FARAR WUTA CHAPTER 5 BY AISHA MAHMOOD

FARAR WUTA CHAPTER 5 BY AISHA MAHMOOD

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Maamah don me yasa zai kira shi? Nace ya kira shi ne? Me yasa zai yi deciding abinda bai shafe shi ba kai tsaye?”+

Muryar Ruƙayya ta fito da ƙarfi a lokacin da take kallon ƙaninta Ahmad dake tsaye a gaban gadon da take kwance. A cikin asibitin da aka kwantar da ita ne, tun bayan lokacin data faɗi take asibitin ba’a sallame ta ba sakamakon hawan da jininta ke tayi babu sauka, don hatta fuskarta da kafafunta dukkansu a kumbure suke suntum.

“To hell with you and him! Shi waye da baza’a kira shi a gaya masa yayi ba daidai ba? Me yasa akan Ma’aruf ƙwaƙwalwar ki ba zata taba hankali bane Rukayya? Meye a duniyar nan ki gani a jikinsa da sauran maza badu dashi? I swear to God idan kika kara daga min murya a yanzu zan sake kiranshi na zage shi a gaban idanunki.”

“Maamah kina jinsa ko? Kina jin abinda yake faɗa?!”

Ta faɗa tana juyawa wajen mahaifiyarsu Hajiya Nafisa dake zaune daga gefe tana haɗa mata tea, idan da sabo ta saba da wannan fada a tsakaninsu, don ko Ashraf da yake sakon Rukayyan basa faɗa tare kamar yadda suke yi da Ahmad ɗin, shi mutum ne kaifi ɗaya mai tsatsatsauran ra’ayi, Rukayya kuma ba’a taka ta tayi shiru, don haka inuwarsu bata taɓa zama ɗaya.

A yanzu ma dalilin ɗaga jijiyoyin wuyan nasu, Ahmad ɗin ne ya zo ne yana shaida musu cewa shi ya sake kiran Ma’aruf akan zancen Hamida, tunda sunyi magana da Ashraf yace zai tuntube su kuma bai sake cewa dasu komai ba, don haka shi ya kira shi da ɓacin ran hakan wanda a ƙarshe wayar tasu bata ƙare da daɗi ba, don Ma’aruf ɗin har gargadi ya masa da cewar labarin zai canja idan har ya sake kiransa.

Ita kanta bata ga aibu a abinda Ahmad ɗin yayi ba, don Allah ya sani idan da Ruƙayya zata bata dama a lokaci guda ne zasu juya dukkan tanadin da suke mata akan Ma’aruf ita da kawarta zuwa sharri, zata fi jin karfin gwiwar cutar dashi akan abinda suke yi a yanzu, don haka ta cigaba da haɗa mata shayin kawai tana jinsu, tana ji kamar Ahmad na furta rabin kalaman dake cikin ranta ne da ba zata iya faɗawa Rukayyan ita da kanta ba.

Kuma sai da taji kalaman nasa na shirin yin tsauri da yawa sannan ta kalle shi tace.

“Ahmad, fita daga wajen nan.”

System ɗinsa da ya ajiye akan Fridge din ɗakin bayan shigowarsa ya ɗauka cike da fushi sannan ya nuna Rukayyan da ɗan yatsa tace,

“Daga yau kar ki sake kirana a matsayin danuwanki duk sanda wani abu ya haɗa da mutumin nan, idan ba haka ba daga ke har shi I’m gonna rip your as* off! (Zaku gane kuranku!)”

Da haka ya fice tana bugo ƙafar ɗakin asibitin, Rukkaya ta koma da baya ta rufe fuskarta da duka tafukan hannayenta biyu lokacin da Hajiya Nafisan ke miƙo mata kofin shayin.

“Kin san halinsa ai sarai, amma kika biye masa kuke ɗaga murya a cikin asibiti, na sha gaya miki da kin ga ransa ya ɓaci kawai ki rabu dashi, wannan shine girman.”

STORY CONTINUES BELOW

Ta girgiza kanta a hankali sannan ta buɗe fuskar tana karbar kofin.

“Maamah ba zan iya shiru akan abinda yake fada ba, kina ji fa yace har gargadi Ma’aruf yayi masa, to waye ya san iyakar abinda ya gaya masa ma? me yasa zai sake ɓata min al’amura ya sake ɓallo wani abu kuma?”

Ta ƙarasa tana karɓar shayin, kuma garɗin abubuwan da aka cika masa da kuma ɗuminsa ya sauka har cikin ƙirjinta, ya sanya ta lumshe idanuwanta a hankali kafin ta buɗe su sosai akan kofin, da ɗaya hannun nata shiga murza bakinsa a hankali ba tare da ta kalli Mahaifiyar tata ba tace.

“Maamah kince kawai aura masa yarinyar akayi ko?”

Taji sanda Hajiya Nafisan tayi ajiyar zuciya kafin tace.

“Tabbatar min akayi cewa a cikin sati uku akayi komai, ance bai taba ganinta ba ma har aka daura auren, sannan yarinyar bata da wani daraja, mahaifinta ance irin sana’ar ƙananun aikin katakon nan yake yi, don haka na tabbatar miki akwai wata manufa ta daban dangane da auren nan da bamu sani ba, amma ba wai aure yayi irin wanda kika sani ba.”

Wannan karon Ruƙayya rufe idanuwanta tayi duka, tana jin yadda wani tiririn zafi na daban da yafi karfin shayin dake hannunta yana cigaba da zurara a cikin ƙirjinta yana kona duk inda ya bi.

“Nima na sani ba auren gaske bane Mami, don wallahi na san babu ta yadda za’ayi yarinyar nan ta shigo cikin tsarinsa, a yanayin arzikinsa dana gidansu ko haukacewa yayi akwai ƴanmatan sa suka fita daraja da yawa da zasu so shi a haka.”

Shi yasa bana son inyi wasa da kowacce irin dama Mami, a yanzu ban damu da duk hanyar da zamu bi mu lalata komai ba, don ban damu da manufar kowa ba, burina kawai kada yarinyar nan ta daɗe a rayuwar Ma’aruf, don ta haka ne kawai zan iya cimma burina Maamah, idan akwai ta, na sani ba zan taɓa iya samun abinda nake so ba.”

Kafin Hajiya Nafisan dake kallonta tace wani abu, ƙarar ringtone ɗin wayarta ya cika ɗakin, don haka ta dauko wayar tata dake gefen bedside drawer ta miko mata, Ruƙayya ta karba tana kallon sunan da ya fito akan screen ɗin, Jawad… Taji ranta ya ƙara dugunzuma ya ɓaci a take, bata san wane irin mutum ne shi marar zuciya haka ba? Me yasa zai cigaba da damunta alhali da kowanne yare da zai iya fahimta ta gaya masa cewa ya rabu da ita? Sai kawai ta danne buttton ɗin wayar gabaɗaya ta kashe ta sannan ta ajiye ta a gefe.

Takaicin dake cike fal da tausayin ƴar tata ya nuna akan fuskar Hajiya Nafisa kafin ta girgiza kanta a hankali.

“Na gaya miki ki kwantar da hankalinki ki samu sauƙi mu koma ki gida, don Hajiya Saude ta gaya min sai da haɗin kanki tukunna sannan komai zai daidaita, nayi miki alƙawarin Ma’aruf da ƙafarsa zai tako har inda kike ya neme ki.”

Wani abu kamar murnushi ya fito kan lebben Ruƙayyan yayin da ta sake jingina kanta baya da jikin gadon kafin a hankali kuma ta ɗago da kofin shayin nan ta kai bakinta.

Daga can jihar Abuja, a cikin gidan rawar da Jawad yake a can sama, inda yaken wani lungu yana zaune akan luntsememiyar kujerar wajen shi kadai, a gabansa wani haddadden kwandon shisha ne da yake zuƙa yana hurawa lokaci zuwa lokaci, a ɗaya hannun nasa kuma wayarsa ce da hasken screen ɗinta ke haska fuskarsa yayin da yake danna number guda cikin contact list ɗinsa ana kuma maimaita masa abu guda daga daya bangaren wayar.

“The number you’re trying to call is currently switched off, Please try again later.” (Lambar da ake kira a kashe take, a sake gwadawa bayan wani lokaci.)

Hannunsa ya sake danna number yayin da aka sake maimaita masa maganar.

“Jawad?? For real? Kai kadai anan sama? Na zata wasa su Sa’id suke da suka ce kana nan ai.”

Wani abokinsa da suke kira da Haro ya ƙaraso daidai wajen yana zama daga gefen kujerar, bai ce dashi komai ba don haka ya sake kallonsa yace.

“Naji rumours din, it was bad man, amma bai kamata hakan ya dame ka ba, kar ka jawowa kanka depression.”

STORY CONTINUES BELOW

Sai a yanzu Jawad ya juyo ya kalle shi, ya san abinda yake magana, jita-jitar dake yawo cewa za’a cire mahaifinsa daga kujerar Minister, har a tunaninsa abinda zai dame shi kenan? To me zai same su idan an cire shin tunda ko a yanzu sun tara dukiyar da ya san har su mutu ba zata kare ba, ya zuki hayakin ya fesar sannan yace.

“Kar Allah yasa a fasa cire shin, al’amarin wannan tsohon ya isa ya dame ni ne Haro? abinda yake gabana daban.”

Kan shishar Haro ya karɓa yana dariya sannan yace.

“Pray tell.”

Sai kawai ya jefo masa wayar hannunsa shima sannan ya jingina da kujerar. Haro ya cafe wayar sannan ya kalli screen ɗinta, kuma sunan da ya karanta na farko akan call log din ya sashi jan tsakin da bai shirya ba.

“Ban san ranar da asirin da yarinyar nan ta naka zai karye ba Jawad, har sau nawa zan gaya maka ka rabu da wannan tsilar abar, ub*n me zata tsinana maka da baka samu ba a duniyar nan? You’re young, kana da kudi, kana da status mai kyau, kana kan lokacinka Man, sannan babu yarinyar da zaka kalla duk kasar nan ka kasa samunta. Me yasa ba zaka yi hankali ka fahimci cewa wannan yarinyar sharri ce ma a rayuwarka ba?”

Jawad ya lumshe idanunsa ya bude yana saurarensa ta cikin sautin kidan dake tashi daga can kasa kuma sai da ya kai har karshe sannan ya girgiza kansa, idanunsa na kallon fitilar dake samansu mai kala-kala a cikin duhun wajen yace.

“Ba zaka gane ba Haro, ba zaka gane abinda nake ji bane, na rantse da Allah idan Ruƙayya bata aure ni ba, ba zata sake auren kowa ba a duniyar nan!”1

***

“What do you find? Me ka samo?”

Faruk ya tambaya riƙe da Tab ɗin hannunsa yana kallon Ma’aruf dake kokarin fitar da lissafin da suka kwashe fiye da awa guda suna yi akan kamfanin wasu abokan kasuwancinsu da suka gano cewar suna da nasu kamashon cikin wannan mummunar asarar da har yanzu suke bincike akanta.

Suna zaune ne daga cikin office din Ma’aruf ɗin, bayan kusan jiran awa uku da Faruk din yayi yana jiran dawowar Ma’aruf da ya bar office din tun kusan sha ɗaya na safe.

Kuma sai da ya dawo sannan ya buɗe email dinsa ya karanta bayanan da Martha sakatariyar tasa ta turo masa sannan suka fara haɗa komai suna tarawa da ƙaiyadewa.

“So shi wannan Mr. Ishmael Grahm ɗin shine ya karbi aikin accountant ɗinsu a farkon shekarar nan kenan kuma sunansu ɗaya da wanda ya tafi har surnane ɗin.”

Ma’aruf ɗin ya faɗa, idanunsa manne da tab ɗin gabansa yayin da muryar tasa ta fito kamar ta ƙwace ne daga cikin tunaninsa.

“What a ina ka ga hakan? Dama sun canja accountant ne? When?”

Faruk yayi tambayoyin yana komawa cikin kan tasa wayar.

“A cikin wanda ka min sending zaka duba, anyi naming dinsa 13th March na wannan shekarar.”

Kuma sai da Faruk din ya kusan zuwa can ƙasa wajen nemowa kafin ya isa inda yake gaya masan, idanunsa suka ƙanƙance yayin da yake karanta bayanin dake wurin.

“Bala’i! B ya akayi hankalinka yaje wajen nan, I was goung through it fa tun safe amma wallahi ban gani ba.”

“Shi yasa na gaya maka na kusa korarka daga aikin nan, ban san me yake ɓata maka tunaninka ba kwana biyu.”

Dariya Faruk ɗin yayi yana cigaba da karantawa kafin yace.

“Aikin Shahida ne wallahi, tunda ta yaye Aarif nake ji kamar watannin farkon auren mu muka koma.”

A lokaci guda Ma’aruf ya tsaya da karanta abinda yake yi ya juyo ya kalle shi, sai kuma ya girgiza kansa sannan yace.

“Baka da hankali Faruk, na daɗe ina gaya maka.”

STORY CONTINUES BELOW

Faruk ɗin ya sake yin dariya yana daukar tambulan ɗin lemon da Martha ta kawo musu kafin yace.

“Inji wanda yake amsa sunan sabon ango, you didn’t even tell me ya yarinyar take.”

Yaya yarinyar take. Maganar ta sake tuno masa da fuskarta a yau da safe kafin ya fito, sati guda kenan da yin auren, kuma a cikin sati gudan nan baya jin magana ta haɗa su wadda tafi kirgen cikin yatsu, wani lokacin dai su kan haɗu da asuba idan jamlock ɗin kofar falo ya rufe bayan ya fita masallaci, zata zo ta buɗe masa idan yayi knocking sanye da dogoon hijabinta har kasa, ranar farko bata ce dashi komai ba, amma a rana ta biyu ne ta fara gaishe shi. Sannan kuma sau da yawa idan ya koma da daddare zai ganta, har ya fahimci wani lokaci ma tana fitowar ne kawai don ta gaishe shi.

Bayan hakan maganganun da suka haɗa su baya jin sun wuce biyar, ya san ranar juma’a da zai fita masallaci ya tambaye ta dardumar sallah ta dauko wata sabuwa kuwa fil mai laushi ta kawo masa, sai kuma ita da ta tambaye shi Panadol ya fita da kansa ya siyo mata, amma bayan hakan baya tunanin wata maganar ta kara hada su don baya son ya takura ta ko kadan, so yake hankalinta ya kwanta ta fahimci cewa da gaske ba abinda zai mata, don a o farkon nan ya lura cewa da gaske a tsorace take dashi.

Ya rasa irin tasiri kalamansa suka yi a zuciyarta, ya kasa gane ma me yasa ta yarda da auren idan har tana tsoronsa haka, wataƙila laifin tun na wannan ranar ne, da ta fito ya ganta, da tun a lokacin zai san tayi ƙanƙanta yayi mata wannan barazanar, don haka yake son da kanta ta karkade duk wani tunani da take yi game dashi da kuma damuwar kalaman nan.

A shekaranjiya da yaji tana waya da wata tana yi mata bayanin cewa har yanzu bata fara girki ba, a cikin muryar tata yaji da wani abu kamar damuwa, wani abu da ya tsaya masa a rai yasa yasa ba shiri a lokacin da ya shiga cikin gida yaji Mami na yiwa Malam Sani lissafin cefenan wata, ya bishi a baya ya ƙara masa wasu kuɗin yace duk abinda ya siya na cikin gidan ya sake siyan rabin sa ya kai mata. 

Komai na wannan auren daban yake da lokacinsa da Rukayya ya sani, babu abu ko guda daya da zai danganta shi da farkon wancan ɗin, kamar komai ɗin yana zuwa ne a kishiyar ɗayan, sai dai abu daya kawai zai iya dorarawa shine a yanzu yana jinsa mutum mai ƴanci tunda babu ruwanta dashi sabanin a wancan da kwanakin farko suka sa shi yaji kamar an tsare shi a wani waje ne da lissafin abubuwan da ya kamata yayi.

“Kaji ai matsalata da kai kenan, da an taɓo wani zancen ba na aiki ba you lack interest, na tabbata da nayi ta jiranka ma anan wani aikin ka tafi yi.”

Faruk ya faɗa yana jawo shi daga cikin tunaninsa, kuma ba tare da ya juyo ya kalle shi ba yace.

“Saboda ni ba mutum bane kenan bani da wasu personal problems, to ka leƙa motata ka gani wanki naje na karɓo sannan na karbo ɗinki, har B&L naje samo maigadi, sannan na tsaya a zoo road nayi aski.”

Faruq ɗin yana nazarin sumar kansa da banbancin ta kaɗan ne da yadda ya ganta jiya, yace.

“A haka wannan gashin naka an aske shi?”

Ya girgiza kansa har yanzu bai kalle shi ba yace.

“A’a fixing nayi.”

Sai kawai Faruq ɗin yayi dariya sannan ya juya kan tasa tab din dake blinking alamun shigowar wani sabon saƙon, suka cigaba da tattauna duk abinda ke gabansu har magariba ta tadda su anan, wanda kafin magaribar suka yi sa’ar ganowa cewa tabbas wannan kamfanin sun karbi kaya na maƙudan kuɗaɗen a hannunsu kuma dukkan receipt din kudin an saka adadin kudin daidai, har ma da alert din shigar kudin cikin bankin kamfanin, amma takardar da Faruk ɗin ya gano cewa an duba balance a wancan lokacin kuma kudin bai kai ba, ita ta daure musu tunani. Don basu san yadda za’ayi alert ya shigo da wani adadin kuɗi ba alhali ba hakan aka turo ba.

STORY CONTINUES BELOW

Anan suka tsaya kasancewar magriba ta taho kusan kowa a Office din ya tashi tunda dama a ƙa’ida ƙarfe biyar ne lokacin tafiyar kowa.

A wajen Hamida ya daɗe bayan yayi sallar magaribar, kuma wannan karon har nuna alamun cewa zata biyo shi tayi, ransa ya cika da farin ciki kafin ta ƙarasa da cewar zata bishi ne ya kaita wajen Maminta, kuma Allah kadai ya san sau nawa ya zura hannunsa cikin gashinsa ya fito dashi kafin ya iso gida, don game da al’amarinta bashi da wata mafita ko kaɗan, abu ɗaya ya sani shine ba zai taɓa iya sake rabuwa da ita ba ko da me Ruƙayya da iyayenta zasu tunkare shi.

Ya tuno wayar da suka yi da Ahmad kanin Ruƙayyan a jiya, yaron bashi da hankali ya daɗe da sanin hakan, tunda har sunyi magana da Ashraf ya gaya masa cewa zai neme su bai ga dalilin  da zai sa shi ya sake kiransa ba, kuma  yadda yake masa magana ma ji yayi idan akwai wani mataki da yafi na haukan, zai iya saka shi a wannan layin, don haka ƙarara yayi masa gargaɗin cewa zai iya sawa a kama shi idan har ya sake kiransa da wannan batun.

Ya riga ya sani cewa duk cikinsu babu wanda zai iya ja dashi don yana da da hujjar da zai kaisu ƙasa ko a gaban waye za’a tsaya, bama wannan ba ya sani cewa babu inda Ruƙayyan zata je ta samo karfin halin da zata iya fuskantarsa a yanzu, tana yawo ne da nauyin waɗannan kalaman ɓoyayyiyar yarjejeniyar da suka yi kamar yadda koda da rana guda shima bai taɓa manta su ba.

Ya isa gida bayan ya tsaya a wani masallaci yayi sallar isha’i, ya shiga da motarsa ciki sannan ya fito ya rufe gate din yana takaicin yadda sai wani satin zai samu maigadi kamar yadda kamfanin suka shaida masa.

Kuma bayan ya ɗauko wayoyinsa biyu daga cikin motar ya dade tsaye a wajen yana waya da Ishaq, a yanzu haɗuwarsu ta ɗanyi wuya, yana ta yawon zuwa Abuja ne akan wani workshop da suka fara a kotun tasu, don haka a cikin satin ma sau daya kawai suka haɗu.3

Magana suke tayi akan gininsu, wasu filaye da suka siya a Lamiɗo Cresent ana musu gini iri ɗaya, bayani yake yiwa Ishaq ɗin cewa zasu canja masu gini don na yanzun an basu kudin kaya mai kyau amma sun siyo wani siminti da bashi da kyau har wani waje a cikin ginin Ishaq din ya rufta. Daga karshe suka tsaya akan Idan ya dawo zasu fara neman wasu ma’aikatan kafin suyi sallama da kalaman da Ishaq din ke gaya masa a mafi yawancin ƙarshen maganarsu.

“Dan Allah ka kula B.”

Ya cije leɓɓensa yana kallon wayar, har yanzu Ishaq bai yarda dashi ba ya sani, gani yake a kowanne lokaci wani abu zai iya faruwa saboda yanayin ciwon nasa, amma shi baya jin hakan, akwai abubuwan da yawa a gabansa amma baya jin sunyi yawan da a cikinsu zai iya samun abinda zai canja yanayinsa, don haka yana amsa masa ne kawai don ko yayi bayanin ba zai yarda dashi ba.

Ya kashe wayar sannan ya debo kayansa na cikin motar ya shiga ciki da ƴar karamar sallamarsa, babu kowa a falon amma ƙamshin turaren wutar daya kula kwana biyu ana yinsa a gidan ya shiga hancinsa. Yayi sallamar da babu mai amsa masa sannan ya cire takalmansa daga gefe ya taka zuwa ciki, zuwa hanyar korodon nan, fitilar dakinta a kunne take kamar kowanne lokaci irin haka idan ya dawo, ya jiyo motsinta daga ciki har da ƙara ma kamar wani abu ya fadi kafin ya zarce zuwa dakinsa.

Wanka zaiyi ya fito ya shiga cikin gida, a can wajen Mami yake cin abincinsa kullum, kafin ya fita dai ya san watakila zai ganta su gaisa, amma zuwa lokacin da zai dawo ma ta riga ta kashe fitilar dakinta ta kwanta, ta kasan kofarta yake ganin hakan idan zai wuce. Ya isa ɗakin nasa lokacin da yake tuno maganganun Baffa sanda yake masa fadan rashin halartarsa wajen daurin auren nan, Baba Usman yana daga gefensa yake cewa.

“… Idan kana tunanin zaka wulakanta yarinyar nan saboda iyayenta ba masu arziki bane Muhammad, ina so ka kalli iyayenka biyu da suke cikin gidan nan, daga ita Kilishin har Maimunan da ta haife ka, ka gaya min waye ya fito daga gidan mai kuɗi, ko kuma ni kaina da nake mahaifinka, ka gaya min gidan iyayena na gado da yake Bakori yaya yake, Mahaifina har ya mutu ɗakin kwanansa na ƙasa ne bai ko kai girman ɗakin nan ba ka sani.

STORY CONTINUES BELOW

Saboda haka na daura aurenka da yarinyar nan ne saboda shaidar halayen kirki da aka yi mata ita da iyayenta, ba don abin duniya ba babu ruwana da abinda mutane ke faɗa wai kwarya tabi kwarya, zaman aure nutsuwa da kwanciyar hankali ake nema a cikinsa ba suna ba, game da aurenka na farko kaima shaida ne akan hakan, don haka ina rokonka kar ka bani kunya a karo na biyu Ma’aruf.”

Ya rufe idanunsa lokacin da ya saki ruwan shower akansa, indai Baffa zai kira shi da sunansa na asali ya sani cewa babban al’amari ne.

***

Doguwar riga ce a jikin Amina ta atamfa kalar milk da sea green, ta daura dankwalin sannan ta yafa wani karamin mayafi shima kalar sea green ɗin da ya tsaya iya kafadunta, ba kwalliya tayi ba don babu ko hoda a fuskarta amma fatar ta da’a kwana biyu ta kara washewa sakamakon canjin ruwa tana haskawa tare da fararen idanunta, kuma kawai ta yafa mayafin ne don bata son fita haka, taji lokacin da  Ma’aruf ya shigo, har wucewarsa ta gani ta kasan ƙofar dakin daidai lokacin da robar vaseline ɗin dake hannunta ta subuce ta fadi.

Sati guda kenan da fara rayuwarta tare dashi amma har a yanzu duk sanda ya fita ya dawo sai taga kamar shine ganinta dashi na farko, taji zuciyarta ta kasa tsayawa waje guda duk da cewar wannan taraddain da take ji a farko ya fara tafiya, don bata san me yasa ba komai yazo ne sabanin tunsninta kuma lokaci yana saukaka mata abubuwa fiye da zatonta.

Ko kaɗan bata ga wani yunƙurin cutar da ita a tare dashi ba, hasalima harkokin gabansa yake, da sun gaisa shikenan ba zai kara bi ta kanta ba. Ita kanta ta fara sabawa da gidan a yanzu, ranar da su Fatima suka zo sun taya ta sake kimtsa komai nata, sauran kayan kwalliyar nan da jakunkuna da takalman dake cikin Ghana must go ɗin nan duk an samar musu wajen daya dace dasu, ta basu kayan kwalliyar ma da yawa da kuma wasu daga cikin undies din.

Sannan a kitchen ma sun jera komai a muhallinsa, store din ya zama babu komai sai iya abubuwan da ba lallai amfaninsu yazo a kusa ba, bata san adadin mamakin da tayi ba na yawan ganin kayan, don bayan wanda aka siya mata kusan duk wanda zai kawo wata gudunmawa kayan kitchen ɗin ne, don haka har wasu abubuwa ta ware a cikin ranta cewar zata ajiyewa Maryam idan lokacin nata auren yazo.

Sauran ɗakunan nan biyu ashe ɗaya carpet ne kawai da labulaye da kuma su tintin a jere, sai ɗayan ne aka tsara shi da wani irin nau’in furnitures masu tsananin kyau da ɗaukar ido, komai kalar grey, milk da kuma ash ne, wani silk bedsheet din da aka shimfide gadon dashi yana ta daukar ido a cikin hasken fitulum ɗakin, Aunty Safiyya bata sani bane da take cewa tayi zamanta a dakinta, dama ba’a tsara wannan don ita ba, shi suka yiwa abinsu, don har wasu fitulu aka saka a tsakiyar ceiling ɗin dogwaye masu haske, ga kalar fentin shima grey ne, labulayen kuma milk gabaɗayansu.

Kasa rufe bakinta tayi a lokacin da su Ummi ke cigaba da santin ɗakin daga inda suka tsaya  a bakin kuma ƙaton akwatin dake ajiye akan gadon, shi ya hana kowannensu shiga don ba sai ta gaya musu ba sun riga sun gama sanin dakin na waye.

Ta fita ɗakin ta rufe kofar a hankali kamar mai tsoron kar a jita sannan ta nufi hanyar kitchen, daga tsakiya akan work table ɗin nan tray din dake dauke da  flask din abincin da ta gama ne, a yau zata danne zuciyartaa tayi abinda ta kasa jiya, shekaranjiya ya aiko aka kawo kayan abinci kamar ya san dana ta matsu ta fara girki da kanta, don haka kai tsaye ta gayawa Samirah cewa ta huta tunda dama ita ke kawo mata abinci kullum, abincin da ita kadai take ci don ko yana sanin an kawo ɗin ma bai taɓa tambaya ba, ta fahimci idan ya dawo yayi wanka wajen Mami yake tafiya yaci abincinsa sannan ya dawo.

Don haka ko jiya da tayi girkin, har dashi tayi amma tana ɗaki tana biya abinda zata ce masa taji ya buɗe kofar falon ya fita, haka ta debi abincinta ta rufe a fridge, amma yau ta gama shirya cewar ba zata bari ya fita ba, ba don komai ba sai don tarin nasihohin nan da aka yi mata suna ta yawo a cikin kanta, gani take kamar laifi take idan zata yi girkin babu shi, don akwai nasa hakkokin akanta kamar yadda shi ya sauke nasa wajen kawo abincin.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan haka ma, ta karanci kalolin kayautata zamantakewa fiye da adadi a wajen Ammarta, abinda ke cikin zuciyarta kenan fal kuma dashi tayi tunanin zata iya cin galabar komai dama, har yanzu bai nuna wata alama ta cutar da ita ba don haka don me yasa ita zata fara da abinda bai dace ba?

A cikin addu’o’in da Gwaggo Balkisa tayi mata tace ‘… Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa..’

To idan bata kyautata masa ba ta yaya zai ji tausayin nata, Me ƴan uwansa ma zasu yi tunani idan hakan ta cigaba? Idanunta suka hasko mata Hajiya Kilishin da yake zuwa wajenta yaci abincin, bata san me yasa ba ita har yanzu zuciyarta bata kwanta da ita ba, ranar da su Samirah suka fara kaita wajenta, hannayenta duka biyu ta kamo tace.

“Barkanki da zuwa cikinmu Amina, zuciyata cike take da murna idan na tuna cewa ƴa ta na kawo gidan nan ba kowa ba, ki saki jikinki ki saba da kowa, don a gidan nan bama taba banbanta kanmu, kowa ɗaya ne kuma kowa yana samun tallafawar ɗan uwansa saboda ƙaunar dake cikin zuciyoyin mu, kuma kema kin shigo kenan cikin wannan lissafin namu, rayuwarki zata canja da dukkan alkhairin da dake tare damu, kuma ina fatan kema zaki bamu damar amfana da irin naki alkhairin.”

Haka kurum a lokacin sai taji maganganun basu tafi har cikin zuciyarta ba, sai taji kamar sun tsaru da yawa ace kai tsaye take faɗarsu daga zuciyarta a wannan lokacin, amma ko da ta daga ido ta kalli fuskarta, sai zuciyarta ta ture wannan kokwanton a gefe, tana tuna mata cewa itace wannan Hajiya Kilishin da ta tallafi rayuwarsu ta ɓangarori da yawa.1

Hajiya Kilishin da kullum Baba yake ambato da kyawawan kalamai sannan kuma kamar yadda ta gani ta itace jagorar wannan gidan, don a yinin yau kawai ta fahimci abubuwa da yawa sai da izininta ake yi, don haka saboda tana ganin itace umul’abasin faruwar wannan auren bai kamata zuciyarta tayi wannan tunanin ba.

Amma Allah ya sani da suka shiga wajen Hajiya Maimunan wadda aka gaya mata itace asalin mahaifiyar Ma’aruf, zuciyarta kusan narkewa tayi tun kafin ta kai ga zama, mace ce har mace, irin manyan matan nan masu tsananin kamala da nutsuwa, fukarta fuska ce da za’a iya amfani da ita a koina a fadin duniya ta wakilci kalmar ‘Uwa a rayuwar bahaushe’ sai dai babu ƙafafu, tana zaune kan Wheelchair ɗinta da Hisnul Muslim a hannunta.

Kuma abinda ya bata mamaki shine itama da fara’arta da komai itama ta karɓeta, tana ta zuba tarin addu’oin fatan alkhairi da kuma fatan zaman lafiya a tsakaninta da Ma’aruf, wani abu data lissafa cewa yayi ƙaranci a kalaman Hajiya Kilishi.

Sai kawai ta ture wannan tunanin ta dauki tray din ta taho falon, sai da ta tsaya tana ta tunani inda zata ajiye kafin ta tsugunna a hankali daga gaban Three-sitter dake gabanta, kuma tsugunnawar tata tayi daidai da fitowar Ma’aruf daga falon, ta dago da kanta lokacin da kafafunsa suka tsaya cak yana kallonta daga hanyar kofar da ya nufa.

Yayi wankan, ya canja yansa zuwa wani bakin wando da dark navy blue riga data dace da kalar daren, kallonta yake yi da mamakin dake nunawa karara a fuskarsa, sai kawai tayi saurin ƙarasa ajiye tray din sannan ta mike tsaye itama. Kanta a sunkuye hannayenta cakude da juna tace.

“Barka da dare.”

A cikin shirun dakin muryarta ta fito kamar wani fukafikin dake tahowa kasa a hankali, Ma’aruf ya gyada kansa yana kallonta har yanzu da mamakin a fuskarsa kafin ya amsa da.

“Kin yini lafiya?”

Haka yake tambayarta kullum,  don haka ta gyada kanta ba tare da ta dago ko ta daina cakuɗa yatsunta cikin juna ba, kuma sai tayi shiru bata ƙara cewa komai ba. Amina ta san ya kamata tace wani abun game da abincin da yake kallo a gabanta amma bata san me zata fara cewa ba, kuma ga mamakinta sai kawai taji yace.

“Wannan abincin…”

“Naka ne…”

Ta ƙarasa da sauri tana ɗago da kanta, idanunsu suka haɗu waje guda sai tayi saurin sake maida kanta kasa ta cigaba da murza yatsunta, amma zata iya karanta mamakin daya karu cikin muryarsa sanda yace.

STORY CONTINUES BELOW

“Masha Allah, kamar kin sani dama yunwa nake ji.”

Wani abu a cikin zuciyarta yayi tsalle da jin hakan, yayi kokarin subucewa daga zuciyarta zuwa kan fuskarta amma ta tare shi da karfi tana cigaba da motsa hannunta, ƙarar takunsa taji yana tahowa don haka tayi saurin tsugunnawa ta ɗauki plate din tana bude murfin flask ɗin farko.

Ƙamshin abincin ya shiga hancin Ma’aruf sanda ya karaso kan carpet din, idanunsa na kallonta tana zubawa yayin da ƙaramin mayafin data yafa kalar kayanta ya zame yana reto a gefen fuskarsta, wani abu yake ji na daban yana shiga zuciyarsa bayan mamaki, sai kawai ya zube wayoyin hannunsa akan kujerar sannan ya ƙarasa kan kapet ɗin gaban abincin ya zauna, ƙamshint turarenta mai sanyi ya shiga hancinsa tare da na abincin don a yadda ya zauna tray ɗin shi kaɗai ya raba tsakaninsu.

Kuma bai ce mata komai ba, yana kallonta ta zuba iya adadin da take so na komai sannan ta ture tray din gefe a hankali ya tafi cikin laushin carpet din kafin ta ajiye plate din a gabansa. Shinkafa ce fara da vegetables a ciki sai kuma miyar dake tashin ƙamshin daya baɗe falon a lokaci guda, akwai wani abu a dan bowl data zuba na cabbage da kuma Irish potato mai hade da nama duk da wanda yake cikin miyar.

Wani abu ya motsa a cikin zuciyarsa cike da yabawa kokarinta dama abincin tun kafin ya kai bakinsa, yana tuna masa da wani al’amari daya shuɗe a labarin aurensa na farko, ba kai tsaye ya samu irin wannan gatan ba.

“Thank you so much.”

Muryarsa ta furta a hankali da wani sauti da yasa numfashin Amina katsewa a kirjinta, ba shiri ta gyada kanta sannan ta mike da sauri.

“Ina zaki je?” Shima yayi tambayar kamar kai tsaye bai shirya mata ba.

“Zanje in kawo ruwa ne.”

Muryarta ta fito tana fallasa bugun da zuciyarta ke yi, kuma kafafunta basu motsa ba sai da ya ɗaga mata kansa.

Ta isa kitchen din ta ɗauko robar ruwa guda ɗaya da ba’a fridge ba, don ta kula duk sanda zata ganshi da ruwa a hannunsa to ba mai sanyi bane, shi yasa lemon data haɗa ma ta kaishi can kasan fridge din baiyi sanyi sosai ba, Samirah ce ta koya mata hada lemon, kuma ta tabbatar tayi komai daidai, sai dai bata san dadinsa ko akasin sa ba tunda bata taba sha a wani waje ba.

Ta isa falon lokacin da idonta ya sauka akansa ta baya ya kai lomar da bata san ta nawa bace cikin bakinsa, zuciyarta ta kara nutsewa cikin kirjinta da tsarin nata ya tafi daidai, a hankali kafafunta suka ƙarasa kan carpet din, tana jin yadda kafar tata ke shigewa cikinsa saboda laushin sabunta. Wannan karon nesa kaɗan dashi ta zauna sannan ta fara ƙoƙarin zuba lemon a kofi.

Ma’aruf ya dago ya kalle ta, har yanzu mamakinta bai bar kan fuskarsa ba, kuma a lokaci guda yaji kalaman da Mamin ta taɓa gaya masa suna dawowa cikin kansa.

… Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma’aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata.

Abinda Mamin bata sani bane, ita kanta Rukayyan tayi iya kokarinta a zamansu, don ta canja abubuwa da yawa a rayuwarta zuwa bukatarsa, matsalar kawai shine don son zuciyarta tayi komai, babu abinda tayi saboda shi ko don ta kyautata masa, don haka itama zai iya yiwuwa ta fara hakan ne don an saka ta, don bin umarnin da ya tabbatar shi tayi har auren nasu ya kasance, yaji zuciyarsa ta matse da wannan tunanin amma kuma sai ya samu sauƙi da hasashen cewa haka ba zai iya zama gaskiya ba.

Ta gama zuba lemon a wannan lokacin, ƙarar awarwaron dake hannunta ya janyo hankalinsa sanda take ajiyewa a gabansa daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga kan kujerar nan, don haka tayi amfani da damar don miƙewa ta bashi waje amma sai muryarta ta tsaida ta.

“Ki zauna.”

Fuskarsa fayau yana kallonta kafin ya juya ya dauki wayar. Ta haɗiye wani abu a makogwaronta a hankali sannan ta dawo da baya ta zauna ɗin, nesa kaɗan dashi kamar ɗazu.

STORY CONTINUES BELOW

Ya ɗauki wayar yana magana ta ciki, ta fahimci da wani yake magana kuma akan harkar aikinsu ne bayan hakan bata gane komai ba, amma kuma yanayin yadda yake maganar ya saka taji zuciyarta na sakewa da amon muryar tasa. Ya gama wayar ya ajiye ta a gefensa sannan ga mamakinta taji yace.

“Faruq ne, abokina ne a wajen aiki.”

Sai ta daga kanta lokacin da ya sake kai wata lomar bakinsa sannan yace.

“Abincin nan yayi daɗi sosai Amina. Kinyi kokari.”1

Wani abu ya matse a zuciyarta daga yadda muryarsa ta ambaci sunanta, kamar zata yi magana amma kuma sai ta sake gyada kanta kawai tana wasa da karshen mayafinta. Kuma Yanayinta yasa Ma’aruf yaji a lokaci guda yana son suyi hira, aƙalla yau maganar tasu ta tsallake babin gaisuwa saboda haka yana kallonta yace.

“Munaya ta gaya min kina son karatu, tace ta samu wasu novels a wajenki. kina da litattafai da yawa.”

Sai da sakanni biyu suka wuce sannan Amina ta yarda da maganar da ya furta saboda ɗan mamakin da ya kamata, ranar da take kokarin samawa litattafanta waje ne Munayan ta shigo ta ganta, a ciki har da wasu English novels dama na Hausa wanda take tarawa tun tana makaranta, shikenan sai suka shafe kusan rabin yinin suna hirar labarai kala-kala har ta ara mata wasu ma ta tafi dasu, don haka ta tabbata a yanzun ma ganinta yayi tana karatun ɗaya daga cikin wanda ta ɗauka.

“Wanne da wanne kika karanta?”

Muryarsa tana fitowa ne kamar yadda take jinta a kullum idan yana waya ko kuma da wani, amma a yanzu da ta san cewa ita yake wa magana sai take ji ta daban, tana saka ta ƴar rikicewar da bata shirya ba. A hankali ta daurewa hakan muryarta ta shiga jero masa sunayen littattafan da ta san sunyi suna amma da yawansu yace bai san su ba saboda yawanci akan Romance ne shi kuma yace ma yafi karanta Non-fiction, yana yi yana cin abincin cike da wani abu da zata iya kira da nishadi.

“Akwai wani ‘The Life we had’ na san zaki san shi.'”

Ta ɗaga kanta da sauri don ji tayi kamar hakan na kaɗe tasirin da muryarsa ke yi a zuciyarta, kuma a lokaci guda bakinta ya ɓalle da wani murmushin da bata shirya masa ba tana tuno yadda akayi ta karanta littafin a wani shagon bakin titin unguwarsu inda ake sayar da shi, zuwanta shagon nan bakwai kafin ta kai karshen littafin saboda yayi mata tsadar da ba zata iya siya ba, kuma wata ƙawarta da suka yi makaranta ɗaya da yawanci litattafan wajenta ma ita ta bata, itace ta dame ta zancensa, bayan sun bar makaranta ne a lokacin ita tana can Bauchi babu ta yadda zasu iya haɗuwa sai dai ta kira ta a waya tayi bata labarinsa. Tana tuna ranar da ta kai ƙarshen labarin da wani a cikin masu tsaron shagon ya gane ya tada ballin sai ta biya, da taimakon Aminu aka rufe case ɗin.

Bata sani ba ko shima murmushi yayi don kanta yana sunkuye amma taji muryarsa ta ɗan canja lokacin da yace.

“Ke ma kamar su Munaya ce ashe, ban san me marubucin littafin yayi da ya siye zuciyarku da yawa ba, babu wani abu da yake gaskiya a labarin nan.”

Amina bata san sanda ta ɗago ta kalle shi ba tana girgiza kai, tace.

“Ai dama Fiction ya gaji ƙirƙire-ƙirƙire da yawa, shi yasa ya kirkiro komai ɗin don ya fito da ma’anar labarin sosai.”

Ya girgiza kansa shima.

“Saboda kawai ya karya zuciyar mutane ne, shi yasa ma ya kashe su daga karshe, daga lokacin da na fahimci itama yarinyar mutuwa zata yi, na tsayar dashi ban ƙarasa kallo ba.”

Sai ta sake ɗagowa ta kalle shi.

“Na zata novel ne.”

Ta fada kamar tana tsoron labarin nasu zai banbanta, amma sai yayi saurin daga mata kai.

“Novel ne, amma lokacin da Munaya ta takura min da zancen labarin bani da time ɗin karatu, so sai kawai na siyo film din na kalla instead.”

Ta gyada kanta sau daya sannan ta sake maida shi ƙasa ba tare da tace komai, yaji wani abu na shiga zuciyarsa yadda ta fara sakewa dashi a yanzu, don haka kai tsaye ya sake tambayarta.

“Baki kalli film din ba?” ya tambaya yana nazarin abinda bata faɗa ba akan furkar ta, kuma sai ta bashi amsar da ya riga ya sani ɗin ta hanyar daga kanta.

“Insha Allah zan kawo miki ki gani.”

Sai ta ɗago ta kalle shi, yayin da hannunta ya tsaya da wasa da mayafin nata.

“Allah ya yarda.”

Ta furta a hankali tana kallonsa, kuma a cikin idanun nata Ma’aruf yaga daren ya tsaya cak kafin ta sake sunkuyar da kanta a hankali, yaji wani abu yaji kamar tausayinta na bi ta kan zuciyarsa.

Tana da rayuwarta ya sani, watakila har ma da mafarkai na abubuwan da take son cimma, amma yanayin yadda auren yazo ya sani cewa yabi ta kan abubuwa da yawa a rayuwar tata, wanda da shine baya taɓa jin zai jurewa hakan, amma ita gata a zaune har tana kokarin yi masa hidima, yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaron sa a lokaci guda, a baya yana jin zai iya bin kowacce hanya don sanin meye haɗinta da Jamal amma tun a yanzu ya fara jin cewa ba zai iya yin abinda zata yi dana sanin haɗuwa dashi a rayuwarta ba.1

***

Washegari da safe Hajiya Kilishi ta buɗe kofar ɓangarenta, fuskarta ta faɗaɗa da wannan murmushin nata mai armashi a duk lokacin da ta ganshi duk kuwa da cewar a jiya tayi ta kallon agogo cikin lissafin zuwansa amma bata ganshi din ba, dalilin da yasa a yau ta tashi da sassafe kenan don ta san yana da karbar magani a yau, don haka ta buɗe kofar zuciyarta na fatan ya kasance Ma’aruf ɗin ne, kuma fatan nata ya karɓu don yana tsaye a gabanta yana murmushin da take jinsa kamar ashanar dake ƙyasta zuciyarta wajen kamawa da wuta.

“Tun jiya muke kallon hanya Ma’aruf…”

Ta fada tana kallon idanunsa da kullum suke gaya mata shi daban ne a lissafinta ba sai ta rantse ba, zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da ta ganshi a gabanta irin haka.1

“Mami I’m sorry, jiya aiki ne yayi min yawa kuma a gida naci abinci shi yasa baki ganni ba.”1

Maganar ta taho kamar wani gingimeman dutsen da ya faɗo daga kolulowar sama ya dira a tsakiyar kanta, a lokaci guda murmushin fuskarta ya ɗauke, idanunta suka tsaya akansa cak a sanda ya kara wayar hannunsa a kunne ya shiga yiwa wani Benjamin magana cewa yayi wa Legal Department ɗinsu bayani su ƙarasa shiryawa kafin ya ƙaraso.

Ya katse wayar ya juyo ya kalle ta a lokaci guda da yanayin nata ya baje, fuskarta ta cakuɗe da murmushin da yasa shi gyaɗa mata kai kafin ya wuce zuwa ciki, Abinda bai sani ba shine wannan karon murmushin ba nasa bane, na halittar da take hangowa a cikin idanunta ce… Amina!2

A yau an ƙaraso gaɓar da take jira, a yau tsarinta zai fara ba sai gobe ba, bata wasa da lokaci balle har tayi sake da koda ƴar mitsitsiyar dama ce… A yau Amina zata shigo cikin ukunta!2

A yau duk wani mahalukin da yake da kusanci da Amina zai shigo cikin lissafinta!5

**I’ve never fallen from quite this high

Fallin’ into your ocean eyes

Those ocean eyes.

                               -Billie Ellish+

A wannan ranar Amina na kwance daga kan gadon ɗakin tana sauraren wani shiri mai taken ‘Allah ɗaya gari banban’ da baya taɓa wuce ta daga cikin rediyon wayarta.24

Idanunta kusan a rufe suke yayin da take sauraren maganganun mutanen dake gabatar da shirin, yau hira ake akan daya daga cikin garuruwan da take son zuwa a rayuwarta, Paris… Don haka sosai take jin daɗin duk wani bayani da baƙin da aka gaiyato suke yi na yadda garin yake da kuma tsare-tsaren su.

Sai dai duk yadda hankalinta ke kan shirin zuciyarta kuma nata zarya a can falon gidan inda ta kammala komai na abincin Ma’aruf ta ajiye masa kaar jiya, a yau ta riga ta tsarawa kanta cewa ba zata fita ba don Allah ya sani bata so yaga kamar tana kokarin shige masa ne ko kaɗan, ƙundubalar da tayi wajen yi masa abincin ta wadatar tunda har yanzu bata san manufarsa akanta ba.

Ko a jiya umarnin da ya bata ne kawai yasa ta zauna ba wani abu ba, yadda muryarsa ta furta ‘Ki zauna’ da kuma yadda ya kalle ta da idanunsa bai bata damar zabi ba ko kadan. Duk da cewa kuwa taji dadin hirar, tsaya… Ba hirar tasu ce ta mata daɗi ba, zancen cewa wannan labarin yana da film ne, don Allah ya sani zata so ganin yadda dukkan tunaninta game da komai na labarin zai fito zahiri.

“… Wato ina gaya maka samun gida a garin nan shine babban abu mai wahala, gidaje ba karamin tsada ne dasu acan ba…”

Hirar rediyon ta cigaba da fitowa yayin da zuciyarta ta fara lissafin kamar yau ya daɗe da yawa, don ko da safe bata ganshi ba kuma yau ita kadai ta yini a gidan, su Sahla da Zahran da suka yi mata alkawarin zasu sake shigo mata yau sun manta da zuwansu makarantar Haddar da suke zuwa shi yasa bata gansu ba.

Tun da tazo gidan basu shigo mata ba sai jiyan, kuma sai a jiyan ta gane ashe su ma suna da magana kamar su Samirah, a cikin gidan idan ta gansu da littafinsu kawai gaishe ta suke yi su cigaba da harkokinsu, amma jiyan da suka shigo tasha labarai kala-kala wanda mafi yawanci ba komai ta gane ba.

Don a baiyane yake yanayin rayuwarsu da tata ba iri ɗaya bane, abubuwan da suka taso suka sansu ita har yanzu saninta bai ƙaraso nan ba, yanayin makarantar su dama ƴaƴan masu kuɗin da suke mu’amala dasu ba iri daya bane da abinda ita ta taso ta sani. Ta tuno wata magana da Aminu ya taɓa gayawa Maryam ranar da yake tsokanarta bayan ta gama kurin cewa ai ita babu inda zata je a raina ta.

“… Nan bayan layin nan idan aka ƙarasa ba sai anje da nisa ba za’ayi iya ɗebo sa’anninki biyar da in suna hira ba zaki taba iya magana ba wallahi sai dai kiyi ta binsu da kallo kina wage baki.”

Itama dai kuwan ta wage jiya, don murmushi kawai tayi ta binsu dashi kamar yadda take yi a wajensu Samirah, don har gwara su Zahran ma, su idan suka fadi wani abu sai ta biya shi sau biyu akanta kafin ta fahimta musamman Surayya da ta fahimci tafi su iyayi gabaɗaya. Suna da daɗin mu’amala sosai, da gaske suke sun karbe ta a cikinsu ba tare da tunanin komai ba,

Ta tuna sanda Samirah ke mata bayanin dalilin da yasa basu je gidansu da biki ba.

“Mu fa bamu san da bikin ku da Yaya ba sai ana saura two weeks da aka haɗa lefe sannan Mami ke gaya mana, kuma ko ranar dinner ma munso mu kai muku cards din. Yaya Shukra ce ma ta bani ranar luncheon na saka a jakar Khadija (wata kawarta) ita kuma sai tazo da wata jakar kuma ta manta bata ɗebo ba. A ranar ni kuma I was so busy kamar me, shikenan ban samu time munje mu ɗauko ba. Da na kira Yaya kuma na gaya masa cewa yayi kar mu damu kawai.”

Amma duk da yadda ta fara sakewa a cikin nasu, tana kewar gida kamar ba gobe, abubuwa da yawa akwai su anan na duk wata buƙatar rayuwa, ga komai sabo koina ƙal-ƙal, gashi babu wanda ya taɓa ko haɗe mata rai har yanzu, idan ta shiga cikin gidan kowa haba-haba yake da ita, hatta su Salma amaren da akayi bikinsu tare dukksnsu sun gaisa a wayar Samirah, da Salman ma ba sau biyu suna gaisawa.

STORY CONTINUES BELOW

Ga Hajiya Kilishi da take nan-nan da ita kullum fuskarta dauke da fara’a tana fadin ita ƴarta ce, Ranar da taje ta gaishe da Baffa ranar ta fahimci dalilin da yasa Baba ya bada aurenta a gabansa ba tare da wani tunani ba, dattijo ne kamili mai nutsuwar da a fuska kadai kowa zaiyi masa shaidar hali na gari, don haka babu wata matsala da ta guskanta a gurinsa shima.

Sannan shi kansa uban gaiyar har yau ko haɗe rai bai taba yi mata ba, amma duk da haka, tafi son rayuwar cikin ƴanuwanta akan wannan, tunda har yanzu zuciyarta bata gama kwantawa da komai ba, tunaninta iri ɗaya ne da Amma dama kuma Fatima, dukkaninsu sun yarda cewa akwai wani abu dake tahowa wanda bai karaso ba, don ba’a ɗora turbar auren da cewar komai ya tafi daidai ba, sun sani cewa ba sun kawo ta cikinsu ne don su nuna mata kirkinsu ba dashi da ƴan gidan nasu, dole akwai wani abu da yake a ɓoye wanda har yanzu basu kai ga saninsa ba.

Su Aminu da Baba ne kawai hankalinsu a kwance don duk sanda suka yi waya da Baban, zai yi ta zubo mata tarin addu’o’in da suke karya zuciyarta, shi har yanzu zuciyarsa guda ɗaya ce game da auren, ya riga ya aminta da Baffa da ma Hajiya Kilishi ta yadda baya taɓa iya hango komai.

Ta lumshe idanunta a hankali tana jin yadda bacci ke shirin ɗaukarta a lokacin, ta shiga ƙokarin kore shi don aƙalla tana son jin lokacin da Ma’aruf zai dawo amma baccin mai nauyi ya ƙara karfinsa, don haka wata zuciyar ta gaya mata cewa zata iya ɗan runtsawa tunda tayi sallar isha kuma bata wani samu baccin safe ba sosai, da wannan lasisin da zuciyarta ta bata taji maganganun cikin rediyon nan suka zuƙe daga kanta a hankali, taji su suna yin nisa da kunnenta kafin a lokaci guda taga Aminu a tsaye daga bayan idonta.

“Me yasa kika kasa Amina?”

Kai tsaye ya tambaye ta yayin da idanunsa ke kallonta, kuma kalaman suka isa kanta amma suka kasa bada ma’ana saboda dukkan tunaninta ya tsaya cak tana kallonsa da dimbin mamaki, Yaushe yazo? Yaushe yazo ko kuma ita yaushe ta bar cikin gidan, don daga nesa tana hango duhuwar wasu dogwayen bishiyu, hakan yasa gabanta fadi da dukkan tsoron da zuciyarta zata iya dauka.

Tayi ƙokarin ta kalli kanta amma sai ta fahimci bata iya ganin jikinta kwata-kwata, kamar idanunta ne kawai a wajen suke ganin komai amma babu gangar jikinta, ta ɗago ta sake kallon Aminun da har yanzu ke tsaye a gabanta.

A lokacin ta kula cewa idanunsa sun canja, kalolinsu ba iri ɗaya ne daga yadda ta sansu ba, sun koma baƙiƙ-ƙirin dauke da kyallin kwalla yayin da fuskarsa ke nuna dukkan wasu kalolin tashin hankalin da bata taɓa gani a fuskar Aminun ba, Aminun mai raha da fara’a, Aminun data sani mai ɓoye damuwarsa a kodayaushe.

“Me yasa kika kasa Amina?”

Muryarsa ta sake tambaya da amon da ya kara  hargitsa ta, kuma bata san lokacin da ya matso gabanta ba sai kawai taji ya riƙo hannunta na dama.

Ta kalli inda hannun nata ya kamata ya kasance, babu komai sai yadda yatsunsa suka riƙe ta, lokacin da ta ɗago da idonta sai taga ashe ya jawo ta ne har sun iso wajen duhuwar bishiyun nan, tashin hankalin ta ya ƙaru don tana jin yadda ƙafafunta da basa nan suke tafiya, da kuma yadda hannayenta ke rawa a cikin nasa.

Hankalinta ya kasu wajen nazarin bishiyun sanda suka tsaya a wani waje, ta juyo tana kallon yadda yanayinsa ke haskawa da dukkan raunin da bata taɓa hange ba, taji ta ƙara rikicewa, taji abubuwa da yawa suna tasowa cikin kanta, tambayoyi fal suna ihu da kokawar fitowa daga bakinta da ta san babu shi balle har ta iya furta su, kowanne lungu da saƙo na tunaninta ya cika da hanƙoro, kamar tana jiran wani abun da bata san meye ba.

Kuma kwatsam sai ta nemi bishiyun nan dake kewaye dasu duka ta rasa, warin ƙonewarsu ya cika hancinta amma babu su ɗin balle kuma alamun wutar, kuma babu wani ɓata lokaci kunnenta ya fara jiyo mata muryoyinsu, Maryam ta fara ji, tana ihu mai haɗe da salati, sai ta jiyo ta Hafsa da Adam ma, kowanne yana kuka mai nuna tsananin azaba, bata san ya akayi ta iya tsinto muryoyin su Fatima, Ummi har ma da ta wasu daga cikin ƴaƴan kawu Malam ba.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma kafin wani abu ya sake giftawa a cikin kanta ta jiyo muryar Baba yana faman kiran sunayen su Maryam ɗin har ma da sauran mutanen da bata iya tantance muryoyinsu ba, hankalinta ya kara tashi duniyarta ta rikice, ihu da hargowar suka cika kanta kota’ina, kuma a lokacin da ta juya zata kalli Aminun sai taga babu shi, a yanzu Amma ce tsaye tana kallonta, fuskarta ɗauke da wani irin murmushi mai ciwo yayin da take kallonta da dukkan wani fata na duniya.

“Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina?”

Tayi tambayar a lokaci guda da itama ta neme ta ta rasa, wajen ya koma babu komai sai tashin ihun ƴanuwanta da kuma hargowarsu yayin da warin ƙonewar nan ya cigaba da cika wajen. Ta kasa gane komai ko kuma abinda yake shirin faruwa, abinda kawai zata ita tunawa kafin ta farka shine daga cikin muryoyin dake ihu, ta jiyo wata murya da ta kasa gane wacece ko kuma inda ta santa, muryar tana ƙyalƙyala wata irin dariyar da bata taɓa jin irinta ba!

Dariyar ta shiga amsa kuwwa a kowanne ɓangsre na wajen yayin da ihun mutanen dake amsa sunan rayuwarta ke cigaba da tashi…. A lokacin ne kuma ta farka a firgice, kafafunta suka mike tsaye akan gadon bakinta na biyo kalaman Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, a cikin ɗakinta take har yanzu, akan gadon da bacci ya ɗauke ta, amma tun yaushe? Don rediyon wayarta da ta bari a kunne yanzu ƙarar shuuuu kawai take fitarwa.

Tasa hannu ta jawo ta da sauri, ta kashe rediyon tana neman lokaci, karfe ɗaya da rabi na dare, wani salatin ya sake suɓucewa a bakinta cike da mamakin yadda akayi tayi bacci mai nisan haka, sai kawai ta wullar da ita gefe ta janyo dankwalinta daya zame akan filon data kwanta tayi saurin ɗaure kanta, koina a jikinta rawa yake har yanzu yayin da mafarkin ke ƙara dawowa cikin kanta, bata fahimci komai a cikinsa ba amma Allah ya sani ta tsorata sosai da yadda abubuwa suka faru don bata iya tunawa idan ta taɓa irin wannan mafarkin a rayuwarta.

Taji maƙogwaronta ya bushe yayin da amon muryar nan dake dariya a cikin mafarkinta ke dawo mata, bata san me hakan

ke nufi ba, bata san waye zaiyi dariya alhali tashin hankali irin wannan yana faruwa ba, kuma har a yanzu tana jin cewa kamar ta san muryar amma ta kasa tabbatar da inda ta santa.

Makogwaronta ya ƙara bushewa yayin da take kokarin saita zuciyarta da har yanzu ke bugawa, ta sauko daga kan gadon, wata doguwar riga ce a jikinta ta bacci da bata kai ƙasa ba ta gaba, don haka kusan tun daga saman gwiwoyinta a waje suke, kuma ba tare da tunanin komai ba tayi hanyar fita daga ɗakin.

Kitchen zata je ta ɗauko ruwa, wataƙila zai iya wanke bugawar da zuciyarta ke yi bayan ƙishirwar, idan ta dawo tayi sallah raka’a biyu kuma, watakila tunaninta zai iya komawa daidai.

Jikinta na rawa har a lokacin da ta isa kitchen ɗin, ta buɗe ƙofar a lokaci guda da hasken fitilar da aka kunna ya shiga idonta kafin shi, yana zaune daga kan worktable ɗin tsakiya na kitchen din, fitilar dake saman wajen ita ce a kunne da labtop a gabansa yana danne-danne, a gefe kuma foodflask ɗin abincin data dafa ne.

Kuma duk da rikicewar da take ciki, ta gane cewar babu riga a jikinsa, wata bakar singlet ce kawai da ta fito da faɗin kafaɗunsa ta kowanne gefe, shima ya dago daga kan labtop din yana kallonta daidai lokacin da ta bude ƙofar.

“Me ya faru? Me ya same ki?”

Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, kuma ba shiri wani abu ya zarce maƙogwaronta jin yadda muryarsa ta fito a cikin shirun daren tana gaya mata kamar har yanzu a cikin mafarkin take, sai ta ɗaga girgiza kanta kawai da sauri sannan ta sake haɗiye abinda ke bakinta kafin tace.

“Ba komai, ruwa zan ɗauka.”

Da haka ta saki hannun kofar ta nufi wajen fridge, Ma’aruf ya bita da kallo zuwa wajen fridge ɗin, yanayin fuskarta a firgice yake sosai duk da kokarin da tayi wajen ɓoye hakan, kuma ko daga yadda muryarta ta fito ya san akwai wani abun, da wuri tayi bacci ya sani don bayan ya dawo yaga alamun hakan duk da yau cikin gida kawai ya wuce wajen Mami, acan yaci abincin darensa ma bayan sun tattauna maganganun da yasa ta kira shi, zancen Hamida.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma bayan ya shigo ya tarad da nata abincin jere a falo, haka kurum sai yaji wani iri, sai yaji kamar bai kyauta ba, ya sani ba zata ji dadi ba idan har ta farka ta ganshi a yadda ta ajiye tunda jiya ta bashi kuma yaci.

Bai tsara komai tare da ita ba, abinda ya sani kawai shine aurensu zai zame masa garkuwa ne har lokacin da zai gama da case ɗin dake gabansa na kamfanin nan kafin ya fara binciken da zai shafe ta. Amma tun jiya da yaci abincin nata, sai yaji wani gefe a zuciyarsa ya kara nutsuwa da ita, har yana gaya masa gwara nata ma akan na Mami, tunda aƙalla ya san ita tayi da kanta, na Mamin kuma idan Samirah bata nan masu aikinta ne kawai.

Don haka dole a yanzu da ya ɗebo aikin daya shirya zai kwana akansa, ya ɗauko abincin daga falo ya taho kitchen tunda babu Dining area a gidan, kuma ba yunwar yake ji ba amma da ya zuba ya fara ci sai yaji kamar dama bai ci komai ba, yaji hankalinsa ya sake nutsuwa sannan aikin da yake yi na tafiya akai-akai yayin da dukkan maganganun da suka yi da Mamin akan Hamida ke dawowa kansa kafin ta shigo a yanzu da yanayinta a hargitse.

Sai kawai ya tura kujerar da yake kai baya ya mike tsaye.

“Wani abu ne ya same ki?”

Ya sake tambaya yana tahowa inda take shirin buɗe fridge ɗin, kayan jikinta yake kallo a yanzu, kamar na bacci ne… wata riga mai tsawo daga baya amma daga gaba kamar an guntule ta har wajen gwiwarta, don haka kafafunta na tsaye a waje, kuma bai san me yasa ba sai yaji wani abu a zuciyarsa na yabawa da yadda ɗankwalin kanta yayi kala ɗaya da rigar, Pink. Kallonsa take yi itama, idanunta farare na nuna dukkan wani alamun tsoron da ba sai ta furta ba, don haka kai tsaye cikin hasashensa ya sake tambaya.

“Mafarki kika yi?”

Amina bata san lokacin da ta ɗaga kanta ba don kayan jikinsa a yanzu sun karawa rikicewarta tasiri, bayan baƙar singlet din nan, three-quarter din wando ne kuma a jikinsa wanda da kadan ya wuce gwiwa, sannan ga muryarsa mai zurfi da taji tana tayar da wasu abubuwa akan fatar ta bayan rawar da jikinta ke yi.

Kuma bata yi aune ba sai jin hannunsa kawai tayi ya riƙo nata ɗaya, ya jawo ta zuwa wajen kujerar daya taso ya zaunar da ita a ta gefen inda yake zaune kafin shima ya zauna.

“Kinyi addu’a?”

Tambayar ta tuna mata da abu na farko da ta kamata a e tayi, amma tsabar rikicewar da tayi, zuciyarta bata kawo mata wannsn lissafin ba, sai ta girgiza ksnta a hankali don ko tayi ƙokarin yin ƙaryar ma bata san me zata ce ba, ba zata iya wani tunani mai kyau ba slhali har yanzu yana riƙe da hannunta sannan ga kafafuwanta tun daga kan gwiwarta a waje daga ƙasan rigar nan, bama za’a lissafa da kayan jikinsa ba…

“Suratul Ikhlas sau uku, Suratul Falak sau uku, Suratul Nas sau uku…”

Muryarsa mai zurfi ta sake faɗa yana kallonta, bata da wani zabi sai ta rufe idanunta, ta haɗiye yawu a maƙogwaronta kafin a hankali bakinta ya shiga karanto su, bata jin sautin muryarta yana fitowa amma tana kaiwa karshe, ya sake cewa.

“Ayatul Kursiyu…”

Ta kai ƙarshe lokacin da taji kamar almara, ƴar rikicewar tata na bin iska, kuma shirun da yayi riƙe da hannunta bai saki ba wani abu ne daya saita numfashinta daga hawa da saukar da yake faman yi, taji kamar hannayen nasa sunyi wa nata wata rumfa ne ko kuma sun zama wani bango da ba abinda ya isa ya ratsa ta cikinsu ya cutar da ita, don haka a hankali nutsuwarta ta fara dawowa jikinta.

“Mafarki ba gaskiya bane, daga shaidan yake zuwa ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru insha Allah.”

Sai kawai ta gyada kanta a hankali yayin da take ture dukkan wani tunani daga cikin kanta tana yarda da kalaman nasa don ta samu zuciyarta ta dawo daidai, Mafarki ba gaskiya bane, ta shiga biyawa zuciyar tata layi bayan layi.

STORY CONTINUES BELOW

Abinda bata sani ba a wannan lokacin shine, wani lokacin mafarki na juyewa tamkar mudubi, ya nuna abinda zahirin ke iya haifarwa!

***

Ƙarfe bakwai na safe.

Idan akwai wani abu daya rage a rayuwar Ma’ruf ta baya, shine ƙaunarsa da football (ƙwallon kafa) shi kaɗai ne abu guda ɗaya bayan sunansa da kuma kamanninsa da zai ce basu canja daga Ma’aruf ɗin da yake a baya ba, Ma’aruf ɗin da yake kafin rasuwar Jamal, amma duk wani abu bayan hakan komai da yake yi ba rayuwarsa bace.

Son football ɗin ne kawai yayi yawa a zuciyarsa da ba zai iya barinsa ba, shi yasa yawanci duk weekend da safe yana stadium ɗin Sani Abacha, team ne dasu guda da suke da ranakun yin wasa da kuma ranakun training, sannan yana ɗaya daga cikin members ɗin dake kula da wajen ma, duk wani taimakon harkar kudi da ake yi a wajen su suke badawa, idan ya gama ya fito haka zaka ga samarin nan ma’aikatan wajen sun biyo bayansa har wajen mota don ya sallame su, don haka babu wanda bai sanshi ba a wajen.

Yau asabar can yayi niyyar zuwa don tun da ya dawo daga sallar asuba ya shirya, amma yayi-yayi da motarsa taƙi tashi, jiya lafiya lau ya ajiye ta kuma a saninsa bata da wata matsala amma sharrin karfe ance ba abinda ba zai iya ba, haka ya hakura ya rabu da ita, sai kawai ya fito da ball ɗin sa daga booth ɗin motar ya shiga training ɗin da ya saba a compound ɗin gidan.

Kusan ƙarfe bakwai da rabi lokacin da wayarsa tayi ƙara daga can saman motar inda ya ajiye ta, kuma sai da ya kai ball din sama sau biyu sannan yazo ya ɗauka, Martha ce.

“Barka da safiya sir, RTL sun bugo waya cewa yau zasu sauka a Kano, don haka meeting din zai zama karfe huɗu na yamma.”

Ta zayyano dukkan bayanin da harshen turanci, hannunsa ya zura cikin kansa don kwata-kwata ya manta da zancen cewa zasu iya yin meeting din a yau, yayi niyyar babu inda zai fita zai zauna ya huta ne don Allah ya sani ya aikatau a cikin satin nan gashi jiya ma bai wani samu bacci mai yawa ba. A hankali ya cije leɓɓensa yayin da ta cigaba da yi masa bayanin cewar sunyi waya da Faruq da sauran board members ɗin nasu ta shaida musu komai, shi gabadaya ya manta ma da nasa takardun da ya kamata ya karanta kafin a shiga meeting din jiya a Office.1

“Sannan kuma Sir ka manta papers na background Information din a Office, dole zaka buƙace su kafin a shiga meeting ɗin.”

Ya sake motsa hannunsa a cikin gashin kansa.

“Na sani Martha, yanzu kuma ban san ya za’ayi ba gashi motata taƙi tashi, amma bari na kira Ishaq sai a ɗauko min tasa.”

“Okay sir.” Ta amsa muryarta a ƙasa.

Da haka suka gama wayar sannan ya shiga laluben nambar Ishaq ɗin da har yanzu bai dawo ba, bugu ɗaya biyu kuwa ya ɗaga.

“A ina ka ajiye muƙullin motarka?”

“Me za’ayi?” Ishaq ɗin ya amsa daga cikin wayar.

“Motata ta samu matsala ne kuma ina da meeting anjima.”

“Ka kira Jamilun?” (Makanikensu.)

“Ban kira shi ba, tunani nake sai anjima tukunna saboda gabaɗaya na manta da meeting ɗin ne.”

Dariya Ishaq ɗin yayi daga ciki yace.

“Wallahi tayar motar nan a sace na tafi na barta, I don’t know ma ya take take yanzu.”

Ya girgiza kansa kafin yace.

“Baka da amfani.”

Da haka ya kashe wayarsa, ya kira Malam Sani.

“Yallaɓai Barka da safiya.”

“Barka dai Malam Sani, nace dan Allah akwai mota a cikin gida ne?”

STORY CONTINUES BELOW

“Ai kuwa Babu ranka ya daɗe, don su Baffa sun tafi gona a tasa shi da Baba Usman, ta Hajiya kuma a tsaye take tun wancan watan don haka na baro za’a kaita asibiti da ta Mami, school bus din kuma ka ganni da ita a ƴankaba.”

Sai kawai ya gyaɗa kansa alamun ya fahimta kafin suyi sallama ya kashe wayar, Martha ya sake kira yace ta kira direban kamfanin nasu kawai ya kawo ta kawo masa takardun.

Da haka ya mayar da ball ɗin cikin booth ɗin motar sannan yayi hanyar cikin gidan, ya shiga cikin falon ya shiga cikin a lokaci guda da ƙamshin wani air freshener mai sanyi ya shiga hancinsa, yana tabbatar masa da cewar matar gidan ta tashi kenan, ya nufi hanyar dakinsa don yayi wanka ya shirya yayin da yanayin fuskarta a jiya da daddare ke haskawa a idonsa da kuma waɗannan siraran ƙafafun nata.

***

Ƙarar kwankwasa kofar gidan ta shiga kunnen Amina a lokacin da take kammala aikinta na karshe a kitchen, ta san ba Ma’aruf bane, don a yanzu ƙwaƙwalwarta ta haddace yanayin nasa bugun kofar duk da ba kullum yake manta mukullinsa ba.

Ta kashe gas ɗin da sauri sannan ta goge hannunta kafin ta fito, har yanzu wani iri take jin jikinta, mafarkin jiyan nan dana abinda ya faru bai gama barin tunaninta ba sam, don bayan ta koma ɗaki a jiyan bata iya komawa bacci ba, sallah tayi sannan ta zauna tunane-tunane har lokacin asuba, kuma sai bayan asubar sannan bacci ya ɗauke ta, baccin da baiyi nisa ba ƙarar wani abu ta tashe ta.

Kuma ba’a dade ba wata yunwa ta dame ta, don haka a gurguje ta karasa karatun Azkar ɗinta sannan tayi wanka kafin ta fito zuwa kitchen, inda anan ta hango Ma’aruf ta cikin sliding windows ɗin dake wajen sink yana ball, ta fahimci ƙarar data tashe ta kenan. Yana sanye da wata loose-fitted riga fara kal, da bakin wando irin na sports, (track pants) da kuma takalmin ball, rigar ta fito da ƙirar jikinsa sosai, sannan yadda yake juya ball din a kafafunsa cikin kwarewa ya tabbatar mata cewar da a cikin filin ball yake tabbas zai iya yin kokarin ture kowa ya ci.

Ta daɗe tsaye tana kallonsa cike da mamaki, don bata taɓa tunanin mutum so committed kamar shi zai samu irin wannan lokacin ba, ta fahimci a kullum ƙara sanin wasu halayensa dake bata mamaki take kuma har yanzu ba’a zo kan wani abu guda da tayi hasashensa game dashi a baya  ya zama gaskiya ba.

Komai zuwa yake saɓanin tunaninta, ita har yanzu bata ga wata alama ta ciwon nan nasa da ta riga ta gama tsorota dashi ba, shi yasa zuciyarta ke ta tantama ma akan idan shi ya rubuto mata wannan saƙon, har Fatima ta gayawa cewa in dai ba warkewa yayi ba, to ba koyaushe ciwon ke tashi ba. Shi yasa tare suka yarda da tsarinta na kyautata zamansu, da tunanin idan ya san bata da niyyar cutar dashi, ba lallai yayi mata wani abun ba duk lokacin da ciwon nasa ya tashi.

Sai dai ita bata tsara da yadda zuciyarta ke jin dadi tun lokacin da ya fara cin abincin nata ba, jiya duk da rikicewar mafarkin nan da take ciki sai da zuciyarta ta faɗa ganin kwanukan abincinta a gefensa… Tunanin hakan ya tuna mata da yadda ya riƙe hannunta a lokacin, har yanzu tana jin kamar shatin yatsun sa akan fatar ta, tana jin kamar akwai wani abu dake ƙonewa a jikinta saboda tasirin yadda yatsun nasa suka zagaye duka hannun nata gabaɗaya.

Da wannan tunanin ta kammala haɗa abincin breakfast ɗin lokacin da ta tsinci bugun ƙofar nan. Kayan jikinta riga da skirt ne na wata atamfa ash da tun ganinta da ita da farko tayi mata kyau wa ido, kuma sai akayi sa’a mai dinkin ya zabi wani ɗinki mai kyau da ya dace da ita don haka suka karbeta sosai, kuma yau bata saka mayafin data saba ba sai ta yiwa ɗankwalin V kawai ta yafa shi a haka.

Ta buɗe ƙofar lokacin da hoton wata budurwa ya shiga idonta, doguwa ce, fara, kamaninta na yare ne amma kuma kyakkyawa ce, ta bazo gashin data ɗora a saman kanta mai kyau sannan matsatstsiyar rigar data saka ma mai kyau ce, don ta fito da kowanne lungu da saƙo na jikinta yayin da hannunta ke rike da wata ƙatuwar jaka irin ta aiki.

STORY CONTINUES BELOW

“Good Morning my name is Martha, I’m…” ( Barka da safiya, sunana Martha, nice…)

“She’s my sectary.” (Sakatariyata ce.)

A lokaci guda muryar Ma’aruf ta faɗa daga bayanta, kuma ba tare da jiran komai ba taji hanayensa masu dumi dun sauka a bayanta, daidai wajen da zip din rigarta ya fara, sannan ƙamshin turarensa ya cika hancinta. Bata san lokacin da ta juyo da kanta ta kalle shi ba, idanunta na nuna mamakin da dukkan wani abu mai hankali a jikinta ke yi na yadda ya tsaya kusa da ita amma shi ba ita yake kallo ba, wadda ta kira kanta da Martha din yake kallo da wani dan guntun murmushi a leɓɓensa.

Kuma bata sake shiryawa ba sanda taji ya jawo ta baya kaɗan yana haɗa ta da jikinsa, kanta ya tsaya daidai kafaɗunsa.

“You’re welcome Martha, meet my wife Amina Sulaiman.”

Sai da numfashin Amina ya katse a ƙirjinta jin yadda ya ambaci cikakken sunanta amma hakan baiyi nisa ba saboda Martha da ta miƙo mata hannu tana jiran su gaisa, sai tayi saurin mika mata nata itama tana murmushin da bata san a yaya ya fito ba.

“You came with everything right?” (Kinzo da komai ko?)

Taji muryarsa daga saman kanta tana sake tambayar Martha ɗin wadda ta ɗaga kai.

“Yes sir, everything is intact, I just need to explain some things to you about Document A.” (Eh yallaɓai, komai ya cika bayanin wasu abubuwan kawai zan yi maka.)

Har yanzu da murmushi a fuskarta ta amsa, kuma sai kawai yasa hannunsa ya sake matso da Amina gefensa, suka bawa Marthan hanyar shiga ciki, ta wuce su kuwa tana ƙoƙarin fito da takardu da kuma labtop daga jakar hannunta.

“Kin tashi lafiya?”

Muryarsa ta tambaye ta tun kafin ta dawo da hankalinta kansa, sai tayi baya da ƙafafunta da sauri wanda hakan yasa ya saki hannun nata, kuma maimakon ta amsa sai tace.

“Barka da safiya.”

Ya shafo gashinsa ta baya.

“Barkanmu dai, hope kin dawo daidai?”

Ta san me yake nufi don haka ta ɗaga kanta sau biyu idanunta akan yatsunta, ya cigaba da cewa.

“Wannan sakatariyata ce sunanta Martha zamu yi meeting anjima ne and I left my things a office shine tazo ta kawo min.”

Bata san me yasa yake mata bayanin mutanen dake rayuwarsa ba, Farko da Faruk ya fara, sannan wani Ishaq da har yanzu bata gabshi ba bands yawan wayar da take jin suna yi, sai kawai ta ɗaga kanta a hankali alamun ta fahimta.

“Zamu ɗan yi briefing a ciki, ba zaki damu ba?”

Da sauri ta sake girgiza kanta, a wane dalilin zata damu, gidanta ne? ya gyada kansa shima sannan ya juya ya shiga ciki, hannayensa duka biyu sanye a cikin aljihunsa duka biyu, don rigar shaddar dake jikinsa bata kai gwiwa ba, kayan kamar ma sababbi ne, light brown, suna ta kyalli a cikin hasken safiyar.

Wajen da ya dora hannunsa a bayanta ya sake ɗauka da irin abinda take ji a hannunta, sai kawai ta shaƙi wani numfashi mai nauyi a ƙirjinta sannan ta rufe ƙofar falon a hankali.3

***

“Me? Me kika ce Amina? Ya kawo wata arniya cikin gidan da sassafen nan?”

Muryar Fatima ta faɗa cikin wayar dake kare a kunnen Amina, a hankali ta rufe idanunta sannan ta kai kofin shayin dake hannunta baki ta kurɓa.

“Ba yadda kike tunanin bane Fatee, yace min sakatariyarsa ce, kuma zancen aiki ma suke tayi wai meeting suke dashi anjima.”

“Duk da haka ni dai banga wannan ya dace ba, ko ba komai gidan aurenki ne ya kamata a mutunta ki a cikinsa ko ba komai.”

STORY CONTINUES BELOW

Saura kaɗan murmushin da take yi ya suɓuce a cikin wayar saboda yadda Fatiman ke yawan fadar ‘Gidan aurenta’ ita kanta da take ciki bata ganin hakan kamar gaske tunda har yanzu babu wanda ya san abinda gobe zata haifar.

“Ni sai naji muryarki ma kamar akwai wata damuwar daban bayan wannan, me ya same ki?”

Fatiman ta sake tambaya, sai tayi ajiyar zuciya kawai, Fatima ta santa ciki da bai kwatankwacin yadda Amma ta santa, don sau da yawa ma abubuwan da zata iya ɓoyewa Amma da Fatiman zata yi shawara su haƙa su binne, ko Maryam da take ƴaruwarta ba komai nata ta sani kamar yadda Fatin ta sani ba, Don haka a yanzu ma dalilin kiran da tayi mata kenan, sai gashi ta gane tun kafin ta kai ga gaya mata.

“Wani mafarki nayi da ya tashi hankalina jita, ban taba irinsa ba Fatee, wallahi na tsorata sosai don har na farka ina jin kamar gaske ne.”

“Ya salam! Allah ya kyauta, kinyi addu’a dai ko?”

Tambayar ta dawo mata da muryarsa sanda ya tambaya jiya ‘Kinyi addu’a?’

“Nayi, har asuba ma ina ta nafila, amma da na sake tunowa hankalina yake kara tashi, gashi na kasa fahimtar komai a cikinsa.”

“Babu abinda yake nufi insha Allah, ki cigaba da addu’a kawai kina kokarin yin taka-tsan tsan da komai insha Allah ba abinda zai faru Amina. Zanje wajen Malam mai almajirai anjima insha Allah in saka ayi miki rubutu, wataƙila wani satin zamu zo da Maryam sai in taho miki dashi.”

“Ba watakila ba, ku zo dan Allah Fatee…”

“Kin san Amma ce tace sai an kwana biyu tukunna.” Ta katse ta, sai ta girgiza kanta kamar tana kallonta.

“Wallahi ko kullum zaku zo na gaya miki mutanen nan basu da matsala Fatee, yanzu kwana biyu ma kusan kullum ni kadai nake yini saboda duk sun koma makaranta, babu mai shigo min.”

Fatima ta girgiza kanta itama.

“A abinda muka sani yanzun kenan Amina, gwara mu jira mu ga abinda lokaci zai haifar kafin komai ya daidaita, kar a sake ɓallo wani abu daban.”

Ta haɗiye wani abu a makogwaronta kafin ta amsa.

“Toh shikenan. Ki gaishe min dasu Mamah da Ahmad idan yazo.”

Sai Fatiman tayi dariya tace.

“Na gaya masa waccar gaisuwar taki ma sai cewa yayi wai kina matar auren yanzu kike cewa a gaishe shi? Wai in gaya miki kiyi azumi guda uku.”

Suka yi dariya a tare kuma da haka suka yi sallama fuskar Amina ɗauke da murmushin dake cike fal da kewar gida kamar kodayaushe. Ta ajiye wayar a gefenta tana kallon lokacin daya nuna akan ɗan screen ɗinta kafin hasken ya ɗauke.

***

“Eh, yanzu zan fito… I will be there in 10 minutes insha Allah. “

Ma’aruf ya faɗa cikin wayar da yake yi a lokacin da ya fito daga ɗakinsa.

“Idan kana yiwa Allah Faruq kar ka tsaya a wani wajen, Let’s not make them wait.” (Kar mu barsu su jira.)

Abinda aka faɗa a cikin wayar yasa shi kallon lokacin a agogon hannunsa kafin ya kashe wayar, a yanzu ya shirya cikin wasu kayan daban ba na safe ba, ƙarfe uku daidai, Martha ta daɗe da tafiya kuma shima bai daɗe da tashi daga kan system ɗinsa ba.

Don bayan tafiyar Marthan anan Amina ta same shi da kayan breakfast ɗinta, ta durƙusa har ƙasa ta ajiye a gabansa, ya tuna yadda skirt din kayanta ya baje a kan carpet ɗin lokacin da ta durƙusa, a lokacin yaji yana don ganin yadda ƴan siraran ƙafafun nan nata suka lanƙwashe da durkusawar, kuma bata ce komai ba ta shiga zuba masa kawai, idonta a kasa, dogwayen gashin idon na sama ya haɗe dana kasa kamar ta rufe su ne gabaɗaya amma kuma tana cigaba da abinda take yi.

STORY CONTINUES BELOW

Bai san me yasa duk abinda tayi yake jin kamar wannan ne karon farko da yake fuskantar rayuwar aure ba, shekarar sa uku tare da Ruƙayya a matsayin matarsa, amma har yanzu ba’a zo wajen da yaga wani abu nata yayi kamanceceniya da irin rayuwar da yayi da Ruƙayya ba, gani yake kamar komai sabo yake faruwa.

Yaso sunyi magana a lokacin nan, amma yawan aikin dake gabansa bai barshi ba, ya raina meeting din daga farko sai a yanzu da yaga yawan abinda za’a tattauna ya san cewa da gaske mutanen suke kuma idan har suka yi nasara ba karamin alkhairi zasu samu tare dasu ba, saboda haka dole ya ture komai gefe ya maida hankalinsa kan nazarin bayanan nasu, kuma watakila itama ta lura da hakan don tunda ta shiga ɗaki bayan yaci abincin tazo ta kwashe kayan bata sake fitowa ba.

Jamilu yazo tun dazu yayi tabe-tabensa a motar komai ya dawo dai, dama ya sani gyaran ba lallai ya zama mai yawa ba tunda motar bata cika bashi matsala ba tunda ya siye ta, don haka bayan ya gama saka links din ya nufi hanyar kofa rike da wayoyinsa kawai, ya riga ya kai duk abinda yake bukatar tafiya dashi motar tun ɗazu, din ya kusan haddace komai, zuciyarsa dama idanunsa kawai biyo dukkan abinda ya san zaiyi magana akai suke.

Ya ɗora hannunsa akan ƙofar falon har ya buɗe lokacin da yaji muryarta.

“A dawo lafiya, Allah ya bada sa’a.”

Idanunsa suka juyo da sauri zuwa inda take tsaye, daga hanyar koridon nan ne alamun daga daki ta fito, hannunta na hagu na riƙe da wani baƙin bokiti data ciko jikakkun kaya dasu, yabi hannun nata da kallo da kuma gaban rigarta daya jiƙe yana tabbatar masa wanki tayi, ɗankwalin da take yafe dashi tun safe ta ɗaura shi a yanzu, yayi baya ma kamar zai zame gashinta na fitowa ta gaba, mai laushi ne da alama don duk ya tashi sama.

Bai san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce a fuskarsa ba kafin ya ɗaga mata kai.

“Ameen ya Allah, nagode sosai.”

Kuma ga mamakinsa sai itama tayi nata guntun murmushin sannan muryarta ta ƙara fitowa.

“Insha Allah meeting ɗin zai tafi daidai.”

Tana faɗin haka ta shige hanyar Kitchen ɗin dake gefenta bokitin na bin bayanta.

***

Dab da magariba ne lokacin, Aminu ya kammala komai na aikinsa na ranar a garejinsu, kuma har yayi sallama da kowa ya fito bakin titi lokacin da wayarsa tayi kara, yana tsaye da gefen titin ya dauko ta ya duba, Baba ne, don haka ya dauka da sauri ya kara a kunnensa yana gaishe shi.

“Lafiya kalau Aminu, kun tashi ne?”

“Eh Baba, yanzu ma na fito zan taho gida.”

“To ka biyo ta nan, akwai kayan da zaka dauka sai mu tafi tare.”

“Insha Allah Baba gani nan.”

Da haka ya kashe wayar, ya sauke ta ɗaga kunnensa daidai lokacin da mai mashin ɗin ya taho da wani irin saurin da ba Aminun kaɗai ba hatta mutanen dake baya dashi basu ga wucewarsa ba sai dai ƙarar injin mashin ɗin da kuma sanda yabi ta kan Aminun dake tsaye a bakin titin ya take shi tun daga kan ƙafafuwan sa.

Salatin mutane har da ihun wasu ya gauraye iska a lokacin da mai mashin ɗin ya murde kan mashin ɗin ya miƙe titi ba tare da ta tsaya ba, kansa na dauke da hular kwano baka don haka babu wanda ya iya ganin fuskar sa.

Wasu daga cikin mutanen suka bishi da jifa amma babu wanda ya same shi, gudu kawai yake yi har lokacin da ya fita daga unguwar baki ɗaya, ta lunguna ya dinga gujewa danja ba tare da ya tsaya a koina ba har ya zuwa unguwar Sardauna Cresent ƙofar gate ɗin gidan da ya fito, inda tun kafin ya karasa mai gadin dake zaune a waje yana jira yayi saurin buɗe masa gate ɗin ya shige.

A gaban wata ƙatuwar bishiya dake harabar gidan ya tsayar da mashin ɗin sannan ta cire hular kwanon dake kansa, daidai lokacin da wayarsa ta shiga fitar da karar vibration daga aljihunsa. Ya ɗago ta ya danna wajen amsawar ba tare da ya damu ya duba sunan mai kiran ba.

“Awa ta biyu a waje kafin yaron ya fito.” Ya faɗa yana ƙoƙarin balle maɓallin rigarsa na gaba.

Daga ɗaya ɓangaren wayar, Hajiya Kilishi tayi murmushinta mai armashi kafin tace.1

“Kace min an gama kawai Awwalu.”

“An gama Hajiya, kema kin san komai daidai yake tafiya.”

Ta gyaɗa kanta a hankali, tabbas haka ne, komai  daidai yake tafiya, me yasa ma zata damu da tambaya? Awwalu ya taɓa kasawa umarninta ne?ko kuwa ta manta sanda yayi babban aikin da yafi wannan a wajen hatsari ne ma? Aikin da shine ginshiƙi samun ƴancin da take kirgawa dashi a kowacce nasarar da take samu.

Bakinta ya sake tafiya da wani murmushin, abinda ya faru yanzu tsaraba ce ga Amina, don ba’a banza zata buɗe mata fuskarta ba, ba’a banza zata san wace ce ainihin Kilishi ba, dole ne ta tunkare ta da kakkarfar hujjar da kokwanton ikonta ba zai taɓa samun waje a zuciyarta ba…. Aminu shine farko a yanzu, kuma idan komai ya tafi daidai zai zama na karshe, amma da an samu wani akasi ƙofar ta buɗe kenan, duk wanda ya jiɓanci Amina ya shigo cikin lissafinta.

Zata ɗaure Amina ne da jijiyoyin jikinta, bata isa ta tsallakewa dukkan sharrinta ba a yanzu, ta riga ta shigo cikin jerin mutanen da take juyawa da yatsan hannunta.

“Ya batun Ma’aruf ɗin Hajiya? Na gaya miki yayi nisa a binciken da yake yi, idan har ya riga mu nemo inda Mr. Okafor yake wallahi abubuwa zasu canja daga kalar da muka san su, ya kamata ki tsayar dashi har sai mun riga shi nemo mutumin nan mun tura shi lahira tukunna.”

Muryar Awwalun ta katse ta daga tunaninta, kuma a lokaci guda sai murmushin dake kan fuskarta ya ɗauke, yanayin fuskarta ya koma wani iri da babu abinda zaka tsinta a ciki, ta haɗiye wani abu a cikin maƙogwaronta tana kallon tarin magungunan Ma’aruf ɗin da ta baje daga kan gadonta, a hankali ta girgiza kanta sannan tace.

“Kar ka damu Awwalu, ina sane dashi so nake ya kammala da mutanen RTL ɗin nan tukunna, idan sun gama daidaitawa kuma kuɗaɗen sun shigo zamu jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne, kafin ya dawo hayyacinsa munyi gaba da kuɗin kuma munyi gaba da shi Mr. Okafor ɗin… Kamar koyaushe sai bayan ya tashi zai fara lalube cikin duhu!”7

***Life is what happen to us when we are busy making other plans.

-Unknown.

**

Ranar lahadi ne da misalin ƙarfe huɗu na yamma, Amina na tare da Samirah da kuma Munaya a kitchen suna aiki tare da hirarsu wanda mafi yawanci Samiran ce ke tsokanar Munaya akan zuwan da tayi, tunda tun farko Samiran ce ta fara zuwa kafin ita kuma ta shigo m daga baya.

“Wallahi sai ayi baƙi kashi-kashi su zo gidan nan su tafi baki ganta ta fito ba, amma kiga wai itace yanzu tazo taya aiki babu gaira ba dalili.”

Cewar Samiran a lokacin da take daka tafarnuwa ƴar kadan da zata saka a miyar dake kan wuta daga bayanta.

Munaya tana yanka carrots ta ɗago ta kalle ta tace.

“Ki kara faɗar abu guda ɗaya ki gani idan ban jefe ki da grater nan ba.”

Amina tana murmushi daga inda take blinding abarba tace.

“Ki ƙyale ta haka mana Samirah, shikenan don tazo sai da dalili? Da nan da cikin gidan ai duk ɗaya ne.”

Samiran ta girgiza kanta.

“Ba zaki gane bane Aunty Amina, saura fa sati biyu ta fara exams, da su Zahra suna nan zasu gaya miki a irin wannan lokacin ba’a ganinta wallahi, idan ta shiga ɗaki sai ta yini akan littafi sallah ce kawai ke tada ita, ko Hajiya sai dai tayi ta faɗan taci abinci, Allah karatun da take yi har na gama rayuwata a duniyar nan ba zanyi rabinsa ba…”

Bata karasa ba kuwa lokacin da Munaya ta saita daidai bakinta da wani katon karas din dake gefenta ta jefe ta dashi, amma duk haka Samiran bata yi shiru ba, ta cigaba da bayanin ta tana faɗin ita bata yarda da zuwan nan nata ba sam, wanda ke saka su dariya.

Amina ta tsiyaye ruwan abarbar a hankali cikin wani katon bowl tana kokari kar ya taɓa ciwon hannunta da bata daɗe da jinsa ba wajen yanka albasa, tana jinsu har yanzu Munaya na rokonta akan ta kyale ta amma Samiran taki yin shiru.

Munaya tana da saukin kai sosai, don tazarar shekarun dake tsakaninsu da Samiran da ɗan yawa, amma idan suna hira irin haka ba zaka ce ba, ta juya tana kallonsu, ita kanta dai ta ɗanyi mamaki zuwan Munayan tunda tun bayan ranar da suka zo gabaɗaya suka gaisa sau ɗaya ra kara shigowa ranar da suka yi zancen littafin nan.

Samirah ce dama kusan kullym zata leko ɗan bsyami ko saƙonta, a dazu ma tazo kawo mata wata darduma ne mai kyau daga Hajiya Maimuna taga tana aikin shine ta tsaya don ta taya ta, bata daɗe ba kuma sai ga Munayan itama ta shigo, ganin suna aikin yasa itama ta tsaya taya su.

“Ki cigaba Kar ki fasa, I have my ways of torturing you kin sani wallahi.”

Munayan ta faɗa yayin da suke dariya dukkaninsu, Amina ta ɗauko bowl din da ta juye ruwan abarbar ta taho don ta saka shi fridge ya ɗanyi sanyi kafin ta ƙarasa abinda zata yi tazo haɗa lemon.

Fridge ɗin yana daga gefen kofar shigowa kasancewar shine na karshe a yadda drawer kitchen ɗin take a jere, don haka ta taho wajen daidai lokacin da Ƙofar kitchen din ta buɗe Ma’aruf ya shigo ciki, yana sanye da wata loose riga fara mai dogon hannu, gashin kansa a barbaje kota’ina kamar yadda yake tun safe kasancewar bai fita ba yau, amma babu banbanci da cewar yana nan din, don tun safen yana ɗakinsa yana faman wani aikin a computer, banbancin jiya da yau shine a yanzu fuskarsa fayau take, babu gajiya irin ta jiya ko kadan, ya riga ya manta duk wannan tunanin meeting din nan, don bayan dawowarsa a jiyan ya bata labarin cewa komai ya tafi daidai tsakaninsu da mutanen da suka yi meeting ɗin.

STORY CONTINUES BELOW

“Kinyi addu’a mai kyau kuma Allah ya amsa.”

Kalaman da ya gaya mata kenan a jiyan wanda ta kwana suna yawo acikin kanta. Shi yasa a yau ma da safe breakfast mai daɗi suka yi yana kara gaya mata irin nasarar da suka yi suka shawo kan mutanen nan ɗaya kamfanin suka kulla alakar kasuwancin a tsakaninsu, hirar dake ƙara sawa tana fahimtar abubuwansa da yawa, tana jin zuciyarta na canjawa game da tunaninta akansa, wasu abubuwa da yawa a cikin kanta na gaya mata cewa ba shine wannan Ma’aruf ɗin da ya bata wannan saƙon ba… Ba shine kuma wanda Iyayenta suka gaya mata yana da matsalar ƙwaƙwalwa ba.

Shi yasa ko da ya gaya mata cewa Ishaq ɗin da suke waya kullum ya dawo daga tafiyar da yayi zai zo a yau, zuciyarta tayi tunanin aƙalla ta tarbe shi da irin tarbar da ya kamata, ba don komai ba sai don ta san hakan ne ya dace kuma ko zata yiwa kanta ƙarya ta sani cewa tana son yadda zamansu ke tafiya duk kuwa da yadda koina a tunaninta ke gaya mata cewa akwai abinda ke shirin faruwa.

Ƙafarta ta ƙarasa wajen Fridge ɗin ne daidai lokacin da ya shigo, taga idonsa ya haska da mamaki yana kallon su Munayan da kuma aikin da suke yi.

“Me yake faruwa anan?”

Muryarsa tasa dukkaninsu juyowa a lokaci guda, kuma a taken fuskar kowannensu ta faɗaɗa da murmushi yayin sa Munaya ta kira shi cikin wani abu mai kama da waƙa.

“Yayaaaaa B….”

A ƴan kwanakin nan Amina ta fahimci kusan duk sanda suka ganshi haka ne, haka gaisuwarsu ke farawa kamar sun daɗe rabonsu dashi, hakan ya tabbatar mata cewar ba ganinsa suke yi sosai a baya ba, a yanzu ne lokaci ya kawo musu shi kusa dasu wataƙila kamar yadda suka saba a ganinsa a baya.

Kuma kafin tace wani abu, dukkansu suka ajiye mata aikinta sunyi wajensa, wani abu ya faɗa a zuciyarta ganin yadda kowannensu fuskarsa ke ɗauke da fara’a sun baibaye shi da maganganun da kallon fuskokinsu kawai yake yi, ba irin Samirah da ta shiga bashi labarin da ta gama bata a ɗazu na wani competition ɗin kamfanin Maggi da aka zaɓe ta zasu je suyi a Abuja, Munaya kuma tana ta maimatawa wai ta gaya masa labtop ɗinsa take so ko kuma ya siyo mata wata sabuwa irinta…

Me yasa ne wai take tunanin akwai wani rami a rayuwar waɗannan mutanen?

Tana jiyo muryoyinsu har lokacin da ta shiga store don neman wani abu ba tare da ita taxe komai ba, kuma ba’a daɗe ba taji an ƙwankwasa kofar store ɗin dake buɗe a hankali sau biyu kafin muryarsa tayi magana a bayanta.

“Akwai ruwa anan?”

Ta juyo ta kalle shi, yana tsaye daga ƙofar store ɗin, ta manta cewa ruwan dake ajiye a kitchen ya ƙare tun dazu kuma bata fito da wani ba, don haka da sauri ta juya bayanta inda katan din ruwan yake a jere ta buɗe na saman ta ɗauko ɗaya, yana tsaye yana kallonta har ta ƙaraso ta miƙo masa, kuma ga mamakinta tana ƙarasowa sai kawai ya hado robar ruwan da hannunta gaba ɗaya ya jawo ta zuwa gabansa, ƙafafunta suka taho dab dashi yayin da ya dago da hannun nata yana kallo, ba shiri numfashinta ya katse a ƙirjinta lokacin da yasa ɗan yatsansa ɗaya ya taɓa daidai wajen data yanke ɗazu.

“Me ya faru?”

Muryarsa ta fito a yana kallon ciwon.

Sai da ta haɗiye yawu tana ƙoƙarin saita tunaninta kafin tace.

“Da wuƙa na yanke.”

“Me kika saka a wajen toh?”

Muryarsa ta sake tambaya a hankali ta yadda har tana jin ƙarar wukar da Munaya ke amfani da ita daga can kitchen ɗin, da kuma nuryar Samirah da ta fita waje tana waya.

Ta sake haɗiye wani yawun a makogwaronta.

“Ba komai na wanke ne kawai.”

Sai ya kawo daya hannunsa yasa su duka biyu ya rike natan, sannan ya buɗa ciwon sosai don yaga zurfinsa, zafin ya tafi har cikin kanta ta runtse idanunta da sauri tana cije lebbenta, sai yayi saurin sakin wajen sannan ya rufe yatsan nata da duka hannayensa biyu kafin yace.

STORY CONTINUES BELOW

“I’m sorry na duba ne na ga yadda yayi and it was deep.” (kuma yayi zurfi.)

Ta buɗe idanunta a hankali sannan ta ɗaga kai ba tare da tace komai ba, kuma bai saki hannunta nata ba sai ya cigaba da rike shi yana kallonta, hakan yasa ta ɗago da idonta kalle shi da ɗan ƙaramin mamaki.

“Aikin me kuke yi haka?”

Ya tambaya tun kafin tayi wani tunanin, sai ta girgiza kanta.

“Abinci ne kawai.”

“Kala-kala haka?”

Muryarsa ta sake fitowa da wani abu da ya shiga bin kowacce jijiya ta jikinta yana kassara ƙarfinta, taji kamar wani yana zazzaga mata wani magani mai karfi ne da aka haƙiƙance zaiyi tasiri akanta, kuma a yadda tata muryar ta fito tana rawa, kamar dama anyi mata baki ne cewar hakan ne zai faru.

“Kace abokin ka zai zo.”

“Ishaq?” Ya tambaya kai tsaye sai kuma ya sake cewa.

“Ya salam duka saboda shi kuke yin wannan aikin?”

Shi ko kadan unaninsa bai kawo masa cewa don Ishaq ɗin zai zo ya kamata ayi wani abu ba, duk da a baya ma idan zaiyi baƙi Ruƙayya kan shirya musu wani abun amma a yanzu ya riga ya manta da hakan kwata-kwata, saboda haka a lokaci guda zuciyarsa taji dadin hakan, sai kawsi ya gyada kansa yana kallonta sannan yace.

“Thank you.”

Ta ɗaga kanta da sauri itama tana fatan hakan ne karshen zancen nasa, don bata san me zata zama ba idan har ya cigaba da magana rike da hannunta a hakan. Kuma kamar yaji fatanta, sai ya zare hannunsa nasa a hankali, taji ɗuminsu yana barin fatarta.

“Zan nemo abu in rufe miki ciwon anjima insha Allah.”

Da haka ya juya ya fita rike da robar ruwan a hannunsa.

A lokaci guda Amina taji kamar numfashinta yayi wata tafiya mai nisa ne sai a yanzu take iya zuƙo shi, ssi kawai ta juya itama ta ɗauko wata robar ruwan ta balle hancinta ta shiga sha yayin da bayanta ya jingina da drawers din store ɗin.

Sai da ta kusa shanyewa sannan ta tsaya, tasa bayan hannunta tana goge wanda ya zuba a gefen bakinta. Bata san me yake shirin fara damunta ba amma koma meye, so take ta tunawa kanta cewa duk abinda ke faruwa wannan gaske ne ba labari ba da komai zai tafi daidai, abubuwa ba zasu tafi kamar a mafarki tare da mutumin da daga shi har ita basu san juna ba sai bayan aurensu kuma har yanzu bsta san manufarsa akanta ba.

Ma’aruf ba zai taɓa sauko da kansa haka akan ita ɗin da ba kowa ba, don ta sani cewa bayan matar daya aura Allah kadai ya san matan daya sani a a rayuwarsa ko ma wanda yake tare dasu a yanzu, to don me yasa hankalinsa zai tsaya akan ita din da ba kowa ba, ita ɗin da sa baiyane yake cewar ba sa’ar rayuwarsa bace.

Ta girgiza kanta tana kokarin rufe robar ruwan, wannan lokacin kamar zubar ruwa ne kawai kafin zuwan tsawa, kamar iska ce mai daɗi kafin guguwa, sannan kamar kaɗawar ruwan teku ne a hankali kafin ambaliyar sa, akwai wani abu dake jiran ta bayan wannan, kawai dai dan adam baya taba sanin lokacin da ƙaddara ko kuma wata masifar rayuwar ke zuwar masa ne.

Muryar Amma ta cikin mafarkin nan ta gifta a cikin kanta lokacin da take cewa

“Me yasa kika yarda ba zaki iya ba Amina…”

A hankali tayi ajiyar zuciya tana fatan Allah yasa koma meye ke shirin faruwa ta iya tunkararsa da ƙafafunta a tsaye, daidai lokacin da a zahiri ta jiyo muryar Samirah ta shigo tana kiranta.

“A ina kika ajiye sugar?”

Sai kawai tayi sauri ta ƙarasa goge bakinta sannan ta ajiye robar ruwan ta fita.

STORY CONTINUES BELOW

****

Karfe Bakwai daidai Ishaq ya iso, kuma Amina bata san me ya faru ba, don minti biyar bayan zuwansa sai ga sallamar ɗaya abokin Ma’aruf da shima ta riga ta haddace shi a waya mai suna Faruk.

Su uku kaɗai suka cika falon da surutu kamar su biyar, kuma duk yadda take ganin Ma’aruf na da magana sai a lokacin taji nasa mai sauki ne, don kafin taji muryarsa taji tasu da yawa musamman Faruk ɗin, don shi yafi Ishaq yi mata magana sosai ma, har matarsa da ƴaƴansa yayi alkawarin kawo mata tunda yace yanzun a sama kawai Ma’aruf ya kira shi yace masa yazo.

Kuma har lokacin da suka zo ɗin su Munaya basu tafi ba, Samirah dai taso tafiya amma sai Munayan tayi ta roƙonta akan su ƙara tsayawa tukunna, wani abu da ya ƙara bawa Amina mamaki don ita kanta ta san babu wani dalili Munayan ba zata yi ta cewa su tsaya ba. Ilai kuwa a lokacin da suka je kai musu abincin nan, a lokacin ta samu amsarta, saboda idon Ishaq na kan Munaya tunda suka shiga har ta juya Kitchen don ta ɗauko wani abun, kuma zata rantse ma taga sanda suka yiwa junansu murmushi lokacin da take zuba masa lemo, Allah ya sani yau ta fara ganin Ishaq ɗin amma sai taji zuciyarta na jiyewa Munaya daɗi idan har hasashenta akansu gaskiya ne, don duk inda nutsatsen namiji yake za’a saka Adam a wannan layin, kuma itama Munaya babu ruwanta da wani hargitsi sam.

Sun ji daɗin tarbar da suka samu kwarai, don ba’a kalamansu kaɗai ta fahimci hakan ba, har a fuskar Ma’aruf da kuma yanayin kallon da yake mata tun lokacin da taje ta sako wani dogon hijabi bayan shigowar su, wani abu da ita kanta taji ta kyauta da tayi hakan.

Bayan sallar isha’i ne sannan suka yi musu sallama suka fita, kuma sun daɗe a waje suna magana don har bayan tafiyar Faruk ɗin shi da Ishaq suna nan, har su Munaya suka tafi ta ƙarasa wanke iya kwanukan da aka ɓata kasancewar basu tara wanke-wanken ko ɗaya ba dama a ɗazu.

Kuma tana sallah lokacin da ta jiyo ƙarar fitar motar Ishaq ɗin, sai dai har ta idar ta gama addu’o’in ta da komai bata ji lokacin da Ma’aruf ya shigo ba ko kuma don haka ta ƙudirta a ranta cewa cikin gida ya shiga. Da wannan tunanin ta ninke sallayar tare da hijabin ta ajiye su a gefe, ta ɗauko wayarta don kiran su Amma, sai dai daga layin nata har na Aminu bai shiga ba, kuma bata son kiran Baba a wannan daren, don haka ta bari zuwa gobe, ta nufi wardrobe ɗinta don ta ɗauko kayan bacci, wata sabuwar doguwar riga ta dauko sannan ta dawo gaban gadon don ta canja.

Ɗankwalinta ta fara cirewa ta ajiye shi a kan gadon sannan ta shiga kokawa da zip ɗin rigarta, amma ga mamakinta saiya riƙe ɓam yaki ko motsi, gashi ciwon hannunta ba zai bari ta rike shi da kyau ba, na dama kuma yaki ƙarasawa can saman, dama tunda tazo saka kayan ta kula yana da matsala amma bata yi tunanin ta kai haka ba.

Har sai da hannunta ya ƙage ta tsaya ta tattaro dukkan ƙarfinta sannan ta cigaba da jansa, kafin a lokaci guda kamshin turaren Ma’aruf ya shiga hancinta.2

***

A waje bayan Faruk ya tafi, sun dade a tsaye shi da Ishaq suna hirar tarin wasu abubuwan da suka shafe su wanda yawanci duk akan matsalolin dake baibaye da rayuwar Ma’aruf ne, sai kuma zancen Abdurrahim, ƙanin Ma’aruf ɗin dake can New York wata makaranta ta Bebaye irinsa, (Rochester Institute of Technology.) Don Baffa ya gaya musu cewa saura watanni biyu kawai ya kammala ya dawo gida.

Bayan wannan sun tattauna zancen Hamida ma inda Ishaq yayi-yayi da Ma’aruf akan ya ɗauko yarinyar daga inda ya kaita ya dawo ta ita cikinsu, amma ya ɓata bakinsa a banza don ya riga ya rantse cewar Ruƙayya ba zata taɓa sanin inda Hamida take ba sai ya kammala da al’amarinta gaba ɗaya, ko shekaranjiya da Mami taso yi masa zancen itama kai tsaye ya dakatar da ita ta hanyar gaya mata cewa lokacin da zai ɗauko ta bai yi ba, don haka itama taja bakinta tayi shiru, don dukkaninsu sun sani cewar idan har ya furta abu, Baffa ne kawai zai iya sauke shi daga kansa, amma ko da suka yi magana da Baffan shima cewa yayi…

STORY CONTINUES BELOW

“Wannan zancen naku ne kai da mahaifiyar yarinyar Muhammad, duk abinda kuka yanke idan har ba kuskure bane mu namu addu’a ne tunda kune kuke da iko akanta fiye damu. Kuma kowannen ku yana da ikon da zai riƙe ta, duk da dai a matsayinta na mace an fi so ta zauna a gaban mahaifiyarta, amma idan har za’a samu matsala wajen tarbiyarta ko lafiyarta kamar yadda aka fara yanzu, to zamanta a wajen naka zai fi.”

Wannan zancen na Baffa shi ya bashi ƙwarin gwiwar cigaba da shirin da yake da niyya wanda yake jiran lokacin kawai. Daga ƙarshe kuma suka ƙare da zancen ginin su wanda Ishaq ɗin ya gaya masa cewar ya samo wasu sababbin masu ginin da zasu fara aikin tunda Ma’aruf ya sallami waɗancan.

Kuma baiyi mamaki ba da Ishaq ɗin baiyi masa zancen Amina ba, don ya riga ya fahimci cewa ba sai yayi ɗin bane, akwai wasu abubuwa da ba lallai sai sun furta su a tsakaninsu ba, wasu abubuwa ne da ƙarara kowannensu ke ganewa idan ɗayan yana ciki, don haka a yanzu ma Ishaq ya riga ya sani cewar ya riga ya yanke koma wane irin hukunci ne game da zamansu ba sai sun ɓata lokaci wajen biya shi ba.

Da haka suka yi sallama, sabon maigadin da ya samo ya sake budewa Ishaq gate ɗin gidan, shi kuma ya koma ciki.

***

Yayi sakanni biyu tsaye daga bakin kofar yana kallon yadda take kokawa da zip ɗin rigarta kafin ta ankara dashi, watakila jikinta ne kawai ya bata cewar yana daga bakin kofar, don a lokaci guda ta juyo da sauri tana kallonsa, fararen idanunta suka zare akansa yayin da a lokaci guda ta saki hannayenta duka biyun suka sauka a gefenta.

“I’m sorry banyi sallama ba ko?”

Sai ta girgiza kanta.

“Babu komai ban ji lokacin da ka shigo bane.”

Ya cije lebbensa tsaye a jingine kofar kafin yace.

“I’m sorry bana so in ɗauki lokaci ne kiyi bacci.”

Idanunsa na kallon fuskarta da yaga kamar tana ƙoƙarin kore wani abu wani abu mai kama da mamaki kafin ta tambaya.

“Wani abu kake so?”

Lokaci ne ya tsaya cak a cikin kansa da wannan tambayar yayin da fatar bakinsa ta bude kamar zai ce wani abu yana kallonta, tsakaninta da Allah ta fadi hakan ba tare da ta san tarin ma’anonin da za’a iya fitarwa daga kalaman nata ba, ganin tana cigaba da kallonsa yasa ya sake cije leɓɓensa na ƙasa sannan ya girgiza mata kai.

“I want to treat your hand.” (Hannunki zan duba.)

Ya faɗa yana kallon yadda fuskarta ke nuna tarin yanayi kala-kala, ƙafafunsa suka tako cikin ɗakin a hankali zuwa inda take tsaye, kuma kamar a wani shiri sai iska ta buso daga windon da yake fuskantar su daidai lokacin da ya tsaya a gabanta, kuma bai ɓata lokaci ba yasa hannunsa ɗaya ya ɗauko nata mai ciwon nan.

Gabaɗaya tsawonta iya kafadarsa ne, gashin kanta da babu dankwali ya taso sama yana shaida laushinsa, da zai iya a wannan lokacin zai zare ribbon din data ɗaure shi ne don ya sauko kafadunta yaga iya tsawonsa, amma sai ya daurewa wannan tunanin ta hanyar kallon yatsun hannunta da yake riƙe dasu.

Ya san cewa shi mutum ne da yake ƙarbar respect daga ɗimbin mutane, kuma a iya kokarinsa yana kokarin ganin ya kyautatawa duk wanda ya shigo hanyarsa, da kuma kaffa-kaffa musamman a yanzu don ganin bai yi wani abu da zai iya cutar dasu ba, amma Allah ya sani bai taɓa haɗuwa da wanda a lokaci guda yaji zuciyarsa na tsoron ciwonsa akanta ba irin yarinyar nan, yarinyar da a baya bai damu da yadda zaiyi kokarin samun bayanin da yake so daga gare ta ba,

Wani bandeji ne mai haɗe da audugarsa a jiki, don haka magani kawai ya ɗiga a jiki daga cikin wata ƴar kwalba sannan ya rufe ciwon nata dashi, ai kuwa ta runtse idanunta a lokaci guda tana jin zafin na tafiya har tafin ƙafarta.

STORY CONTINUES BELOW

“Zuwa safe zaki iya cirewa sai a saka wani, insha Allah a kwana biyu zai warke.”

Ya faɗa yana sakin hannun nata, kuma duk da zafin da take ji haka ta shiga daga kanta da sauri alamun ta fahimta.

Ya rufe maganin sannan ya wuce ta zuwa wajen da mudubin ɗakin yake, ya ajiye roll ɗin plaster da kuma kwalbar maganin akai sannan ya juyo ya dawo inda take tsaye tana cigaba da danne ciwon.

Kuma bata yi wani tunani ba lokacin da ya tsaya a bayanta, dab da ita sosai, don haka da sauri ta juyo gabadaya ta kalle shi amma sai ya saka hannayensa duka biyu akan kafaɗunta ya juyar da ita.

“Zan taimaka miki da zip ɗin ne…”

Ya faɗa muryarsa na fitowa dab da kunnenta sosai, kuma kafin tayi ƙokarin kamo tunaninta muryar tasa ta cigaba da cewa.

“Akwai abubuwa da yawa game dani a zuciyarki na sani, amma ina so a saman komai kisa a ranki cewar ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah.”

Ya furta hakan yayin da hannunsa ya kai kan zip ɗin, sauran yatsunsa na ɗaya hannun suna taba fatar bayanta, sai kawai ta rufe idanun gabadaya tana ƙoƙarin saita numfashinta, kuma da ja ɗaya kawai hannunsa yayi ya sauke zip ɗin sai dai bai kai shi har ƙasa ba, daga daidai tsakiya ya barshi, taji sanda yatsunsa suka dauke daga saman fatar ta, da kuma sanda yake matsawa, sai ta buɗe idonta lokacin da ya zagayo daidai saitin ta.

“Nagode.” Ba zata ba taɓa iya tantance yanayin yadda muryar tata ta fito ba, ya gyaɗa kansa.

“You are welcome, sai da safe.”

Da haka ya juya ya nufi kofar ɗakin yana rufo mata ita.

Sakan ɗaya, biyu, uku, suka wuce Amina tana ƙoƙarin saita numfashinta kafin a hankali ta ɗauko rigar baccin nan ta karasa abinda zata yi, wanda har ta gama komai ta kashe fitilar ɗakin kalamansa na yawo a cikin kanta.

…ba zan taba cutar dake ko in takurawa rayuwarki ba insha Allah.

Sai kawai ta rufe idanunta sannan ta dunkule jikinta akan gadon, kuma bata bawa zuciyarta wani damar tunani ba don bata san buhu nawa zata kwance na tambayoyin da bata da amsar su a zahiri dama cikin kanta ba.

Ya rabbi lakaal hamdu kam yanbaghi li jalaali wajhika wa adheemu sulɗaanik.

Bakinta ya furta addu’ar hankali yayin da take jin ma’anar ta na tafiya har ƙasan zuciyarta.

***

Washegari…

Ƙarfe goma na safiyar Litinin, a irin wannan lokacin Amina ta saba da wani irin shiru don ko’ina tsit yake, duk wani mai fitar safe ya daɗe da yin gaba, ƴan makaranta da masu aiki da mafi yawanci sun fi yawa a kowanne gida.

Tana daga kitchen a lokacin tana ƙoƙarin fara aikinta ta tsinkayi ƙarar ƙwanƙwasa kofar, mamaki ya ɗan kamata don ta san babu wanda zata yi tunanin zuwansa a wannan lokacin, ta gyara zaman ɗankwalinta yadda ta yafa shi sannan ta fito daga kitchen ɗin ta iso ƙofar falon kuma ba tare da tunanin komai ba ta buɗe ta,a lokaci guda siffar Hajiya Kilishi dake tsaye ta shiga idonta tun kafin sakon saninta ya ƙarasa ƙwaƙwalwar ta.

Tana sanye da wata haɗaddiyar lafaya ruwan makuba (maroon) da ta nannaɗe ta tsaf a jikinta, fuskarta kamar kullum ɗauke da wannan murmushin nata, murmushin dake haska annurin fuskarta a kodayaushe yana ƙawata kammaninta.

Babu dalili Amina taji gabanta ya faɗi amma tayi saurin kore hakan wajen yin nata murmushin itama.

“Sannu da zuwa Mami, barka da zuwa.”

STORY CONTINUES BELOW

“Barkanmu dai Amarya. Yau dai na ajiye kyuiyata a gefe nazo ganin ɗakin amarya.”

Wani murmushin mai haɗe da kunya Amina ta sake yi kafin tayi baya don bata hanya tana kara fadin ‘Barka da zuwa’, kuma kai tsaye kuwa ta shigo haɗe da sallama yayin da ƙamshin daddaɗan turarenta ke rufo mata baya.

“Wa’alaikum salam.”

Ta amsa sallamar tana rufe ƙofar har a lokacin da murmushi a fuskarta, murmushin da a lokaci guda ya ɗauke sakamakon juyowar da Hajiya Kilishi tayi tun kafin ta kai tsakiyar falon tace.

“Idan akwai muƙulli rufe ƙofar dashi Amina, akwai maganar da zamu yi ne.”

Zuciyarta ce ta fara bugawa a kirjinta kafin ta juyo ta kalle ta, amma ganin murmushin dake kan fuskarta har yanzu, yasa itama ta dawo da wani dan guntu kan leɓɓenta sannan tace.

“Toh Mami.”

Da haka ta rufe kofar tana ƙoƙarin gayawa zuciyarta cewa gabanta ba faɗuwa yake ba sannan ta juyo ta ƙaraso ciki.

A lokacin ta zauna daga tsakiyar kujera mai cin mutum uku a falon don haka ita tameni waje daga ɗaya karshen ƙaton carpet ɗin ta zauna tana fuskantar ta.

“Barka da Asuba Mami, fatan kun tashi lafiya?”

Ba kallonta take ba amma daga yanayin yadda muryarta ta fito wajen amsawa ta fahimci har yanzu murmushin take yi.

“Mun tashi lafiya, Ya bakunta kuma? Ko da yake ai naga su Samirah sun saka kin saba tuni.”

Bata ce komai ba illa wasa da karshen skirt dinta da take yi tana cigaba da murmushin da zata kira na dole, don bata san me yasa zuciyarta ta kasa zama waje ɗaya ba.

Hajiya Kilishi ta kalli ƙaton screen din Tvn dake tsakiyar falon dama sauran kayan kallon da aka jera akan hadadden stand ɗin Tvn da dubu tamanin da biyar ta bayar aka siyo shi sannan tace.

“Gidan shiru ke kaɗai baki ko kunna Tv ba?”

Da wani murmushin a fuskarta tace.

“Ai ba’a hada Tvn ba har yanzu Mami.”

Muryarta ta fito ƴar ƙarama a cikin shirun dakin, kamar tana son ta shaidawa Hajiya Kilishin ƙanƙanta da kuma rauninta.

“Baku gaya min ba ai, gashi jiya kuwa yaro mai gyaran satelite ya shigo har cikin gida, da ya karaso ya hada muku, amma a bar ki a gida haka shiru, shi ya fice ya tafi hadaniyar gabansa ba zai tuna da wani sha’anin Tv ba.

Sai ta sake girgiza kanta tana cigaba da murmushin.

“Ba komai Mami, duk sanda aka sa baza’a makara ba ai.”

Ta fadin hakan lokacin da take kokarin mikewa, amma a lokaci guda Hajiya Kilishin ta tsayar da ita.

“Ina ziki je kuma?”

“Mami, kayan breakfast zan kawo miki.”

Ta faɗa taka kallonta, sai ta girgiza kanta.

“Barsu nagode, dawo ki zauna.”

Umarnin dake cikin muryar ya kaɗa hantar ta, taji wani abu yana ƙoƙarin ɓallewa daga cikin zuciyarta, amma sai tayi saurin ture hakan ta dawo ta zauna ɗin, hannunta na taɓa hannun kujerar gefenta kamar tana neman taimakon ta.

Kuma zaman nata sai ya zama kamar shine farawar wani shafi na farko a rayuwata, don watakila idan zata bada labari, zata fara ne ta kansa, daga lokacin da kafafunta suka sake komawa kan carpet ɗin nan da kuma lokacin da muryar Hajiya Kilishi ta sake ratsa shirun ɗakin da cewar.

“Amina kunyi waya da mutanen gida kuwa jiya?”

Sai da ta haɗiye wani dunƙulen abu da bata san sunansa ba a kirjinta sannan ta girgiza kai.

“A’a Mami, na kira su dai jiyan amma bai shiga ba.”

“Ina wayarki?” Kai tsaye ta sake wata tambayar da ta fito kamar tsawa.

Kan Tv’s stand ɗin nan ta nuna inda bayan fitowarta da safen ta saka ta a caji.

“To matso ki kira su.”

Wannan karon sai da ta kalle ta tsawon wasu sakanni fuskarta na haskawa da mamaki sannan ta matso a hankali zuwa wajen wayar, lokacin da ta cire ta daga caji taji kamar hannunta na rawa amma tayi saurin fara dannawa ta lalubo nambar Amma.

Sai da ta sake kallon Hajiya Kilishin da murmushin fuskarta ya rage tasiri kafin ta kara wayar a kunnenta, kuma cikin wata iriyar sa’a, bugu ɗaya biyu sai Amman ta dauka, sautin muryarta kadai ya doka wani abu a ƙirjinta tun kafin ta fahimci abinda take faɗa.

“Amina yi haƙuri, tun jiya bamu kira ki ba, muna asibiti ne sai da safen nan muka fara samun nutsuwa…”

“Asibiti? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!… Me ya faru Amma? Me ya faru?”

A yanzu ta tabbatar hannun nata rawa yake, don tana jin yadda yake tafiya tare da bugun zuciyarta.

Daga cikin wayar Amma tayi ƙokarin gyara muryarta kaɗan sannan tace.

“Aminu ne mai mashin ya taka shi jiya da daddare a wajen aiki, amma sun ce jikin nasa da sauƙi kar ki ɗaga hankalinki, yanzu mu ma zamu shiga mu ganshi…”

Zancen ya katse a lokaci guda da Amina ta nemi wayar a kunnenta ta rasa. Hajiya Kilishin da a yanzu ke tsaye akanta riƙe da wayar tasa hannu ta ɓare bayanta ta fito da batirin ta jefar dashi gefe, sannan ba tare da ɓata wani lokaci ba ta karya wayar gida biyu itama.

Kuma taku biyu kawai ya mayar da ita baya kan kujerar da ta taso, ta cigaba da kallonta har a yanzu da ragowar murmushin nan a fuskarta kafin muryarta ta fito cikin wani irin sauti da yake ainahin halittar ta, sautin da yake manne a kirjinta tare da zuciyarta dake ƙawata mata tarin hanyoyin da kullum suke ɓullewa ga nasararta, sautin da a duniya kaf, mutum huɗu ne kawai suke sanin da kasancewarsa, sai a yau da ta zabi Amina ta zaman cikon ta biyar ɗin, cikon da take fatan zai zama mataki na ƙarshe da take da yaƙinin zai kai ga nasararta.

“Barka da shigowa cikinmu Amina.”1

Kalamai biyar ɗin data furta kenan wanda ta lissafa cewa adadinsu ya dace da lambar matsayinta, murmushi kan fuskarta cika taf da tarin kalaman da take shirin ɓare mata a yanzu wanda zasu sa ta fahimci wacece Kilishi tun daga tushe da kuma dukkanin abubuwan data aikata a rayuwarta.9

***

Wane shiri Ma’aruf ke yi akan ƴarsa Hameeda da kuma Ruƙayya?

Me ya yankewa zuciyarsa akan Amina da har Ishaq ya fahimta?3

Ku gaya min ina rayuwar gidan nan ke tafiya?

Munaya and Ishaq, me kuke tunani?2

Hajiya Kilishi…3

Ina gaya muku har yanzu sunan matar nan kawai kuke ji, next chapter zata buɗe muku abubuwa da yawa game da ita…2

Babi na gaba zai nuna muku me ake nufi da ainihin kissa da kisisina irin ta mata kamar Kilishi, wanda suka yarda cewa kowacce mace zata iya samun duniyar da take so a tafin hannunta… Ba boka ba malam!

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE