi can fa ana ta ɗiba a ɗakin Amma, kuje ku ɗebo naku kafin ya ƙare don wallahi har yaje rabi.”
Ummi ta miƙe da sauri tace.
“Mu nawa ne a dakin?”
“Ai kawai je ki ɗebo ashirin, in ma da saura ma kara.” Cewar wata a cikin ƙawayen Aminan suna ƙyalƙyalewa da dariya gabaɗayansu.
Ummi ta fita daidai lokacin da Fatima ta shigo rike da plate guda biyu na banɗashen gurasar, Maryam kuma ta juya ganin ba zata samu abinda tazo nema ba.
“Wallahi kowa ya ɗauke hannunsa kafin in ajiye.” Cewar Fatiman ganin yadda kowannensu yayi shiri da hannunsa.
“Dalla malama ki ajiye kawai meye haka wai?” Cewar Shukra.
“Wallahi sai kowa ya ɗauke hannunsa, salon ina ajiyewa in rasa.”
Ta faɗa tana dariya, yayin da hayaniyarsu ta ƙaru kowa na fadin ta ajiye, ai kuwa tana dire farantin kafin ta mika nata hannun ta nemi gurasar ta rasa, sun wawushe ta tsaf suna ƙyalƙyala dariya, kuma yanayin fuskar Fatiman yasa Amina dake daga gefensu yin dariyar itama, lebbenta yayi talewar da har haƙoranta suka fito, don abu ne da ba yau suka saba ba, tun a makaranta sun saba irin wannan abin da an kawo abinci kawai wanda ya samu ya samu.
Kuma dariyar taji tana tafiya har ciki ƙirjinta, tana taɓo wani abu da ya kamata dama ace yana nan, wannan farin cikin da mace ke ji a lokacin aurenta.
A cikin hayaniyar da ɗakin ya ƙara ruɗewa dashi Aunty Ma’u tazo ta kira ta, tana fita taga Aminu ne yazo da mai hoto, aka shiga ɗaukar hoton kowa da ƙungiyarsa, Aminu na tsaye shine mai bada umarnin dake sa kowa yin dariya, don haka kusan duk a hotunan an ɗauka ne Amina na dariya, tayi kyau a cikin kayan da suka zauna a jikinta sosai ga kuma skirt ɗin kayan daya buɗe ta ƙasa, ita kanta ta yarda cewa telan nasu Ummi ya iya ɗinki ba’a banza suke ta yabonsa ba, kuma a kowanne hoto ita idonka zai fara gani saboda shigar kayan nata farare tas da kuma baƙin gashinta daya fito ya haɗu da baƙin ƙunshin hannaye ta yana ƙara haska farin.
Hatta Amma tayi kyau cikin shigar wani lace da ya dace da maman Amarya, itama tana ta dariyar da har ta mantar da ita haushin da zuciyarta ke ciki game da kayan jere da suka kai aka ƙi karba.
Ranar da su Tanti suka tafi za’a fara jeren nan, ranar zuciyarta ta sake yin baƙi game da al’amarin auren, don a waya Hajiya Kilishi ta kira tana gaya mata cewar ai su basu ce su kawo kaya ba, wai mahaifin yaron daya bada kudi ayi gyaran gida ya bayar har dana komai don haka su sun riga sun gama jeran su amarya kawai suke jira.
Sai da ƙyar bayan Tanti ta dage cewar baza su kawo ƴarsu haka ba sai da abinda zata kalla itama ta san cewar iyayenta ne suka yi mata kamar kowacce ƴa, sannan Hajiya Kilishin tasa aka fitar da kayan gado guda daga wani ɗaki suka jera nasu, kayan Kitchen kuwa suka zube mata gabaɗaya don shi dama abubuwan da aka ajiye basu da yawa, sai a sannan ne zuciyar Amman ta ɗanyi sanyi, amma har a wayewar garin yau bata dawo dai-dai ba sai a yanzu da Aminu ya saka ta yin dariyar dole.
Kuma duk yadda bikin ya kai ga zuwa a gaɓar da kowa ke ganin ba’a shirya ba, yayi mutuƙar yin daɗin da wataƙila ko da sun shekara ne suna tanadi haka komai zai kasance, banbancin kawai na farin cikin da za’a samu a zuciyoyinsu ne.
Wajen yamma, Adam ya kawowa Amina saƙon wata sallaya mai kyau da kuma alƙur’ani daga Abdallah, a hannayenta Amina ta rungume ledar ba tare da tace komai ba, idanunsa kawai take hangowa a ranar da ta gaya masa aure zata yi, yana kallonta da yanayin da bata iya fassara shi ba.
“Dama na gaya miki, ba wani son ki yake yi har cikin zuciyarsa ba.”
Haka Fatima tace lokacin da ta gaya mata yadda suka yi, amma sai ta girgiza kanta ta bata amsa.
STORY CONTINUES BELOW
“Cewa yayi dama ya sani ba lallai ya iya aurena bane Fati, yace ya san ba lallai ni ko iyayena mu iya jurewa tazarar dake tsakani na dashi ba.”
Da yamma Fatima dasu Ummi suka sa ta canja zuwa wani material kalar ruwan madara, a lokacin kuma kusan duka ƙawayen nasu na nesa sun tafi sai mutum uku kawai da kuma wasu daga cikin ƙawayen su Ummi, kalar kayan ta ƙara fito da hasken fararen idanunta, suka saje sosai cikin wani ɗauri mai kyau da Momi ta sake yi mata.
“Kece amarya ta farko a wannan lokacin da naga anyi bikinta bata yi make-up ba Amina, Allah ya shirya miki halinki.”
Cewar Momin sanda take ɗaura mata ɗankwalin, sai kawai tayi wani murmushi tana kallon ƙunshin hannunta yayin da wata ƙawarsu ta ke cewa.
“Amma kuma tayi kyan da wasu amaren ma da yawa basu yi ba, kin san natural look ƙarshe ne.”
Da haka sai hirar ɗakin ta koma kan kwalliya, kowa na faɗin ko a kwalliya simple make-up tafi kyau, wasu kuma na lissafo masu kwalliyar da ko heavy make-up ɗin suka yi tana yin kyau. Ta sani itama da aurenta bai zo a karkace ba zata yi kwalliyar, amma babu kalar tanadin data shiryawa wannan, ƙunshin ma don su Momi sun takura ne kuma ta san shine abinda kowa zai fara lura dashi akanta.
“Dama da kika haɗa kayanki baki ɗebi waɗancan litattafan ba?”
Fatima ta tambaya daga gefenta sanda idonta ya kai kan wani kwali a can saman durowarsu na litattafan makarantar ta, litattafan da ta san ba zata taba rabo dasu ba, don kullum cikin bitarsu take yi.
“Maryam ce ma ta haɗa kayan ai, ni ban san me da me ta haɗaba, kawai dai tace min ta hada su ne tare da sauran kayan akwatunan.”
“Allah yasa dai bata haɗa miki da kayan sawa da yawa ba, don yawa zasu yi miki idan aka hada da sababbin, gwara ita a ta ɗan ƙara akan nata. Ina ledar su sallayar da aka kawo, bari na haɗa na kaisu kusa da akwatunan, kar a manta.”
Fatiman ta faɗa tana ƙokarin miƙewa, sai dai kafin ta kai ga miƙewar Amina ta jawo hannunta da sauri, ta juyo ta kalle ta, idanunta sun kaɗa daga farinsu ta girgiza mata kai.
“Ki zauna kawai Fatee, ki bari ko anjima sai ki ɗauko su.”
Muryarta da kaɗan tafi kuka, kukan dake kwance a ƙirjinta tun bayan ɗaurin auren da su Kawu Mallam suka kirata soro bayan dawowarsu, Kawu mallam ɗin ya danƙa mata sadakinta dubu ɗari a hannunta, da kuma bayan tafiyarsu da ƴanuwansu na Niger suka ƙaraso suna faɗin angon bai je ba… Kalaman da suka sata tambayar me yasa take yaudarar kanta ne? da kansa yazo har nan ya gargaɗe ta tun kafin komai yayi nisa don haka don ya fara nuna mata bala’in da ta kawo kanta cikinsa hakan ba komai bane.
Har bayan sallar magariba gidan nasu a cike yake, koina yayi kaca-kaca da ruwa da kuma abincin da aka zuzzubar, sannan ga tarin wanke-wanke fal a gefe, don haka ana idar da sallar magaribar ƴanuwansu na Niger suka fara aiki kotaina, Allah ya taimaka da wutar Nepa don haka akwai haske koina.
A lokacin ne kuma motocin ɗaukar amarya suka hallara!
***
A cikin motar dake tafiya kan titin Lamido cresent, ɗan karamin mayafin da Ruƙayya ta yafa akan doguwar rigarta ya zame ya sauka kan kafaɗunta, gashin kanta baƙi sidik da ya haɗu dana ƙarin data nannaɗe cikin bun ya fito ta cikin hasken street lights da kuma na fitilar motar ƴan sandan dake jiniya a bayansu, amma bata damu ba, hannayenta na rawa ne yayin da take kokarin sake kiran layin mahaifiyarta daya katse saboda rashin service yanzu da suke magana.
Ta samu kiran ya shiga a lokacin da muryar Ashraf dake tuƙa motar da kuma ta abokinsa Bilal da suke kira da B-man ta shiga kunnenta. Ashraf ɗin ne ke tambayar abokin nasa idan har lambar wayar da suke jira an turo masa, amma a gajarce kawai ya bashi amsa yana girgiza kai.
STORY CONTINUES BELOW
“Ina jin ki Ruƙayya kuna ina?” Muryar mahaifiyar tata ta shiga kunnenta daga cikin wayar.
Sai a lokacin ta jawo mayafin ta sake rufe kanta sannan tace.
“Maamah muna hanya, mun ɗauko Bilal ɗin yanzu zamu tafi can sabon garin, su Ibrahim ma sun je sun taho da police ɗin suna bin mu a baya, muna jira ne yanzu a turo masa da number wanda ya sani a gidan don a tabbatar idan tana nan.”
Daga cikin wayar Hajiya Nafisa tace.
“Ko bata nan ku ƙarasa ku sami iyayenta ko kuma duk wani wanda zai iya baku bayani akanta, duk abinda ake ciki da kun isa you let me know, yanzu zan kira Daddy in gaya masa.”
Ta gyaɗa kanta kafin kiran ya katse, idanunta na tafiya kan abokin Ashraf ɗin dake danna wayarsa hankali a kwance, tsawon kwanaki kenan suna nemansa amma ba’a same shi ko a waya ba sai a yau da da wanin abokin Ashraf ɗin ya kira cewar gashi nan ya dawo daga Ondo, don haka ba shiri suka taho har wajen da aka kwatanta musu yana nan, kuma cikin sa’a suka same shi. Amma don rashin mutunci irin nasa bai fito ya same su ba sai da suka yi kusan awa guda suna jiransa, har su Ibrahim da Ahmad da suka je suka taho da police ɗin da aka kai report wajensu, sannan ne ya fito da uzurin cewar wasu abubuwan yake kammalawa da baza su iya jira ba.
Kuma duk da irin tashin hankalin da yaji suna ciki da kuma ma babban labari na ɓatan ɗan mutum guda, bai nuna ko a jikinsa ba bayan Allah ya sawwake guda din da ya furta. Ta sani cewa shi kansa Ashraf ɗin yaji haushi amma bai nuna bane saboda abu suke nema daga wajensa dole sune a ƙasa, amma duk da haka ta fahimci cewa akwai wani abu ne da ya faru da babu wannan kalmar ta abota a yanzu tsakaninsu.
Sai dai ba wannan ne a gabanta ba yanzu, a cikin kwanakin da suka gabata, zuciyarta ta mutu ta miƙe fiye da ƙirgan mai ƙirga, ƙarya ne ta iya kwatanta tashin hankalin da take ciki, tashi hankalin da sai da ya shafi kowa a gidan nasu gabaɗaya, ya zamana ba abinda ake yi banda fafutukar neman Mary ko ta wacce hanya amma basu same tan ba, hatta mahaifinta dake can ƙasar Romania yana aikinsa kullum sai yayi waya tsakaninsa dasu da kuma ƴansanda akan abinda ake ciki.
Idanunta kaɗai idan ka kalla sune shaidar rashin baccin da kuma na abincin da take ciki. Ta rantse a ranta fiye da sau shurin masaki cewar Mary zata gwammace bata zo duniya ba idan har suka kama ta, tunaninta baya iya lissafa abinda ya kamata tasa ayi mata.
Sun isa cikin unguwar ta sabon gari a lokacin da duhu ya riga yayi sosai, a lokacin kuma gabanta ya shiga faɗuwa cike da tsananin tsoro ganin irin cakuɗaɗɗun layikan da suke wucewa da kuma mutanen cikinsu, zata yi rantsuwa ba adadi cewa Mary ba zata taɓa rabarsu ba inda ta san daga waje irin wannan take fitowa, amma a haka ta zauna tana kula da ƴarta tsawon watanni bakwai.
Kwatancen Bilal ya kai su har wai takurarren gidan da mutane ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, bata san lokacin da ta dunƙule ƙarshen mayafinta akan bakinta ba yayin da kwalla ta shiga fitowa daga idanunta da suka riga suka kaɗa, zuciyarta bata iya kwatanta mata cewa Hamida tana wannan wurin ko kaɗan.
Ibrahim da Ahmad da suka fito daga motarsu bayan sun tsaya suka bada shawarar cewa ta tsaya su suka shiga ciki, amma jikinta na rawa ta girgiza musu kai, ruhinta zai bisu ciki ne ko da ta tsaya ɗin.
Ashraf da Ahmad ne suka fara shigewa gaba sai Bilal da kuma Ahmad, ita tana daga bayansu sai kuma ƴansanda biyar dake rufa musu baya, warin iskar gidan ta fara shaƙa kafin ta fahimci girman da yake dashi daga ciki, ga tarin ƙofofi birjik daga kowanne gefe inda hayaniya ke fitowa kamar zata fasa kunne.
Kuma ganin ƴan sandan yasa hayaniyar gidan ta ƙaru har da masu ihu suna shigewa ɗakunansu, a tsakar gidan su Ashraf da kuma ƴansandan suka shiga tambayar cewa Mary suke nema, kuma wasu ƙattin inyamurai da su kaɗai suka tsaya suka shaida musu cewar Maryn dake gidan sun fi mutum ashirin.
STORY CONTINUES BELOW
Koina a jikin Rukayya kawai rawa yake yayin da take kallon ƙofofin ɗakunan da dukkan fatanta na duniya, da ƙyar da kwatance aka samu wani a cikinsu ya gane wadda suke nema, kuma kai tsaye suka shaida musu cewa kwana biyu da suka wuce Maryn tare da iyayenta suka kwashe kayansu tsaf! suka tafi garin su.
Sai da ƙyar ƴan sandan nan suka samu mutanen nan suka fito musu da wani tsoho da akace ɗanuwansu ne. Kuma shima ganin ƴan sandan ya ruɗa shi, ya dinga rantsuwa bai san komai ba sai da yaga da gaske ana shirin tafiya dashi sannan yayi bayani cewar ya san yarinyar da ake neman, kuma har da ita a dalilin barin su Mary garin bayan ciwon mahaifiyarsu.
Ruƙayya gabansa taje ta tsugunna a lokacin yayin da yake bayani da gurɓataciyar hausarsa.
“Wani mutum ne anan yazo ya dauki yarinyar ya tafi dashi, kuma Mary yace ya bawa yarinya maganin bacci mutumin zai kamata, kuma the madam she’s serving zai ce ta ɓatar da yarinya, ita bata san yadda zata yi ba, don haka sun kwashe kaya nasu sun tafi.”
“Shi mutumin da yazo ya tafi da yarinyar waye shi?” Wani daga cikin ɗansandan ya tambaya tsaye akansa.
“Mary yace shine oga na inda babanshi Mr. Okafor yake aiki.”
“Ka san wajen aikin nasa?”
Ya ɗago cike da tsoro yana kallon ɗan sandan.
“Ka san wajen da baban nata yake aiki?”
Wannan karon Ruƙayya ce ta tambaya, muryarta na rawa da dukkan fatan na cewar amsar da zai bayar ta kasance abinda take son ji, kuma cikin abinda zata iya kira da sa’a, sai ya daga kansa yace.
“Eh ya sani, wajen inda ana…”
Bai karasa ba ɗan sandan ya bashi umarnin tashi su tafi, jikinsa na rawa ya miƙe tsaye ya shige gaba, aka sanya shi a motar ƴan sandan bayan sun fita, suka fara yin gaba sannan su kuma suka shiga nasu motocin suka bi su.
Wannan karon Ibrahim ya shigo motarsu ya zauna a wajen Bilal da shi ya koma motar Ahmad, tana ji kowannensu na waya, Ashraf da matarsa yana gaya mata inda suke, Ibrahim ɗin kuma da Daddy yana yi masa bayanin abinda ya faru.
Fuskarta ta juya waje idanunta na bin fitulun kan titi ke haskawa akan gilashin da kuma fuskarta, hawaye take sharewa da gefen mayafinta yayin da hannyenta ke rawa kamar zuciyarta, bata iya hango yadda zata kasance idan har bata sami Hamida a wajen nan ba.
Sun iso daidai gaban wani dogon gini mai ɗauke da gilasaivda kuma fitulu kamar rana, akwai manya-manyan rubutu a sama wanda bata iya karantawa ba saboda halin da take ciki da kuma ƙwallar da ta taru a idanunta. Ashraf da ya tsayar da motar ya juyo ya kalle ta, kuma ganin yadda take share hawaye yasa ya girgiza kansa yace.
“Stay inside, bari muje mu gani.”
Da haka ya buɗe ƙofar motar ya fita, Ibrahim na bin bayansa.
Sai kawai ta kifa kanta akan cinyoyinta ta shiga rera kukan da take kasancewa a cikinsa duk dare, gani take idan har ta rasa Hamida rayuwarta ta gama rushewa gaba ɗaya, ba lallai ne ta samu fatan da dashi take ganin zai sake gina rayuwarta ba.
Don samun Ma’aruf shine ƙarshen fatanta yanzu a duniya, bata hango komai a gabanta sama dashi, wani gefe na zuciyarta na jin cewa zata iya hakura da Hamidar ma idan har rayuwa zata iya dawo mata da Ma’aruf ta wata hanyar, amma ta san daga shi har iyayenta babu mai sake kallonta idan babu yarinyar, don haka ba zata taɓa rasa ta ba.
Wayarta tayi ƙara a lokacin daga gefenta, ta kalli screen ɗin tana karanta sunan Jawad da ya fito tar! akai, tun da ta barshi a hotel ɗin nan bata ƙara bi ta kansa ba, ya kira wayarta sau da yawa bata ɗaga ba, a jiya da yamma har gidansu yazo amma ta aika masa da saƙon ba zata iya fitowa ba, tana kallonsa ta tagar ɗakinta ya juya da motarsa ya fita.
“Babe I’m really sorry, ki manta maganar da na gaya miki dan Allah, just talk to me!”
Sakƙon message ɗinsa bayan katsewar kiran ya nuna akan wayar, sai kawai ta ɗauke kanta tana kallon waje, bata lissafa Jawad a cikin matsalolinta na rayuwa ko kaɗan.
Ta kalli wajen daidai lokacin da idonta ya kai kan su Ashraf da ƴan sandan nan, magana suke da wasu mutane a ƙofar wajen basu shiga ciki ba, kuma ta cikin hasken fitulun wajen taga Ibrahim ya dafo kansa ta baya tare da riƙe ƙugunsa alamun wani abu ake gaya musu da ya sa shi mamaki don ta hango mutanen na magana.
Ta hango Ashraf daga gefen tsohon da ya rako su yana sauraren mutumin kafin ya dunƙule hannunsa ɗaya akan bakinsa alamun nasa mamakin shima. Ba shiri ta buɗe handle ɗin motar ta fita, hasken fitulun wajen na shigar mata ido amma bata damu ba ta ratsa ta tsakanin sauran ƴan sandan da kuma Bilal ta isa gabansu, ta isa gabansu lokacin mutumin ke cigaba da cewa.
“… Ai na gane wanda yake bayani, shine dai Ma’aruf ɗin manajan kamfanin nan, sai dai idan kuna da hanyar da zaku same shi a gida, amma bana jin ko ranar litinin zai shigo, don yau aka ɗaura aurensa na gaya maka!”
Ya rufe bakinsa lokacin da ta cikin hasken fitulun wajen ƙwaƙwalwar Rukayya ta karanto mats manyan rubutun dake saman ginin… ‘Bakori Enterprises’
Kuma wayar hannunta da ta fara faɗuwa, ita ta juyo da hankalin kowa a wajen kafin su ankara da tata faɗuwarta har ƙasa!
***A cikin sabon gidan mutane sun fara raguwa sosai, ba kamar a ɗazu da koina yake a cike da mutane ba, Aunty Safiyya ta taho daga hanyar falo ta biyo wani ɗan dogon korido mai ɗauke da ɗakuna ta shigo ƙofar ɗakin dake gefe, a cikin ɗakin duk ƴan uwa ne na kurkusa sai kuma amaryar dake tsakiya kanta a sunkuye tana faman kukan da babu sauti sai hawaye kawai da take sharewa.+
Aunty Safiyan da ta shigo tace.
“Na rasa yadda akayi aka manta da tsitsiyoyin nan wallahi, yanzu da ba sai a share gidan ba kafin mu tafi.”
“Aunty ai na zata sharar dare babu kyau.”
Ummi dake kokarin dora akwatuna can saman wardrobe din dakin tare dasu Momi ta fada tana juyowa.
“Wannan ai kamawa tayi…” Cewar Aunty Ma’u.
“Baki ga falon nan ba duk kasa ce wallahi, don bana ji akwai wanda ya shigo babu takalmi.”
“Ni maigidan ma nake ji, haka zai shigo yaga waje duk ƙura?”
Ɗaya daga cikin matan Baban Kurna tace.
“Da za’a iya tunda akwai kofa ta baya sai a shiga gidan a tambayo su wallahi.
Mahaifiyarsu Ummi da itace zaune a gefen Amina rike da hannayenta ta girgiza kai tace.
“A hakura kawai, gobe da safe insha Allah sai su Maryam su zo su kawo mata kawai, su taya ta sharar ma.”
Ta fada tana kallon Maryam din dake tsugunne a gaban Amina ta riko ɗaya hannunta.
“Ɗan kunnayen nan naki suna cikin wata ƴar ƙaramar jaka pink, ina jin a cikin wata Ghana must go aka saka.”
Cewar Maryam din tana kallon idanun Aminan da duk yadda suka yi ja saboda kuka wannan kyallin na cikinsu na nan. Ta san ba zata amsa ba saboda haka ta cigaba da cewa.
“Hijaban sallarki ma suna cikin wannan karamin akwatin na undies, Amma ce tace in sa miki anan.”
Sai ta gyada mata kai kawai tana ƙara share hawayenta lokacin da Aunty Safiyya ke tambayar su Ummi idan sun kwashe kayan cikin akwatunan kafin su dora su.
“Duk mun zuba su a cikin wadrobe ɗin, na kayan kwalliyar nan ne da kuma wannan Ghana must go ɗin zamu bari a ƙasa.
“Eh, ku barsu ta gyara ta kanta, sai ku zo mu tafi kuma don goma ta wuce.”
Jin haka yasa Fatima ta taho daga wajen su Ummin tana ƙarasowa gaban Amina, lokacin da Maryam ke cewa.
“Idan zamu zo goben zamu zan taho da Hafsa insha Allah.”
Fatiman ta sunkuyo tace.
“Amina litattafan nan naki ba’a ɗebo ba, sai dai daga baya ko Aminu ya kawo miki.”
Sai a lokacin ta ɗago da idanunta ta kalle su, me yasa ne suke ta yi mata zancen kaya bayan ba abinda ke gabanta kenan ba? Mantawa suka yi cewa tafiya zasu yi su barta? Su barta a wannan wajen da bata san makamar abinda zata fuskanta ba, ko Abdallah ta aura ai dai sun san cewa wannan lokacin mai ciwo ne a wajenta, balle kuma mutumin da bata san ya yake ba balle takamaimai halinsa. Aunty Ma’u ta miƙe tsaye tana gyara mayafinta tace.
“Sai hakuri Amina, kin ji dai duk nasihar da akayi miki daga can gida, sannan su ma iyayen mijin naki kinga yadda suka karɓe ki, sunce ƴa suka karba ba suruka ba tunda dama duk ɗaya ne, kuma kowa ya san halinki Amina, duk wanda ya sanki yabonki yake yi… Mutanen nan sune basu sanki ba, kuma yanzu ne mafarin zamanku, dan Allah ki ɗorar da halinki a wajensu Amina… Don wannan gaɓar itace mafi alkhairin rayuwarki, ki sa su zasu zo suna bamu labarin kyautatawarki…”
STORY CONTINUES BELOW
Ba shiri Amina ta sake fashewa da wani sabon kukan da ya nemi mazauninsa a zuciyar duk wanda ke ɗakin, taji zuciyarta na sake karyewa da tausayin kanta, kalaman suna tuna mata da na Gwaggo Balkisa a dazu kafin tahowarsu, ɗakin Amma da suka cika aka kaita don ayi mata wannan fadan na al’ada, kuma sai da kowa ya gama nasa sannan ita Gwaggon ta kamo hannayenta duka biyu tace.
“Amina kin sani cewa daga yau sabuwar rayuwa zaki fara wadda babu iyayenki bale kuma sauran ƴanuwanki a kusa, zaki zama ɓarin wani mutum daban da zai bukaci tsananin kulawarki,
Kiyi amfani da hankalinki da kowa yake yabo ki zame masa mata kuma Uwa, ki kokarin zame masa komai a rayuwa ta duk wata hanyar da zaki iya.
Ba abu ne mai wuya ba Amina, don maza banbancin su kadan ne dana yaro ƙanƙani, kulawarki kawai yake buƙata sai ki ganshi a tafin hannunki. Kar ki dauki kulafucin barin gida ki sa a ranki fiye da ƙima, shima nasa iyayen zai bari yazo ya zauna dake, banbancin kawai shi namiji ne da zai daure ke kuma mace ce, ki saki ranki ki saba da sabuwar rayuwar da zaki fuskanta don itace rayuwarki ta yanzu dama ta gaba.
A kowanne aure akwai sirri Amina, ki riƙe sirrin gidanki ki riƙe sirrin sa, ki zauna lafiya kamar mahaifiyarki, kina ganinta dai shekaru fiye da ashirin kenan da muka kai ta daki amma daidai da rana guda bamu taba jin bakinta ba. Kiyi wa mijinki biyayya, ki girmama shi, idan kika yi haka kema kin girmama kanki.
Mace mai wayo ita ke gina gidanta Amina, sakarya kuma da hannunta take rusa shi.”
Don haka a yanzu ma da Aunty Ma’u ta fara sai taji kukan da ta sha ɗazu ya sake dawo mata sabo. Fatima ta taho ta rungume ta daga tsaye tana gaya mata abinda kowa ke faɗa, cewa tayi haƙuri, kuma sai su Ummi ma suka karaso suna tayaa ta, tanajin yadda kukan bata ke jijijiga jikinsu kafin Aunty Safiyya tasa su suyi gaba.
“Wannan shine dakin da muka kawo miki kaya, watakila zaki ga sauran biyun dake gefe sun fi shi kyau, amma kiyi zamanki a cikinsa Amina, don shine mutuncinki.”
Aunty Safiyya ta raɗa mata a kunne lokacin da kowa ke mata sallama, kuma tana ji tana gani dukkaninsu suka tafi, tayi niyyar tasowa suje ko wajen kofa ne amma mamansu Ummi ta hana, tace tayi zamanta kawai.
Ta dade a zaune tana kallon hannyenta bayan tafiyar tasu, ji take yi kamar an saka ta a wani jikin ne da ba nata ba, an ce komai nisan jifa kasa zai faɗo, ta yarda da auren nan kamar wasa, zuciyarta na hango mata shi a can nesa sai gashi tun ba’a je koina ba har anyi an gama, kowa ya taka rawarsa ya matsa, an bar mata filin da tace zata iya yakin a cikinsa.
Kamar wani yana kallonta da kyar ta ɗago idanunta tana karewa dakin kallo, kayan cikinsa dama ta riga ta sansu, har gadon a waya Aminu ta nuna mata don tare suka je shi da Baban wajen masu kayan katakon, labulen kuma duk a tsakar gidansu akayi ta dagawa ranar da su Aunty Safiyya suka siyo daga kasuwa, carpet din da aka shimfida a kasan gadon ma, a ɗakinsu aka jingine shi.
Don haka ginin gidan da shine baƙo a wajenta take kallo, ɗakin kato ne yasha fenti da kuma tsarin fitulun da ba sai an gaya mata ba ta san masu tsada ne. Ta tuno yadda taji su Ummi nata yabon sauran bangaren gidan, ba shiri taji wani abu ya wuce ta makogwaronta, kowa ya sani cewar akwai dalilan da suka kawo ta wannan gidan, ba’a banza kamar ita zata sami irin wannan wajen ba, kowa ya sani cewa akwai wani abu daban a tare da auren nan, kawai kowa yayi shirun ne yana jiran ganin abinda zai biyo baya.
Tafi minti goma tana tunane-tunanen abinda zai iya faruwa da kuma mafita kala-kala, amma duk abinda ta kamo sai ya suɓuce idan ta tuna cewar a yau zata yi ido biyu da mutumin da aka daura mata aure dashi, mutumin da ya riga yayi mata gargadin cewa kar ta yarda ta aure shi, zuciyarta ta sake matsewa kamar zata fashe zuwa wasu dubunnan ƙananan atoms.
Da kyar ta cillar da komai a cikin kanta ta miƙe ta nufi toilet din dake manne a dakin, kuma sai da numfashinta ya tsaya sanda idonta ya kalli ciki, toilet ne da yasha adon wasu baƙaƙen marbles masu kyalli da santsi, anyi wasu hadaddun drawers a ciki da wani bakin katako da ya dace da kalar marbles din, ta ja numfashi a hankali sannan tayi addu’a ta taka kafarta ciki a hankali tana jin sanyinsa na ratsa ta.
STORY CONTINUES BELOW
A gaban katon mudubin ciki ta tsaya tana kallon yadda idanunta suka yi ja dama yadda fuskarta ta dan kumbura, sai kawai ta bude fanfon kasan sa tayi alwalarta, ta haɗa da wanke wuyanta dama rabin bayanta, kuma dadin ruwan yasa wata zuciyar tace mata taje ta ɗauko sabulu a akwatin cosmetics ɗin nan tayi wanka gabaɗaya amma ta girgiza kanta. Ba yau ba, ba yanzu ba.
A akwatin undies ɗin nan da Maryam tace ta dauko hijabinta guda daya, ta dawo kan carpet din dakin tayi sallah raka’a biyu, bayan ta idar ta dago da hannayenta da niyyar addu’a amma sai ta rasa ma me zata roƙa, saboda haka sai kawai ta dunƙule jikinta waje ɗaya ta ɗora kanta daga gefen gadon tayi shiru.
Shirun da a cikinsa taji lokacin da aka buɗe kofar dakin.
**
Karfe sha ɗaya daidai ta iso da Ma’aruf ƙofar gidan, ginin ya tsaya a gabansa kamar wani tsauni, babu wanda zai ce ma a cikin gidansu aka fitar dashi, don gate dinsa yayi gefe da yawa ta daya bangaren. Ya lashe lebbensa na kasa daya bushe yana gayawa zuciyarsa cewa sun zo matakin da suke jira, sakon ya isa kuma maimakon ya dawo cike da kwarin gwiwa sai ya dawo da wani raunin da kalaman da Ishaq ya gaya masa a dazu suka yi sanadiyarsa.
“Ka sani cewa wannan ba labari bane Ma’aruf, ba labari ne da zaka rubuta a yadda kake so kuma har ka kai ƙarshe da son zuciyarka ba. Na fahimci dukkan abinda ka faɗa da kuma dalilin da yasa ka dawo ka yarda da auren, amma hakan baya yana nufin cewa ka tsallakewa abinda zai iya faruwa ne.
Kar ka manta a baya ciwonka ko matakin HypoMania bai kai ba abubuwan da suka faru suka faru, yanzu kana stage na karshe Ma’aruf, kai da kanka kana tsoron wannan matakin, ba sai ka gaya min ba, a idanunka kawai nake gane cewar kaima kana tsoron faruwar wani abu kamar yadda kayi tunani a farko, tunda ni da kai mun sani cewa ba lallai ne mu iya binne komai ba a wannan karon…”
Ya sake lashe leɓɓensa yana jin yadda har a yanzu tasirin kalaman ke yawo a cikin kansa, gargadi Ishaq ɗin yake yi masa ya sani, gargadin da shima ya riga yayi wa kansa duk da cewa bai tsara komai game da auren ba bayan cewar yana son samun bayanansa daga yarinyar, zai tafi da abinda lokaci ya bashi ne kawai yana kuma ƙoƙarin kiyayewa dukkan abinda gaban zata haifar, haka ya gayawa Ishaq, ya kara gaya masa cewar shi yanzu abubuwan dake gavansa ma Allah yayi yawa dasu, sai yaga komai ya lafa masa tukunna ma zai maida hankali kan yarinyar.
Ta cikin glass ɗin motar ya hango ƙofar gate ɗin shiga wajen su Mami dake can gefe, babu kowa a wajen alamun da gaske dare yayi don ya sani cewar an sha hidimar mutane tunda yau ne rana ta karshe a bikin.
Wayarsa ya jawo ya kira Mamin, bugu daya biyu, kuwa ta dauka tunda dama jiran isowar tasa take, har a hanya ta kira shi taji idan ya taho.
“Ma’aruf…” Muryarta dake shaida dimbin gajiya ta kira shi da sunansa.
“Mami na iso amma ba zan shigo ciki ba.”
Sai da ta ɗanyi shiru kafin muryarta tace.
“Kai da mutane ne?”
Ya girgiza kansa.
“Ko Ishaq ma nace yayi zaman sa kawai. I’m alone.”
“Tohm shikenan da safe na ganka, dama bana son kayi dare sosai baka iso bane, don tun wajen
Isha’i suka ƙawo ta, anyi muku addu’o’i masu tarin yawa, hatta ƴan uwan Hajiya Maimuna da basu so abin da farko ba sun yaba sosai da ita da kuma ƴanuwanta Ma’aruf, Ina fatan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa a zaman da zaku yi, Allah ya baka ikon sauke sabon nauyin da ya hau kanka.”
Bai san lokacin da ya haɗiye wani abu a makogwaron sa ba kafin ya amsa a hankali, don ji yayi kamar itama tana tuna masa da abinda Ishaq ya faɗa ne.
“Insha Allah Mami. Nagode.”
Yaji kamar ta gyada kanta kafin ta sake cewa.
“Na san da wuya idan kaci wani abun, ga abinci nan ma nasa Samira ta tanadar maka tun dazu, a miƙo maka ne?”
STORY CONTINUES BELOW
Ya girgiza kansa tun kafin ma ta ƙarasa, fon baya tunanin a yanzu ko ruwa zai iya sha, tarin abubuwan da ƙwaƙwalwar sa da kuma zuciyarsa ke rabawa basu da adadin da har zai sami nutsuwa ta cikinsu.
Saboda haka sai kawai ya canja zancen da cewar.
“Na zata ma kowa yayi bacci Mami.”
“Baccin mai gaskiya? Yanzun nan fa suka dawo daga kai sauran amaren, ai gidan nan yana nan kamar rana don baka shigo daga ciki bane, kuma naku ɓangaren ai yasha dab-dalarsa, sai da kayi haƙuri da abinda zaka gani.”
Wani guntun murmushi da bai san dalilin sa baya suɓuce a gefen fuskarsa, don shi a yanzu baya son ganin yarinyar baya jin akwai abinda ya dame shi na harkar auren, sai kawai ya zaro hannunsa daga cikin gashin nasa yana bude kofar motar dashi sannan yace.
“Shikenan Allah ya bamu alkhairi, Allah ya huta gajiya, ta amsa kafin ya kashe wayar. Ya tsaya daga wajen yana kallon ginin gidan kafin ya sake komawa kan wayarsa ya danna wata number, bugu ɗaya biyu matar dake ɗaya layin ta dauka, kuma bayan sun gaisa ta tabbatar masa da cewar Hamida tayi bacci sannan ya katse wayar.
Inda ya kira ɗin, wani Creche ne kamar asibiti inda ake bawa yara kulawa ta musamman, na wasu ƴan Turkey ne musulmai, amma akwai hausawa a cikin ma’aikatan nasu, asibitin da aka kwantar da Hamidan ne da farko suka bashi shawarar ya kawo ta wajen, kuma sai hakan yazo daidai da cewar bai shirya kaita gida a lokacin da ake hidimar bikin nan ba.
Ranar farko da suka je, tayi rigimar cewa ba zata zauna, amma cikin ƙwarewar aikinsu da kuma tarin abubuwan wajen dake kama zuciyar yaro, sai rigimar tata bata je ko’ina ba.
A iya kwanakin nan yana zuwa kullum ya ganta wanda hakan yasa yayi sabo da ita sosai don har ta fara sakewa dashi tana amsa duk ƴan ƙananan tambayoyin da yake mata, da farko ne duk maganar da zai yi mata sai dai ta kalle shi kawai, sai bayan barinsu asibitin ne da ya kawo ta nan sannan ta fara yi masa magana, kuma ya fahimci tana da maganar sosai, kawai bata gama sabawa dashi bane har yanzu, amma ya san aƙalla suna making progress din da za’a zo gabar da zata fahimci cewa shi mahaifinta ne.
Ya sake kallon gidan, babu maigadi don haka shi ya shiga da motar, sannan ya sake rufe gate din ya dawo, ƙafafunsa suka taka kan barandar gidan sannan ya tura ƙofar falon ya shiga a hankali.
Hasken fitulun ɗakin ya shiga idanunsa tare da hotunan kayan da suke ciki, daga kujeru labulaye dama carpet ɗin cikin komai kalar Army green ne da kuma brown, babu wajen dining don haka kofofin korido biyu ne kawai da ya san ɗaya ta kitchen ce ɗaya kuma ta hanyar ɗakuna, sai kawai ya juya a hankali ya rufe kofar falon.
Iskar da akeyi a waje mai zafi ce, yaji ta bayan ya fito daga Acn motarsa, amma a yanzu da ya shigo gidan yaga yadda labulayen falon ke dagawa sai yaji kamar ba irinsu ɗaya da ta wajen ba. A hankali ya zame takalmansa daga kafarsa sannan yayi gaba, ya kuwa ji ƙurar da Mamin ke fada amma bai damu ba, ya shiga hanyar koridon a lokacin da yake jin wani abu kamar bugun zuciyarsa na ƙoƙarin canjawa.
Ƙofofi uku ne a ciki, kuma bai buɗa kowacce ba don guda ɗayan dake gefe da kuma ta can karshe ta kasan kofofinsu ya kula duk fitulunsu a kashe suke, ta farko daga gefen daman sa ce kawai hasken cikinta ya saje da na cikin koridon.
Don haka kai tsaye ya ƙarasa gare ta ya ɗora hannunsa akan mariƙinta, sannan ya buɗe ta a hankali ba tare da tayi wata ƙara ba, kuma babu wani hijabi idanunsa suka sauka akan matar da kowa ke kira da tasa, ɗan karamin frame ɗin jikinta na naɗe a gefen gadon ɗakin, ta jingina kanta da gefen gadon idanunta a rufe, rabin fuskarta na shigewa cikin gadon yayin da hasken fitilar ɓangaren ɗakin ya haske ɗaya gefen fuskar tata.
Hijabin dake jikinta ne ya shaida masa cewa sallah tayi, kuma kafin ya iya sake wani tunanin ta buɗe idanuwanta duka biyun ta kalle shi.
Bai san me ya zata ba, bai san yadda yayi tunanin zai zo ya ganta ba, bai taɓa ma hasko ta a cikin kansa ba balle ya kintaci yanayinta, amma a lokaci guda yaji wani abu ya balle daga cikin zuciyarsa ganin ƙanƙantar ta, don duk a lissafinsa irin Ruƙayya zai gani, amma wannan ƙarama ce sosai, idanunta are so young haka ma jikinta ƙarami ne, yawun da ya sake haɗiyewa yana kallonta yasa wannan karon Adam’s Apple dinsa motsawa sama da ƙasa. Kuma a lokaci guda kallon dake cikin idanunta ya canja zuwa wani abu kamar tsoro, yaga ta mike tsaye da sauri rike da hijabinta sannan ƙafafunta suka yi taku biyu baya, a yanzu ya tabbatar tsoratar tayi.
STORY CONTINUES BELOW
*
Lokacin da ta mike tsaye tana kallonsa, zuciyarta ta shiga tseran kilomitoci a ƙirjinta, yayin da take jin ƙafafunta na rawa kamar ma zasu iya daukanta ba, don haka ba shiri zuciyar tata ta shiga ambaton kalaman Innalillahi har zuwa ƙarshe yayin da take cigaba kallonsa.
Bata yi tunanin kawai bude ido zata yi ta ganshi tsaye a gabanta ba, bata ma yi tunanin haka yake ba, yadda take hango shi a tunaninta ya zarta hakan, dogo ne sosai ɗan siriri amma kuma mai cikar halitta, ba fari bane ko kadan haka nan ba baki bane, idanunsa na kallonta da wani yanayi da suke lumshewa, fuskarsa fayau yana tsaye yana kallonta daga bakin ƙofar, kayan jikinsa kalar ruwan toka ne mai irin sealed dinkin nan, babu ko hula akansa sai gashin kansa mai yawa da ya taru.
Zuciyarta ta cigaba da fat, fat, tana kallonsa, so take yi ta tantance idan har shi ɗin ne ma ko kuwa aljani, tunda bata ko ji sallamarsa ba, sai kuma wata zuciyar tace mata ta yaya mutumin dake shirin fara nuna mata wutar da ta kawo kanta zai fara da yi mata sallama?
Taji kamar ta tafi ta shige toilet din dakin kawai ta kulle kanta, amma wani bangaren zuciyarta ya ture hakan, yana gaya mata cewa ya kamata ta jajirce ta fara ganin abinda zai yi tukunna, don ta gayawa zuciyarta zata iya yafi cikin carbi, kuma dukkan kalaman da ta faɗawa mahaifinta dama kowa suna nan a cikin kanta, don haka bai kamata ta fara karaya tun yanzu ba. Kuma ga mamakinta sai abinda take jira din ya faru.
“Assalamu alaikum.” Muryarsa mai zurfi ce da a lokaci guda ta daɗa hargitsa tunaninta, tasa numfashinta katsewa a maƙogwaronta.
Ma’aruf ya sake lura cewa a tsorace take, don bayan yanayin fuskarta yana iya ganin yadda ta damke hijabin jikinta da duka hannayenta biyu tana cigaba da kallonsa, bata amsa sallamar ba, kamar ma bata ji yayi ba, kamar jira kawai take yi yayi wani abu ta ɓace daga dakin.
Ya fitar da numfashin daga ƙofofin hancinsa, me ya zata dama ga yarinyar da yayi wa wannan barazanar, don haka ya sani cewar yanzu a farko dole ne yayi kokarin kore wannan tsoron nata game dashi, yasa ta fahimci cewa a yanzu
ba abinda ke gabansa game da ita kenan ba.
“Ki kwantar da hankalinki, na shigo ne don kawai mu gaisa ki san cewar ba ke kaɗai ce a gidan ba, idan akwai wani abu da kike bukata kuma zaki iya gaya min…”
Kalaman suka daki zuciyar Amina ta yadda numfashinta ya tsaya cak! Wani abu a cikin kanta ya gaya mata cewar hatta lokaci sai da yayi shawara sau biyu kafin ya motsa. Kallonsa kawai take yi da tsananin mamakin da ta kasa auna shi a mizanin hankalinta.
Ya fahimci ba zata yi magana ba don haka ta ga ya sake riƙe hannun kofar sannan ya furta mata.
“Sai da safe.”
Ya rufe ƙofar daidai lokacin da kafafunta suka kasa ɗaukarta gabaɗaya.
**
Hasken safiyar dake shigowa ta liner labulen ne ya tada ita, ta kifta idanunta tana kallon yadda wajen yayi mata kyau a ido, yadda hasken ya haɗe da kalar labulen dama liner yana ratsowa ta cikinsu, amma duk da kyan nasa sai taji kewar gida ta kamata, taji tana kewar ɗakinsu har ma da katifarta don ba zata iya tuna rana ta ƙarshe da taje wani wajen ta kwana ba tun bayan data gama makarantar Boarding fin da tayi.
Ta rufe idanunta ta buɗe tana sake kallon windon wanda tsawon yadda take ganinsa yasa ta tuna cewa a ƙasa take, akan carpet din nan, don anan bacci ya dauke ta bayan zuciyarta ta cika da sake-saken al’amarin da ta kasa ganewa.
Ba irin tunanin da bata yi ba da abinda bai zo kanta ba a jiyan nan, amma daga ƙarshe da ta tattara duk lissafinta da kuma abubuwan da aka gaya mata dama abinda ta shirya, sai taga cewar bata da wani zaɓi illa ta fara fahimtar manufarsa akanta kafin ta yanke hukuncin da zata iya kare kanta dashi.
STORY CONTINUES BELOW
Ta miƙe zaune a hankali tana son daidaita ganinta, a sannan ne ƙwaƙwalwarta ta tuna mata cewar bata yi sallar asuba har gari ya waye haka, ƴar wayarta dake gefe ta jawo tana tunanin yadda akayi alarm ɗinta bai tashe ta ba amma sai ta tarar ta mutu saboda ba caji, don haka ta mike da sauri ta nufi bandakin a lokacin da idanunta suka sake kallon ƙofar dakin ta tabbatar muƙullin data kulle ta dashi yana jiki har yanzu kafin ta shiga ciki.
Bayan ta idar da sallar ta daɗe tana addu’ar neman gafara da kuma ƙwarin gwiwar tunkarar duk abinda ke gabanta kafin ta mike, a cikin akwatin kayan kwalliyar nan ta samo sabulu, ta shiga tayi wanka, kuma duk da cewar komai sabo ne a wajenta bata sha wahalar gane kan fanfunan dake ciki ba tayi wankan ta fito.
Ta dawo cikin ɗakin dake ƙara tuna mata cewar rayuwarta ta canja da gaske, don har yanzu yanayin da take ciki ba zata iya fassarashi ba, aayƙin da take ji daya ne kawai na cewar ƴan gidansu zasu zo, don haka da ƙyar ta ture duk wani tunani dake ranta ta shirya cikin wata doguwar rigar da hannunta ya fara kaiwa a cikin kayan dasu Ummi suka jera mata jiya, bata ɗaura ɗankwalin ba sai kawai ta yafa shi akanta.
Ta kalli kanta a mudubin ɗakin tana ganin yadda idanunta suka fara washewa da kukan da tasha a jiya kafin tasa duka hannayenta tana gyara zaman ɗankwalin akanta, siraran awarwarayen da har yanzu ke hannunta suka shiga rawa suna tuna mata da zamansu, don haka tayi saurin cire su gabaɗaya ta ajiye akan mudubin sannan ta juya ta kalli kofar dakin.
Kai tsaye ta ture komai a ranta ta nufi kofar ta buɗe ta, korido ne mai dan tsawo dake dauke da ƙofofin ɗakuna guda uku, ta sani cewa dole a daya daga cikin dakunan ya kwana tunda yace mata yana nan, don haka bata ko yi gigin bude kowacce ba kafafunta suka taka suka fita zuwa falo, anan ne, zuciyarta ta narke da kowanne abu na cikinsa dake shaida haɗuwarsu tun daga nesan da take, komai yana haɗewa cikin kalar ɗanuwansa cikin wani simple ado daya dace da wurin.
Ta jinjina kai a hankali kafin ƙafarta ta tafi zuwa daya korido ɗin anan, tana jin yadda fatarta ke sulalewa akan santsin wajen duk da ƙurar data lura akwai, kofar wani katon kitchen anan da komai na cikinsa ash ne da kuma fari, akwai store mai ɗan girma data buɗa ta tarar da kayanta fal a ciki, wasu ma duk a cikin buhu suke ba’a buɗe ba.
Ta dade tsaye tana kallon kayan da kuma tsarin drawers din kitchen din kafin ta hango wats kofa a can gefen fridge, taje ta bude ta, hanya ce mai dan fadi dake zagayawa kowanne bangare na gidan, inda daga can jikin katangar kuma ta hango wata kofa data tabbatar ta nan ne ake shiga cikin gidansu. Ta rufe kofar ta dawo tana sake komawa store din nan don ganin kayanta, tsji wani abu kamar magana amma bata tabbatar ba ta cigaba da duba kayan.
A lokacin ne kuma ta jiyo muryarsa, kamar irin ruwan saman dake sauka a lokaci guda tana ƙarasowa hanyar kitchen ɗin, ba shiri hannayenta suka nemi hannun kifar store ɗin amma kafin ta iya rufe ta gabadaya, ya karaso don hannun nata ya tsaya cak tare da numfashinta, idanunta suka hango mata shi ta zirin ƙofar da bai gama rufuwa ba, kuma a lokaci guda taji zuciyarta tayi kuli-kulin kubra ta faɗo daga wata sama mai nisa.
Ashe jiya bata lura da tsawonsa sosai ba, a yanzu daya canja cikin wani yadi kalar sararin samaniya da irin ɗinkin rigar da bai kai gwiwa ba, bata jin a cikin abokan Aminu gabadaya data sani akwai wanda zata iya kwatanta shi tare dashi. Ta hadiye yawu tana kallon yadda idanunsa ke lumshewa da sauraren abinda ake gaya masa ta cikin wayar kafin yayi magana.
“Me kace?” Muryarsa a hankali ta fito, da wani irin amon da yasa jikinta girgizawa, numfashinta yana katsewa ba gaira ba dalili. Me yazo yi ne ma a kitchen din?
Ta ga ya girgiza kansa sannan ya zura hannayensa cikin gashin kansa yana motsa su, a lokacin ne kuma iska ta buso mata da ƙamshin turarensa, wani abu kamar ƙamshin musk ko mint, ko kuma meye hancin nata ya jiyo mata, sai kawai ta juyar da kanta gefe yayin da muryarsa ta sake fitowa.
STORY CONTINUES BELOW
“That issue aside Faruk, ba yanzu zamu neme shi ba, let’s give him atleast two weeks to settle down, (mu bashi kamar sati biyu da zai huta) babu wuya zamu kama shi a sannan. Yanzu let’s just focus akan waɗannan mutanen, I have somewhere to be now amma zan kira Martha ta min sending duk wani back-up da muke dashi akansu, zuwa yamma we decide where to meet sai ka kawo naka mu ga me zamu fitar.”
Murza ƴan yatsunta kawai Amina ke yi tana fatan ya juya ya fita, amma ga mamakinta sai kawai taji wata muryar mace ta taho tana faɗin.
“Yaya baka ganta bane?”
Kuma kafin ƙwaƙwalwar ta ta gama lissafawa, wata budurwa ta shigo cikin kitchen ɗin hannunta dauke da wani katon food flask, doguwar riga ce a jikinta shade din albasa (onion color) da wani dan karamin mayafi data yafa a sama maroon colour.
“Bata nan kitchen ɗin?”
Ta sake tambaya tana ƙarasowa ciki fuskarta ɗauke da murmushi, a lokaci guda taji wani abu ya ratsa ta har tafin kafa, don babu wata kwana-kwana ta gane ƙannensa ne suka zo, kuma shigowar sa kitchen ɗin ita yake nema. Taga yadda hannayensa ke motsawa a cikin gashin nasa alamar bai san me zai ce ba lokacin da yarinyar ta tafi tana ajiye food flask ɗin can kusa da gas cooker.
Sai kawai tayi karfin halin ɗauko wani jug a gefe sannan ta buɗe ƙofar store ɗin ta fito, zuciyarta na gaya mata ai tunda a yanzu ƙirgen ya tashi daga su biyu ta tsira.
“Sannu da zuwa.”
Muryarta tasa duka su biyun juyowa suna kallonta, yarinyar ta washe baki cikin fara’a sannan ta taho da sauri ta rungume ta.
“Ashe kina ciki, Barka da safiya.”
Sai da zuciyarta ta buga a kirjinta saboda mamaki, mamakin da ta daure cikin nata murmushin itama tana rungume ta.
“Sunana Samira, tare muke da Surayya da Munaya suna falo, fatan kin tashi lafiya?”
Ta faɗa bayan ta janye daga jikinta, sai ta ɗaga kai da nata murmushin mai fadi ta amsa da.
“Lafiya kalau, nagode sosai.”
A lokacin ne kuma idonta ya kai kansa, ta san kallonta yake tun da ta fito don tana jin tasirin yadda idanun nasa ke shiga jikinta, gabanta ya faɗi sakamakon haɗa idanun da suka yi, kallon da yake mata mai cike da nazari ne, kamar yana saka scanner cikin idonsa yana son tantance ta.
Kuma a lokacin ne babban al’amarin safiyar ya faru, bakinsa ya motsa da wani guntun murmushi yana rufe idanunsa ya buɗe su akanta, kamar ma ƙifta mata idanun yayi, abinda kafin ta gama tantacewa ya juya ya bar kitchen ɗin.
A kusa da kafafunta taji cikinta ya faɗi gabaɗayansa har ƙasa tsabar tsurewa da kuma mamaki, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa kafin muryar Samirah ta cigaba da magana cikin tunaninta, sai ta hango kanta ta tsugunna tana ƙoƙarin tattara jikinta waje ɗaya kafin ta iya fahimtar me take cewa.
“Abinci muka kawo muku kafin mu fara zagayen gidan sauran amaren, gamu nan da kaya fal cikin mota kowacce tayi mantuwarta… Na san kema kinyi taki ko?”
Bata gama daidaita tunaninta ba, don haka bata san sanda ta ɗaga mata kai ba tace.
“Ina tashi nima naga na manta chager wayata.”
“Ai sai a hankali ma zaki yi ta neman wasu abubuwan, Ya Shukra har da system ɗinta gabadaya ta manta kuma project ɗin masters take yi…”
Ta gyada kai tana ƙoƙarin murmushi sanda wata ta ƙaraso cikin kitchen ɗin itama, watakila itace zasu yi sa’anni ɗaya ko kuma ace ta fita da kadan, tana da glasses wanda kana gani ka san medicated ne, ita kuma bakar abaya ce a jikinta wadda ta fito da ɗan hasken fatarta don ita ba fara ce sosai kamar Samiran ba, zata iya jera su layi ɗaya da yayan nasu.
STORY CONTINUES BELOW
“Ashe kina nan matar Yaya…”
Ta fada da nata murmushin itama tana karasowa kuma ga mamakin Amina itama sai kawai ta rungume ta tana fadin.
“Oyoyo, we welcome you into the Family dear, jiya mutane basu bar mu mun ganki ba.”
A yanzu ƙwaƙwalwar Amina kwancewa tayi gabadaya, don ita ko a gyangyadi bata taba kawowa haka abubuwa zasu kasance ba, ko jiya sai da su Aunty Ma’u suka gaya mata cewa tayi taka-tsan tsan da ƴanuwansa.
“Ƴan gayu ne na karshe Amina, kija jikin ki ki tsira da mutuncinki…”
Haka Aunty Ma’un ta raɗa mata a kunne.
To me yasa ne komai yake faruwa saɓanin tunaninta ne? Ko dai akwai wani abu da ba daidai yake tafiya bane?
“Sunana Munaya..”
Ta kara faɗa tana miko mata hannu, sai tayi karfin halin mika nata tana murmushi itama.
“Yanzu zaki ganta kamar normal mutum amma idan kika tabo wajen karatu zaki fara tunanin aljana ce.”
Samirah ta faɗa tana kallonta.
Sai kawai ta girgiza kanta.
“Yarinyar nan ta raina ni da yawa, kar ki yarda da ita.”
“Wallahi da gaske nake Aunty Amina idan kina da ƴanuwa a Buk ki tambaye su kowa zai ce miki ya san GB (Genius Brain) haka suke ce mata, irin ƙwaƙwalwar su ɗaya da Yaya.”
Munaya ta girgiza kanta tana murmushi.
“Astagfirullah, Allah ka tsare ni daga sharrin yarinyar nan, zo muje ku gaisa da Surayya, tana can tana ta aikin pressing waya.”
Da haka Munayan taja hannunta suka yi hanyar fita, Samurah ta biyo bayan su.
A falon wadda suka kira da Surayya na zaune kan kujera mai zaman mutum ɗaya tana ta faman danna wayar hannunta, daga ƙasa kuma wasu ƴan mata biyu ne su ma da kallo daya zaka yi musu ka san ƴan aiki ne, gabansau dauke da wasu trays din dake dauke da food flask har hudu da kuma jug na lemo shima kala biyu, alamu su suka shigo dashi daga motar da Samirah tace suke.
Kuma da shigowarsu Surayyan da zata ce sun yi sa’anni da Munaya ta dago da nata murmushin itama sannan ta ajiye wayar ta taho ta rungume ta, a yanzu Amina taji kamar ta saba ne ma da yanayin gaisuwar tasu.
“Na san ma wannan mai bakin ta gaya miki sunana koh?”
Ta tambaya tana kallon Samirah da tayi wajen ƴan aikin nan tana gaya musu akwai wata baƙar keda da badu shigo da ita ba.
“Nima tun kafin in shiga ta gabatar dani ai.” Cewar Munaya tana neman waje kan daya daga cikin kujerun.
Amina ta daga kai tana murmushi.
“Ta fada min, naji dadin ganin ki kuma.”
“Haba dai godiyar tamu ce ai, na san na samu wajen zuwa idan Mami ta matsa min da zancen waya, da fatan dai ba zaki damu ba idan kina ganina a compound din gidan nan.”
“You dey mad? Kike fada a gaban yarinyar nan? Kema kin san kamar Mamin taji ne ai.”
Cewar Munaya tana dariya, Surayya ta kalli Samiran dake tsaye tana jinsu.
“Ta gaya mata mana, itama ai tana da nata secret din a wajena.”
“Ba dai zancen wannan cake pack din Ya Salma bane, wlhy sai inyi confessing in fada, tunda idan nayi cake din ai har da Mamin ake ci ace yayi dadi.”
“What? Kayan Salman kika dauka? Amma bata sani ba har yanzu ko?” Cewar Munaya.
Surayya ta koma kan kujera tana sake ɗaukar wayarta.
STORY CONTINUES BELOW
“Ki bari kawai, kuma wallahi guda daya ne a cikin kayanta, ranar da ta nema ta rasa, inaga Yaya Ishaq za’a kira yayi aikinsa a gidan nan.”
Suka kyalkyale da dariya gabadayansu yayin da Amina ke tsaye har yanzu da jug din nan data dauko a hannunta tana taya su da murmushi.
A lokacin ɗaya yarinyar nan ta dawo daga waje. Samirah ta karbi kedar tana miko mata tace.
“Gashi Aunty Amina, cupcakes ne na san zaki iya yin baƙi a cikin satin nan, wadannan kuma abinci ne breakfast da Dinner, naga yayan ma ya fita, flask din da na kai Kitchen kuma miya ce a ciki, murfin suka balla yanzun nan da safe shi yasa na riƙo shi kar ta zube.”
Wannan karon Amina ta tabbata mamakin da take ciki ta kai ta har wuya tana shirin nutsewa.
“Kar ki wani damu idan yarinyar nan ce ina jin sai kin dinga korarta daga gidan nan akan abinci…”
Kafin Munayan ta karasa fada wayarta tayi kara. Sai ta miƙe tana cewa…
“Ya Shukra ce, kuzo mu tafi kafin ta fara mitar nan tata.”
Surayya ta mike kuma ga mamakin Amina sai suka zo suka sake rungume ta daya bayan daya suna gaya mata cewa in suka dawo zasu shigo sai suje cikin tare ta gaida su Mami. Itama ta rako su har kofa tana fadin su gaishe su.
Bayan sun fita, ta tsaya daga barandar falon tana kallon compound din gudan da yasha wasu interlocks masu ƙyalli, da kuma shukokin wasu kananan bishiyu a jikin katangar da basu fara girma sosai ba.
Ji tayi zuciyarta ta washe da wani abu da baza ta iya fassara shi ba, mamaki na yawo akanta har yanzu na yadda abubuwa ke canjawa daga zaton ta, kirkinsu yasa taji sun burge ta sosai yadda basu ɗauki kansu wani abu ba, taji zuciyarta na dokin ta saba dasu fiye da haka, kafin ta juyo ta dawo tana rufe kofar ɗakin, idonta ya kai kan tarin flasks din nan tana tunanin yadda zata yi da abincin, ko da yake ba ita kaɗai suka kawowa ba har dashi ta sani.
Zuciyarta ta buga da ta tuno cewar zai sake dawowa gidan ya same ta, ta tuno kallon da yayi mata har da murmushi da yadda taji a lokacin tana kasa tantance tsoro ne ko akasin sa… Ashe dukkan abubuwan da take hangowa da sauki sun sha banban da tunaninta…
Kwankwasa kofar da akayi ya katse tunaninta, ta tafi da sauri ta bude tana fatan su Maryam din da take jira ne, su din kuwa… Har da Hafsa dasu Mimi da Fatima da wasu daga cikin ƴaƴan Baban kurna, su takwas, sun riko wasu sauran tarkacenta da tsintsiyoyin nan… Ranta ya karasa yin fari ƙal ta hau rungume su daya bayan daya tana murna, rungume sun da bata san tayi ba sai da taji Fatima na cewa.
“A ina kika koyo wannan sabuwar gaisuwar kuma?”
Ita kaɗai ta cije lebbenta tana murmushi.
**
A cikin ɗakin Hajiya Kilishi, ta kalli kawarta Salamatu tana girgiza kai.
“Banbanci na dake kenan, bana faɗuwa na hakura, a sannu nake bin abu ina gutsira har in kai ga ci, kuma nasha gaya miki hakurin da kika kasa a tare da Shamsu (mijinta) kenan. Shi yasa har rayuwa ta kawo ki wannan gaɓar.”
Hajiya Salamatun ta girgiza kanta itama.
“Gaɓar da nake cin duniya ta da tsinke ba, kar ki kawo wannan zancen kuma bayan mun gama na Saratu, mu tattauna abinda ya kawo ni, Ya zaki yi da al’amarin ƴar tasa?”
Hajiya kilishi ta kalle ta sosai tace.
“Na gaya miki ai, saboda ban samu nasara akanta a asibitin nan ba hakan baya nufin na hakura, ai na rantse sai naga bayanta don ko wajen uw*rta ba zan bari ta koma ba tunda har zata fara zame min ƙalubale tun daga yanzu. Babu wanda ya isa ya shiga zuciyar Ma’aruf da tasirin da yafi nawa Salamatu kema kin sani.
Saboda haka matsalolin nawa zan hade guri guda, bayan tsinannun asibitin nan da suka hana ni kwana a wajenta sun sallame ta, wani Creche wai ya kaita a hanyar Bompai saboda kin san muna cikin sha’anin bikin nan. Saboda haka a yanzu da komai ya lafa zan saka ne ya dawo da yarinyar wajen ita Aminar, ta yadda zan aiwatar da manufata hankali a kwance.
Kin san dai dalilin da yasa na shiga na fita ya auri yarinyar nan, saboda daga ita har iyayenta zan iya juya su sannan an tabbatar min tana da sanyi halin da al’ummar gidan nan kaf zasu karbe ta cikin ƙankanin lokaci, na gaya miki tana da irin fuskata Salamatu, fuskar da zata daɗe tana yin abun da ba mai iya ɗora zarginsa akanta.”
Hajiya Salamatu ta kalle ta tsawon wasu sakanni tana nazarin maganganunta kafin ta girgiza kanta tace.
“Kin san nice mai gano miki da matsalar dake ba kya taba hangenta Kilishi, jiya da suka kawo yarinyar nan banga fuskarta ba, amma daga yanayin jikinta kawai na san ƙarama ce, kuma idan har halinta ne zai sa jama’ar gidan nan su sota, ba kya tunanin zuciyar yaron ma zata iya ta karkata kanta?”
Hajiya Kilishi ta gyaɗa kai tana murmushi.
“Daɗina dake ragon azanci Salamatu, ai dama haka nake so, in ba haka ba don me nake ta koɗa ta da ƴanuwanta a wajensa, so nake ta siye min zuciyar kowa har shi ɗin kamar yadda nima nayi, ta yadda a nutse zan sa ta dinga kai min saƙona kowacce kusurwa babu mai zarginta.”
Hajiya Salamatu ta sake girgiza kanta.
“Baki gane ba Kilishi, abinda nake nufi shine idan har ta siye zuciyar Ma’aruf da darajar da zata fi taki nauyi fa? Idan har yayi nisa a duniyarta ta yadda ba zai iya jiyo ko da muryarki ba fa?”
Wannan karon dariyar da Kilishi tayi sai da ta ratsa kowanne bango a dakin ta kuma fita ta windon ɗakin da yake a rufe, tabi iska zuwa nisan da ƙarfin amonta zai iya kaiwa, hatta jikinta sai da ya girgiza saboda nauyin dariyar, kafin ta kalle ta sosai tace.
“Ita kanta yarinyar ai na shirya mata Salamatu, sau nawa zan gaya miki ne Ma’aruf nawa ne ni kadai?!”2
***
Tafiyar ta fara! Insha Allah.