Gangar jikinsa na aura12

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter 12

Hannah ta zama tamkar wata tauraruwa mai haske cikin taurari a makarantarsu. Akwai kungiyoyi (clubs) a makarantar da yawa, tun Hannah tana aji daya ta shiga kungiyoyi daban-daban. Kuma duk wasannin kwaikwayon da za a yi a kowacce kungiya sai an saka Hannah ko tana so ko bata so saboda kyawunta. Tun ana sata a matsayin yarinya har aka zo ake saka ta a matsayin budurwa. Don haka Hannah ta kware sosai wajen iya wasan kwaikwayo suna fita suje makarantu daban-daban a fadin kasarnan, kamar su F.G.C Azare, F.G.C Bauchi, F.G.C Kano, F.G.G.C Bakori dadai sauransu, saboda kyawun Hannah da iya acting dinta ya jawowa F.G.G.C Kazaure suna da farin jini a wajen daliban sauran makarantu, kowa ya budi baki sai ya ce a F.G.G.C Kazaure da suka zo makarantarmu akwai wata mai kyau Hannah abubakar ta iya wasa. A yau da yamma su Hannah ne suke gwaji (rahazal) din wani wasan kwaikwayo da zasu je Unity Gwaram suyi, sati mai zuwa. Kungiyar *yan Hausa fulani ne suke yi, Malam Haisam shine shugaban *yan Hausa club, shine Malamin kungiyar (club master) don kawai ya farfado da al’adun Hausa a makarantar, ya kuma hada kan Musulmai yara da manya ya zamana sun hadu a waje daya yare daya suyi raye-raye da wake-wake da wasannin kwaikwayo tare.
Hannah Abubakar itace a matsayin yarinyar mai suna Talatu cikin wasan kwakwayo, Maryam Tijjani itace a matsayin saurayin ciki mai suna Abdul. Haisam ne ya rubuta labarin wasan kwaikwayon. A yadda wasan kwaikwayon yake Maryam Tijjani (Abdul) saurayin ciki shine zaiyi tafiya kasar libiya karatu sai yayi shekaru hudu acan sannan zai dawo. Ga budurwarsa Hannah wato Talatu a cikin wasan, sunyi alkawarin zasuyi aure daman sai tafiya tazo masa yazo tafiya ya barta. Daman Haisam ya gutsuro takarda ya rubutawa kowacce abunda zata ca a wajen. Sai ta rike tana karantowa harta rike kafin ranar da zasu yi ba sai da takarda ba. A yau kusan *yan aji shida kakaf suna zaune a hall nan ne wajen da ake yin gwaji (rahazal) din, da wasu da yawa daga cikin *yan aji biyar, hudu da uku *yan kungiyar.
Maryam Tijjani (Abdul) ita ce ta taho da jakar kaya katuwa a rataye a kafadarta tazo wucewa suka hadu da Hannah (Talatu) dauke da kwarya a kanta zata je kogi debo ruwa. Abdul ya sakarwa Talatu wani lallausan murmushi na so da kauna cikin sassanyar murya Hannah (Talatu) ta ce “Abdul ba dai tafiya ba, ya ce “Tafiya zanyi Talatu nazo ne daman inyi miki sallama, sai kwaryar dake kan Talatu ta fado kasa dan gigicewa. Ta rushe da kuka. Abdul a gigice ya ajiye jakar dake hannunsa, Hannah ta fara karanto takardar da Haisam ya rubuta musu ta ce “Abdul kayi min alkawari ba zaka yi aure ba a can har sai ka dawo ka aure ni karka je can ka sami *yar larabawa ka aura ni ka manta dani. Haisam yasa tafi sai duk aka dau tafi  a hall din. Haisam ya ce “Kunyi kokari wajen yayi kyau kema Maryam Tijjani ki dage ki bata amsa dan Allah banda dariyar nan da kika saba. Maryam Tijjani ta ce “To bazan yi dariya ba, ta daga ido ta kalli Hannah (Talatu) wani kallon soyayya da Hannah take, tayi wani narai-narai da idanuwanta kai ka ce a gaban saurayinta na gaske take. Sai dariya ta kwacewa Maryam Tijjani sai kowa yasa dariya. Haisam ya ce “Gaskiya kina bata mana lokaci kullum muka zo dariya kawai kike yi saura kwana uku fa mu fita edcusion idan kinsan baza ki iya ba na sa wata. Maryam ta ce “Uncle Allah Hannace take sani dariya baka ga kallon da take yimin bafa kamar ta sami saurayinta da gaske sai kashe ido take. Haisam yayi dariya ya ce “Tsabar ta fiki iya actin kenan, shi daman wasan kwaikwayo ana son duk abunda aka baka kayi kokari ka nuna abun kamar da gaske ne, wajen kuka kayi kuka, wajen murna kayi murna. Kema kiyi mata kallo kamar kece saurayin kin hadu da budurwar da kika fi so a duniya. Wannan yana nunawa kenan Hannah ta iya actin sosai kamar da gaske. Kowa ya hau dariya ana yiwa Maryam tsiya, kema ki yi mata kallon soyayyar mana ko baki iya ba ne?
Haisam ya tashi yaje ya karbi takardar hannun Maryam ya ce “Koma gefe ki dinga kallon yadda zamu yi sosai don ki koya. Ya ce da Hannah “To kara karanto naki, Babu kunya Hannah ta narkar da idanuwanta ta kashe murya lallausa ta dubi Haisam kallo cikin ido ta ce “Abdul kayi min alkawarin ba za kayi aure ba a can har sai ka dawo ka aureni kar ka je can ka sami *yar Larabawa ka aura ni ka manta dani anan. Haisam ma yai marairaice ido ya kurawa Hannah ido kawai wannan kallo da Haisam yake yiwa Hannah ya sosa mata wani waje a zuciyarta ya ce “Talatu ba zan yi aure ba, kuma ba zan manta dake ba, ko a ina nake, ko da GANGAR JIKI NA bata tare dake ruhina yana tare da ke, soyayya baiwa ce, Hannah kina raina a koda yaushe, ina sonki Hannah. Taji gabanta ya fadi don jin yaune rana ta farko da Hannah ta san ma’anar wakar nan da take yi tayi shiru tana tunani tana kallon Yaya Haisam tasan tabbas wannan wajen a cikin wakar nan da take yi masa ya dauko kamar daga sama ta ji Yaya Haisam ya ci gaba da cewa “Ina son ki, ina son ki Hannah! Bazan manta dake ba kina raina har abada. Wannan karan ba karantowa yake a takarda ba kuma ba Talatu ya ce ba, Hannah ya ce. Sai Hannah ta fara ja da baya tana tafiya a hankali tasa hannu ta rufe idanuwanta tana murmushi. Kunya ta kama ta, gaba daya *yan kallon sun zubo mata ido suna kallon saurautar Allah, domin kowa ya san wannan kallon kadai da suke yiwa junan su ya fi karfin gwaji balle kalaman da yake fita daga bakin Haisam, ba a jikin takarda yake ba, sai kunya ta kama Hannah ta fita da gudu daga hall din. Haisam yaja wani dogon numfashi ya juya ya kalli sauran daliba ya ce “Kuje ma karasa gwajin da daddare. Ya fita ya nufi gidansa. Dalibai su ka firfito suna gulmammaki “Wannan anya Hannah da Auncle Haisam ba soyayya suke yi ba, ke kinga kallon da suke yiwa junansu Uncle Haisam kamar ya rungumeta fa. Haka dai suka shiga dakunansu kowacce ta nufi bangarenta.
Rauda ta sami Hannah a kwance kan gadonta ta dora filo a kanta babu abinda take tunanowa sai idanuwan Yaya Haisam sai kuma tsananin mamakin yadda ya rike baitukan wakar nan da take yi masa tun tana aji daya. Ta ce a ranta “Ashe ma’anar wakar nan kenan banda yarinta, nake kaikaicewa nake rera masa ko da gangar jikina bata tare da kai ruhina yana tare da kai. Har Nusaiba take cewa Hannah meye ruhi na ce ina jin larabci ne ashe ban san Hausa ba ce tsaba a lokacin. Ruhina! Ruhina!! Hannah ta fada yayin da ta sake kankame filo a kirjinta. Tsaki taji anayi a kanta ta bude ido sai taga Rauda a murtike. Tayi furgigit ta tashi zaune ta ce “Rauda har kun dawo? Rauda ta katseta ta ce “Haka za ki ce mana har mun dawo da can zamu kwana? Ko muma son wani muke yi da zamu bishi gidansa? Yaya Haisam dai yana da wacce yake so kuma an gama magana gara kowacce ta koma kauyenta ta sami wani bakauyen ta aura amma Haisam sai Ramlah. Hannah ta ce “Rauda me ya faru, wani abun aka yi? Nusaiba ta ce “Ke Rauda meye haka wasan kwaikwayo ne fa kowa yasan gwaji ne ba gaske bane, wai ke Rauda me yasa bakyason a zauna lafiya ne? Rauda tayi tsaki ta fice tana cewa “Duk gulmace-gulmacen da ake ina sane. Dan iskan kauye ya fi na birni iya iskanci da rashin mutunci.
Hannah ta fashe da kuka, tayi ta kuka kamar ranta zai fita. Nusaiba na lallashinta da kyar Hannah tayi shiru suka je suka yi alwalar magaruba. Bayan sunyi sallar isha’i sunci abinci karfe takwas dai-dai sai suka je suka kora dalibai kowacce ta fita ajinsu don yin prep din dare. Uncle Haisam ya fito daga gidansa takwas da rabu yazo ya kirawo *yan Hausa club don suzo su karasa gwajin wasan kwaikwayo da suke yi. Ta bayan wundo ya hango Rauda tsaye akan bencin Hannah tana ta gurza mata rashin mutunci har cewa take da ba’a san asalin balbela ba da sai ta ce Madina ce garinsu. Yaga Hannah a zaune tayi shiru tana hawaye, ran Nusaiba ya baci ta taso ta shigarwa Hannah kamar zasu daku da Rauda. Sai Haisam ya leko ta wundo yayi musu tsawa ya ce su fito waje yana son ganinsu.
Suna zuwa gabansa kallo daya suka yi masa suka san babu wasa yau a murtike yake kasancewar sun san bacin ransa babu kyau sai kowacce ta fara rawar jiki. Ya daka tsawa ya ce kowacce tayi kneel down bayan sun yi ne ya tambayi Nusaiba me ya faru. Nusaiba ta zaiyana masa dukkan abunda ya faru tsakanin Rauda da Hannah tun daga na yamma har na yanzu. Ya juya ya kalli Rauda ya ce “Rauda haka ne? Ta gyada kai gami da tabe baki ta ce “Haka ne kuma gaskiya na fada. Haisam ya fusata ya kaiwa Rauda mari tayi sauri ta kwanta a kasa bai sameta ba. Ta ce “Yaya Haisam yau ni zaka mara akan Hannah? Haisam yayi shiru hannayensa a cikin aljihu kansa a sunkuye a kasa. Can ya dago ya ce da Nusaiba ta tashi ta shiga aji. Ya dubi Rauda wacce ke durkushe akan gwiwarta a gabansa Rauda ta rushe da kuka. Haisam ya ce “Rauda tun ba yau ba, tun kuna aji daya na lura kin kafawa Hannah karan zuka a makarantar nan, yanzu kece kadai kika rage a cikin masu takurawa Hannah zan iya daukar kowanne mataki kuma akanki muddin baki fita harkar Hannah ba ki kiyaye, idan kuma kin ki ni zan fiki farin ciki don zaki ga abunda zan zartar a kanki. Ko Amratu kanwata *yar shekara bakwai zan iya hukunta ta muddin ta nemi takurawa Hannah wannan alkawari nayi wa Allah kuma sai na cika shi don Hannah amana ce a wajena. Kamar a mafarki Rauda take jin kalaman Yaya Haisam, tana fada a ranta “Lallai abun nasa babbane da gaske ya ke. Daga karshe ya ce ta tashi ta shiga tana sharbar kuka ta mike a fusace ta shiga aji. Ya shigo shima ajin ya kalli Hannah wacce ido yayi mata jawur don kuka ya ce Hannah ki kira sauran *yan Hausa club ku taho Hall ku sameni mu karasa Rahazal din. Cikin ladabi Hannah ta amsa masa. Ya fita ya nufi hall. Hannah ta ce “Rauda muje hall Yaya Haisam na kira. Ta dago ta harari Hannah ta ce “Bazan je ba kuma na fita daga club din ko za’a sani dole ne? Hannah zata ce wani abu Nusaiba taja hannunta ta ce “Kyaleta mu tafi mu kira sauran.
Hutu ya kusa karewa har ana shirye-shiryen fara first term exermination. Kowacce karatu take haikan. Sunyi jarabawa an basu sakamako kafin ranar hutu. Hannah ce tazo ta daya a ajinsu wannan karon, Raudah ta biyu, Nusaiba ta uku. Ranar hutu bayan anyi assembly hutu da wur-wuri kafin kowa ya fara tafiya Haisam yazo ya sami Hannah, Rauda, Nusaiba da wasu kawayensa a zazzaune akan barandar hall suna ta hira. Bayan sun gaishe shi sai ya ce “Hannah taso ga Safiyanu yazo daukarki, idan muka sauke ki a gidan uwar biyu zamu wuce dashi Dan Musa can Jahar Katsina acan yake neman aure zamu kai kayan gaisuwar surukai. Su duka suka kyalkyale da dariya. Hannah ta ce “Oh Yaya Safiyanu daman aure zai yi ko ya fada mana sunanta, ranar nida Nusaiba muka ga hotonta a motarsa muka ce budurwarsa ce ya ce wai shi ba budurwarsa bace. Nusaiba ta ce “Haka ne kuwa a bayan hoton an rubuta Dan Musa har nake cewa Dan Musa kuma sunan mace dan Musa ya ce eh haka ne sunanta.
Haisam yayi dariya, sannan ya juya ya kalli Rauda tasha kunu ta kawar da kai gefe daman tunda akayi wannan abun bata cika yiwa Hannah magana ba musamman idan taga Haisam da Hannah. Ga Uwa Uba Hannah ta kwace mata position tazo ta daya, sai take jin haushinta kamar ta kashe Hannah. Haisam ya ce “Rauda ni ba Kano zanje ba sai mun dawo daga Dan Musa don a gida ma nace kada a turomun da Mota. Auwal ne zaizo daukarki ko direba? Tace “Sai dai direba Yaya Auwal yana Maiduguri ya ce “Oh haka ne fa, to ki gaishe dasu Hajiya sai wajen jibi zanzo Kanon. Idan muka tafi yau ba damar muyi tafiyar dare dole mu kwana sannan washegari mu dawo Kazaure, wata kila in kwana a cikin gari jibi muje Kanon da Safiyanu. Rauda ta ce “Zasu ji, Allah Ya kiyaye hanya. Hannah ta kira wasu Juniors suka dauko jakunkunanta suka zuba mata a mota. Tayi wa kawayenta sallama tana zolayar su tana cewa yau itace farkon tafiya duk makarantarnan ta barsu su *yan kwantai ne. Rauda ta tabe baki ta ce “Yanzu watakila har kowa ya isa gida ke baki isa gida ba, saboda hanyar garinmu kwalta ce sambel ba kasa ba.
Hannah da Nusaiba ne kawai suka gane Raudah bakar magana ta fada, wato Hannah Bakauyiya ce kenan take nufi. Sai Hannnah tayi murmushi kawai ta tafi ta shiga mota tana dagawa su Nusaiba hannu har suka fita get.
A gidan Uwar biyu su Haisam suka sauke Hannah, Haisam ya shiga cikin gidan ya bawa Uwar biyu kudaden motarsu da wanda zasu kaiwa Mahaifin Hannah suka yi godiya yayi musu sallama ya juya ya tafi, har yaje kofar fita ya juyo ya ce “Ko yanzu zaku tafi mu aje ku a tasha. Hannah tayi sauri ta ce “Yaya sai da yamma zamu tafi ina so inje gidajen kawayena a nan cikin gari, yayi murmushi ya ce “Wato akuyar daure ta sami sake, su Hannah an iya yawo ko? Su duka suka yi dariya sannan ya fita. Da misalin karfe biyar uwar biyu da Hannah suka isa Babban Mutum, suka je suka iske gida a hargitse anyi tashin hankali. Malam Habu Mahaifin Hannah kuka yake wiwi. Cikin rikici da rudani Hannah ke tambayar meya faru Babanta yake kuka? Iya Abu ta tuntsire da dariya tayi buda da shewa ta ce “Tambayi Ubanki, karshen tukatiki tik, yau Allah Ya nuna mana gaskiya. Hankalin Hannah da Uwar biyu ya sake tashi sosai, suna so suji me Iya Abu take nufi da wannan habaici nata. Malam Habu ya sharbe hawaye da babbar riga ya ce “Muje zaure in fada muku abunda ya faru. Da yake daman a tsakar suka iske su suka je zaure suka zazzauna Malam Habu ya nisa gami da langabar dakai ya ce “Idan ka haifa dole a jawo maka, daman ance dan kuka shi ke jawa Uwarsa zagi. Uwar biyu da Hannah su dai sun kagu suji abunda ke faruwa ya ce “Yanzun nan babu dadewa watakila kun hadu da wata bakar mota katuwa a hanyar shigowa garin nan, wata futsararriyar yarinya ce tazo ta cimin mutunci a kofar gidan nan har ta tara mun mutane. Hannah ta ce “Wace ce Baba? Cikin rudani da fargaba ta tambaya ya ce “Farko da tazo sai ta tsaya ta karemun kallo a wulakance sannan tace naji kunya wallahi. Daman yarinyar ma *yar talakawa ce, yake bata mun lokaci a kanta. To Baba bari in fada maka ka jawa yarka Hannah kunne ta kiyayi mijina idan ba haka ba ni zan zamo ajalinta domin zan iya kashe duk yarinyar da zata rabani da Haisam abun sona. Kuma ka cire *yarka daga makarantar nan domin idan bata bar makarantar ba Haisam ba zai bar makarantar ba ya rabu da ita, muddin Hanna ta sake komawa makarantar to kuwa har makarantar zan bita in zartar da abun da na yi niyya. Ba tana takamar ita kyakkyawa bace to zan kwara mata wani abu a fuska (acid) fuskar ta sale ta kwakkwabe har makarantar zan tarar da ita in yaso sai inga fuskar da zai sota. Don soyayya Hannah take yi da mijina ba karatu ba. Har sakamakon jarabawar  kanwata yake dauka ya bata tazo ta daya a ajinsu. To na gaji, wannan shine lokaci na karshe da na bawa Hannah idan taki ji ta koma makarantar to wallahi ta kuka da kanta. Malam Habu ya sharbe hawaye yaci gaba da cewa “Da wata *yar makaranta tana sanye da kayan makaranta irin naki *Yar Baba itama tana taya ta suka yimin tas, Iya Abu na ihu tana dariya tana cewa daman ta sani ba tun yau ba Hanne karuwanci aka kaita tayi ba makaranta ba yanzu gari duk ya dauka maganar ake yi don a gaban mutane aka yi haka. Ta ce Hannah ta ci sa’a da ban sameta ba da sai ta faffalla miki mari sannan suka shiga mota suka tafi. Hannah bata iya cewa komai ba sai ta sunkuyar da kai kasa tana kuka Malam Habu ma kukan yake Uwar biyu ta matse hawaye ta ce “Kuyi shiru, ku daina kuka wannan duk abune na shirme da karya ita wannan yarinyar data zo ina tunanin matar da Malam Haisam zai aura ce take ganin son Hannah yake alhali kowa yasan Haisam a matsayin Yaya koma ince Uba yake a wajen Hannah tun tana karama fa inah, ai zancen so ma bai taso ba. Hannah karatu take a makaranta babu wata soyayya daga wannan hutun ma baza su sake dawowa ba har sai sun gama makarantar ma kwata-kwata, saura wata bakwai su gama.
Malam Habu ya zabura ya ce, “Wacce komawa ai Hanne tazo kenan baza ta koma ba ina wani zancen saura wata bakwai Hanne ta gama, ai ko saura kwana bakwai ne Hanne ta gama karatu bayan a gaban mutane aka ce ba karatu take yi a makarantar ba soyayya take yi sannan in bar *yata ta koma ai sai a dinga cewa tana can tana iskanci har wata bakwai ba ta komo gida hutu ba, ni dai abunda zance muku Uwar biyu ke da wannan yaro Haisam Allah Yayi muku albarka amma Hanne ba zata sake komawa ba karatun ya isa haka duk kawayenta harma kannanta duk sunyi aure gara itama in hadata da wani a dangi tayi aurenta baki alaikum kafin a kone mata fuska. Daman abunda muke ji a redio gaskiya ne ace an fesawa wani ko wata wani ruwa a fuska ta kwakkwabo gaske ne to ba zai faru akan Hanne ba. Karatun da tayi na baya ya isa nagode madalla. Cikin rudewa Uwar biyu ta ce “Haba Malam Habu yaya zaka yi mana haka? Baka kyauta masa ba yarinyar nan duk zance take Haisam ba zai barta taje gurin Hannah ba balle tayi mata wani abu. Bama a barin kowa yaga dalibai in ba ranar visiting ba dokar makaranta ce.
Malam Habu ya mike ya shiga gida yana cewa “Nifa na gama maganata Uwar biyu kiyi hakuri ki bar maganar komawar Hanne makaranta. Ai ko karan hauka ne ya cije ni ba zan bar *yata taje inda za’a hallakata ba ina Hanne ina kishi da wadannan gogaggun *yan birni masu kudi? Tunda tana ganin mijinta son Hanne ya ke ai sai a hakura da taimakon, na baya ma Allah Ya saka. Ya shige ya bar Hannah tana matse hawayen dake idanuwanta da wani farin hankici dake hannunta ta ce da Uwar biyu, “Kyale shi ya tsorata ne kafin hutu ya kare zai yadda idan na wayar masa dakai a hankali na lallabashi sai dai idan hutu ya rage sati guda kizo don muji mai zai ce in yaki yadda sai Yaya Haisam yazo ko kuma ya turo Principal idan kuma yaki yarda na shiga uku karshen karatuna ya zo. Hannah ta rushe da kuka, Uwar biyu tace “Yadda za’ayi shine Haisam zan turo yazo garin nan Mahaifinki ya kalli kwayar idonsa ya ce ya hanaki ki koma makaranta, Haisam zaizo da kansa. A haka Hannan da Uwar biyu suka yi sallama. Hannah tayi-tayi da Uwar biyu ta shigo cikin gida ta huta sannan ta tafi Uwar biyu ta ce ba zata shiga ba, ina zata iya shigowa wajen Iya Abu masifaffiyar matar da zata iya kashe mutum ma don rashin imani. Hannah ta raka ta har tasha ta shiga mota sannan hannah ta dawo gida.
Tofa Malam Habu?Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE