FARHA CHAPTER 2

FARHA 
CHAPTER 2

Dariya sosal takeyi har suka gifta qofar fadar sannan suka rabu kowacce ta nufl gdansu da sallarnarta ta shiga gdan tana qwalawa iyayenta Kira fadi take “Ummah Mamah albishirinku yaudai banyi tsokana ba nifa dama na fada muku yarannan Rahmah da Rahina su daina bina sune karfofl idan muka fita dasu sai sunsa na raba hali a amma kuma sheg…” hadiye maganrtayi muqut saboda ganin fitowar mutumin da suka rabu dazu dashi a qofar makarantarsu da Baffanta daga turakar Baffan tsugunawa tayi tana gaida Baffa ya amsa da cewa “ uwata sarkin rikici duniyama tsoronki take ya karatun ” sosa hancinta tayi tana harararsa tace”to qlau amma wlh dukan da yaya Anass yayimin jiya ya shigeni kuma bazan yafe…” sake hadiye mgnr tayi saboda kallon da taga Baffa yana watsa mata ta miqe tana dariya tace. 
“Kayy Baffa irin wannan harara haka muje na rakaka ka raka baqon naka amma Allah Baffa ya fiye shisshigi da shiga sharo ba shanu nidai garama mutum ya fita daga rayuwata idan ba hakaba nidai kowa yasan ni aljana ce ehee” ba Baffa ba hatta Mai martaba HAFEEZ saida ya dara duka Baffan yakai mata yace “kajimin ja’irar yarinya wato dole sai kin qarasa shirmenki k0 zaki bacemin daganan kosai na canza miki kamanni” daki ta shige tana turo baki binta yayi da ido harta shige dakin yanajin wata muguwar faduwar gaba yarinya 
qarama amma tana neman hana zuciyarsa kwanciyar hankali. 
Suna fita sukayi sallama daidai lkcn driven sa da excourt dinsa suka iso suka bude masa ya shiga suka tafi. Juyawa Baffa yayi ya shiga gdan ya fara dokawa matansa kira fitowa sukayi da sauri suka isa inda mijin nasu yake, kujera yaja yar tsuguno ya zauna yana sharce gumi yace “akwai matsala Hajara da Inno tabbas akwai matsala FARHANAH ta debo ruwan dafa kanta da babu mai hanashi dafata sai Allah Mai martaba sarki Hafeez yazomin da wani rikitaccen al’amari wai auran FARHA yake nema kuma a cikin sati daya tak” dagowa sukayi dukkansu sukace “Farha fah kace Baffan yara wannan shashashar yarinyar zaice yanason aure haba Baffa to kai kuma me kace masa?” qara share zufa yayi yace “to me kuke tunanin zance ma wannan taqadirin isasshen sarkin namu ya fahimce ni na fada masa Farha yarinya ce qarama kuma quruciyarta da gyara tanada rawar kai yace shi yaji yagani kuma yanaso shima rainonta zaiyi harta hada hankalinta duk da haka na kuma nuna masa rashin amincewata qarshe sai yacemin nayi haquri kawai auransa da Farha rubutaccen Al’amari ne 
saboda haka nayi fatan alkhairi kawai” 
Shiru gurin ya dauka cike da mamaki a fuskar kowanne Ummah ce tace “nidai gsky wannan Iamari ban amince dashi ba dama Rahmah yace ko Rahina sunfi wannan dukan taran hankali amma ace wai Farha ce mater sarki Hafeez gsky akwai matsala babba saboda ni nafi tunanin auran ma na manufa ne badon Allah za,ayishi ba” Mama ce ta cafe da cewa “ to yanzu maye mafita kunsan dai tunda ya tako qafa da qafa yazo gdannan bai dauki abin da wasa ba kuma babu abinda zai fasar da aurannan sabida haka inaga mafita ya kamata mu naima“ Baffa ne ya dago yace “to wacce mafita Inno ai kawai haquri zamuyi mu zubawa sarautar Allah ido tunda bamu isa mu kaucewa umarnin sarki ba kodan tsira da mutuncin mu ba abune me wahala a gurinsa ba ya tozarta mutum shiyasa tun mutuwar mahaifinsa Sarki Hambali na ajiye rawani na na shugaban malaman fada saboda shi amma duk da haka ban tsira daga kaidinsa ba saida mulkinsa da ikonsa ya ratso ta gdana bisa jagorancin
fitinanniyar yarinyar nan. na tabbata da bata taboshi ba bazai san da zamana ba ni 
bammasan tsautsayin daya hadasu ba nasan Farhanah ta zama gawa ta gama” 
Fitowarta daga dakin ce tasashi yin shiru ta kallesu tare da zama kusa da mahaifin nata ta dora kanta a cinyarsa a sanyaye tace “nifah banice na fara tsokanarsa ba shine suka batamin uniform dina da ruwan gulbi nikuma na fasa musu glass din motarsu kuma wlh bazan yafeba saina qara fasa mishi na wata motar tunda ya bata muku rai” shafa kanta yayi cikin tausayinta yace “da kina yafiya da kinfi haka Farha yanzu gashi inda rashin yafiyarki yakaiki Mai manaba zai kulleki yazo neman auranki a matsayin mata ta sunnah ba kuyanga ba ba baiwa ba kuma ya bada waadin kwana bakwai zaa daura auranki dashi a kaiki 
gidansa kinga sai kita ramawa da hujjah ko?” 
Yana fadin haka ya tashi ya fice ta bisa da kallo saida yakai qofar gidan ta kurma ihu tace ‘na rantse da Allah zaa mutu har liman idanba idan ya kuskura ya aureni ba yasin saina zubar masa da mutunci saina mayar dashi kamar bawa a gdan sarautar AlIah ya isana ma da yace yanasona zai kulleni mugu azzalumi macuci mema zaiyi dani yar qaramar yarinyata dani yasin wlh Allah sai nayi masa addu‘a ya makance ya kuturce ya zama gurgu kuma ma 
Insha Allahu sai anyi masa juyin mulki muga ta tsiya yehhhh mugu mugu sarki Hafeez…” 
Ganin tana neman tara musu jama‘a yasa Mama rufe mata baki tace “waike dan uwarki bakida hankali ne wannan ihun da kikeyi shine zaisa ya fasa abinda yayi niyyah k0 me sakarya kawai duk sa’anninki sun girma sunyi hankali amma bandake” turo baki tayi gaba tana qaqalo qwallah tace “toba kune kuke gulmata ba wlh idan kuka sake ma wannan wawan dan sarkin ya aureni Allah saina daina kwana a gdannan kuma na daina cin abincin gdannan sannan idan naga dama na gudu daga garinnnan zanyi kowa ma ya huta” miqewa 
Mama tayi saboda bata jure haukan yartata. 

‘WACECE FARHA‘ 

Farhanah Usman Giyyade shine asalin sunanta Mahaifinta malam Usman Giyyade asalinsa dan Usulin Bauchi ne cikin qaramar hukumar Giyyade fulani ne na asali masu kiwon shanu mahaifin mallam Usman yayansa uku Baffa Jafar Baffa Balaji da Baffa Shehu wato mahaifinsu Farhanah shine qarami a jadawalin halhuwar gdansu shiyasa daya tasa maimakon kiwo da suka taso sunayi shi sai aka dorashi akan karatun Muhammadiyyah yawon karatunsa ya kawoshi cikin birnin Bauchi dake anan arzikmsa yake lkcn ya auri 
Ummah wato Inno harda yaronsu daya Anas. 
Ya samu karbuwa gurin tsohon Sarki mahaifin sarki Hafeez wato sarki Hambali saboda 
dattako da kamalarsa yasa ya bashi matsayi mai girma na shugaban matasan malaman fada tafi tafi harya kasance shine shugaban malamai kuma shine limamin fada, yaransu biyu da Ummah lnno ya auro Fulanin Adamawa Hajjara wato Mama lkcn da aka kawota Bauchi ko Hausa bataji sai fullanci zamansu gwanin dadi da uwar gidanta komai tare sukeyi bazaka taba ganin daya babu daya ba Anass da Mussah sun tasa sannan Allah ya bawa Hajjara qaruwarda namiji Yusuf sai bayan shekaru biyu Ummah ta haifi Rahmah sannan Mama ta haifi Farhanah tun daganan Mama Hajjara bata qara alhuwa ba babu
dadewa Ummah ta haifi Rahina shikenan haihuwa ta tsaya cak a gdan. 
Kyau da wayon Farha da kuma shagwabarta shine yasa ta zama kamar itace qarama a gdan dayawan mutane suna dauka Rahina yayarta ce saboda kowa komai Farha saboda Allah yabata farin jinin mutane dayawan mutane suna kiranta da me kyau ko a makarantar bokonsu sai kace Pretty sannan zaa gane Farha kake nema, yanzu haka tanada shekara sha biyar kuma tana S S 2 a secondary school duk da bambadanci da fadan Farha sosai malamanta suke sonta saboda tana kwashewa a aji hakan yasa takejin kanta kirarinta 
kenan Duniya uwar rikici shikuma Baffan ta yace duniyarma tsoronki take. 

‘ASALIN LABARI’ 

Yau Iitinin ce tun asuba Farha ta tashi tayi wanka ta shirya domin zuwa makaranta 7:24am ta gama shirinta tsaf ta fito gaishe da iyayen nata tayi ta miqe zata fita Ummah tace “bakici abinci ba zaki tafi” yatsina fuska tayi tace “kin manta yau Iitinin azumi nakeyi” tana fadin 
haka ta juya ta fice a qofar gdan suka hadu da qawarta Binta suka rankaya suka tafi. 
A hanya take bawa Binta labarin abinda ya faru jiya dafe qirji Binta tayi tace “Allah ya taimakeki Farha kin tako sa,a wlh har Sarki Hafeez da kansa yace yanason auranki gsky nayi miki murna ke nimafa da zaayimin aurennan wlh so nakeyi” tsaki taja tace “qyale tsinanne wlh na tsaneshi baki ganshi ba jiyafa da naganshi ido da ido a gdanmu wani garnaqeqe dashi wlh qirar samudawan farko ne dashi wannan matarsa ta shiga uku aini wlh tsoronsa zankeji idan ya tsaya a gabana saifa ajera irina goma sannan zasu taba kansa” dariya Binta tayi ita kuma ta daure fuska tace “wato dariya ma nake baki k0?” dariyar dake cinta ta guntse tace “to ai kece da abin dariya Wai garnaqeqe koma dai ya yake kinsan babu fashi tunda ya furta saiya aiwatar ni bama wannan ba Farha karatunki fah keme burin zama Dr?” idanunta ne ya kawo ruwa cikin sanyin murya tace “ai guduwa zanyi a nemeni a rasa kamar yanda Samiran gdan Ali me dawaki tayi kinga ai kowa yama huta k0?” kallonta tayi da 
sauri daidai lkcn da suka shiga cikin makarantar tace 
“Tabdi kinaso kema ki batawa kanki dasu Baffa suna kenan a rinqa cewa dake karuwa yarinya idan ma kin gudu bazaki tsira ba wasune a banza zasu Ialata maki rayuwa garama ki tsaya ki auri Sarki koba komai zaake kiranki matar sarki kuma muma ma dangwali arzikin hange fada daga nesa ya kau tunda kina cikin gdan sarauta muma dole wata rana mu shiga kuma fah bakisan wani abuba shifa Sarki Hafeez ance duk sati a makkah yake sallar juma’a….” nuna Binta takeyi da hanu tana dariya har saida takai qasa tsayawa Binta tayi sororo tana kallonta ganin ta janye hanunta daga kanta tana nuna wani
guri yasata saurin kallon inda take nunawa, 
Qululuuuuu cikin Bunta ya bayar ganin tawagar fadawan da suke nufosu sauke Idonta tayi akan shugaban zugar sanye yake da jar alqabba da jan nadi komai na jikinsajane hatta kwagirin hanunsa, qasa tayi da idonta cike da mugun tsoron ganin ya tsaya kusa da qafafun Farhan da har yanzu bata daina dariya ba, jikin Binta har bari yakejira kawai take taga dogaran sun rufesu duka amma ga mamakinta sai taga ya rusuna ya sanya daya hanunsa ya dagota duk da idanunsa cikin baqin glass suke amma kowa dake gurin yasan ita yake kallo, sake kallonsa tayi harda yin dage saboda ta kalleshi sosai kuma fashewa tayi 
da dariya cikin dariyar qeta tace. 
“Ai ni bantaba addu’a Allah bai karba ba wlh jiya nayi addu’ar Allah yasa ka makance ka kuturce ka gurgun… Tsawa dogaran suka daka mata wadda tasata wata muguwar razana ta fada jlkinsa ta shige cikin alqabbarsa tana cukuikuiyeshi tana fadin “Allah ya isana ban yafeba da kukasa cikina ya qulle da muryoyinku masu kamada duro eh din an fada Sarkin naku ya gurgunce idan da wanda ya isa yazo da tabani a jikin wannan basamudai yaga yanda zai zama gari yanz ….. ” sake qanqameshi tayi ganin wani dogari ya zaburo yana ihu yana cewa. 
“Allah yaja kwanan sarkin duniya fushin Mai martaba ya tabbata akan mara kunyar yarinyar an…” shigewa ta kuwayi tsakanin qafafunsa ta tsuguna tana fadin “wayyoh! shikenan zasu 
kasheni da yar service wayyoh ni Wayyoh Baffana” baisan lkcn da murmushi ya kwace masa ba, daga masa hanu yayi da sauri ya dakatar dashi zubewa yayi a qasa yana buga kansa da 
kasa yana fadin “tuba nake adalin Sarki mai zamani haqiqa ni bawanka ne me tuba da 
neman yafiyarka Allah ya taimaki Mai martaba sarkin talakawa” 
Damqar hanunta yayi da qarfi har saida qashin hanun yayi qara ya fizgeta ya nufi staff room din principal din makarantar dogarawansa suna binsa yana shiga ya watsata ciki ya juya yayi tafiyarsa, hanunta take karkadawa tana hawaye tana murguda baki saida yayi nisa ta dago ta kalli inda yake tace “mugu kawai Allah ya isa mai qirar samudawa kawai yasin da nima basamudiya ce da rangwashi daya zanyi maka na huda kanka qwaqwalwar ka ta tarwatse ta watse” shidai principal din bai kulata ba harta gama kukanta da ihun hanunta zai cire ta tashi zata fita har taje bakin qofa ta juyo tace “kuma wlh saina hadaka da Sarki nace daya kawoni ko sannu bakace min ba kuma dole mutum yacemin  MATAR SARKI HAFEEZ ehee ko mutum yayi ta aikinsa” miqewa yayi ya zari bulala ta diba a Guje ta shiga Class dinsu ta shige qarqashin bancinsu. 


Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE