FUSKA BIYU COMPLETE
FUSKA BIYU COMPLETE
NA leko a hankali ina sanda bana son mama ta
ganni nasan sae tace na saka hijabi, in har kin
ganni da hijabi, to ki tabbata islamiya ko sallah,
don ko an matsa min nasa dana fita waje zan
aiko dashi. Anyi fadan , anyi dukan , an gaji an
barni sai addua inji mama. Na kusa kofar fita
inajin mama tana fadin “ke! Ke!! Ke!!! Asma’u ai
tuni na falla da gudu. Gidansu aminiyata Rahma
zan je, ina sonta gashi ta juri zama da halina na
masifa da tsokana, duk da ana cewa sai hali yazo
daya ake abota, amma ni da Rahma ba haka
bane, ita tana da gudun zuciya sam batason fada
haka nan ita ma’abociyar sanya hijabi ce, duk
kawar danayi sai mun bata, amma banda Rahma.
Na kalli gidan dake kallon namu, maza ne zaune
a barandar gidan kusan su hudu. Yaya Ali ne da
abokansa a raina nace sarakan sa ido , riga da
wando ne a jikina na jeans da farar shirt ko ince
top, ta dame ni sai dan karamin gyale irin shigar
da nakeso kenan a duniyata, kuma a ganina ban
wuce wannan shigar ba, tunda yarinya ce ni ‘yar
sha biyar.
zan sha kwana layin su kenan sai gata, nace
gidan ku fa zanje Rahma. kefa sai ina ? tayi
dariya , nima gidanku zanje . nace to mu koma
naku gidan wai ta ce a’a ni fa da shirin islamiya
na fito , lokaci nayi sai mu wuce. naja tsaki to zo
muje , amma Allah ban so komawa gida yanxun
ba , tace saboda me? nace kin san Allah Rahma
ban san me na ma yan gidanmu ba , duk sun
tsane ni. tace ba tsana ba ce Asma’u , don nasan
bai wuce ana miki fadan natsuwa ba. Na harare
ta bansan me nayi na rshin natsuwa ba, kina
nufin ban da natsuwa ko me? Ganin yanda na
hayyako mata yasa tace , “Allah ya baki hakuri
Asma’u , ba ina nufin ba ki da nutsuwa bane , kin
san…..”na katse ta “nidai yi min shiru malama zo
muje in zaki. “muka taho sungun-sungun babu
mai magana da wani, don ta mantar min da
fushina sai tace ina Suraj? nan ko na soma
murmushi , nace daxun shine ya dauko ni daga
makaranta. hirar suraj muke har gidanmu , ta nufi
gurin su mama ni kuma na nufi dakinmu, don na
daura zani akan wandona, nasani na nufi mama a
haka laifin zai zama biyu
sai dai kash! ina isa dakin na samu su yaya yina
masu cin ubana Anty Ainau da Anty fati da Anty
salima, zan juya Anty salima tace “ke zo nan ‘yar
iko zo gidan uban wa kikaje a haka? nace “ni ba
fa inda naje” na nufi sasansu mama ina yan
kunkunai ku kun cika takura gara naje gun mama
a haka bata da saurin hannu ku kam yanxun kun
duki mutum. na samu Rahma su nata gaisawa da
mama ta amshi rezar da mama ke yanke farce
tana yanke mata. na shiga na dan rabe mama
tace dago ta dube ni tace “yanxun Asma’u ba za
ki taba jin magana ba? kin fi son kina yawo haka
sai kace arniya? haka kika ga yan uwanki koko
haka ki kaga Rahma tana yi? ko Aisha da take
kanwar ki ta fiki hankali. na bata rai sannan na
ce “to ni me nayi mama? ni ba a sona a gidan
nan kowa sai yayi ta min fada” mama tace to sai
ki rama mara kunyar banza , ba’a son naki me
ake da mara ji? ki canja halinki mana ki gani in
ba’a daina miki fada ba, karamarki dake sai
shegiyar kafiyar tsiya , tace uban me aka miki
zaki tsira min kuka? bansan shigowar yaya
usman ba sai dai
sai dai rankwashi naji kus a kaina, yace shegiyar
yarinya daxun uban wa na ganki da shi a mota ya
dauko ki daga makaranta? ya kama kunne na
baza ki rabu da dan iskan suraj din nan bako sai
kin sha wahala? cikin kuka nace bafa ni bace ya
usman, ya kara kai min mari ina wasa dake ne?
ban sanki bane kenan? yasa kafa ya shure ni na
saka ihun da duk yan gidan suka taru amma abin
takaici babu wanda yace yaya usman yayi hakuri,
saidai suce ya kara min gara ma su umma da
hajiya sunce kece ai rashin jinki yayi yawa
Asma’u, ace ayi ta fama da mutum? yi hakuri
Usman, yace haba hajiya yarinyan nan ta fita
zakka a gidan nan in dai kaji an kawo kara nan
gidan to ita ce. dazun fa motor yaron nan suraj
na ganta ya dauko ta daga makaranta bayan
Alhaji ya hana ta kula shi. mama ta fito tana
fadin sai ma an hana ta, ta dubi yayunta mana
su aina’u wa taga tana kula samari cikinsu? ina
ce tun suna secondary duk wanda yazo gurinsu
cewa suke yi je gurin mahaifinsu. amma ita da
yake ta sa maza a ranta ‘yar kankannuwarta yau
ta tsaya da wannan gobe da wannan kai ranar
dai naci duka tamkar.
ranar dae haka naci duka kamar jaka sannan na
nufi dakinmu na kwanta a gadon mu ina kuka.
rahmace ta ke ta bani baki har aka kira sallah
nata tashi fuskata ta kumbura don kuka , nayi
alwala nayi sallah haka ma Rahma, ta nufi dakin
mama don shirin islamiya don can ta ‘aje
kayanta, nima na saka nawa duk gidanmu nice na
dinka wando a kayan islamiya(not clear but ana
fadin yanuwanta duk dogowar riga suke sawa na
islamiya ita ta dinka wando ranar dae duk wanda
xae mata fada xaece ta ringa koyo da halin
kawarta Rahma har ta ji haushin ta ) ta biyo ta
tana kira na ban tsaya ba sae tayo gudu ta same
ni , muna fita lungun layinmu ta baya muka bi
sannan muka kama hanyar islamiya, kamar daga
sama nafa motar suraj na tsaya itama rahma ta
tsaya yayi parking ya fito kyakkyyawan yaro dan
masu kudi mai takamotoci na kece raini, ya nufo
mu baby lafiya? na soma hawaye ya kama
hannuna. oh please stop crying my baby
Rahma ta dube ni cikin takaicin yanda na tsaya
ya rikr min hannu zomuje ka da muyi latti fa
asma’u . nace ki tafi sai nazo. tace yanxun nan
fa ya usman ya ce ki daina kula samar, na daka
mata tsawa ina ruwanki? ta wuce yaja hannuna
muka shifa mota ya share min hawaye da
yatsanshi, fadamin me aka miki? nace wai ya
usman ne yace na daina kula ka hrda dukana,
yace to baby ke yanxun yaya kika gani zaki iya
rabuwa dani ko ko yaya? ni dai gaskiya baby ba
xan iya rabuwa dake ba, nace ai nima suraj ba
zan barka ba bayan duk garin nanm kai ne kadai
me sona, su fa ba wani sona suke yiba, yace to
mujr in kaki makarantar, yace bari mu dauki
rahma, nace barta kawai itama yau haushinta
nakeji. ina shiga ajinmu duk sauran yan ajin suka
gyara xamansu dan bani guri. nice na zabi gurin
kuma nace nan ne gurina duk da kasancewa
kowa yana zam a ko ina, amma ana shakkar
zama wurina , saboda masifata duk da karfi ne
dani ba suna tsorona kasancewarbamu taba
danbe ba shiyasa suke min kallon karfi.
na zauna ina tunanin yanda ba’a sona har zuwa
san da rahma tazo. malam ya shigo yana rubutu.
ba yabon kai ba, saidai ai min shaidar rashin ji,
amma in dai karatu ne daga boko har islamiya
nayi zakara. yanda malamai suka sanni da rigima
haka suka sanni da kokarin karatu, wannan shi ne
yas nake da farin jini cikin dalibai , suke kuma
shakkata. hour kofar gidanmu motar ta tsaya, na
fito tare da godiya tacemin zai zo anjima nace to
sai dai yatsaya daga farkon layin a wurin wani
gidan dake duban gidanmu ya Ali ne shi da wani
wanda ban tantance shi ba , sai dai ina ganin kila
shima dan gidan ne, yana ta min kallo mai kama
da harara na wuce ina ce ma wanda ya rago min
hanya sa anjima . yaya umar ya dubi kaninshi
Aliyu yace, Ali wannan yarinyar yau ganina da ita
na uku kenan, tana shiga gidan baba Alhaji itama
‘yars ce? aliyu yace Asma’u? ‘yarsa ce mana
itace mara jin gidan, yace na kula daga zuwana
shekaran jiya zuwa yau na lura bata da kamun
kai, su Abubakar suka barta ta baci haka? Aliyu
yace ai ya uwar yarinyar nan ‘yar daru ce da
taurin kan tsya.
[1:28PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1—–2
suna iya bakin kokarinsu. ya umar yace ‘yar
wacece a cikin matan gidan? Aliyu yace, ‘yar
mama ce ka ko san albasa batayi halin ruwa ba.
ya umar yace ‘yar mama? Ali yace kana mamaki
ko? wallahi ‘yarta ce daga ita sai aisha auta, ya
umar yace lallai kam albasa bata yo halin ruwa
ba, mama da dukkan yayanta salihai ne kai kaf
gidan ma babu mai wata matsala shiyasa naje
mamaki kaya matsattsu jibi atamfar dake jikinta
yanxun tamkar tayi nishi su yage haka suke a
jikinta. Aliyu yace kaga kadan ma ba dan tana
shan wahala ba ma kila da tsirara xata dinga
yawo kuma ga smari kamar hauka yau
wancangobe wancan, ‘yar karamar yarinya
jamilar gidan nan fa ta girme ta . ya uwar yace
kai haba? Ali yace wallahi bata wuce 14 ba, ya
umar ya mike ya nufi cikin gida yana fadin shi fa
ganinshi an barta ne
ina zaune bakin gado inayin note shema’u ta
shigo “Asma’u ki zo in ji alhaji ” na dube tacikin
faduwar gaba don nasan kiran babanmu dani
babu alkhairi , kila ma an kai mishi karata , na ce
to me nayi? tace oho in ce kina zuwa ko ko in ce
baza ki zo ba? na harare ta sannan na mike. shi
kadai acikin madaidaicin falon nashi yana zaune
yana lissafin wasu kudade gefe yaya Abubakar ne
da yaya usman, suma suna ta rubutu nasan
harkar kasuwancin su ne. na zauna gefe nace
gani Alhaji, a tare ya abubakar da ya usman suka
jeho min harara sannan suka cigaba da aikn su.
Alhajiya ajiye kudin hannunshi gefe yace Asma’u
wato kina da kunnan kashi ko? a raina nace
tome kuma nayi? yace tambayar ki nake yi?nace
a’a yace me yasa ba kya jin duk abin dana gaya
miki da wanda ‘yan uwanki suke gaya miki? na
sun kuyar da kai ya cigaba “na raba ki da yaron
nan suraj amma kin ki ji ko? ke ba mashi ba ko
wani saurayi na hana kin ki yarda duk yaushe
kika tafasa har da zaki kone? wato baza ki dubi
yayyanki ba babu wacce take tsayuwa da wani
saurayi fa sai da izini na. ma’ana sai an gana
dashi sannan na yarje musu kin ga suna tara
maza saike?
to kiran da na miki yanxun na yanke hukuncin
tunda ke ba zaki yi abin da nakeso ba to kema
bazan miki wanda kikeso ba . tunda nine na haife
ki ba kece ki ka haife ni ba, kuma ni da mahaifiyar
ki baza ki sa mana hawan jini ba, don haka na
daina biya miki kudin makaranta , na daina miki
sutura , ke na daina miki komai ki dai ci abinci
sadaka sannan shi wanda na rabaki da shi ki ka
ki,sai ki ce masa ya fito, sadaki kawai zai bada a
daura muku aure, ki debi yan kayanki ki bishi
allura bazan sai miki ba. tashi ki bani guri na
soma kuka domin duk iya shegena ina tsananin
son makaranta kuma ina karatu sannan nasan ina
son suraj amma munyi da shi aure sai na shiga
jami’a lokacin shi kuma ya soma aiki tunda
yanxun yana A.B. U zaria. (garin su xee lolz)
nace don Allah Alhaji ka tamake ni mana? ina son
karatu na , yace sanin kina son ya sani kuma zan
katse miki shi ba? yaya zan so abin dakike so?
alhalin ke da na haifa kina kin wanda ni nake
so ? zan kuma magana yaya Abubakar ya daka
min tsawa tashi shegiya.
dakin mama na zame ina cewa cikin ihu , ki
taimaka min
mamana don Allah zan mutu tace menene? na ce
alhaji ya cire ni
daga makaranta wai zai min aure bayan gasu
anty Aina’u nan su da
suke poly ai sune ma zasu musu aure ba ni ba,
na tsaya ina ta rusa
kuka, ta ce hakan ne ya dace da ke tunda ba kya
jin magana Asma’u
duk kin bi kin maida kanki ‘yar iska kin zubar
mana da mutunci a
gari? da gudu na nufi dakin umma suna zaune da
anty fatima na
fada kan umma na ce umma ki min rai mana
Alhaji yace ya cire ni
daga makaranta ku roke shi na tuba ba zan kuma
yin komai ba, tace
so naea zaki ce kin tuba amma ai tuban muzuru?
tunda kin ja yayi
fushi dake ba shi kenan ba. jin ba sa’a na nufi
hajiya gara ita tadan
lallashe ni tare da bani baki kuma tace mu bari
ya huce sannan naje
na roke shi tare da daukar alkawarin daina
halayena, kai ranar naga
tsawon dareban fasa ba haka nan ban karya ba
bare na nemi kudin
mota, hasalima a sace na fito tun daga sabon
kawo har F.G.C malali
a kafa san da na isa har an tashi break sai dana
yi hawaye don
takaicin missing din darasi har. 3 yanda muke
shirin fara. test
dinnan.
haka da muka tashi bayan da Rahma ba tayi ba
akan na zo muyi
goyo a mashine amma naki, haka nan ta hakura
ta tafi su shema’u
da hadiza da Aisha suka hau mashin a gabana
hakan ya kara sani
yanke hukunci bani da mai kaunata duk gidanmu.
na iso badarawa
na gaji sosa na samu guri na zauna hutawa nake
yi can kamar daga
sama sai ga suraj cikin mota , ya fito yazo har
gabana ina kallon shi
ban ko matsa ba , yace nasha yawon nemanki
baby tun daxun naga
Rahma ta sanar dani kina tahowa a kafa kuma a
kafa kika je
makaranta . nace meyasa tace baki fada mata
ba, na dube shi duk
kan ka ne suraj, baba yace saidai ka fito muyi
aure na gama
makaranta ba zai kara biya mun ba, yayi shiru
bayan ya tsugunna
kusa dani, yace to yanxun yaya zamuyi? nace
shine ban sani ba, yace
yanzun dai taso muje na ce, a’a yaya zan shiga
motar ka? a kuma
ganina? yace sai na sauke ki bayan layinku , na
mike na shiga a
hankali muke tafiya, tare da neman mafita a
karshe muka yanke
shawarar zamu na haduwa a bayan layinmu kuma
ba zai dinga zuwa
da mota ba kuma yace ko ma nake so na
tambaye shi zai
na tambaye shi zai min yace ma zai saya min
waya sai na boye ta mu dinga magana, son da na
shiga gida ana sallar la’asar ban kula kowa b ni a
dole ba’a sona na daina kula kowa haka na yanke
shawara nayo alwala nayi sallah nasa kayan
islamiya Aisha ta shigo. Asma’u kizo inji mama,
na nufi dakin na shiga a raina nace nasan dai laifi
nayi tunda dama nice uwar ‘yan laifi mama ta
dube ni ga abinci nan a kicin tun da yake ke kn fi
karfin ki manamagana ‘yar gaisuwar da kike
mana a raine yau bamu samu ba, idona ya ciko
da hawaye na ce na koshi , tace to ai shi kenan
kila mai hure miki kunnan ya baki wanda yafi
namu an hana ki zuwa makaranta amma don ki
nuna ma duniya cewa bamu isa. ba kin tafi, na
soma sharar da hawaye cikin shessheka na ce
mama na ga ne term bai kare ba kar ayi asarar
kudin mama tace ina ruwanki , me biyan yace ki
daina zuwa ko sai yaje har makarantar yasa an
goge sunanki zaki daina zuwa? ba tare da na
sake wata magana ba, na mike na nufi dakinmu ,
na cire hijabin na kwanta kan gado ina mai
tausayin kaina tare da tunanin anya kuwa
gidannan ba tsinto ni suka yi ba?