Gangar jikinsa na aura 27

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter27

Bayan ta gama kwalliyar ne ta tashi daga gaban mudubin, ta tsaya cak a tsakiyar dakin tana shawarar yadda zata yi. Shin ta hau gado ta lulluba ne? Ko ta datse kofa da mukulli tayi kwanciyarta
ne, ko kuma ta koma ban daki ta rufe kanta ne? A gaskiya Yaya Haisam ba zaiji dadi ba, ita kuwa bata son ta bata masa rai ko kadan a rayuwarta saboda Haisam bai taba bari wani ya bata mata rai ba balle shi da kansa burinsa kullum ya faranta mata ya ganta cikin farin ciki. Ji tayi burum ya bude kofa ya shigo, ta tsorata taja da baya. Haisam ya kura mata ido yana yi mata murmushi ya tura kofar dakin ya rufe da mukulli ya nufo inda Hannah ke tsaye a hankali. Yasa hannhu biyu ya jawota kan kirjinsa ya rungumeta tsam yayin da dukkansu zuciyoyinsu suka hau bugawa a lokaci guda kowannensu yana
jin yadda ta danuwansa ke bugawa don tsananin farin cikin da suka tsinci kansu a wannan lokaci.
Kowannensu kwakwalwarsa na kokarin ta tantance masa shin da gaske ne ko kuwa mafarki suke yi. Hannah ta dago da kanta a hankali ta kalli Haisam don ta tabbatar shi din ne kuwa, dai-dai lokacin shima ya dago yana kallonta don shima ya tantance tunanin da yake irin na Hannah ne. Cikin sanyayyar murya Haisam ya ce “Hannah kece kuwa
ko mafarkinki nake yi kamar yadda na saba yi kullum? Da kyar ta iya magana ta gyada kai ta kashe ido ta ce “Abun da nake so in tabbatar kenan don nima ina kokonto a zuciyata. Kafin ta rufe bakinta sai taji bakinsa cikin bakinta. Nan da
nan ta sulale ta tsuguna a kasa tasa hannu ta rufe fuskar ta. Haisam ya tsuguna a gabanta yasa hannu ya dago da fuskarta yayi mata kallon ido cikin ido ya ce “Kada ki manta ada GANGAR JIKINKI bata tare da ni RUHINKI ne yake tare da ni, amma a yanzu GANGAR JIKINKI DA RUHINKI suna tare dani don haka karki ji nauyina ni mijinki ne. Ya mike tsaye ya jawo hannunta ya tasheta tsaye suka zubawa juna ido. Ta kashe ido cikin zazzakar murya ta ce “Kaine farin cikina, abun yardata, abun
alfaharina abun da nafi so a rayuwata na mallaka maka zuciyata tuntuni a yanzu kuma na mallaka maka GANGAR JIKINAAAA. Ta dora kanta akan kirjinsa ta lumshe ido yayin da shi kuma yasa hannunsa daya ya rungumeta yasa daya hannun yana shafar lallausan gashin kanta. Hakika ma’auratan nan yau sun fi kowa farin ciki a rayuwarsu jinsu suke tamkar ba’a cikin duniya suke ba domin a wannan duniyar tamu akwai bacin rai su kuwa basa ji, ana ciwo su kuwa sumul suke ji sai tsantsar farinciki da yake nukurkusarsu. A tsakiyar gado Hannah ta jita yayin da Haisam ya shiga sumbatarta, yana sinsinar kamshin da takeyi, yana lasar duk ilahirin sassan jikinta. Sai a yau Hannah tasan tayi aure kuma ta sami tsantsar soyayyah har dama yadda ake yinta, ashe Bello Madu shafar mai yake yi mata bai san yaya ake yin soyayya ba. Kuma shima Haisam sai yau yasan yayi aure don da zuciyarsa a dagule take hankalinsa a tashe yake idan yana tare da Ramlah!!!
 shi kansa bai san sanda yake yiwa Hannah wasu abubuwan ba sun raya daren yau sunna.
Yau ango da amaryarsa idanuwansu basu ga barci ba. A kunnensu aka kira assalatu. Dakyar da sudin goshi Hannah ta samu ta zare jikinta daga jikin Haisam don ya cukukuiyeta ya rungume ta kam kamar zai fasa kirjinsa ya zurata a ciki. Hannah ta mike da kyar saboda duk gabobinta sun jigata, ta
shiga ban daki tana shiga ta sakarwa kanta shayar ruwan zafi ta dai-daita ta surka da ruwan sanyi daidai wanka. Bayan ta gama wanka sai ta daura alwala ta fito sai Haisam ma ya shiga. Bayan ya fito ne sai ya saka wata doguwar riga Hannah kuma ta saka bakar doguwar riga mai dan kwali suka yi
jam’i suka yi salla. Ba su bar kan sallaya ba sai da gari yayi haske kamar karfe bakwai na safe suna lazimi da hailala da hamdala ga Ubangijinsu Sarkin Sarakuna daYa basu dama da ikon yin aure. Saboda suna tsananin kaunar junansu. Hannah ta mike tabar Haisam a zaune yana jan carbi ta fita ta sauka kasa ta shiga kicin. Butar ruwan zafi ta jona ta cika flask saita fasa kwai da yawa ta soya waina masu kaurin gaske ta zuba a faranti ta debo ta hau sama..
A kwance akan gado taga Haisam har ya fara dan bacci, bude kofar da tayi ne ta tashe shi. Ya daga ido ya dubeta sai yayi murmushi ya ce
“Daman kicin kika shiga da sassafen nan. Hannah tayi dariya tazo ta ajiye katan faranti me dauke da plate din wainar kwai da flask din ruwan zafi. Ta sake fita ta dauko wani faranti mai dauke da kofuna biyu da cokula kanana da madara, suga da millo ta zo ta ajiye a kusa da farantin farko, ta karaso wajen gado inda Haisam yake kwance ta durkusa har kasa cikin sassanyar murya ta gaishe shi, ya makale murya yana kwaikwayon maganarta ya amsa. Su duka suka tuntsire da dariya. Haisam ya tashi zaune ya zuro kafafuwansa kasa daga kan gado ya jawo Hannah a jikinsa ya ce “Hannah ai yanzu nafi karfin gaisuwar ina kwana Yaya a wajenki. Kinsan irin gaisuwar da zaki dinga yimin?
Hannah ta girgiza kai ta ce “Ban sani ba. Ya ce “Duk sanda zaki gaishe ni idan ni dakene sai kizo ki tsotsi bakina ki rada mun a kunne gaisuwar, idan kuma da mutane a wajen sai ki mika min hannu mu gaisa.
Irin wannan gaisuwar zaki dinga yiwa Yayarki Ramlah ki mika mata hannu kuyi musabaha sannan ku gaisa. Hannah ta ce “Zanyi yadda ka ce insha Allah. Yayi murmushi ya ce “Na gode my love, af na manta ban tambaye ki ba yaya jiya? Hannah ta rufe fuska da tafikan hannunta ta ce “Shi yasa naga ya dace kasha ruwan tea da sassafen nan saboda na ga ka gaji. Haisam ya harareta ya ce “Au nine ma na gaji banda ke? To gobe ko ruwan tea din ma baza ki iya tashi ki dora ba ni da ke zanga wanda zai iya motsi da safe, ai tausayinki naji yau. Hannah tayi dariya ta ce “Yi hakuri dan Allah ni ba haka nake nufi ba.
Bayan sun gama karin kumallo ne suka koma kan gado suka kwanta. Hannah na kwance akan kirjin Haisam tana shafawa a hankali yayin da shi kuma yake shafar gashinta da gefen fuskarta ya zuwa
wuyanta suna hira mai dadi har barci mai dadi ya sure su, kowannensu ya dora da mafarkin dan uwansa. Basu tashi farkawa ba sai karfe biyu saura kwata ana sallar Azahar. Bayan sunyi wanka sun caba ado sunyi sallah sai Haisam ya kama hannun amaryarsa suka nufi bangaren Ramlah wacce tuntuni tasa an shirya musu abinci kala-kala da yake tasan anan zasu dinga cin abincin rana dana dare saboda Haisam ya dakatar da Kukun Hannah sai nan da sati biyu sannan zasu zo suci gaba da yin abinci kada suzo su dame su, su rage musu wani bangare najin dadi.
Ramlah na ganinsu ta taso da fara’a da murna ta rungume Hannah sannan ta rungume Haisam ta sumbaci kumatunsa ta ce “Kun tashi lafiya? Suka amsa mata da “Lafiya kalau. Ta kaisu wajen katafaren teburin cin abinci mai dauke da nau’ikan girke-girke kala-kala. Suna cin abinci suna hira suna tuntsira dariya kai kace gidan biki ne. Haisam ya iya surutu da hira haka Ramlah ma tana da magana Hannah ce dai sai tayi da gaske tunda ita ba gwanar surutu bace. Tana jinsu suna ta surutu sai dai tayi dariya idan na dariyane idan kuma Haisam yayi mata tsiya Ramlah ta shigar mata tana tare mata don ita bata iya surutu ba sosai kuma ko ba haka ba tana ganin Haisam da Ramlah da wata kima da girma a wajenta don haka take jin nauyin tayi ta shiga hirarsu da zolaye-zolayen da suke yi,
da suka gama cin abincin sai suka koma kan kujerun falo suna kallo. Haisam da Ramlah akan doguwar kujera suke a zaune, Hannah kuma na wata kujera a gefensu. Suna kallon kaset din bikin Hannah da Haisam na shagalin da aka yi a Tahir Guest wanda dan asharalle, boda da police band suka cashe. Ango da amarya aka dallaro a tsakiyar fili yayin da suka kurawa junansu ido Hannah na hawaye a kaset din. Ramlah tayi ajiyar zuciya ta ce “Soyayya. Haisam ya dan harareta ya ce “Meye wani soyyaya. Ramlah ta tuntsire da dariya ta ce “Meye to abin hararar don nace soyayya? Kawai cewa nayi soyayya masoya na gani. Haisam yayi murmushi ya ce “Nasan da magana a bakinki haba Ramlah kece fa, nasan halinki sarai. Tayi dariya ta ce “Da dai zance wani abu amma na fasa tunda har kasa a ranka zance wani abu. Haisam ya jawo hannunta
ya murde ya ce “Saikin fada zan sake ki. Hannah tayi murmushi ta ce “Yaya Haisam karka karya mun Aunty na fa. Ramlah tayi dan kara ta ce “Yallabai yi hakuri sake ni zan fada maka. Haisam ya sakar mata hannu ya ce “To fadi ina saurarenki. Ramlah ta gyara zama ta dube shi tayi murmushi ta ce “Kafin in fadi abinda zan fada don Allah zanyi muku *yan tambayoyi zaku amsa mun? Haisam ya ce “Zamu amsa miki yaya zamu yi tunda Allah Ya hadamu da *yar jarida. Ta juya ta kalli Hannah ta ce “Kefa kanwata idan na tambayeki zaki bani amsa tsakani da Allah, akwai abunda
nake so inji ne sai in hada in fadi abun da yake raina. Hannah tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa ta ce “Mai zai hana in baki amsa Auntyna zan amsa duk abinda na sani, insha Allah. Ramlah ta jawo lokar jikin centre table ta dauko wani dan littafi da biro ta ce “Yallabai ta kanka zan fara tambayoyin. Ya gyara zama ya ce “Ina jinki, sharadi daya idan kika yi min karkatacciyar tambaya saina kara murde miki hannu. Ramlah tayi dariya ta ce “Na yarda, tambaya ta farko ita ce zaka iya gaya mun yaushe ka fara son Hannah a zuciyarka.
Hannah ta juyo ta kurawa Haisam ido tana son taji amsar da zai bata

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE