Gangar jikinsa na aura1

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA

AURA  chapter1

Chapter 1

Wata kwarababbiyar mota
kirar bus mai karar
fatattakekkiyar salansa ce ta tsaya a bakin get din
makarantar yan mata ta
gwamnatin tarayya dake
garin Kazaure, wato
F.G.G.C. Kazaure. Tana
tsayawa kondastan motar ya ja kofar ya bude
“Barararaa” saboda
kwankwatsewar da kofar
motar ta yi sakamakon cin
ruwa da gafje-gafje da
tsabar tsufa.
Wani dattijo mai kimanin
shekaru saba’in da doriya
ne ya fito, da wata yar
yarinya tana biye dashi
wacce shekarunta ba zasu
wuce shekaru goma sha daya ba, Bayan sun furfito
kondastan motar ya
zagaya baya wato but ya
dauko wata katuwar
akwatin karfe irin ta *yan
makarantar wacce aka dafka sunan mai akwatin
garza-garza da fenti baki wato
HANNE HABU IMAMU. Ya
ajiye gefe ya sake janyo
wata karamar katifa
wacce take daure ya dora akan akwatin, sannan ya
dauko wani bokitin karfe
sabo dal yana sheki shima
an fenteshi da sunan mai
bokitin wato
HANNE HABU IMAMU. Daga karshe ya mayar da kofar but din ya
rufe ya juyo ya kalli
dattijon wato Malam Habu
ya ce “Baba baka fa cika
mana kudin motarmu bafa,
gashi har kun sauka” Malam Habu ya sake
marairaicewa ya ce “Dana
da Allah fa nake hadaka
kuyi hakuri kudin da yayi
saura a aljihuna ko gida
bazai mayar dani ba, sai na nemi ciko kayi hakuri dan
Allah, dan haka nema nace
ta zauna a maleji yanzu
baza ka tausayawa tsoho
ba, karbi arba’in din?”
Kondasta ya sake fusata ya ce “Dalla Baba kana
bata mana lokaci ga
fasinjoji har sun fara tsaki
sun kagu suma a kaisu
inda zasu. Ka zauna kana
mana magiya tun dazu muma fa ba’a bati muke
shan man motar da muke
jigilar nan bafa, da kasan
kudin motar taka bai cika
ba me yasa ka hau? Har
zaka ce wai yarinyar a maleji ta zauna, maleji ba
cikin mota bane? Baka san
har a sittin muke daukar
na maleji ba, daga inda
muka dauko ku zuwa nan
nayi maka ragi nace ka kawo hamsin dinma gashi
kaki biya sai wata arba’in
ka bani, kai wallahi Baba
saika ciko mana gomarmu
kaji ko?
Direban motar dake zaune a wajen tuki wanda yake
jin duk abinda suke yi, sai
yanzu ya waigo inda suke
yayi magana ya ce “K.b
wai yane? K.b ya ce “Har
yanzu wannan tsohon bai daina magiya ba wai shi ayi
masa ragin goma kudin
yarinyar nan data zauna a
maleji, Hansin nace ya
biya, ya wani bani arba’in.
Kuma ma dan rainin hankali harda cewa kudin
aljihunsa bazai mayar
dashi gida ba, wato yana
da kudin, cikawa ne bazai
yi ba. Malam Habu ya danji
dadi ganin direban yayi magana ko zaice a bar
masa amma sai yaji
kalamansa sabanin
tunaninsa gara ma abinda
kondastan ya fada masa,
cewa yayi in har bazai biya ta dadin rai ba to zasu
farka aljihunsa su dauki
gomarsu, Malam Habu ya
rike baki don mamakin irin
wannan rashin mutunci,
can ya nisa ya ce “Allah Ya kyauta, bari na baku
kudinku abin duk bai kai
ga haka ba, yasa hannu a
aljihunsa na dama ya
dauko wata
cukurkudaddiyar naira biyar ya sake saka hannu
a aljihunsa na bangaren
hagu ya dauko gudar
naira ashirin da kwandaloli
guda biyar, ya hada
kwandalolin nan guda biyar da cukurkudaddiyar naira biyar din nan ya mikawa kondosta ya ce
“Gashi dana Allah Ya
kiyaye. Ba kunya ba
tausayin tsohon nan yasa
hannu ya karbe yana
gurnani “Daman kana dashi ka tsaya kana bata mana
lokaci duk fasinjoji sun
kagu, direba ya juyo ya ce
“Yayane K.b ya baka, sun
cika? K.b ya ce “Eh sun cika
jamuje J.J.C. Malam Habu da yarsa Hanne suka bi
motar da kallo har ta hau
titi ta kure sannan
hankalinsu ya dawo kan
kayansu.
Malam Habu ya kalli yarsa Hanne wacce hawaye ya
gauraye idanuwanta da
kumatunta, abin ya bashi
mamaki ganin Hanne na
kuka alhali kuma ita take
son karatu take murna da zasu taho, ya sake juyowa
sosai ya kalleta yaga
hawaye neke zubowa
daga idanuwanta daya
nabin daya, ya ce “Yar
Baba, kukan me kike yi?
 Karki cemin yanzu bakya
son makaranta bayan ke
aka kira fadar mai gari aka
tambayeki kika ce kina so.
Ba’a son raina ba nima na
kawo ki makarantar nan ke kika amsa musu. Shine
kuma yanzu kike kuka?
Idan kinsan bakya so to ni
a wajena tafi nono fari sai
mu juya kafin mu shiga
ciki. Kansila da mai gari su suka tilastamin in kawo ki
amma badan haka ba nima
bazan rabu dake ba na
kawo ki nan uwa duniya,
babu wanda kika sani.
Hanne ta girgiza kai cikin shesshekar kuka ta ce
“Baba ba makarantar bace
bana so, rashin kunyar da
masu motar can suke yi
maka shine ya sani kuka.
Malam Habu yaji hawaye ya cika masa ido amma sai
ya jure yayi murmushin
karfin hali ya ce “Allah
Sarki yar Baba, babu
komai duniya ce. Duk
wanda yaga girman tsohon wani, za’a ga
girman nasa. Haka kuma
duk wanda ya raina
tsohon wani sai an raina
nasa, zamani ne ya canja
babu sanin girman Allah, ko an hada mutum da
Allah kamar an hadashi da
sa’ansa, wani cewa zaiyi
daina hadani da Allah
karka cuceni
Wa’iyazubillah. Ya ci gaba da cewa “goge hawayenki
yar Baba kizo in dora
miki akwatin mu shiga ciki
kada dare yayi min kinga
har la’asar tayi. Tasa gefen
gyalen da taci damara dashi ta goge idanuwanta
kana ta matso ya ciccibi
akwatin karfen nan ya
dora mata a kai shi kuma
ya dauki bokiti da katifa a
daya hannun sa’annan suka juya suka doshi cikin
babbar kofar shiga
makarantar, yaci gaba da
yi mata nasihohi masu
ratsa jiki yana nuna mata
wannan abin da aka yi masa a gabanta ya zama
darasi a wajenta duk
lalacewar tsoho koma ba
tsoho bane na gaba da ita
kada tayi masa fitsara. Ta
zamana ko a ina take kuma kome ta zama ta
girmama na gaba da ita. Ta
zama mai taimakawa
mabukata, kasancewar
tasan talauci ta kuma
dandanashi tana kan dandanashi.
Masu gadi uku suka iske a
bakin kofar shiga cikin
makarantar, suna
zazzaune, Malam Habu yayi
musu sallama gami da mimmika musu hannu,
Hanne ma ta duka ta
gaishesu, bayan sun amsa,
Malam Habu ya ce “Yarinya
na kawo makarantar nan,
ta ina zanbi mu shiga ciki? Daya daga cikinsu ya ce
“Mikewa zakuyi sosai zaku
tarar da ofishin Malamai
dana shugaban
makarantar. Malam Habu
yayi godiya suka wuce, har sun danyo nisa suka ji
masu gadin nan sun kwalla
musu kira bayan sun
dawo, sai daya daga
cikinsu ya kallesu sama da
kasa ya ce “Dan Allah Malam muna da tambaya
sai bayan da ku ka wuce
tambayar ta fado mana.
Malam Habu ya gyara
kayan dake hannunsa
gami da yin murmushi ya ce “To Allah Yasa na sani.
Ya ce “Wai shin me kake
tambaya ne? Yar
makaranta ka kawo daliba
ko kuma mai aiki ka kawo
gidan Malamai a nuna maka gidan Malamai
(staff quaters)? Malam Habu ya
ce “A’a daliba na kawo
yar makaranta ce. Su
duka suka kyalkyale da
dariya suna tafawa wani harda buga kafa a kasa.
Abun ya daurewa Hanne
da Mahaifinta kai. Menene
abun dariya? Ko nan ba ita
bace makarantar yan
mata ta gwamnatin tarayya dake Kazauren ba?
Malam Habu ya tambaya
suka ce “Nan ce
makarantar daka ambata
amma watakila kayi batan
kai ko baka ji dai-daiba. Malam Habu ya ce “Batan
kai kamar yaya? Daya ya
ce “Nan makaranta ce ta
*ya*yan masu hannu da
shuni, *yan birni masu
kokari, ba haka kawai dan ance yarka taci
makaranta ba kaje ka
suyo akwati da katifa
kazo ka zabi makarantar
da ranka yake so ka shiga
kace ga dalibaba.
Daya ya ce “Ko dai waccan
makarantar ce ta
gwamnatin jiha suka rasa
suka shigo nan. Koda yake
ko can dinma dakyar su
kwashi wannan. Sannan na karshe ya ce “Ku dai ku
tsaya babu mamaki nan
din taci abun ai na Allah ne,
Malam ina takardar shaidar
taci nan makarantar?
Malam Habu ya ce “Mu babu wata takardar
shaidar cin makaranta a
tare damu, ni dai kansilan
garinmu yazo har gida ya
ce jarabawar da yata tayi
a birni ta fito kuma duk karkararmu ita kadai taci
mai garinmu ma ya turo
inje ya shaida min ya ce
lallai-lallai nan taci in
kawota, ya ce min
makarantun yan mata a Kazaure guda biyu ne data
gwamnatin tarayya data
gwamnatin jiha, ta
gwamnatin tarayya taci in
kawota. Amma ni babu
wanda yayi min zancen takarda. Suka sake
kecewa da dariya. Daya ya
ce “Malam sai kuyi waje
don baza ku shiga ba babu
takardar shaida, ku koma
ku sami kansila ko maigarin naku su baku
takardar shaida sai kuzo
ku nuna sannan mu barku
ku wuce. Yau gashi kusan
kusan wata daya ke nan
da aka riga aka gama kawo yara har sunyi nisa
da fara karatu, kai sai
yanzu kake kawo yarka.
Malam Habu ya ja yarsa a
sanyaye suka yi waje,
zuciyarsu cike da mummunar damuwa.
Hakika Nigeria muna cikin
wani hali. Inji Malam Habu a
lokacin da yake ajiye
kayan dake hannunsa a
waje, ya kamawa yarsa akwatin dake kanta suka
sauke kasa. Suka tsaya
suka yi cirko-cirko suna
kallon masu gadin nan,
wadanda har yanzu basu
daina yabo musu bakaken maganganu ba. Malam
Habu ya nisa ya ce “Allah
Sarki rayuwa, Allah Ka
fimu sanin halin da muke
ciki kai zaka fitar damu,
yar Baba zauna a gefen akwatinki kinji kafin
muga yadda Allah zai yi
damu. Isa kansila da
maigari suka ja mana
wannan wulakancin. Ni
nasan a rina, shi yasa da farko naki fur da akace
za’a kaiki birni daukar
jarabawa, kuma kema da
akayi kiranki me yasa kika
amsa musu? Kika ce kina
son karatun, ga irinta nan ai.
Hanne ta zauna a hankali
jikinta yayi sanyi, wanda
ko yatsanta wuyar
dagawa yake yi mata.
Zuciyarta cike da damuwa, babu abin da take tunawa
illa komawarta gida
haduwarta da iya Abu
kishiyar uwarta da

yaranta….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE